Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tayi Tace inaganin fah RAMADAN ya tafi RAMADAN ya dawone.... SAILUBAH Tace ban gane bah Murmushi XEE taqarayi Tace share kawai. Akwai magana 'Yar Uwa. Amma sai mun ha'du SAILUBAH taqara riqe wayar tata Tace gayamin yanxu Tace kawai saimun ha'du gobe dan xamu gun 'dan iskan naki ya dubani Daga nan nabiyo kiban shawara.... Tace da qarfe nawa Tace da kamar Sha biyu haka xan fita yana dubani dai xaki ganni Toh SAILUBAH Tace da kashe wayan tata XEE na qoqarin shiga bedroom KHAMIS ya rungumeta ta baya yana cewa za'ayi gulma kenan gobe Murmushi XEE tayi Tace gulmar wa xamuyi my Luv..... Juyowa yayi da ita gabansa Yana cewa mutanan Suna da yawa ai. Matsalar dai bansan tawa xa'ayi bah. Ya qarashe yana me qaremah qirjinta kallo Harararsa tayi Tace me kake kallo. Murmushi yayi da cewa abubuwana manah Kwatar kanta tahauyi tana cewa yanxufa kadawo my Luv Yace aina sani. Ko wani abu nace xan miki😬.... Marairai CE mishi tayi tana cewa to to to kasakeni pls kaga wanka xanshiga Qara matseta yayi Yace Yauwa dai-dai kenan...... Sanda suka samu nutsuwa XEE takallesa Tace abun naka ya fara yawa kwana biyu. Kallanta yayi cikin so da qauna Yace nima ina mamakin hakan Murmushi tayi da lafewa ajikinsa Tace Wlhi tsakanin shakaran da jiya da yau ba wani jin da'din jikina nake ba Da sauri Yace na lura da hakan. Kindai rigani furtawa ne kawai Meyake damunki my luv.... Nima ban sani my d. Xaki bari xuwa gobe ne Ku muje ya dubaki ko muje yanxu aa mubari sai goben Shafata ya hauyi yana qara maqalqale abarsa😀 Sosai XEE tayi nasarar 6ata tunanin KHAMIS Bayaji baya Gani Sam akanta banda soyayyarta da qaunarta da tayi masa mugun kamu 6:00pm Sauri sauri gudu-gudu FAWAS yakeyi dan dawowa gida Dadynsa ya kallesa Yace wai saurin me kakeyi ne haka. Na lura a kwanakinnan lokacin tashinka nayi kale tafiya kodako Komai bai kammala ba Sosa qeya FAWAS yayi yana Murmushi Yace Wlhi Dad wani uziri ne yake sani sauri haka Yace toh yau ai ranar hutume Kuma kaga in baka tsaya kafitar da abin nan dakyau ba baxasu iya samunsu gobe ba Turo baki FAWAS yayi Yace Dad sunsan yau ba ranar aiki bane mexaisa Su matsa maka akan hakan Murmushi Dadyn yayi mai da cewa haba my son gobe suke buqata. Qara turo baki FAWAS yayi da juyoma da Dadyn nasan laptop 'dinsa Yace kagani fa Dad. Saura ka'dan. Insha Allah gobe Xan qarasa fitarwa Shuru Dadyn yayi masa Ganin hakan hakan yasa FAWAS bashi kiss a hannu ya fitta yana cewa bye Dad. Saika tawo..... Direct FAWAS gida ya nufo dan yasan yanxu matar tasa tasamai gaba akan Komai Danta dena yarda dashi kwata kwata Samunta yayi afalo tana kallo taci wankanta na riga da wando sun matseta aynun Tana ganinsa tatashi fuskarta farin ciki fal Yaxo ya rungumeta da cewa Gaskiya kinyi kyau Sosai YAYATA Nagode mijina. Dama ka 'daure a haka Murmushi yasakar mata yana cewa kicire Komai aranki daga ke bawata macen da xata sami wajan xama axuciyata Tace ina.... Ban yarda ba. gwara dai indinga ankarewa dakai. dan tunda RAMADAN yace min in nutsu da