Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
napkin, zarni kwar. Tace in taso mu tafi gidan malam. Na mike da sauri muka fice ba tare da ta leka dakin mahaifiyarta tayi mata sallama ba. Tafiya muke fankam fankam tamkar fatake, muna tafe muna tayar da kura kamar shanu, mu dukanmu hankalinmu a tashe. Na juya na dube ta nace ummi malamin nan kuwa yana da gaskiya? Nifa har yanzu banga komai ba. Ummi ta tabe baki tace uhmm ke dai bari. Ai shiyasa nake so muje mu ritsa shi kafin ya gudu, macucin banza. Kinsan mijina ya sake ni kuwa? Korar kare yayi min fa. Na zabura na dafe kirji nace au daman kinsan macuci ne kika kaini wurinsa. Tace ke dai muje muji abinda zai ce mana. Na fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun. Allah ba Ya dorawa bawanSa abinda ba zai iya ba sai dai bawa ya dorawa kansa. Ina zan sami himilin kudin da na ranta in biya masu shi, ummi yaya zanyi? Ummi ta dubeni a fusace tace to ni kinsan irin zaryar da ake yi min a gidanmu saboda bashi? Ke dai kawai Allah ya rufa mana asiri. Na fusata nace babu wanda ya taba saka ni a tozarci da tashin hankali a rayuwata irinki. Ta harare ni tace dan Allah aisha ki rufe min baki, gara kema baki aure shi ba balle ya sake ki, nifa har da goyo, na zama bazawarar karfi da yaji. Haka dai muka tafi muna ta fada a hanya kamar zamu cinye kanmu a cikin bus. Tana jin haushina ni har nafi jin haushinta fiye da malamin ma. Muka iske shi a zaure yana ganawa da wasu guda biyu da alama hamshakan masu kudi ne, daga ganin motar da suka zo da ita da kuma kayan da yake jikinsu. Malam yana ganinmu sai ya bata rai, bai amsa gaisuwarmu bai sai bakinsa ne suka amsa. Muka wuce jikinmu a sanyaye zuwa cikin gidan, da kyar daya daga cikin matansa ta bamu tabarma muka zauna sai wani irin kallon banza suke yi mana dan suna suyar dakwalen kajin da aka karba daga wajen mutane na sadaka amma suke juyewa a cikinsu babu wata sadaka. Shi da iyalansa sun zama tika tika saboda da cin kaji da raguna da suke karba da sunan za'a rabawa almajirai. Na zunguri ummi na nuna mata kajin da ido, ta gyada kai ta fada a hankali tace eh kudinmu ne, ai yau sai na masa rashin mutunci. Can malam ya shigo ko kallonmu baiyi ba ya wuce dakinsa, yayin da matarsa daya ta dinga wucewa da abinci kala kala tana kai masa, kamar shayi, kaji soyayyu, wainar kwai da biredi. Mu dai muna zaune muna kallon ikon Allah. Su kayi kasonsu a faranti yara da manya suka dauka kowa yana ci babu ko sala daya da suka bamu. Malam yaci ya gyatse, yazo ya wuce ya shige wanka. Ya fito ya shiga daki ya fesa kwalliya da farar shadda mai kyau sannan yazo ya wuce ciki daki in da yake ganawa da baki. Sannan ya aiko matarsa yace ta kiramu. Muka shiga muka iske shi a tsaye a tsakiyar dakin, muka sake gaishe shi ya amsa a gaggauce. Yace daman yau mu kayi daku zaku dawo? Haushi ya kama mu, sai ummi ta kalle ni, nima na kalle ta sai ta murguda baki tace yau ne laraba ko? Kuma yau kace mu dawo. Ya kalli agogo yace kuma ce muku nayi kuyi sammako? Ummi ta fada a fusace, kamawa tayi ka ganmu yanzu kasan ba lafiya ba. Ni dai ina zaune a lungu nayi kuri ina kallon irin wannan damfara kiri kiri, a lokacin da zai karbi kudinmy yana fara'a yanzun da muka zo karbar aiki rai ya baci. Ummi tana durkushe tana kokarin sakko da goyonta. Sai yace ba sai kin sauke goyonki ba yanzu zan sallame ku