Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
BIRNI. sai kin nutsu dakyau Kin kama mijinki dan inbah haka ba wannan ta wajan tana daf da sace xuciyar mijinki ina sanki dashi pls karki sake taxo ta dama miki lissafi kimin alqawari Murmushi HAMEEDA tayi cikin kuka ta 'daga mishi kai Tace nagode RAMADAN nayi maka alqawari xan nutsu Qara riqe hannun junior yayi Yace ina San Ganin Auntyna dan lokaci na kusantoni.... Gabansu ne ya fa'di. Junior Yace pls brother kaika'dai fah nake dashi Murmushin dai ya qara yi Yace kanada Allah kuma inaso kariqi ibada Sosai kamar yanda nariqe Ahankali suke tura gadan nasa Suna hawaye har suka kai inda SAILUBAH take kamar gawa dan taqi farfa'dowa Ahankali RAMADAN yakai hannunsa ga nata ya riqe gam...... Aiko nan take SAILUBAH tajah wani numfashi ta wangale idanta qur yana kallan sama Al'amarin da yaba likitoci mamaki kenan Ahankali RAMADAN Yace Auntyna...... Afurgice tajuyo garesa... Ganin yanda jikinsa yake shiyasa komai ya dawo mata Wani gigitaccan kuka tasake Tace pls Qanina pls dan Allah pls dan Allah karka min haka Kamanta kace xan Haifa maka yara da yawa. Meyasa xakacemin dama kayi fatan ka rigani mutuwa. Kamanta kabarni nima baxan iya rayuwa ba.... Murmushi yayi mata Yace Auntyna banda lokaci ga 'dan uwana kiso shi dan Allah... Kinsan shikadai ya ragemin Kibama yarana tarbiya ban yarda kisake wani bare ya mallake ki matsayin matarsa ba.......... Yana fa'din hakan Yace la'ilaha'illallah Muhammadur rasulullah. Sallallahu alaihiwasallam. Rai yayi halinsa ga MUH'MD RAMADAN SENIOR..... Wan game ido😳 SAILUBAH tayi Da tashi afurgice. Takalli XEE Tace me kenan😳 Shuru ko wannansu yayi mata....😟😟😟😟 Ganin haka yasa ta shafa fuskar RAMADAN na girgixawa Tace Qanina Ganin da tayi bai motsaba shiyasata sulalewa ta xube a gadan kuma gefan cikinsa Hakan yayi dai-dai da xubewar junior da XEE asume Yayinda FAWAS ya kalli KHAMIS a gigice suma suka xube sume HAMEEDA ta kwalla qala nan take Su Momy sukayo 'dakin........ ❌❌❌❌❌ an canceling wani Babban jigo a SAMAREEN BANAH. Wato Senior RAMADAN Mu fuskanci sabuwar rayuwa da wa'yannan bayin Allah masu karatu... Cigaba..... *To wai mexaisa ni Rahamat in tsaya gaya muku irin tashin hankalin da SAILUBAH tashiga akan mutuwar Qaninta kuma mijinta Senior RAMADAN* *Bayan nasan ku kanku kunsan shaquwa da SOYAYYAR da take tsakaninsu* *Tsayawa fa'din tashin hankalin da tashiga xaisa in cika shafin bayanan da zan muku agaba* *Dan haka Ku kimanta da kanku masu karatu......* 🇭ar akayi arba'in 'dinsu RAMADAN SAILUBAH batasan inda kanta yake vah Abin ne yaxo mata biyu Ga mutuwar mahaifi gata miji Da wannan ne xanji ni SAILUBAH..... Ahankali Junior ya kalleta dan shika'dai ne yaji wannan furucin nata Girgixa mata kai yayi Yace kidubi Allah shi xaiji dake Tun Junior KHAMIS FAWAS XEE Suna kallanta suji hawaye ya xubo musu har hawayan ya dena xubowa suka fara binta da addu'a Duk kwana uku XEE da HAMEEDA sukanje Su 'debe mata kewa da danne xuciyarta KHAMIS FAWAS ko Kullun sai sun dubata. Hakanko yana yimata da'di in kuma