Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
naki Tace oho fah Na dai CE mishi ya shirya kalmomin daxai gayamin wa'yanda xan tunkari Abban dashi Yace wai yarigada ya gama shiryasu XEE tayi dariya Tace hmm Wlhi RAMADAN ya gama samunki SAILUBAH. Gashi yafitoh da manufarsa qiri qiri akanki. xai juyaki kamar waina. Kuma gashi qaramin yaran da kika raina. Shiyake qoqarin lalata miki tunani SAILUBAH tajah tsaki Tace ina ganin fah jifana yake da addu'a dan kinsan gwanine wajan addu'a XEE Tace aikema ba baya bah Saiki bishi da taki Tace Xanyi qoqarin yin hakan Ni yanxu damuwata 'daya kar lokacin da Abban nawa ya ibam min yacika RAMADAN 'din ya tiqani da qasa XEE tayi dariya Tace shegen yarone ya iya da kansa. Sai kiga kuma ya baki mamaki xuwan lokacin Tace hmm niyanxu fah tsoro yafara bani XEE Tace haba saikace ba mace bah. karya wani baki tsoro. Idan lokacin yayi Yanemi kawo miki shirme kice ya Aure ki👈🏻 kawai....... Da sauri SAILUBAH tawaro ido 😳 Tace what.... Kinsan ko me kika CE. bayan kinfi kowa sanin banda burin Auran qaramin Ina kike tunanin RAMADAN xai kaini Pls Ki share kawai dan ba Abu bane me yuhuwa😔 XEE Tace kawai nasan me yasani fa'da miki hakan Kigane mana SAILUBAH Wlhi ina tabbatar miki idan kikayi wasa kikaci gaba da biyema RAMADAN saikin fa'da tarkwan MASEEFAR SOO fiye da yanda naji akan KHAMIS Tananne Xaki gama da makircinsa gabaki 'daya idan kikace ya Aureki Sai kitsaya kiji mexaice miki Sauran bayani xan gaya miki in mun ha'du. Xan saurari abokin Mustafan Dan yace min anjima xaixo xan gaya mishi Gaskiya inada wanda nakeso Ta qarashe da kashe wayan bata jira cewar SAILUBAH ba SAILUBAH tayi sororo da waya ahannu kafin Tafa'da tunani me xurfi akan zancikan XEE FAWAS ne yasaka Dadynsa agaba yana xuba mar shagwa6a fa'di yake. Dan Allah Dady kuje gidansu HAMEEDA da gaske xa'a 'Aurar da ita ga 'dan uwanta. Banaso na rasata Dadyn nasa ya kallesa Yace katabbatar yanda kake santa haka take sanka Yace Wlhi Dady fiye da yanda nake Santa take sona Dadyn ya ta6e baki Yace ai shikenan. FAWAS ya rungumi Dadyn nasa Yace I luv u Dady Yace me 2 my son Yace toh yaushe xaku Yace gobe Wani tsalle FAWAS ya daka yana murna Yace Allah ya barmin kai my Dady....... Ni kuma ya kashe maka ni ko Momy tafa'di hakan tana shigowa room 'din Xuwa FAWAS yayi Yakama hannunta yayi mata kiss. Yace idan kika tafi Momy nima binki Xanyi Yana fa'din hakan yabar room 'din dan yaga fuskarta a murtuqe yana tsayawa dogon magana qila ta canjama Dadyn nasa ra'ayi Taxauna kusa da Dadyn Tace ina rokwanka da Allah karka biyema banxan tunanin FAWAS Akan me xaije ya 'daukomin 'YAR QAUYE ga 'YAN BIRNI masu aji yaje ya kwasu mana wahala Gaskiya ban yarda da wannan Auran nasa bah Dan haka kawai naji natsani yarinyar Dadyn yajah numfashi Yace kiyi hakuri Momyn FAWAS baxan iya barin 'dana cikin damuwa ba Shi ka'dai Allah yabani ina sanshi bana San tashin hankalinsa Tunda Yace yaji ya gani