Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nasa ya baiyana kan fuskarsa ba. Saima Murmushi da yayi da cewa kamanni kawai mukayi dashi. Amma maganar hali kowa da nasa.... Harararsa dai taqara yi da cewa indai hali na gari ne kasan dai ya fika Yace ai haka Allah yake bayinsa kiga wani yafi wani..... Bu'dar bakinta sai cewa tayi dama kai Allah ya 'dauke ya barni da Ramadan😬..... Dariyar takaici ce ta kwacema Junior yayi Sosai yana kallan kwayar idan da aika mata da wani shu'umin kallo Yace ai dake ba yanda kika iya da ikwan Allah sai kiyi hakuri da rashin masoyinki Kuma shi yasan me yake nufu daya 'daukeshi yabarki dani 'dan iskan naki Yanxu dai ba wannan ba. tunda kukan ya 'dauke. Nasamu nutsuwa ka'dan..... Hau in dubaki pls Wlhi tun jiya ban samu bacci cikin hankalina ba dan wannan ciwan nakin Pls my baby tashi kinji yi hakuri👏🏻... Bayanda ta'iya dashi haka takwanta ya fara mata scanning 'din tana binshi da harara dan gani take da gaiya yake juya mata abun scanning 'din Batasan shi damuwarsa yaga meyasa mishi ita agaba bane...😬 Yana gamawa ya aika mata da muguwar harara Bata kulasa ba sanda taxauna a kan kujera tamayar mai da tata hararar kana Tace kaga yaro. yanxu dai kayimin aiko. saika gayamin matsalata kaban maganin naqara gaba.... Karki qara cemin yaro dan yanxu nadoshi 26 years Ta6e baki tayi cikin raini Tace toh ina ruwana dan kadoshi 26 Agirme dai kasan ba girmata kayi ba. Ko makawo ya shafamu yasan na girme maka nesa ba kusa ba. Kaga ni ba wannan ba kagayamin matsalata dan gabana ya fara fa'duwa😳..... Badai ciki bane dani ko Kasan ko cikin Su KAULEET banji Komai ba sai kwa'dayi da..... Saurin katseta yayi cikin takaici Yace idan bakimin shuru ba. Wlhi saina tsinka miki mari... Kona tambayeki ki gayamin ne.. Yarinya sai surutun tsiya kika ajiye... Ya qarashe maganar da jan tsaki Shuru SAILUBAH tayi tana kallansa tana tunani aranta meyasa Junior ya gama rainata ne haka..... Tana cikin tunaninne ya katseta da cewa ya akayi kika kamu da cutar appendix Appendix😳.... Ta maimaita da waro ido tare da tashi kana tayi narai narai da ido😟 Yanxu yankani xa'ayi acire ko😳 Wayyo ni SAILUBAH... Kaban amsa katsaya kana kallona...... Murmushi yayi Yace eh yankaki xanyi kuma gobe in Allah ya kaimu..... Da kuka tafitta daga office din Murmushi yayi da girgixa kansa ya 'dauki laptop dinsa da wayoyinsa da kulle office din Lokacin daya fito hartaja motarta ya 'dagama maryam hannu alamar sai Allah ya kaimu. Ta gya'da mishi kai da Murmushi SAILUBAH ko saka Kakah da Innah tayi agaba tana musu kuka wai gobe xa'a cire mata appendix Lallashinta suka dinga yi abin tausayi abin dariya..... KHAULEET Tace kiyi shuru Momy..... KHAULAT Tace wai Kullun ne sai kinyi kuka Momy Shuru SAILUBAH tayi musu Dan Sosai tatsorata da ciwan da kuma fargabar xa'a farke mata ciki 😳 Shiko Junior baibi takanta ba. Sai washe gari daya shiga gidan dankai Su KHAULAT skull Ya kalleta ka'dan ganin tana Cikin damuwa sai yayi Murmushi dasan ya ta6ota Yace baki iya gaisuwa