Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suka faru tsakaninta da dr shuraim da kuma mataki na hudu da abida ta karanto mata. Barr muazzam ya dubi aisha farida cike da rashin fahimta yace to ni kamar ni ta yaya zan yi mata biyayya? Kuma kamar baraka wacce tayi biyayyar a baya bata ci riba ba, sai da ta share shi ta fara samun saukin wulakancin? Aisha farida tace ai a ganina duk daya ne mu ukun. Yanzu kamar baraka taci gaba dayi masa haka har lokacin da zai karkato sosai, yana son zaman nata sai ta dawo tayi masa biyayya sosai, tayi duk abin da yake so, ta bar abinda baya so, ta nan zai fara mantawa da nafisa. Ko kuma zai fara kokonto ko ya rike matarsa ne, ya rabu da waccan don na tabbata ba zatayi masa biyayyar da baraka take yi masa ba. Saboda wadannan dalilan nawa na farko kace babba ce har ta dade da gama jam'ia. Na biyu tasan yana sonta don haka zatayi ta jansa a kasa kasan halin mata. Barr muazzam ya gyada kai yace lallai kanwata na yadda da tunaninki, kamar kina zaune a wajen duk yadda kika fada haka ne. Aisha farida tayi dariya tace kai kuma a bangarenka kaci gaba da nuna mata ka sami wata bata gabanka yanzu. Kada ka bari alakarku ta rabe, ku cigaba da yawan haduwa ko bayan ta dawo gidan a matsayin abokinta zaka ga ta dawo. Kada ka fada mata da wasa kake da wuri, kayi ta kyautata mata, kanayi mata duk lallashi da tarairaya. Kayi ta yin duk abin da kasan tana so, ka kiyaye wanda ba taso tabbas zataji kai kafi dacewa da rayuwarta, ko bata zo tace tana sonka ba, zata nuna alamu. Barr ya gyada kai yayi murmushi yace gaskiya ne wannan kinyi hikima, Allah Ya sa mu dace. Bani lambarki don muci gaba da tattaunawa a waya. Ya zaro wayarsa daga aljihun, aisha farida tana karanto masa lambar yana rubutawa har suka cika. Sannan ya kira lambar ta shiga, amma wayar tana gida. Aisha farida tace idan na shiga ciki zanyi saving. Barr muazzam ya zaro kudi daga aljihu, naira dubu biyu ne 'yan dubu dubu guda biyu, ya mika mata nan fa ake tataburzar, don aisha farida ta tubure ba zata karba ba, shi kumwa yace sai ta karba. Ko zubarwa zatayi sai dai ta zubar. Sai da ta ga ya dage sosai har ransa zai baci sannan ta durkusa ta karba, tayi masa godiya suka yi sallama ya tafi, tashiga gida cike da farin ciki kamar kuwa yasan suna cikin tashin hankalin rashin kudi, asibiti duk ya cinye musu kudin. Cefane ma sai harhade harhade ake yi, a dafa a ci ba dadi don kar a mutu. Ciwon abida kamar da wasa, abu ya fara tsananta hankalin kowa ya fara tashi, don har hussaini yayi waya ya sanarwa da iyayenta da 'yanuwansu na shagamu. Babban likitoci yanzu take gani a asibitin kashi, don ciwon ya wuce kananan likitoci. Magani take dirka amma fa a banza, ko alamun canji bata ji a jikinta. Daga nan sai suka rabu da zuwa asibitin kashin ma, suka dawo gida aka fara na hausa, wannan yace sanyin kashi ne, waccan tace mayu ne. Kowanne magani hussaini yaji sai ya karbo ya kawo, burinsa matarsa ta sami lafiya. Abinka da mai ilimi aisha farida bata son wannan gwafje gwafejen magungunan gargajiyar ko hussaini ya kawo ya bata, sai ta boye bata bari tasha. Gara ma na shafawa a gabobi tana shafa mata kamar na sanyin kashi da aka karbo musu a wajen sarkin ruwa na wudil. Maganin sanyi kashi ne da man shanu ake kwabawa a shafa a gababin. Sai man tafarnuwa dashi ma akace ta dinga shafa mata a gabobi shima tana shafa mata kullum da daddare kafin su kwanta. DUK KYAN TAKALMI 2* 11 Babu abinda abida ke iya yi, sai anyi mata tana kwance kawai. Amma tana magana radau kuma idan an bata abinci tana ci sosai. Sai tsananin sanyin da take ji, sai tayi ta makerketa duk da bargunan da aka lufga mata, kuma a lokacin zafi ne. Ba asiha farida da hussaini da 'ya'yan abida ba kadai, duk wani mahalukin da yake da dison imani a cuciyarsa hankalinsa sai ya tashi idan yaga ciwon nan kuma ya tausaya mata. 