Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta sun bata musu aiki. Yaya hussaini ya wuce ba dadi, nima na fita. Sanda nagama zan fita aka ce min kunja mota kun tafi. Tambayarka ta farko kuma wanda nake waya dashi wani ne sunansa barr muazzam , bansan kai kira ba da na bashi hakuri na katse wayarsa na amsa taka. Amma kayi hakuri. Sai ya tashi zaune daga kwanciyar da yakeyi yace waye barr muazzam? Na fahimci dalilin da yasa yanzu bana gabanki, kinyi min kishiya, laifin me nayi bansani ba? A ina na kuskure in gyara? Taji tausayinsa ya kamata sannan tambayar ta daga mata hankali. Tayi ajiyar zuciya tace Allah sarki my love , sai naji kamar zanyi maka kuka da ka jera min wadannan tambayoyin. Nagode ma Allah da Ya sa duk abubuwan da ka tambaya bai zamo gaskiya ba. Yaya shuraim kai kadai ne a raina, ko a gaban idonka, ko a bayan idonka kai nake so. Baka taba yi min laifi ba balle naji haushi na canza ka. Haka baka kuskure ba, balle nayi tunanin wani. Barr muazzam wani bawan Allah ne da Allah Ya hada ni dashi a kano, ya taimake ni a lokacin da na shiga ukuba, sai muke gaisawa. Ya kawo min alewar bikinsa da dr janan bai same ni ba, shine yake shaida min a waya. Dr janan sunusi? Shuraim ya tambaya cike da mamaki. Aisha farida tace kwarai kuwa itace, dan ya taba bani tarihin rayuwarsa da ita. Wacce kwanakin baya ta shiga matsala har aka tsare ta ko? Dr shuraim yace tabbas ta dade ana shariar nan wacce aka ce ta nemo izzudden taki nunawa. Nasan janan, kawata ce ai. Kwarai Kwanaki tayi min waya ta fada min zatayi aure, ashe kin sansu? Aisha farida tace ban taba ganinta ba, sai dai mijin da zata aura. Dr shuraim yace shikenan ba matsala. Ki bani labari mai dadi mana wanda zai sani inyi bacci mai dadi tunda lukman yayi mun bakin ciki yau bazan ganki ba. Yace ya gaji anjima ba zai rakoni in ganki ba. Aisha farida tayi dariya tace zanso nima ka kwanta ka huta don kun sha hanya. Sai na biyu ina so in mika doguwar godiyata a gare ka bisa dawainiyar da kake yi mana da jinin jikinka da kuma dukiyarka, Allah Ya saka da alkhairi. Sai labarin da yafi kowanne dadi, yau farida ta zama ta shuraim, shima ya zama nata. Sai ya kyalkyale da dariya yace bani labarin me ya faru? Haka dai suka cigaba da hirarraki masu dadi cike da so da kauna har tsawon awa guda. Abida na kwance ta kafawa farida ido sai murmushi takeyi, tana murna a zuciyarta tamkar ta mike tayi rawa don babu hali ne. Tana adduar Allah Ya tabbatar da alheri a yi auren nan ko bayan ranta. ASUBA TA GARI AISHA FARIDA!!! BABI NA GOMA SHA TARA! Abu kamar wasa karamar magana ta zama babba. Auren farida da shuraim sai kankama yake sake yi. 'Yan lungu yanzu sun gasgata, don da jita jita akeyi ko kuma ana ganin abin ba mai yiuwawa bane, wahalar da kanta kawai zatayi, yaudararta zaiyi ya tafi don ba ajinta bane. Sai gashi idan da a sati sau daya ake ganinsa , yanzu a sati a kalla yazo sau biyar. Ba sai an fada ba, rayuwa da tukunyar su aisha farida ta canja gaba daya, sun fara bankwana da talauci, dr shuraim ya tsaya musu. Tun ba a yi auren ba ma har ta kidime ta canza salo da yanayi, kai kace ba wannan faridar bace ta