bane.... Gallamai harara tayi batare datace mai Komai ba...... Khairat CE tashigo tana cewa LA Ya Junior kawosu na kaisu. Yace taki skull 'din fah Murmushi da cewa ai muna da walimar skull 'din yau kuma mah sai anjima. Yace haka nefah Toh sai kisa dareba ya kaiku yanxu Maza... Tace toh Haka tagama hannunsu sukabar falan Junior ya dawo da kallansa kan SAILUBAH Yace karfah kisa wani damuwa aranki danna shirya wasu dabaru daxan miki wanda xaisa baxa kiji xafin komai ba Da sauri tasaki fuskarta Tace Allah da gaske😀..... Murmushi yayi Yace Allah my baby Tace toh yanxu ya Xa'ayi Yace yanda xa'ayin kenan Kishirya keda Kakah ko Innah muje yanxu dan ayi da wuri. Kinga yanxu 7:30am kafin 9:00 nasan ankagama komai... Tace anamin xan dawo gida Yace aa Tace xan kwana kenan 😳 Yace bama kwana 'daya ba kuma ba biyu ba. Sannan ba uku ba Tace taf kace aikin babba ne Kuma xansha jinya Murmushi yayi yana danna waya batare da yace mata Komai ba Kiran XEE tayi tagaya mata ita da FAWAS.... ****** Dake aikinsu ne Sam bai samu matsala ba Yayi mata aikin cikin sa'a da nasara..... Yau satinta 'daya a sibitin D'akin da take tamkar a 'dakinta take XEE CE da HAMEEDA suke mata sannu XEE Tace gaskiya SAILUBAH Junior yana baki kulawa sosai HAMEEDA Tace wlhi kuwa kamar RAMADAN... Murmushi SAILUBAH tayi Tace Karki ha'dashi da RAMADAN HAMEEDA danba halinsu 'daya ba Junior fa bashida kunya idansa atsaye yake. Duk duniya ba wacce ya raina kamarni. Kunafah kallo Haka xai qaraci min rashin kunyarsa ina kallansa in kasa mai komai...... Shigowarsa ne yasata yin shuru tana harararsa dan haushinsa takeji sosai saboda yayi mata qarya akan baxataji Komai ba game da aikin da yayi mata. Xama yayi kusa da ita Yace har yanxu baxa'a dena fushin dani bane Kawar da fuskar tata tayi daga kansa tare da qara 'daure fuskarta.... Kumawa yayi inda tajuya fuskar tata Yace kitemaken kidena wannan fushin dani dan ba'abinda yake tayarmin da hankali kamar shi Kallansa tayi ka'dan Tace ina dabarun naka suke Murmushi yayi Yana qarema fuskarta kallo Yace duk nayi miki Su Tace toh naji xaman ya isheni haka pls asallameni naqara gaba Harararta yayi Yace bayanxu ba Da sauri Tace yaufah satina 'daya Kuma nasamu lafiya Akan me xaisa na xauna Ta6e baki yayi Yace nace baxa'a sallameki yanxu ba saikin qara sati 'daya... Ahakan mah in bai mun ba saina qara miki kwanaki Yafa'da hakan yana me xuba mata abinci a plate Harararsa tayi Tace Wlhi gobe xan tafi abina dan baxan xauna in qara iban kwanaki haka ba Murmushi yayi Yace taurin kanki yanada yawa my baby Amma baxan hanakin ba Allah ya kaimu goben sai kije in gani..... xata qara magana ya katseta da cigaba da cewa kinga malama ni ba wannan bane agabana gyara nabaki dan kinfara shigar lokacin wasu. Yaqarashe da kallan abincin dake hannunsa Mugun kallo tawurga mishi da cewa baxanci ba.... Yace idan har bakici yanxu ba aikinki warwarewa xaiyi Murmushi tayi ganin xai mata wayo.... Tace shekaran jiya bai warware ba jiya bai warware ba sai yau 'Daure fuska yayi kamar