Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya daki hancinansu. Aisha farida tace humm lallai abin ma son kaine ko anty, ashe har da hanta da koda aka yayyanka a ciki shine ba a sako min bako daya sai maigida aka tulawa gasu nan burjik a ciki. DUK KYAN TAKALMI 2* 7 Abida tace me kika yi masa haka a rayuwa da zai tsane ki? Ba zai tsane ki ba, saboda kin riga kin kai kararsa wajen mahaliccinsa, zan sake baki wasu adduoi masu zafi wadanda suke kara soyayya da tausasa zuciyar wanda kake so. Idan kina karanta su hakika dole yaji yana sonki sosai. Adduar itace "Allahumma ya mukallibul kulubi wamusarrafuha kaifa ya sha'u usaibarul muhabbati fi kalbi (ambaton suna) bi hakki ismikal wadudu Ya wadudu. Ya wadudu sai dubu daya da dari daya da goma sha daya. Kiyi tayi kullum har zuwa lokacin da zai sanke kece mai dambu sai ya hadu da kaunar dambun da aikin wanna adduar su fara aiki. Ni kuma a lokacin zan fada miki abu na hudu da zaki rike nan gaba, kinsan yanzu uku na fada miki shine ADDUA, HAKURI da RIKE MUTUNCI. Bazan fadi na hudun ba, sai a lokacin da kika tabbatar min ya gama saninki. Idan ya ganki a ko ina zai shaidaki, zai kira sunanki, zaiyi miki murmushi, zaki gaishe shi ya amsa cikin farin ciki, to sai na jeho miki makami na hudu wato taryo soyayyarsa. Aisha farida ta lumshe ido don dadi tace kamar a mafarki nake jina. Sai nake jin bayaninki kamar na samu shuraim na gama. Abida tace shi yasa ake so mutum ya rike Allah, Shi zai biya masa bukatunsa banda bin boka ba ko 'yan bori. Shiyasa mata muka fi yawa a wuta, saboda karamin tunaninsu da gaggawa. Gaggawa kuma daga shaidan take, yanzu da kika riki Allah zaki ga yadda Allah zai taimake ki, ko baki samu shuraim ba zai musanya miki da wanda ya fishi, kuma zai tanadar miki babban rabo a lahira. Aisha farida ta gyada kai tace haka ne. Allah Ya sa mu dace, wadanda suka bata irin su Ummi Allah Ya ganar dasu gaskiya. Abida tace amin. Ci abinci ki fita kije ki cefano min kayan dambu. Asuba ta gari AISHA SHURAIM!! Washe gari aisha farida tayi sammakon zuwa ofishin dr lukman tayi sa'a kuwa tana isowa kamar tare suka zo, shima yazo yana bude ofis dinsa, don haka sai suka dunguma suka shiga tare. Ta gaishe shi ta ajiye katon kwandon mai dauke da katon food flask din abinci, babban na jiya ne da farantai hudu da cokula hudu. Dr lukman yayi murna da ganin dambu kuma yayi godiya. Yau ma yayi kokarin bata kudin taki karba, tayi gaggawar fita daga ofishin ta rufo masa kofa. Misalin karfe uku da rabi ta koma ofishin ta iske ofishin a kulle baya nan, amma ta jiyo muryarsa a ofishin dr shuraim, don haka sai ta sadada ta bar wajen. Ta dade a labe tana hango kofar ofishin ko zai fito bai fito ba, sai ta hakura ta tafi gida. Yau dai bata walwala sosai, don bata jiyo sakamakon jarabwar dahuwar dambu ba. Shin gogan nata yaci koma bai ci ba? Ya yaba ko ma bai yaba ba? Data fadawa abida sai tayi dariya tace ai ya ci ma kawai tunda kika jiyo muryar dr lukman a ofishinsa suna tare, babu yadda za'ayi yaga dambun yaki ci. Aisha farida tace ya za'ayi kuma gobe? Abida tace dan wake zanyi musu ki kai musu tunda shuraim yana son dan wake. Aisha farida tace a'a kada ayi, ki bari dai a kwana biyu kada lukman din ya zargi wani abu, ko yaji tsoro. Abida tayi darriya tace tsoron me? Idan kika kai musu dan waken kika dauko duka food flask dinn sai muyi shiru muji abinda zasu ce, kuma muji wanne suka fiso, suka fi jin dadinsa. Sai mu dinga yi musu shi. Aisha farida tace ni sai nake ganin kamar