dakyau shiyasan me kake aikatawa awaje.... Me gaskiya ne. Me hankali ne. Ga shi da sanin abinda ya dace Lefine dan nariqe abinda yace min Girgixa mata kai FAWAS yayi da cewa ki share kawai Allah yanxu ba wata macen da xata 'dauke hankalina Tace harda Aymana Jan numfashi yayi Yace ankai sadakinta fah. Tace kaine kakai ko Harararta yayi da cewa eh nine nakai nanda sati biyu xaki ganta a gidan nan... Yana fa'din hakan ya shigewa bedroom dan tsaftace kansa Bayan ya fitone yaga ganta tana fitomai da kayan da xaisa Bayan yasa ya feshe jikinta da turare Yace ina hamed Tace yana gun Momy yanxu suka dawo daga unguwa. Yace Yauwa dai-dai kenan kinga sai kiji dani ko.... Tace dame fah Yace da Komai Dariya tayi Tace ina dai fitar da manjannan namu na mata. Dan haka kanutsu ba Komai xaka samu anan ba . Dan na lura harda wani rawar kanka agun😀.... Ya mutsa fuskarsa yayi Yace Saura kwana nawa Tace goma Yace what😳 In mutu kenan Murmushi HAMEEDA tayi dajan hannunsa sukayi dining yana bata tana bashi abincin Suna hirarsu me da'di cikin qaunar juna *(kamar Rahamat da masoyanta a SAMAREEN BANAH😀)* - Cikin dare ciwan ciki ya farma SAILUBAH.... Sosai take ta murququsu saican daga baya ya lafa mata Washe gari ko XEE Suna tare da junior Yace angaida Aunty XEE... gayamin miye matsalar Tace haba Junior kafi kowa sanin abin daya kawomu KHAMIS Yace bar 'dan rainin hankali mana Murmushi junior yayi Yace dafarko Xanyi miki scanning inga lafiyar mahaifarki Tace toh Haka takwanta a 'dan gadan da ake scanning 'din ya hau duba lafiyarta. Bayan wasu minti biyu Yace angama Aunty tashi XEE Tatashi tana cewa bansan adadin scanning 'din da akamin arayuwa ba Murmushi junior yayi Bayan sun xauna da cewa wannan yasha bambam da Wanda aka saba miki Da sauri KHAMIS Yace me kagani kenan😳 Yace alkairi Amma sai ambani goro xan fa'di Murmushi XEE tayi Tace hmm toh idan na haifi 'ya mace xan baka ita..... Waro ido😳 Junior yayi Yace tab kafin lokacin ai namata tsufah. Kuma wacce xan Aura me kishi CE Saidai kimin alqawarin idan kika haifi 'da namiji xaki bashi KHAULAT Kinga Ahmed saiki bashi KAULEET dan naga bashi da hayaniya xai iya da surutunta Dariya KHAMIS yayi😂 Yace gaskiya wannan ha'din naka yayi Dariya itama XEE tayi Tace indai wannan ne nayi Da sauri junior Yace aa ba ruwana Kar lokacin yayi yaran subaki kunya. Saidai kawai kimin alqawarin xakidinga addu'a akan Allah ya tabbatar da hakan Murmushi tayi da cewa hmm aika rigada ka furta Yanxu dai gayamin gaskiya dan Allah banda kwayayan haihuwa ko😰 Murmushi Junior yayi Yace yaushe rabanki da al'ada. Shuru tayi tana lissafi axuci KHAMIS yayi Murmushi ka'dan Yace xatakai wata biyu da sati uku Jan numfashi Junior yayi Yace toh tana da ciki 'dan wata biyu da sati biyu. Gabaki 'dayansu tashi sukayi atare cikin matuqar mamaki.... Aiko a 'dimauce XEE Tace Wayyo Allah dagaske cikine dani Junior 😳 Yace bana dai rantsewa akan abu Sosai Amma Wlhi cikine dake. Rungumarsa KHAMIS yayi I Luv u brother yafa'da yana mai kiran number na FAWAS FAWAS na office Yana aiki aidajin