Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [10:45PM, 02/11/2016] Rahamat Nalele: 👯👯👯👯👯 *SAMAREEN* 👯 *BANAH* 👯👯👯👯 *TASU SALAN SOYAYYAR* *Na Rahamat Muh'md Rufa'i Nalele* Part 1..... *Nutsu da kyau me karatu ka karan farkwan labarin nan da kyau kuma kar kayi gigin mantawa. Dan xai temakema wajan gane ya abin xai kasance nan gabah* Sunana SAILUBAH KASIM. Ina garin KANO da xama awata unguwa da akekira fage Ina da shekara ashirin da biyar aduniya wato 25 years Na kasance mace mace kyakkyawa san kowa in wanda ya rasa Ni farace soll doguwa me kyan bafali Ina da hq da breast na 'daukar hankali Bancika qibaba sannan baxa'a kirani siririya ba Komai nawa ya ha'du kamar yanda kowace mace takeso ta kasance Idan na kalli kaina a mirror hmmmmmmm Dole najah numfashi anan Dan ni dake da kai bana buqatar kufitoh kuce Ya SAILUBAH kin ha'du Na sauke alqur anin me girma inada ilimin addini daidai gwargwado dan baxa'a kirani jahila ba Ayanxu ina U:J ina fannin san kasancewa cikakkiyar doctoh Sai dai bawani damuwa nayi da karatun bah dan inada burukan da suka shige min gaban karatun Na kasance mace mesan ku'di Mesan na mallaki gida da mota Sannan ku'di su ratsani Inasan namiji 'dan gaye 'dan kwalisa me ilimi wayayye me hankali Sannan ya kasance miskili ya kasance ni ka'daice xan mallaki dariyarsa da komai na halittarsa Ya kasance nika'daice tasa abin dubawarsa amma in aka cire iyayansa da qannansa Ya kasan me hakuri sannan me kishi akaina Ya kasance naxama nice madubin dubawarsa. Shikuma yaxama shakallo agareni Ina da burin Auran Attajirin Alhaji me ku'di da nera Irin Alhazawan garin abuja nan Maso ku'di da albaxaranci Bana burin Auran qaramin yaro kamar wanda ya girmeni da irin shekara uku haka Na fisan na Auri wanda yabani akalla shekara goma sha biyu haka na saka araina baxan ta6ata auran qaramin yaro bah. dan na raina qarfinsa da jarumtarsa Acikin unguwarsu akwai wani gida me kyau da 'daukar hankali wanda ya kasance gidan xuwana ne ako da yaushe naga damar xuwa Inada aboki RAMADAN wanda shine ya kasance wanda yakejin sirrina nayi matuqar shaquwa da RAMADAN irin shaquwar nan da akekira da inbakai baxan iya rayuwa bah Ina san RAMADAN dan ya kasance yaro memin ladabi da biyayya duk da shi 'din miskiline Amma ya ha'du tako ta ina dan ina qaruwa dashi tako ta ina Dan yafini ilimi yafini hankali sannan ya fini nutsuwa Duk shawarar da nanema agun RAMADAN idan yace min iyi kasa bar kaza nabarshi har abada Yaro ne qarami 'dan shekara ashirin cif ba qari ba rage ayau Idan me karatu ya koma baya toko xai gane naba RAMADAN shekara biyar kenan Saidai RAMADAN funannan yaro ne. Xaki gane waye shi idan tafiya tai tafiya Tunda natashi banta6a ganin idan mahaifiyata bah Dan tada'de da rasuwa tun ina jaririya Ayanxu dai ina hannun matar babana ko ince muku Kakata Ba lefi suna kula dani sosai saidai matar babana tana da san ku'di ba nawasa bah Amma duk da san ku'din nata nafita Babana dacan yayi ku'di Sosai daga daga