Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron kazata da cinkosa, babban burina ba wuce inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan karami mun cunkushe gashi su dukka yaran abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba katifar sai zarni take dan haka na hakura da katifar na bar musu. Na koma kwana akan tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike talaucina na kama kaina bana sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa lafiya muke wadanda aka kwantar dasu sakamakon wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam tana nunnana mana yadda ake aiki, domin neman karin bayani sai tace bari ta hada mu da kwararren likita wanda ya kware a bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga muma muka bita a baya da alama dakin daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai yake yi musu cikin harshen turanci kai kace baturen america ne, kalmomin kimiyyar (botanical names) da yake ta ambato yana jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa kawai na fara hangowa daga nesa sai na tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban hango jan kunne ba da farin gashi irin na turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye da bakaken kaya riga da wando (suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana matso ciki sai na fara hango gefen fusakarsa, wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a duniya wato hasken duhu (chocolate color). Ko dana sake samun daman na matso kuda dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin wadannan dara daran idanuwan ba masu tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu gashin ido da gashin gira masu yawa da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan da ake kira african American, hukuncin da na yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka hadu suka same shi bakar fata da farar fata. Saurayina guda daya nake kulawa mai suna musbahu, lungun mu daya dashi kowa yasan mu tare, yana sona sosai nima haka saboda yana kula dani. Tun sanda na gama sakandire yake so ya aiko gidanmu ayi zancen aure sai aka sami matsala daga gidansu, mahaifiyarsa bata sona 'yar kanwarta take so ayi musu auren gida, shi kuma ni yake so ya aura.mahaifiyarsa ta tsane ni haka kawai, ko a hanya na gaishe ta bata amsawa shiyasa na daina zuwa gidansu don da ina zuwa wajen kanwarsa jamila kawata ce ajinmu daya a shekara. Musbahu ma yaji labarin duka dana sha saboda aron kaya, sai naga ya siyo min leshi guda daya da atamfa ya hada min da naira dari biyar kudin dinki, sannan yayi min fada in daina boye masa sirrina saboda yadda yake sona a ransa, matsalata ai matsalarsa ce. Yace duk sanda na shiga matsala in fada masa ko bashi da kudi zai ciyo bashi yayi min komai in dai baifi karfinsa ba. Yaci gaba da bani hakuri akan halinda yake ciki shi da mahaifiyarsa, ita ta hana shi ya turo gidanmu zancen aurenmu. Ya umarce ni da mu dage da addu'a Allah Ya karkato da zuciyar mahaifiyarsa kaina taji tana sona ayi auren dani. Sakamakon jarabawar mu na sakandire ya fito naci credit takwas, geography ne kadai naci pass shima dan a ranar da muka yi jarabawar bani da lafiya. Sai misbahu yace idan ya sami kudi zai saya min form din jamb in wuce jami'a. Sai nace ba zan iya karatu a jami'a ba saboda 'ya'yan masu kudi ne sukeyi, bani da mai bani kudin mota da kudin sayan handout, gashi dole sai an saka sutura masu kyau. Sai shima ya gasgata zancena yaga shima bashi da halin da zai dauki nauyin duk wadannan sabida dan abinda yake samu ba mai yawa bane. Duk da wasu lokutan sukan sami ayyuka da yawa suna samun kudi a business center yake aiki, suna typing a computer, suyi kalandu ko meme. Sai yace to zai samo min management in fara, nan ma nace bana so nafi son inyi schl of nursing saboda ba ruwana da neman kayan sakawa, suna da uniform, sai yace shikenan zai binciko yaji duk yadda akeyi a shiga amma in fara jin ra'ayin yayana. Yayana ya amince da shawararmu kuma yaji dadi musamman da musbahu