da. A yanzu farida ta zama gangariyar 'yar gayu. Komai nata mai tsada ne (high class) , kama daga suturunta, takalmanta, da jakunkuna, mayukan shafawarta da kayan kwalliyarta. Sai ta canja tafiya, ta canja magana ta kuma canja tsarin rayuwarta. Bata wulakanta 'yan lungu amma bata cika shiga cikinsu a yita wasannin banza ba da surutai barkatai. Zama da dr shuraim ta koya nutsuwa ga jan aji , magana ma sai an daidaita baki. Haka ba a cika dogayen jimla da hausa ba sai an tottoshe da turanci. 'Yan lungu sunyi gulmar, sunyi zumden, sunyi yaficen, abin ya wuce tunaninsu. Sai cigaba suke gani kala kala musamman da suka ga ta fara aiki ya daukar mata mai adaidaita sahu ya kaita ya dawo da ita. DUK KYAN TAKALMI 3* 10 Abida na tsakar gida tana kallon bakinsu bata ce musu komai ba suka gaji, har takai ta kawo ma sun zo sun same ta don suji wani labari game da wannan aure na farida, sai ta nuna musu ba lallai sai dr shuraim ba, duk wanda yafi alkhairi a farida shi zata aura. Basu ankara ba sai suka ji tashinsu, sai ana gobe zasu koma sabon gidansu suka fada musu. Mamaki ya rufe jama'a, 'yan rakiya mata lodi lodi suka bisu don su ganewa idanuwansu. Gida mai kyan gaske babu abinda ba'a zuba ba, tun daga gadaje a dakuna uku da kujeru a falo duk shuraim ya siya, gida gini bulo da bulo sama da kasa duk tiles. Rayuwa sabuwa ta tabbata a gidan hussaini, farida bata rasa kudi. Dr shuraim yana bata, ta dauki albashinta kuma. Babur ta fara siyawa yayanta, kuma ta canja wa 'ya'yanta makaranta ta kudi anan court rd, mai adaidaita ya kaisu ya dauko su. Sun koma sabon gida ba dadewa aka saka ranar kawo kayan sa rana da na lefe gaba daya. Kudin mota baiyiwa su aisha farida wuya ba, suka turawa magabatansu a shagamu, mata bakwai maza uku suka shigo mata suka zo kano don karbar kaya. Abida bata mance da kawayenta na tsohon gidansu ba, fiye da bus uku suka ciko suka zo don su ganewa idanuwansu. Tunda kan 'yan uwan shuraim kallo ya fara kafin a bude kayan lefe. Masha Allah! Tabarakallah! Kaya sun yi kyau. Akwatuna shida da kit biyu. Da saitin sarkokin gwal da awarwaraye hudu manya. Wata uku kacal aka saka ranar bikin, kowa yana sam barka tsakanin dangin amarya da dangin ango, har aka watse. An sha dauki ba dadi a bangaren dr shuraim kan maganar aurensa, 'yan uwansa mata da yawa basu son auren, kasancewar sun iske dangin amarya basu da hali. Cece kuce kala kala sukayi tayi amma shuraim bai damu ba , tunda mahaifansa sun yadda, sunyi masa fatan alkhairi , don haka suje suce duk abin da zasu ce. Da farko dai mahaifiyarsa taki yadda, amma da yake tana jin maganar mijinta, kuma kaifi daya ne, duk abin da ya fada ya zauna a gidansa dole a bi. Amma a sanda guguwar rigimar ta buso daga bangaren matar shuraim wato faiza sai ta kore ta danginsa saboda tafi karfi. A sanda shuraim ya shaida mata a waya cewar zai kara aure aure cikin lallabawa da tattausan kalamai, sai ta hasala tayi ta zage zage har da koke koke wai bata yadda ba. Ya shaida mata aikin gama ya gama, saura wata uku, kuma ba zai fasa ba. Haka aka tashi dai baram baram a wayar, shi ba dadi, ita ma ba dadi. Bayan sati guda da wayarsu