samun Cikin XEE yatashi da murna yana cewa Alhamdulillah pls bani ita in mata murna 😀 Da farin ciki XEE take cemai FAWAS da gaskene inada ciki Yace na tayaki murna Aunty XEE 😀 KHAMIS na qar6ar wayan XEE tafashe da kuka tana cewa Allah Allah Allah kaji qan RAMADAN da raban baxaiji wannan abin farin Cikin ba 😭 Asanyaye KHAMIS Yace Wlhi numbarsa nafara dannawa tunanin da nayine yasani danna ta FAWAS Yafa'di hakan hawaye na xubo mishi Shima Junior hawayanne ya xubo mishi Yace Allah yaji qanka brother Amiien sukace KHAMIS na tuqi Amma XEE gani takeyi kamar bayi yake bah Damuwarta taganta gaban SAILUBAH tabata labari me da'di Aiko KHAMIS nayin faking tafice.... yana my Luv.... Tana cewa sai kadawo 'daukata Yace ni ko Tace eh bye✋🏻bye✋🏻😀 Yace Allah idan baki bani kiss ba. xan hukuntaki yau😀..... Cak XEE tatsaya Tace iye Murmushi yayi mata Ta hararesa da cewa ka hukuntani 'din mana. Nima kaga saina rama tawajan in cin abinci kaga sai babynka yafito da qashi😂 Waro ido 😳 KHAMIS yayi Yace no my Luv karkimin haka pls Dariya XEE tayi da cewa da wani idanka agun😡 sainayi sati banci Komai bah Yace Allah xan miki kuka Tace imma kayi xan share maka😀 Yace Niko my Luv Fari tamai da ido🙄 Tace bye my sweetypie saika dawo... Tana fa'din hakan tashige ciki.... Murmushi KHAMIS yayi shidai yana matuqar san Matarsa bayajin xai iya haqurin rashinta gareshi.😀 Tashin motar yayi Yana kiran Dadynsa Da murnarsa Yace Dady xaka samu jika nan da 7mnts 😀 Da murna dadyn nasa ya biye mai yana me cewa naji da'di my son😀 Suna gama wayan ya kira momynsa itama tana 'dauka Yace albishirinki momyna Tace goro kuma fari tas Yace 'Yarki Aunty XEE tanada ciki😂 Ai xambur Momy tatashi dana cewa banasan wasa my son gayamin gaskiya Dariya yayi Yace inni nayi miki wasa ai junior baxai miki ba Momyna. Ki kirashi kiji Wlhi tana da ciki mubarshi a 7mnths🙈 Murmushi Momy tasake Tace toh bani ita injita Bana tare da ita dan tana gun Aunty LUUVAH saidai in koma in bata tunda banyi nisa ba Tace aa kabarta tadawo my son sannan katambayeta me takesan ci Da Murmushi Yace toh momy Ko kuma bari na kirata Yace ok bye..... 'Yar Uwa inada ciki wata biyu da sati biyu🐠💃🏼 XEE tace da SAILUBAH hakan Da sauri SAILUBAH Tace kai haba 😀 Tace wlhi da gaske Murna Sosai SAILUBAH tayi bayan sun nutsu ne Tace ina jinki kince da magana gayamin na xa'ku inji miye ne.... gyara zama XEE tayi tana dariya Tace hmm sirikar tawace tasani a gaba game da batun ciki.... Ni naga tadena sakewa dani Ko magana nayi mata daqar take amsawa Tun abin baya damuna hardai yaxo ya fara damuna Shine nace yau xanxo mutattauna akai Ai in gaya miki muna zuwa gun junior yana min scanning yaga ina da ciki har wata biyu da sati biyu😀 Dariya SAILUBAH tayi Tace hmmm har yanxu Ashe akwai irin wa'yannan sirikan Yaushe akayi Auran.. XEE tata6e baki Tace ganemin hanya dai...... Kan SAILUBAH tayi magana wayan XEE ta'dau ringing Tana dubawa taga Momyn CE Takalli SAILUBAH Tace ke gata tana kira SAILUBAH Tace 'dauka muji....... 'dauka XEE tayi tana me cewa hello Momy........ Daga can 6angaran Momyn KHAMIS ce tsaya da waya a hannu kallo 'daya xaka mata Kasan tana Cikin farin ciki Tace 'yata kina dai lafiya ko Qiftama SAILUBAH ido XEE tayi Tace lafiya lau Momy.... Murmushi Momyn tayi Tace naji abin farin cikin daya samemu kikula kanki dakyau kinji Da jin kunya XEE tafurta toh Momy Insha Allah.... Me kikesan ci na dafa miki XEE tawaro ido Tace banajin sha'awar Komai Tace haba 'yata fa'di mana aiba Komai bane Murmushi XEE tayi Tace toh tuwan albo miyar ku6ewa da man shanu Da murna Momy Tace Yauwa 'yata Insha Allah kina dawowa Xaki samu a dining yana jiranki Murmushi dai XEE taqara yi Tace toh nagode momyna saina dawo. Toh Momyn Tace da kashe wayan tanamai farin ciki Sosai XEE ko suna ha'da ido da SAILUBAH suka sheqe da dariya tare da tafawa kuma atare suka furta heyyy sirika taji batun jika😂 SAILUBAH Tace ni naga rayuwa ni FATEEMA Wato wasu sirikan haka suke. Sam basu jin kunyar nuna damuwarsu akan qaddarar da Allah ya 'dorama marasa haihuwa da wanda rabansu yake da nisa..... XEE ta camke da ga irinsu dai kingani... Tanajin batu harda son yimin hidimah SAILUBAH Tace mungama da wannan kiji dani da Junior kuma XEE Tace wani abu ya kuma faruwa ne kuma bayan Wanda kikace min jiya Girgixa kai SAILUBAH tayi Tace aa kawai inaso ki gayamin dalilin da yasa nakejin shakkarsa ne Murmushi XEE tayi Tace xai iya yuwuwa kodan dan kwarjininsa ne yake sawa kikejin shakkarsan Qara girgixa kai SAILUBAH tayi Tace bana tunanin haka dan ko kallona yayi jikina mutuwa yakeyi Idanko ya kafeni da idansa rikicewa nakeyi Musamman idan hakan ya 'dau lokaci gani kawai nakeyi RAMADAN 'dinane Murmushi dai XEE taqarayi Tace hmm indai hakane toh ba shakka yafara tufeki da addu'a ne kamar RAMADAN namu😂 Waro ido SAILUBAH tayi Tace mexaisa yayi min hakan Tace kika sani ko Yana San cigaba da killacekine kamar yanda 'dan uwansa yayi miki abaya Matsowa SAILUBAH tayi Sosai jikin XEE Tace ban ganeba pls bani haske 😳 Dariyace ta kwacema XEE Tace aike baki gane Komai imba ganinsa kikayi abayyane ba.....😀 Amma kisani Junior ba kamar RAMADAN bane kibari ahankali xai gyara tunaninki Danni tunda ya cilla miki kuliya nakejin tsoransa 😳 Dan kallo 'daya Xaki masa kisan hatsabibi ne...... Kan SAILUBAH tayi magana Cikinta ya mur'da mata Aiko da sauri tadafe cikin tana cewa Wayyo Allah Da sauri XEE Tace lafiya Cije baki SAILUBAH tayi bayan ya'dan lafa mata Tace Wlhi XEE tin jiya nakejin wannan ciwan Cikin ya hanani sakewa Tace toh kinsha magani Tace eh nasha amma ban wani ji Komai bah Ya kamata ki gayama junior ya dubaki gobe gaskiya Harararta SAILUBAH tayi Tace saiya rainani ai Kawai sai inje ince mishi naxo ya dubani XEE Tace eh mana Kuma kina wani maganar raini ai kibar batunshi kawai dan indai rainine junior ya gama rainaki Tsaki tajah Tace Wlhi jira nake yayi min wani iskanci da rashin kunya inyi maganinsa da kyenkyaso..... Ke kuma yayi maganinki da kuliya ko😀 XEE Tafa'di hakan da Murmushi...... Haka ko akayi. XEE da KHAMIS Suna komawa gida XEE tatarar da liyafar da momy tayi mata na tuwan