Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yamma akayi walima da yamma a farfajiyar gidansu farida,aka zuba kujeru da yawa da manyan dardumai.mata ne zalla da kananan yara sai amarya da ta sha alkyabba,kawaye nta suka zagayeta tana kan darduma a zaune daga gabagaba. mata guda uku ne suka yi waazi a wannan waje,dukkaninsu akan falalar bin miji suke magana.saboda yadda aazin ya ratsa zuciyoyin mata,sai kowacce jikinta yayi sanyi har da masu zubar da hawayen imani.daga karshe abida ce ta karbi lasifikata hau kujerar malamai ta dubi dandazon matan da suka taru a wajen,yawansu ya kai yadda baza su kirgu ba,yara,manya,yanmata da tsofaffi.sai tayi murmushi tayi musu sallama,sannan tayi bismillah,ta dubi aisha farida. Like · 2 · 9 April 2013 Hajara Haruna Mahmud Ta ce,nasiha zanyi miki ya ke kanwata farida game da zaman aure.na farko iani miki nasiha da ki bi mijinki domin aljannar mace tana karkashin tafin kafar mijinta.yake kanwata,ki fi shi farin ciki idan yana farin ciki,sannan idan yana bakin ciki ki fishi bakin ciki.ki kwantar masa da hankali.ya ke kanwata aisha,ki lura da lokacin cin abincinsa,domin mayunwaci mafadaci ne.duk lokacin da kika lura lokacin cin abincinsa yayi toh ki tanadar masa kafin ma ya iso.idan ya shigo gida bayan kinyi masa tara irin ta darajawa,toh ki gabatar masa da abinci ba sai yace ina abincina ba?don idan bari ma ya tambayi abinci to ransa ya baci ma kafina a kawo masa abincin.wani ma sai yaji baya shaawar abincin,sai yaji gara ya tafi hotel ya ci mai dadi,duk ranar girkinki sai yaki dawowa yaje yaci awaje. Ya ke kanwata ki lura da lokacin da mijinki yake jin bacci,ki bar shi ya kwanta ya huta saboda wadansu matan sai sanda mijinsu yake jin barci zasu tayar da shi su ce suna da magana,yayi-yayi ta bar maganar sai da safe tace wlh sai ka saurareni.daga lokacin da kike hana mijinki yayi bacci a lokacin da yake jin barcin to kina haddasa kakkaurar gaba ce wacce ba zata gushe a tsakaninki da shi ba. ya ke kanwata ki zauna a shirye ki nunawa mijinki koda yaushe kina bukatarsa.duk wani yanayi na kwarkwasa ki dinga nuna masa.duk lokacin. Da kike zaune da shi. Ki dinga shafar dukkanin sassan jikinsa yadda zai yi farin ciki. Ya ke kanwata ina horarki da yin ado ki lura da ina yake fara kallo a jikinki da zarar ya shigo cikin gida. Wani mijin fuskar matarsa yake fara kallo,wani mijin da ya shigo kirjin matarsa yake fara kallo,wani bayanta yake fara kallo. To ki nutsu ki gane inda naki yaje fara kallo. Idan fuska ce ki kula da lokacin dawowarsa kafin ya shigo sai ki gyara fuskar ki wanke ki saka hoda ki saka jagira,jan baki,eye shadow da dai sauransu yadda fuskar zata yi kyau sosai. Da ya zo sai ki yi kokarin nuna masa fuskar kina murmushi. Idan kirjin yake fara kallo to ki tanadi bra mai kyau,irin mai karfen nan mai gyara kirji. Tunda kin san kirjin yake fara kallo to ba zai so kirjin ya ragwargwabe ba. Ko bayan kin haihu sai ki bi duk hanyar da za ki bi kada ki bari ya tamule,don wasu matan su suke kwararraba kansu da zarar kin haihu sau daya yaga kin tsufa sai ya fara sha'awar ya auro wata budurwar mai kirji a cike. To amma idan kika iya kula da kanki,ba ki lalace ba