Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
miki yabani 1k harna saywa sa'id takalmi kito? abinda tace haka ne na tuna Allah sarki misbahu yana sonki har yanzu amma wannan uwar tasa bata kyautawa danta ba taci amanar haihuwa koda yake mijin wata baya auren matar wani mijinki na nan tafe.Aisha ta dago ta dubi abida saita mayar da kai ta kwanta jikinta a sanyaye ta fada cikin marainiyar murya insha'allahu.Abida tace ina dr shuraim? Takaici ya hana ta magana har zuwa wani lokaci mai tsawo babu wanda ya sake magana a cikinsu abida tayi ajiyar zucia tace farida kin cika sarewa baki da juriya akan abunda kike nema ki zama jaruma ki jajirce har sai kin sami duk abunda kike so kada ki tsorata domin qaramin aiki ne samun shuraim amma kin biyea maganar qawaye duk sun tsorata farida ta girgiza kai tace ba zai yiwu ba nan da nan farida ta juyo ta dube ta cike da mamaki marar misaltuwa ta fada a bayyane ikon Allah yai naga abunda yafi qarfina sai suka kwashe da dariya su duka abida ta gyara zama taci gaba dayi mata tsifa yayin da har yanzu farida na kwance ta dora kanta akan cinyarta abida tace idan dai har yanzu kina son shuraim bana so ki fitar da ran sumunsa domin Allah yana bawa bayinsa duk abin da suka roqe shi;farida ta girgiza kai tace aunty na haqura da dr shuraim ko maganarsa bana so ayimun abida tace kin haqura akan dole ko kin daina sonsa ne kwata-kwata?Aisha tayi shiru yayin da hawaye ya cika mata ido idan ta matse sai wani ya sake tsattsafowa abida ta shafa kanta tace kiyi haquri kukan naki zai koma dariya da izinin ubangiji idan baki manta ba na umarce ki daki riqe abu 5 wannan abu 5 din zai kaiki da samun nasara ki sami shuraim cikin ruwan sanyi uhmmm farida ke ambato tana kwance ta kasa magana sai bugun zuciyarta ke tsananin yi.Abida tace bazaki tambayeni abu 5 din bane? cikin sanssayar murya tace meye abun 5 da zan riqe? abida tayi murmushi gami da jiyar zucia tace Alhamdulillah a cikin 5 din nan zan fara fada miki 3 daga baya inga miki saura 2 a hankali.Aisha ta daga kanta a hankali ta dubi Abida zuciyarta cike da fargaba abun da abidar zata fada tana tantama ko zata jure su don ta qudiri aniyyar ba zata sake yin wahala ko zubar da ajinta ba wurin shishigewa dr shuraim abida tayi daria tace kada ki tsorata zaki iya ba wani abun wahala bane.farida tayi ajiyar zucia ta dafe qirji ta lumshe ido gami da qirqiro wani basashen murmushin da bai kai zuci ba ita dai a ranta tafi son abar maganar dr shuraim kawai shi yafi sauqi.abida tace abu na farko dana keso ki riqe a rayuwarki itace addu'a idan kika yawaita addu'a akan dukkan lamuranki zaki ci nasara Aisha ta gyada kai tace ina addu'a sosai ma kuwa abida tace wannan ta musamman ce a tsakaninki da shuraim ki roqi Allah ya zabar muku abinda da yafi alkhairi amma ke alkhairin wajenki shine ki sami soyayyarsa tunda kina sonsa,babu hijabi tsakanin ubangiji da bawansa ki roqi duk abunda kike nema a dunia da lahira idan dai halak ne ki zayyano masa duk yadda kike so babu kunya Allah mai karbar addu'a ne idan kika riqe addu'a ki yarda Allah zai amsa miki kin cika abu daya.Aisha ta gyada kai naji menene na 2? Abida tayi ajiyar zucia tace abu na 2 da zaki riqe bayan addu'a shine kizama mai tsananin haquri sai mai haquri ne yake cin ribar rayuwa ki daure ki jure duk abunda zaki gani haka duk nisan lokacin da za'a dauka ki daure kada ki qagu ko ki girgiza ko ki razana ba'a yiwa Allah dole kuma gaggawa daga shaidan take ma'ana duk tsawon lakacin da za'a dauka kafin shuraim ya karkato gareki kada ki gaji kiyi fushi