gaske Yace Allah idan bakici ba ina tabbatar miki yau Xaki kwana da cigawan ciki Ya qarashe da kallan XEE dayi mata nuni akan tasa baki Murmushi tayi Tace kici SAILUBAH dan aikinsa ne tunda yace kici kici kawai mudai lafiyarki muke nema Xanci Amma da kaina Kiyi hakuri kibari in baki pls Wai da raina da lafiyata saika dinga maidani baby Eh dan ni har yanxu baki wucce wannan wajan aguna ba Yaqarashe da matsawa kusa da ita Sosai ya kafeta da ido badan tasoba tafara kar6a tana ciki shiko yana bin kwayar idanta da kallo Wanda hakan ke qara narkar da zuciyarta Jitake kamar tashige jikinsa dan qamshinsa ya isheta Gawani shegen sweet dayake tsotsa Sosai takejin San tajishi itama abakinta dan qamshin ya gauraye bakinsa... Murmushi yayi da kwantar da murya qasa-qasa yanda ita kawai xataji maixaice mata Yace kwa'dayayyiya baxan sam miki ba Ashagwa6e Tace Amma Kasan qamshin yana damuna ko Murmushi ya qarayi da cewa in sammiki kenan Da sauri ta'daga mishi kai Sosai ya qurama bakinta ido da ciro sweet 'din daga bakinsa yasaka mata abaki........ Jan numfashi XEE tayi tana rayawa aranta anyi 'dan iska anan😂. Sai burkita mata 'Yar Uwa kuma qawa yake gashi ba 'digwan kunya a idanshi HAMEEDA ko burgeta yayi saibinsu take da Murmushi dan Allah yayi HAMEEDA da San Luv Ahaka FAWAS da KHAMIS suka shigo Sanda gabansu Yafa'di tunaninsu Senior RAMADAN ne ya dawo.... KHAMIS ya daki fa'darsa yana cewa kashiga da yawa fah Ba kunya Yace idan ba hakan CE takasance ba baxata bani ha'dinkai bah FAWAS Yace hmm bi asannu dai dan Auntynmu Ya qarashe da kallan SAILUBAH yana mai cigaba da cewa am sorry Aunty LUUVAH ya jikin dai Tace da Sauqi FAWAS kace ya sallameni Murmushi yayi da maida kallansa ga Junior Wanda ya dage sai bata abinci yake. Kuma kallo 'daya xaka mata Kasan aladole take cin abincin..... Yace kaga malam sallamemu mutafi KHAMIS Yace haba kaduba fa bata gama warwarewa ba Yace ai ita taji ajikinta normal take ko Aunty LUUVAH Murmushi tayi Tace Wlhi ba abinda baxan iyaba FAWAS kaika'dai ne kake fahimtata Amma KHAMIS bakin shi 'daya yake da wannan.... Taqarashe da kallan junior D'aga mata gira yayi Yace banda sunah ko. Tace bansani bah......... *** **** Yanda tasashi agaba da mita ita ya sallameta kotatafi abinta Shiyasashi sallamarta tadawo gida Wanda hakan yabashi damar cusa mata manufarsa cikin hikima da aiki da hankali Saiya fake da wai yana bata kulawa ne dan rashin lafiyar tata Su Kakah dai kallansu suke kawai Yanxu kijisu suna fa'da anjima kuma kijisu Suna dariya. Sosai suka gano son SAILUBAH Junior yake Wanda hakan yayi musu da'di Sosai *Bayan wasu Lokuta* Junior fa ya shagwa6a SAILUBAH Sosai dan indai yana waje tana waje bawanta yake xama dan bata kulawa A online ko tun tana jamishi aji hardai tabada kai yadinga 6ata mata tunaninta Soyayya Sosai sukeyi... Saidai baita6a kiranta ba Tunaninsa yana kiranta xata gane shi Shiyasa yaqi kiranta Kuma yaqi yarda tasan Waye shi da inda yake Haka itama Sam bata ta6a kiransa ba Dan aganinta xai rainata Yanda