Sun tafi hawaye ya xubo mata dan tuna Qanin nata..... Junior shine yake sata a gaba da abinci taci dan samun lafiyarta Idan takallesa kawai xuciyarta gaya mata takeyi dama Qanin nata ne ya ta rungumesa ko tasamu Sauqi Bata iya yin bacci dan tasaba da jikin RAMADAN Saita 'dauki awa a toilet tana tuna yanda takema Qanin nata wanka yake xuba mata shagwa6a Idan junior yasata gaba akan taci abinci tuno Qanin nata takeyi tana bashi abincin Idan taxauna kan kujera saitaga kamar xaixo ya 'dane kan cinyarta yana shafata da xuba mata shagwa6a Idan KHAMIS da FAWAS sukaxo gareta atare saitafa tunanin yanxu Qanin nata xai 6ullo saiko taga junior ne ya 6ollo Sosai junior yayi nasarai shagwa6ata wajan bata kulawar data dace Ataqaice dai Junior ya bata lokacinsa wajan 'dauke hankalinta Sosai akan Komai Ya 6ata tunaninta da bata abinci abaki Ya 6ata tunaninta dayi mata kalmomi masu da'di Ya 6ata tunaninta da ganinsa Komai xatayi shi yake yimata Damah ita 'yar shagwa6a CE dan haka Komai xatayi agabansa ashagwa6e takeyi Yayinda yake daurewa dan ba qaramin jefashi takeyi a maseefa bah Shidai damuwarshi tafuta daga takaba ya bata wata biyu ko uku kafin ya GYARA TUNANINTA *Al'amuran sunfara faruwa ne kamar haka* Bayan futarta daga takaba aka rushe gidansu. Nanko take aka tada gini matsakaici gida akayi meban sha'awa Wanda yaba harabar gidan fili Sosai nashan iska Wata uku aka 'dauka aka gamah Komai Kakah Tace xata kuma gidan Dan haka SAILUBAH Tace dama ita gidan nata ya isheta dan ko'ina tashiga RAMADAN Qaninta take tunowa Dan haka taroqi Innah Yalwa akan taxo sukomah gidansu gabaki 'daya Innah tayarda dan Sam bata San rabuwa da SAILUBAH dan Allah ya jarabceta da Santa Haka suka ha'du da Kakah xaman nasu gwanin ban da'di Yayinda hakan yayimah Junior da'di Sosai aransa. Ga yaransa kusa dashi kuma ga sahibarsa kusa dashi Sam Junior baifara yimah SAILUBAH iskanci ba saida yaga tayi wata biyu da dawowa gidan😳 Ta "kama. isa. rashin san raini duk yafara nuna mata. Abinko ya farone da wata rana da yadawo daga office 'dinsa kansa nayi masa ciwo Yace bara ya dawo gida ya huta Bayan yayi wanka ne yaci abinci ya kira FAWAS Yana cewa aiki ya sami Auntynku tunda tacinye lokutan dana iban mata Dariya FAWAS yayi Yace xa'a fara buga wasa kenan Yace Sosai mah FAWAS yajah numfashi Yace hmm ina tausaya mata da wannan wasan naka kasanfa tasake dakai Yace abinda ya dace kenan FAWAS ya gyara xama akan kujeraisa ta office 'dinsa Yace ai 'daxu da safe danaje gaisheta bakaga wankan da tayi bah Tayi kyau Sosai kamar 'dan uwan mu RAMADAN bai Aureta ba Har KHAMIS yana cewa yanxu samari xasu mata cahhh aka.... Dan ubansu ko xasu barta dan bata gama warwarewa ba. Junior ya fa'di hakan ransa amatuqar 6ace Dariya Sosai FAWAS yayi Yace jimana Malam ai saika tsaya kaji qarashen labari nah Dan kanna ba KHAMIS amsa Wani Yaro ya shigo yana cewa wai ana sallamah da SAILUBAH inji Alhj tukur...... Da sauri Junior Yace what😳 FAWAS Yace yah Wlhi kuka tasa mana wiwi wai yanxu samari xasu sata agaba Ina gayama sam taqi fita.... Junior