Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Alhaji Aminu Wannan wane irin hatsabibanci ne..... Cikin sanyin rai yace maganar auransu ya ummi akwai matsala ne Tace basaika ganar dasu axahiri bah Kawai ka kwantar da yaro baccin ba gaira ba dalili Waikai saika fahimtar dashi cikin baccinsa Bakayi tunanin ibadun da suke kanshi ba. Ka wani sashi kallan wasu bankwan matane...... Tana fa'din hakan ta bigi SAILUBAH da maryam nan take suka xagwanye suka xama toka alamar babusu duk alaye ne Sannan tacigaba da cewa kacire fuskarsa kasaka taka danya temaki matarka bashi xai baka shiga rayuwarsa yanda kake so bah...... (Meke faruwa ne💁🏼 sisters) Qara sunkuyar dakai Junior yayi Yace bin umarninki farillane gareni kauce miki matsalane ga rayuwata Damuwata Ki sauka daga wannan fushin da kikeyi dani Dan yana sani shiga tashin hankali Nasan nayi kuskure ya ummi Kiyafemin Baxan qara maimai irin hakan ba..... Cikin sanyin rai tace kasan kai ka'dai muka haifa nida mahaifinka Baxan iya juya maka baya wajan in yafe maka ba Ina sanka yarona. Amma kacanja hali abunnan da kayi yayi matuqar ta6a xuciyata Ka sani bana san wasa da ibada Bana san wasa da alkin Allah Qara sunkuyar da kansa yayi cikin nadama yace wlhi ya ummi Sam nashagala akan ibadarsa Kinsan ba haka nake ba Kiyafe min Shafa kansa tayi Tace nayafe maka allah yai maka albarka.... Jeka kagyara komai. Sannan kagaishe min da RAMADAN 'din kace injini yayafe maka duk nasan yana ganina kuma yana jina....... Angama ummina Nan yatashi ya 6ace cikin nadamar abinda ya aikata..... ****** ****** ****** ****** Yana kwance a asibitin aminu kano yana sauke numfashi ahankali ahankali alamar baccin kwanciyar hankali yakeyi Gashi ansaka mishi ruwa me sinadarin abinci aciki.... Gefe guda tawaje SAILUBAH ce da XEE FAWAS da KHAMIS Momy da Dady da Khairat Dukkaninsu damuwace 6ace 6ace afuskokinsu SAILUBAH tarame duk tafice daga hayyacinta Kallo 'daya xaka mata kasan tayi kuka dan ga sheda nan yanda idanta ya kumbure Momy mah haka XEE sarkin tausayi ba'a barta abayaba wajan taya SAILUBAH kuka Ba'a maganar FAWAS da KHAMIS dan sunfi kowa shiga tashin hankalin halin da 'dan uwan nasu yake ciki Cikin sanyin rai Momy Tace SAILUBAH kisaki ranki kinji abinda doctor yace ai Tace Momy naji jinake tamkar baxai tashi bah Musamman idan natuna xancikan da mukayi dashi anar daran daxai kwanta Ina san RAMADAN Momy pls kuyi wani abu akai Dady Wlhi narasashi nima rasani xakuyi...... Tana fa'din hakan taje taxube ajikin Abbanta tana cigaba da cewa kana gani Abba ko. yau ina qirgawa kwanansa hu'du Baci ba Sha Abba. Sannan ba magana. Haka kuma ba motsi...... Shafa kanta yahauyi cikin tausayawa Allah yana qaunar yaran nan RAMADAN dan jiyake tamkar shiya haifeshi..... Kan yayi mata magana Dady ya kalli SAILUBAN cikin damuwa Yace kiyi hakuri 'Yata xai tashi Munsan yanda kike da RAMADAN Kinfi kowa shaquwa dashi. Ina tabbatar miki da cewa xai tashi insha Allah Shuru SAILUBAH tayi kawai KHAMIS ya girgixa kai hawaye na xubo mishi yace