yazo har kofar gidanmu ya sa akayi masa sallama da yayana hussaini ya kara yi masa bayani. Yace zai taimaka min da wata dawainiyar kudin makarnatar sai ya amince yayi masa godiya. Musbahu da yayana ne suka hada gwiwa suka bani duk kudaden da ake bukata na shiga makarantar koyar aikin jinya ta malam aminu kano dake unguwar court road. Karatun shekara uku ne a shekara ta uku ne muke zuwa asibiti koyar aiki don haka karatu na yi tayi haikan, ban taba samun matsala ba cinye jarabawata nake yi koda yaushe. A asibitin malam aminu kano ake horar damu koyar aiki (attachment). Ina zuwa kkullum daga unguwarmu sharifai zuwa court rd akan acaba saboda idan nace zan hau bus zan bata lokacina zanyi in makara. Kudin acabana kit da kit babu canji wata rana ko purewater zan sha sai dai kawayena su saya min. Duk da idan za'a je sayan abinci ko shan lemo sai in gudu bana binsu saboda kullum sai dai su saya min, ni kuma na fara jin kunya sun gane bani dashi. Kawata khadija sani ismail kadai wacce bata gajiya da taimakona kuma duk sanda tace muje cin abinci naki zuwa ko na sulale na gudu sai ranta ya baci, har tayi fushi dani. Sai inyi tayi mata bayanan karya in kirkiro uzurin dana je nayi ba guduwa nayi ba sai ta ki yadda tasan karya nakeyi. Ba ita nake ji ba, sauran kawayenmu nakeji don suna nuna min bakin hali daga baya kuma in dinga jin kananan maganganu cewar na cika san banza kullum bana fitar da kudina ina sayawa kaina abu balle in sayawa wani, sai dai ni kullum a saya min. Rashin sani yafi dare duhu, KALLON KITSE sukeyi wa ROGO. Hakika ni mai yawan tsafta ce in kula da fararen kayan makaranta ta, kullum tsaf dani, ina kalkale jikina tas a wanke ga karin guga. Gani nafi duk 'yan ajin mu kokari yawanci ni nake basu amsa. Khadija bazata iya rabuwa dani ba dan bata da kokari sai dai gata, tunda iyayenta suna da hali. Duk wasu manyan littattafai na karatu (text book) babanta yana saya mata duk tsadarsu, sai nafi morarsu don ni ce mai hazakar karatun ba ita ba. Da taimakon Allah da taimakon khadija sani nake cin jarabawa dan ba zan iya sayan littattafan nan masu tsada ba. Badan Allah Ya sa na iya kitos ba ina yiwa makwabta, da wata rana ma ba zanje makaranta ba saboda duk ranar da yaya hussaini ya tashi bashi da kudi sai yace in hakura kada inje makaranatar randa ya samu naje. Ni kuma bana so inyi fashi, da kudin kitson nake harhadawa in tafi duk da kitso a unguwar bashi da tsada, kan manya naira talatin ko arba'in, na yara kuwa naira ashirin ko goma ne. Ban taba fadawawa kawayena sirrina ba, duk da yawan kawayen da nake dasu a ajinmu mata da maza, sai dai ayi hayaniya wasa da dariya a watse, ina taka tsantsan da harshena a koda yaushe. Babu wanda a cikinus ya san yadda gidanmu yake, basu taba zaton haka nake rayuwa ba, sai dai sun fahimci wani abu akwai wasu matsaloli wanda ba zasu boyu ba. Suyi ta zargi da sake sakensu a ransu su kadai, ni dai bazasu ji daga bakina ba kuma ba zasu iya tara ta su tambaye ni ba. Ni daman bana zuwa gidan kowa balle azo gidanmu, mu hadu a abakin gate ne mu rabu idan an tashi. Bana jin dadin rayuwata a wannan bangaren saboda bani da wata takamaimiyar kawa ko masoyin da zan amayar musu da radadin da zugin matsalolin da suke addabata. Kawata guda daya, itace aminiyata, yayata, masoyiyata wato matar yayana abida. Muna zama ni da ita mu raba dare ko mu yini muna tattauna matsalolinmu, koda yaushe ina samun nutsuwa da kwarin gwiwa idan abida ta bani hakuri akan talaucin da na tsinci kaina da shawarwari, sai inji sanyi a raina, tawakkali ya kama zuciyata sai inji ta tuno min da nasihohin da mahaifina yayi min a baya. Idan nayi haka sai in dawo da walwalata, ni burina guda daya ne shine in gama karatuna in fara aiki in taimaki kaina, in taimaki 'yan gidanmu. Babbar matsalar ma da tafi damuna shine zaman cakudi a gidanmu, cikin tsagoron kazanta da cinkoso, babban burina ba wuce inga mun bar gidan nan da umguwar mu canja gida ko haya ce dai mu kama gidan da muke mu kadai. Dakina daya da yara, ga dakin dan karami mun