yake 6ata tunaninta haka itama take 6ata tunaninsa Sai su'dauki lokaci metsawo Suna chating batare dasun damu ba Amma duk da haka idan suka ha'du baya 'daukar raininta Toh dama ita batasan dashi take chating ba Shiyasa wani xubin saiyata kallanta yana Murmushi Nashi salan kenan (Allah yaji qan Senior Ramadan😭) ***** Sam SAILUBAH bata kula samari koka'dan Dan abin ya qara maimaita kansa. Wani baxawarinta yaxo gareta attajiri dashi yayi ko rashin sa'a dan akan idan Junior yaxo. Ko cikakkiyar gaisuwa basuyi ba Junior ya 6ata musu Komai ta wajan wasa da hankalin SAILUBAH Haka shima ya ficce Sam batasan ya akayi ba (Allah Sarki😰 Karki damu SAILUBAH xamu gyara tuninsa) Ganin hakan yasa Tace tabar kula samari kenan har abada....... ********** Yau takama lahadi ranar Hutu ga 'Yan boko Ruwa ake xabgawa shiyasa duk tauraran nawa Suna nad'e a gado XEE tana kwance agadanta cikinta ya dameta da motsi tajuyo da kallanta ga 'dan mijin nata Tace gobe ne birthday nasu KHAULAT ko Yace eh........ Tashi tayi agigice saboda wani naushi da cikin nata yayi mata KHAMIS wanda yake tura saqo a laptop ya kalleta ka'dan da cewa ina fatan dai lafiya Tace naushi na yayi Gaskiya nagaji Allah katemakeni na aihu yau na huta..... Murmushi KHAMIS yayi Yace Aunty XEE kenan Tace yau kuma katuna RAMADAN ne Yace Wlhi kuwa Banda haka kinsan kina watan takwas ina ke ina aihuwa yau Tace ai ana haifar bakwaini Sai kuma aka gaya miki ana haifar takwasni Murmushi tayi da cewa baka sani ba..... Waro KHAMIS yayi 😳 da cewa aa fah😳. Ina addu'ar Allah ya kaiki watan tara kafin Ki haifamin Babyna Tace oho dan ba..... Katse yayi wajan saurin cewa gaya min wani abu pls mubar wannan haka Murmushi tayi da aikamai hararar wasa Tace toh zanci farfesun ganda... Kallanta yayi da tashi da Murmushi akan fuskarsa Yace muguwa kawai Kinsan Dady bayaci haka Momy haka ni Kuma Kinga ana ruwa kawai danki tadamin da hankali shine xakice farfesun ganda xakici ko D'agamai kai tayi da shagwa6e fuska Tace Allah da gaske nake Yace ko Tace eh Yace toh albishirinki Tace goro Yace 'daxo daxan dawo gida naga gandar me kyau gun wani mutum haka kawai naji araina inasan in siya Dan haka nasiya dana dawo nabama Momy nace tayi farfesu dashi Batayi mamaki ba dan tayi tunanin koke kikeso Dan haka yanxu bara inje in kar6o miki. Kinga muguntarki takoma kanki ko😀.... Turo baki XEE tayi Tace toh baxanci bama nafasa Ta6e baki yayi Yace toh saime😏 dama aina mugunta ne Haka yakoma yaci gaba da aikinsa itako tasamai ido lokaci lokaci tana aika masa da hararar wasa Shiko binta yake da murmushin mugunta irin burinta dai bai cika innan ba. Na bashi wahala..... FAWAS ko futuna yakeji musamman yanda yakejin yanda ake sheqa ruwa dan haka yana maqale da Matarsa yana lalla6ata dan ahannu yake Saura ka'dan Komai ya wanxo sukaji kukan Ahmad Awahale Yace my boy menene Yace Dady kabu'de xan 'dauki chokulet 'dina ne Yace ina na 'dakin Momy Yace ya qare. HAMEEDA taxare jikinta daga nasa tabu'de wata durowa ta'dauko mishi kana ta gyara kanta