Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tace habah meye abun burgewa a iya fada kuma?ni zubar da mutunci ne fada dole ce tasani sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu daya ba balle suce nazo zan kwace musu miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi dani saina na zama abar zagi,abar kyama daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara bare wani miji? Insha'allah sai Aisha farida tayi auren da babu wacce ta taba yin irinsa a gaba daya unguwar nan bana a layin nan ba ko gidan nan Allah yana tare da mu kuma da shi muka dogara yan gulma suka hau gasgata maganata suka hau nadama suna fadar alkhairin Aisha farida data taba yimusu a rayuwa nan da nan na bar wajen na kyale su suna ta kame- kame kanka ce kwabo dandali ya rore ya qare daya bayan daya suna ta sulalewa suna guduwa saboda kunya Aisha farida ta riqe baki don mamaki gami da farin ciki abunda abida tayi.tayi mata dai-dai ta burgeta tayi murmushi tace anty abida dama ke iya fada?amma bantaba ganin kinyi ba?abida tace habah meye abun burgewa a iya fada kuma?ni zubar da mutunci ne fada dole ce tasani sun kaini qarshe ina ruwansu da tsakanina da mijina idan zancen kudi ne zasu suyi duk zagin da zasuyi suyi akan haqqinsu ne mu muka taba su haqqinsu ne muka jawo wa kanmu amma ace tsaftar dana keyi da girki dana keyi da tsaftace 'yayana duk laifi ne ina ruwansu?aida haushi mu ba mijinmu daya ba balle suce nazo zan kwace musu miji banzaye,qazamai maimakon suyi koyi dani saina na zama abar zagi,abar kyama daqa-daqa dasu sai suyi kwana 3 ba wanka suna yawo da dauri qirji a tsakar gida ba kitso bare yankan qumba,bare ayi zancen su qunshi da turaren wuta ko turaren jiki basu gyara jikinsu ba ina zasu gyara yara bare wani miji? Aisha farida kwarai kuwa hakane ai ana zuba qazanta a gidan nan dukansu qazamai ne duk dakin daka nufa warin datti ne abida tace kece ma mai iya shiga dakunansu har ki zauna ki cakumi gashinsu ki kitse ni ina zan iya jure wari?ai shi yasa. Nakeso kici gaba da dagewa har sai kin sami dr shuraim shi kadai yafi dacewa da rayuwarki wani juyi Aisha farida tayi tashin farko ta kifa ta kwanta ta juya baya bata sake cewa komai ba saboda bata da abun fada taki jinin a ambaci sunan dr shuraim a halin yanzu balle ayi hirarsa.Abida tayi dariya tace au kiran sunan shuraim ma ba kya so shi ne kika juya mun baya? masoyin naki ne ya zama haka yanzu a wajenki?haba farida kada kiyi fushi kada ki sare da wuri mutane suna rasa ransu wajen neman abinda zuciyarsu keso ke yanzu wacce wuya kika ji har da zaki zame?keda shuraim kuna nan daram ba gudu ba ja baya ina nan akan bakana duk kyan takalmi qafa ce zata tattaka shi''Aisha farida ta jawo filo ta dora kanta ta toshe kunnenta sabida bata buqatar ci gaba da sauraron abun da abida ke cewa tamkar tana zuraro mata tsohon gyambon data dade da warkewa bata fatan gyambon nan ya dawo mata danye tafi son idan ya warke ya warke kenan har abada bata buqatar dayen ciwo ko maqiyinta bata masa fatan ya shiga halin data shiga. Abida ta fice tana daria ciki-ciki fitar abida ke wuya sai ta tashi zaune ta jawo jakar makaranta ta zubo littafanta da manyan text books dinda ta aro daga wajen khadija isma'I'll don ta karanta abubuwan da akayi bata nan.tabbas an wuceta. Da yawa sai tayi da gaske zata kamo su tana karatu zuciyarta na zogi idan ta tuno dalilin daya ja mata wannan matsalar sai taji haushin kanta da kanta ta qudiri niyyar