allah ya tabbatar da alkairi Duk sukace Ameein FAWAS yamiqa mah XEE ruwa yace Aunty XEE wanke fuskarki ta6a Murmushi yaqe tayi takar6a ruwan batare da tayi yunkurin wankewa bah Shi kam yayi nasa kukan dan RAMADAN wani 6arene na rayuwarsu Tabbas idan sukayi rashinsa sunyi babban rashi arayuwarsu......... Murmushi junior yayi bayan gajin abinda suke cewa Can ya shige ta gabansu batare da sungansa ba ya shiga 'dakin da RAMADAN yake Sanda ya xuba mishi ido na tsawan minti biyu kana yayi murmushi shidai yana San yaran Ga nutsuwa ga ibada ga hankali ga tausayi uwa uba ga shegen wayo a soyayya Cikin nutsuwa ya shafi gefan fuskarsa..... Ahankali RAMADAN ya bu'de fuskarsa yana me tsaida ganinsa ga Junior Can ya tashi afurgice ya dafe kansa dayaji yana baraxanar tarwatsewa Cikin wani hali ya nuna Junior da yatsa yace Junior Murmushi yayi yace na'am Ashe dai xaka shaidani Yace meke faruwa dani Yace abinda kagani cikin baccinka Yace da gaske bacci nake ko idona biyu. Yace da axahirine aida kafi ganin bala'in dayafi haka Yace na mutu acikin baccina Amma bandena ganin Rayuwar da KHAMIS FAWAS Auntyna suke bah Yace dake bacci komai mah xaka gani Yace me yasa hakan tafaru afareni. Yace saboda nine Duk surkullena ne Duk shirina ne Duk ba gaskiya bane Sannan rayuwarku baxata kasance hakan ba Kayafemin RAMADAN nashiga rayuwarka dan nafahimtar dakai wani abu. Saidai ban kaiga cinma burina bah aika gani ummina tanemi da indawo dakai daga waccan duniyar Da 6acin rai RAMADAN yace gayamin tun yaushe nafara wannan baccin Yace yau kwananka hu'du Yace akwana hu'du duk naga wannan rayuwar dana gani... Yace kawai da gaske Yace toh da wane buri nakwana acikin daran da wannan bacci yayi awan gaba dani Shuru Junior yayi.... Shima RAMADAN din shurun yayi kawai yana kallan Junior wanda mamaki ya hanasa sakewa Gashi kamar shi dan ba abinda ya rabashi da Junior Can Junior yace awannan daran kayi sallah karoqi allah daya hana auran SAILUBAH da Alhaji Aminu....... Amatuqar raxane RAMADAN ya tashi Yace kana nufin kwanciyata acikin wannan dare shiyabaka damar shiga cikin mafarkina kashirya min wannan surkullan wanda naga kabayyana a 'dan uwana jinina. Ka 6ullo lokacin da akayi auran auntyna. Kakawo min xancan wai wani wan mahaifinmu wai shiya kashe mana mahaifinmu kan dukiya. Kuma mahaifiyarmu tamutu wajan haihuwarmu. Kadawo kana rayuwa damu cikin gidanmu. Har kakoma karatu waje. Naxo na auri Auntyna sailuba tahaife min yara biyu. Naga rayuwar Aunty xee da khamis rayuwar fawas da hameeda. Bayan na mutu ban dena ganin rayuwarka da auntyna ba dasu dukkansu. Da irin wahalar da kake bata da rainin hankalinka. Daga qarshe ka aureta ita da wata maryam asannan ne kafara bayyana musu ainihin kokai waye. Kajasu dan kanuna musu yanda waje take saika kaisu garinku gun mahaifiyarka Nan tanuna 6acin ranta kan abin daka 'aikata agareni.... Wannan shine film 'din daka sakama memoryna acikin baccina ko Junior ya hararesa yace hmm qaramin yaro dakai sai riqe abubuwa Ji yanda ka lissafo komai baka manta komai bah Harararsa shima RAMADAN yayi ya tafe kansa wanda yake masa ciwo da gaske Tunani ya shiga kan meyafaru dashi wannan ranar da har wannan aljanin ya shiga cikin rayuwarsa........ Yauwa ya tuna da abinda ya faru a ranar... Cewar bakinsa... (Muje zuwa sisters 😀) Yeeee🤣🤣 RAMADAN yaga rayuwa *Dama kyan karatu waiwaye........ Inji hausawa sukace adan tafiya.....* *Me karatu kaima tuno wannan Page 'din. Dan tun daga shi junior ya d'ora lamarinsa a baccin da RAMADAN yayi wannan daran da komai ya fara gudana* *Ni dakai dake mun karanta wannan page 'din amma bamu ta6a kawowa daga shine baccin RAMADAN yasomah ba.... gaskiyane Junior hatsabibine inji Aunty Rahamat Nalele *Page d'in baya *Shidai RAMADAN ya tuna lokacin da suka dawo daga qauyen takai wajan gaisuwar rasuwar abokin wanda har FAWAS yayi wata budurwa HAMEEDAH 'Yar QAUYE. Ya tuna lokacin daya dawo yayi wanka nufar gun Auntyn tasa SAILUBAH yayi ga abinda suka xanta ita dashi* Tana kwance a gado XEE na gefanta ga qawayanta nan sai hira suke Saiya shigo 'dakin XEE ta 6allamai harara Tace ban ta6a ganin qani mesa Auntyn shi cikin damuwa da tashin hankali ba kamarka RAMADAN....... Da sauri ya katseta da cewa haba Aunty XEE kidena haka. Yanxu xakisa taqara jin haushina bayan KHAMIS ne Babban me lefi dayaqi gaya mata inda nake Tace eh Gaskiya. dake gaka gata ai dole ka kanemi kare kanka. Karka wani saka KHAMIS dan bashi da lefi Ya kalleta da Murmushi Yace toh Naji bashi da lefi Ya maida kallansa ga Auntyn tashi wacce ta kafeshi da ido tun shigowarshi Yace Barka da yammaci my Aunty Ta sauke ajiyar xuciya Tace me yasaka ramewa haka Ya tashi yana cewa tunani da tashin hankali Tashi itama tayi Tace muje Ba musu suka jero tare har xuwa gidansu part 'dinsa Ta xauna gefan gado shi kuma yana kan kujerar da take fuskantarta Tace wane tunanine haka da tashin hankali yasaka ramewa Ya kalleta ka'dan Yace kema ai kin rame Sosai Tace kaban amsata Yace hmm tunaninki Auntyna mana.... Wai a tunaninki rabuwa dake xai barni na xauna lafiya ne. Hmm Sam hakan baxai yuhuba Dan daga ranar da kika bar gidanku xuwa gidan wani toh Ki tabbatar baxan qara samun kwanciyar hankali arayuwata bah Saban danayi dake ya kai matsayin da in tunaninki yayimin yawa xan iya rasa rayuwata........ Kuka SAILUBAH tasamai Sosai..... Duk da hankalin RAMADAN ya tashi Amma sai ya share dan yanxu burinshi yayi mata abinda xaisa taji xafi fiye da yanda yakeji axuciyarsa Nan ya hau 6arar mata da kalamai cikin qara kashe mata xuciya da takaici Fa'di yake narasa me kika gani ajikin wannan mutumin Sam bai dace dake ba Ina ganin ma 'dan shan jinine Dan bashi da fuskar imani Ki kula dashi Sosai mana Gashi shi ba wani kyakkyawa bah. Kawai Kinga ku'di kin yarda yaxama miji agareki Akan ma wane dalili xaki yanke igiyar shaquwarmu saboda shi Nayi baqin ciki da takaicin hakan. Bani da wani buri daya wucce in tayaki neman xabin ranki. Kyakkyawa me aji me ku'di me maseefar kishinki. Nayi addu'ar istahara nayi Sallah akan Allah ya bani