da bu'de qofar Tace gashi..... Kallan hannunta yayi yana yatsina fuska da cewa toh ina Dadyn nawa Tace xaka kar6a ne ko xaka tsaya yimin surutu..... Kar6a yayi yana cewa toh Momy kimatsamin naganshi mana...... FAWAS najin haka yayi saurin gyara kansa.... HAMEEDA ko Murmushi tayi da matsamai ya shigeta...... aiko yana Ganinsa ya 'dane gadan yana cewa Dady tashi muyi wasa..... A wahale FAWAS Yace banajin da'di my son kaje gun momyna kuyi Murmushi yayi Yace aa naka bake so.... Duk yanda yaso da yayi masa wayo 'ki Ahmed yayi Ba yanda FAWAS ya iya dashi dan Sosai 'dan nasa yasamai gaba haka yasauka ya biyemai sukadinga buga boll HAMEEDA na kallansu tana bin mijin nata da murmushin mugunta Shiko yana maida mata dana xaki gane kuranki..... Mutumin nawa ko yana kwance shima a nalla'de kan gadansa yana tunanin mutuniyar tasa Ganinta online yasa yafara bata kalamai kamar haka ```Nayi tunanin baxaki hau yanxu bah``` SAILUBAH dake kwance afalo tana chatin da wata qawarsu taga shigowa nashi sakwan Dama tagaji da hirar da ita dan haka tayi saurin kar6ar sakwan nasa da bashi amsa kamar haka..... ```Na haune ko Allah xaisa naganka akai``` ``` hmm kinada wayo my Luuuuu. nasan badanni aka hau ba. karkiyi wani alaye``` ```Xanso kayarda da abinda nace``` ```Na yarda``` ```Yauwa dama ina so yau nasan kai Waye. Ina San jin muryarka. Ina San ganinka.``` ````Da gaske kike babyna``` ```wlhi da gaske. Kuma in ban ganka yau ba. ka tabbatar nadena kulaka``` ```farkoma awane gari kake kuma wacce unguwa``` Shuru Junior yayi Can ya fara bata amsa da cewa a kano yake a unguwar Fage dayi mata kwatancan nayin da yake.... Da mamaki SAILUBAH Tatashi tana bashi amsa cike da al'ajabi ```Toh ai unguwarmu 'daya``` ```Gayamin awane gida kake``` Murmushi Junior yayi kafin yaja numfasa..... ```Kinga masoyiyata kar kimin qarya. Taya xa'ayi muna layi 'daya nakasa ganeki``` Afusace Tace..... ```kaga Malam kafitoh k'ofar gidanku nima in fitoh kaga saimu tabbatar da gaskiyar xan xanmu``` ```Ana ruwa a uguwarmu sosai😳. Dan haka kibari a'dauke``` ```Ai ruwan ya tsagaita yanxu. dan haka kafitoh nima ganinan``` Toh Yace mata tare da tashi yana gyara kansa da rayawa aransa yau xai cika burinsa na farko. SAILUBAH ko dake agyaranta take dan haka gyalanta kawai ta'dauka tafitoh waje A'kofar gidan nasu tatsaya tana tana wulla ido ta'ina masoyin nata xai 6ullo Junior ne yafitoh da shigar sanyi a jikinsa kallo 'daya xaka masa yabaka sha'awa dan yayi kyau Sosai Suna ha'da ido ta hararare shi Sanda ya qaraso gareta Yace wow kinga inda kikayi kyau kuwa Tace nagode Yace Wlcm Garin bai baki sha'awa ba. Kiduba yanda yayi wani lublub dashi. Sai qamshin qasa ne ketashi Tace eh yayi kyau Sosai pls karka cikani da surutu Yace to fushin namiye Tace kasan ka 6atani da bani abinci shine yau naqi ganinka ko Murmushi yayi da cewa ke soyayya nakeyi yau Kinsan in ina yinda manta kowa da Komai nakeyi..... Ya qarashe maganar yana mai kallan saman layin da qasan nayin. Kallo 'daya xakamai Kasan wani abu yake