akwai inda zanje don sauri nake yi. Ummi tace ko yanzu zaka sallame mu ai na sakko da 'yata tasha nono ko? Tunda ta farka tana kuka. Yace meye ma yake tafe daku? Ummi ta waigo ta sake dubana tace kinji ya manta ma. Saina sankare a zaune na tabbatar mun fada hannun mayaudati kamar yadda kawayena khadija da maryam suka fada. Ummi ta sake cewa malam gaskiya komai ya kwabe tsakanina da mijina, har ya sake ni. Ga kawata ma taji shiru bai zo ba. Yace kuje zan bincika naga abinda yake faruwa, amma aiki dai na gama. Ummi tace wanne bncike kuma, kai da ka mance abinda muka fada maka. Ya zazzare mata ido yace ke ba'ayi mana tsiwa ana kibi a hankali. Ummi ma ta zare masa ido tace tsiwwa ko zance gaskiya? Ni dai ba zan gidan nan ba sai an san abin da za'ayi, kudin da muka biya a banza kenan, bashi muka ciyo muka kawo maka. Aisha farida kiyi magana kyayi shiru. Na fada a sanyaye mai zance ummi? Ya jawo wata jakar leda a fusace sai ga daurin rubutu kashi kashi, ya miko min daya ya mikawa ummi daya, ya sake kwance wata ledar ya miko min laya daya, ya mika mata daya. Duk iri daya ce. Yace kuje kusha rubutun nan a tsaye, sannan ku kasance layan nan a jikinku sai kuyi kokari ku hadu da mazan da kuke so, ku tambayesu duk abinda kuke so daga gare su zasu yi muku. Ummi ta karba ta tabe baki tace mu fa ba wani abu muke nema a wajen mazan ba illa soyayyarsu. Yace to ai haka nake nufi ko soyayya ko kudi duk zasu baku. Na zuba abubuwan daya bani a cikin jakata na mike tsaye nace da ummi taso mu tafi. Ta mike a fusace tace zamu tafi malam, sai dai gaskiya idan bamu ga canji ba zamu dawo, asan abinyi dan bangane irin wannan aikin ba. Muka fice yayin da ya bimu da harara, muka fito tsakar gida dukkanin mu rai a bace. Matansa sunyi carko carko suna kallonmu domin suna jiyo duk abubuwan da ummi take fada. Ta harare su tace Allah Ya isa kudinmu da ake damfarar mu ana cin kaji, ko wacce shegiya tayi bul- bul da abincin haram. Ni dai nayi wuf na fice kada a biyo mu da duka, har zaure suka rako ummi suna zaginta tana zaginsu. Naja hannunta muka tafi, a hanya ta fashe da kuka don takaici, ni kukan ma na kasa yi sabida tsananin tashin hankali. Tace dani aisha kinga macutan malamai ko? Wallahi ni ban taba kula da cutar da wannan dattijon yake min ba sai yau. Duba kiga yadda komai ya dagule mana. Nayi ajiyar zuciya nace yanzu ummi meye abinyi? Tace kije wajensa ki gwada ki gani bayan kin sha rubutun kin daura layar. Nima yanzu gidan yassar zanje in gani ko zai kula ni, idan abinda ya bani bai yi aiki ba wallahi sai na dawo na tarawa malamin nan mutane. Nace kina ganin wannan rubutun da layar daya bamu ta gaskiya ce? Ta wa da naki fa iri daya ne, babu wani suna daya tambaya balle ace kowa daban, rubutun ma daga gani ba namu bane saboda baiyi niyyar bamu komai ba sai da yaji kince babu inda zakije idan baiyi wani abu ba sannan ya bamu. Tace ke dai muje mu gwada mu gani. Mukayi sallama na hau acaba zuwa asibitin malam ummi kuwa ta hau bus zuwa unguwar zango gidan yassar. Ina sauka na bude jakata na zaro kullin runutu na tashi tsaye kamar yadda ya umurce ni na shanye, yayin da na ciro layar nan na damke a hannuna na nufi ofishin sahibina. Ina mai karanto adduoi don neman dacewa. Zuciyata cike da fargaba. Na tura kofar ofishin a sanyaye gami da yin sallama, zazzakar muryarsa ce ta amsa sannan na tura kai