baya ne karayar arxiqi tasa meshi Ayanxu bashi dashi Saidai bama rasa na sawa abakin salati Abu 'dayane ya bari adukiyarsa. shine gidanmu. Gidanmu babban gidane kuma ginin xamani Dan a unguwarmu in kacire gidansu Ramadan akyau toh cika saka gidanmu Inada qawaye masu bu'dad'dun ido da wayewa fiye da tunanin me karatu Wannan shine labarina akataqaice 👯👯👯 Sunana RAMADAN Nasir yaro 'dan 20 years Na kasance ina da buri 'daya arayuwata shine natashi da maseefar san wata mace me kyan sura. Da komai Tayi tako ta ina Ina santa Ina santa Ina santa Ina da abokana ye biyu Fawas da Khamis Duk ra'ayinmu 'daya yake dasu Amma mutane da dama suna cewa nafisu nutsuwa da hankali Na kasance 'dan gaye me san tsafta da qamshi Duk unguwarmu ni ka'daine nafita xakka a iya wanka Dan nayi xaman jos anan nasamo Sirrin Inada kalamai masu tsayawa arai Sannan Auntyna Tace ni futunanne ne Ya ta6e baki sannan yaci gaba da cewa Idan hakane Ku da kanku xaku sheda hakan idan kuka cigaba dabin Aunty Rahamat Nalele Suna na KHAMIS Inada shekara ashirin daidai yau Ban tsaida wani buri araina ba tukunna Sai dai inada san mata saboda Suna sani nisha'di. mata abin farin cikine kowane 'Da namiji ne 👯👯👯👯 Suna na FAWAS Inada shekara ashirin daidai yau Ina da San mata Sosai kuma inada burin Auran mace wacce ta xarce shekaruna da kamar shekara biyar haka ko shidda Kuma bana san Auran wacce ta Waye nafisan Auran 'Yar qauye me halin yarinta Tab😳 👯👯👯👯👯 Suna na Zainab Amma ana kirana da XEE dan nafisan akirani da hakan Inada shekara ishirin da biyar. Ina da saurayi Surajo ina matuqar sanshi da kishinsa Sannan ni ta hannun damar SAILUBAH CE dan duk acikin qawayanta nice babbar qawarta 👯👯👯👯 Suna na Hameeda Ya'u ina xaune a qauyan takai Babana ya rasu Mamana mah haka Ina hannun qanwar babana Innah Hansai Ba qaramin ganamin axaba take bah Duk aikin gidan ni nakeyi duk wani aika ni nake xuwa mata haka duk wani Girki ni nake yi Duk da ko tanada yara Amma Sam bata sakasu sai ni Sosai nake hango tsanata acikin idanta Bata sona bata qaunata Ta hana duk wani saurayi tsayawa dani wai tafiso na xauna inta yimata bauta Ayanxu shekatata ishirin da hu'du 24 Bani da wani buri araina sai na kallan cigaba da bautar da nakeyi *Toh Madallah masu karatu kunji tushen kowa acikin wannan littafi nawa. dan haka sai kugyara xama kusha karatu* SAILUBAH yarince maisan ku'di kamar yanda tafa'da Amma duk ku'din da xata samu basa rufe mata ido Dan ko yanxu SAILUBAH tasamu ku'di xata iya kyautarsu gabaki 'daya dan Allah yayota da San temakwan mutane Tana da kyauta Sosai ba 'dan ka'dan ba da tausayi SAILUBAH 'Yar gayece Sosai Duk unguwarsu ba'ayi yarinya me wankanta bah Zama na musamman samarin layin nasu suke dan kawai suga fitowarta Duk unguwar ba wanda baisan SAILUBAH da halinta ba Kyauta San Mutane San ku'di fa'dar Gaskiya.............. Koda ko kar sa'an babanta ne kayi abunda bai dace ba toko ba shakka saita wanke ka da soso da sabulu Duk unguwar ba Wanda baisan