haske akan lamarinki dashi..... nagani Cikin mafarkina Auran shi nadama ne agareki Ni fah baxan 6oye miki ba. In bake baxan iya rayuwa sak kamar yanda aka sanni ba Kuka take Sosai yana qara jefah mata qiyayyar Alhaji Aminu Can dai dayaga kukan yayi yawa kuma yana maseefar damun xuciyarshi sai ya matso kusa da ita ya kama hannunta Yace toh kiyi shuru kidena kukan nan tunda kina sanshi baxan qara kushe miki shiba tunda ranki na 6aci kiyi hakuri Ki dena bana so. inba so kike Ki hanani bacci ba. Yafa'di hakan da leqa fuskarta cikin kusanci dasan qara hargitsa mata kwanya Aiko ta shaqa Dan yanda yayi kusanci da ita ka'dan ya rage bakinsu ya ha'du dana juna Ganin yasami abinda yakeso dan jikinta ya mutu mu'dus. qiris take jira ta xubemai ajiki. Shiyasa ya 'dan janye kansa ka'dan daga gareta tare da jifanta da wani kallo Wanda atake yasan ya gama kunce mata Komai. Ta lumshe idanta tare da dafe kanta Tace bana sanshi bana sanshi Na da'de dasanin Kaine kwanciyar hankalina RAMADAN Ban San me yake damuna ba. Kina sanshi tunda kike min kuka akansa. Kuma aida bakya sanshi ko kusa baxaji sha'awar kar6ar abin hannunsa bah. RAMADAN Ya fa'da dasan qara harxuqa xuciyarta Aiko cikin fusata Tace wai kai wane irin 'dan iskane Nace bana sanshi bana sanshi bana sanshi Amma sai qara Sa xuciyata xafi kakeyi tun kwanaki can da suka wucce nayi dana sanin sanin shi Yariga da ya samu guri gun Abbana ya hanashi kallan ra'ayina Ya kakeso nayi ne RAMADAN. So kake na haukace Naji Komai bana jin da'dinsa aduniyar nan saboda qaurace min da kayi. Sam nalura bakasan farin cikina To bara kaji na rantse da Allah ka kara min haka sai mun sami mummunan matsala dakai Dan narigada na auna na garo ba abinda yake tadamin hankali kamar rashinka kusa dani Da 6acin rai Tatashi da niyar barin 'dakin....... Cikin sauri ya Sha gaban da yanayin damuwa...... Yace 6acin ranki tashin hankaline agareni Ki temaken kisaki ranki ko nasami nutsuwata Tace matsamin in fitta ko kasha mari....... Yasan acike take dashi Komai xata iyayi masa Saidai kash yayima kansa alqawarin baxai barta tatafi awannan yanayin ba Dan yanasan yau ya bala'in hargitsa mata kwanya Dan haka cikin yi mata baxata ya rungumeta da kashe murya irinta Wanda yake yin kuka Yace kimin rai auntyna kiyafemin nasan narabu dake kenan yau har abada. baxan ta6a yafema kaina bah idan har xuciyarki batayi sanyi munyi bankwana cikin farin ciki bah....... Tundaga tsayar kan SAILUBAH taji wani abu na yawo ajikinta Wanda yasa ta rikice Komai na jikinta ya tsaya cak..... Cikin wata murya me sanyi Tace toh naji sakeni Cikin sanyin jiki ya raba kansa daga jikinta idan shi akanta yana San gano wani Abu Yace kin hakura ta kallesa ka'dan cikin wahalalliyar murya Tace ya xanyi dakai RAMADAN Pls ina buqatar ka'daita Ya bu'de 'kofar suka fitoh tare har 'dakin Kakah ya kaita dan nanne ba kowa. Yace toh Ki huta my Aunty. Ko kulashi batayi ba Yayi Murmushi dan yana san ta qara harxuqowa dan bai gaji da maseefar taba Idan tana magana sam bayaso