yajah numfashi Yace waisu wa'yanne irin mayune daxasu xomah mace daga fitta daga takabah FAWAS Yace ainaga tada'de da fitta ai Yace ina wani da'dewa anan. Anaso mace tayi 1 year Amma ko 5 mont batayi ba. Sunfarasa gabah Murmushi FAWAS yayi Yace kaga malam karkayi wani basaje kawai kashigeta dan idan katsaya sanya kanaji kana gani wani xaiyi maka shigar sauri Murmushi Junior yayi Yace da'dina daku karantar sO shine abu nafarko da yayi nasarar sace xuciyarku Niba Senior bane daxan 6ata lokacina wajan bin ra'ayinta Nawa umarnine kawai😀 Shege kana wata mubinka fetir jamu muje muga naka SALAN a sO FAWAS ya fa'da da sheqewa da dariya😆 yana meci gaba da cewa Amma fah kasani Aunty LUUVAH tana dai-dai da tunaninka. Saidai dake mun lura da shagwa6ar da take xubah maka ba mamaki kasameta yanda kakeso. Tunda har yanxu nalura bagane Komai take bah. Xakaji da'din buga wasan da ita...... Murmushi Junior yayi da kashe wayan dan FAWAS badai xulaya ba Kiran KHAMIS yayi lokacin wayar bata kusa dashi Dan haka sai kawai ya miqe yana lumshe ido da takaicin Ganin SAILUBAH dabaiyi da safeba Yasani tanacan tana tunaninsa ko lafiya dan takira number nasa kusan sau uku Amma yaqi 'dauka haka kawai.... Janyo wayarsa yayi ahankali yafara rubuta mata sa'ko kamar Kullun dan tunda tafita daga takaba yafara damun xuciyarta. ```Assalamu alaiki``` ```na gaya miki ni ba'ko ne agareki uwar 'ya'yana.``` ```Zanso ki'daure kibani masauki xuciyarki``` ```Ina so kisani. Shima so halittarsa akayi``` ```Sannan acikin xuciyata samun akayi``` ```Na rigada na xubar da ajina gareki nabaki xuciyata ha'de da gangar jikina``` ```Kullun mafarkina ganinki nakeyi gani gaki da kyawawan yaranmu muna cikin farin ciki da nusha'di``` ```pls kisoni luuuuuuu``` ```Dan duk duniya ba wanda yake miki irin san da nake miki``` ```Dan Allah kibani xuciyarki mukasance a shinfi'da 'daya``` Wannan shine abinda ya tura mata da wani layinsa Yana tura mata ya gyara kwanciyarsa danyin baccine. Saidai kamar yanda yasaba mafarkinta yi yayi gata da yaransa Suna wasa irin na sO da qaunar nan....... Mafarkin nasa ya katsene dan jin yanda ake jan qafarsa... Yana bu'de ido yaga KHAMIS ne Murmushi yayi Yace na Aunty XEE yane KHAMIS yayi Murmushi Yace muje baranta mu'dan Sha iska kaji Tashi Junior yayi yana cewa Owkie Sun haura sama can barandar tasu wanda hakan ya basu damar ganin Komai na gidansu SAILUBAH Junior yakira Khairat awaya Yana ce mata takawo mai drink..... Ko minti 'daya batayi bah takawo mai Yace dts gud my baby Tayi Murmushi da barin gun.. KHAMIS yaja numfashi Yace Wani abu ne yake damuna Nafara gayamah FAWAS 'daxo Yace kawai saimun ha'du Junior ya ture drink 'din gabansa Yace hmmm ina jinka Yace naga alamun kamar Momy tafara canjamah XEE da sanin danayi musu dah.... Junior ya qara gyara xama. Kamar yaya fah. Na lura Momy aihuwa kawai takeso shiyasa tafara canja mata Abin da yaban mamaki dan gani nayi idan kaduba bafawai nakai Aure bane kawai sone yayimin mugun har suka samu sakayi min Saidai abin takaicin shakaru ka'dan tatada hankalinta