cunkushe gashi su dukka yaran abida fitsarin kwance sukeyi dan haka sun ruba katifar sai zarni take dan haka na hakura da katifar na bar musu. Na koma kwana akan tabarma, idan na tashi da safe sai inyi salla akai in nada in jingine a lungu sai zan sake yin wani sallar sannan in shimfida. Har yanzu kayana a jakar bagco yake a gefen shimfidata, rayuwata ba irin na 'yan matan 'yan boko bace, tamkar a kauye nake ba'a birni ba. Ko inyi tunanin shiga hanyar banza, ban taba sha'awar makalewa gidan kawaye ba ko arar kayan kawa, na rike talaucina na kama kaina bana sha''awar kayan wani. Daga makaranta sai gida, a gidan ma nafi zama a daki kullum ina karatu. Idan kaga na fito aiki nazo taya abida, wankan 'ya'yanta , tsarkinsu ko aikin girki. Sai 'yan gidanmu da sauran 'yan unguwa suka shiga yimin shaidar girman kai ne dani dan ni 'yar boko ce, basa ganin fara'ar da nake yi musu. Kullum ina gaishe su ko basu ganni ba, tabbas mutum ba'a iya iya masa, saboda dan Adam ya kasance mai butulci ne. BABI NA UKU Wata rana ranar litinin da misalin karfe daya na rana muna cikin a sibiti, a bangaren marasa lafiya muke wadanda aka kwantar dasu sakamakon wasu kurajen da suka feso a jikinsu. Muna biye da ma'aikaciyar jinya matron maryam tana nunnana mana yadda ake aiki, domin neman karin bayani sai tace bari ta hada mu da kwararren likita wanda ya kware a bangaren fata. Ta tura wani daki ta shiga muma muka bita a baya da alama dakin daukan darussa ne sabida naga kujeru ne zalla da allo makale a jikin bangon. Kamar yadda naji ta ambaci sunansa, dr shureim imran. Mun iske shi tsaye a tsakiyar ajin tare da wasu daliban likitoci guda 3 maza biyu, mace daya da alama sunzo sunyi masa tambayoyi ne akan wasu abubuwan da basu gane ba. Bayanai yake yi musu cikin harshen turanci kai kace baturen america ne, kalmomin kimiyyar (botanical names) da yake ta ambato yana jerowa layi layi da ka ba tare da yana duba littafi ba, kai kace shine ya lakaba musu sunan don ya haddace. Muna sake kutsawa cikin ofishin yayin da zazzakar muryarsa, daddada take sake shiga kunnuwanmu sai duk muka kagu mu isa gabansa don mu kalli fuskar mai muryan nan daddada. Kasancewar kofar ta cushe muna shiga don muna da yawa, ga dalibai likitoci nan suna kokarin fitowa sun gama daukar darasin. Kowa ya kagu yayi ido hudu da mai daddadar muryar nan, keyarsa kawai na fara hangowa daga nesa sai na tabbatar bakar fata ne dan uwana saboda ban hango jan kunne ba da farin gashi irin na turawa ba. Bakin gashi ne tattaura irin namu na hausawa, sai dai gashin a gyare yake yana shekin mai kuma ya kwanto lambar zuwa karshen keyarsa. Kansu babu hula, yana sanye da bakaken kaya riga da wando (suit), farar riga mai dogon hannu daga ciki, ya daure wuyansa da jan kyalle wato necktie. Dana matso ciki sai na fara hango gefen fuskarsa, wata lafiyayyiyar fata na fara hangowa mai dauke da launi mai tsananin kyau. Irin kalar da take tsada a duniya wato hasken duhu (chocolate color). Ko dana sake samun daman na matso kusa dashi sai ga gefen fuskarsa tar ina gani wato idonsa daya da gefen hancinsa, sai kawai naji wata mummunar fadywar gaba ta far min ni ma bansan dalili ba har wadanda ke kusa dani zasu iya jiyo karar ajiyar zuciya danayi. Tunda nake a rayuwata ban ta ba ganin irin wadannan dara daran idanuwan ba masu tsananin haske daga ciki, da bakar kwayar ido mai tsananin baki, aka zagaye idon da wasu gashin ido da gashin gira masu yawa da tsananin baki, ya gyara su sunyi kira mai kyau suna sheki. A nutse ya waiwayo da kyakkyawar fuskarsa gaba daya ya dube mu, bani kadai ba duk wata 'ya mace da take wajen sai dataji a ranta dama ace wannan kadarar mallakarta ce. 