sha'kuwarta da RAMADAN ba Suna San junansu Sosai dan shi'din abokinta ne Mutane da dama idan sukaga SAILUBAH da RAMADAN xasu skull dake skull 'dinsu 'daya ba qaramin sha'awa suke basu ba Fa'di suke tsakanin SAILUBAH da RAMADAN wayafi kyau ne RAMADAN Yarone me hankali da nutsuwa Sam baya shiga sabgar daba tashi ba Komai xaiyi anutse yake yinsa Baya 'daukar raini Yarone me farin jinin jama'a musamman mata RAMADAN na kowa ne dan Allah yayoshi da kwarjini Duk inda kika kai da abinki idan kikayi toxali da RAMADAN sai kinso Ki mallakeshi a matsayin mijin Auranki Ya ha'du ne tako ta ina RAMADAN yayi Yana da da'din murya haka kallo 'daya xaki mai kisan anyi balaraban yaro RAMADAN cikakken 'dan rainin wayone Sam baxa ki gane inda yasa gaba ba Yana ji da Auntynsa SAILUBAH. Sam baya San 6acin ranta Duk Wanda yake tare dashi yasan da xaman wannan Sai dai fah ahakan baqamin takurama SAILUBAN yake ba akan samarinta Shi ka'daine namiji agidansu Kuma Wanda kamanninsa yafita daban dana kowa Sam RAMADAN bai ibo Komai na iyayan nasa bah Mutane na mamakin wannan yanayi yanda RAMADAN ya futa xakka agidan nasu Kome yasa hakan (Tabbas kwakwalwa tana buqatar caji agun🤔) Su ukune agun mahaifan nasu Akwai yayar RAMADAN Saudat wacce ta kasance qawar SAILUBAH Sai shi RAMADAN 'din Da qanwarsa Khairat Mahaifinsu Alhaji Naziru me ku'dine Sosai Ya shagwa6a Su da ku'di Sosai Haka ba qaramin SOO sukema RAMADAN ba Kome yasa haka🤔 RAMADAN Yana da San karatu Sosai gashi da ilimi tunda ya taso ya fara xuwa makaranta bai ta6a fa'duwa akan Komai bah Yanxu haka saura bai fimai 1 year ya gama kammala karatunsa ba Inda yake san xama cikakken likita wato doctor Yaxama kenan ra'ayinsa 'daya da Auntyn Sa SAILUBAH Idan Nace muku RAMADAN 'dan rainin hankali ne karku musa min Haka KHAMIS iyayansa Suna da ku'di Sosai shima an shagwa6a shi Sosai da ku'di Su biyu iyayansa suka Haifa Ianada Yaya Rahamat tayi Aure tana garin Abujah da xama Ganin hakan KHAMIS shi 'daya shiyasa shi abinda yakeso kuma iyayansa suka biye nasa KHAMIS Yanada San karatu inda yakeso yaxama cikakken loya Wato ya karanci low Shiko FAWAS iyayansa shi ka'dai suka Haifa Ba qaramin ji dashi suke bah Sun shagwa6a shi da ku'di Sosai *To Madallah me karatu gyara xama* Yau take talata kuma antashi da ruwan sama yaf yaf yaf gwanin sha'awa SAILUBAH sauri sauri gudu gudu takeyin Komai dan sunada karatu qarfe tara RAMADAN ya shigo falan hannunshi 'dauke da Wasu takaddu Yace Auntyna lokaci ya fara tafiya fah Da sauri tajuyo xatayi magana sai kuma tatsaya kallansa kamar alokacin ta fara ganinsa Ya 'daga mata gira tare da qarasowa kusa da ita ya kar6i 'dan kunnan hanunta Yace in saka miki ko Tayi saurin 'dagamai kai Tace kayi kyau Sosai Qanina Yayi Murmushi Yace Nagode Auntyna Gyarawa Sosai tayi ya saka mata 'dan kunnan ta'dauki gyalanta da 'yar jakarta tamaqala Idan RAMADAN na kanta yana qare mata kallo. Ta 'daga mai gira Yayi murmushi Auntyna tsaya na photo Wayanka saita cika da pix 'dina Yace in bake acikinta Wlhi bata da amfani Tace kayi breakfast kuwa Ya 'dan Sosa qeya Yace nayi Tabishi da kallo ka'dan hmm bakayi ba Yace toh Kinga lokaci yayi........ Cire gyalanta tayi tashiga kitchen kawai. RAMADAN yaja numfashi tare da kallan agogo yana tsaki Bai ankareba sai gata qatan faranti ahannunta. Wanda ke 'dauke da lafiyayyan tia da kuma soyayyan dankali da kwai Ta dire a gabansa Tace nabaka minti uku kayi Maza Yace Aunty banajin yunwa... Ta katse shi da jefa mishi wata muguwar harara Bashiri ya fara ci Yayinda ita kuma ta xauna tana amsa waya Hello Alhajina ina kan hanyar xuwa makaranta Yace Amma naso inxo in ganki yanxu. Plx Ki bani ha'din kai yanxu naganki Aini takace. Kabari ina dawowa xaka ganni. Yace toh Allah ya dawomin dake lafiya AmEEn Nagode. Tafa'di hakan da kashe wayan RAMADAN najinta Yace Auntyna dawa kikayi waya Ta gallamai harara cikin 'daure fuska Tace ban sani bah Yayi Murmushi Yace pls gayamin Wlhi ba'abinda xai faru Tace hmm yama faru Wlhi saina baka mamaki idan kayi sanadin da Alhaji Jamilu ya dena xuwa gareni Ya kalleta ka'dan dayin murmushin rainin hankali Yace baxanyi Komai bah Auntyna Amma dan Allah gayamin yaushe kuka ha'du da har ya kasance ban sani bah Tace jiya muka ha'du a jifatu yaje siyayya Amma shine ko jamishi aji bakiyi ba kika amsheshi daga ganin farko Ta gallamai harara Tace ban jah mishi ajinba Yace me yasa Cikin maseefa Tace saboda shi me ku'dine yayimin tun kallan farko dana masa Yace Amma......... Tayi saurin katse shi da cewa. Wlhi RAMADAN ba wani abu daxaka fa'damin inji inbar mutumin nan dan yana da ku'di Sosai Kyautar farko daya min jiya dubu 'dari uku ya ban Yace haba Auntyna...... Na rantse da Allah ka cikani da surutu xakasha mari Shuru RAMADAN yayi yaci gaba dacin abincinsa Can ya kammala Yace toh mutafi ko. Yafa'da da 'daukar Wasu takaddunta Suka fitoh ya bu'de mata gaban motarshi tashiga shima ya shiga da jansu suka ficce daga gidan Direct gidansu XEE sukayi Suna parking tana fitowa Tayi kyau Sosai cikin shigar riga da siket 'yan kanti Ta shiga motar ta xauna tana mita wai basuxo da wuri ba RAMADAN Yace lefin Auntyna ne fah Tace aina sani tasaka gaba kayi breakfast ko Yace ko shakka babu. SAILUBAH Tace hmm kema kisan inba ni'din nasashi gaba ba baci xaiyi ba Haka dai sukayi B;U:K university. Sunayin parking wata kyakkyawar budurwa tayi saurin isowa garesu Cikin rashin kulawa SAILUBAH da XEE suka fito dayin department 'dinsu RAMADAN yafitoh da Murmushi akan fuskarshi Yace ha'a kaga kyakkyawar yarinya. Tauraruwa me dishashe hasken taurari. Gayamin me ya tsaidake a wannan lokacin da yadace ace kina can kina 'daukar darasi Cikin jin da'di da dariya akan fuskar Amina Tace baxan iya fahimtar Komai ba inhar banganka ba Tunda naxo idanuna suke min ra'da'di dan rashin ganinka da basuyi ba Yace toh gani sun ganni sai hankalinsu ya kwanta Tayi Murmushi. Xanso muje shan iska anjima Ya kulle motar tashi yana fa'din xanfi kowa farin