duk ba zai damu da sai yasan waye yake dahowa ba, balle ya sanni. Abida tayi murmushi tace kin manta abinda nake fada miki, ki zama mai hakuri duk mahakurci shi yake cin riba. Aisha farida ta jinjina kai tace haka ne, shikenan zanci gaba da hakuri. Abida tace yawwa tashi muje mu daka yaji mai dadin gaske yadda zasuji dadin danwaken sosai. Sai ki siyo tumatur, albasa, kokunba duk a yayyanka musu a ciki. Aisha farida tayi dariya tace har naji yawuna ya tsinke, gaskiya danwaken nan zaiyi dadi, zaiso shi. Rana ta uku ranar alhamis kenan kamar kullum da sassafe aisha farida ke fitowa daga gida tana fin kowa sammako. Tayi jira fiye da awa biyu sannan dr lukman ya iso. Sai da ya jima da shiga sannan tabi bayansa. Yayi farin ciki da ganinta, sai dai yayi matukar mamaki da jin dadi da ya ga ta sake dire masa wani kwandon abinci a gabansa. Yace lafiya, meye wannan kuma? Dama kin dauki kwandon jiya? Ta girgiza kai tace nazo baka nan sai na wuce gida kawai. Wannan wani ne na kawo muku, wannan karon ba dambu bane, wani launin abincin gargajiyar ne. Dr lukman yace a'a 'yar shagamu kinaso muyi fada ko? Yaya zaki tayi mana wahala, kartai muna taruwa muna cinyewa babu ko sinsinmu? To gaskiya bazan karbi wannan ba, ki koma dashi gida, ko ajiyar ma bazan yi ba. Aisha farida tayi dariya tace yi hakuri yayana, daga yau shikenan. Yace kwanukan jiya suna ofishin dr shuraim, kuma bana jin yazo yanzu, don bai cika zuwa da wuri ba. Ina da mukullin ofishinsa bari in bude in dauko miki kwandon da farantai da cokulan, amma ainahin food flask din ta tafi dashi gida, dambun jiya yayi dadi sosai, har yafi na shekaran jiya. Sai yace dole ya kai wa babansa yaci yaji irinsa, donshi ya koya masa cin dambu. To wallahi kinji yadda akayi, sai anjima zai zo zan ma sake yi masa waya kada ya mance dashi a gida, lallai lallai ya taho dashi. Tuni farin ciki ya cika zuciyar aisha farida, taji tamkar ta daka tsalle don murna. Tayi dariya tace ba koma dr ai ko food flask dinnan ba yanzu zan dauka ba, sai da yamma. Yanzu aji zan tafi. Sukayi sallama aisha farida ta tafi, kowannensu na farin ciki. La'asar sakaliya Aisha ta tunkaro ofishin dr lukman saita hango gogan nata yana shige da fice tsakanin wannan ofishin zuwa wancan dauke da wasu fayil don haka saita diro daga kan barandar ta shige lungu ta samu waje ta zauna har saida ta ga fitarsa ya shiga motarsa ya tafi gida bata bari ya ganta ba.ta tashi cimak ta nufi ofishin dr lukman hankalinta a kwance baby wata fargaba dr lukman ta iske shi kadai da alama shima ya miqe yana shirin tafia gida yana ganinta yayi dariya yace yar shagamu gaskia kin iya girki kice daman tun farko a shagamu na nemi mace ba'a yobe ba kinsan yadda mukayi santin dan waken nan dr shuraim har cewa yayi week end zaizo in kaishi ya gaida kakata mai dambu da dan wake da yake nace musu itace take daho min Aisha ta tuntsire da daria tace lallai kuwa daka zo shagamu an baka mata daka sha girki mai dadi ya miqo mata kwandunanta guda 2 yana godia tana godia suka yi sallama ta tafi tana fitowa bakin get ta dane acaba sai gida tana mai farin cikin zuwa sanrwa da abida labari.Abida na ganinta sai tabi ta daki suka rungume juna suna murna tun ma kafin abidar taji labarin abunda ya faru. Aisha tace zauna in baki ki sha suka zauna Aisha ta zayyana mata suk abubuwan da suka faru yau tsakaninta da dr lukman da abunda dr shuraim ya fada.Abida tayi murna sai ta shiga bubbude food flask din ta bude na farko saiga kudi yan 500 sabbi har guda 4 tayi