yana Santa ni kuma xan xanje ga iyayañta dan Aura masa ita Ke in banda abinki idan ya Aurota basai Ki maida ita 'Yar birnin bah Shuru Momyn tayi dan tasan tunda yace xai Aure masa ita tatabbata baxai fasa ba Nan taji wata tsanar HAMEEDA ta kamata cikin ranta Ta kuma sa aran nata xataci ubanta inhar tayi kuskuran yarda ta Auran mata 'da.... Farin ciki fal xuciyar FAWAS yake shiri dan kaima abokana yan nasa labari Sosai ya shirya cikin shigar qananun Kaya ya 'dauki wayarsa yana niyar kiran KHAMIS dan suha'du gidansu RAMADAN.... KHAMIS ko fa'dawarsa gado bayan yagama waya da RAMADAN bacci yayi abinsa bai samu tashi ba har sai kusan qarfe 1:20pm Ya sake wanka yayi Sallah Sannan yahau shirya kansa Yana feshe jikinsa da turarene yaga kiran FAWAS ya shigo wayar tasa Ya 'dauka yana cewa yane FAWAS Yace pls muha'du yanxu gidansu senior Yace Owkie nima yanxu nake San kiranka mu ha'dun ba matsala FAWAS Yace OK Suka ajiye waya Nan KHAMIS ya ibi ku'di da'dan yawa yana tuna jiya ya hango jakar tauraruwar tasa ba ku'di Ya fitto falo ne yaga Dad 'din nasa da mum Suna cin abinci Ya kallesu ka'dan Yace barka da ranah mum Dad Suka kallesa batare da sunce Komai ba Ganin haka yasa yanufi fitta.... Mum Tace bakaci abinci ba xaka fitta Yajuyo a shagwa6e Yace na qoshi Tata6e baki Tace toh asauka lapia Ya fitta yana jin haushin iyayan nasa Dad ya kalli mum Yace lalle idan yadawo kisashi agaba yaci abinci Dan xan iya jure Komai akansa Amma banda abinda xai ta6imin lafiyarsa Mum tayi Murmushi Tace toh Inaga fah yafara fushi da mune Dad Yace eh ga alamu sun nuna kam KHAMIS ya kalli direban gidan nasu Wanda yake kai Momy unguwa Yace yau banajin fita da mota pls kaini gidansu RAMADAN Yace toh ranka ya da'de Senior RAMADAN da junior ko wani Kaya suka saka iri 'daya Wanda ya bala'in kar6arsu Dadyn nasu ne ya kawo musu Duk iya ha'duwarka idan kayi tuxali dasu saikaso ka qaraci kalanka akansu Senior da junior sun ha'du iyakar ha'duwa Baka isa ka banbance tsakaninsu waye kasani bah Kamar tasu ta6aci Abu 'dayane xai saka gane waye wannan waye wancan shine wayewarsu Junior yafi senior wayewa nesa ba kusa ba Dan daga idanshi da kallansa xaka gane hakan shiyasa yakejin kansa as big gay Yayinda Senior yafi junior shagwa6a abayyane Da iya makirci da bin ra'ayin mutum ya 6oye nasa Idan ko yaso baiyana nasa ga Wanda yakesan baiyanawa Saiya marairaice yadinga aika sakwan nasa cikin hikima da aiki da hankali da nutsuwa Hakanne yake sawa mutane da dama suke ganin wayewarsa da tabbatar da cewa ya iya da kansa Junior ya kalli 'dan uwan nasa Yace 'daxo kada'de agun Auntynka Allah yasa dai ta yafe maka Yayi Murmushi Yace ai bayanda xatayi dani 'dan Uwa dole ta yafemin Junior yayi Murmushi Yace salan soyayyarku tana burgeni Sosai brother. Idan kuka xama ma'Aurata abin xaiyi da'di da bada sha'awa. Senior Yace hmm kaidai bari Ina tausayama soyayyya da qauna idan muka xama ma'Aurata nida ita Junior ya qara yin