na shiga. Kallo daya yayi min ya dukar da kansa kasa bai sake dagowa ba yaci gaba da rubuce rubucensa. Na gaishe shi ya amsa a shelake yayin da fuskarsa babu annuri. Na dade a tsaye bai ce dani komai ba kuma yaki dagowa ma ya kalle ni. Nayi ajiyar zuciya na tambaye shi a tsorace dr lukman ya zo kuwa? Da yazo da baki ganshi ba. Amsar da ya bani kenan. Nace likita ina da tambaya game da kurajen fuska. Sai yace dani ke fita ki bani wuri, nan ba ofishin dr lukman bane, ya koma ofishinsa a room 8 an gama masa gyaran, kada ki sake shigowa nan nemansa. Nayi sadan sadan na fice, na dade a tsaye a bakin kofar daga waje ina takaici tamkar in rusa ihu. Sai wata zuciyar ta raya min ko in saka layar a bki in tauna zata fi aiki. Sai na zura ta a baki ina taunawa na sake tura kofar na zura kaina ciki. A tsaye a tsakiyar ofishin na iske shi yana duba wani littafi a jikin durowar littattafan dake kusa da bakin kofar. Nace dan Allah likita zan iya bar ma sako ka bawa dr lukman? Naje ofishinsa baya nan..... Ban rufe bakina ba naji ya banko kofar ya rufe booom saura kada ya bame da fuskata, ba dan na daka tsalle nayi baya ba, daya illata ni. Tunda na kalli kofar waje bansake waiwayr ofishinsa ba, na saka a raina ni dashi har abada koda kuwa zan mutu banyi aure ba a duniya dan wannan wulakancin ya isa. Naji na tsane shi na tsani kaina. Na tsani ummi da ta saka ni a hanyar halaka kuma na tsani malamin daya cuce ni ya tagayyara ni. Na toho da layar daga bakina na farke ta saiga takadda a ciki babu abinda yake ciki sai zanen wani hatimi mai gida gida an rubuta alifun, ba'un, ta'un kawai aciki. Na fusata na yayyaga kuci kuci na watsar yayin da kuka ya turnuke ni. DUK KYAN TAKALMI 14 Kawata ummi wacce na taba baki labari tana son wani malamin mu a sakandirw abdulyasar shi kuma baya son ta amma daga baya ya fara sonta har ya aure ta, ita na tuntuba don ta bani shawara. Sai tace dani malamai ne suka yi mata aiki, dole akayi masa yazo ya aure ba a hayyacinsa ba. Don haka sai ta jani wajen malaminta ya ce in kawo masa naira dubu ashirn da biyar zaiyi min asirin da dr shureim zai zo har inda nake da kansa, ya aure ni. Dogon salati abida ta dauka ta dafe kirji tace farida boka? Me ya kaiki bin bokaye akan wannan 'yar karamar matsalar? Sai na daga ido da sauri na dube ta, ina mamakin yadda ta ambaci matsalata 'yar karamar matsala. Nace a raina lallai abida bata san yadda dr shureim take ba da yadda halayensa suke ba shiyasa take ambaton haka. Abida ta dora hannu aka tace innalillahi wa inna ilaihir rajiun. Aisha farida kinyi kuskure. Wai shin ina wayon nan naki? Ina dubarunki? Ina iya zama da jama'ar da kika koya daga wajen magabatanki? Ai wannan matsalar taki karama ce. Ke kika zamar da ita babba gashi kin cuci rayuwarki duniya da lahira. A duniya kin jawowa kanki bashin da zai kaiki zuwa ga kotu a daure ki, kin dauko hanyar rugurguza karatunki. Sannan kin taba lahirarki domin ibadae ki ta ragu saboda damuwa da kika jefa kanki, kinje wajen boka mai duba wanda Allah Ya haramta, duk wanda yaje wajen mai duba, mai zuba wuri ko mai bugun kasa kuma ya gasgata abin da ya duba ya fada masa tabbas bashi da sallah har kwana arbain , Allah ba zai karba ba. Idan kika mutu a tsakanin wadannan ranakun me zaki cewa Ubangijinki? Kin zama makaryaciya domin karairayi iri iri kike shirgawa wanda ada ba halinki