akan tanasan jika. Yanxu Da kumah banyi Auran bafah Junior Yace da bata damu ba KHAMIS yajah tsaki Yace toh yanxun mah karta damu mana Murmushi junior yayi Yace dole tadamu yanxu. Saboda in takalli 'dan FAWAS Ahmad da biyu na nasan xuciyarta xata qara tunxurata akan dama naka ne Kuma kaga koyaushe Suna kai mata xiyara Shuru KHAMIS yayi Can junior yaci gaba da fa'din ga shawara... Da sauri KHAMIS Yace inajinka Yace xanso na dubata naji yanayin da takeji ajikinta da sauransu Kaga saina 'dorata akan magunguna koxa'a dace duk da dai nasan kunyi na asinitin ko kumama ince kuna kai. Murmushi KHAMIS yayi Yace hakane kam Xadai kagammun kawai....... SAILUBAH CE tafitoh daga cikin falon Su KAULEET da KAULAT Suna biye da ita sunyi kyau Sosai Cikin shigar dogayan riguna da hijabi gayunsu SAILUBAH ko wani jan les ne ajikinta riga da siket 'Dinkin siket 'din yayi baxar daga qasa ta saman kuma ya matse mata qugu da futar da tsarin gun Rigar kuma 'Yar daidai CE Tayi 'dauran 'dan kwaninta irin na Aisha tsamiya Gyalanta me shara-shara sai xuba qamshi takeyi Hannunta maqare da agogo. Haka yatsunta saqale da xubunan xinare. Batayi wani make-up ba dan daga man baki da fauda ba wani abu afuskarta Amma dake ita'din me kyau CE bakuga yanda tayi bah Tsayawa tayi tana qaremah motocin harabar gidan kallo tana ruwan idan Wanda xata hau.... Junior Yace ina xata haka KHAMIS yayi Murmushi Yace 'daxu dai da safe tacemin tana San xaga gari dan tagaji da xaman haka. Bata gaya maka bane Yace dake yau tacinye adadin lokutan dana ibammata shiyasa Sam ban shiga mun gaisa bah KHAMIS ya miqe ya dafa qarfan gun yana cewa da mamaki kam Amma fah tayi kyau sosai. Dan tafi 'daxu ha'duwa. Tashi shimah junior yayi Yana wani yatsina fuska Yace baxan bari tayi futannan bah KHAMIS Yace aisaika hanxarta. Aikine dai yasameka Allah Sarki senior 😀 Tsaki Junior yajah Yace angayama ni shine kawai nawa umarnine da 6atawa KHAMIS yayi dariya Yace gaka ga ita ai. Jeka ina kallanku daga nan Junior yayi Murmushi Yace harka tunamin da wata ranah.... Kan KHAMIS yayi magana harya bar gun Ahankali ya tura "kofar gidan. Karab ko suka ha'da ido da ita Gaban SAILUBAH ya fa'di kamar koyaushe dan ayanxu idan tayima Junior kallan farko Gani take Qanin nata ne Saita da'da yimasa kallo na biyu Sannan take yarda Junior ne.... Harara ya watsa mata Bayan yaje daf da ita Ya wani ya mutsa fuska Cikin raini Yace xuwa ina haka Kallansa tayi Sosai saitaga yau ya koma mata 'dan iskanta sak😂 Dan haka itamah tawatsa mishi nata hararan Tace inda ka'aikeni Yace toh baxaki bah... KAULAT da KAULEET suka rungumesa Suna cewa Dady Rage tsawansa yayi ya rungumesu yana dariya Yace ina xaku KHAULAT Tace shan ice-cream Momy tace mana Yace gud my baby..... Wlhi baka isa ba saina futa. Ko angayama banda lafiya ne da xan xauna waje 'daya kamar wata mayya SAILUBAH Tace hakan ranta amutuqar 6ace Murmushi Junior yayi dan damah so yake tafusata... Ya shafa kan KAULEET Yace toh maxa kuje gun momyna kujirani yanxu xanxo nakaiku ko. KHAULAT Tace toh Dady Amma da Momy