kice kin haqura.sai na 3 shine ki riqe mutumcinki. Kada ki fito da maitarki fili ya gane halin da kike ciki na sonsa ma'ana kaja ajinki.Aisha ya yamutse fuska alamar nuna rashin fahimtarta a fili abida tayi murmushi tace zaki fahimce sai a hankali.farida ta tashi zaune ta dubi abida zuciyatra cike da quna tace aunty abinda kina nufin inyi ta bin shuraim ina zubar da ajina yana wulaqantani shine haquri? idan ba haka ba yaushe shuraim yasan dani balle yasan ina haquri dashi wata rana yaso ni?kin kasa gane waye shuraim idan ba office muka je ba bama ganinsa abun da ya fiye min sauqi shine na rabu dashi ni yanzu ko a hanya ma bana so mu hadu bawai na tsane shi bane ko yayimun wani laifi aa ko kadan bana zarginsa don bai ma san abun da anke yi ba sai dai don na samarwa zuciya ta salama.abida ta girgiza kai ai wannan itace juriyar da haqurin da nake kiyi ki taka inda yake ki ganshi ya ganki sannan kija masa aji Aisha taji tamkar abida ta dora mata dunia akanta don nauyin da kanta yayi taji hawayen takaici ya tsatsafo mata ta girgiza kai tace aunty abida zancen jan aji kuma a nan in har naje inda yake? ai na sayi wulaqanci da kudina abida tayi murmushi tasa gefen hannunta ta gogewa farida hawaye tace ki biyo ni a sannu a hankali zaki fahimce ni kuma zaki ga canji a wajen dr shuraim insha'allah ke dai kija mu je ki riqe matakan 3 addu'a.haquri da riqe mutunci.farida ta koma ta kwanta akan cinyar abida a sanyaye yayin da hawaye yayi ta zuba ta tuna mata abinda taci gaba dayi mata tsifa tana zayyano mata dadadan kalamai game da yadda zata sami shuraim idan har zata riqe addu'a zata riqi haquri.Aisha farida tana yin duk abun da abida ta shawarceta ta duqufa da yin addu'a safe da rana harda tsakar dare dama can ita gwanar yin addu'a ce tana da juriyar yin addu'a sai dai lokacin taji a ranta kamar abun ba zai yiwu ba bata lokacinta kawai takeyi sai ta tuno abubuwan da abida ta fada mata cewar ta roqi Allah duka abinda take so kada ta boye babu hijabi tsakanin bawa da ubangijinsa sai taci gaba dayi bata gajiyawa.tafi ambaton Allah kasan ina son shuraim idan da alkhairi shima ya soni. A CIKIN ASIBITI Aisha farida ce ke zaune akan wata doguwar kujera tana jiran matron maryam ta fito daga duba mara lafiya a babban dakin mata, zata bata sakon data aike ta ta karbo. Duk da ita ma daliba ce zata iya shiga, amma security ta hanata wucewa tace sai dai ta jira anan kasancewar shugaban asibitin aminu kano ne yake zagaye. Don haka manyan likitoci sai tururuwar wucewa ciki suke yi. Tana zaune tana jira har ranta ya fara baci, don ba don sakon nan ba da babu abinda zai rabota da karatunta, ita yanzu bata so a wuce ta koda dakika daya ne. Taji tamkar ta barwa security sakon inta fito ta bata, sai ta tuna zai iya bata kuma sakon yana da muhimmanci, don ba dan faridar ba ma da matron ta yadda da ita babu wacce zata aika ta karbo mata. Kudi ne da wasika ta karbo mata daga wajen matron aisha, a dakin 'yan awo. Aisha farida taja dogon tsaki sannan ta harari security din da ta jawo mata wannan dogon bata lokacin, sannan ta duba agogon dake daure a tsintsiyar hannunta. Karfe goma da rabi na safe daidai, ta daga ido zata kalli kofar dakin da matron ke ciki. Kicibus idanuwanta sukayi da abin da ya gigitata har sai ta zuciyarta ta daki allon kirjinta don firgici. Bata manta da ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun ba, yayin da ta daure bata nuna razanar da tayi a fili ba. Dr shuraim ne ya tunkaro inda take a zaune, yana tafe tamkar dawisu, cikin kyakkyawar shigarsa wato bakar