bane kuma kinsa makomar makaryaci wuta ce. Baki kyauta min ba farida da baki fada min matsalarki ba har sai da komai ya cabe. Na girgiza kai nace na hakura da dr shureim yadda iyayena suka bar duniya na san na rabu dasu har abada haka na rabu da shi daman bai san abinda nake yi ba. Wallahi anty abida ba da ganfan na dorawa kaina sonsa ba haka na tsinci kaina, nima ba da son raina ba. Abida tace haba haba kamar yaya zaki hakura dashi bayan wadannan bala'I da kika fada a dalilin sonsa ai ba zai tafi a banza ba. Nayi miki alkwarai da izinin Allah (SWT) sai kin sami soyayyar dr shureim cikin ruwan sanyi. Na kasa kunne ina sauraron maganar abida tamkar tatsuniya. Na dauke ta a matsayin mai iya zance don hankalina ya kwanta kawai. Duk da nasan babu abin da ya gagari Allah, amma abin da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa. Abida ta luta da tunanin da nake yi a zuciyata ta ga alamar ban yarda da abubuwan da ta fada min ba. Tace aisha farida kin manta da yadda akayi na auri yayanki hussaini? Kin manta ra'ayinsa na son girma ba zai auri kanwarsa ba a lokacin da iyayenmu suka yi sha'awar hadamu aure yake kokarin bijirewa? Kin manta yadda muka fara zama dashi a gidan nan, ni dake muna tsoronsa ko muryarsa muakji jikinmu sai ya dau rawa muna guje guje? Yaya kika ga zamana dashi a yanzu? Bari in fada miki abinda baki sani ba farida, yayanki hussaini a tafin hannuna yake yanzu idan naso in daga shi sama, idan naki sai in kifa shi kasa ya fado. Yaya hussaini a halin yanzu baya iya bacci idan ina fushi dashi sai ya bani hakuri na hakura sannan hankalinsa yake kwanciya. Hussaini baya boye min komau na game da samunsa, baya boye min duk halin da yake ciki na game da abokan sa zuwa danginsa balle 'yan matan waje domub mazan zamaninan ba'a rasa su da 'yan matan zamani, ko basu ce suna sonsu ba su 'yan matan zasu kawo kansu. Ki tambaye ni ya akayi haka ta faru? Ta ina na samo kansa? Farida wallahi ban taba zuwa wajen wani boka ko malami ba nace ina neman a mallake min hussaini. Mutane suna mamakina yadda nake tankwasa hussaini yake yin abinda nake so, har wasu kawayena da 'yanuwana suke tsokana ta wai ina hada su da malamina wanda ya tankwara min hussaini. Idan na fada musu ban taba zuwa wajen wani malami ba a rayuwata sai suki yadda. Aisha farida bana addua har karshen rayuwata in taka kafata wajen wani malami ko boka don yayi min adduar mallaka. Ina daga hannayena sama in roki Allah Ya mallaka min mijina, mu zauna lafiya, yasoni kamar yadda nake sonsa. Na girgiza kai nace na fada cikin kuka anty abida na hakura da dr shureim saboda bai san halin da nake ciki ba, mutumin da baya kallon fuskata baya amsa min gaisuwata, ta yaya zai soni? Kawayena guda biyu har mota gare su kyawawa ne, ko khadija bata fini kyau ba. Maryam ta fini kyau suma dole suka gaji da wulakancinsa suka hakura dashi. Na rasa yadda zanyi in daina sonsa duk da adduoin da nake kwana ina yi don Allah Ya yaye min sonsa amma sai karuwa yake yi na fada tsaka mai wuya, hatta da karatuna ya tabarbare saboda sau biyu supervisor dina yana zuwa yana duba ni daga makarantar mu bana nan. Don haka na san in banyi da gaske ba dole sai na maimata attachment dinnan wata shekarar. Ko a littafi ban taba karanta labarin wacce ta fada irin wannan matsananciyar soyayyar da na fada ba, makauniya kuma gurbatacciyar