sai gata a Nigeria ita da mahaifiyarta. Ba sulhu ne ya kawo su ba, rigima ce tsantsarta. Mahaifiyarta tace sai dai ya saki 'yarta , dama can ita ba son auren take yi ba. Tunda yace zaman nigeria zaiyi tasan zai cuce su. Ta gangaro kan mahaifansa tace dama sun tsani 'yarta faiza, sune suke hadasu fada. Da kyar rigiman nan ta lafa, su dai mahaifan shuraim ba su rama ba, amma 'ya'yansu sun rama musu, akayi ta cece kuce. Shuraim ne yayi ta bada hakuri har aka samu hayaniyar ta sauka, zuciyar kowa ta dan lafa aka zauna taro a babban falon mahaifinsa aka fara bayanai da yadda za'a gano bakin zaren. Kiri kiri matar shuraim ta fada wa mahaifiyarta tana son mijinta, ba zata iya rabuwa dashi ba. Mahaifin shuraim yace to ki kwaso kayanki kizo ki zauna da mijinki da 'yarku a gabanku. Karatun fa? Inji mahaifiyarta ta fada a fusace tana harararta. Tace saura 'yan watanni na gama, zanje na gama na dawo na zauna. Ta sha adduoin albarka a wajen mahaifin shuraim da shuraim din kansa, gami da danginsa. Yayin da ta sacewa mahaifiyarta gwiwa don ba haka taso ba. Ta fusata tace to ko sau daya kada kizo kice an miki wulakanci, kije can ki karata. A daddafe ta bari sukayi kwana uku sannan suka koma london. Kafin su tafi kullum kuka faiza take yi wa shuraim tana cewa baya sonta yanzu tunda zai auri wata. Ya iya dadadan kalamai masu kwantar da hankali, gami da bayanai masu ma'ana ya hada da yi mata alkawari zaiyi musu adalci a tsakanin su. Sai taji sanyi a ranta, ta kuma yadda da duk abinda yake fada mata. Rabuwar lafiya yayi da matarsa, uwar ce dai ko sallamarsa bata amsa ba a airport. Hankalinsa ya kwanta a wannan bangaren kuma bashi da sauran rigima. Duk dauki ba dadin da suka yi aisha farida bata sani ba, bai bari ta sani ba. A bangaren ta matsala kadan ta samu daga musbahu, a inda ya tayar da hankalinsa, ba ci ba sha da yaji abar kaunarsa zatayi aure ta barshi. Ya hada kayansa zai bar garin, zai shiga yawon duniya a rasa shi har abada. Tunda ya rasa farida, to shima mahaifiyarsa da matarsa sai sun rasa shi. Hankalin 'yan gidansu da mahaifiyar sa ya tashi, mahaifiyarsa da kanta tayiwa aisha farida waya ta shaida mata halin da musbahu yake ciki kuma suka roke ta tazo ta bashi baki ko zaiji. Sai kawai ta fashe da kuka ta kashe wayar. Abida tazo ta iske ta tana kuka ta tambaye ta suka zauna suka yi shawara. Ta bata shawara ko bata je wajensa ba, ta saka kati a waya ta kira ta bashi hakuri akan yayi tawakkali , ya daure ya karbi kaddararsa , zai yiwu shi ba alkhairi bane a gareta, itama haka. Ya zauna kada yace zai gudu, baisan inda zai fada ba. Kuma Allah Zai barshi da gudun tunda bai yadda da hukuncin da Ya yanke masa ba. Haka aisha farida tayi, sai bayan kwana biyu ta kira shi a nutse tayi masa nasihu masu ratsa zuciya. Har sai da yaji ba zai tafi ba, ya fasa. Yana kuka, tana kuka, tanayi masa fatan alkhairi da godiya. Shima irin wadannan adduoin ya dinga zuraro mata har ta kashe wayar. Banbancin bikinta da na barr muazzam sati uku ne, don haka sanda taje dinner party'n bikinsu a tahir guest palace da daddare ta tafi musu da katin bikinta ita ma. Barr muazzam yayi farin