ba zai tunanin neman wata ba In a gargajiyance ne akwai abunda larabawa suke yi kirjinsu ba ya tamulewa,alkamadin nan da kuka sani tana da amfani. Da zarar kin sa rananr da zaki yaye danki kamar sati uku kafin ranar da zaki yaye shi sai ki dinga yin kunun alkama da nono ko madara,madarar fulani ba yar kanti ba. Ki sha kofi daya da safe kofi daya da yamma. Bayan kin yaye yaron ma sai ki sake yin sati uku kina sha,sati 6 kenan. Sannan randa kika yaye yaron kuma sai ki saka bra wacce ta matse ki sosai to wannan zai hana shi ya zube duk da gyara ba zai yi kamar kari ba. Ya ke kanwata ki lura da wuraren da mijinki yake sa ido a jikinki in bayanki yake fara kallo to akwai bukatar ki koyi tafiya idan yace miko min buta sai ki juya kina jujjuyawa ki wuce gaba yana biye da ke kice za ki kai masa har bandaki. Ya ke kanwata kada ki yarda mijinki yaga abun ki a jikinki, ki kiyaye hancin mijinki kada ki yarda hancin sa yaji wani karni,doyi ko bashi a jikinki to duk lokacin da ya shigo dakin ki ko baby warin sai yaji kamar da warin ba zaki taba yin farashi a wajensa ba,kin zubar da ajinki a wurinsa.saboda dauda ta dade tana kashe aure sai a dauka wata aljana ce take zuwa ta raba aure nan kuwa alnakiya ce kawai. Ya ke kanwata ki kyaye kunnen mnki kada ki yarda ya ji mummunar magana daga bakinki. Ya zamanto duk abinda zai fito daga bakinki zuwa kunnen mijinki to magana ce ta girmamawa,jan hankali ko ta tayar da sha'awa. Misali da na ganka sai naji jikina ya yi wani zim don dadi (haha) yake kanwata a lokacin da mijinki yake kwance dake ki nuna tunda kike a duniya ba a taba dadada miki ba irin a wannan lokacin domin wannan zai sa kullum ya yi sha'awar kasancewa tare dake. Ya ke kanwata magana ta karshe da zan fada miki ki guji bakin kishi,kishin da zai sa ki kasa zaman lafiya da mutanen gida. To wannan kishin zai saka tsana a zuciyar mijinki,kishin da mace za ta yi shine wanda na fada a baya,ya zamanto ba ya ganin wata mace a duniya sai ke.duk abunda zaki yi ya zamanto idan yana rumfar kasuwarsa ko office ke yake tunawa.amma kishin da zaki sa mijinki,abokiyar zamanki ko makotanki cikin fitina to wannan kishi ne na lalatar zamantakewa na aure. Allah ya nuna mana ladubba na aure babu laifi mace taci abinci tare da mijinta.ta bangaren maza kuma addini ya nuna kada ango yaje dakin amaryarsa haka hannu ba komai ya nemi dan wani abu da zasu lasa kamar dan nama,lemo ko dan cincin ya tafi da shi dakin amarya. Da farko yayi mata sallama ita kuma wajibi ne ta amsa ba wai ta dinga noke-noke ba wai sai an sayi baki. To bakin dukka ya biya tunda ya biya sadaki. Bayan nan sai ya shiga dakin da farko ya kama gashin madigarta ya rike sai yayi addua yana tsaye a kanta. "Allahumma inni as'aluka min khaira ha wa khaira ma fiha wa khaira ma jabaltaha alaihi wa'auzubikha min sharriha wa sharri ma fiha wa sharri ma jabaltaha alaihi. Ma'ana "ya Allah ina rokonka alkhairin wannan amaryar tawa da alkhairin da ka halicce ta akai kuma Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrinta da sharrin da yake tare da ita da sharrin da ka halicee ta akai" saboda wata ballagazar daga ya kai hannunsa kanta sai ta buge hannun ta ce zai