sauri ta bude daya food falsk saiga yan 1k har guda 3 suma sabbi sai su duka suka bude baki suna mamakin wannan kudi da suka gani Aisha tasa hannu a hankali ta debo yan dari biyar din ta shinshina saita a jiye a gefe ta sake yan 1k ta shinshina saita lumshe ido tayi murmushi ta dubi abida tace wadannan kudin daga dr shuraim suka fito shinshina kiji qamshin turarensa Abida ta karba da sauri ta shinshina tace ehmm qamshi farida har a jikin kudi kike gane qamshin turaren masoyinki?lallai kin laqanci qamshin turarensa to shine ya zuba wadannan kudi kenan dr lukman ya zuba yar dari 500 dinnan daya ga kinki karba?Aisha tayi fari da ido tace Allah sarki mai karbar addu'a kalli daki-daki yana koro mana hanyar haduwa da shuraim a cikin ruwan sanyi yanzu ga kudinsa ya shigo hannu cikin hikimar ubangiji sai ta fara kuka Abida tace kada kiyi kuka kici gaba da dagewa da addu'a to yanzu kin ga kudin dr shuraimkinyi kuka ina ga ranar da kika ganshi kacokan a qofar gidanku yazo zaance balle ranar da zaki ganshi a dakinki a matsayin mijinki?sumewa zakiyi kenan don dadi?Aisha tayi daria tace gobe jumu'a yaya za'ayi a sake musu ko a bari?abida tace aa tsahirta gobe jumu'a sai kije ofishin dr lukman kice doctor ranar litinin me kuke so a dafo mukudambu ko dan wake kiji abunda zai zaba saiki zo tun ranar asabar mu fara aikin hada musu mai dadi da kunun gyada ko kunun tsamiya zakiyi musu mu zuba kofuna qanana zasu so shi kinga suma duk abincin gargajiya ne Aisha tace gaskia koba a fada ba dr shuraim zai so kunu sosai shike nan haka za'a yi.Anan dai suka bar hirar Aisha ta hadawa abida dukka kudin 5k ta ce ta riqe a wajenta ba sai ta dau ko sisi ba tunda ita ce take cefanen nan a aljihunta asuba ta gari farida shuraim. Khadija sani isma'I'll ce ta duni Aisha tace wai me yasa kullun idan nace kizo ki rakani babban daki na maza saiki turje ki tsaya daga nan kice inje in dawo ba kya son shiga?Aisha tace babu komai wlh ni dai kibar ni nan kije ki dawo zan jiraki ko hour nawa zakiyi khadija tace idan dai bazaki raka ni ba nima ba zan je ba daman ba wani abu zanyi ba illa in leqa ta wajen ofis din kyakyawan likitana dr shuraim musu mukeyi da mrym kinsan yanzu ta saki ranta ta daina kishin dani data ga ta rasa nima na rasa kuma bazamu samu ba mu duka sai dai in mun hadu muyita labarinsa cewa tayi yafi kama da larabawa ni kuma nace kyan indiyawa gare shi shine nake so mubi ta ofishinsa mu tantan ce nida ke kinjin Aisha ya ne ya buga bummm!don fargaba nan da nan taji hankalinta ya tashi tace a ranta daman har yanzu khadija da maryam basu daina son abuda nake matuqar so ba? Lallai ashe akwai hargitsi a nan gaba gara ma dai kawai in haqura da son mutunmin nan in hutawa raina abida ce taqi haqura dana cije na daure na watsar da son koda kuwa zuciata zata lahanta koda ciwon zucia zai zama shine ajalina in mutu in huta.sai taji kwalla ta cika mata ido sai khadija ta mungure ta sannan ta fara fahimtar maganar khadija keyi khadija ta kalli farida tayi murmushi tace kiyi min wannan taimako yau dai ki raka ni har ofishinsa ba komai zanyi ba illa in kare masa kallo in tantance nidai nasan akwai wanda yayi min kama dashi a film din india Aisha ta fusata tace shirme kenan haba khadija kamar wasu yan primary?ki tuna fa jami'a muke shirin gamawa kuma manyan ma'aikata muke shirin zama ma'aikatan ma na jinya masu kula da lafia jama'a wadan ake girmamawa a al'umma ya kike abu kamar marar ilimi?kinsan mutumin nan kinsan halinsa ke za ki fadawa wani irin salo