Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
min cewar idan ta riga ni mutuwa inyi mata addua kamar yadda na yiwa mahaifina. Nayi mata addua sosai kuma ban manta ambaton innalillahi wa'innalialhir rajiun ba har gari ya waye. Sai dai nayi kuka mai yawa saboda na kara wayo na san zafin mutuwar sosai ba kamar da ba, na tausayawa kaina sai nafi tausayin kanwata munauwara. Gata karama ita kadai ta rage babu uwa, babu uba, babu ni 'yar uwarta. Nasan a gidanmu 'yan ubanci akeyi kowa yana tattalin 'yan dakinsu, nasan sai dai dangin mahaifiyta ne zasu dauke ta suma kuma duka kanwar ja ce, talauci ne tsagoronsa. Rashin kudin motar da za'a kai gawarta shagamu shi ya hana yaya ya kai ta can a binne sai kawai ya buga waya ya sanar dasu wannan mummunan labari. Sun kuwa gigice da jin haka sai suka yanke shawara gara wasu su taho kanon ayi jana'iza a binne ta anan. Allah Ya rubuto anan kasarta take. Da suka iso sai akayi mata sallah aka binne ta. Kafin kwana bakwai wasu daga cikin danginmu sai da suka zo kano sukayi gaisuwa sannan suka koma, wasu da yawa basu sami damar zuwa ba, da yake a can ma ana zaman makokin don ba kowa yake da kudin zuwa ba. Da akayi albashi ni da yaya hussaini da matarsa mukaje shagamu don yin gaisuwa da kuma zancen abinda ta bari. Baiwar Allah bata da komai daman mijinta bai bar mata komai ba, dan matan basu samu gida ba! Basu samu gona ba. Ko mu 'ya'yan kudi kadan aka bamu da akayiwa gidan da gona kudi wani yayanmu ne ya saya dan ba zai rabu ba. Daga ragargajejjen gadonta sai tsumokaren kayanta aka ajiye mana shine gadonmu. Na kasance marainiya babu uwa ba uba, sai ni sai halina sai kuma yayana hussaini da matarsa sai Allah. Kuma ina godiya ga Allah a kowanne lokaci don ban mantawa da nasihohin da mahaifina yayi min ta karshe. Allah yana ganina, kuma Yana taimakona, Bai bari na tagayyara ba. Babbar baiwar da Allah ya min itace daya bani jama'a, masu sona suna da yawa a duniya, mata da maza. Yara da manya kowa yana yabon halayyata koda kuwa an kushe ni sai kaji ana yabona. Na godewa Allah Shine gatana shine majibancin al'amurana. Aisha farida ta rushe da kuka hade da hawaye mai radadin fita. Hawaye ne yake ta kwaranya tamkar an bude ruwa a famfo. Barrister Mu'azzam ya juya ya dubi abokinsa barrister nuruddeen shima ya kalle shi sannan suka juya su dukka suka sake duban aisha farida, suka cigaba da mamakin wannan yarinya mai surutu da zazzakar murya, ga iya magana tana fitar da kalamai dalla dalla a jejjere tamkar wacce wani ya labe yake rada mata. Wannan itace fadi ba'a tambaye ki ba, amma fa sunji dadin sauraron labarinta, yayi ma'ana kuma sun karu da abubuwa da yawa na game da zamantakewar rayuwa. Sannan sun tausaya mata, ta cancanci a tausaya mata domin rayuwarta tana cike da abubuwan ban tausayi. Daga ganin ta a kidme take a dimauce ta fado musu ta gaishe su, kafin su amsa ta sami kujera ta zauna ta hau basu labari. Yau ne rana ta farko da suka fara ganinta a rayuwarsu itama haka, farida batasan wacce irin damuwa bace ta hana su zama a gidajensu suka fito a cikin daren nan suka zauna a wajen shakatawa mai suna "fish park" dake nassarawa GRA. Barrister muazzam ya zaro dan karamin handkerchief fari kal daga gaban aljihun rigarsa (suit) ya mika mata ba tare da yayi magana ba, ta dago da jajayen idanuwanta tana gogewa wani sabon hawaye fil yana bulbulowa daga idanuwanta. Barrister muazzam ya mika hannu a sanyaye kan teburin dake gabansu ya dauko wani kwalin lemo ya tsiyaya a cikin kofuna biyun da suke gabansu ya mika mata, sai ta karba sannan tayi godiya ta fara kurba a cikin nutsuwa yayin