ko Yace eh mana Da gudu suka nufi barin harabar gidan Suna tsalle gwanin ban Sha' awa Yadawo da kallansa ga SAILUBAH cikin 'daure fuska Yace Kinga malama shige gida Tace toh ubana Yace ai basai kinyimin gatse ba Dan da gaske yanxu kamar uba nake agareki dan Allah ya kar6i abinsa saiya ha'da da masoyinki mijinki me kula dake gayamin kina da wani Wanda ya wucce nine ayanxu.... Wata muguwar harara tagalla masa xuciyarta tayi mata xafi da amsar daya bata. Saita rasa mema xatace mishi Ganin dashi kuma yayi tarasa nacewa shiyasa shi kai hannunsa kumatunta ya shafo faudanta yana kallo Yace eh ba shakka kam. harda wanisa pawda Xaki neman mijin Aure tun yanxu ko Amma kin ban mamaki ko shekara 'daya brother baiyi da mutuwa ba har xuciyarki taraya miki kifita nemo miji 😰 Ki duba wannan wankan da kikayi dan kawai maxa suganki Su biki su yaba Gaskiya kinci amanar sO Na tabbatar da ace xai dawo yaganki haka daya tsaneki.... Kuka SAILUBAH tafashemai dashi wiwi tana cewa Allah ya isa tsakanina dakai An gayama ni 'Yar iska ce da xanje neman Maza Yace aiko baki fa'da ba. me hankali kallo 'daya xai miki yagane cewa maxa kika fitoh nemah Ran SAILUBAH ya qara 6aci Tace 'dan iska kawai Yace baxanji haushi ba idan kince min 'dan iska dan nasan kinji takaicin yanda nagano manufarki ne Wani kukan ya qara kamata tashige falan nasu tana qara rerawa. Wanda hakan kuma ya fara damun xuciyar Junior kenan Dan haka yabita yana cewa kifitoh Ki tafi abinki rayuwace ai. Dan na tabbatar inda kece kika mutu brother bashi ba 'Yan mata har abada😆... Bata kulasa ba tayi 'dakinta da xama a hannun kujera tana cigaba da kukanta Kaka takallesa Tace me kamata ne Yace Bakomai Innah Tace ya xakace Bakomai bayan yanxu tafuta da dariya Murmushi yayi Yace bara in lallaso muku ita toh Yana fa'din hakan yayi 'dakin nata yana cewa haba uwar 'Ya'Yana..... Wannan Suna da yake kiranta dashi yana tsumah xuciyarta Ahankali ya durqusa a gabanta Yace kiyi hakuri kinji baxan sake gaya miki magana haka ba Insha Allah.... Ya fa'di yana mai goge mata hawayan Cikin wani yanayi na sO Suna ha'da ido ya sakar mata wani shegen Murmushi Wanda yasata rintse idanta tana jin wani fa'duwar gaba na shigarta Ya qara yin Murmushin da tashi ya dafa hannun kujeran yana cewa toh kiyi dariya mana Tace baxanyi bah Yace idan bakiyi ba xaki jefani cikin wani hali Tace me xaisa kashiga halin Yace saboda ke amanata ce agareni Idan na 6ata miki wlhi rasa nutsuwata xanyi Ashagwa6e Tace indai hakane kabarni Yace nabarki Amma kibari gobe ranar hutuce nakaiku. Tace hmmmm Xaxxagar hoda yayi ya shafa mata Yana cewa gwara na 6atar miki da wannan hawayan danna sami nutsuwa Harararsa tayi Tace Allah karka qara cewamin zanje neman Maza Yace toh kidena fitta man Tace baxan dena bah Yace toh kar kimin rashin kunya mana Da mamaki Tace nice xan maka rashin kunya ni sa'arkace wai Yace Amma dai Kinsan Komai qanqantar 'da namiji gaba yake da mace... Qaryane Wlhi Tafa'da tana mai danna wayarta da ganin sakwan daya shigo mata tun 'daxo Naxari tashigayi ka'dan bayan tagama