murmushi Yace kayi kyau Sosai wannan wankan na Waye Yace natane Amma xanyi rakiya. Qila in duba wata budurwata idan nayi ra'ayi Kan junior ya qara magana saiga FAWAS ya shigo ya tsaya yana kallan wannan yana kallan wancan Yace gays baxai iya gane waye senior o junior ba Wlhi Junior Yace harda rantsewa Yace ai gaskiyane... Senior ya dafa shi Yace toh gani senior FAWAS yayi dariya Yace aha Yanxu nagane tawajan qamshin ka Kasan naka da nashi ba 'daya bane Junior Yace shine yasa ai nace muku xaku dinga ganemu nan gaba FAWAS ya xauna kusa da junior yana bashi amsa da cewa aikuwa kayi gaskiya Senior Yace yadai Yace kaidai bari Yau ina cikin farin ciki over Senior Yace kamar ammaka albishir da cewa gobe HAMEEDA xata xama mata agareka FAWAS yayi dariya Yace kusan haka Nan ya kwashe yanda sukayi da Dadyn shi ya gaya masa Junior yayi Murmushi Yace angama da shafinka Saura KHAMIS da brother FAWAS yayi Murmushi Yace aikowa danni yanxu 'dan tayasu addu'a ne Senior yayi yaqe Yace hmm kunsan Auntyna ahannuna take sai yanda nayi da ita Ina tabbatar muku har ayanxu nafiko kwanciyar hankali a soyayya FAWAS ya 6ata fuska Yace ban gane bah Senior yayi dariya Yace nufina kai momynka bata lamunce maka ba. Kaga Akowane lokaci xata iya jefaka a matsa Haka KHAMIS baida goyan baya akowane bangare Ni kuwa fah😳 ina yin ihu na kwanta ciwon qarya ayanda Abban Auntyna yake kan dukin xuciya da ita Nace ita nake so xai Auramin ita. FAWAS yayi shuru Junior Yace idan kuma tace bata sanka fah. Senior yayi wani shegen Murmushi Yace baxata CE ba Saidai xata ban wahala Sosai 👌🏻 Dan dana kwanta ciwan saitafi kowa rikicewa Nina san da hakan 👈🏻 Tanajin silar ciwan xata bada ha'din kai Da xaran mun xamah ma'Aurata saita fara ban wahala Idan kuma na mata ciki🙊 sai tafara sonah😊 Ya qarashe xancan da Murmushi..... Wanda hakan yayi daidai da shigowar KHAMIS Ya kallesu Yace anyi gwulmata Junior Yace Sosaima Yayi Murmushi da xama yana cewa kutayani Baqin ciki gobe xa'akai sadakin shegiyar yarinyar nan Senior yayi dariya Yace to saime Cikin fusata KHAMIS Yace Aunty XEE mana. Atare suka saka mai dariya. FAWAS Yace baka fara rikicewa Dad mum bane shiyasa Yace hmmm ai kabarsu kawai xan gyarosu Dan inaji Dad na fa'din idan nadawo tasani gaba naci abinci xai iya jure Komai Amma banda lafiyata Kaga tunda naji Wlhi Suda kansu xasu nemi bani XEEE Senior Yace yes kace kasamo mafita Yace Sosai Yandai kurakani inje gunta dan Allah Wlhi haka kawai yau tun Asuba idanuna sukesan ganinta FAWAS Yace munji Amma kafin nan bara na baka labarin yandau tawa matsalar takau KHAMIS yawaro ido Yace kana nufin dad mum sun yarda da HAMEEDA matsayin surukarsu Yace eh Amma waccan 'dan iskankan ya rikitamin kwanya akan Momy Kasan duk abinda Yace 'dad'dai kune basu yuhuwa Yafa'da yana kallan senior RAMADAN Wanda yake Murmushi KHAMIS yajah tsaki Yace shareshi gayamin pls Nan FAWAS yabashi labari KHAMIS yayi dariya Yace da gaske indai