tadena. dan haka ya leqa fuskarta Yace toh xan tafi fah Auntyna..... Kamar xatayi kuka tace wai me xan maka Ba xaka barni nasamu ka'daicin bane. Yace da naso kitashi mu'danyi hira ta bankwana Da maseefa tatashi ta kallesa kamar xata falleshi da mari Tace baxan tashi ba. wai hirar dole ce Nace ina buqatar ka'daici kabarni man Sai yayi kalar sanyi irin na abin tausayin nan Yace toh shikenan Auntyna Allah ya baki hakuri. Ya nufi hanyar futa Aiko saita fashe da kuka. Bai tsaya ba ya futa abinsa Yana Murmushi fa'di yake aransa Auntyna kenan duk Sallah idan nayi ina ha'daki da Allah ya xa'ayi Ki xauna cikin kwanciyar hankali akaina. Sam hakan baxai yuhuba XEE tatareshi a farfajiyar gidan Tace shigowarku 'daxo naga SAILUBAH daga dukkan alamu tayi kuka Yanxu kuma kafitoh kana Murmushi wai me yasa Sam bakaso kaganta cikin kwanciyar hankaline Yace Aunty XEE kenan. Wlhi duk duniya bawanda yafini San ganin kwanciyar hankalinta Kawai batasan Auran wannan shegen ne Ni kuma dama basan shi nake ba. Saina bata haske akan hakan........ Ta katseshi da fa'din Ka hargitsata dai meyasa ka tsani ganinta da kowane 'da namiji. Yace saboda duk wa'yanda take ha'duwa dasu basa dacewa da ita Sam Ke Kinsan burunta Auran namiji me aji Kyakkyawa Me ku'di over Me kishinta Me shakarun da suka xarce nata Sosai Shin tsakaninki da Allah har yanxu ta ha'da me wannan abubuwan gabaki 'daya XEE tayi shuru. Can Tace gaskiya aa Yace hmmm Kinga Ki share kawai wannan Auran nata ba inda xaije dan xatayi rayuwa ne da Wanda ko kusa bai dace da itaba Kin santa sarai idan tace ta tsani abu bata sanshi ba tayanda xa'ayi tarayu da wannan abun cikin xaman lafiya Wlhi ta tsaneshi batasan ha'dinta dashi yanxu Tayi nadamar saninshi Ki rubuta Ki ajiye ba'inda Auran sun nan xaije Idan kin shiga ciki yanxu dan Allah kice tadena kukan ya isa haka Na barki lafiya. Yana fa'din haka ya wucceta ya ficce daga gidan XEE tabishi da kallo baki sake Kana tayi 'dakin khakha. Har lokacin ko SAILUBAH kuka take ta kalli XEE cikin kukan Tace yaxanyi da RAMADAN XEE yaxanyi dashi Tace hakuri SAILUBAH hakuri xakiyi dashi Tace na rasa me yake damuna akansa.... XEE Tace hmm nihar narasa wane tunani Xanyi akanku....... Katse tunaninsa junior yayi wajan cewa bayan fitarka daga gidan Dukkan Ku kunshiga tashin hankali a wanannan daran Inda kai kakwanta da tunanin mexai faru gobe da auran Auntynka SAILUBAH Shin Auranta xai yuhu kuwa Ganin da kayi bacci baida alamar saceka awannan dare shiyasa katashi kadinga Sallah kana kaima Allah kukan ka yayi maka maganin damuwarka Bayan ka idar saika kwanta ayanda na lura kana cikin farin ciki baka kwanta da damuwa bah Hakan yasa nayi amfani da wannan kwanciyar taka na d'ora surkullena akanka Tundaga lokacin baka tashi ba sai yanxu da Allah yayi ikwansa akanka.... Da sanyi sanyi RAMADAN yace acikin surkullanka naga gari ya waye har munsaka ankwanmu ni da FAWAS da KHAMIS na auran nata Anyi mata auran ankaita garin abujah Idan nayi tunani dakyau mijin data auran me kisa ne d'an mad'igone