ba zata sake bawa zuciyarta wannan dama ba balle takai ta ta baro ta.bata fito ba sai data ji ana kiran sallar magrib fitowarta keda wuya tayi kicibis da yayanta ya dawo daga aiki ya kuwa wurgo mata harara sai ta zube a qasa ta kwashi gaisuwa ko amsa mata baiyi ba ya shige dakinsa Aisha farida ta sake gasgatawa har yanzu da sauran rina a kaba maganar bata wuce ba kenan da saura?ta miqe a sanyaye taje tayi alwala ta dawo daki tayi sallah kafin ta idar taji motsin shigowar abida daga dukkan alamu wajenta tazo don har yanzu tana tsaye a kanta sai da ta idar da wuri taji abinda ke tafe da ita tana idarwa ta juyo ta dubi abida tace aunty lafia? Abida tace ki zo inji yayanki amma kada ma ki damu ba wani abu bane kinsan dai duk abubuwan dana shirya to duk abunda ya tambayeki ki haka zaki tsara masa yanzu ya du da mijin uwani a qofar gida suka tattauna suka wa juna haquri shine zasu je wajen yan sandan su sunar musu cewar an sulhunta an janye qara ba sai kun je ba.Aisha farida ta miqe da sauri dafe da qirji tace anti abida me zance masa game da cikon 5k dinsa da kike ce zasu ciko min?Abida tace a hakan zaki barshi zasu ciko din,idan basu ciko ba ai laifinki bane kuma ba zai kai ki qara ba dai shima sai ya dauki asara daba ki samo 12k bama ai dole ya nemo yayi belinki ba tunda ba zai bari a daure ki ba wata da watanni.nasan dai zaki sha fada ne da zagi kawai zagi kuwa baya qari idan da sabo ai kin saba'' Abida ta wuce gaba Aisha na biye da ita a baya ta sunne kai a cikin hijabi hannayenta kuwa dukka 2 na dafe da qirjinta sai karanto addu'io take iri-iri ba adadi tana mai neman agaji daga wajen rabbil samawati duk abun da zai zo yazo mata da sauqi.Allah mai amsar addu'ar bawansa sai ya sanyaya zucia yaya husaini maimakon yayi mata fada data bayyana a gabansa sai ya shiga yi mata nasiha yaji tamkar shima ya fashe da kuka lokacin daya ga hawaye a idon qanwarsa sai yaji tausayinta ya shiga nasiha mai hade da rarrashi yace farida haha farida kefa mai hankali ce mai sanin ya kamata ga natsuwa nayi mamakin yadda kike jefa rayuwarki cikinmatsla don kawai ki fitar da wasu daga matsala ba'a hana taimako ba amma kina so kina so kice min bata da dangi ne ko dangin mijin sai ke kika fiso sonta dasu?suna raye zasu bari ta mutu ne basu samo kudin da za'ayi mata tiyata ba sai ke?farida kinsan halin da muke ciki,ta kanmu muke yi,bamu da wani mataimaki sai Allah kullun hade-hade da kame- kame mukeyi sannan muci abinci sai naji tamkar na bar garin nan saina tuna talauci dana baro a shagamu har gara nan ma.ki riqe maraicinki ki riqe talaucinki ki riqe matuncinki ki riqe karatunki ki lallaba ki gama ki fara aiki ko zamu sami sa'ida babu ke babu sake cin bashin wani babu ke babu katsalandan akan matsalar wani ki tashi ki tafi Allah ya kiyaye gaba Aisha farida ta rushe da kuka tace nagode insha'allah zan kiyaye ta fice ta nufi dakinta ta shige ta takure tayi ta rusa kuka tana nai tuno iyayenta da suka rigamu gidan gaskia tabbas husaini ya fada mata gaskia dole ta nutsu tasan me ye a gabanta kuma ita wace ce a rayuwa?hawaye ya surnano daga idanuwan husaini yasa hannu ya goge abida ta matso kusa dashi ta fada cikin sassanyiyar murya tace yaya kaima kukan kake yi?kada ka damu fa kada ka saka damuwa a ranka ciwo ya same ta tsautsayi ne qaddara ce komai yazo qarshe ba za'a sake ba insha'allah. DUK KYAN TAKALMI 2* 3 Husaini ya girgiza kai yace ina son Aisha saboda babanmu yana sonta tayi