albo da miyar ku6ewa Xama tayi taci ta qoshi KHAMIS nakallanta cikin matsanancin sonta Anan kiran HAMEEDA yashigo wayanta tana maice mata natayaki murna Sosai Aunty Murmushi XEE tayi Tace nagode sosai HAMEEDA Murmushin itama tayi Tace Bakomai ai.... Junior ko da yamma daya dawo Bayan ya gyara kansa saiya nufi gun masoyiyar tasa da yaransa.... A harabar gidan yaganta gefe guda kuma Su KHAULAT ne suke wasansu Kallo 'daya yayi mata yasan akwai abinda yake damunta Dan haka ya xauna kusa da ita Yace uwar 'YaYaNa meyake damunki.... Harararsa tayi Tace ban sani bah Ta6e baki yayi Yace Karki sanin mana dan antambayeki shine xaki gayamin magana.... Afusace Tace angaya mana nice gaba dakai kokaine gaba dani Wlhi Junior kafita daga idona Murmushin tura haushi yayi mata Yace idan nafuta daga idan naki na tabbatar bake ba rufeshi Idan ko kika rufe shi makauniya Xaki xama wawiya kawai.... Sororo SAILUBAH tayi tarasa dalilin dayasa Junior ya bala'in rainata haka Memakwan tanemo kallamar daxata gayamai danta hucce haushinta Saikawai tasamai kuka Tanayi Yana bin bakinta da kallo tare da aika mata wani Sirrin taccen kallan Wanda yake narkar da xuciyar wanda akayi danshi Kukan nata yana ta6a xuciyarsa Amma bayajin xai iya katse mata shi.... Cak tatsaya da kukan tare da tashi daga gun da daniyar shigewa falan nasu Dake yana san takulasa su'dan ta6a fa'dan nasu sai kawai ya bita da kalmar. Si si si......... Afusa tajuyo Tace acan baya yayanka yayimin wannan kiran karuwan Najah mishi kunne akan ni ba karuwar bace....... Au haba😳 saiyace miki me Junior ya katseta da fa'din hakan Da kuka ta gallamai harara Tace 'dan iska kawai Allah xai ha'daka da daidai kai tagyaramin tunaninka..... Da Murmushi junior ya qaraso gabanta Yace ai kece daidai ni my..... Shuru yayi yana 'daga mata gira... Wata muguwar harara ta banka mishi dajan tsaki xatabar gun Yasha gabanta yana mai cewa haba mana 'Yan matana..... Ke kin isa kibar nan gun ban nuna miki ni cikakken 'dan iska bane Ja da baya SAILUBAH tafara yi tana mai mishi kallan tsoro dan batasan me xai mata bah Murmushi yaqara yi bayan ya kaita qarshen bango qiris yarage ya jikinsu ya ha'du da juna..... Ganin haka yasa ya tsaya da Cewa yarinya sai tsoro Amma bakinta bai dena tsiwa ba😀 Jeki kawai.... Xanyi maganinki ne duk ran da kika shigo hannuna Amma kafin nan 'dan gayamin gayamin mana me yake damunki my babyna Gaban SAILUBAH Yafa'di jin yanda ya canja mata kuma yana tambayanta cikin lallami..... 'Dan qarfin hali tayi ka'dan ta harareshi Tace nace maka bansali bako... Ko ana dolene sai kasan me yake damuna Murmushi yayi dakai 'dan yatsansa kan le6anta yana shafawa kamar yana saka mata jambaki...... Qara ta kwalla da cewa kyenkyaso kyenkyaso..... Da matuqar raxana Junior yayi baya Yana waige waige Mara kunyan banxa mara kunyan hofi Xanyi maganinka ne Wlhi Har 'dakinka xanxo in gyara maka xama.... SAILUBAH CE me fa'din hakan tana mai hararansa Kana tayi falansu fuskarta cike dajin da'di Dake tsoran kyenkyaso ajinin Junior yake da sauri yabar gun