murde mata kai. To iyayenta basu taba fada mata ba ko malamanta. Ko da ya manta to ki cire dankwalinki ki mika masa kai,ki tuna masa idan ma bai sani ba ki fada masa yadda zai yi idan ke kin sani. Kuma ba amrya kawai ba ko da wani abu kika siya kamar gida,mota ko dabba kafin ka fara amfani da abin ka yi wannan addua. Idan dabba ce an ce ka dafa bindin kamar kaza sai ka kama bindinta ka yi wannan addua to ba za ki ga wani abun bakin ciki game da wannan dabbar ba. Haka idan sabon gida ne ya dafa saman gidan yayi wannan addu'ar in mota ya siya ya daga saman motar yayi wannan adduar. Bayan ya yi wannan adduar to sai ya zauna a kusa da ita su rungumi juna su yi godiya ga Allah da yasa suka zama halal ga junansu sannan ya gabatar da wannan dan kayan makulashen da ya shigo da shi su ci,ana ci ana hira ta sha'awa da bege. Amma an fi so kafin ciye- ciyen su fara gabatar da sallah raka'a biyu nafila,kai ne daman liman sai ka daga hannu ka yi muku addua,Allah ya raba ku da sharrace-sharac cen makiya,ya baku zuria ta gari,amarya tana cewa amin.in duk sun kammala wannan suka shiga kwanciya miji ya kusanto matarsa sai yayi wannan addu'ar yace bismillahi Allahumma jamnibnashaidan a wa jannabul shaidana ma razaktana. Ma'ana,da sunan Allah,ya Allah ka nisantar da shaidan daga garemu,kuma ka nisantar da shaidan daga abunda ka azurtamu da shi. Manzon Allah (S.A.W) ya ce idan Allah Ya azurta su da da a wannan saduwar da suka yi to babu rabon shaidan a jikin wannan dan. Ba zai iya cutar da shi a jikinsa ba ko a zuciyarsa ba. Ba ranar angonci kadai ba duk randa zaku sadu miji yayi wannan addua idan ya manta ki tuna masa. Ba amarya kawai ba,babu wacce bata karu da nasihohin abida ba. Kuka yayi mata face-face a ido kafin ta gama kamar yadda ya yiwa aisha farida. Ta tabbatar yau abida ta cika amanar da ta dauka ta rike ta tun tana karama har zuwa wannan ranar data aurar da ita,ranar da za ta damkata a hannun mijinta. Aisha farida ta taso da sauri tana kuka ta rungume abida suna ta kuka.kanwar amarya manauwara ita ma ta taso ta zo ta rungume su suna kuka.yayin da yan'uwa da sauran jama'ar dake zaune a wajen suka dinga fashewa da kuka don tausayinsu. Aisha farida ta dago ta dubi jama'ar dake wajen ta sharce hawaye. Tace" aunty abida ta yi min komai wanda uwa da uba suke yi wa yarsu. Tun ina karamata har izuwa ranar da zata raka ni gidan mijina. Alllah shi ne gatana abida ita ce jigo kuma jagorar data kaini ga samun nasarar komai da na samu a rayuwata.karatuna,zama da jama'a,farin cikina da mijin da na aura. Abida ta hana dan cikinta abu ta bani dan uwana yana hana ni abu ita ta ba ni.anti abida bata son taga damuwata,balle ta ga kukana. Ina yi mata fatn Allah ubangiji Ya saka mata da gidan aljanna,Ya raya mata 'ya'yanta Ya yi masu albarka ko bayan ranta.Allah ka bani ikon cigaba da yi mata biyayya da amfani a rayuwa duk da nasan ba zan iya biyanta ko da rabin2 abun da tayi min ba. Aisha farida ta rushe da kuka sai jama'a suka dauka gaba daya suna shi albarka suna gasgata bayanan Aisha farida,musamman yan uwansu yan shagamu.sannna aka watse daga wurin walima domin ana ta kiran sallar magriba. Bayan sallar isha'I aka sake