nemah..... Tsaki SAILUBAH tajah cikin 6acin rai Tace yanxu har soyayyarka tafini muhimmanci... Ka tuna fah ni amanace agareka... Wai dan ke amanace agareni sai karna fifita soyayyata saboda ke Inaaa baxai yuhu ba Inasanta over Wlhi akanta xan'iya barin kowa da Komai Xan iya barin Komai Ina MASEEFAR SONTA Gwarama kicire wannan dan tayimin illa da yawa Ki dai yi hakuri kawai naganta yanxu saina baki ko my baby Ya qarashe da sakar mata shu'umin Murmushi Itako mugun kallo ta wurga mishi Tace bana so Wlhi In saika ganta xaka ban abincin kabarshi nagode Yace hmmm Xama kici ne Am dan Allah ban shawara Kinsan ban ta6a ganinta ba Kawai dai muna catin ne Kuma wani iko na Allah ahakan tatafiyar da xuciyata Ina Santa da yawa my baby pls ban shawara yanxu idan tafitoh mexance mata Dariya SAILUBAH tayi Tace hmm Lalle nemah Kana nufin duk wannan xagewar da kake akanta baka Santa ba Yace Wlhi ko waya bamu ta6a yiba Tace toh ya'akayi kasamu Num nata Yace ina tunanin KHAULAT CE ko Khairat tsakaninsu wata taha'damin as love Kinsan Suna 'dauka Tace Lalle sunha'daka da wahala Kuma baka ta6a ganinta ko'a dp nata bah Yace bata SA photo Sam Tace kace taha'du........ Kanya bata amsa wata 'yar makwaftansu tafito dana wullah ido da alama yaran aike take nemah..... Aiko da sauri junior ya kuma bayan SAILUBAH yana salati qasa qasa yake cewa nashiga uku my baby kodai itace wannan Kut gaskiya mummunace dan Allah da'da kareni karta 'dauka nine😳 Da sauri SAILUBAH Tace bangane ba kana nufin kunyi da ita Xaku ha'du yanxu ne Eh mana. Wai tace alayi 'daya muke da ita. Shine Tace nafitoh yanxu itama gatanan fitowa Juyowa SAILUBAH tayi tana kallansa gabanta na fa'duwa tafara kiran numbar da suke catin da saurayin nata Aiko sai gashi taji ringing a ajjihunsa Da kanta tasa hannu tajiro wayan tana dubawa taga sabowar waya dal Kuma ba wacce tasanshi da ita bace Ga Num nata na yawo akai ahankali ta kallesa Tace wannan wayar fah ta6e baki yayi da cewa baki sanni da itaba Tace ina wacce nasankan da ita Yace tana gida mana Yafa'da yana mai kar6ar wayan dacigaba da cewa Kinga kuma tana kira.... Ya dace na amsa daji muryata yanxu Shuru tamai tana qare mai kallo tundaga sama har qasa Kana Tace nice wacce kake fa'da junior😰..... Kamar gaske ya waro ido 😳 yana cewa kut keeee Amma kin bala'in rainani Kirasa Wanda xaki yaudara saini Kinsan lokacin dana 6ata akanki Hawaye ne ya xuboma SAILUBAH Tace Junior kana cutar dani Nice na yaudareka ko kai Afusace Yace saiki gayamin ta'inda na yaudareki Ina da Num naki akan wannan wayanne Ko kina saka hoto a dp naki ne daxan gane kece.. Tace toh nima ai bakasa hotanka a dp kuma bada aynihin Num naka kake chatin dani ba Mugu kawai. Wlhi Allah saiya sakamin wasa da hankalin da kakemin Kinga malama. kar kiyi wani alaye dama can sonah kikeyi shine yasaki yaudarata tawannan Hanyar Toh bari kiji Wlhi banta6a yaudarar kowa ba. Haka nima bamai yaudarata Wlhi tallahi saikin Aureni Afusace tanunashi da yatsa Tace Wlhi baxan Aureka ba Bana sanka bana sanka To