ya nufi gun yaransa su KHAULAT dan gani yake da gaske kyenkyason yana gun😂 Daran wannan rana dai haka SAILUBAH tayishi cikin ciwan ciki..... Ana kiran assalatu kuma ya lafah mata Anan ta'daure tayi Sallah takwanta Koda Junior yaxo 'daukarsu KAULEET mah tana bacci ya tambayi Kakah Tace tana bacci ta lurama kamar batajin da'di ne Jiki asanyaye yakaisu skull Hakan kuma yayi office yana me tunaninta..... Yana aiki Yana tunanunta can yaga baxai iya samun nutsuwar data dace ba. Sai kawai yafara mata rubutu kamar haka ```Fatan alkairi gareki my Luuuuu. Hankalina yakasa kqanciya saboda qaunarki``` ```Kitemakeni Ki gayamin me yake damunki. pls my baby``` SAILUBAH ko na kwance wayan na hannunta lokacin da sakwan ya isa gareta..... shuru tayi Bayan takaranta. Can tabashi da amsa da. ```Ba abin da yake damuna``` ```Fa'di gaskiya dai dan Wlhi akwai abinda yake damunki``` ```Toh kai waye daxan maka qarya 😙``` Tsaki Junior yajah da janyo 'dayar wayarsa ya kirata Tana ganin kiransa tayi Murmushi dan Kakah tace mata 'daxo dayaxo ya tambayeta Ashagwa6e ta 'dauka da muryar mara lafiya Tace mara kunya meyasa kakira ni😡. Murmushi yayi Yace 'dan gayamin meyake damunki pls Tashi tayi daqar da cewa ka dameni fah Akan wane dalili xaka takuramin akan lalle saikaji meyake damuna Cikin lallami Yace haba mana my baby kinhana xuciyata nutsuwa kinsata cikin fargaba tunjiya Ki temaken ki gayamin Kinga ke 'Yar amanata ce Dole naji matsalarki..... Da 'dan jin haushi Tace kar kagafah dan yace kakula dani kanemi takuramin kana 'dan micicinka dakai😡 Dariya CE😂 takwacema Junior danjin yanda takirashi da 'dan micici. Gaskiya yakamata yayi maganinta danta rainasa da yawa. Cewar xuciyarsa... Bai nuna mata jin haushinshi ba danshi damuwarsa yaji meyake damunta ko hankalinsa xai kwanta Still da lallami Yace dan Allah dan soyayyarki da brother ki gayamin dan Wlhi kikaqi fa'damin yanxu xanxo gidan kuma Allah saina saki kuka..... Dan haka maxa fa'da min kan raina ya 6aci😡.... Afusace Tace ya 6aci mana.... Haka kikace ko.. Yayi saurin katseta da fa'din hakan Shuru tayi xuciyarta nayi mata xafi tarasa dalilin dayasa takejin shakkar wannan 'dan iskan yaran😂....... Xansiya miki ice-cream Babyna pls gayamin kinji.... A shagwa6e Tace ciwan ciki ne yake damuna... Ai shikenan yanxu xaka barni na huta ko... Jan numfashi yayi da cewa inaso kixo kisameni a office 2 4:00pm Yana fa'din hakan ya kashe wayan... Kobakomai ya'dan samu nutsuwarshi Itako gyara kwanciyarta tayi tana fa'di aranta baxata ba... Wani ikwan Allah hud'u nayi ciwan ya kum cafkarta Daqer tasamu kanta aiko gudu gudu tayi wanka tashirya lokacin yayi daidai da dawowarsu KAULEET daga madarasa sukace xasu bita Takalli Khairat wacce ta 'daukosu Tace kiji dasu pls yanxu xan dawo. Tace toh Aunty Bata 'dauki wani lokaciba saigata a asibitin Da nutsuwa tayi parking tafito tana qarema asibitin kallo Sosai dan wannan ne xuwanta na farko... Sosai asibitin ya burgeta mutuqa danya ginu ginin wayewa Tana tafiya ma'aikatan gun nabinta da kallo da yaba kyawunta Komai