kama dashi don haka idan na dube ta ina yawan tunawa dashi hawayenta ne yake tayar min da hankali.farida abar tausayi ce marainiya babu uwa ba uba nida nake riqe ta talaka ne ina matuqar tausayinta idan na ganta a cikin qawayenta yan gata masu mota baiwar Allah bata damuwa a haka take daurewa tayi karatu sai naji tamkar dama ina da yadda zanyi farida mata sami duk abubuwan da yan mata suke buqata kamar kayan kwalliya da dinkuna to babu misbahun ma da yake sonta yake taimakonta shima an raba su fatana Allah ya fito mata da miji na gari inda zata huta ko bayan raina ta taimaki kanta kota riqe min 'ya'yana ba''Abida tayi shiru tana tunani a ranta tace babu mijin daya dacewa da ita irin dr shuraim insh'allah farida saita sami shuraim ko don na hucewa mijina takaici a ransa ko don in cika masa burinsa na ganin farida ta sami gidan hutu nayi alqawalin zan yaqi zuciyar shuraim da addu'a da kuma kyautatawa har sai yaso farida yaya husaini ya katse tunanin da abida keyi yayi cimak ya miqe tsaye yace zanje waje malam yusha'u na jirana mijin uwani zamu je wajen yan sanda nan don a janye casa dinsu Aisha.Abida tayi masa fatan ya dawo dashi lafia ya fice da sauri.da Aisha ta idar da sallar isha'I ko abinci bata ci ba wajen datayi sallak kan tambarmarta a wajen ta kudindine ta kwanta babu abin da take yi sai sheshekar kuka da ajiyar zucia har barci ya dauke ta. Babu irin tashin da abida bata yimata don taci abinci taqi tashi tace ta qoshi a haka ta kwana saboda gajia da barcin data keji basu bari taji yunwaa ba bata farka ba sai da asuba kiran assalayu a kunneta ta miqe a nutse tana mai addu'io taje tayi alwala tayi sallah sannan ta shiga cuku-cukun yin wanka da saka kayan makaranta so take gari ya waye ta fice saboda gidan ya zama mata tamkar kurkuku haka tunaninta da hankalinta kakaf ya koma kan karatunta bata da wani buri illa taga ta gyara inda ta kuskuren kuma ta kamo yan ajinsu inda suka wuceta ta zamana mai nadama akan kuskuren data tafka a rayuwarta a kwanakin baya a dalilin shuraim sai kuma ta qudiri niyyar natsuwa da cire duk wani abu da zai gundiri rayuwarta giftawar husaini ta gani ta tagar dakinta ya dawo daga masallaci zai shiga dakinsa sai tayi wuf ta fito ta durqusa ta gaishe shi ya juyo ya dube ta duba mai cike da tausayi kasancewar yaga ta rame idanu wanta duk sun kode mata musamman data kwana 2 baka kwalli ba ya fada cikin yar siririyar murya farida lafiayar qalau kuwa ko baki lafia?tayi sauri ta sunkuyar da kai qasa gami da yin murmushin qarfin hali ta girgiza kai tace babu abinda yake damuna yay yace za a tafi makaratar ne har kinci dumame?ta gyada kai tace eh yasa hannu a aljihu ya dauko wata tsohuwar 200 ya miqa mata kamar kullun kamar yadda ya saba bata kudin acaba zuwa da dawowa da kuma na shan pure water.ta durqusa ta karba tayi godia ta shiga daki shima ya shige daki tana shiga ta mistsika yan powder a fuskarta ta gyara dan guntun hajabin da yake jikinta sai ta rataya jakarta a kafada gami da saqula 200 a zip din dake jikin jakar ta fito a bakin qofa suka hadu da abida lokaci daya suka yiwa juna murmushi Aisha ta gaishe ta abida ta amsa gami da cewa har kin fito ki tsaya kisha koko mana.Aisha tace sauri nake kada na makara supervisor nake son gani abida tace yunwa kuwa baza ta dame kiba ba kici komai da daddare ba na jiya da ranar ma da yawa kika ci ba Aisha ta langwabar da kai tace ba damuwa idan na dawo zanci abida ta kuncegefen zaninta ta