suit, hannunsa rungume da file. Kallo daya tayi masa tayi saurin dauke idanuwanta, haka nan da nan ta kawar da fuskarta gefe daban, ko da ya karaso saitinta sai tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa har ya wuce bata dago ba. Wucewarsa ba dadewa sai taji wata sassanyar murya wata mata tayi mata sallama, da ta daga kai ta dubi matar sai taga wata zankadediyar ce fara sol, doguwa 'yar gayun gaske, mai kamshi na alfarma. Gefenta kuwa wata 'yar budrwa ce ke goye da yaro a baya, da alama dai mai aikinta ce ke goye da danta. Aisha farida tayi murmushi gami da amsa mata sallamar. Ta zauna kusa da aisha farida, sannan ta umarci mai aikinta ma tazo ta zauna, yayin da ta dubi aisha farida ta gaishe ta hade da tambayarta. Sai dai fargabar da farida ke ciki ta sake karuwa, don wannan zankadediyar matar dr shureiim take tambayarta. Aisha farida tayi sauri ta girgiza kai tace a'a bansan shi ba, sai dai ki tambayi security, nasan dai duk manyan likitoci suna ciki. Sai matar tace ai naga kamar security din nan bata da mutunci, bari kawai in kira shi a waya, da zan fito daga gida munyi waya yace min yana nan female medical ward, naga kuma ba a bari a shiga. Ta jawo wayarta sabuwa dal kirar blackberry ta matso sunan dr shureim idanuwan aisha farida na kai yayin da taci gaba da zazzare ido tana tunane tunane kala kala daban a ranta. Shin wannan wacece take neman abin kaunata? Toko matarsa ce? Cikin harshen turanci tayi masa magana tace faridarka ce ina nan female medical ward, an hana ni shiga. Aisha farida ta maimaita a zuciyarta. Faridah! Faridah!! Daman yana da wata farida bayan ni? Lallai abida tana so ta kaini ta baro ni, domin wahala kawai zansha babu alamar nasara a nan. Sai ta tuna da abubuwan da abida tace cewar tayi addua kuma tayi hakuri. Farida ce ta katse tunanin da aisha farida keyi, ta dube ta tace gashi nan zuwa ashe, baya ciki ya dan fita. Aisha farida ta gyada kai tace okay! Matar ta sake duban aisha farida tace yaya na ganki a nan zaune, ke ba ma'aikaciya bace, ko wani kike jira? Aisha farida tayi murmushi tace wata matron nake jira, ta shiga ciki aini daliba ce. Security ta hana ni shiga. Kuma dai yau ne ake hana mu shiga shima saboda shugaban asibitin yana zagaye. Haj farida tace toh shiyasa naga duk an koro 'yan zaman jinya a waje? Alla dai Ya ba wa kowa lafiya. Nima wallahi yarona na kawo bashi da lafiya, kwana yayi zazzabi kuma ga amai. Aisha farida tace subhanallah, ko hakori ne? Haj farida tace anya kuwa hakori ne? Bana jin hakori ne, don ya gama hakoransa, shekarunsa fa biyu da rabi, don kin ganshi a baya ne kamar jariri. Ina ga canjin yanayi ne, kinsan sauron kasar nan. Aisha farida ta gyara zama tace daga wacce kasa kukazo? Haj farida tace daga london, ai can nake aure. Nan da nan jijiyoyin jikin aisha farida suka rike, ta kasa cewa komai, babu makawa itace matar dr. To amma sai dai in 'ya'yan nasa guda biyu ne babbar mace ce, kuma tayi wayo don tana amsa waya radau. Cikin sanyin murya aisha farida ta tambaya shi kadai ne danki, ko akwai wasu? Haj farida tayi murmushi tace akwai yayarsu na baro ta a gida. Tabbas matar dr ce wannan, amma Allah yayi kyau da gayu a nan. Ai ruwa ma ba sa'an kwando bane, ina ni ina jera kishi da wadannan mata masu shigen kama da matan hurul ain? Aisha farida ta fada a ranta. Taji gaba daya bata da sauran wani tunani, kuma tasan shuraim yayi mata nisa. Rashin sanin shuraim na hakika ne abida take wannan daddagwar tana cewa sai anyi. Haj farida ta dubi aisha tayi murmushi tace yaya sunanki? Aisha farida tayi