cikin hakan. Maxe jeki kar darisa Su wucceki da yawa Ba musu Amina tabar gun cikin jin da'din Ganin masoyinnata Gab da RAMADAN xai shiga department 'din nasu wata ta tareshi da sauri Ya dafe kai cikin Murmushi Yace yane Asma'u Xuciyata bugawa take in bata ganka bah Amma na lura Sam xuciyarka bata damu dani ba Sam Haba nutsuwata abin kwanciyar hankalina. Wlhi dake natashi araina Meyasa toh kakasa nemana Kin sanni da karatu banasan nayi missing 'din Komai. plx nutsuwata Ki lamince min nashiga na miki alqawarin yau xan baki lokaci na musamman dan kimallaki kalmomina Tace toh Allah yasa ina maka fatan alkairi Ya shigeta yana cewa tare dake........ Karatu ne Wanda sukayin shi cikin nutsuwata ahaka suka tashi inda SAILUBAH ta kalli RAMADAN Tace Amma fah abubuwa da dama na kasa fahimtarsu XEE tayi dariya Tace aike Kullun a haka kike Tayi Murmushi dacewa ai banda matsala tunda gani ga Qanina. RAMADAN Yace aikuwa ammafa Auntyna kidinga lura saboda wata ranah. Taturo baki da cewa toh naji muje gida nafara jin yunwa ba sai mun jira KHAMIS ba ....... KHAMIS 'dinne ya katsesu da fa'din dawai tafiya xukuyi kubarni bayan yasan yau ban fitoh da mota ba. XEE ta kafeshi da ido Tace ya fa'da mana Ammma fah kayi kyau sosai Tafa'da da shigewa motar Ganin SAILUBAH da RAMADAN sun shige. Yayi Murmushi Yace kai Aunty XEE ina wani kyau anan. Yafa'da shima yana mai shigewa cikin motar Cikin nutsuwa RAMADAN yake tuqin motar KHAMIS Yace Kasan wani abu Sai ka fa'da Wlhi fitowata 'daxo na ha'du da wata xanka'daxiya...... Ta ha'du Sosai dan tatara duk wani abinda kowane 'da namiji yake buqata awajen mace Dana kai agoge min motata tsayawa nayi daniyar agama goge min natafi da ita lokacin ko wanka banyi ba Sai gata tayi parking motar tata akusa dani Ta fitoh tana wani yauqi da rangwa'da. dan Allah Malam motata nakeso a wanke min nanda 10 minutes Ba sai ta cillamin key nata bah RAMADAN Yace kut😳 Wlhi ina gayama sai kawai naxuba mata ido kusan na 2 minutes Ka katsaya kana kallona ko baka 'daya daga cikin masu wankin ne Ta katsemin tunanina da fa'din hakan..... Kan nayi magana wanda yake goge min motar tawa Yace tab Hajjiya shima kawo tasa yayi. Baki lura da hutun da yake tare dashi bane Kasan dake 'Yar iskace saita juyo da kallanta. Ayya am sorry Na watsa mata wani kallo Nace Karki damu xan wanke miki aikin kai wajan kinma wucce Tayi Murmushi Tace ba qarya ka ha'du ga muryarka tayimin da'di Sosai dama kana tare dani dana saka agaba dan kawai nadinga jin kalmominka..... Kan na bata amsa yaran ya gama gogemin tawa Saina bata kina Nace taje ta aiwatar da 'quxirinta xan kawo mata tata motar har gidansu Tayi dariyar jin da'di toh Nagode Sosai Allah ya saka toh bara namaka kwatancan gidanmu....... Na katseta da fa'din bana buqatar sani dan inaso in baki mamaki wajan kawo miki gidanku batare dakin gayamin bah Baka fah sani ba Nace karta damu Haka tatafi da motata tabarmin akwalar tata Kasan yanxu damuwata bansan gidansu bah kuma