dauko 100 ta miqawa farida tace kici abinci a can don nasan dole kiji yunwa farinciki yaa lullube Aisha ta karba gami da murmushi ta duqa tayi godia sannan ta juya ta nufi hanyar fita harta kai zaure sai taji muryar abida ni kiran sunanta sai ta juyo ta tsaya cak!tana dubanta kanar marar gaskia ta qarso inda take taja. Hannunta zuwa bayan kyauren zauren. Ta fada cikin rada daman inaso na tambaye ki dazu, to nasan halin kunnen hussaini, sai ya jiyo mu. Hankalin farida ya tashi ta dafe kirji tace me ya faru? Abida tace dr shuraim mana, zaku hadu yau kuwa? Kafin kace kwabo farida ta bata fuska ta kara da kai gefe, ta zumburo baki. Tace ba zamu hadu ba. Ta juya a fusace zata fice. Abida ta sake jawo hannunta tace fushi kike don naayi mmiki zancen shuraim? Kin daina sonsa ne? Aisha farida tayi caraf ta fada cike da gadara da takaici tace eh. Sai abida ta kwashe da dariya, yayin da aisha farida ta fice a fusace ko waiwayowa ba ta sake yi ba. A hanya ta hadu da musbahi ya fito daga gidan akan babur dinsa zai tafi wajen nema, sai ya tsaya a kusa da abar kaunarsa yana mata murmushin kauna. Sai dai kash! Zuciyar masoyiyar tasa a bace take, sai ta kawar da kai taki yin dariya ta gasihe shi ranta a bace. Wai kwana biyu nan wa yake taba minke? Musbahu ya fada yayin da yake duban fuskarta, yake murmushi. Ta kawar da kai gefe ta fara tafiya ba tare da ta bashi amsa ba. Yayi sauri ya sake biyo ta, ya tari gabanta har yanzu yana zaune akan babur dinsa. Abun mamaki sai yaga hawaye yana zubowa daga idanuwanta, nan da nan sai hankalinsa ya tashi ya shiga lallashinta yana bata hakuri, gami da rokonta ta hau bayan babur dinsa ya kai ta asibitin. Da farko taki sai da kyar ta hau suka fara tafiya. Ba tare da wani ya sake magana ba a cikinsu, sheshekar kuka kawai farida keyi a ciki ciki. Cikin marainiyar murya ta ambaci sunansa tace makarantarmu za ka kaini ba asibiti ba. Nan da nan ya amsa mata da to...to farida. Har bakin ofishin malam basiru ya kaita, ta sauko tayi masa godiya ba tare da ta dube shi ba. Ya kira sunanta cikin lallausar murya, ta juyo a tsanake tana sauraronsa, sai taga hawaye ya surnano daga idanuwansa, ta sake dubansa sosai, sai tayi mamaki tace lafiya? Yace farida kiyi hakuri ki yafe min nima ba da son raina haka ta faru ba. Ta tambaya cike da damuwa meya faru? Yace kwanan na ga kin shiga matsananciyar damuwa, har aka ce an kai wajen 'yan sanda an kulle ki duk da ba fada min takamaiman laifin da kikayi ba. Farida da ace tun sanda kika gama sakandire muka yi aure, da na killace ki duk da haka ba ta faru ba. Amma nasan komai mukaddari ne daga Allah, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwar da yake so ba, sai yadda Allah Ya so dashi. Sanin kanki ne duk duniya ke nakeso, kuma har abada ba zan daina sonki ba, matsalar daga wajen goggo ne ba don ita ta haife ni ba ina tsoron bakin uwa ba da tuni nayi faci da maganarta munyi auren mu. Na kasa son matar da ta aura min, na kasa cire raina a kanki. Ba yadda zanyi nace kada kiyi aure ki jirani, idan nayi haka na zalunce ki, tunda bansan ranar da goggo zata hakura ba amma kada kiyi gaggawar yin aure ki barni, kullum ina ta fadawa Allah, nasan kema kinayi. Toh muci gaba. Farida ta rushe da kuka, tabbas musbahu yayi gaskiya, abin da yake ranta kenan, cewar ba don yaki aurenta ba da ya za'ayi ta afka cikin wannan hatsarin? Sai ta juya da sauri ta nufi ofishin da tazo, yayin da musbahu yake kwalla mata kira taki