cancada kwalliya kawayen amarya ne kawai da abokan ango babu yara babu tsofaffi. Hadaddiyar dinner ce za'a yi a royal tropicana daga can za'a wuce da amrya gidanta da yake ahmadu bello way,sai su hadu da sauran mata da tsofaffi yan rakiyar amarya a can, duk da daman wasu tunda yamma suke can suna ta jere. Dr shuraim ya kawata sabon gini a sabon gida wanda ya tsantsara shi tamkar a turai mai dauke da bangarori biyu iri daya sak. Kowanne ya kunshi dakuna uku,faluka biyu,dinning area,katafaren kicin da bandaki guda biyu. Dakuna biyu!falo daya kicin da dinning area dr shuraim ya zuba kaya gaba daya yan waje ne,carpet da labulaye da fenti duk sun yi iri daya,kalolin purple da pink. Ita kuma amarya suka zuba nasu kayan a daki daya da parlour daya ta roke shi da kyar ya yarda ya bar musu don da ya ce komai ma su bar shi. Tana gudun surutun danginsa saboda an daukaki alada,haka gara ma sai da danginta suka mata. Adashi yaya husaini yayi abida da ita kanta faridar. Yan shagamu ma sun taka rawar gani wajen hado kudade aka hada da kudin aure da sadaki aka siyo mata komai dai-dai karfinsu. Sai a yau su uwani su ummulkhair suka sake gasgata maganar abida da tace su zuba ido su ga mijin da aisha farida zata aura. Yau sun gani kuwa da idanuwansu. Tun daga gate din shiga gida zuwa farfajiyar gidan ma abar kallo ce don an kayata da shuke-shuke da tsuntsaye,liluka,swimming pool kamar ba a kano ba. Cikin gida kuwa ba ya kwatantuwa aisha ta haye a rayuwar duniya dai,yadda bangarenta yake haka bangaren kishiyarta faiza yake,bambancin kala ce kawai ita komai nata shudi ne da baki. Gidan iyayen ango aka fara wucewa da amrya,abban shureim yayi mata nasihohi akan ta zauna ta bi mijinta lafiya,nasihohin da yayi mata masu ratsa jiki ne.daga can aka zarto da ita gidanta,bangaren kishiyarta fa'iza aka wuce da ita suka iske falon nan nata a cike dankar da hadaddun mata kai kace su suka zabi kyawu da kudi sannan Allah Ya basu. Kawayenta ne da kawayen mahaifiyarta,danginta da wasu daga cikin dangin dr shureim masu bin bayanta.wasu sunyi musu faram-faram.wasu kuwa ban da hararta da kallon banza babu abinda suke yi musu,kai ka ce su aka yi ma kishiyar. Faiza kuwa na zaune ko uffan ba ta iya cewa har aka gama bayanai saboda tsananin kunar da zuciyarta ke yi mata. Dangin farida ne masu bayani har suna kiran ga 'yar su amana,farida bata da matsala tana da ladabi akwai bin na gaba ga hakuri da kawaici. Suka yi kidansu suka yi rawarsu suka fito. Hankalin aisha dai ya fara tashi taga alaamr ko faiza na da niyyar su zauna lafiya wadannan matan da suka baibayeta zasu iya zuge ta ta burkuce. Koma dai me ye ba ta damu ba ba abun da ya kawo ta ba kenan. Kuma zata yi iya kokarinta don ta cika burinta. Ita ma kanta ta ga kyawu da tsarin gidanta sai ta ji kukan dadi ya rufe ta,ta yi ta godewa Allah a zuciyarta. Babu abin da jama'a suke cewa sai addua da shi albarka da fatan nemar musu zaman lafiya.Allah ya sa gidanta ne sai dai mutuwa ta raba. Sai kuka ya sake kece mata a lokacin da ta ga duk sun watse an barta ita kadai,fiye da awa biyu sannan abokan ango suka rako shi. Bayan su dr lukman sun gama yi masu tsiya da barkwanci suka tafi suka