'Yan dubiya basa karewa layi layi mata suna shiga, wasu na fitowa. Sai yanzu 'yan gida da 'yan unguwa suke zayyano kyawawan halayen abida. Idan akace yau asabar da lahadi ce lokacin yaya hussaini yana gida baije aiki ba, to mazan unguwa da abokan aikinsa sai suyi ta tururuwar zuwa dubiya. Kuma yawanci basa zuwa hannunsu haka , suna riko kayan dubiya kamar ayaba da lemo, ko kayan shayi, wasu kuma sai su ba da dan kudi suce a sayi magani. Aisha farida ta labe tayi kuka har ta gaji, addua take Allah Ya tashi kafadun abida uwarta, ubanta, yayarta kuma kawarta, sannan aminiyarta mai bata shawara. Aisha farida ta tari yaya hussaini a bakin kofar dakinsa ya shirya ya fito zaije aiki. Bayan ta gaishe shi ta shawarce shi tana son ta kai abida asibitin malam aminu kano a duba to ko Allah zai sa a dace. Hussaini yayi shiru can yace kina ganin aje asibitin nan alhali na tabbatar ba ciwon asibiti bane, tunda ga kasusuwan sun kumvura suna ciwo, amma likitocin kashi sunce basu ga komai ba. Aisha farida tace ina ga ai ba bangarensy bane, wata kila ciwon ba a jikin kashi yake ba, gara in kai ta tunda can akwai likitoci manya manya zasu gano ciown. Hussaini yace kinga abin da yasa nace bana asibiti bane, idan tana bacci sai tayi ta zabura har sai na rirrike ta cikin dare. Aisha farida tace haka ne yaya, ai asibitin ma suna da maganin razana da zabura. Ya lalubo kudi ya bata yace suje, Allah Ya sa adace. Aisha farida ta harhada 'yan kudaaden da take adanwa na masu dubiya, misbahi ma dubu daya ya bata, haka wani yayansu da yazo daga shagamu shima dubu daya ya bata, taje ta hado cefanen dambu ta shirya wa rabin ranta dr shuraim. Bayan ta yi wanka ta fesa kwalliya da wata doguwar rigarta bakai mai dankwali (abaya). Sai ta shirya abida aka kirawo musu mai adaidaita sahu yazo har kofar gida. Sai da matan gidan suka taimaka mata aka rirriko abida aka saka ta ciki domin duk gabar da aka rike mata ciwo takeyi mata. Sai ta dau kuka kamar wacce ake balla mata kashinta don azaba. Aisha farida rike da kwandon abincinta ta shiga adaidaita sahi suka tafi. Ta dubi abida ta zubo da hawaye don tausayi tace wannan dambun ne nayi wa su dr shuraim in kai musu ko in kyale su? Abida tayi murmushin karfin hali ta cije baki saboda tsananin ciwo ta gyada kai tace ki kai masa. Mai adaidaita sahu ya kai su har bakin GOPD kafin su sauka, sai aisha farida ta shiga ciki da sauri tayi magana da maikatan suka bata kujerar tura marar lafiya. Lebura daya ta dauko kujerar ta biyo ta da ita. Nan ma sai da aka agazawa aisha farida sannan aka dora abida akan kujerar saboda tsabar ragargazar da kashinta ke yi har kara zaka ji yana yi bas! Bas! Idan ta motsa. Aka turata aka shiga dasu wajen bude file kasancewar duk ta sanu ba ta bi dandazon layi ba aka bude musu, nan da nan aka mika musu file din dakin likita. Nan ne fa za asha jira sabida likitoci basu karaso ba, don haka dole a sha jira akan bencina. Aisha farida ta dubi abida wacce har yanzu take kan wheel chair tace inje ofishin dr lukman in dawo, zaki iya zama ke kadai? Abida tayi murmushi tace kije a tsanake ki gama abinda kike yi, kada ki damu don kin