karanta sakwan Tace maye kawai Junior dake kallanta idansa kan le6anta Yace Waye haka Takallesa tajan tsaki Tace wani ne yaketa damuna da kalamai Toh Ki blocking nasa mana inda gaske yana damunki Tace share kawai dan..... Dan kalamansa na miki da'di ko Yayi saurin katseta da fa'din hakan. Tace eh Amma bai fara birgeni bah Yace gaba ka'dan dai... Tace xai fara birgenin Yace kawai na fa'da ne dan nasan ba wanda xai iya burgeki Tace hmmm meya dawo dakai da wuri haka Yace ciwo Meyake samunka Ciwan sO Wacece wacce kake Son Fateemah A ina take Fage Da sauri takallesa kana nufin unguwarmu 'daya Yace eh Amma bai xama Lalle Ki santa ba. Tace ko Yace Yah Tace tana da kyau Yace komai naku 'daya. Tace wane layi take Kinga malama tsaya haka. Xaki isheni da tambaya kamar wata matata.. Yafa'di hakan da miqewa yana gallah mata harara Murmushi tayi Tace nidai ban ta6a ganin mara kunya kamarka ba Wlhi..... Murmushi yayi mata kawai ya futa daga 'dakin itama tabishi abaya Innah Tace ka lallashetan. Yace gata kin ganta. Kakah Tace aikuwa kam Haka ya ficcewa xuciyarsa tam farin cikin hanata futan dayayi dan kar maxa Su gane mishi ita😂 (Munga senior RAMADAN mah😆) KHAMIS ya kallesa Yace meya sata kuka Yace badai ni bane Yace amanace dai gareka. Murmushi junior yayi mai kawai --------------- Washe gari ko da misalin qarfe biyu tagama shirinta tana Jan tsaki akanma wane dalili Junior xaice saidai sufita tare.... Tana saqar xucinta ya shigo palan yana cewa uwar 'Ya'Yana gani naxo Tana jinsa tayi bansa dashi Shiko Jan KAULEET da KHAULAT yayi suka ficce yana yima Su innah sallamah Tanajin fitarsa itama tafitoh cikin shigar doguwar tayi kyau Sosai Tace toh Kakah Innah saimun dawo. Adawo lapia Tunda tafitoh idansa yake kanta dan baqaramin kyau tayi masa bah Amma Sam bai bari tagane ita yake kallo ba dan gilashin dake idansa Duk yaran suna baya dan haka tashiga gaba tana qare mishi kallo dan jin qamshin dake fitta daga jikinsa Shege ya iya wanka😂... Abinda Tace kenan aranta Yace nafiki kyau ko Ta Kawar da fuskarta tana ya mutsata Tace ko kusa..... Murmushi yayi da fa'din wannan axahiri yake ai... KHAULAT Tace Dady kafi Momy kyau Yace nagode Babyna KAULEET ko cewa tayi Momy kemah kinyi kyau Ammafah Dady yafiki kyau😀 Murmushi SAILUBAH tayi kawai Wani wajan shaqatawa sukaje Wanda yasasu jin da'di Sosai Amma ga Junior abin ba haka yake ba Dan duk hankalin maxajan wajan Idansu akan SAILUBAH yake Dan haka Bashiri Suna 'Yan ciye ciyensu Yace sutashi sutafi Harararsa SAILUBAH tayi Tace asan raina naso nakai qarfe biyar Amma tunda kace haka muje. Saidai baxan qara fita dakai bah Wlhi Murmushi yayi Yace Naji dai muje Da 6acin suka dawo gida Bayan sun biya supermarket sunyi siyayya Yana yin fakin cikin gidan nasu sukaga wani qatan mutum attajiri xaune akan kujerun harabar gidan Gabansa cup ne da drink da alama ya 'dan da'de da xama agun. Kallo 'daya Junior yayi masa yagane nemane ya kawoshi Nan take kishi ya cika xuciyarsa SAILUBAH ta kallesa Tace wannan kuma Waye Yace oho miki. Ai Kinsan batare muka shigo bah