da shima ya dauki daya kofin ya kwankwadi lemon a cikin kofin ya mikawa abokinsa shima ya karba ya fara sha ba tare da wani daga cikinsu yace uffan ba. Sai aisha farida ta fara tunanin ko kurame ne bata sani ba tazo ta hau su da surutu, saboda tun sanda ta zo ta zauna ana fiye da mintuna talatin babu wanda yayi ko tari a cikinsu har yanzu sai kallonta kawai sukeyi da ido. Ta kurbi lemo ta ajiye kofin akan teburi ta sharce hawaye da hankicin dake hannunta tayi murmushi. Tace bayin Allah shin baku magana ne, ko kurame ne? Kallonta kawai suke yi har yanzu babu wanda ya tanka mata, su kalleta su juya su kalli junansu. Sai taji hankalinta ya tashi, tayi ajiyar zuciya tace yaya sunanku? Barista nuruddeen ya dubi barr muazzam ya kifta masa ido alamar kada yayi magana. Suka ci gaba da sauraronta tana ta magana ita kadai, sai taji ta zama tamkar wata mahaukaciya wacce bata san ma abinda take yi ba, taji duk ta tsani rayuwarta, sai ta tashi a sanyaye ta juya zata tafi. Barr muazzam yaji tausayinta sai yace aisha farida meyasa zaki tafi? Ta juyo da sauri ta dube shi sai ta girgiza kai tace kuyi hakuri ban san na takura muku ba, na shiga masifa, na shiga kunci har na dimauce ban san dalilin da yasa nazo wajenku na dinga zazzago muku labari baku tambaye ni ba. Na ganku kammalallu dan haka na zata zaku karbe ni hannu bibibuy , kuba bani shawara dan ban san abinda zanyi ba anan gaba. Barr muazzam yace dawo ki zauna, shirun da mukayi miki don bamu sanki ba kuma bamu san manufarki ba kinsan duniya abar tsoro ce bai kamata nan da nan ka yarda da mutumin da baka taba gani ba. Kuncin rayuwar kuwa mun fiki shiga shine ya fito damu nan ko Allah zaisa muji dan sanyi. Ta dawo ta zauna a sanyaye ya yin da take tuhumar kanta da laifin rashin hankali,tana jin haushin kuskuren data tafka daga ganin mutane bata san su ba kawai ta zo ta zauna ta hau basu labari,ta fadi sirrinta bayan ba'a tambaye ta ba,lallai dole suyi mata kallon wata sakarya. Ta tambayi zuciyarta shin ko cutar tabin hankali ce ta kama brain din ta domin sanda ma ta fara magana bata sani ba. Mu'azzam ne ya ktse tunanin da take yi ya ce "ni sunana Barr Mu'azzam,abokina kuma Barr. Nuruddin. Mecece takamaimiyar matsalarki? Menene dalilin da ya fito da ke daga gidanku zuwa nan a cikin daren nan? Naga ba tare da mijinki ku ka zo sayan kifi ba kamar yadda nake ganin wasu ma'auratan hausawanmu na yi? Me kika fito nema? Wanne irin taimako kike nema daga garemu? Kina so mu saya miki kifi ne ko kuwa kudin mota ki ke nema? Ta yi murmushi ta ce "gaskiya ne,na cancanci a tambaye ni domin ban yi kama da mai kamun kai ba. A rude na shigo nan dan yau ne rana ta farko dana taba zuwa nan,ban san inda zan nufa ba sai na hango ku kawai na ji a raina tamkar naga yayyena,wadanda zasu iya taimakona shine na taho wajen ku ko Allah zai sa ku kwace ni daga mugun dan sandan da yake shirin cutar da rayuwata. Barr nuruddin ya dubi abokinsa ya tsuke fuska ya ce "kai kada fa ka yayumo mana ruwan dafa kanmu,ka bar yarinyar nan ta kama gabanta. Me yasa ka dawo da ita har ta yi niyyar tafiya? Ka cika kwashe- kwashe kamar baka san irin yan matan nan ba ne yan club? Idan ba yar club ba wacce budurwar kirki ce zata baro gidan iyayenta ta shigo wajen nan da dare? Ka duba ka ga nisan unguwarsu tun daga cikin gari zuwa nan? Zuwa ta yi ta tsara mu ko daya daga cikinmu zai dauke ta. Ke yarinya ki kama gabanki mu ba irinki bane,je ki can ki sami yan uwanki irin ki. Shawarar da zan baki kuma ita ce ki koma skul ki taimaki lyf din ki don yawan duniya ba riba sai asara,akamr yadda kika ce mahaifinki ya yi maki wasiyya