barni, ni kadai zan zauna a cikin kabarina. Ni kadai zan zauna babu mai tayani zama, saini sai halina. Sai aisha farida ta runtse ido yayin da kuka ya kcece mata, ta kasa magana saboda jama'ar dake kallonsu. Cikin sanyin jiki ta dauki kwandon abincin ta tagi. Hawaye yake ya tsaya har ta kusa isa ofishin dr lukman don haka ta sami lungu ta labe tayi kuka har ya isheta, ta goge hawayen ta fito. Amma kuwa kallo daya zakayi mata kasan kuka ta sha, don idanuwan sunyi luhu luhu. A sanyaye take tafiya cikin nutsuwa ta kwankwasa kofar ofishin dr lukman ta shiga. Bata iske shi ba, sai wasu daliban likitocu guda biyu ta samu suna zazzaune suna jiransa. Bayan sun gaisa sai ta tura kwandon abincin a lungun da saba ajiyewa, sannan ta tambaye su inda ya tafi. Suka tabbatar mata yace su jira shi yanzu zai dawo, ba zai dade ba. Sai ta sami kujera ta zauna tana zama sai taji an bude kofa, yayin da gaba daya hankalinsu ya tafi wajen kofa. Dr lukman ne a gaba, dr shuraim ba biye dashi. Kowannensu da laptop dinsa a rataye a kafadarsa. Idanuwan dr shuraim akan aisha farida ya fara dira, yayin da ya jima yana kallonta sannan ya dauke idonsa. Ita kuma murmushi kawai takeyi tana mai sunkuyar da kai tana jin kunya. Dr lukman ya dube ta yayi dariya yace 'yar shagamu daga ina kika diro? Na dauka ai da aka gama karatu sai kika hada 'yan komatsanki kika koma shagamu. Tayi dariya tace ina nan yyayana, kai ka share ni ai ba ka nemana gashi kuwa na taso takanas na zo in gaishe ku. Dr lukman yayi dariya yace kin kyauta 'yar shagamu, ni daman nasan kinfi ni kirki, to bari inje in sallami daliban dana zaunar tun dazu suna jirana. Ya juya ya dube su yace to ku taso muje lab din in nuna muku. Suka bi shi a baya suka fice, sai ita sai gogan nata dr shuraim kadai aka bari a ofishin. Yana zaune akan kujera ya bude laptop dinsa yana dube dube. Ta dubi zankadediyar fuskarsa sai taji zuciyarta ta hau dukan uku uku saboda tsananin kyawun dataga ya kara yi. Ta fara tambayar kanta da kanta “anya kuwa mutumin nan bai fi karfina ba? Anya kuwa zan kai labari a tafiyar nan? Anya kuwa hakata zata cimma ruwa”? Sai bayanan abida ya fado mata cewar babu abinda ya gagari Ubangiji, samun dr shuraim ba wani abin wahala bane idan har ta rike matakan nan guda biyar. Ta silmiyo daga kan kujera ta gaishe shi cikin wata kintsatsiyar murya bata mike daga durkuson ba har sai da ya amsa mata, sannan ta koma ta zauna. Tayi shiru kanta a sunkuye a kasa, sai dai su biyu suna hada ido in dai ta dago zata kalle shi, sai taga shima ya dago ido ya dube ta. Sunyi mintuna biyar cur babu wanda ya sake magana a cikinsu. Sai taji muryarsa kamar a mafarki ya ambaci sunanta. Yace aisha farida, 'yar shagamu, 'yar acaba. Wanne ne sunanki a cikin su. Sai ta dago ta dube shi tayi masa lallausan murmushi ta sunkuyar da kai ta sosa goshi alamar kunya. Tace sunana aisha farida umar shagamu. Yayi wani dan siririn murmushi yace kin amsa sunayen uku daya kika cire, mai yasa? Ta girgiza kai tace ai na daina hawan acaba yanzu. Yayi murmushi yaci gaba da daddanna laptop dinsa. Yace kinsan sunan wa kike dashi? Sunan mamana ne aisha, haka farida sunan kanwata ce wacce take bina. Ya akayi kike amfani da sunaye biyu? Aisha farida tayi murmushi tace mai suna aisha ai farida ce duk daya ne. Yace okay kenan ummata da farida sunansu daya ni ban ma taba ji ba. Aisha farida tayi murmushi tace haka ne, ai ba kowa ne ya sani ba. Ya dube ta da wutisyar ido yace baki da lafiya ne? Ta dago ido da