Hakkane Momy xata iya bata maka shiri Shawara 'dayace shine kadinga lalla6ata duk abinda Kasan tanaso kadinga yi mata Insha Allahu xata hakura Kaga Komai yayi daidai kenan Yace toh xan gwada in gani kasan tsohuwar tafiya rikici ne KHAMIS Yace har takai nawa tsofaffin Junior yayi Murmushi da girgixa kai Senior Yace toh yanxu ina muka nufah Da sauri FAWAS Yace Qauyan takai..... KHAMIS ya gallamai harara Yace gun Aunty XEE dai Senior yayi Murmushi Yace toh muje ko Junior yatashi Yace bara in rakaku mota FAWAS Yace baxaka bimu bah. Yace aa Wlhi ina buqatar hutu Sosai yau. Gawani littafin Auntyna Rahamat da nake karan tawa KHAMIS Yace me sunanshi Yace wai shi SADEEQ🍇 Senior Yace aisai kata fama... Sunfitoh harabar gidan nasu ne sukaga fitowar Momy tana cewa Yauwa Ku kiramin Auntynku SAILUBAH nakirata har yanxu shuru Kan suyi magana saigata tashigo Momy taqara she da cewa Yauwa gatamah 'Daya Bayan 'daya SAILUBAH take gallansu Duk sunyi Sosai sai qamshin turare suke Tace kaga samarin banah. Sai ina haka FAWAS Yace Aunty qauye Atare SAILUBAH da Momy sukace qauye Yace eh Momy Tace gunwa Ya Sosa qeya dayin shuru Ganin haka yasa Momy shigewa cika tana cewa maxa xo nan SAILUBAH Tace toh Momy Ta maida kallanta ga senior da junior takasa babbance Waye natan acikinsu Tata6e baki da shigesu... Har takai 'kofar falan senior Yace Auntyna Tajuyo Yayi saurin xuwa gurinta Yace kinyi kyau Sosai Dama tasan tayi kyau dan yanxu tayi wanka Tace kaima haka 'dan Qanina Yace toh tsaya na mana photo Tace toh Ya karkace ya 'daukesu Yace wow munyi kyau Sosai tamkar masoyan cikin film 'din *luv story* Tace ban San film 'dinba Ya watsa mata wani kallo cikin shagwa6a Yace kina San kigani Tace aa Yace toh shikenan saimun dawo Tace katawo min da ice-cream pls Yace angama my Aunty Tana kallo suka shige mota junior ya rufe yana fa'din saisun dawo suka ficce daga gidan Lokaci 'daya suka ha'da ido da junansu Junior ya 6alla mata harara dayin part 'dinsu SAILUBAH tayi Murmushi Tace xaka gane kuranka ne yanxunnan 'dan iska Tafa'di hakan da shigewa cikin falan Momy Aikine da Momyn xatayi wasu baqi 'yan uwanta shine takesan Su ha'da musu abinci merai da lpy Kafin sufara SAILUBAH Tace bara na'dauko wayata agida Momy Tace toh kiyi sauri Tace toh Direct SAILUBAH gun megadin gidansu tayi Tace BABAH megadi kasamo kyenkyasun Yace eh. Yamiqa mata Su a baqar leta taduba taga sunkai biyar tayi murmushin mugunta Tace nagode Sosai Ahankali tatura 'kofar 'dakin. Junior yajuyo ya kalleta Yayi Murmushi Yace 'Yar daqiqiyar Auntyn brother ya akayi ne Tamai shuru Ya ta6e baki Dallah malama meya shigo dake Nanma shuru mai Saiya tashi yana Murmushi Yace Allah nagode. Maka daka turomin wawiyar nan yau xan nuna miki yanda ake iskanci. Bani kike kira 'dan iska bah SAILUBAH dai shuru tamai tana jin rashin kunyar da yake xuba mata Bata ankare ba sai ganinsa tayi agabanta Yace waye 'dan iska..... Tayi Murmushi Tace kaine