dama angaya miki nima sanki nake Maixanyi dake tsohuwa dake Kawai Xan aureki ne dan in nuna miki ba'a yaudarata Da kuka wiwi tashige gida..... Murmushi yayi yabi bayanta Ajikin Innah taxube tana cigaba da kukanta Innah Tace toh yanxu kuma menene Tace kuduba Junior Innah sai wasa yake da hankalina ashe shine wanda nake CE muku yana damuna a waya da sakwanni....... Katseta yayi da cewa qarya Tace Innah ita take damuna Yanxu kukan da takeyi 'daya ne Shine wai dan nace baxan Aureta ba Toh kiyi shuru Xan aureki danba qaramin illa kikamin wajan yaudarata da soyayyarki ba Kakah saiku saida xan Aureta Ku tattauna da Dady cewa minshirya kammu muna San juna da Aure Saidai kuja kunnanta ba ita ba wani 'da namiji Murmushi Su Kakah sukayi atare sukace Madallah Toke kidena kuka tunda Yace xai Aureki mana.... Yauma xamu tattauna da Dadyn naku akan hakan....... Wani baqin Cikine ya tokari SAILUBAH a qirji. Watoh junior ya tabbata 'dan iska kuma makiri maqaryaci A gabanta yanxu ya sharara mata qarya bayan raina mata hankalin da yayi Tayi mamakin yanda takasa cewa Komai harsuka qarashi xancikan nasu suka barta dashi agun Yana ganin Su innan sun barshi da ita yayi saurin matsowa gareta yana mata murmushin mugunta Yace am so sorry my Baby ina tare da sanki araina Sosai nake sanki... Toni bana sanka Junior Yace meyasa Saboda kai 'dan iska ne Kuma mugu Mara tausayi Daka kasance RAMADAN dana soka... Kama fuskarta yayi Yana shafawa cikin wani salo na Luv Yace kisoni Ki huta my baby dan xan baki duk wani farinci da kike nima arayuwarki Wlhi in kikaqi tsaida tunaninki akaina ina tabbatar miki ni ina dai-dai da in gyara miki shi Ina sanki ina sanki ina sanki Kuma inada mummunan kishi akanki Dan haka Ki kiyaye.... Yana kaiwa nan yasakar mata kiss da sakin fuskar tata ya ficce daga falan a bakin get yaci karo da Khairat dasu KAULEET a hannunta Aiko suka cukukuyeshi Yace kun gama mah Momy 6arna ko Khairat Tace aiko Ya Junior bakaga 6arnar dako sukayi ba..... Yace ai daga ganin wannan dawowar bata shiri bace KHAULAT Tace Dady gobe ne birthday ko 😀 Murmushi yayi Yace eh.... Khairat Tace yanxuma xanje kar6o musu wasu kayansu ne gun Aunty xema Yace dare yayi banaso kije ko ina yanxu Tace yamma ne fah Ya Junior.... Harara ya gallamata da cewa barnan.. Aiko ba shiri tayi ciki Shiko yaja mutanan nasa sukayi gidansu.. Shigowar Khairat ne yasa SAILUBAH dawowa daga duniyar data fa'da Khairat na qara gaisheta Amma Sam bata San tanayi bah. Kwakwalwarta tatsaya cak wajan tuno xancikan da Junior yayi mata.... Toh Aunty nina tafi tunda kinqi cemin Komai Khairat Tace da SAILUBAH hakan cikin gajiyawa.... A 'dan furgice takalleta da cewa Sowie mashiga wani yanayi ne Tace dama Momy ce tace inkin gama hutawa kixo kiga yanda aka shirya Komai Tace OK..... Har kwanciyar bacci SAILUBAH bata dena jin xancikan Junior suna mata kurwa a kunne bah Dan haka sai takasa hakuri sanda takira XEE tagaya mata tana kuka XEE dai lalla6ata tadingayi dan tada'de tana mamakin me Junior yake jira dahar