ta waiwayo ma balle ta amsa. Tana shiga ofishin taci s'a ta iske malam basiru yana nan shi da abokinsa malam sulaiman. Bayan ta gaishe su sai ta barke da kuka marar kakkautawa, sai suka shiga damuwa suka shiga yi mata tambayoyi, lafiya take kuka? Suka bata kujera ta zauna cikin sheshekar kuka ta fara bayani. Sannan suka fahimci inda ta nufa da kuma dalilin kukan nata. ba 31 da 32 zan ci gaba da 33 Supervisor ya turo hula gaban goshi yace rashin lafiyar da kikeyi ce ta hana ki aiko 'yan uwanki suzo su fada min ko kuma ki aiko a rubuce a kawo min? Gashi yanzu sau biyu ina zuwa duba ku ba kya nan, yaya kike so nayi miki yanzu? Kije kawai wata shekarar ki dawo ki maimata attachment din. Ta sake fasa kuka taci gaba da ba da hakuri. Mal sulaiman ya dubi abokinsa yace a'a ba za'a yi haka ba, ka dai duba ka taimaka mata. Itace fa monitor kasan aisha umar bata da wasa, lalura ce ta jawo haka da dai Khadija sani ce, kawarta ba zan ma shiga zance ba, don nasan bata da kokari. Malam basiru ya gyada kai yace shikenan kije nan da kwana biyu zan shigo asibitin in duba kiki zama cikin shiri dan a koda yaushe zan iya fadowa. Ta durkusa tayi godiya. Aisha umar ta fito tana matse hawaya, amma zuciyarta cike da farin ciki, hankalinta ya fara kwanciya. Tayi mamaki da ta iske musbahu har yanzu yana nan yana jira bai tafi ba. Jikinsa na rawa ya kunna babur ya karaso inda ta ke yana tambayarta ta gama su tafi, ko akwai inda zai kaita kuma? Ta girgiza kai tace cikin asibiti kawai zanje. Ta hau babur suka tafi har yanzu ma dai babu wanda yake magana a cikinsu, tana nuna masa hanya har ya kaita inda take so, sannan ya tsaya. Tana saukowa sai taga ya dauko kudi ya mika mata, dubu daya 'yan dari biyar guda biyu. Yace karbi wannan bashi da yawa, a cikin kudin da na ranto miki ne ma zanje na biya su, amma ba zai gagara ba. Daga nan zuwa yamma zan cika in biya su. Aisha farida ta girgiza kai tace ka barshi na gode. Yace a'a ki karba farida babu komai, a shirye nake nayi miki duk abin da kike so idan baifi karfina ba, ko bani dashi zan nemo bashi na baki. Ta mika hannu ta karba a kunyace, ta duka tayi godiya. Ta dube shi sai taji sanyi a ranta ganin annuri a fuskarsa murmushi kawai yake yi mata naso da kauna. Ta rike kan babur dinsa tana murmurdawa ta dube shi tayi fari da ido. Tace musbahu na gode da dawiniyar da ka dade kana yi dani, nagode da kulawarka da damuwar da kayi dani a tsawon zamana da kai baka taba gajiya dani ba. Ko kadan ban taba zarginka ba akan rashin aurenmu, nasan daga inda matsalar take, ina adduar Allah Ya zaba mana abin da yafi alkhairi amma ba zan boye maka ba musbahu bana jin a jikina zamu iya aure, don banson nayi auren da zan kasance bani da kwanciyar hankali. Saboda mahifiyarka ta fito baro baro bata son abun. Koda naji sonka zai mamaye min zuciyata nakan yi addua Allah ya yaye min, sai nayi sauri na juya akalar zuciyata wani bangaren. Musbahu ya girgiza kai alamar takaici yace yanzu aisha farida har addua kike Allah Ya cire miki sona a ranki, koda yake bakiyi laifi ba idan kinyi hakan, amma ni ban taba fatan na daina sonki ba, ko da kuwa bama tare. Wa kike so yanzu bayan ni? Nasan dai ba zaki rasa ba, tunda a maganarki yanzu kin furta wata kalma da take nuna hakan....ke 'yar shagamu, lah lah lah zance ma kikeyi da sassafen nan? Muryar da ta jiyo daga bayanta kenan ita da musbahu suka waiwaya da sauri, maza biyu ne suke tafe akan doguwar barandar, su dukka suna