ciki da ganin farida da shuraim a wajen bikinsu. Da farko ma bai ganeta ba, saboda kyan da tayi ta goge, ta waye ta tsatso da wani kyau na daban. Duk da dandazon taron nan kowa yana kokarin ya gaisa da ango da amarya, sai da muazzam ya taso ya tare su ya kamo hannun amaryarsa ya gabatar mata da aisha farida da ya dade yana bata labarinta. Daman ta san shuraim har ta gayyece shi bikinta, shuraim ma ya gabatar mata da farida a matsayin amaryarsa. Daga karshe muazzam ya kaisu wajen barr nuruddin suka gaisa, suka zauna a kurkusa. Tabbas daga gani babu tambaya, nuruddin yayi mamaki da ganin farida, shi bai taba tunaninta ba tun wacccan ranar, sai ya dinga tuno wulakancin da yayi mata a baya, yana jin nauyinta. Ya sake yin mamaki da yaga matarsa ma ta santa, sun kebe sai hira suke yi kuskus suna ta tuntsira dariya kamar sun saba. Ya kalli shuraim ya sake kallonsa, ya tabbatar ya hadu, Allah Ya tsara halittarsa a nan ko ba'a fada masa ba yasan akwai kudi da ilimi, kuma ita zai aura. Ya tara tambayoyo jifgi guda a zuciyarsa yana so ya samu muazzam ya jero masa su akan farida. Baraka ta dubi aisha farida tayi murmushi tace ina ta jin labarin aisha farida kullum, sai yau Allah Ya nuna min ke. Babu abinda zance miki ni da muazzam a duniya sai dai godiya, kin ceci rayuka. Ni da na zata ma soyayya kukeyi da barr muazzam, sai daga baya na gane jininku ne ya hadu, ya bani labarin ki da likita, kuma naji dadin ganinku a tare. In Sha Allah kuma zanzo bikinku duk da watan haihuwana ne wannan. Farida tayi dariya tace nafi kowa farin ciki da dukkanin mu Allah Ya amsa adduar mu , Ya bamu wadanda muke so. Ina nafisar ta sa take? Yaya suke a yanzu? Baraka tayi dariya tace ai ko zancenta ba yayi, ko kiransa tayi sai ya katse. Baya son abinda zai bata min rai, yanzu duk abinda nake so shi yake min. DUK KYAN TAKALMI 3* 11 Tunda bikin farida da shuraim ya rage saura sati guda basu zauna ba, daga ango da amarya har danginsu. Sai shirye shirye akeyi kala kala. Bayan yinin biki da kowanne bangarorin biyu zasuyi, akwai shagulgula har guda biyu da dangin ango da amarya zasu hadu a waje daya ayi. Daya da yamma za'ayi a tahir guest palace sai dinner a Chinese dragon da daddare za'ayi, kowanne kuwa sai da aka fitar da anko. Kayan fitar bikin ango da amarya daban aka dinka musu yadda zasuyi shigar kala iri daya tsadaddun gaske. Asabar ce yau misalin karfe biyar na yamma n shuraim ya sauke aisha farida a kofar gidan kawarta khadija sani dake sokoto td don ta mika mata katin gayyatar bikinta ta fito su tafi. Saboda akwai wurare da yawa da zata kai kafin magriba ya mayar da ita gida,saboda dokar da yaya hussaini ya saka mata cewar duk inda taje ta dawo gida kafin magriba ko da kuwa tana tare da shuraim ne tunda ba a daura aure ba. 