Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
turmutsitsi da wahalar zaman haya na siya mata gida a shagamu mai kyau na siminti, na bawa mijinta motar haya bus yana tuki yana samun na cefane, na biya mata makka taje ta sauke farari ta dawo na hada mata jari tana 'yar sana'a a cikin gida tana samun na batarwa,ita da 'ya'yanta suna saka sutura masu kyau suna makaranta mai kyau. Musbahu tsohon saurayina kuma tamkar dan uwana yanzu shima nayi masa rana don na bashi dubu saba'in ya kama shago na siya masa computers 3 da injin photocopy ya bude business center tasa ta kansa ya daina aiki a karkashin wasu. sai ga mamarsa data tsaneni da matarsa an rakosu gidan nan tana ta kuka tana neman gafara a bisa tsana da cin mutuncin data yi min a baya.harda cewa dama ace baya zata dawo mana data bar Musbahu ya aureni ashe ina da mutunci haka.tayita kallon gidana tasan nayi musu zarra, kyauta ta ban girma nayi musu na suturu da kudi mai yawada zasu tafi kadan kenan daga irin rahamomin da Allah yayi min duk a sanadiyyar shureim bai rageni da komaiba dan nima ban rageshi da komai ba.khadija tayi ajiyar zuciya tace"ai ko baki fada ba Aisha umar kallo 1 za'ayi miki mu2m yasan kina cikin daula,jikinki ya nuna kuma muma shaidu ne don babu abinda bakya yi mana,kici gaba da godewa Allah sai ya kara miki"Ummi tayi ajiyar zuciya tace"shiyasa nazo daukar darasi kibani dama indinga zuwa kullum har tsawon wata guda inji ina ganin abubuwan da kikeyi ni ban iya komai ba.AF tayi dariya tace"zaki iya zuwa kullum amma banda ranar weeEnd don mijina yana gida"Ummi tace to, a wata zan zo sau KWANA ASHIRIN DA HUDU. Saboda naga alamar har yanzu GANGAR JIKINSA NA AURA, zuciyarsa na wurin amaryarsa surayya. gara inkoma kacokan indinga koyi da abinda YARENA ADDININA, yazo mana dasu.duk wanda na tara na fada masa abunda Yasar yakemin sai yace INA RUWAN WANI, dan abaya anyi min shaidar tsiya as sanni da bin bokaye. nakan cewa Yasar KAI KAFI CANCANTA' ka lura da cewar na canza yanzu bana bin bokaye irinna da bai cika kallonaba ma balle yasan nayi kwalliya tsabar yariga dayayi min shaidar kazanta abaya.sai Ummi ta fashe da kuka.Khadija ta tabe baki tace wannan shi ake kirada ADON DAWA'kenan kinyi kwalliya abanza don baya lura"AF tayi murmushi ta dafa kafadar Ummin Yasar ta girgizata tace"kwantar da hankalinki kawata,sannu ahankali zaki gane kan mijinki.Yasar zai zama takalmin takawa tana rufe bakinta sai ga Dr.shureim ya shigo, ya dubesu 1by1 yayi murmushi. yace Farida, hakika ni takalmin kafarki ne, nayi miki lamuni ki takani kije duk inda kikeso dani 'DUK KYAN TAKALMI' a kafa ake takawa......................** *************** *************** *************** *********ALHAMD LILLAHI karshe DUK KYAN TAKALMI 4 Aisha farida tayi karfin hali tace ba damuwa, ai laifina ne dan banyi kama da mai kamun kai ba, tunda ba'a tambaye ni ba nazo na fara yi muku surutu, nasan ba'a son mace marar kamun kai. Barr muazzam ya girgiza kai yace zuwanki nan ba laifi bane dan kin zo kin zauna a kusa damu, kujeru ne a jejjere kowa zai iya zuwa ya zauna. Da kika zo kika same mu kinyi mana sallama duk da tun kafin mu amsa har kin zauna. Daman kamata yayi ki gabatar mana da kanki kuma kinyi hakan sai dai kika zarce da bamu labari shine abinda ya daure mana kai kenan. Kallon junan da kikaga muna yi ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin ko na sanki ne. Aisha bani labarin takamaiman abinda ke damunki, muma nan da kika ganmu matsala ce take addabarmu, ki saki jiki ki fada mana mu dake sai mu taimaki juna da shawarwari. Barr nuruddeen ya fusata ya mike tsaye ya dubi abokinsa yace malam in ka gama kazo ka same ni a cikin mota mu tafi, dan ba zan iya zama ina sauraron wannan shirmen naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji ba, daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau hira da ita kai ma kana baza sirrinka, idan taji matsalar ka me wannan zatayi maka? Itama bata san yadda zatayi da kanta ba balle ta bawa wani shawara. Kada ka sake ka ambaci sunana a cikin labarinku kai dai ka fadi taka matsalar. Ya juya a fusace ya tafi bai daina fada ba yana tafe yana magana yana wurwurga hannu har ya fice daga cikin gate din. Aisha farida da barr muazzam suka bishi da kallo har sai da suka daina hango shi. Ta sunkuyar da kanta kasa sai hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar da komai ba komai ba. Kece fa kika gama bani labarin cewa zaki iya zama da kowanne irin mutum a duniya. Inji brr muazzam. sai tayi murmushi ta shiga goge hawayenta tace ko kusa ban damu ba, banji haushi ba. Kawai dai abokinka yayi min kallon ballagar mace, 'yar tasha, 'yar club, karuwa kenan. Shine mutum na farko a rayuwata daya taba jifata da wadannan munanan sunaye, saboda bai sanni ba, sai dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba da bani labarin rayuwarki, ina jin dadin sauraronki. Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da irinkukannan yaukimani wata takwas kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa mamawa kinsani cikintausayin ki,maganardanakeyi yanzuhaka nakasa tsayarda hawayendake zuba'a idona. kitaimaka kibani lbrin cigabanki da daukakardakikasamu kozansamisukuni yau...wallah nafisa natausayamiki sosai. BABI NA BIYU Da na karasa makarantar primary sai yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen sabongari na zana jarabawar common entrance ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa sai naci jarabawa aka turani makarantar da na zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo, gashi bansan kowa ba a makarantar amma daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na yi suna a makarantar nan da nan malamai ma suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min siyayya ba da biyan kudin makaranta ba kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar, sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani hakuri cewar zai mayar dani makarantar gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na koma makarantar shekara naci gaba da karatu, daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa da yaran hausawan da suka sami horon turanci tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science class) har Allah ya kaini aji shida aka bani shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana kwatance dani saboda kokarina. Da muka gama makarantar ita da malamai sai da sukayi takaicin rashina saboda ba'a sami madadina ba. Bayan gama makarantata da wata uku yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani kudin mota da guzuri na zuwa shagamu, saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da 'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani. Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba. Ina samun wasikun kanwata munauwara akai akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3 anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu, dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan 'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk da rashin wadatar da muke ciki a kano sai naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi, gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye da ashirin, yare kala kala kamar hausawa, yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban. Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin. Saboda tausayin halinda na same ta kusan dukka kayana na sakawa na bata kyauta, sannan na hada mata mayafai, sarkokina, takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk kudaden dana samu na bata dukka kudin mota na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu komai duk na rabar da kyana kuma da masu kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin, yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan haka na daina zuwa taron biki ko gidan kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana suka ga ina arar na abida? Irin wannan gutsiri da tsomar sai da ta wuce kan matan gida ta koma wajen mazansu, su kuma suka tseguntawa yayana hussaini, suka ce masa bai dace in dinga arar kayan abida ina fita kofar gida ina tsayawa da samari ba, ina yawo da kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a duhune sai a zaci abida ta fara bin maza. Sukayi ta zuba masa bayanan da dole hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi mummunan baci. Ya shigo dakina ransa a bace ya iske ni a kwance yace min in kira abida itama ta shigo nan dakin yana da magana da ita. Mukazo muka durkusa a gabansa muna karkarwa saboda yadda muka ga ransa a bace gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya umarci abida ta fada masa gaskiya kada ta kuskura tayi masa karya akan abinda zai tambayeta, haka nima ya gargadeni kafin ya yi mana tambayoyin. Muka yi masa alkawarin zamu fada gaskiya, ba zamuti karya ba. Cike da fargaba mai tsanani muke sauraron abinda zai fada mana. Ya cewa abida da gaske ne aisha farida tana aron kayanki ta saka ta fita yawo a gari? Sai abida ta dafe kirji tace Innalillahi wainna ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da nan ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace eh haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da ta fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta hada kayanta ta tafi gidansu. Na rushe da kuka na dinga rokarsa ya yafe mata ba laifinta bane nice na tambaye ta. Nima din ya yafe min na daina daga yau. Sai ya rufe ni da duka yana duma, yana tattaka ni da kafa tamkar zai kashe ni. Munafukan matan gidan ne suka zo suka kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci sai fada yake yana zaginmu wai sai mun harhada kayanmu mun bar masa gidansa. Ana bashi hakuri tamkar zuga shi akeyi dakyar ya haukra ya kyale mu amma tun daga lokacin baya raga mana, komai mukayi sai ya hantare mu, sai harara koda yaushe. Sai na daina fita koina , koda yaushe ina fama da dinkin yaga da zare da allura. Abida ta iske mijinta a dakinsu ta ajiye masa abinci sannan ta durkusa ta gaishe shi. Ya amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba ta zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje. Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye tace ka yafe mana laifukan da muka maka, munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu, rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada maka bane halin da ake ciki kada ranka ya baci, ashe dana fada maka ma zaifi sauki. Aisha farida ce ta rabar da kayan sakwarta kakaf a shagamu saboda tausaya musu da tayi, ta gansu cikin tsumma, shine ta dawo bata da kaya sai yagaggu. Dan haka bata iya fita wajen kawayenta shine nake bata aron kayana ta saka tana dawowa take cirewa, bansan abinda 'yan gulma suka fada maka ba har ya jawo ranka ya baci ka dauki mataki cikin fushi. Sai yayi shiru yana sauraronta can yace ai duk laifinki ne, meyasa ba zaki fada min halin da ake ciki a cikin gidana ba har sai da wasu suka fada min a waje? Kinsan irin zaman da mukeyi da 'yan gidannan, zaman saka ido ne, duk shige da ficen mu akan idonsu. Ashe gaba daya lungunnan gulmar ku ake yi shiyasa raina ya baci. A take ya bata naira dubu biyu yace ta bani inje in sayo atamfofi guda biyu 'yan naira dari takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu. Abida mace mai hakuri da tsananin wayo, ta iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa, tabbas macen da bata da hakuri da wayo ba zata iya zama dashi ba, sai gashi da kansa yayi nadamar aninda yayi mana, sai yaji kunya yazo yana lallaba mu. DUK KYAN TAKALMI 5 Saurayina guda daya nake kulawa mai suna musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan mu tare, yana sona sosai nima haka saboda yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu auren gida, shi kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a shekara. Musbahi ma yaji labarin duka dana sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi guda daya da atamfa ya hada min da naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada in daina boye masa sirrina saboda yadda yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da addu'a Allah Ya karkato da zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya fito naci credit takwas, geography ne kadai naci pass shima dan a ranar da muka yi jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan ya sami kudi zai saya min form din jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin mota da kudin sayan handout, gashi dole sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk wadannan sabida dan abinda yake samu ba mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da yawa suna samun kudi a business center yake aiki, suna typing a computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to zai samo min management in fara, nan ma nace bana so nafi son inyi schl of nursing saboda ba ruwana da neman kayan sakawa, suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da shawararmu kuma yaji dadi musamman da musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi masa sallama da yayana hussaini ya kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya ta malam aminu kano dake unguwar court road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka karatu na yi tayi haikan, ban taba samun matsala ba cinye jarabawata nake yi koda yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin acabana kit da kit babu canji wata rana ko purewater zan sha sai dai kawayena su saya min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna min bakin hali daga baya kuma in dinga jin kananan maganganu cewar na cika san banza kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi dare duhu, kallon kitse sukeyi wa rogo. Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk wasu manyan littattafai na karatu (text book) babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi sai yace in hakura kada inje makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abkin gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin rayuwata a wannan bangaren saboda bani da wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan amayar musu da radadin da zugin matsalolin da suke addabata. Kawata guda daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu, koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata, ni burina guda daya ne shine in gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron kazata da cinkosa, babban burina ba wuce inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan karami mun cunkushe gashi su dukka yaran abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba katifar sai zarni take dan haka na hakura da katifar na bar musu. Na koma kwana akan tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike talaucina na kama kaina bana sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa lafiya muke wadanda aka kwantar dasu sakamakon wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam tana nunnana mana yadda ake aiki, domin neman karin bayani sai tace bari ta hada mu da kwararren likita wanda ya kware a bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga muma muka bita a baya da alama dakin daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai yake yi musu cikin harshen turanci kai kace baturen america ne, kalmomin kimiyyar (botanical names) da yake ta ambato yana jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa kawai na fara hangowa daga nesa sai na tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban hango jan kunne ba da farin gashi irin na turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye da bakaken kaya riga da wando (suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana matso ciki sai na fara hango gefen fusakarsa, wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a duniya wato hasken duhu (chocolate color). Ko dana sake samun daman na matso kuda dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin wadannan dara daran idanuwan ba masu tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu gashin ido da gashin gira masu yawa da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan da ake kira african American, hukuncin da na yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka hadu suka same shi bakar fata da farar fata. See Translation An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge

Chapter 22 of 23