jim kadan, can tace sunana farida. Wow! What a coincidence is that? Sunanmu daya ai nima farida sunanan. Matar ta fada yayin da takeyin dariya, fararan hakoranta suka dau walkiya. Aisha farida ma tayi dariya tace oh haka ne kuma naji sanda kina waya kin fadi sunanki. Yaya sunan yaronki? Tace rislan. Aisha farida ta gyada kai tace rislan suna mai dadi, yaya sunan yayarsa ta gida? Tace sunan mamanmu ne aka saka. Aisha amma muna kiranta da momi. Aisha farida tace Allah Ya raya su. Haj farida tace amin. Yawwa ga dr shuraim nan zuwa. Aisha farida tahi wuyanta ya sage, har ba zata iya juyawa ta dubi bangaren da ya taho ba, don haka can gefe ta juyar da kanta har ya karaso gabansu ya tsaya. Kamshin turaren jikinsa mai sanyi shine ya daki hancin aisha farida, yayin da tattausar muryrasa da hadadden turancinsa yake ta dukan dodon kunnuwanta a inda aka hau dambe tsakanin zuciyarta da idanuwanta, idanu suka su juya su kalle shi, yayin da zuciyar ke son kallon abin da take kauna. Idanu suka rinjayi zuciyar aisha farida taki dagowa ta kalle shi Me yake damun dana ne? Oh my God rislan ciwo ne ya taba min kai? Inji dr shuraim a lokacin da yake shafa kan rislan. Haj farida tace jiyya bamuyi bacci ba wallahi, sai naji kamar yau in yanki ticket in juya london. Dr shuraim yayi murmushi yace no kar ki damu, mu nan asibitin muna da kwararrun likitocin yara, bari in kira kawata dr rukayya. Ya dauko hadaddiyar wayarsa kirar blackberry ya matso sunan dr rukayya ya fara da sallama, sannan ya gabatar da kansa. Yace dr shuraim imran ne yake magana, nasan baki san wannan layin nawa ba ko don sabo ne? Dr rukayya tayi murmushi tace ai kowa ya sanka da canje canjen layi kullum. Ya aiki? Dr shuraim yace alhmdlh, dama ina so in turo miki patient dinku, sister tace farida imran yaronta bashi da lafiya nake so ki duba shi, duk wani taimako da ya kama kiyi musu. Dafatan dai kina cikin asibitin? Dr rukayya tace haba meya abin yi min magiya, kanwar ka ai kanwata ce, to ka turo ta razo ina nan speciality yanzu. Dr shuraim yace nagode, gata nan zuwa. Sannan ya kashe wayar ya mayar aljihunsa DUK KYAN TAKALMI 2* 5 Aisha farida taji wani irin sanyi a ranta da Allah Ya sa kanwarsa ce ba matarsa ba, sai a lokacin kamanninsu suka bayyana. Tabbas kamarsu daya tamkar an tsaga kara. Har yanzu bata kallonsa ta juyar da kanta can gefe, amma fa kunnuwanta radau a bude tana sauraronsu. Dr shuraim ya dubi 'yar uwarsa yayi murmushi yace kinga ni yanzu ina tsakiyar aiki, bari in samo wacce zata raka ku speciality don nasan baki san kan asibitin nan ba, da sai in kwatanta miki, kuma ma da nisa. Ya dade yana kallon aisha farida, sai taji a jikinta kamar ana kallonta, tana dago ido sai suka hada ido dashi, nan da nan ta bata fuska, har da murguda baki, ta kawar da kanta gefe, don kada ma yaga fuskar aikenta. Shima yayi saurin dauke idanuwansa daga kanta ya bata fuska, ya juya ya nufi wani office ba jimawa ya fito tare da wata daliba likita na biye dashi a baya. Suka iso inda aisha farida ke zaune. Haj farida kuwa sai takalo aisha farida takeyi da hira, yayin da ita kuwa bata cikin hayyacinta. Dr shuraim ya kade mata hankali gaba daya ta rasa me yake damunta, sai da ta sake ganinsa ta tabbatar har yanzu sonsa na nan dankare a zuciyarta sai taji haushin zuciyarta da take jawo mata masifa iri iri. Dr shuraim yace ga dr zainab dalibata ce zata raka ku, kuma zata tsaya ki gama komai, sannan ta dawo. Dr zainab farin ciki fal a zuciyarta fara'a cike a fuskarta saboda yau dr shuraim ya kula ta har ya zabe ta ta raka