da launin wulaqancinsa.ke kika cemin min kin haqura dashi baki yadda kika burge ni ba har kika umarci muhammad saurayinki ya kawo kudin aure ya kawo aka saka muku rana tamkar matar aure kike saboda anyi miki baiko ma'ana anyi wa wani alqawalin bambancinki da matar aure kadan ne mijinki kyakyawa dan gayu mai ilimi babban ma'aikacin banki da kadan shuraim yafi shi kyau habah khadija kada kibani kunya mana ashe har yanzu akwai namijin da zai burge ki bayan mijinki?kada fa ki zama irin matan nan da zasu yi aute kuma suna son wasu mazan a waje babban bala'I ne yin haka dunia da lahira halaka ce.idan kin san zuciayarki bata kwanta da auren muhammad ba gara kada ayi kice kin fasa kizo mu tayaki yaqin neman soyayyar wannan dan wulaqancin!kahadija ta tuntsire daria tace dadina dake Aisha umar akwai fadar gaskia komai dacinta wlh ko dan bazan zama daga cikin irin matan nan da kika zano ba insha'allahu ba zan sake zuwa ganinsa ba daman sai na manta dashi sai maryam ta tsokano min zancen itace har yau bata gama haqura ba Aisha umar ta kalli barandar can ki gani. Aisha ta wurga ido da sauri dr shuraim imran ta hango yana tahowa tafia yake a tsanake fuskarsa cike da fara'a jama'a suna ta gaishe shi yana amsawa idonsa ne ya wurga ya wurgo kansu Aisha farida wadanda ke tsaye a jikin bishiyar dake kusa da barandar da yake tafe kai kace ita da khadija saurayi da budurwa ne suke zantawa sun fuskanci juna suna tsaye cirko- cirko babu wanda ya sake magana a cikinsu yayin da khadija ke kallonsa tana yi masa murmushi. Aisha kuwa sauri tayi ta juyar da kanta gefe bata duban bangaren da yake ma Aisha taji tamkar ta kurma ihu don takaici tada ji khadija ta maqe murya ta gaishe shi saii ya amsa cikin farin ciki ya wuce abinsa sai da yayi nisa khadija ta zungure ta tace amma bakida kirki kina ganin malaminki amma kika qi gaishes shi ? naga alama fa baiji dadin ba da baki gaishe shi ba Aisha ta tabe baki tace yaya akayi kika san baiji dadi ba? Khadija tace saboda naga irin kallon da yake yi miki ne leqen fuskarki yane tafe yana waiwaye so yake ki juyo ya ganki Aisha tace ai ba dole ne in gaishe shi ba tunda in an gaishe shi sai yaga dama yake amsawa ke rabi ni da wahala kinji ta kaina nake bani da lokacin kowa.khadija tace kin huta ai shiyasa kike burgeni ina son halinki ko bayan idonki ina fada daman tun farko ma dai naga alamar kin tsani dr shuraim ko zancensa ba kya ayi miki Aisha tayi wani lalausan murmushi ta gyada kai tace me yasa zan tsani musulmi dan uwana ?aa wlh ban tsane shiba ko kadan ina sonsa so tamkar raina zai fice kamar yadda nake son dan uwana na jini saboda shi ma musilmi ne musulmin ma mumini mai riqe addini irinsa khadija tayi doguwar ajiyar zucia ta dauka Aisha ma zata ce itama ta mato a sonsa yadda itama take sonsa sai taji farida tayi kwana.suna tafe suna firarsa har zuwa bangaren da suke wato wajen masu ciwon hawan jini da ciwon suga Akan barandar da suke tafe a nan shuraim ya taho suna daga ido sai suka hango shi daf dasu shi yana tahowa su suna tafia sai suka yi gum da bakinsu don birarsa suke a lokacin dan halak yaqi ambato inji khadija Aisha ta duqar da kanta qasa bata sakw dagowa bahar sai daya gifta ya wuce kamshin jikins ya daki hancinta sai ta lumshe ido ta fada a zuciayar ya Allah ina son wannan bawa naka sannu likita sanna da qoqari kalaman da suka rikito kunnen Aisha ke nan daga bakin khadija take fadawa dr shuraim dai-dai sanda yazo giftawa ya fada cikin qasaita thank u ya wuce abinsa Aisha farida