Ta kira ni wata ranah a waya hankalinta tashe take shaidamin mijin nata meshan jinine Kuma 'dan ma'digone Sannan me kisa ne Zai kasheta inbanxo gareta bah...... Junior yayi Murmushi yace anyi haka dan hankalinka ya tashi washe gari kanemi dady daya barka kaje garin abujah Ya tambayeka dalilin xuwanka kabashi tabbacin kanaso ne kawai kaje gidan Dady Auwal..... Da sauri RAMADAN ya katseshi da cewa yauwa ya akayi Dady Auwal ya koma garin abujah bayan a jos yake nasan acan na ta6a rayuwa ka'dan Junior yasheqe da dariya yace shiyasa nace maka surkullan nawa kenan In banyi hakan bah tayaya surkullan xaitafi yanda nakeso Tayaya xan baiyana matsayin 'dan uwana...... Harararsa RAMADAN yayi da dafe kansa alamarin damuwa Dariya Juniorn ya qarayi Yace sainayi amfani da ha'duwarka da Shahuda da kayi a jifatu Na fara 6ullowa ta gidansu. Katuna garqama maka bindigogi da mahaifinta yayi akan abinda na aikata masu yayi tunanin kaine Shuru RAMADAN yayi kawai yana kallan Junior Gaskiya aljanu hatsabibaine she'danu Musamman yanxu daya ke qara tuna yanda amafarkin junior yaxama 'dan uwansa Da yanda yanuna mishi suna da wani wan mahaifinsu mugun mutum Wanda yake rike dashi Junior Wai shine ya kashe musu mahaifinsu Harda yanda shi kansa ya auri Auntynsa SAILUBAH da rayuwar da yaga sunyi shida ita. Rayuwa me tsayawa arai Har wai ya haihu Ya haifi 'yan biyu KHAULAT da KHAULEET Yaxo kuma ya mutu Baidane ganin rayuwar dasu FAWAS da KHAMIS XEE da Auntyn tasa ha'di da HAMEEDAH sukeyi ba fannin auratayya da sauransu Ya kuma mutu saka makwan gobara Wai har XEE tasamu matsalar haihuwa bata haihu da wuri bah HAMEEDAH kuma ta haifi Ahmad Shima ogan Junior sai rainama Auntynsa hankali yake Toh abin tambayar RAMADAN anan shine miye dalilin dayasa Junior ya shirya mishi wannan surkullan cikin baccinsa har ya ibi kwana uku yana yi...... Dakyau yake Kallan junior yace yanxu naji komai ina so ka gayamin dalilinka nayi min wannan surkullan cikin bacci NAH Murmushi yayi yace dalilan nawa guda uku ne.......... Na Farko SAILUBAH tasaka buri a rayuwarta nasan namiji me ku'di over Namiji me kyau 'dan gaye Namijin da xai sota ya qaunaceta har qarshen rayuwarta Namijin daya fita shekaru ya girme mata nesa ba kusa ba Sannan yanayin shigar da takeyi ita da XEE tasa6a ma addinin muslinci Duk wani namiji me lafiya idan yayi ido biyu da ita da XEE sai yaso ya mallakesu a matsayin matansa Hakan mu aljanu munada kwa'dayi sosai munasan mata masu irin wannan shigar Na da'de ina sha'awar SAILUBAH Na da'de inasan auranta Amma tsoran mahaifiyata ya dakatar dani Kana qoqari sosai wajan yima SAILUBAH Addu'a Kana qoqari sosai wajan ganar da ita abubuwa Xan gaya maka dalilina na 3 wanda xaisa kagamsu lallal saka baccin da nayi bana banxa bane Haqiqa akwai cakwakiya arayuwarku dukkanku Kai RAMADAN FAWAS KHAMIS HAMEEDAH SAILUBAH XEE Zaku samu abinda kukeso Amma zakusha wahala arayuwar taku Shin kasan wacece HAMEEDAH wacce FAWAS yayi mata ganin Farko a qauyan takai kafin ka kwanta baccinka Shin