sauri ta dube shi cike da mamaki ta girgiza kai tace lafiyata kalau. Ya girgiza kai yace shikenan, naga kinyi kama da marar lafiya ne, ko kuka kikayi ne? Wannan tambayar tasa ta sake bata matukar mamaki, sai taji kamar a mafarki. Tayi shiru har zuwa dan lokaci sannan tace eh. Ya dago ido da sauri ya dube ta sai ya cika da mamaki yayin da ya maimaita amsar da ta bashi eh??! Yaci gaba da duban laptop dinsa ya ma rasa tambayar da zaiyi mata. Ta sharbe hawaye tace yayata ce bata da lafiya sosai, har bata iya tafiya ita na kawo asibiti. Yayi shiru na wani dan lokaci sannan ya nisa ya ce me yake damunta? Aisha farida ta zubo da hawaye mai dumbin yawa tace an kasa gano ciwon. Dr shuraim ya girgiza kai yace a'a bakuje inda za'a gano muku ciwon ba dai, har akwai ciwon da ba a ganewa, ko wanda bashi da magani? Aisha farida ta matse hawaye da hannunta ta dagi da jajayen idanuwanta ta dube shi, ta girgiza kai. Tace asibitin kashi na dala muka yi ta zuwa suna bata magani, amma bata jin sauki. Sai ma gaba yake. Shine yau na kawo tana, tana GOPD a layi, likitocin ne basu karaso ba. Ya tambaya cike da kulawa yaya take jin ciwon? Aisha farida ta kwatanta masa duk yadda ciwon ya fara har izuwa yanzu. Sai yayi shiru can yace ciwon yayarki rheumathoi athritis ne ko systemic lypus erythramatosis. Aisha farida ta kalle shi cike da rashin fahimta tace na'am? Ya girgiza kai yace kada ki damu likitocin da zasu duba ta yanzu zasu hada da likitan da ya dace. Allah Ya bata lafiya. Aisha farida tace amin nagode. Sai ta mike a nutse ta duka tace zan tafi saboda kada likitocin suzo a kira mu bata iya tafiya, nice zan shiga da ita. Ya gyada kai yace okay, Allah Ya ba da sauki. Ta fice cike da farin ciki, tana fita ta dafe kirji tana ambaton Allah na gode ma Ka, Allah Ka sake cika min burina akan shuraim. Tana tafe tana fara'a tamkar an biya mata kujerar makka. Sauri take ta karsa wajen abida ta bata labari, amma da ta tuna abida babu lafiya sai jikinta yayi sanyi musamman data je ta iske abida ta galabaita a inda take zaune, ta gaji da zaman duk jikinta ciwo yaje. Hawaye kawai ke fitowa daga idanuwanta. Ita kadai tasan me takeji, sai dai duk wanda ya dube ta yasan tana jin jiki saboda gaba daya gabobinta a kumbure suke. Aisha farida ta rike ta, ta gyara mata zamanta tana mai lallashinta tayi hakuri likita yazo. Suna zaune shiru aisha farida na ta sake maimaito hirar da suka yi da rabin ranta, sai tayi murmushin jin dadi ta waiwayo da sauri ta dubi abida tana shirin ta bata labarin dr shuraim sai taga mawuyacin halin data ke ciki, sai taji hawaye ya cika mata ido. BABI NA GOMA SHA DAYA Aisha farida tayi kuka, har ta godewa Allah a wannan rana ta asabar saboda jikin abida ya matsa, babban yayanta yaya lurwanu yazo da mota har kofar gida, yace a bashi ita ya tafi da ita shagamu ayi maganin hausa. Yaya hussaini ya zama bashi da zabi kasancewar shima yana ganin ciown bai yi masa kama da na asibiti ba, don sunyi ta yin na asibitin babu alamar jin sauuki, kullum ciow kamar kara shi ake yi. Aisha farida ta dage wajen yi musu bayani, sunki su fahimce ta, suna ganin don ita 'yar boko ce kuma malamar asibiti shiyasa take son a dauwama da na asibiti don likitoci ba sa kaunar a hada maganinsu dana gida. Sunfi karfinta, tana ji tana gani yaya hussaini da yaya lurwanu suka ciccibi abida tamkar 'yar jaririya da kayanta aka saka ta a mota. Yaya lurwanu ke tukawa, yaya hussaini yana zaune a gefensa, yayin da ita kuma aka kwantar da ita a bayan