Tace karka nemi ka gayamin magana daga tambaya Galla mata harara yayi Yace ninace tambayeni ai 'Yar rainin hankali. Kwafah SAILUBAH tayi tafice daga motar da nufar gun mutumin.... Junior yaja tsaki KAULEET sarkin surutu Tace Dady Kullun sai kunyi fa'da da Momy ne Ahankali ya kalleta da Murmushi Yace aa my baby ba fa'da muke bah 😆 Xata qara magana yasa mata sweet abaki. Shuru tayi kamar yanda KAULAT tayi tanata shan nata sweet 'din Bu'de musu yayi mukayi ciki da murnar dawowarsu Sannan ya maida kallansa ga SAILUBAH Ahankali taxauna tana cewa sannu dai Da Murmushi Alhjn Yace Yauwa sannu SAILUBAH kundawo Tace eh Yace madallah. Dama 'daxo naxo kakarki Tace kin fita Amma bada'dewa xakiyi ba Jin hakan yasa Nace bara in jiraki Wato SAILUBAH sO da qaunarki CE tayi min mugun kamu dafatan wani be rigani bah.... Kallan Junior SAILUBAH tayi Aiko karab suka ha'da ido Gabanta ya fa'di idanta ya fara mata gixo akan anya ba Qaninta bane yake kallanta....... Nan xuciyarta tafara jagula mata lissafi Kuma taqi 'dauke idan nata akansa kamar yanda shima yaso dan yasan in tana kallansa baxata iya Komai cikin nutsuwarta bah Danshi yasan kansa😬...... Bakice Komai ba.... Alhjn ya katseta A'dan tsorace ta kallesa bakinta na 'dan rawa Tace ban ban banji me kace ba.... Murmushin mugunta junior yayi dan yanda yaga bakinta na rawa yasan tashiga yanayin da yake San tashiga ne Alhjn Yace cewa nayi sO da qaunarki ne yayi min mugun kamu ina fatandai ba Wanda ya rigani....... Dake hankalin SAILUBAH nakan junior tanajin bu'de 'kofar motarsa takai kallanta garesa Aiko ya jingina ajikin motar Yana kallanta da shagwa6e fuskarsa Yace Auntyna...... Da sauri SAILUBAH tatashi tana cewa Qanina..... Shuru Junior yayi mata yana aike mata da wani sirrintaccan kallo Ahankali ahankali tafara nufushi tana xuwa daf dashi Tace kadawo gareni ko Wani shegen Murmushi yasakar mata tare da ware hannunsa tayi saurin rungumarsa tana cewa I Luv u Qanina Cikin wani salo Junior ya qara rungumarta yana cewa me 2 my luuuuu...... Agigice SAILUBAH ta 'dago da kanta Cikin mayen sO takama fuskarsa da dukkan hannunta biyu takai bakinta cikin nasa🙈 tafara kissing 'dinsa Sosai afurgice🙊. cikin nutsuwa ya 'danyi dabarar hanata. Ganin hakan yasa ta qanqameshi Sosai takwantar da kanta a qirjinsa tana sauke numfashi...... Ahankali ahankali yafara shafa bayanta Sanda Junior ya tabbatar da futan Alhajin nan daga gidan Sannan ya 'dago da ha6arta ya fara shafa fuskarta ahankali cikin nuna MASEEFAR SONTA. Duk ya furcitata ta futa a hayyacinta Ahankali Tace dan Allah karka qara barina RAMADAN Tafa'di hakan idanta cikin nasa Murmushi ya sakar mata da rabata da jikinsa a hankali Yace mexaisa na barki. Amma ai shi nakin ya tafi inda ba'a dawowa. Kidawo cikin hayyacinka mana da Junior kike fah😀 Ya kamata muje musauke farali La'asar na jiranmu ya qarashe da yafa gefan fuskarta cikin kulawa Yana fa'din hakan ya nufi barin gidan..... Sororo SAILUBAH tayi sai yanxu hankalinta ya dawo jikinta😳 Tayi saurin dafe kanta da jingina a jikin motar. Ba xatoh ta fashe