soyayya don bai san dani ba balle ya san abinda nake yi ba. Sai na rushe da kuka. Abida tayi murmushi ta dafa kafada ta sai ta girgiza ni tace haba farida, ke macece fa, dama akwai wani da namiji da zai baki tsoro duk haduwarsa? Ina so ki yadda da kanki, ki dauka duk in da wata mace ta je zaki iya zuwa, ki dauka duk abinda tayi zaki iya yi. Ki manta da farar fatar baturiyar da yake aure, ke bakar fata sai ki fita a wajensa. Sai naji abida ta fara bani haushi da wadannan maganganun nata masu kama da almara. Na rasa yadda zanyi in fahintar da ita waye dr shureim. Na tambaye ta cike da damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin manta kissar matan nan da akayi mana a makarantar islamiya? Kin manta matar nan da take wajen malami ta nemi da ya bata abinda zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu, an samu sabanin malamai, sabanin malamai kuwa rahama ce duk dai abu daya suke nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa malamin cewar maganin mallaka take so ya bata, sai ya umurce ta data je cikin daji ta nemo masa gashin idon zakanya mai rai da shi zai hada mata asirin mallaka. Matar nan ta firgita da jin wannan babban aiki sai tace dashi malam ina zanje in samo gashin idon zakanya mai rai ai bazata bari a tsinka ba saboda fadanta. Cinye mutane take yi. Malam yace shi dai gaskiya saida wannan gashin zai iya hada mata wannan magani. Matar nan ta tashi ta koma gida zuciyarta cike da zullumin tadda za'a yi ta iya cirar gashin idon dabbar da tafi kowacce irin dabba a duniyar nan hatsari. Da farko sai taje kasuwa ta sayi rago aka fede mata ta dauki himilin nama ta shiga dawa, tana hango zakanya da 'ya'yanta daga nesa suka fita neman abinci sai taje bakin ramin ta ajiye mata naman nan ta gudu ta labe. Da zakanya ta dawo sai ta iske abinci lafiyayye a kofar dakinta ita da 'ya'yanta suka taru suka ci. Washe gari ma haka matar nan ta kawo gyararren rago ta ajiye mata bayan ta tafi kiwo ta sake labewa bayan ta ajiye. Zakanya taje neman abinci ta dawo ta iske abinci har gida suka ci ita da 'ya'yanta. Haka matar nan ta dinga yiwa zakanya sai dai su dan matsa daga bakin ramin don su dawo su tarar da abinci. Da zarar sun matsa kuwa matar sai tazo ta ajiye musu sai su dawo su tarar da abinci kamar kullum. Zakanya ta tabbatar lallai kawai wata mai kirki da take kyauatta mata dan haka ko sanda taga matar ta ajiye mata abinci bata biyo ta nemi ta lahanta ta ba. Ba sai dai tazo taci kawai. Har suka fara sabawa tana ajiye mata abinci a gabanta bata guduwa. Har ta kai ta kawo matar ta fara shafa jikin zakanyar nan bata motsawa. Tayi ta shafata don sabo har ranan matar ta samu ta tsigi gashin idon zakanya ba tare da zakanyar taji zafi ba. Mata ta kaiwa malam gashin nan ya karba ya duba ya tabbatar gashin idon zakanya ne mai rai don yaga jini jini a jikin gashin. Sai ya cika da mamaki ya tambayeta ta yaya akayi ta samo gashin? shine ta bashi labarin yadda tayi. Malam yace to haka zakije ki yiwa mijinki kamar yadda kika yiwa wannan zakanya babu wata mallaka da tafi hanyar nan da kika bi kika saba da zakanyar nan. Na tambaye ta cike da damuwa ta yaya zan samu soyayyarsa, har nafi baturiya farar fata da yake matukar so? Na fada miki fa bai sanni ba, yana dai ganina daga dukkan alamu ma ya tsane ni da zara ya ganni yake hada rai. Abida ta sake yin dariya tace