Shiko xira hannuwansa yayi a qugunta yana Murmushi Suna qeshar numfashin juna. Xai kai bakinsa cikin nata ta'daga mai ledar hannunta Tace kyenkyaso😊..... Da sauri ya saketa yajah da baya yana xaro ido😳 Yace pls dan Allah Karki cutar dani plssss Tayi murmushin yaqe Tace daga shigowata kakirani da daqiqiya da wawiya ko Yace narantse miki da Allah baxan qara fa'da miki bah Tace rantsuwarka tabanxa In tambayeka man Ya xuba mata ido atsorace Tacigaba da fa'din. Meyasa ka rainani kamai dani tamkar sa'arka Ya Sosa qeya Yace Wlhi Auntyn brother na dena raina ki Tace amsa nakeso kaban Yace nima bansan meyasa ba Tagallamai harara Tace o baka sani bako Yace eh Aiko nan tabu'de ledar saiga kyenkyaso 'daya yafitoh Wani ihu junior yasaka ya daka tsalle sai ganinsa tayi kan gado Idan shi ya fara juyawa hankalinsa yayi bala'in tashi SAILUBAH tazauna gefan gadan tana qoqarin sakar masa wani....... Aiko ya fashe mata da kuka cikin qaramar murya Yace am sorry...... Yana fa'din haka yayi baya luuuuuuu asume SAILUBAH tayi dariya tajuya ta make 'dayan da takalmi Sannan ta'dauko ruwa ta yayyafa masa Aiko nan ya farfa'do yana raba ido yana kallo ta share wanda ta kashe tasa a abun xuba Shara tadawo Tace nayi alqawarin saina saka suma sau uku..... Agigice junior ya waro ido Yace so kike Ki kasheni😰 Ta gallamai harara Tace kamutu man ina ruwana Ya marairaice Yace dan Allah dan soyayyarki da manxan Allah kiyafemin Wlhi baxan qara yimiki Komai Tace maqaryaci kawai Tafa'di hakan da take mishi wani akan gadan Aiko ganin yandan kyenkyason yake nufushi shiyasa yawun bakinsa kafewa Jikinsa yafara karkarwa Ya rumtse ido Yabu'de ahankali. Lokacin yayi daidai da hawan kyenkyason kan qafarsa Nan take idanshi yayi qasa. Jikinsa ya mutu Ashe da'da sumewa yayi SAILUBAH dake yau taso mugunta ko tausayinsa bataji bah taqara make wannan tasashi agefe Sannan taqara yayyafah mishi ruwa Wannan karan bai farfa'do ta da'di ba Dan haka hankalinta saiya tashi ta qara yayyafamai Nan ya farfa'do Suna ha'da ido yayi mata shuru kawai yana kallanta Tayi Murmushi yana kallanta. tada'da futa da wannan Wanda taqara kashewa tadawo Yanda yaga tana qoqarin sakar masa wanine shiyasa shi runtse ido. hawaye ya xubumai Yace AUNTY..... Dan Allah kibarni haka.... Cak SAILUBAH tatsaya dan yanda ya ambaci sunan nata saitaga kamar senior ne yake rokwanta.... Tayi shuru.... Jin shurun yayi yawa ne shiyasa ya bu'de idansa ya sauke akanta Ta hararesa dayin kwafah Tace kaci darajar Yayan ka Tafa'da da ficcewa . Junior yajah numfashi ya dafe kansa Yace Wlhi baki sani kuka abanxa bah xamu ha'du ne Wlhi saina ramah....... Tashi yayi yabita cikin gidan A kitchen yasamesu ita da Momy har sun fara aiki Yace Momy Tace na'am SADEEQ SAILUBAH ta kallesa da sauri Tace mah Momy dama sunansa SADEEQ Tace eh duk dai ana kiransu da Suna 'daya ne Tace OK Yace Momy me kikajin tsoro Tace tsoro kuma Yace eh. Kingani inajin tsoran kyenkyaso Tayi Murmushi Tace ka'dangare nakejin tsoro junior Yace toh Auntyn brother fah Tace SAILUBAH Yace eh...... Kantayi magana SAILUBAH Tace aini ba abinda nake jin tsoro ko momy Momy tayi Murmushi Tace kinman kina jin tsoran kuli....... SAILUBAH takatseta da cewa dan Allah Momy Karki qarasa Junior murmushin mugunta Yace Wato tsoran kuliya takeyi ko Momy Tace harda sumewa ma kuwa Yace yes........ Yayi Wlhi Yana fa'din haka ya ficce Tsoro ya kama SAILUBAH Su senior ko direct gidansu XEE suka nufa Saidai KHAMIS yayi mugun gani dan sun tarar da ita XEE 'din tana hira da Ameer Wato abokin Mustafan dayaso SAILUBAH Ikwan Allah kuma shima xuwanshi kenan Tunda XEE ta hango motar RAMADAN tasan KHAMIS na cikin motar Nan take sai hankalinta yakaso gida biyu Sam sai tadena jin me Ameer 'din yake CE mata FAWAS Yace ga Aunty XEE da wani can fah RAMADAN yaqi qarasawa inda suke yadai tsayar da motar tashi nesa dasu. Yana cewa kut😊 KHAMIS... Wannan xai iya yi maka kwacanta fah😳 kaduba yanda suke daf da juna..... KHAMIS dai shuru yayi musu danji yayi xuciyarsa na masa xafi kuma tana bugawa fat fat fat Nan take hankalinsa ya tashi Ya qurama Ameer 'din ido yanaso ya hango me tagani atare dashi dahar yaburgeta yasata tsayawa dashi.... Bai hango Komai bah. acewarsa sai muninshi daya gani da kuma rashin dacewarsu 😬😬😬 Cikin 6acin rai ya bu'de motar ya fitoh RAMADAN Yace kayi aiki da hankali 'dan Uwa danna lura da yanda hankalinta ya bar kansa yayo kammu KHAMIS yajah tsaki Yace story kenan... Atare FAWAS da RAMADAN suka samai dariya. Yana jinsu ya sharesu Ayanda XEE taga fitowar KHAMIS sanda taji gabanta ya fa'di Tun daga nesa yake aika mata da mugun kallo Ganin yakusa xuwa garesune yasata 'dauke idanta akansa Ya qaraso cikin ladabi Yace barka da ranah yayana Ameer ya kallesa cikin Murmushi Yace Barka Qanina. KHAMIS yayi mishi kallan raini afaqaice Sannan ya maida kallansa ga XEE wacce ta dawo kallansa ya gallah mata harara Yace in gaya masa ne Cikin 'dan rikicewa Tace me kennan Bai bata amsa bah ya maida kallansa ga Ameer Yace yayana ammata miji..... Ameer ya qara tsaidai idanshi akan KHAMIS Yace eh tagayamin Ahankali KHAMIS yajah numfashi Yace ai Ashe kaji Yace eh saidai ai ba'a 'daura ba Afusace KHAMIS Yace Amma dai Kasan bai dace kanemi qara aya akai ba. Ameer Yace eh Yace toh itadin ta Yayana CE Dan haka kabarta kawai Ameer yayi Murmushi Yace naga alama samaree Danga kishi na yawo a kwayar idanka Yace nifah ba neman maganarka nake bah. Kawai kabar nan Saura sati 'daya bikinta Amma kawani xo kana san ka 6ata mata tunani pls Malam jeja da Allah XEE taqurama KHAMIS ido tana hango maseefar kishin da yake mishi yawo a fuskarsa Ameer yayi Murmushi dan yaran yayi masa kwarjini Ya shige motarsa yana cewa toh samarii nabarka da matar yayanka lpy Allah ya baka ha'kuri. Yana fa'din hakan yajah motarsa Idan KHAMIS ya sauka kan na XEE Tace ya tafi fah Ya bita da harara Yace ko Xaki bishine Itama