mota. Aisha farida ta mika hannu ta tagar motar ta rike kumburarrun yatsun abida a hankali yayin da hawaye ya surnano daga idanuwansu su duka. Aisha farida tace Allah Ya baki lafiya. Abida ta girgiza kai tace ba zan dawo ba farida, ki kula da 'ya'ya na, kada ki manta abu uku dana fada miki. Ki zama mai yawan addua, mai tsananin hakuri mai yawan kama mutuncinki. Biyun kuwa ba yanzu zan fada miki ba sai nan gaba idan ban mutu ba. Yaya hussaini ya juyo da sauri yana kallonsu ba tare da ya fahimci abin da suke ba, shi da lurwan suka cika da mamakin jin kalaman da marar lafiya ta ke furtawa. Hussaini ya tambayi aisha farida meye hakan kuma yake nufi? Zance me kuke yi? Aisha farida ta goge hawaye tace a'a sako take bani. Yace sakon me kuma naji ana maganar soyayya? Ki koma gida ki kula da yara, gasu can suna ta kuka, nima gobe zandawo na bar miki dari biyar a daki akan katifa. Idan anyi wa yara hutun makaranta sai mu dunguma mu tafi shagamu, ni ina jin ma gara ku kaura can kacokan, ni zan dinga zuwa ina dawowa, gara mu hakura da zaman kanon ma. Kirjin aisha farida ya buga bamm! Don fargabar tana tunanin yaDda zata rabu da rabin ranta dr shuraim. Ta zame hannunta a hankali daga hannun abida, sai abida ta dago ido ta dube ta, tayi mata murmushi. Tace Allah Ya baki nasara akan abin da kike nema. Kuka yaci karfin aisha farida, ta rushe da kuka. Tace Allah ya tashi kafadunki anti abida. Nan da nan yaya lurwanu yaja mota ya tafi, saboda suma sun fara jin hawaye yana zubo musu don tausayi. Idanuwan yaya hussaini ya cika fal da kwallah. Aisha farida ta kame a inda take tsaye tana kallon motar har sai da suka kure sannan ta juyo gida. A hanya jama'ar unguwa sai sannu suke yi mata, da kuma fatan Allah Ya ba wa abida lafiya. Kowa ya tausaya wa aisha farida ganin kukan da take sharba, idanuwanta sunyi jajawur. Ita kanta tana so kukan ya tsaya, amma yaki saboda tsananin kunar da take ji a ranta. Ta kama hannun 'ya'yan abida su hudun dukka maza, faruk, sa'ad, muhd, da ishak idan taja hannun wannan sai wannan ya arce da kuka. Da kyar matan gida suka taya ta da kamo su ana lallashi da alewa da biskit. Da kyar suka zazzauna a daki suka daina kukan. Aisha farida ma tazo ta zauna a gabansu tana kallonsu, ba tare da ta iya musu magana ba. Abin duniya ya ishe ta, ta rasa abin da yake yi mata dadi. Ji take tamkar zuciyarta zata fashe. Tana ambaton Allah kar ka kashe abida, ina son abida a rayuwata. Wayarta ce tayi kara, ta mika hannu a sanyaye ta dauka, ta duba wata lamba ce bakuwa babu suna, sai dai lambar ta musamman ce, saboda kusan lambobin duk iri daya ne. Tayi ta kallon lambar amma batayi mamakin wanda ke kira ba, domin 'yan ajinsu da dama suna karbar lambarta su kira ta maza da mata. Saboda bata cikin hayyacinta , don haka bata son yin magana har wayar ta katse ba ta amsa ba. Can ta mike ta fito tsakar gida ta jawo risho ta dora ruwan zafi a karamar tukunya, ba tare da ta san abin da zata dafa ba. Ta dubi babban dan abida faruk tayi murmushin karfin hali tace yaya me zamu dafa yau? Maganar ma shi ma dakyar yake yi, sai ya langwabar da kai yace wake da shinkafa. Ta dubi sa'ad mai binsa tace kai fa dan lelena mai zan dafa muku? Shima yace wake da shinkafa. Sai ishak yace shinkafa da miya. Mohd yace a'a tuwon shinkafa da miyar taushe. Aisha farida tayi dariya tace a'a su yaya sun fiku gaskiya, ku rage min aiki tunda muna da yaji mai dadi da daddare sai inyi mana tuwo. Tana zaune a dokin kofa tana tsice wake sai wayarta ta