barsu. Aisha ta iske angonta mai ilimin addini ya aiwatarda duk addu'o'I da nafilfilin daya kamata ango ya yi shi da amaryarsa a daren farko. Ya cika da tsananin farin ciki mai dimbin yawa,so da yarda ya karu akan amaryarsa a lokacin da ya same ta cikakiyar budurwa wacce ta kare kanta daga wasu mazan kafin ta yi aure. KYAN TAKALMI 3* 14 Kuskuren da wasu yan matan zamanin nan ke tafkawa kenan a rayuwa,daga inda suke fara jawo tsana,zargi,ras hin yarda har karshen auren,kuma babu inda auren yake zuwa ake rabuwa idan suka bari wani da namiji ya fara saninsu a waje. Don haka dole 'yan mata su yi yaki da zuciyoyinsu su yi taka tsan-tsan da mayaudaran samarin zamani ko da kuwa zasu aure su ne to a guji zina har sai bayan an daura aure. Allah yasa mu dace. Satin ango guda a dakin amaryarsa kamar yadda shari'a ta tanada.sati guda nan da yayi ya fiye masa shekaru hudun da yayi da aurensa a baya,don ya sami nishadi. Lallausan lafazai,ladabi da girmamawa bayan abinci masu dadi daga wajen amaryarsa. Ya yi wa Allah godiya da ya sami farida a matsayin matarsa. Ya kudiri niyyar cure ta ba zai bari ta subuce masa ba a rayuwarsa. Sai yaji bambarakwai da ya koma bangaren fa'iza saboda rayuwar hutu ta iya.sai sha biyun rana take tashi daga bacci. Kafin ma ayi maganar abun karin kumallo kuma ba ita zata yi ba.kofa zata budewa masu aiki su shigo gidan daga can bangarensu.kuku ya shiga kicin,mai shara da wanke- wanke da goge-goge ta fara.wanka kawai zata yi ta ci ado da riga da wando ta zauna a falo tana game ko kallo. Anci sa'a dai tana sallah da zarar lokaci ya yi sai ta tashi,bayan wannan bata san a yi wa miji wahala ba. Da zarar ya bata mata rai zaka ji tana ce masa 'you are very stupid' su a can karamar kalma ce wannan dan mace ta furtawa miji. Sabanin abin da ya ga farida na yi. Tunda asuba take tashi ta shiga hidimar miji da kalkale gida,ta ce ba ta bukatar masu aiki.ko cokali zata ba shi sai ta durkusa har kasa,haka idan ya kira ta. Sai yake jin kansa yana fasuwa tamkar ya zama sarki,sarki da ake girmama shi a fadarsa. Hutu ya dauka daga wajen aikinsa yayin da ya sa farida ta rubuta takardar barin aiki saboda ba ya bukatar ta yi ta wahala saboda dan albashi. Ya yi mata alkawarin zai bata babban aiki da zarar sun kammala ginin katafaren asibitin da suke ginawa shi da mahaifinsa a zoo road. Shi dai ba zai bar aminu kano ba zai dinga shiga lokaci2 amma zai fi ba wa asibitinsu muhimmanci. Kafin nan faiza ta kammala karatunta ta dawo gaba daya ita ma sai ya sakata a asibitin a bangaren data karanta wato acct section. Watanni biyu faiza tayi tare da farida kafin lokacin jarabawarta yayi don sun kusa fara jarabawar karshe. Shureim yayi kokarin samarwa aisha visar london,kamr ta sa har ta tsawon shekaru biyar duk sanda suke son shiga sai si shiga kawai. Don haka shuraim,farida da faiza tare zasu tafi su yi zaman wata biyu har sai ta kare su kauro gaba daya. Takaici ya cikawa faiza zuciya don bata so ba shuraim yace zai taho da farida,da ta so su tafi su biyu abar ta saboda a fara zame mata barazana wajen dauke zuciyar mijinta. A cikin watannin nan biyu data yi Aisha ta gama da mijinta,ta gama da iyayensa,ta gama