kamar xuciyata takamu dasanta Dan Wlhi yau nakasa fahimtar Komai na karatu. sai San ganinta da xuciyata dake kwa'dayin qarayi RAMADAN ya kalli Su SAILUBAH ka'dan Yace Auntys suna nan fah. Dan haka ka ankare. Sam KHAMIS ya manta Suna tare dasu Cikin yanayin sanyi ya kallesu Yace am sorry my Auntys SAILUBAH ta gallamai harara Tace 'yan yara daku sai San mata yanxu idan aka baku su ya xakuyi dasu. Ta'ina xaku fara sarrafasu Ina ja muku kunne Wlhi kufita daga harkar mata dan sunfi qarfin Ku kubari Ku qara shekara goma nan gaba saiku nemesu KHAMIS da RAMADAN suka kalli juna Inda sabo sun saba shan fa'dan Auntyn tasu Cikin 'daure fuska RAMADAN Yace toh munji KHAMIS Yace 20 years fah Aunty XEE Tace eh baku kai soyayya ba. Na roqeku kubar kula mata...... Dai-dai nan RAMADAN yayi parking a'kofar gidansu XEE Tafi toh tana cewa Qawata saimun ha'du anjiman SAILUBAH Tace wane Kaya xamu sane aciki Tace eh toh musa let 'din nan mana Tace red 'din Tace eh shi Kana takalli KHAMIS Tace toh kuhuta samari Yace toh Aunty XEE sukayi gaba Ita mah tayi gidansu tana tunanin KHAMIS itadai tana sanshi yaran na burgeta ga iya wanka kamar RAMADAN Gashi hancinta baya manta qamshinsa Maman ta kalleta Tace ya dai naganki kina Murmushi Tace Wlhi mamah KHAMIS ne yake birgeni Tace ayya KHAMIS ai yanada hankali Tashige toilet tana cewa ba lefi kam Hakama suka sauke KHAMIS agidansu RAMADAN Yace karka damu abokina akwai mafuta KHAMIS Yace nasan bama rasata. Xan nemi FAWAS mah RAMADAN na parking a farfajiyar gidan nasu SAILUBAH Yace Auntyna Na 'danga wayarki Tamiqa masa da ficewa daga motar tayi falansu Annan tatarar da Abbanta yana cin abinci Umma na gefanshi Wato matar Abban nata dake haka suke kiranta Tace sannu da gida Abba Yace sannu kundawo lafiya Tace lafiya lau Yace toh Madallah in kin gama cin abincin naki kixo kisa meni Gabanta ya fa'di Tace toh Wanka tayi ko cin abincin batayi ba taje gunsa Yace dama xan da'da tuna miki ne akan batun tsaida Miji Wlhi kika cikamin ciki xan aurar dake ga wanda naga dama Tace kayi hakuri Abba ka qaramin lokaci Yace ke kika sani nidai na qara miki lokacin Dan yana wuccewa baki kawomin Wanda kike so ba Wlhi kinji na rantse saidai kawai kiji Nace kitashi kibi mijinki SAILUBAH ta sunkuyar da kanta cikin ladabi Tace insha Allahu hakan baixai faru bah xan kawo Wanda nake so Yace Allah yasa jeki Nan Tatashi xuciyarta cike da tunani kala kala RAMADAN ko gidansu yayi direct yayi part 'dinsa. Dan gidan nasu acike yake tam da mutane 'yan biki yaune walimar yayarsa Saudat gobe 'daurin Auranta Ya baje a gado yanata bincikar wayan SAILUBAH. Har yasami abinda yake nema watoh number Alhaji Jamilu Wanda SAILUBAH tayi waya dashi 'daxo Nan ya kirashi ringing biyu ya 'dauka cikin sauri yana fa'dan Allah yaja da xamaninki tauraruwa RAMADAN ya runtse ido Cikin kamilalliyar murya Yace ba ita bace na kiraka ne in gaya maka wani abu Alhaji Jamilu Yace toh ina jinka Yace Kasan da cewa tarayyarka da ita haramun