kafin ya rasu" aisha farida tayi dariya maimakon ta ji haishi sai ta gyada kai tace "gaskiya ne yayana na ji dadin shwararka kuma zan dauka insha Allah zanyi amfani da ita. Sai nauyi da kunya ya kama barrista mu'azzam ya ji kamar ya nutse a cikn kasa saboda baranbaramar da abokinsa yake yi,baya kara,ba kunya balle jin nauyi yake maganarsa,ya harare shi yace haba nuraddin kai fa mtsalata da kai kwaba mahgana babu taunawa. Ka bari ka ji uzurinta idan ka gama jin inda ta nufa sai ka yanke mata hukunci. Kamar ba lauya ba ai sai ka gama sauraron labarinta tun daga farko har karshe sannan ka gama jero mata tambayoyi ta gama amsawa ka kula da inda ta nufa sannan ka yi mata nasiha ba fada ba. Yanzu da a kotu muke sai ka fadi a sharia dan kawai kana jin haushin ka sai ka huce akan yar mutane,to ba ita ta kar zomon ba ko rataya ba'a bata ba. Posted by Bashir Sani Mahmud on 22 Aug 2017 Aisha farida tayi karfin hali tace ba damuwa, ai laifina ne dan banyi kama da mai kamun kai ba, tunda ba'a tambaye ni ba nazo na fara yi muku surutu, nasan ba'a son mace marar kamun kai. Barr muazzam ya girgiza kai yace zuwanki nan ba laifi bane dan kin zo kin zauna a kusa damu, kujeru ne a jejjere kowa zai iya zuwa ya zauna. Da kika zo kika same mu kinyi mana sallama duk da tun kafin mu amsa har kin zauna. Daman kamata yayi ki gabatar mana da kanki kuma kinyi hakan sai dai kika zarce da bamu labari shine abinda ya daure mana kai kenan. Kallon junan da kikaga muna yi ina tunanin ya sanki ne, shima yana tunanin ko na sanki ne. Aisha bani labarin takamaiman abinda ke damunki, muma nan da kika ganmu matsala ce take addabarmu, ki saki jiki ki fada mana mu dake sai mu taimaki juna da shawarwari. Barr nuruddeen ya fusata ya mike tsaye ya dubi abokinsa yace malam in ka gama kazo ka same ni a cikin mota mu tafi, dan ba zan iya zama ina sauraron wannan shirmen naku ba. Bansan sanda ka zama marar aji ba, daga haduwa da 'yar tasha sai ka hau hira da ita kai ma kana baza sirrinka, idan taji matsalar ka me wannan zatayi maka? Itama bata san yadda zatayi da kanta ba balle ta bawa wani shawara. Kada ka sake ka ambaci sunana a cikin labarinku kai dai ka fadi taka matsalar. Ya juya a fusace ya tafi bai daina fada ba yana tafe yana magana yana wurwurga hannu har ya fice daga cikin gate din. Aisha farida da barr muazzam suka bishi da kallo har sai da suka daina hango shi. Ta sunkuyar da kanta kasa sai hawaye ya fara zubowa daga idanuwanta. Kada ki yi kuka aisha, ki mayar da komai ba komai ba. Kece fa kika gama bani labarin cewa zaki iya zama da kowanne irin mutum a duniya. Inji brr muazzam. sai tayi murmushi ta shiga goge hawayenta tace ko kusa ban damu ba, banji haushi ba. Kawai dai abokinka yayi min kallon ballagar mace, 'yar tasha, 'yar club, karuwa kenan. Shine mutum na farko a rayuwata daya taba jifata da wadannan munanan sunaye, saboda bai sanni ba, sai dai ina fatan ya sanni nan gaba. Barr muazzam yace yi hakuri kanwata, ki cigaba da bani labarin rayuwarki, ina jin dadin sauraronki. Haqiqa Aisha farida,labarinki yakai maqura gurintausayi,nayi kuka sosai,rabena da irinkukannan yaukimani wata takwas kenan.tunrasuwar yayata,ayau nafisa mamawa kinsani cikintausayin ki,maganardanakeyi yanzuhaka nakasa tsayarda hawayendake zuba'a idona. kitaimaka kibani lbrin cigabanki da daukakardakikasamu kozansamisukuni yau...wallah nafisa natausayamiki sosai. BABI NA BIYU Da na karasa makarantar primary sai yaya hussaini ya kaini wata makaranta a wajen sabongari na zana jarabawar common entrance ta shiga makarantar federal. Allah cikin ikonsa sai naci jarabawa aka