nata yayi SAILUBAH fata ha'du ha'duwa taban mamaki qaryane kamata kallo 'daya batare da kaqara na biyu ba. dukko ajinka (Dake😀 nake 'Yar uwa. duk mesuna FATEEMA ni Rahamat nace kin ha'du kinyi ba abin kushewa gareki ina miqa gaisuwata gareku masu Suna FATEEMA✋🏻) Sabo da tsabar kallan da maryam take binta dashi ne yasata nufarta da murmushi Tace qanwata ina tambaya ne A nutse Maryam tace toh inajinki madam. office 'din wani doctor junior yakesan Ki nunamin Shuru maryam tayi da shiga tunani Waye Junior.... Can Tace bangane Waye bah madam Dafe goshi SAILUBAH tayi dan tunowa datayi tabar wayanta a mota Tajuya da niyar komawa wata doctor chiyomah Tace ko doctor Sadeeq kike magana sister Da sauri Tace Yah shi nake nufi Tace muje in nuna miki... Haka suka jera tanuna mata office 'din Tana turo 'kofar Suna ha'da ido dashi... Yana xaune kan kujera tana juyawa dashi yana yima wani bayani akan damuwarsa Da Murmushi Yace Wlcm my baby... Ya fa'di da tashi daga kan kujeran da mata nuni akan ta zauna akai Sanda ta hararesa kafin ta xauna Ganin haka yasa ya maida kallansa ga mutumin da yake ma bayani Wanda yasaki baki yana kallansu.... Yace mai nagama dakai pls idan kafita kacema shafi'u baxan qara ganin kowa yau ba sai gobe in Allah ya kaimu. Asukurce mutumin Yace toh nagode doctor Allah ya saka Yace Amiien.... Bayan futar mutumin ne ya maida kallansa gareta Cikin raini Yace yanxu 4:26 haka mukayi dake Tace Banga damar xuwa lokacin ba akwai abinda xakamin ne.... Murmushi yayi Yace a office 'dina kike fah malama Wlhi kikamin rashin kunya dukan tsiya xan miki Dariya tayi mai kawai😀 Ganin hakan yasa ya koma kusa da ita da xama kan table 'din Suna fuskantar juna Yace toh gayamin ya kike jin ciwan..... Yanda yasata agaba da kafeta da ido hakan ya tuno mata Senior sai taga kamar shine Dan haka cike da shagwa6a tagaya mai yanda yake mata Shagwa6ar na tsuma xuciyar Junior ya lumshe ido da cewa xan miki scanning yanxu inga matsalar Sai yanxu tatuna dawa take Lalle ne ma. Sai kawai ta'daga rigarta yaga cikinta ya qara rainata Sam baxata yarda ya mata ba. Dan haka Tace ni bawani scanning 'din da xakamin kaban magani kawai Yace toh baxan bayar ba dan sinaga matsalar Tace Wlhi baxaka....... Saurin katseta yayi da cewa Wlhi saina miki Kinma rainani da yawa yarinyar nan Wane doctor kika sani me hankalin daxai baki magani bayan baiga matsalarki ba..... Yanda tashagwa6e mai fuska kamar xatayi mai kukane yasashi tsayawa da xancan nasa yana harararta da cigaba da cewa Kika min kuka saina wau wan ka miki mari wlhi😆 Waro ido😳 tayi da cewa yanxu saika iya marina... Matsowa kusa da ita yayi Yace kigwada yimin musu kigani man.... Kanta qara magana sukaji ana kwankwasa 'kofa Tsaki yajah ahankali Yace yes... Maryam CE tashigo..... Yanda taga junior yasa SAILUBAH agaba kamar wani mijinta shi yasa xuciyarta bugawa tayi saurin safe qirjinta😳 wani tari ya kamata hankakinta ya bala'in tashi.... Dake shi'din yasan meya haifar mata da hakan Murmushi yayi da bu'de wani qaramin furiji dake kusa dashi ya 'dauko