da kuka 😭 Yana Jin kukan nata ya share da bu'de 'kofar get 'din gidan ya ficce yana dana sanin barinta da yayi tayi kissing 'dinsa Yauxu tajefashi a maseefa yau yaji lallausar le6anta👄 lips 👄 da yake fatan mallaka🙉 Iuv u❤all Da kukan tayi falon nasu Innah tace ikwan Allah wai meyake damunki ne SAILUBAH Shuru tayi mata da shigewa 'dakinta KAULEET Tace Dady ne yasata kuka KHAULAT Tace aa Kullun ai saitayi kuka ko Innah Murmushi innan tayi Junior ko Bayan ya idar da Sallah lamo yayi a gadansa yana tuno Al'amarin daya faru Lumshe ido yayi yanaji aransa damah Su dauwama a wannan yanayin. Wayarsa ya janyo yafara mata rubutu kamar haka ```Xuciyata na bugawa my Luuuuu. Da alamah baki cikin kwanciyar hankalinki``` ```Gaya min Babyna meya faru dake. kinji nutsuwata``` Yana gamawa ya tura mata Itako kukanta take Sosai dan tuno da Senior da tayi Tana Cikin kukanne taji shigowar saqo Bata duba ba. Tatashi tayo Alwala tayi Sallah dayima Senior addu'a Kafin tamiqe a kujera da niyar kiran XEE Saidai Ganin sakwan nata yasata dubawa Shuru tayi tana tambayar xuciyarta wai waye ne wannan Cikin Takaici tabashi amsa da ```wai kai waye ne``` Junior nagani yayi Murmushi ```Mesan xama miji agareki nahar abada``` Jah numfashi tayi kafin tabashi amsa da..... ```bana San kowa ya xamah miji agareni dan na rufe babin aure arayuwata``` Yace..... ```Xako kiyi kisa inhar baki aureni ba. Dan ina tabbatar miki da cewa mutuwa xanyi``` Dariya tayi da cewa.... ```Toh kamutu man. ina ruwana``` Murmushi yayi ```wlhi baxan mutu ba harsai na mallakeki matsayin matata kin haifamin yara kyawawa kamarki. Masu kyan sura da yalwar gashi me santsi da sheqi. Masu fararan ido tamkar madara. Masu lallausar fata me tafiya da ruhin mutum``` Gyara kwanciya SAILUBAH tayi.... ```Alamu sunnuna xakayi surutu da yawa``` Murmushi ya qara yi..... ```hmmm Kiyi mafarkina my Luuuuu. Tunda na fara damunki. Saidai Ki share hawayanki kafin kiyi mafarkin nawa``` Tashi SAILUBAH tayi da mamakinsa wayace mishi tayi kuka da sauri ta fara typing..... ```Wayace maka nayi kuka``` Murmushi dai ya qara yi ganin tambayar tata. Bai bata amsa ba ya ture wayan yana tuno lips 'dinta👄 da lumshe ido cikin son ya qara jinsu Ahaka baccin yamma yayi awan gaba dashi Itako SAILUBAH ganin bai bata amsa ba saitaja tsaki da Neman layin XEE. Ringing ko biyu wayan tayi XEE dake falanta tana chatin ta'dauka da cewa 'Yar Uwa yadai Tace hmm kedai bari. Wlhi XEE banta6a ganin 'dan iska irin junior ba Dariya😀 XEE tayi Tace a'iya sanina dai tunda RAMADAN yarasu junior bai miki Komai bah Tace toh ya fara yanxu. Dan yadawo da rashin kunyar da yake min. kinsan ma me yayimin 'daxo XEE Tace meya miki....... Kwashe Komai SAILUBAH tayi tagaya mata taqara da cewa dake 'dan iska ne barina yayi nadinga aika masa da sakwannni 😀 Sanda yajini dakyau kafin ya ankarai dani 🙈 Waro ido😳 XEE tayi da cewa tab😊 Eh ya tabbata 'dan iska Yanxu kun qara ha'duwa ne Tace inafah yana can ina gida Saidai kinsan dake ya kware a iskanci baxai wani nunamin komai bah Murmushi XEE

Chapter 26 of 33