dau ruri. Nan da nan yara suka hau tseren dauko waya, ana dambe dai kamar za a yar da wayarta samu ta karba. Taba dubawa taga lambar dazu ce, sai ta tabbatar ko waye wannan mai kiran wayar tana da muhimmanci tunda ya sake kira, don haka nan da nan ta danna. Cikin nutsuwa tayi sallama, taci gaba da sauraron mai wayar, mace ko namiji? Muryar namiji taji ya amsa da wa alaikumul salam. Tayi kasake tana sauraon abinda zai fada mata, har yanzu bata gane muryar ba. Amma daga dukkan alamu ta taba jin kamilalliyar muryar. Ya tambaya don Allah ina magana da aisha umar ne? Ta amsa da eh aisha ce. Yayi gyaran murya kadan yayi murmushi yace farida kina magana da dr shuraim imarn ne, daga nan asibitin aminu kano. Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai. Kalmar da aisha farida ta fada kenan a cikin zuciyarta, yayin da ta sulale ta durkusa gwiwoyi guda biyu a kasa don mamaki da kidimewa. Ta rasa kalma daya da zata furta, sai gumi take jikinta yana bari, ta rasa inda take. Shin mafarki ne, ko kuma idonta biyu? Ya ambaci sunata har sau biyu. Farida! Farida!! Tayi doguwar ajiyar zuciya, ta lumshe ido ta amsa cike da ladabi, cikin sassanyar murya na'am. Yace kina mamaki ne? Kada kiyi mamaki. Na sami lambarki ne daga wajen dr lukman jiya aiki ya hana in kira ki, sai yau da yake weekend ne, ina gida. Ta mike ta shige dakin abida ta turo kofa ta datse saboda hayaniyar yara, ta sami lungu ta shige ta takure kai kace sanyi take ji. Ta gaishe shi cikin nutsuwa. Ya amsa cike da fara'a ya tambayeta ya mai jiki? Cikin sanyi jika tace da sauki. Yace yaya maganin da take sha, tana samun sauki? Tayi jim kadan tace tana sha dai, amma ciwon kamar gaba yake tayi. Yace subhanallah, to yanzu abinda za a yi, ranar litinin ki kawo ta wajen zan hada ta da likitan da ya kamata ta gani, wato rheumatologists. Ba damuwa idan nayi masa magana zai duba ta ko babu appointment. Hawaye ya surnano daga idanuwan farida, ta marairaice murya tace ai bata nan, anzo daga gida an dauke ta, wai na hausa zaayi. Babu yadda banyi ba su kyale ta muci gaba dana asibiti suka ki....... Bata rufe bakinta ba sai ta rushe da kuka cikin wata irin sautin murya mai ban tausayi. Dr shuraim ya zabura yace subhanallahi, wannan suna so su jawo mata ciwon koda, daman ciwon yana da alaka da ciwon koda. Kada su sake su bata sassake sassake ta sha, don akwai mummunan hatsari wajen shan jike jike. Kuka kawai farida ta keyi, ba tare da ta iya magana ba. Yayi ajiyar zuciya ya ambaci sunata cikin wata lallausar murya. Yace farida kuka kike yi? Daman ke haka kike sarkin kuka ce? Na hadu dake fiye da sau hudu kullum kina kuka, meya damuwarki? Ta girgiza kai ta goge hawaye tace babu abinda ban fada musu ba, babu irin maganar da banyi ba akan su kyale ta, suka ki. Mijinta ma tun ba ya yadda yanzu har ya yadda. Yanzu ko nay waya shagamu nayi bayani kada su bata maganin hausa ba zasu saurare ni ba. Shine nake jin tsoro kada su jawo mata ciwon koda.... Ta sake barke wa da wani kukan DUK KYAN TAKALMI 2* 12 Ya sake jan doguwar ajiyar zuciya yace kada ki damu, mu dukka muslmaii ne, mun yadda da Allah Shi ne mai warkarwa, ba magani ba. Muyi addua Allah Ya bata lafiya, Allah Ya tsare duk wani tsautsayi. Ya ya kike da ita marar lafiyar ne, mamarki ce? Aisha farida ta marairaice murya tace anti abida yayata ce, kakanninmu daya, kuma tana auren yayana da muke uba daya, itace marikiyata tun ina karama, itace tamkar uwata, ubana, yayata, kuma aminiyata mai bani shawara akan duk