ya'ibi lokaci me tsawo haka bai nuna mata manufar tasa ba...... *Kishin Maza* Haka ko akayi Washe gari takama birthday 'dinsu KAULEET da KHAULAT Da misalin 2:30pm wajan shaqatawar ya cika Sosai Amma ba irin wannan cikar ta hausawa ba Dan kowa yana teburinsa da abun ta6awarsa Sosai wajan ya qawatu 'Yan mata da samari sunfi cika gun Harda manya manyan attajirai wa'yanda sukaje gun dan kawai su gwa'da sa'arsu agun SAILUBAH ko xasu dace Sai qawayanta da 'Yan Uwa da abokanayan arxiqi XEE da HAMEEDA sune ahannun damanta KAULEET da KHAULAT da AHMAD da wasu yaraku ne xagaye awani ha'daddan gu Wanda yake fidda wutta Ba qarya mutane sunga birthday 'din yara 'Yan gata Sosai jama'ar gun shagalin ya burgesu gefe guda kuma Suna yagar kaxa da kora drink abin sai wanda yagani Ankashe ku'di Sosai bana wasa bah Dan wannan birthday ya bambanta da Wanda jama'a dadama suka sani Toh😳 Al'amarin ya faru ne lokacin da wani matashin saurayi Wanda baxai wucce shekara talatin da biyu ba. Sai yajah kujerar da take fuskantar SAILUBAH ya xauna yana aika mata da kallan Luv... Tunkan yayi mata magana Junior ya kalli FAWAS Yace wancan yashiga gonata fah😌 KHAMIS Yace toh miye... Ka share kawai dan Kasan Auntyn tamu ba kulasa xatayi bah Yace da sake fah😳 Kaduba yanda suke fesin 'din juna kamar wasu tsofaffin masoya Murmushi FAWAS yayi da cewa karfa kishi ya tona asirinka yau.... da sauri Yace na yaushe kuma.... Bayan jiya tafaru taqare.... Kan FAWAS ya qara yin wata magana tuni junior yatashi ya nufi inda SAILUBAH take..... [8:38AM, 11/03/2017] R🇦HAⓂ🇦T Nalele: Daga yanayin yanda yake tafiyar tasa kaxasan yanajin iskanci Sai tafiyar tashi tabada wani salo da ki'dan da yake tashi Duk illahirin matan da maxan dake gun idansu komawa yayi gareshi Dan sak komansa komawa yayi irin na 'yan iskan nigoginnan Ga madarar kyansa da take 'daukar hankalin duk wanda yayi gigin yimishi kallo 'daya KHAMIS ya kalli FAWAS Yace gaskiya junior 'dan iska ne kaduba yanda yake tafiya FAWAS yayi Murmushi Yace hmm kakula mana. kishi ne ya kusan ceshi da yawa..... Saurayin ko qara kafe SAILUBAH yayi da ido Yace ina sanki SAILUBAH Murmushi tayi da cemai dan Allah kayi hakuri malam Da sadakina ahannu Ma'ana wani ya rigaka Yace toh ai sadaki ba Aure bane..... Koh.... Junior yafa'di hakan yana mai qarasowa gun da dafa table 'din gaban nasu.... Kallo 'daya SAILUBAH tayi masa gabanta ya tsinke ya fa'di dan ganin yanda ya sauya kamanni Haba malam. Waye kai da xaka shiga xancanmu batare da neman ixini ba Saurayin yace da Junior haka Murmushi yayi Yace sanin koni Waye ba abu bane me mahimmanci agareka Fa'dar abinda nakeso shine me mahimmanci agareka tace kayi hakuri da sadakinta ahannu Bata Barka haka ba sanda taqara maka dacewa ma'ana wani ya rigaka Amma dake kune irin 'Yan iskan nan wa'yanda basu'daukar fa'dakarwar muslinci abakin Komai shine kike cewa ai sadaki ba Aure bane ko.... Toh ya'isa haka.... Ka bari.... Dan ita 'din bata kowa bace face ta SADEEQ...... Qaddarar Auranta akansa

Chapter 28 of 33