tafia take kawai amma tamkar ta hadiyi zucia don jin haushin barar da ajin da khadija keyia wajen bawan Allah nan. Khadija ta zunguri Aisha tace saki dago da kanki dodon naki ya wuce don naga ko kallonsa ba kya son yi ikon Allah shi kuwa sai ya tsura miki iso yayi ta kallonki don Allah ki dinga gaishe shi bin na gaba fa bin Allah ne Aisha tayi ajiyar zucia tace Allah yabamu ikon bin shugabanninmu amma wadanda suke bin Allah khadija tayi daria tace shegiya Aisha umar akwai iya magana nasan baki yarda da abun dana fada miki ba zaki dinga gaishe shi ba kenan?kin jini ne dai kawai Aisha tace uhmm kawai take fadin sai kuma gyada kai take tayi tamkar kadangaruwar ta kasa cewa komai saboda ganin dr shuraim dinnan da tayi yau yayi mummunan fama mata son data keyi masa Aisha shuraim haquri shine maganin zaman duniya! Aisha ta cika mamaki a lokacin da yaro ya leqo dakinta yace tazo wani yana sallama da ita a qofar gida a motarsa a zaune ta duba agogo karfe 7:30 na dare ko isha'I ba'a kira ba yadda take zaune akan abun sallarta sanye da hijabi da carbi a hannuta haka tayi zunbur ta miqe tace da yaron tsaya ni mu tafi tare ka kai ni wajen mai yin sallamar dani faruk ta gani dan abida a tsakar gida tace idan mamarka ta idara salla a kace mata anyi kirana a qofar gida ina zuwa ya amsa da to aunty Aisha zaki siyo mun alewa da biscuit?aisha ta girgiza kai banyi maka wannan alqawalin ba nima nan daka ganni na dade ban sha alawaba ta wuce da sauri ita da dan aike ta kama hannunsa tace yaro a ina mai motar yake?wayace ka kira?yaron yace a wajen ya tsaya kafon a hayo sai ya kirani yace inzo nan gidan nan mai bishiyar dirimi in kira masa Aisha umar qanwar husaida mijin abida shine nake ta leqawa ina tambaya har aka nuna min dakinki mamaki ya sake lullube farida ta dafe qirji tace inalillahi wa inna ilaihi raji'un Allah yasa baqon nan baqon Alkhairi ne toni waye wannan?ba dai dr lukman bane balle in saka ran dr shuraim sune kadai nasani a dunia masu mota su kuwa basu san gidanmu ba haka yaro yaya suffar mutumin take?yaro yace dogo ne haka fari mai dan gemu a habarsa kyakyawa mai kudi motar hadaddiya Aisha ta juya kawai tana kallon yaron tana mamakin yadda yake suffanta mutumin.tabba s suffofin dr shuraim ya zano mata amma tana tabbacin ba dr shuraim bane a wanne dalilin ma zata saka ran dr shuraim zaizo gidansu mutumin da har yanzu bai game gane taba a hanya balle wata hulda ta hada su harma ya tako a qafarsa ya zo inda take don haka ta cire dr shuraim a tunanin ko shine sai ta koma sake saqen wasu daban suna tafe fakam- fakam sai sauri suke zubawa ta sake juyowa ta dubi yaron tace yaro shi kadai ne koda macea motar?yace shi kadai ne! Aisha ta fada a bayyane toni Aisha waye wannan da akwai mace a motar sai ince khadija ce ta kawo min mijinta mu gaisa yaro kawo bakin wata dalleliyar motar qirar BMW baqa wuliq sabuwa dal!har sheqi take ya ce ga motar mutumin yana ciki, Gabanta ya yanke ya fadi daf-daf taja ta cije ta tsya a gefe tace kwankwasa masa gilashi kace masa gata ka kira ta don inga ko waye yaro ya qarasa da sauri ya daddage ya daki glass kai kace qofar qarfe yake bugawa lallausan hannu hade da kyakyawar fuskar dan adamu ne ta fito fili sai gashi ya bayyana a lokacin da ya sauke gilashin wundonsa qasa Aisha ta kaikace tana leqensa daga nesa har yanzu bata gane shi ba kasancewar akwai duhu wajen duk da akwai hasken redio motarsa na haska shi kadan yaron ya dawo wajen farida yace ki qarasa kinga har yabani N100 Aisha tace