lamurana. Sai yayi murmushi ya lumshe ido yace amma kin iya kwatance yadda mutum zai gamsu. Ko kon taba bata labarin wani dr lukman da abokinsa dr shuraim da suke cinye miki dambu da danwake? Aisha farida ta kwashe da dariya tace a'a baka bani izinin na sanar mata ba. Yayi dariya yace nasan kin fada mata. Ta sake tuntsirewa da dariya tace sai dai yanzu na fada mata. Yayi dariya yace to Allah Ya sauwake Ya bata lafiya sai anjima. Aisha farida tace nagde Allah ya saka maka da alkhairin, sai anjima. Ya kashe wayar yana lumshe ido saboda jin dadin muryarta. Har yanzu aisha farida sankare take a lungu ta kasa sauke wayar daga jikin kunnenta. Ji take tamkar mafarki take yi, yayinda farinciki marar misaltuwa suka cika zuciyarta, ta cika da mamaki marar adadi, sai ta tuna da bayanan ABida da tace babu abin da ya gagari Ubangiji. Idan bawa ya roke Shi, yana amsa ma sa duk sanda Ya so. Ta ajiye hannunta a hankali daga jikin kunnenta ta dafe kirji taji sassanyayiyar bugun da zuciyarta take yi. Ta daga hannu sama tayi wa Allah godiya sai ta malale ta kwanta akan katofa tamkar ruwa. Ta jawo wayar da sauri ta duba lambar, ta kayatu ita kanta lambar abar kallo ce, sai ta sumbaci wayar. Ta dannan lambar ta kira, bugu daya ta shiga ta fara ruri, sai taga an kashe. Hankalinta yayi mummunan tashi, nan danan ta zabura ta tashi zaune ta dafe kirji, yayin da farin ciki datake yi ya koma ciki. Ta fada a bayyane innalillahi wainna ilaihir rajiun! Me ya kaini sake kiransa, gashi ya katse? Shikenan zai tsane ni. Ta na zaune ta hada kai da gwiwa tana tunani sai taji wayarta tayi ruri. Nan da nan ta zabura ta dauka ta duba, sai taga lambar dr shiraim ce, tay sauri ta dannan gami da yin sallama cikin nutsuwa. Ya amsa mata gami da cewa naga kin kira ko? Ta lumshe ido tace eh daman zan tambaye ka ne, ranar litinnin dambun zan kowa muku ko danwake? Ya girgiza kai tamkar yana gabanta yayi murmushi yace a'a babu, ba sai kin kawo mana komai ba, mungode. Ta marairaice tace haba doctor meyasa, ni ina so na kawo muku. Yace a'a ki bari sai wani lokaci, idan muna bukata zamu fada muki. Yanzu na kira ne naji halin da marar lafiya ke ciki, don na damu nasan ciwon nan yana da tsananin zafi, sannan na damu da yadda naga kinta ta koke koke na kora najji halin da kuke ciki. Tayi murmushi tace nagoda ka kyauta, nayi farin ciki da jin kiranka. Ko zan iya saving din lambarka don mu dinga gaiswa. Yace ba damuwa, zaki iya. Tayi godiya, shima yayi mata godiya, suka kashe waayar. Tayi tsalle akan katifa ta dire don murna. Ta dubi gabas da yamma, kasa da sama tana tunanin wanda zata ba wa wannan kyakyawan labari. Ta tuno abida, taji yau dama abida na nan ta fada mata yadda sukayi da dr shuraim. Taji hawaye ya cika mata ido, ta fada a bayyane. Allah sarki anti abida, Allah ya baki lafiya. Tana rufe bakinta faruk ya shigo dakin da gudu ya ce anty aisha ruwan da kika dora a wuta yana ta tafasa tun dazu, har ya kusa ya kone. Ta zabura da gudu ta fito don ita har ta manta da shi, tabbas yaro yayi gaskiya , ruwa dai ya gaji da tafasa har ya kusa konewa. Sai da ta kara wani yayi zafi sannan ta zuba wake da shinkafa suka dahu. Ta ba wa yara suka ci, yayin da farin ciki ya kosar da ita, ta kasa ci, yunwar ma bata ji. Bayan tayi sallahr azahar sai ta dinga jero nafilfili ba adadi, duk ta godiya ce ga Allah da ya kawo mata dr shuraim. A cikin satin nan haka take yini cike da farin ciki, saboda ta sami dr shuraim, sai dai matsala daya ce take

Chapter 14 of 23