turani makarantar da na zaba wato FGC kano. Yayi min sayayya iya karfinsa ya kaini, ya bibbiya dukka kudaden makarantar da aka bukata, ya dawo gida ya barni a can. Nayi kuka saboda rashin sabo, gashi bansan kowa ba a makarantar amma daga baya na saba da dalibai 'yan uwana sai na fara jin dadin rayuwar makarantar. Jama'a na sona saboda yadda nake da fara'a, ladabi da son aiki bana kiwa don haka kowa yana son ya jani a jiki saboda ina da matukar tsafta. Na yi suna a makarantar nan da nan malamai ma suka sanni saboda kwazona da wayo, ga iya magana. Na gama aji uku hutun da zamu shiga aji hudu aka cireni, abu ya ci tura hidimomu sun karu, yayana ba zai iya cigaba da yi min siyayya ba da biyan kudin makaranta ba kasancewar shima ya hayyayyafa. A jejjere ba kakkautawa abida take haihuwa, 'ya'yanta na farko ma 'yan biyu ne maza abubakar da umar, sai ta haifi mace mas'uda ga wani cikin a jikinta ko yaye ta goyen bata yi ba. Ga kudin haya ya karu, cefane ya karu, farashin abinci ya karu, gashi an kara kudin makaranta ya kusa ninka na da ma. Daman duk sanda zan koma makaranta sai ya ciyo bashi kafin ya harhada ni in tafi. Ya kira ni daki ya zaunar da ni yayi min bayanin halinda ake ciki, sai ya bani hakuri cewar zai mayar dani makarantar gwamnati ta ;yan mata dake shekara. Dole na koma makarantar shekara naci gaba da karatu, daga aji 4 na fara, sai na zama zakaran gwajin dafi nafi kowa kokari saboda dana sami horo a FGC a wajen yaran kabilun da basa jin hausa da yaran hausawan da suka sami horon turanci tun daga primary. Ajin kimiya na shiga (science class) har Allah ya kaini aji shida aka bani shugabar dalibai, duk wata gasa ko muhawara ta turanci tsakaninmu da wasu makarantun ni nake tsayawa makarantarmu, idan bana nan babau abinda yake tafi dai dai. Shugabar makarantar mu tana alfahari dani, kullum tana kwatance dani saboda kokarina. Da muka gama makarantar ita da malamai sai da sukayi takaicin rashina saboda ba'a sami madadina ba. Bayan gama makarantata da wata uku yayana ya harhada 'yan kudadensa ya bani kudin mota da guzuri na zuwa shagamu, saboda duksanda yake zuwa shi da matarsa da 'ya'yansa ina makaranta ba'a zuwa dani. Tsofaffin abokan hirata har sun gaji da tambayata wasu ma sun mutu, haka wasu daga cikin yayyena sun murmutu duk banje ba. Ina samun wasikun kanwata munauwara akai akai duk sanda ta sanda ta sami mai zuwa sai ta bayar an kawao min, ta shaida min cewar an cire ta daga makaranta tana secondary aji 3 anyi mata aure saboda rashin kudi. Ni kadai yaya hussaini ya saka a mota zuwa shagamu, dana isa garin shagamu a tasha na hau acaba zuwa gidanmu, ban manta hanya ba. Da yawan 'yan gidanmu basu shaida ni ba sai daga baya suka gane ni, sunga na girma nayi kyau. Duk da rashin wadatar da muke ciki a kano sai naga na fisu kyawun gani, cikakkiyar lafiya da gogewa. Na zagaya dangi na kusa dana nesa har sai da naji kafafuwana zasu gutsire saboda yawansu. Na ziyarci gidan kanwata dake agege a lagos anan take aure, rayuwarta abin tausayi, gida ne irin na haya mai dauke da dakuna fiye da ashirin, yare kala kala kamar hausawa, yarbawa, igbo, da wasu yaruka daban daban. Bandaki daya ne kacal, tunda asubahi ake fara layin shiga bandaki. Mijinta iliyasu shima dan shagamu ne amma a lagos yake facin taya, ita kadai ce sana'arsa. 