da danginsa kowa yana sonta saboda da'arta,kyauta, ladabi,iya karbar baki dss. Har wasu na tunanin ko da wani baki. Asiri ta shigo ta asirce gida gaba daya, yayin da masu hankali suka lura tsabar kirkinta ne da iya zama da mutane ya jawo mata duk wannan. Abida tayi mata nasihohi masu ratsa jiki a lokacin da ta je ta yi mata sallama zasu tafi london su zauna har tsahon wata biyu. Aisha farida tayi mata alkawarin yin amfani da duk abunda take fada mata,kudi mai dimbin yawa ta tulewa abida da mijinta a gabansu har sai da suka tsorata da ganinsa suka tambaye ta in da ta samu. Ta shaida musu shureim ne yake bata kyauta wani ragowar na cefane ne don kudi mai yawa yake ba su kullum har ya fi karfin na cefanen. Sannan mahaifin shureim ya ba su kudi(dollars) mai yawa da zasu yi wannan tafiyar kadan ta dauka ta canza musu sauran. Ta umarce su da su cika su sayi fili a unguwa mai kyau a hankali zata gina masu. Kafin ta tafi sai da ta turawa kanwarta munawwara kudi dubu hamsin ta fara yin jari kafin ta dawo. Wannan shine karo na farko da aisha ta fara hawa jirgi,suka hay daga bab zuwa lagos daga can suka hau zuwa london. A katafaren gidan mahaifin shureim suka sauka sai dai su kaiwa mahaifiyar faiza ziyara.babu irin kallon banza da wulakancin da yan'uwan faiza basa yi mata idan taje gidan,har shuraim ya fara jin haushi ya fara kin son ya kaita,ita kuwa sai tayi ta rokonsa sai sun je tare saboda tasan kishi ne kawai ke damunsu. Da suka zauna da ita sai suka fara gane halin aisha tana da kirki suka fara sakar mata fuska,haka baby yar gidan faiza ta shaku da ita sosai koda yaushe suna tare duk inda zasu je. Aisha tayi kallon duniya da abunda ke cikinta kyau da tsari a garin london ba'acewa komai. Sun zagaya koina a birnin har sun shiga kasashen da suke makwabtaka dasu don bude ido sunyi siyayya sun shakata su dukka ukun. Watanninsu biyu a london faiza ta gama zana jarabawarta ta karshe ta kammala degree,sannan suka dinguma suka wuce saudiyya,ya zo daidai da lokacin aikin hajji suka sauke faralli,duk da su shureim ba hajjinsu ta farko ba ce.farida ce ta farko. Ta nutsu ta yi hajjinta yadda Allah yace,sannan ta yi addu'oin nemam zaman lafiya da kwanciyar hankali a aurenta,da rayuwarta ta duniya da lahira gaba daya. Tayi wa Allah godiya da ya bata wanda take so a duniya shi ma yana sonta kuma yana kula da ita.suka dawo gida kano aka bude sabuwar rayuwa zama ne na din3. Aka samarwa baby makaranta mai kyau a akno ta shiga. Bayan an kammala ginin asibitin aka saka masa suna imran memorial hospital,ya samarwa kowacce a cikinsu ofishinta a cikin asibitin da albashi mai tsoka. DUK KYAN TAKALMI 3* 15 Af mai kula da dukkan nurses da leburorin asibitin, yayin da fa'iza ce mai kula da duk kudin da yake shigowa asibitin, abban shuraim shine mai kula da duk likitocin da suke asibitin, shima yana zama ya kula da masu matsalar fata kudine sosai ake biy kafin a ganshi. Dr lukman yana zama a asibiti duk ranar litinin da laraba, dr dayyabu yana zuwa duk ranar alhamis da yamma. dr janan mu'azzam likitar mata (gynae) duk ranar juma'a sda asabar da yamma. Dr muhd lktr tiyata yana zuwa duk ranar talata da laraba.dr ruqayya lktr