ruwan gora SAILUBAH tayi saurin kar6a tamiqa mata tana cewa sannu meyasaki tari haka.... Kar6a maryam tayi duk tawani rikice. saita kasa shan ruwan SAILUBAH ta qura mata ido tanasan yin wani tunani.... Murmushi Junior yaqarayi kana ya 'dauki cup da zagowa gun maryam 'din ya kar6i ruwan da tsiyaya mata har lokacin da Murmushi akan fuskarsa. Yace bu'de bakinki nabaki Sai lokacin 'dan hakalinta ya dawo tayi saurin girgixa mishi kai da cewa aa barshi... Wani shegen kallo ya sakar mata Yace ban isa ba kenan Da'da girgixa mishi kai tayi da bu'de bakinta... ahankali yakai ruwan bakinta. Dammmmm gaban SAILUBAH ya fa'di. Kuma daidai lokacin ya kalleta tako aika mishi da mugun kallo......... Aiba shiri yasaki cup 'din jikake tass ya fa'di qasa da fashewa........ Dukkansu bin cup 'din sukayi da kallo SAILUBAH tajah wani shegen tsaki dajin haushin junior tare dajin tsanar maryam lokaci 'daya.... Da sauri suka kalleta dan baqaramin tsaki tajah ba Da kuma saurin maryam Tace dan Allah kiyi hakuri madam bansan...... Saurin katseta Junior yayi tawajan kama hannunta daniyar subar office 'din Suna fita ya sake hannun nata Yace meya kawoki guna.... A rikice Tace maganar gaskiya na manta meya kawoni doctor. Amma dan Allah kayi hakuri hakan baxata qara faruwa ba Yace baxanji da'di ba idan taqara faruwan... Murmushi tayi Tace Insha Allah baxata qara faruwan bah Amma dan Allah matarka CE Wani kallo ya watsa mata wanda yasa jikinta mutuwa Yace kina da matsala da hakan ne Girgixa kai tayi Tace aa kawai dai naga tana da kyaune Murmushi yayi da cewa kije gida a nutse mery... Ina kuma miki fatan idan kintashi yin bacci kiyi mafarkin daxai faranta ranki... Da 'dan murmushin yaqe Tace nagode.... SAILUBAH ko yana shigowa tarufeshi da maseefa fa'di takeyi ban ta6a ganin Mara kunya kamarka ba. Dan tsabar iskanci agabana xaka ba 'Yar iskar budurwar ka ruwa abaki😀... Wato itama tarainani kamar yanda karainani ko..... Kallo 'daya yayi mata ya gano bama baman kishi dajin haushinsa ne cike tam a kwayar idanta Idan Yace baiji da'di ba yayi qarya Dan haka yayi mata shuru kawai Yana jinta dayin rubutu jikin wani book Ganin yayi mata shuru shiyasata fashemai da kuka... Tana tuhumar kanta da meyasa taji wani abu game dashi ne yanxu Shiko arikice ya bar rubutun yayi gunta yana lallashinta da cewa aransa ita Komai kuka ne.... Toh kiyi shuru mana Wlhi baxan qarayin hakan a gabanki ba Aiko jin hakan yasa taqara volume 'din kukanta da qarajin haushinsa wato baxai dena kwatakwata ba. Bayan hakan take San ji Batayi aune ba taji yana share mata hawaya da tsaftataccan hankacif 'dinsa yana cewa kiyi hakuri my baby baxan qara ba kinji Harararsa tayi Tace dashine ko kusa baxai yimin hakan ba. Danshi me qaunata ne kuma yasan darajata baya bari wani ya raina ni. Gaskiya nayi Babban rashi arayuwata😭 my baby my RAMADAN Qanina ka dawo gareni.... Kishine ya motsoma Junior Amma dake lallashinta yake San yi dan yagama saninta yanxu dan ta'dauki awanni tana kuka ba Komai bane. Hakanne yasa bai bari kishin

Chapter 27 of 33