'Ya'yansu biyu a lokacin. Saboda tausayin halinda na same ta kusan dukka kayana na sakawa na bata kyauta, sannan na hada mata mayafai, sarkokina, takalmana, guda dai dai na rarrage. Duk kudaden dana samu na bata dukka kudin mota na komawa ta kano kadai na ware. Muka sha kuka tare da nazo tafiya, kukan da muke na tunawa da iyayenmu ne da kuma kukan rabuwa, don munsan zamu dade kafin mu sake haduwa. Na dawo kano jakata kwalam babu komai duk na rabar da kyana kuma da masu kyan na tafi dasu. Tsummokaran, tsofaffin, yagaggun kadai na bari a gida. Haka nazo na dinga karancin kaya duk sun ragargaje dan haka na daina zuwa taron biki ko gidan kawayena. Abida tayi ta min fada tace nayi garaje ai ba'ayin haka tun da nasan ban ajiye wasu ba a lufge kuma bani da mai dinka min wasu ai bai kamata in rabar ba. Idan fita ta kama ni dole sai dai in ari kayan abida in saka inje, ina dawowa in cire mata. Abinka da cakudi, zaman saka ido, kowa yana kula da shige da ficenka. Gulmammaki iri iri bayan zumde da yafice zaka ga anayi mana, abin ya kai har su dinga kiran 'ya 'yan abida suna bugun cikinsu suna tambayarsu wai ina kayana suka ga ina arar na abida? Irin wannan gutsiri da tsomar sai da ta wuce kan matan gida ta koma wajen mazansu, su kuma suka tseguntawa yayana hussaini, suka ce masa bai dace in dinga arar kayan abida ina fita kofar gida ina tsayawa da samari ba, ina yawo da kawayena a gari. Idan ba an lura ba in a duhune sai a zaci abida ta fara bin maza. Sukayi ta zuba masa bayanan da dole hankalinsa yayi matukar tashi, ransa yayi mummunan baci. Ya shigo dakina ransa a bace ya iske ni a kwance yace min in kira abida itama ta shigo nan dakin yana da magana da ita. Mukazo muka durkusa a gabansa muna karkarwa saboda yadda muka ga ransa a bace gashi mutum ne mai zafin zuciya. Ya umarci abida ta fada masa gaskiya kada ta kuskura tayi masa karya akan abinda zai tambayeta, haka nima ya gargadeni kafin ya yi mana tambayoyin. Muka yi masa alkawarin zamu fada gaskiya, ba zamuti karya ba. Cike da fargaba mai tsanani muke sauraron abinda zai fada mana. Ya cewa abida da gaske ne aisha farida tana aron kayanki ta saka ta fita yawo a gari? Sai abida ta dafe kirji tace Innalillahi wainna ilaihir rajiun! Ya daka mata tsawa mai firgitarwa yace baki bani amsa ba. Nan da nan ta fara hawaye, jikinta na karkarwa tace eh haka ne. Sai ya kai mata mari har sai da ta fadi kasa, ya fada cikin fushi yace to ta hada kayanta ta tafi gidansu. Na rushe da kuka na dinga rokarsa ya yafe mata ba laifinta bane nice na tambaye ta. Nima din ya yafe min na daina daga yau. Sai ya rufe ni da duka yana duma, yana tattaka ni da kafa tamkar zai kashe ni. Munafukan matan gidan ne suka zo suka kwace ni dakyar, ransa yayi matukar baci sai fada yake yana zaginmu wai sai mun harhada kayanmu mun bar masa gidansa. Ana bashi hakuri tamkar zuga shi akeyi dakyar ya haukra ya kyale mu amma tun daga lokacin baya raga mana, komai mukayi sai ya hantare mu, sai harara koda yaushe. Sai na daina fita koina , koda yaushe ina fama da dinkin yaga da zare da allura. Abida ta iske mijinta a dakinsu ta ajiye masa abinci sannan ta durkusa ta gaishe shi. Ya amsa dakyar cikim fushi, bata damu ba ta zauna a kusa dashi ta dauko muhuci ta fara yi masa firfita. Sai yayi mata tsawa yace ta bari baya so, ta tashi ta fita ta bashi waje. Cikin lallausar murya tana zubar da hawaye tace ka yafe mana laifukan da muka maka, munyi kuskure, fushin da kake yi damu ya hanamu sukuni, bama jin dadin rayuwarmu, rayuwa tayi mana kunci. Dan ban fada maka bane halin da ake ciki kada ranka ya baci, ashe dana fada maka ma zaifi sauki. Aisha farida ce ta rabar da kayan sakwarta kakaf a shagamu saboda tausaya musu da tayi, ta gansu cikin tsumma, shine ta dawo bata da kaya sai yagaggu. Dan haka bata iya fita wajen kawayenta shine nake bata aron kayana ta saka tana dawowa take cirewa, bansan abinda 'yan gulma