hararar tashi tayi Tace ban sani bah Ya wurga mata wani mugun kallon daya sata shigewa gida batare data shirya ba Yana niyar juyawa ya tafi Babanta ya fitoh.... Cikin ladabi KHAMIS ya gaisheshi Ya amsa da kulawa yana cewa Yauwa dama ina nemanka KHAMIS yayi Murmushi Yace Allah yasa ba lefi nayiba Babah Yace aa bakayi lefiba Dama inaso in tambayeka ne da gaske kai da ZAINAB kuna San junanku KHAMIS yayi qasa dakai Cikin kunya da ladabi Yace eh Babah Kuma ina rokwanka da Allah karka rabani da ita Wlhi ina Santa Babah yayi Murmushi Yace KHAMIS kenan ai Zainab tayi maka girma kaje kanemi daidai dakai mana..... Annabi Muhammadu ya Auri Nanah khadeejah wacce taxarce shakarunsa. BABAH karka rabani da Aunty XEE ina santa inna rasata mutuwa xanyi Babah yayi shuru can Yace toh jeka Allah ya shige mana gaba Yace AmEEn Da barin BABAN anan Yana shiga motar RAMADAN yajasu Suna tafiya KHAMIS na tsaki Dan daya rumtse idansa saiya dinga ganin hotan XEE da Ameer yanda suka tsaya FAWAS da RAMADAN sun fahimci meyake damunsa kishi. dan haka sukaqi kulasa Sai hirarsu sukeyi har suka iso qauyan takai Anan FAWAS yanemi Yaro yakira masa HAMEEDA Kamar Kullun tana cikin hayaqi innah na surfah mata bala'i dan yau tunsafe take mata shi Dan kawai tayi mata asarar tulu wajan ibo ruwa...... Yaro ya shigo yana fa'din ana sallama da HAMEEDA Nan HAMEEDA takalli yaran Tace FAWAS ne Yace eh dan haka yace in gaya miki.... Da sauri tatashi daga gindin murhun tajah hijabinta xatabi yaran..... innah takatseta da cewa uwar 'yan san maxa bidai ahankali karki kwasomin ciki kan lokacin yayi HAMEEDA tayi shuru tana jinta. Tana kuma rayawa aranta FAWAS meyasani da har xaiyi mata ciki😬....... Innah taqara katseta da cewa. Kisan yanda xakiyi kisamammin ku'din tulu na Toh HAMEEDA Tace mata Tana fittowa tagansa kan dakalinsu Yayi mata kyau Sosai Tace Barka da xuwa Yace Barka masoyiyata Tace da fatan kaxo lafiya Yace lau lau Tace kayi kyau Sosai Yace kamar yanda kemah kikayi kyen Tace ina wani kyau ajikin "dan qauye Ya waro ido cikin murmusawa Yace Wlhi ayanxu nafi ganin kyen 'yan qauye fiye da 'yan birni Tace meyasa Yace saboda ke my luv. Kintafi da xuciyata Har takai idan an tambayeni inane garinmu sai kiji nace qauyan takai HAMEEDA ta rufe idanta cikin jin da'di Tace da gaske Cikin kwaikwayan muryarta Yace Allah da gaske Sukayi dariya lokaci 'daya Zama tayi kusa dashi tana fa'din yasu mamah da babah Yace hmm Momy Dadyna Tace eh Yace Suna lafiya suncema in gaisheki Tace ina amsawa Yace yau bakisa turareba Tace 'daukin ganinka ne yasani mantawa Wai har sai yaushe xaka denamin xuwan baxata ne Yace amin afuwa nadena daga yau Tace nayi maka Yagyara xama Yace hmm naxo miki da kyakkyawan labari ne Tace toh ina jinka Yace gobe Dadyna xasuxo Neman min Auranki Cikin murna HAMEEDA takallesa Tace Allah da gaske Yace Allah. Tace Naji da'di Sosai Yace ai nafiki jin da'di dan Allah Allah nake kixama mata agareni Ki koyamin yanda ake xaman Aure Ta harareshi ka'dan Tace kai ko Yace bake kikace ba Tace toh basai ka manta bah Ya tashi yana girgixa kai Yace idan na manta ai namanta kaina Kinsan ba abinda yake raina ayanxu irin Auranki ki'dorani akan hanya Taturo baki Tace har xaka tafi Yayi Murmushi yana kallan bakinta Yace yanda kika turo bakinnan kamar nakama fuskarki na tsotse shi....... 