kana da sanin cewa mahaifiyar KHAMIS qaddarar allah ce kawai xatasa tasota musamman idan kaga mummunar tsana da xata nuna agareta Baxa ka ta6a sanin SAILUBAH tana MASEEFAR qaunarka ba har sai nan gaba saidai ita 'din wawiyace agurinka kai ka'dai ne xaka iya da ita Xaka San kokai waye ne ta sanadin KHAMIS Banda haka ikwan Allah ne kawai xaisa kasan kokai waye Wannan Sirrin Dadynka ne..... Matsowa yayi ga RAMADAN ka'dan yaciga da cewa. Hmmm HAMEEDAH bala'i ce futunace FAWAS ya fa'da tarkwanta XEE alkairi ce ga KHAMIS Amma iyayen nasu baxasu so ha'din ba ko misqala zairatin. Saidai bayanda suka iya da ikwan Allah Karigada ka 6ata tunanin SAILUBAH tuni. Kai baxa kasha wahala akanta canba Abokana yanka FAWAS KHAMIS qaunarka suke da gaske Tabbas San junanku kuke da gaskiya Haka XEE qaunar SAILUBAH take da gaske Kamar yanda yake ita qawar alxiqi ce Nasan xaka xargeni kamar yanda naga tsanata akwayar idanka yanxu Meye dalilina nayi maka hakan. Duk wannan baxai gamsar dakai ba. Ko Kuma ince bai gamsar dakai 'dinba Ina sanka RAMADAN saboda ibadarka Ina sanka saboda kyakkyawan halinka Ina sanka saboda wayanka da dabararka Nasan kaji abinda mahaifiyata tace kagani kuma da idanka Xanso ka yafeni kamar yanda kagaya taruqi arxiqin hakan Kamar kuma yanda kaga nadamata axahiri *Xan tafi baxaka sake ganina bah har sai randa kuka sami abinda kuke so komai yaxo muku qarshe* *Aranar xan qara baiyana agareka in gaya maka dalilina na uku. Dana saka yin wannan baccin....* Zan qara gaya maka maka HAMEEDAH bala'i ce. Saidai qarshen wasan nata nadama ne. Ammafah ba wani can bah Qaddarar da zatasa kusami sauqin wasu abubuwan shine kar6ar uxirin mahaifanku na fitta waje dan qarasa karatunku Na tafi RAMADAN Kayi abu me amfani ga rayuwarka Ba akanka aka fara irin wannan baccin da mafarkan bah dan haka karkasa wata damuwa aranka Ina muku fatan alkairi.... Dakata.... RAMADAN ya katseshi wajan fa'din hakan Cikin nutsuwa yaciga da fa'din Ku aljanu maqaryata ne tataya xa'ayi in yarda da abin daka gayamin yanxu Ko kanaso kaxama bokana ne. me bani sarrin abinda yake gaba Na yafe maka abinda kamin Amma kasani bansa duk abinda kafa'da dangane da rayuwar da xamuyi a gaba ba cikin xuciyata Saboda ni sani irin wannan nema nake agun allah bani nema agun wani Ban yarda da abinda kace bah. kawai nafi yarda da cemin da kayi in yafe maka sannan baxaka qara bayyana agareni bah har sai kaga cikar burinmu..... Murmushi Aljani Junior yayi yace lallene kwa xanka na fa'din gaskiyarka yana burgeni Hakan kake. tun kana yaro. tabbas akan gado hali Ba shakka mahaifinka babban mutum ne. me gaskiya da rukwan amana da riqe alqawari Banda haka dabaxai bar kintsattsan 'da kamarka ba Tabbas mahaifinka me girma ne Wanda yayi ilimi mexurfi Harya kaishi da aikata abinda ya dace me kyau Na tabbatar xaka iya xama kamarsa Rashin yarda da abinda nace maka yana 'daya daga cikin abinda mahaifinka bai yarda dashi bah Wato neman sani agun aljan Hakan ba lefi bane Saidai ni musulmine Wanda yasan abinda