kanwarsa, don haka ji take tafi kowa samun shiga. Tayi sauri ta duka ta gaishe da haj farida yayin da ta hau shafa kan rislan tana ta faman iyayi. Tanayi tana satar kallon dr shuraim, shi kuwa gogan abin da yafi tsana kenan, irin wannan shishigin sai ya fara bata fuska. Aisha farida tayi murmushi a zuci tace a ranta wayyo zainab ina tausaya miki indai dr shuraim ne zaki hadu da tsagewar zuciya bama bugun zuciya ba. Muma nan munyi mun warke. Haj farida da mai aikinta suka mike suka dunguma suka fara tafiya har haj farida ta wuce sai ta tuna ba tayiwa aisha farida sallama ba, sai ta waiwayo da sauri. Tace af kawata, takawarata na tafi ko, sai Allah Ya kara sada mu da alkhairi. Aisha farida ta dube ta, tayi dan murmushi ta gyada kai. Tace yawwa sai anjima Allah ya sadamu da alkhairi, Allah Ya bashi lafiya. Yayin da dr shuraim ya dubi kanwarsa ya juya ya dubi aisha farida da alama yana mamaki kuma daga dukkan alamu akwai alamomin tambaya a tattatre da bakinsa. Abin da kunnen aisha farida ya jiyo mata bayan sun juya suna tafiya shine ya dubi kanwarsa yace a ina kika san wannan yarinyar har ta zama kawarki, kuma takwararki? Haj farida tayi murmushi tace a nan na santa, yanzu ma na taba ganinta a duniya. Dr shuraim yayi dariya ya girgiza kai yace hmm mata, akwai kwashe kwashe, daga dan zaman da kukayi tare shikenan har kunsan juna, har da dogayen lanarai da sanin sunan juna. Suna ta maganar har sukayi nisa ta daina jiyo abin da suke cewa Aisha farida tayi ajiyar zuciya yayin da farin ciki ya rufeta, tasan dr shuraim yanzu ya santa duk inda suka hadu zai shaida fuskarta sannan zai tuna da sunanta tunda dai ba zai mance sunan kanwarsa ba uwa daya uba daya ba. Ko ba komai aisha farida taci riba tunda har ya damu yake yi wa kanwarsa tammbayoyi akanta. Ta fara Allah Allah a tashi daga asibiti taje gida ta bawa abida labrin cigaban da aka fara samu......bata gama tunanin da takeyi ba taji karan takalmi ana tahowa a baranda, ko da ta daga ido dr shuraim imran ta hango yana tahowa. Kallo daya tayi masa sai tayi sauri ta kawar da kai gefe, sai da ya wuce ta sai ta sake juyar da kai wani bangaren ta rantse shi dinne dai ba zata kalla ba. Abin mamaki sai taga ya wuce yana kallonta har da waiwaye. Don son ya gasgata abun da yake gani, sai ya dawo ya sake wucewa ta gabanta, wannan karon ma can gefe ta muskuta bayan kan ma har da jikinta ta juya ta nuno masa keya. Ya fice ya sake dawowa, sai yaga ta juya daya bangaren gaba dayanta. Tabbas ya shaida dashi take ba zata kalle shi ba. Baifi minti uku da shiga ba dakin marasa lafiya ba, sai gashi ya fito a karo na uku yana ta waya, amma fa yanayi yana duban aisha farida donya ga abun da zata yi. Sai tayi saurin dangwafar da kanta kasa ba ta dago ba har ya wuce waje, iyakacinsa kan baranda yaje ya dawo har yanzu wayar yake yi, da alama da kanwarsa farida suke magana tana wajen likita. Bata dago ba, sai da ta tabbatar ya shige babban dakin kwanciya na mata. Sai mamaki ya rufe aisha farida matukar mamaki kuwa. Wato ashe rububin nan da mata sukeyi a kansa da kallonsa, da shishige masa dadi yake ji kenan? Da gangan yake basarwa yasan ana sonsa kenan, ai ga shi yanzu bai ji dadi da ta share shi ba, tabbas ya bata satar amsa ya hadu da shariya sai ta rama duk abubuwan da yayi mata, inyaso ta rabu dashi daman ta fitar da ran samunsa. Bata gama tunanin da takeyi bi sai ta tsinkayo shi ya fito shi da matron maryam suna tafe suna magana har da kyakyata dariya. Dariyarsa tana tayarwa da aisha farida hankali, saboda sai yayi dariya kyawunsa yake kara