kin manta kissar matan nan da akayi mana a makarantar islamiya? Kin manta matar nan da take wajen malami ta nemi da ya bata abinda zata mallake mijinta. Kissar ta rabu gida biyu, an samu sabanin malamai, sabanin malamai kuwa rahama ce duk dai abu daya suke nunawa. Na farko aka ce ta da ta fadawa malamin cewar maganin mallaka take so ya bata, sai ya umurce ta data je cikin daji ta nemo masa gashin idon zakanya mai rai da shi zai hada mata asirin mallaka. Matar nan ta firgita da jin wannan babban aiki sai tace dashi malam ina zanje in samo gashin idon zakanya mai rai ai bazata bari a tsinka ba saboda fadanta. Cinye mutane take yi. Malam yace shi dai gaskiya saida wannan gashin zai iya hada mata wannan magani. Matar nan ta tashi ta koma gida zuciyarta cike da zullumin tadda za'a yi ta iya cirar gashin idon dabbar da tafi kowacce irin dabba a duniyar nan hatsari. Da farko sai taje kasuwa ta sayi rago aka fede mata ta dauki himilin nama ta shiga dawa, tana hango zakanya da 'ya'yanta daga nesa suka fita neman abinci sai taje bakin ramin ta ajiye mata naman nan ta gudu ta labe. Da zakanya ta dawo sai ta iske abinci lafiyayye a kofar dakinta ita da 'ya'yanta suka taru suka ci. Washe gari ma haka matar nan ta kawo gyararren rago ta ajiye mata bayan ta tafi kiwo ta sake labewa bayan ta ajiye. Zakanya taje neman abinci ta dawo ta iske abinci har gida suka ci ita da 'ya'yanta. Haka matar nan ta dinga yiwa zakanya sai dai su dan matsa daga bakin ramin don su dawo su tarar da abinci. Da zarar sun matsa kuwa matar sai tazo ta ajiye musu sai su dawo su tarar da abinci kamar kullum. Zakanya ta tabbatar lallai kawai wata mai kirki da take kyauatta mata dan haka ko sanda taga matar ta ajiye mata abinci bata biyo ta nemi ta lahanta ta ba. Ba sai dai tazo taci kawai. Har suka fara sabawa tana ajiye mata abinci a gabanta bata guduwa. Har ta kai ta kawo matar ta fara shafa jikin zakanyar nan bata motsawa. Tayi ta shafata don sabo har ranan matar ta samu ta tsigi gashin idon zakanya ba tare da zakanyar taji zafi ba. Mata ta kaiwa malam gashin nan ya karba ya duba ya tabbatar gashin idon zakanya ne mai rai don yaga jini jini a jikin gashin. Sai ya cika da mamaki ya tambayeta ta yaya akayi ta samo gashin? shine ta bashi labarin yadda tayi. Malam yace to haka zakije ki yiwa mijinki kamar yadda kika yiwa wannan zakanya babu wata mallaka da tafi hanyar nan da kika bi kika saba da zakanyar nan. Don haka babu wani asiri da ci idan babu biyayya, na kaskan da kai, ba tsabta, ba kalamai mai taushi tsakanin mata da miji. Nima nan da kika ganni da wannan kissar nayi amfani har na sami hussaini tamkar jaririn da sai an dauka, sai an juya, haka zaki bi ki samu soyayyar dr shureim. Na dube ta a shelake nace ta yaya? Ta nisa tace zan fada miki abubuwa guda biyar idan kika kiyaye zaki sami shureim a garabasa ba tare da kin wahala ba, kamar kibtawar ido da bismillah. Fardida duk inda namiji ya kai da ji da kai, da daga kai karshensa dai mace zai aura kuma dole ta bautar dashi ko yaki dan kada ya bare sai yayi dan Allah Ya wajabta akansu dole suyi. Dole ne miji ya ciyar da matarsa, dole ne tufatar da ita, dole ya nemo mata muhalli, dole ya kai ta asibiti idan bata da lafiya. Idan aka sami marar tsoron Allah wanda ba zaiyi dan Allah ba to zaiyi ko dan kada duniya ta zageshi. Dan idan ya bar ta cikin