Musulinci ya yarda dashi Idan kaso kayarda dani wannan ruwanka yayana. Idan kaso kaqi yarda dama ban gaya maka da wata manufah. Bare naji xafi Kamar yanda nace maka abaya baxan qara bayyana a gareka ba harsai can gaba. Tabbas kasa aranka haka abin xai kasance Na barka lafiya allah ya sadamu da alkairinsa..... Yana fa'din hakan ya 6ace 6at Dafe kansa RAMADAN yayi yana ji kamar yana bara xanar tarwatsewa. Cikin wannan hali dadynsa yashigo dan yaji kamar motsi a 'dakin..... Ganin RAMADAN axaune shiyasa shi saurin qarasawa gareshi ya riqe hannunsa cike da matuqar Farin Ciki ya kwallamah Momy...... Aiba Momy bace kawai tasheqo da gudu ba dukkansu ne sukayo 'dakin banda SAILUBAH data tokare a bakin k'ofah tana dafe qirjinta da da sauke numfashin farin ciki Dukkanin su cah suka mishi akai kowa burinshumi yaji yayi magana Shiko sai binsu kawai yake da kallo Can Abban SAILUBAH yaje ya kira doctor Bayan yay masa Wasu gwajeje yace toh madallah komai ya tafi yanda akeso. Yanxu me kakeji a jikin naka Cikin sanyin murya Yace bani jin komai Yace toh masha Allah sai ko yanxu xa'a iya baku sallama. ya qarashe maganar da kallansu Dady Da murna sukace aiko hakan yayi.... Sai kallan FAWAS KHAMIS XEE RAMADAN kawai yana musu Murmushi kamar yanda yake 'dauke akan fuskarsu Can ya kalli Momy da dady Abba yace Momy ina Auntyna..... Ai dukkansu kallan qofah suka sai sukaga wayam ba SAILUBAH ba alamarta FAWAS yace tana waje dan yanxu tagama kuka akanka Momy Tace hmmm Allah sarki ai mungode mah allah daya tasar mana kai Da SAILUBAH binka xatayi Murmushi yayi ya kalli XEE yace Aunty XEE ya naga idanki jawur Harararsa tayi tace idan muka rasaka RAMADAN ba qaramun rashi zamuyi bah. Yace idan dai na canko duk kukan nawa ne Tace ga xahiri Murmushi ya qara yi cikin jin da'di ya tashi yana cewa Abba bara in 'dan kintsa Kaina ka'dan Cikin jin da'di yace. Toh RAMADAN Kintsa kansa yake yi Amma xuciyarsa tanaga Auntynsa dan Allah Allah yake yayi ido biyu da ita Bayan ya fitoh Momy ta saka masa abinci tana cewa maxa kaci yanxu da safinsa Murmushi yayi yace xanci Momy Amma girkin Auntyna itama saina sauke nauyin dake kaina na sallaloli Tace toh shigarka toilet anbamu sallamah muje gida kayi acan Yace toh Sun fitoh harabar asibitin ya hangeta cikin motar dady har sun fara gaba Cikin kallan shagwa6e yace da Momy allah Aunty fushi take dani lefin me namata Murmushi Momy tayi tace wannan tsakaninku RAMADAN kafi kowa sanin abarka Atunanina Farin Ciki ne yayi mata yawa shiyasata kasa fuskantarka Murmushi yayi yana me rayawa aransa gwara da kikace atunaninki momy wannan fushin na wukunci ne....... Suna ISA harabar gidan KHAMIS da FAWAS sukace bara suje gida dansu fa'dama iyayamsu tashin nasa Yace ok ya gode da kulawarsu Dakar kafa'darsa sukayi suna dariya ahaka suka ficce a motar FAWAS Yarage daga shi sai ita agun dan haka yaje gareta ahankali yana cewa Aunty kiyi hakuri da lefina Afusace tajuyo rannan amugun 6ace tagalla masa wata muguwar hararar data qara mata kyau

Chapter 32 of 33