lallai ka caba kaje na gode tafia take a nutse amma a tsorace kamar ace kulle tace cas!nauyi kunya fargaba da tsanaanin tsoro sun gallabe ta ta isa jikin window da yake zaune ya zuba mata ido yana kallonta fuskarsa cike da annuri yana nuna farin cikin da ganinta ta kasa kallonsa saita duqa ta gaishe shi ya amsa cike da fara'a hadi da cewa hajia Aisha farida yar shagamu nasan zakiyi mamakin ganina ko?wannan karon da sauri ta dago kai ta dubi kyakyawar fuskarsa domin tana jin muryarsa ta gane ko wanene tabbasa muryarsa ta tabbatar mata dashi dinne wanda take zato a lokacin data dubi fuskarsa.dadi marar misaltuwa suka tabbata a zucia yar Aisha ta dafe qirji ta fada cike da mamaki marar adadi barista mu'azzam yau kaine a gidanmu nayi matuqar mamaki hade da dinbin farin ciki dana ganka a gidanmu ka kyauta gaskia Allah ya bar zumunci yayi daria yace miki wannan shine zuwana na farko aina sha zuwa nansai in aika yaro ya dawo yace min. Ance ba kya nan kai rannan ma ce min kayi gidan naga wasu maza 3 a zazzaune akan tabarma suke cemin kina ciki amma shwararda zasu bani kada in sake dawowa ba kula zaki yiba haka yayanki ma idan ya ganni korar kare zaiyi min.na fahimci dai hassada ce kawai na tafi na barsu yau dai Allah yasa na sami yaro mai wayo nace ya shiga ciki ya nemo har. Dakinki ya kirawo ki amma wanne irin zama kuke da mutanengidanku haka shin bakwa shiri ne? sai hawaye ya fara surnanowa a idontaAisha tana sharbewa da hijabinta barista mu'azzam ya warwaro toilet paper ya miqa mata yace aa qanwata kin fara koke -koken naki ko?bana son kukan nan yanzu zaki kore ni fa Aisha farida ta goge idanuwanta tace na daina kuka yayana abun ne yabani mamaki muna zaune dasu zucia daya muna qoqarin kyautata musu su basa qaunarmu ba'a son ci gabanmu ko zaka rufe motar kazo muje kan dakalin qofar gidan mu zauna kada in shiga motarka ayi ta yamudidi dani a unguwa da sharri kala-kala Alhamdulillah daka san yadda mutanenmu suke. Barista mu'azzam yace kwarai kuwa yi gaba zan biyo bayanki kada a ganmu mun jera muna tafia Aisha tayi sauri ta shiga gida don dauko sallaya da pure water. Abida tabi ta daki a gigice tana tambayarta wai waye yazo a dalleliyar mota ne, naji matan gidan nan suna ta yamadidi, har suna aika 'ya'yansu suje su gano musu ke. Aisha farida ta rike baki tace mun shiga uku da zaman haya, au faruk ba fada miki sakon dana bashi ba, nace ana kirana a waje na tafi. Abida tace bai fada min ba a tsakar gida nake jiyo gulmar. Kada fa kice min dr shuraim ne? Aisha farida tace in dr shuraim ne ba sai mu gudu ba? Bashi bane, barister muazzam ne. Ta kwashe labarin daya bata ta fadawa abida, na 'yan hassada. Mamaki ya rufe abida ita ma sai da tayi kuka. Aisha farida ta hanzarta daukar sallaya da pure water guda biyu ta fice da sauri ta iske har barrister muazzam ya karaso kofar gidan, kasancewar bayan magriba ne don haka yawancin mazan gidan duk suna masallatai, sai anyi sallar ishai zasu dawo. Ta shimfida akan dogon dakalin mai fadi, sannan ta umurce shi da ya zauna. Yana zama sai ta duka ta mika masa pure water ko sanyi babu, ya karba yayi murmushi yace nagode ki zauna mana ya zaki tsaya a tsaye, ai ina ganin akwai tazara a tsakanin mu idan kin zauna a karshen dakalin, ni ma ina karshe ba za a ce kinyi rashin kunya ba dai ko? Don naga alamar unguwar nan taku abar tsoro ce, suna da saka ido da gulma, koda yake duk cikin gari haka suke, 'yan gargajiya ne kawai. Babu maganar wayewa a tattare dasu. Aisha farida tayi murmushi ta zauna