yara tana zuwa ranar lahadi da juma'a da yamma bayan likita daban daban da suke asibitin na dindindin. barr. mu'azzam shine babban lauyan asibitin shima da ofishinsa a ciki don haka duk wani mai isa da kudi da mulki a kano koma ince a kasan nan ya bude file a asibitin nan saboda iya aiki tsafta da tsari. makudan kudi suke samu a kowacce rana wanda yake isarsu su biya duk wani ma'aikaci hakkinsa dakuma karo kayan aiki daga kasar waje. bayan shekara 1 dr.s ya dauki nauyin karatun AF don ta karo ilimi abangaren nurse, tayi amfani da takardunta suka bata shekara 1 n half zata sami shaidar degree akan nursin.Hutu kawai take zuwa nigeria kuma da albashinta take zuwa bayan kudin abinci da shuraim yake aika mata.kan ka ce kwabo AF ta rikide gaba daya ta zama yar gayun gaske, haka kyakkyawa har kamar sai an wanke hannukafin a taba ta. haka naira da pounds sun zauna mata, tuni ta kaftarawa su yaya hussaini gida mai tsananin kyau a unguwar jan bulo, ta siya musu motar hawa. ta canza masa aiki ta samar mas a asibitinsu a matsayinsa na mai kula da masu gadin asibitin suma da ofishinsu. kan ka ce kwabo rayuwar hussaini ta canza dashi da iyalansa tayi kyau, ya saka 'ya'yansa a makaranta mai tsada, shima kansa da abida har suna iya taimakon danginsu na shagamu ba sai sun jira AF ta aiko musu ba. Allah bai bawa AF haihuwa da wuriba har sai da ta kammala karatunta ta dawo gida, sannan ta samu ciki don a lokaci faiza ta sake haihuwar mace mai suna fadila har ta yayeta. santalelen jariri AF ta haifa mai kama da shuraim aka saka masa suna imran, sunan mahaifin shuraim. yadda abba yake ji da imran kai kace bai taba yin jika ba a duniya sai a kansa. wannan kauna ta samo asaline da kaunar da yakeyima uwar dan wato AF a sanadiyyar kula da girmamawan da take masa. idan kaji abba yayi kukan yunwa tabbata AF bata kasan don da tananan gida ko office xata aiko masa da abinci kala kala kamar kunun gyada, tsamiya, kanwa, dalayi da sauransu. idan a bangaren abincine dambu, danwake, kwadon zogale, rama, masa, sinasir, wainar 'yar tsala, farfesun kaza ko naman rago amma dahuwardadawa na gargajiya shi yafiso. haka take yiwa mahaifiyarsa hidimomi na dafe dafe da ladabi da biyayya. komai takeso kan tace tayi har tayi mata, don haka suke son AF ba don faiza taji haushi ba sai don bazasu iya boyewa ba. ita kanta faiza baza ta iya cewa AF tayi mata laifi ba sai dai kawai tayi kishi da ita don ta aure mat miji,amma babu wata kyautatawa da girmamawa da bata yi mata ita da 'ya'yanta. a dole Faiza ta fara canzawa tana kwaikwayon wasu abubuwanda AF keyi duK da bazata iya yin duka don bata saba da wahala ba. yau falon AFa cike yake da kawayenta kai kace hada baki sukayi a rana daya suka kawo mata ziyara har su hudu kowacce kuma da ban tazo. hidima kawai AF take tayi masu da kayan abinci, lemo da kayan marmari kalakala. maimuna kanwar abidace ke zama a gidan tana taimakonta da hidimomin gida kuma take rike mata yaro. suka jera musu kayan dadi kalakala babu wacce bata cika tumbinta ba a cikinsu har suka bari. bayan ciki ya dauka sai murya ta washe sannan falo ya hautsine da hira. hoton shuraim da AF khadijah sani isma'il ta kafawa idanu tayi