'Ya'yan abida dukka hudun ne 'yan rakiya suna zazzaune a bayan mota sunyi dai dai da kayan ciye ciye da shuraim ya dau nauyin tulo musu. Suci biskit su kora da alewa, sai su dora da ice cream da shawarma. Ehm! Dadi kan dadi wai kunama ta harbi gyambo, abinda basu taba ci ba a yau gashi sun samu. Kada ki shiga ki zauna kiyi ta labari fa a ciki. Shuraim ya fada a lokacin da ya kashe mota dai dai wani bakin gate. Ta dube shi tayi murmushi ta gyara farin gilashin fuskarta tace bazan zauna ba yayana, yaya za'ayi in iya zama inyi hira alhali nasan kana jirana? Ina mika mata zan fito. Ta juya ta dubi yara tace ku zauna yanzu zan fito ba sai kun bini ciki ba. Ta bude mota ta fito, takawa take a nutse kafarta sanye da wani cogen takalmi mai tsinin gaske, launin baki da bakar jakarsa. Sai ya kara mata tsawo. Doguwar rigar jikinta (gown) da aka dinka mata a jikin super holland purple da baki ta sake fitowa da kyauwn dinkin. Dr shuraim ya bita da kallo saboda kyauwnta da yake gani, ji yake tamkar zai hadiyeta don kauna. Tana shiga gidan khadija ta iske ta a falo ita kadai tana kallon MBC action, bayan ta amsa sallamarta ta nuna mata kujera ta zauna, sannan ta sake kallonta sosai, sai a lokacin ta gane aisha umar ce. Khadija ta zabura ta mike tsaye, ta jawo dogon salati ta dire, ta rike haba tare da dafe kirji. Tace aisha umar dama kece na kasa gane ki? Ikon Allah kece kika zama haka? Daman maryam ahmad tace idan na ganki yanzu ba zan gane ki ba. Saboda kin sauya gaba daya kin zama 'yar gayu. Dariya kawai farida ke kyakyatawa, khadija ta matso kusa da ita ta zauna ta shafa jikinta, ta sake nanikarta don ta tantance kamshin turaren da take ji a jikinta , tabbas designer ne. Kudinsa ba zai gaza dubu ashirin ba. Ta janye dankwalinta don taga gashinta. Sai taga waccan cunkusheshen gashin na farida mai tauri da ba a shamfo sai kitson zane kullum yanzu ya sha mai (relaxer) yayi yalo yalo kamar na larabawa, baki sidik da shi, ya warware ya mike daman can mai yawan gashi ce da tsawo, don haka ya wuce kafadarta. Babu abinda khadija ke kira sai ikon Allah! Aisha umar yaushe kika zama haka? Aisha farida tayi sauri ta gyara daurin dankwalinta ta mike tsaye tana dariya tace Khadija bana son wulkanci, wane irin tonon silili kike yi min haka? Ke dai wani labarin zamuyi shi idan muka hadu, yanzu sauri nakeyi na bar shi a kofar gida. Katin bikina na kawo miki, rana ita yau yini da party. Ta zaro wasu hadaddun katina guda biyu ta mika mata daga cikin hadaddiyar jakar dake rataye a kafadarta. Ta juya da sauri ta fara tafiya. Khadija sani ta watsar da katunan akan kujera ta biyo bayanta da sauri. Tace ke aisha umar ko ruwa ba zaki tsaya ki sha ba? Dan mai adaidaita sahu ba sai ki sallame shi ba sai in mayar dake anjima da daddare ba? Ko angon ne ya fara hana ki kaiwa dare a waje? Lallai kina ji da wannan angon naki, ance mai kudi ne shi ya tsaya miki, ance yana sonki tamkar ransa. Auwal dan ajinmu yace min a likita zaki aura , rannan na hadu dashi auwal din a ministry of health yace min tare kuke aiki. Wai meye gaskiyar maganar? Aisha farida dai har yanzu dariya take yi, tace khadija don Allah ki ajiye tambayoyin nan naki sai mun nutsu zan amsa miki su. Daidai lokacin khadija ta tura kofar gate din suna kokarin fitowa, ta daga kai ta dubi dankareriyar motar da aka kawo aisha farida a ciki, sai tayi ajiyar zuciya kafin tayi magana. Sai ta daga kai ta hango santalelen saurayin da yake tsaye a jikin motar. Ya kalle ta, ta kalle shi, ta daka tsalle