a tsorace ta sake gaishe shi, sannan tace yaya muazzam sai hakuri, bamu da fridge kuma inda ake sayar da ruwan sanyi babu saboda munfi sata ba a kawo mana wuta ba, zaka ji ruwan babu sanyi. Muazzam yayi dariya yace kada ki damu, yanzun nan na sha ruwa har roba biyu a mota, na karba ne dai don kar kiji babu dadi, nagode. Aisha farida tayi dariya tace a'a nice da godiya, naji dadi da na ganka, Allah Ya bar zumunci. Ina abokinka barr nurruddin? Ina baraka matarsa? Ina kuma matarka dr janan? Barr muazzam ya kwashe da dariya yace har kin daura mana aure ne ta zama matata? Duk suna nan lafiya kamar yadda kika barsu, babu wanda ya sauya a cikinsu. Nuraddin yana nan yana taurin kansa, da gallazawa baraka. Haka itama baraka tana nan tana hakuri. Ko da yake kwanan nan ta fara ce min hakurinta ya fara karewa, zata fadawa magabata a raba auren. Ita kuwa janan tana nan a daure ana ta tafka sharia babu wani canji a tsakanina da ita. Iyayenta ne dai kawai suke ganin kokarina da nake a kanta, ita har yanzu bana gabanta. Ni har haushin kaina nake ji wata rana ince to wai me yasa na nace sai janan bayan a gari ga 'yan mata nan reras wadanda ma suka fi ta kyau da kwalliya, saboda a yanzu idan kika ga yadda janan ta koma idan kinsan ta a da ba zaki ce ita bace, kamar wacce aka sauya ta gaba daya duk tayi muni, tayi baki, an aske wannan gashin nata mai tsawo sai kwas kwas. A ficika wani ba zai dauke ta ba, amma har yanzu zuciyata bata daina sonta ba, kuma ita kadai nake so bana son wata. Wannan al'amaro yana bani tsoro da mamaki. Aisha farida ta girgiza kai tace Allah sarki rayuwa, har naji tausayinka. Wannan shine ake kira soyayyar gaskiya, so saboda Allah kenan ba don wani abu ba. K KYAN TAKALMI 2* 9 Dr lukman yace kin tabbata baki gane abin da yake nufi ba? Kada ki boye min komai. Aisha farida ta girgiza kai ta zubo da hawaye da ya cika mata ido tace bansani ba wallahi. Yace to jeki zanyi miki waya anjima kada kiyi kuka. Aisha farida ta tashi da sauri ta fice yayin da dr shuraim ya bi ta da harara. Tana fita sai ta rufe kofar kuma ta labe ta dora kunne a jikin kofa tana sauraronsu. Dr lukman ya juya ya dubi shuraim yace wai me yake faruwa ne? Yarinya ce fa kimtsatsiya. Tana bin maza ne ma'aikata? Dr shuraim yace kaji matsalar ku kenan, baku da kyakkyawan zato, nan da na sai ku ballo bala'I. Meya kawo wannan zargin kuma? Dr lukman ya juya ya dubi dr mohd yace don Allah dr a kasar hausa idan aka dubi mace akace ki kama mutunci da darajarki ta 'ya mace meke nan? Ba 'yar iska ba kenan? Dr mohd yace kwarai kusa, kasan bature ne su a london ustazan mata ake fadawa haka. Suka kwashe da dariya su dukka, dr shuraim yace uhumm kai kake ganin hankalin yarinyar na, ai ni tuni nasan maciji sari ka noke ce. Nafi ku karantar halayanta. Wato tunda Allah Ya halicce ni a duniya tsakanin jinsin mace ko namiji ban taba ganin wacce ta iya hawa acaba irin wannan yarinyar ba. Sai su dr lukman suka kwashe da dariya, yayin da dariya ta kubcewa aisha farida sai tayi sauri ta toshe bakinta. Dr shuraim ya bata fuska yace ai ku abin ma dariya ya baku? Wallahi ba abin dariya bane, ya kamata kayi mata fada. Hawan jini ne kawai rannan banyi ba, shekaran jiya ne ma ba adade ba. Caraf zaka ga ta haye acaba da yake ba nauyi ne da ita ba, kuma ta kware. Dan acabar nan ya wulwula da ita suna kallon kudu sai sai gasu sun juyo arewa ba tare da ya duba ko ya saka sigina ba, suka rufta kan wasu 'yan acabar suka tafi tangal tangal kamar zasu fada

Chapter 12 of 23