sanye da wando da riga na bakar suit wuyansu sakale da abin gwaji. Ko ba a fada maka ba manyan likitoci ne. Dr lukman ne mai maganar, na kusa dashi kuwa dr shureim ne, daga dukkan alamu daga duba marasa lafiya suke, domin da daliba na biye dasu a baya. Ta dubi dr lukman tayi murmushi ta rufe ido da hannayenta biyu ta fada a kunyace a'a ba zance nake yi ba, yayana ne. Musbahu yace yayanmu ai kanwata ce na kawo makaranta. Gogan naka dr shureim baice komai ba, amma yana tafe yana dubanta kasa kasa har suka wuce. Kallo daya tayi masa ta watsar ba ta sake waiwayarsa ba, taci gaba da duban abin kaunarta musbahu, ta shiga yi masa bayanin inda tasan dr lukman. Abin mamaki abinda ya sake tsorata ta sai taji musbahu yana yabon kyawun dr shureim. Yace shi kuma daya likitan yay sunansa? gaskia yana da kyau irin wannan ne fa yake sawa wasu mazan suke hana matansu zuwa aiki idan suna ganin mazaje kyawawa irin wannan sai su tsani mazan su sai taji zuciayarta ta harba bumm! don fargaba ta tambayeshi me kace?ya maimaita abun da fada tace a ranta haqiqa na daukowa kaina ruwan dafa kaina amma Allah ya hayar dani dana gane gaskia gaskia ce wato 'yar uwansa maza ma kyawunsa suke gani balle yan mata lallai shuraim ba sa'an soyayyarta bane zuciata tayi garajen cusa kanta wajen ajalinta.tayi zuciayarta ta yamutse fuska tace bansan sunansa ba nima dai ina ganinsa dai kawai misbahu yace kina burgeni farida duk irin kyalkyalin dunia bai cika damunki ba har dana fara kishi musamman dana ga yana kallonki qasa- qasa na dauka shima ya sanki Aisha tayi murmushi tace ni banma kalleshi ba balle insan yana kallona kai ka lura da hakan misbahu yace aini tun daga nesa na hango su suna tahowa kece baki gansu saboda kin juya baya tunda ya tunkari mu yake kallo har na tsorata na dauka shima yana ciki Asiha tace aa ni ban ma sanshi bama zai wuce babur dinka yake harara bana ji ance ya tsani yaga mace ta hau babur.misbahu ya kwashe da daria yace kai dalibai akwai sharri waya fadawa haka?a zamanin kuwa ai sai an hada da hawan babur abu zai tafi dai- dai ba kowa yake da kudin daukar taxi drop na musamman mu talakawan da muke zaune a lunguna koda yake su manya ne matansu ba zasu hau babur ba sai mota ko? farida ta tabe baki tace shi ya sani wannan matsalarsa ce ni har bana son zancensa ma ya cika dagun kai. Dadi ya kama misbahu kansa ya fara huruwa wato saboda sonsa da farida keyi har bata ganin fuskar wani da namiji sai shi sai ya shiga washe baki tamkar sakaran daya ga sabon dinki yace in dawo na dauke ki idan kin tashi? ta riqe baki ce rufa min aisir misbahu qasada ce ma yanzu dana hau mashin dinka a unguwarmusaboda safiya ce babu jama'a da bazan hau ba sai a yi mana sharrin da ba zamu fita ba.anga mun fita tare sannan da yamma aga mun dawo me kake tunanin za'a ce mana?kaje kawai nagode sai wani lokaci idan Allah ya sake hada mu a hanya don goggo ta hana ka zuwa qofar gidanmu kuma bana so ka saba mata ta juya ta tafi tabarshi zaune akan babur yana dubanta zuciyarsa cike da da tsananin sonta gami da takaicin abun da mahaifiyarsa tayi masa ina ma za'a hada farida da matarsa?aiko kusa basu hadu ba farida mutun ce kuma abar so ce yarinya kyakyawa mai fara'a ga son mutane iya magana tafiya a nuste da dadadan kalamai mai dadin murya da iya kallo da sai kaji kwakwal war kanka za zillo.ga kyakyawan halaye bata da hassada ba kyashi ko mugunta bai motsa ba har sai da ta bace masa ya daina hango ta yayi