ne Dan babu kyau Nema acikin Nema Dan da sadakin wani akanta yanxu haka baifi watanni bane bikinta Cikin muryar tashin hankali Alhaji Jamilu Yace Wlhi ban san An kawo sadakinta ba RAMADAN Yace toh yanxu nagaya ma danni qaninta ne Yace Nagode Sosai yaro Allah ya maka albarka RAMADAN Yace AmEEn da kashe wayan Sannan yayi blocking 'din number Sa da delete 'dinta RAMADAN kenan ya tsani yaga kowa da Auntyn nasa. Shiyasa yake koran mata samarinta sanranshi. Tayi fa'dan tayi maseefar Sam bayaji. Iya kacinsa da ita shine ya bata hakuri SAILUBAH ko daqar taci abincinta burinta tagama taje gun Qanin nata suyi shawara Hakako akayi. Data gama Komai saitaje tasamu kakarta Tace kakane bara naje gidansu RAMADAN Tace har lokacin walimar yayi ne SAILUBAH Tace wai walimar walimar Saudat Tace eh mana. Taxoma nemanki 'daxo keda XEE wai kimata lalle ne kome tacene oho na manta Girgixa kai SAILUBAH tayi Tace sai qarfe hu'du walimar da sauran lokaci Tana fa'din hakan tafito daga falan nasu Tafi toh kenan idan ya sauka alungun Gidansu wata Baraka dake kusa dasu Saita dinga jin kamar kukan yarinya. Cikin qarfin hali tayi lungun Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Tafurta hakan da qarfi. Dan Ganin wani narkeken qatan garde a'kalla xaiyi shekaru arba'in 40 Ya danne wata yarinyar makwaf ciyarsu 'Yar miciciya batafi shekara goma ba Aiko SAILUBAH me xatayi inba kurma ihu ba. tana fa'din jama'a kuxo ga wani axxalimin mutum yana San 6atama yarinya rayuwa....... Kan kace me😳 tuni gun ya cika da jama'a Suna tafi da Allah wadai da shi da mamakinsa mutumin ya saka wandansa SAILUBAH ta cukume masa riga Tace Amma kai kam Allah yayi tsinannan tsowo Fasiqi axxalimi me mumunar xuciya 'dan iska Kalli yarinya qarama kana san 6ata mata rayuwa Idan iskancin kakeji mexai hana kaje gidan karuwai kayi da wacce ta dace dakai. Tunda xuciyarka tamace da son abinda Allah bayaso RAMADAN Wanda yafito dan rahotan da qanwarsa takai masa. Xuciyarsa tacika da takaicin Auntyn tashi yayi dabarai kwatan mutumin ahannunta........ Kan yayi magana sai gani sukayi Iyayan yarinyar sun rufe mutumin da duka Sosai Mutane na fa'din gwanda aci ubansa Suna tayasu dukansa SAILUBAH takai hannu xata tayasu itama..... RAMADAN yajah hannunta sai Gidansu A farfajiyar gidan yasake mata hannun nata Yace haba haba Auntyna meya kaiki aikata haka. Kamata yayi da kika gansa kimasa wa'axi tsakaninki dashi. Amma bai dace kitara mishi jama'a haka ba Tunan asiri bashi da kyau ai cikin maseefa ta hayyaqu miki tace banyi hakan da kaso ba. Irin sune 'yan iskan da in ba haka akayi musu bah baxasu dena abinda suke ba Yace toh wai ke ina ruwanki meya shafeki kawai kinje kintara jama'a maxa da mata kowa yana kallanki harda wani kai hannunki jikin qaxamin mutumin. kin dai kwafsa kawai kiyarda da hakan Yafa'da kamar xai rufeta da duka Tace baxan yarda da hakan ba danni abindayi dai-dai ne Kana maganar abarsa ya6ata mata rayuwa kenan ko dan ba kasan

Chapter 1 of 33