ta kallo,can tayi ajiar hrt tace "ikon allah ashe dr.s mijinkine, mukayi ta wahalar da kanmu a kansa? maryam ahmad tayi ajiyar hrt ta sake rungume danta tana jijjigawa tace " matar mutum kabarinsa kana taka allah na tasaa.gashi nima na auri miji mai sona ina jin dadin zama dashi. rakiya musa tace, "nifa da gani nayi kamarAF ta tsani dr.s basa shiri kwata kwata." ummi yasar tace" ai ni yau takanas zuwa nayi in dauki darrussa akan zamantakewar aure. yanzu yasar ya dan fara yabawa da hankalina shiyasa ya mayar dani gidansa sai dai kash! har yanzu kishiyata surayya ta fini fada a wajensa duk da haka dai muna zaune lfy da ita da surukata da facalata. yanxu so nake in samu in sake shiga hrt dinsa ba da neman gudunmawa daga bokaye ba kamar yadda nayi imanin bakya bin bokaye amma kika sami shuraim. kin zama abar kwatance a cikin mata. kece babbar malamata wacce tayi min silar canza rayuwata daga gurbatacciyar hanya zuwa hanya madaidaiciya. ada na sha wuya a sanadiya bacewar basira na sabawa mahaliccina" A.f tayi tagumi tana kallonsu 1by1 har suka gama maganarsu. murmushi kawai takeyi yayin da dadi ya kamata tana farinciki da suka gane komai. ta gyara zama tace "nagodewa Allah daya ganar daku, nadode da kyautar da Allah yayi min a duniya wacce zata zamemin hanyar shiga aljannah a lahira. dan daga lokacin da mace tayi dace da samun miji ngari addininta ma ya gyaru. mace dakinta guda2 ne gidan mijinta sai kuma na2 kabarinta, na shiga gidan mijina ba fita inshaAllah sai kuma kabarina ne ya rage nabi ta hanyar data dace na auri masoyina da nake yimasa soyayya saboda Allah, narike kissar matar nan data debo nonon 'bauna ina lallashinsa muna zaune lafiya sannan na rike nasihohin nan guda goma wanda Abida tayimin a ranar walimar aurena wacce uwa ya kamata tayiwa 'yarta a ranar da za'a kaita gidan miji. na haddace su a kwakwalwata kuma ina yin amfani dasu ina ganin falalarsu. a yau shureim baya kallon wata mace a duniya sai ni AF, baya son ya jiyo muryar kowacce mace sai tawa, bashi da wani tunani sai nawa kuma babu boka ba mallamai sai tsabar kyautatawa shima kuma bashi da buri a duniya irin ya kyautata min. wannan kishin da mata sukeyi da kishiyoyinsu baya gabana bantaba saka mata ido ba inga abunda takeyi balle inji haushinta haka bani da burin in koreta, burina kadai in zauna da mijina lafiya.shureim yana da adalci a tsakaninmu baya bambamtamu. a halin yanzu na mallaki komai a duniya daidai gwargwado, motocinmu na hawa na zamani guda bibbyu babu ta kasa da million4 suturuna masu tsadar gaske, mayukan shafawa da kayan kwalliya masu tsada (designers), abinci sai wanda na zaba zanci.shureim baya dannewa iyalansa hakkinsu tsakanina dashi sai addu'ar Alkhairi da fatan yazi gaba da samun budi a rayuwarsa ta duniya da lahira.yayimin komai sannan yayiwa 'yanuwana dan yanzu dangina 'yan shagamu sunyi sallama da wannan dankararren talauci da muka sha fama. na dauki nauyin 'yan sakandire da yawa harsu gama,na dauki nauyin masu shiga jami,oi DUK KYAN TAKALMI 3* 16 na dauki nauyin taimakawa iyaye da suka tashi aurar da 'yan mata da kayan daki ko samarin da suke hada lefe.kanwata Munauwara ta rabu da

Chapter 21 of 23