ajiyar zuciya ya girgiza kai ya kunna babur dinsa ya tafi a sanyaye gabobinsa sunyi sanyi. DUK KYAN TAKALMI 2* 4 Cikin satin nan kakaf babu abinda farida keyi sai karatu agida da makaranta. Bata shiga kawaye, har a gida ba ta fitowa tsakar gida. Tana lungu ko da yaushe littafiinta ne a hannunta. Burinta ta kamo 'yan ajinsu inda suka wuce ta, ga uwa uba a cikin satin supervisor dinta zai zo ya duba ta. Ta cire damuwa a ranta, haka bata da sauran tunani yanzu, sai karatunta. Abinci ma ba ta fiye son ci ba, sallah ce kawai ta zame mata dole ta tashi tayi, sai bacci barawo idan ya sace ta, tayi kadan ta farka taci gaba. Kafin kace kwabo farida ta rame, kowa ya kalle ta sai yayi maganar ba ta damu ba, haka bata tsahirta ba. Burinta taci nasara akan abin da ta sa a gaba. Duk da wannan jajircewar da tayi, da dagewa ta haddace kusan duk inda take tunani za'a tambaye ta daga kowane bangare na karatunsu zata amsa. Amma sai ta hada da addua tana mai neman taimakon Allah akan karatunta. Alhamdulillah da supervisor yazo dubata a karo na farko ta amsa tambayayin dukka har sai da yayi mamakinta. Sati mai zuwa karo ba biyu ya sake zuwa ya duba ta, a wannan lokacin ta sake shiri sai yaji rugurguza tambayoyin da ya jero mata har ma tana kara masa bayanai akn abin da bai tambaye ta. Ya jinjina mata, kuma ta burge shi matuka. Taci maki da yawa don tafi dukkanin 'yan ajinsu ci. Daga karshe ya shawarce ta yadda take da kokari ta daina wasa da karatunta, taci gaba da dagewa ta fita da sakamako mai kyau, shi kuwa yayi mata alkawari zai taimaka mata wajen neman aiki, kuma ko cigaba da karatunta take so zai taimake ta. Farida dai sai farin cik take tana yi masa godia ji take tamkar an sauke mata nauyin da yake kanta sai yanzu hankalinta ya kwanta walwalarta ta dawo ta shiga cikin qawayenta kamar da suka ci gaba da karatunsu da kuma koyon aikinsu.idan ta dawo gida taci gaba da wasa da dariyarta ita da abida da 'ya'yanta duk da Asiha bata nunawa 'ya gidansu da maqotansu bacin ranta akan abubuwanda da suka yimata suna gaisawa sosai tayi musu fara'a amma ta daina zama cikinsu tayi hira dasu kuma sai suka dinga jin kunyarta ba kasafai bama suke iya hada ido da ita ba saboda kunyar abun da suka yimaya domin Aisha tana da kirki kuma tana taimaka musu ta kowace hanya.tun yaya husaini na tambayar kudin da ka ranta 5k har ya gaji da dadin bakin abida yayi shiru ya daina tambayarta.ranar lahadi misalin qarfe goma sha biu na rana bayan abida da aisha sun gama aikin tsaf sunyi wanka sunyi wa yaransu wanka sun tura su islamiyya yayin da yaya husaini ke cikin daki yana shigar baccin gajia kamar yadda ya saba ranar labadi ce kawai baya zuwa aiki itace kadai ranar hutunsa a sati.don haka abida da yaranta basa garajen yin shige da fice a dakin abida kada a tashe shi tunda sassafe take hado musu yan komatsansu ta kawo dakin Aisha a karo masa qofa daga ya karya kumallo yake kwacia saida azahar kuma zai farka.Aisha ta gama rangawa abida kitso ras a kanta kai ka ce fula ce akasa dan kyau sannan itama abida taya ta tsifar nata kan Aisha na kwance akan tabarta yayin data dora kanta akan cinyar abida wacce ke zaune ta mimmiqe qafa hira kala-kala Aisha ke zaune ke rerowa abida hirar da data yanzu ta shagamu data kano hade da qawayenta na makaranta.abida ta dubi Aisha sai tayi murmushi misbahu kuwa yana nan? farida ta gyada kai gami da yin murmushi .misbahu yana nan kin manta kwanaki na fada

Chapter 10 of 23