bayyana. Aisha farida ta mike tsaye a nutse tana duban Matron maryam ita kadai, yayin da suka tunkaro inda take tsaye. Bai kalle ta ba, haka itama. Matron maryam ta dafa kafadarta tace Allah sarki 'ya ta yi hakuri na zaunar dake ko? Ina so in fito aka tsayar dani ai munyi waya da ita tace ba ta baki sakon ma yana nan waje shima yazo tun dazu, gezawa zai kai. Wannan shiriirta tawa dai Allah Ya shirya na barku ku biyu kuna jira, ke baki sanshi ba shi bai sanki ba balle ince ki bashi. Gashi baki da waya da na baki lambarsa, dole dai sai nazo. aisha farida tayi murmushi tace babu komai matron. Ta duka cikin ladabi ta mika mata 'yar karamar ambulan din. Matron maryam ta karba tayi godiya fuskarta cike da fara'a. Dr shuraim na tsaue a gefe hannayensa dukka biyi na cikin aljihun wandonsa kansa a sunkye a kasa bai cika kallonsu ba, yayin da aisha farida take gaggawar barin wajen, matron kuwa sai tsayar da ita take tana damunta da surutai barkatai. Dr shuraim ya dubi agogon dake hannunsa ya huya ya dubi matron yace sister maryam zan koma ciki, zamu hadu anjima, kinsan ina duba patient. Tsaya tsaya kanina, gara mu gama magana don idan ka zille min bansan sanda zan sake nemo ka ba, da gaske nake ni da mijina muna neman visa london ya za'ayi kenan? Aisha faroda ta samu ta sulale ta barsu nan a tsaye suna magana. Tana tafe tana mamakin wannan kyauta da Allah yayi mata a yau, Ya jeho mata sahibinta ta ganshi har ta gaji sabanin da, da sai ta yini tana zagaye bata ganshi ba. Tabbas abida tayi gaskiya, babu abinda yafi irin ka daga hannu ka roki Allah abinda kake so, zai biya maka bukatunka cikin gaggawa. Ta kudiri niyyar zagewa ta lullunka yin addua fiye da yadda take yi a baya. Ta isa wajen 'yan ajinsu sunyi aiki yadda ya kamata, har zuwa lokacin tashinsu, kowa ya lura yau aisha farida tana cikin walwala har ma wasu na tambayarta meyasa take murna yau. Da ta isa gida tun daga tsakar gida abida ta lura da yawan fara'arta don haka sai tabi ta cikin daki tana tambayarta. Lafiya meya faru yau naga kina ta fara'a? Ko aisha farida bata fada ba, abida ta canki daidai cewa tayi nasan dr shuraim ne ya saka ki walwala yau. Aisha farida ta kwashe da dariya ta gyara zama ta zayyane mata duk abubuwan da suka faru a yau. Tambayar da farida ta furta itace anty meye abunyi a nan gaba? Abida har kamar tafi farida farin ciki, sai tayi dariya tace ki zuba min ido gobe ni nasan abin da zanyi masa. Mamaki mara iyaka zaka iya gani daga idanuwan farida, zatayi tambaya abida ta katse ta, tace kada ki tambayeni, ki saka min ido kawai. Allah Ya kaimu gobe. Asuba ta gari AISHA SHURAIM!!! Washe gari da asuba kiran farko aisha farida ta bude ido, abin mamaki sai ta dinga jin motsi a kofar dakinta. Ta kame a kwance sannnan dai ta tabbatar ba aljanu bane, haka ba bakin dare bane wato barayi. Motsin abida ne don ta jiyo tarinta. Aisha farida ta cika da mamaki me ya fito da abida ne daidai wannan lokaci? Shine me takeyi a waje ta dade haka? Aisha farida ta mike a hankali tana sanda taje ta tura window ta leka duhu kirin tsakar gida, amma da hasken fitilar kwai a gaba abida, tana gaban murhu tana dahuwa. Sai mamaki ya sake lullube zuciyar aisha farida. Ta ambaci sunan abida atsorace a hankali cikin rada. Nan da nan abida ta dago ido ta dubi window tayi murmushi tace farida tsoro kika ji? Kada ki firgita nice dahuwa nakeyi. Aisha farida ta maimata dahuwa? Me kike dafawa da tsakar daren nan? Abida tayi dariya tace asuba ce ai yanzu, idan ya dahu zaki gani. Tayi wuf ta bude kofa ta fito tana kokarin bude tukunyar