ta koma cikin gida da gudu, ta labe a jikin gate din tana salati. Aisha farida ta firgita itama tabi bayanta da sauri ta rike ta tana tambayarta lafiya? Khadija ta rike kirji tace aisha umar kamar dr shuraim nake gani a kofar gidana? Lafiya ya biyoni? Ba dai asirin da nayi masa bane yanzu ya fara cinsa ya biyo ni har gidan mijina? Yaya zanyi yau? Aisha farida tayi dariya tace ta yaya dr shuraim zai san gidanki har ya biyo ki? Wa ya fada miki asiri yana ci? Tabbas sihiri gaskiya ne amma bai cika kama wanda yayi imani da Allah ba. Dr shuraim ni ya kawo, don ni yazo gidannnan, shine angona. Khadija ta bude ido da baki gaba daya tana duban aisha farida, mamaki marar misaltuwa zaka gani a idanuwanta. Tace aisha umar yanzu dr shuraim zaki aura shine baki fadawa kowa ba? Ashe daman kema kina sonsa a lokacin da muke sonsa kika boyewa kowa? Ta ya kika same shi? Ke kuwa wane irin asiri kikayi masa haka? Aisha farida ta girgiza kai tace babu asiri acikin lamurana, sai dai addua. Addua na rike, ita ta kaini ga matsayin da ban taba zato ba. Khadija nayi alkwawri idan na samu nutsuwa zan fada miki dalla dalla yadda muka hadu da dr shuraim har ya zama mallakina. Sai anjima, sai kinzo bikina, adireshin wuraren duk suna jikin katin. Aisha farida ta juya ta tafi, yayin da ta bar khadija a sankare a tsaye, baki a bude don gigicewa da mamaki. Daga gidan khadija, gidan maryam ahmad suka wuce dake unguwar sallari. Irin wannnan mamaki da figici da ya samu khadija sani shi ya fadawa maryam ahmad. A lokacin da ta fito har mota don su gaisa da angon kawarta, ta iske dr shuraim ne. Sai da aisha farida ta tare ta don ta kusa faduwa don tsorata. Ta shiga yiwa farida rada tana cewa ke dr shuraim ne wannan ko kaninsa? Aisha umar ina kika same shi har zakuyi aure? Labarin yana da tsawo! Amsar da ta bata kenan ta shige mota suka ja suka tafi ta bar maryam a sankare a kofar gida. Aisha farida ta sake kyalkyalewa da dariya tace tunda kace Allah ai ka gama daure min jijiyoyin jikina. A lokacin tabbas nima mutum ce kamar kowa, kuma mace yadda suke mata. Naji abinda suka ji a raina, amma sai na fisu hakuri da tawakkali. Na sama raina har abada ba zan same ka ba gara ma kada in jefa kaina cikin wahala. Don haka ban cusa kaina ba, ina gefe ina addua, Allah masanin komai, sai Ya bani kai a lokacin da ban taba zata ba. Dr shuraim yayi murmushi ya lumshe ido yace na fahimce ki, kuma na gamsu da bayananki. Amma maiyasa kika tsorata baki zo kin gwada sa'arki ba? Kika sani ko kici nasara ki same ni? Ta girgiza kai tace karfina ko wayona da kwarkwasata ba zasu amfana min komai ba. Saboda naga 'yan mata da suka fini komai basu same ka ba. Yayi dariya yace kin taba sanin kina da kyau kuwa? Kyawun da tunda nake ban taba ganin wacce ta yi min kyau kamar ke ba. Tun ranar da na fara ganinki a duniya na tabbatar kina da kyau , da zan iya samunki da naji dadi. Sai aisha farida ta dafe haba ta bude baki tayi ajiyar zuciya ta langwabar da kai gefe. Tace shikenan my dear tunda har abin ya zama ba'a. Dr shuraim ya juyo a hankali ya dubi kwayar idon abin kaunarsa yace na taba yi miki karya ne? Toh ki yadda da