suka fada maka ba har ya jawo ranka ya baci ka dauki mataki cikin fushi. Sai yayi shiru yana sauraronta can yace ai duk laifinki ne, meyasa ba zaki fada min halin da ake ciki a cikin gidana ba har sai da wasu suka fada min a waje? Kinsan irin zaman da mukeyi da 'yan gidannan, zaman saka ido ne, duk shige da ficen mu akan idonsu. Ashe gaba daya lungunnan gulmar ku ake yi shiyasa raina ya baci. A take ya bata naira dubu biyu yace ta bani inje in sayo atamfofi guda biyu 'yan naira dari takwas takwas inyi dinkin dari bibbiyu. Abida mace mai hakuri da tsananin wayo, ta iya zama da mijinta duk zafin zuciyarsa, tabbas macen da bata da hakuri da wayo ba zata iya zama dashi ba, sai gashi da kansa yayi nadamar aninda yayi mana, sai yaji kunya yazo yana lallaba mu. DUK KYAN TAKALMI 5 Saurayina guda daya nake kulawa mai suna musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan mu tare, yana sona sosai nima haka saboda yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu auren gida, shi kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a shekara. Musbahi ma yaji labarin duka dana sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi guda daya da atamfa ya hada min da naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada in daina boye masa sirrina saboda yadda yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da addu'a Allah Ya karkato da zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya fito naci credit takwas, geography ne kadai naci pass shima dan a ranar da muka yi jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan ya sami kudi zai saya min form din jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin mota da kudin sayan handout, gashi dole sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk wadannan sabida dan abinda yake samu ba mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da yawa suna samun kudi a business center yake aiki, suna typing a computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to zai samo min management in fara, nan ma nace bana so nafi son inyi schl of nursing saboda ba ruwana da neman kayan sakawa, suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da shawararmu kuma yaji dadi musamman da musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi masa sallama da yayana hussaini ya kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya ta malam aminu kano dake unguwar court road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka karatu na yi tayi haikan, ban taba samun matsala ba cinye jarabawata nake yi koda yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin acabana kit da kit babu canji wata rana ko purewater zan sha sai dai kawayena su saya min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna min bakin hali daga baya kuma in dinga jin kananan maganganu cewar na cika san banza kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi dare duhu, kallon kitse sukeyi wa rogo. Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk wasu manyan littattafai na karatu (text book) babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi sai yace in hakura kada inje makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abkin gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin rayuwata a wannan bangaren saboda bani da wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan amayar musu da radadin da zugin matsalolin da suke addabata. Kawata guda daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu, koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata, ni burina guda daya ne shine in gama karatuna in

Chapter 2 of 23