tsumma, ba abinci za'a nuna ta agari ace matar wane ce baya kula da ita. Dan haka DUK KYAN TAKALMI, duk tsadar takalmi, ba za'a daura shi a wuya ba ko a goshi ba, dole kafa za'a saka kuma a taka a kwata, shiga daji, a shiga bandaki, a tako kazanta, a taka bola ko a tako kaya dashi. To haka dr shureim zai zama a wajenki da izinin Ubangiji, babu boka babu malam. Naji tamkar tana busa mi sarewa a kunnuwana saboda dadadan bayananta, na gyara zama nace meye abu biyar din da zan kiyaye....? Ban rufe bakina ba sai muka ji ana buga mana kofa kamar za a karya, hayaniyar matan da muke jiyowa daga nesa ya matso bakin kofar dakin mu. Fadi ake ke aisha farida, ki fito ko a balle kofar nan. Yaya zakici kudin mutane ki shiga daki ki buya, ga 'yan sanda nan an kira su, suna kofar gida za'a tafi dake. Ko ki bude ko a kirawo su, su shigo ciki su tafi dake. Na dora hannu aka na fashe da kuka nace anty abida yaya zanyi? Na shiga uku , yanzu ankwa 'yan sandan nan zasu saka min su wuce dani ta gaban mutanen unguwar nan ko kamar wacce nayi sata kowa yana ganina ko? Hawaye ya zubo daga idanuwanta itama, sai ta mike tsaye ta tashe ni tsaye nima, ta dafa kafaduna da hannayenta biyu. Tace kiyi ta karanta innalillahi wainna ilaihir rajiun. Ki fita kice da yan sanda su rufa miki asiri kamar yadda Allah ya rufa musu asiri, su taimake ki kada su saka ki a gaba, zaki hau babur kije can sai su same ki acan ba sai sun saka ki a gaba ba. Nace ai bazasu yadda ba, sai sun saka ni a gaba kamar wacce tayi sata. Tace ke dai kici gaba da addua, ki fada musu hakan zasu yadda. Idan kinje can ki basu hakuri kice a baki kwanaki biyu zaki nemo kudin ki biya su, ni kuma anan zan tilastawa yayanki dole ko rance ne ya fita ya nemo a biya su kudinsu kaddara ce ta hau kanki kada ki damu. Kuma koda wasa kada ki sake ki fadawa wani ko wata abinda kikayi da kudin nan, dan kada ma labari ya dawo kunnen yayanki kenje wajen boka, ki barshi a kawarki kika taimakawa aka yi mata tiyata mijinta bashi da hali, yafi sauki dan idan muka kusukura mu ka bari yaji wannan labari sai ya bata mana rai. Dazu na siyar da samiruna hudu na biya su maijidda, dahare da dija dillaliya da kikaje suma kika ranto kudadensu. Wata tace dari takwas kika karba mata, wata dari bakwai, wata dubu daya, suma na suka zo suke daga min hankali suna nemanki danaji kudin ba yawa sai na aika kasuwa aka karyar min da su nazo na bibbiya su. Na uwani ne naji kudin da yawa ba zan iya biya ba. Kiyi hakuri aisha farida, kiyi ta istigfari game da wajen bokan da kika je, kinyi wa Allah laifi kuma kiyi ma Sa alkawari har ki koma gare shi ba zaki sake zuwa ba. Kiyi ta karanta wannan adduar ta neman biyan bashi "Allahumma bi jalika an haramika wa agnani fadhlika amman siwaka". Sannan ta bude kofa da sauri muka fito saboda bugun da ake yi ya tsananta. Dandazon matan gidanmu da matan unguwa da yaransu sun taru suna kallona. Abida na rike da hannuna muna kuka muka nufi hanyar waje. Muryar yaya hussaini mukaji ya daka tsawa mai firgitarwa har sai da kowa ya firgita. Yace da matarsa ta sake ni in tafi ni kadai ta dawo daki inje can in karata ni kadai. Ni da ita muka fashe da kuka. Ta rungumeni sannan ta lalubo hannuna ta damka min kudi naira dari biyu. Ta juya ta bar mi, sai na cigaba da tafiya a sanyaye na fice yayin da dandazon mata suke biye dani suna

Chapter 8 of 23