don taga abin da ake dafawa. Abida ta rike mata hannun. Tace idan ya dahu da safe zaki gani, abincin mijina ne. Aisha farida tace bulaguro zaiyi? Abida tace eh. Aisha farida tace ina zaije? Abida tace lagos. Aisha farida tace zai bi ta shagamu? Abida tace ba lallai bane don daga ofis zasu tafi. Aisha farida tace zai dade ne? Abida tace zai kwana biyu, kina da sako ne a fada masa? Aisha farida tace a'a zan so muyi sallamai dai kafin ya tafi saboda halin tafiya. Abida tace kada ki damu zan masa magana kafin ya fita sai kuyi sallama. Aisha farida tayi murmushi tace anti bari nayi alwala inyi nafilfili kafin a kira assalatu, sai inzo inci dadi, ina jin dai kaje ne ake rababbaka mana. Abida tayi dariya ba tare da ta bata amsa ba. Doguwar sujjada aisha darida keyi tana ta addua tana kai kukanta wajen Ubangijinta Ya bata abin da take so wato dr shureim idan har shine mafi alkhairi a gare ta. Idan kuwa babu alkhairi tana rokon Allah Ya yaye maata sonsa Ya bata wanda ya fishi alkhairi. Sai taji hawaye yana surnanowa daga idanuwanta, don tana tausayawa kanta da kanta, halin da ta tsunduma na soyayya. Ba ta bar kan tabarmar sallarta ba sai bayan datayi raka'atanil fijr da kuma sallar asuba, ta tofa adduoi a tafin hannunta ta shafa a fuska sannan ta mike zuciyarta cike da farin ciki tana da tabbacin Allah Ya amshi adduointa. Don shi kadai ne mai bayarwa wahidul kahharu. Daga nan sai ta shiga cuku cukun yin wanka da shiryawa saboda tafiya asibiti. Kafin ta kammala gari ya waye wasai, sai ga abida dauke da dan faranta da cokali a ciki ta mikawa farida. Aisha farida ta karba da sauri cike da mamaki, sai ta duba taga ai dambun shinkafa ne ya sha zogale da gyada, ya tiraru kuwa sai kamshi yake yana hayaki, da zafinsa kau. Ta koma ta zauna ta dandana, sai taji zakwai ya sha maggi da gishiri, ga dan yaji yaji sabida attaruhu da albasar da aka yayyanka yiri yiri a ciki, aka turara dasu sai kamshi yake tashi, hade da kamshin man gyada ziryan. Aisha farida ta girgiza kai ta sosa kunne tace tunda Allah Ya halicce ni ban taba cin dambu mai dadi irim wannan dambun ba. Lallai yaya yana cabawa irin wannan haduwa haka? Abida dai na tsaye a kanta murmushi kawai take yi bata ce komai ba har yanzu yayin da aisha farida ke faman turawa a cikinta tana ta santi. Aisha farida ta dagi ido ta dubi abida tace abin mamaki kuma dambu da aka sanshi da shakewa mutum makogoro sai gashi wannan dambun baya shake mutum silif silif yake wucewa. Wai, yaushe rabon in karya kumallo a gida, lallai yau zanfi jin dadin aiki don cikina yayi nauyi. Allah dai ya saka da alkhairi, Yaya hussani yayi sa'ar mata. Da dambun zai tafi a cikin food flask su dinga ci a hanya? Abida ta fita bakin kofa, sai ga tata shigo riki riki dauke da dan kwandon roba mai marika, irin wanda ake saka flask din abinci. Aisha farida tace lallai haduwa irin wannan sabon food flask haka? Yau aka bude shi daga leda duk saboda yayana tabbas babu mu babu kara aure. Abida tayi dariya tace bude ma kiga yadda aka shirya ciki. Aisha farida ta jawo kwandon ta daga wani babban hankici sakin ulu, wanda dashi aka lullube saman. Ta zaro wani dallelan flask mai madaidaicin girma, tsaka tsaki karkashinsa kuwa farantai biyu ne na tangaran da babban cokalin diba wato serving spoon da cokula biyu dukkansu sababbi ne filfil a wanke tas tas. Aisha farida ta gyada kai tace lallai wannan kwandon abin sha'awa ne tun kafin na bude ma abinda yake ciki. Abida tace bude mana ki gani. Aisha farida tayi bismillah ta bude, tana budewa sai wani kamshi

Chapter 11 of 23