😳😳 Atare shi da ita suka waro ido Dan harga Allah tunaninsa axuci yafa'di xancan Ashe abayyane ya fa'deshi Tace LA LA LA 😳 Dama kaima irin 'yan iskannanne wa'yanda nake ganinsu a film irin turawan nan Cikin ankarewa Yace nima wani naji yagayama budurwarsa acikin irin film 'din Taqara turo baki Tace toh shine nima xaka gayamin Yace toh kiyi hakuri manah dan bansan na fa'da bah Tace Allah karka qara dan maganar iskanci CE FAWAS Murmushi yayi ya shafi gefan fuskarta Yace baxan qaraba YAYATA shikenan Ta 'dagamai kai da qara turo bakin Yace Allah in baki dena turowa bah. xan qara fa'da Ta hararesa Tace toh kaqara mana Allah sai in denah kulaka Ya waro ido 😳 da Murmushi Yace kika dena kulani ai na shiga uku na banu Yanda ya xaro idan shiya bata dariya Tace nima ai nashiga ukun dan nayi gangancin da xuciyata taxugani nadena kulaka. Na tabbatar saina kwanta ciwo Ya qara shafar fuskarta Yace toh YAYATA ga wannan nina tafi bye bye ta kar6i ku'din tana cewa karka kalli kowace mace dan Allah Yace toh YAYATA Tana kallo sukajah motarsu suka qara gaba Wayar KHAMIS tayi qara yana dubawa yaga tauraruwar tasace XEE. Yajah tsaki dan baidena hangota da Ameer bah. Wanda hakan yake qara sa xuciyarsa jin xafinta. Yaqara jan tsaki batare daya 'dauka bah. Yace xanyi maganinki ne RAMADAN yayi Murmushi Yace pls ka 'dauka Yace Wlhi baxan 'dauka bah saina hukuntata....... FAWAS yayi dariya Yace 'dan iska karka 'dauka mana natabbatar yau dai baxayi baccin farin ciki ba Yace mexai hanani yi Yace dan baka tsaya kaji kalmominta ba Tsaki kawai KHAMIS yayi Sannan yama kashe wayarsa gabaki 'daya _______ Kusan qarfe goma Sha 'dayane na dare duk Suna tare yau club xasu Junior na kallansu yanajin hirarrakinsu Fawas ne mecewa Wlhi ba abinda nake sha'a ayanxu irin kiss Senior Yace Shege HAMEEDA ta rikitaka kenan Yace hmmm naso in rage xafi da Aymana KHAMIS yajah wani dogwan tsaki..... Atare senior RAMADAN da FAWAS suka kwashe da dariya FAWAS Yace dallah Malam ka dememu da tsaki. Idan kana San kwanciyar hankalinka kabu'de wayanka mana RAMADAN Yace bar 'dan iska karya bu'de yata tsakin. FAWAS Yace ni tausayin Aunty XEE nema ya kamani Wlhi. RAMADAN Yace nima haka. Nasan yanxu tanacan cikin damuwa ya hanata samun nutsuwarta...... Da 6acin rai KHAMIS Yace lokaci na tafiya in baxa kuje ba nayi gida Atare senior da FAWAS suka tashi Senior ya kalli junior Yace 'dan Uwa katashi muleqa da kai mana. Junior yayi Murmushi Yace aa kuje Cikin sake fuska KHAMIS ya kar6a da cewa pls muje dare dan Allah Junior xaiyi gaddama FAWAS

Chapter 14 of 33