magana ta, kina da kyaun da ba a ko ina ake samunsa ba, babu kantin da za'a iya samunsa a saya. DUK KYAN TAKALMI 3* 12 Yace,na taba miki karya? toh ki yarda da maganata,kina da kyan da ba a koina ake samunsa ba,babu kantin da za a iya samun irinsa a saya saboda dalilaina masu zuwa.na daya kina da kyakkyawar fata irin ta 'yan kasar itiofiya,mai hasken duhu(chocolate color).na biyu,kina da gashi mai kyau,irin na asalin Africa mai gazar-gazar da baki,irin wannan gashin shine a girarki da fatan idonki.na uku,kina da kyawun kwayar ido dara dara,farare sol!idan kina kallon mutum sai yaji wani yarr a jikinsa saboda kina da idanuwan nan da ake kira sexy eyes.na hudu,hancinki bashi da tsayi sosai,haka bashi da fadi ya dace da fuskarki.na biyar,bakinki dan karami,kina da hakora farare sol,ga 'yar siririyar wushirya a tsakiya.ga ki da fara'a idan kika yi dariya sai gefen kuncinki su loba dukka biyun,na shida,Allah yayi miki wata irin murya mai dadin gaske,wacce ko yar uwarki mace taji muryarki sai ta waiwayo balle da na miji.dadadan lafuzzanki su suke karawa muryarki dadi.na bakwai,Allah ya miki kirar jiki mai kyau,a dire kike,baki da kiba,ba ki da rama.sannan bakiyi gajarta ba,ba kiyi tsawo zalolo ba.amma duk wannan bai jaa hankali na na fara sonki ba,sai da na gama karantar halayenki na tabbatar kina da hankali,kirki,t awakkali,sannan kina da aji. Abubuwa biyu ne suke tafiya da tunanina a wajen mace,shine,idan mace tana da aji da kuma kamun kai wacce ba yar iska ba.kin yi sa'a kina da duk wadannan.aisha farida tayi hamdala a zuciyarta,tayi murmushi a sarari,ta dube shi tayi fari da ido.ta ce,nayi sa'a da nayi dace na sameka.Dr shuraim hakika kana da kyau babu inda Allah ya rage ka tun daga halittarka,ilimi da dukiya.duk wadannan basu dameni ba,sai na dinga lura da halayyarka.na shiga halin damuwa alokacin da ka gwada ni cewar zaka tafi da ni gidanka ko ba kayi bayani ba na fahimci abun da kake nufi,sai na kudiri niyyar rabuwa da kai har abada,kyawunka, dukiyar baza su taba burgeni ba,tunda kake sabawa Allah.sai daga baya na tabbatar ba haka kake ba,kai mutum ne mai tsoron Allah da tausayi shine na saki jikina na tabbatar nayi dace da miji nagari.su dukka sukayi dariya a lokaci guda. Dr shuraim yace kin cika mai hankali mai zurfin yunani,kuma ba zakiyi da na sani ba tunda kika farga kika san kyau da kudi ba komai bane in dai mutum bashi da hali na gari.matsalar da ke damun yanmatan zamanin nan ke nan,shi yasa ake samun matsala a zaman aure,sakin aure ya yawaita a kasar hausa.hirar so da kauna da fahimtar juna suka yi tayi,har suka isa kofar gidansu.yayin da yaran suke baya suna ta hidima da kayan dadi,sai ci suke tayi,ya ki ya kare saboda ledoji da yawa ya ciko musu.aisha farida tayi godiya suka fito daga motar suka shiga gida,dr shuraim yana daga muau hannu,su ma suna daga masa har ya tafi.su dukka suka ji kamar kada su rabu da juna,sai kuma gobe idan Allah yaa kaimu zai dawo don yanzu ba ya fashin zuwa wajen farida.ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA!!! BABI NA ASHIRIN BIKI!BUDIRI! BIREDEDE! Rana bata karya sai da uwar diya taji kunya.tun ranar laraba aka fara gudanar da shagalin bikin farida da angonta dr shuraim.akayi kamu laraba,alhamis akayi kunshi,jumaa akayi sisters eve da yamma.ranar asabar aka daura aure da misalain karfe goma sha daya na safe abisa sadaki mafi kankanta don neman albarkar aure,kuima a ranar akayi yinin biki.dangin farida sunzo da yawa maza da mata daga shagamu,tun sanda biki ya rage sati guda suka fara zuwa don su taya ta murnar biki.a ranar asabar da daddare akayi hadadden party a hotel din tahir guest palace,wanda mutane da dama suka halacci wajen. Manyan likitoci abokan ango da kawayen amarya,da yanuwaansu da abokan arziki kowa yazo.makada kala kala sunzo kamar mai dawayya,dan asharalle,yaron saadu bori,fati niger,rabi mustapha,kowannensu an bashi fili ya cashe.wannan yayi sai ya matsa ya baiwa wani fili.babu abun da ake kira sai likita shuraim angon sista farida.barista muazzam da amaryarsa janan,barista nuradin da uwargidansa baraka su ma sun hallara.yan unguwansu ta da duk sun zo babu wanda yasan adadin wadanda suka zo,saboda yawansu.taro yayi taro har amarya da ango basu iya gane wadanda suka zo da wadanda basu zo ba.kallo daya zaka yi wa ango da amarya ka tabbatar suna tsananin murna.idan ka kalle su zaka san maauratan nan suna tsananin son junansu.sun ba wa kowa shaawa sosai saboda sunyi kyau matuka,shigarsu ta burge kowa,kowacce rana akwai kalar kayan da zasu saka kala daya. Kawayen amarya su ma sunyi nasu ankon,dangin ango da irin nasu ankon daban.'yan shagamu ma da irin nasu ankon daban.masu daukar hotuna da bidiyo suna ta aikin dauka,sai yau mutane da yawa suka gasgata shuraim yayi saar mace mai kyau,don kyawunta ya fito kamar ba ita ba.ana daf da za a tashi sai ga uwar gidan shuraim faiza ta shigo fili,ta yi wa kowa ba zata ita da kawayenta guda biyu hafsat da halima su ma mazauna london ne,tare suka zo daga can.don da shuraim yayi yayi tazo bikin tace baza ta zo ba,toh ashe ta taho bai sani ba.ta danne kishinta tayi ta musu kari da daloli sai a lokacin aisha farida ta fara ganinta,ita ma haka,don ko a hoto ma bai taba nunawa ko wacce ba.kyawunta bai tsorata aisha farida ba ko kadan,don bata fita kyau ba.fari kawai zata nuna mata,tsayinsu daya,har farida ta fita tsawo da yawan gashi.faiza ce ma ta tsorata da ganina aisha farida saboda tayi mata ba zata,ba ta zaci ta hadu haka ba,don 'yan gulma sun tsegunta mata yar talakawa ce,baka mummuna,ashe abun ba haka yake ba. Faiza ta kudiri aniyar zama na kishi,ba kishin dokedoke da zage zage ba sai dai zata nuna mata ruwa ba saan kwando bane.wayewa da gogewa a cikin wayayyun duniya tabbas abun da ta sani farida bata sani ba,kuma ba zata taba sani ba.zata san tayi garajen aure mata mili,don mai karbar shuraim ahannunta sai yayi shirin yaki sosai DUK KYAN TAKALMI 3* 13 Sai dr shuraim yaji dadi da ganin faiza ta saki ranta,suka gaisa da farida sosai,har da baby yarsa mai kama da uban kamar an tsaga kara.babu wacce ta fi jin mamaki da ganin aisha farida ita ce amarya sai kanwarsa da suka hadu da ita a asibiti.suna ganin juna suka shaida kansu,suka gaisa cike da farin ciki. Washegari ranar lahadi da

Chapter 20 of 23