'Yan uwansa maza ma sai da suka raya a ransu dama ace sune shi, ga kyau ga ilimi. Ashe a da dana ke hango gefen fuskarshi ban hango komai ba, kyau mai sunan kyau sai ka kalle shi gaba dayansa daga kafarsa zuwa kansa. Dogon mutum ne sosai ma kyawun sura, bashi da kiba da yawa, haka bashi da rama. Yayi kama da irin bakaken turawan nan da ake kira african American, hukuncin da na yanke masa kenan dan ko kusa baiyi kama da 'yan nigeria ba! Tabbas ruwa biyu ne suka hadu suka same shi bakar fata da farar fata. Duk da tashin hankalin da na shiga da naji bayananta sai nayi murmushin karfin hali nace subhanallah! Bai kamata kice zaki bi kowacce hanya ba gara ma kice zaki bishi da addua in da alkhairi Allah ya yi. Khadija tace bawai ina nufin zan fita daga musulunci ba akansa ba, amma fa dole saina saka malamaina sunyi min addua. Na fahimci maryam ahmed da mansura mahmud suna sonsa kin san su da bin malamai, in ban dage ba sai sun janye hankalinsa. Gaskiya tunda nake a duniya ban taba ganin Kyakkyawan bakar fata irinsa ba, ko kin taba gani? Na girgiza kai nace ban taba gani ba, amma shima yana ji da kansa dan yasan ya hadu kuma mata suna nuna masa haka. Ba kya ganin 'yan matan nan medical student suna ta kawo hare harens garshi? Khadija tace tabbas na gani, shiyasa nace sai nayi da gaske fa. Ai mu uku ne kadai muka amayar da maitarmu a waje, nasan mata da yawa sun dasa a ajin fada ne kawai basu yi ba. Kin burge ni aisha umar, sai naga kwata kwata ba ya gabanki, ko a bayan idonki muna yabonki don kina kama kanki bakya shiga rigimar da tafi karfinki. Sai kawai nayi murmushi nace a raina kallon kitse kike yiwa rogo, aini zuciyata tuni ta kunsa min abinda zuciyoyinku basu kunsa muku ba. Tabbas nasan burina da fatana akan dr shurain yafi nasu. Aisha umar kalli motar can, inji khadija yayin da ta matse 'yan yatsunna don gigicewa. Na juya da sauri, sai naga wata dankareriyar mota baka mai farin gilashi. A cikin motar kuma zankadeden mutum ne, sanye da farar riga da bakin gilashi a fuskarsa. Ya kalle mu, muma kallonsa mukayi sai ya kawar da kai ya fisgi motarsa da gudu ya nufi gate din fita. Na dubi motar har da waiwaye sannan na juyo na dubi khadija nace motar nan ta hadu, haka mutumin da yake cikin motar ma ya hadu. Wanene shi? Tace au baki gane shi bane? Dr shuraim ne likitan da muke zancensa yanzu. Dan halak yaki ambato. Sai nace kai bashi bane, ai shi bakar suit ya saka. Tace bakar ta saman ya cire, ya bar farar ta ciki. Baki shaida jan neck tie din bane? Sai nayi shiru saboda haduwarsa tafi karfin tunanina, sama ta yiwa yaro nusa ba zai iya tabawa ba sai dai ya daga ido ya hango. Sai na tuna ai Allah ne ya halicce shi wanda ya halicce ni, babu wanda yafi wani a wajensa sai wanda yafi bauta masa don haka na daina raina kaina. Na kudira a raina zan sake rikar addinina yadda zan sami babban rabo a lahira, koda kuwa ban sami wanda nake so a duniya ba. Zuciya ta fara warwarewa daga kuncin daya damke ta na son maso wani. Tun ina sauraron surutun da khadija takeyi har na daina ganewa, burina kawai in ganni a gida na shige lungun dakina. Ina hau yamutsattsiyar tabarmata in kudindina inyi ta aiyano ni tare da abin kauna ta shuraim. Ina daukar jakata sai nayi musu sallama na nufi gate din fita a sanyaye ina tafe ina tunani. Na fita waje na tsayar da acaba kamar kullum na haye ya kai ni kofar gidanmu. Tun daga zauren gidanmu nake cin karo da matan gidan suna ta hidindimunsu na saye da sayarwa da surutin da suke yini suna yi, ayi gulmar wannan, a zagi waccan, yau sai suka ganni ba kamar kullum ba. Da bayan na gaishe su sai in dan zauna ayi barkwanci sannan in wuce cikin gida, yau babu kanta da kyar nake magana, sauri kawai nake yi in shige ciki. Sunyi zaton yunwa nakeji, har suke zolayata da cewa abida ba ta nan, ba'ayi abinci ba. Na wuce abu na, na iske abida tana dafa a binci a risho. Tana ganina tayi kasake tana kallona, ta san akwai damuwa tunda bata jiyo muryata ba, bata gano murmushina ba saboda ina da yawan dariya. Ta dube ni tace aisha farida kalau kuwa, ko allura zakiyi wata mara lafiya ta kwace ta tsira miki? Nayi dariya nace haba dai ayi haka kuwa? Bana jin dadi dai. Tace Allah ya sawake, shiga daki kihuta kafin abinci ya dahu ki ci zaki murmure. Ina shiga daki na cire uniform dina sai na daura tawul na dauki kwandon wanka zan je in watsa ruwa dan inji dan sanyi a jikina saboda na kwaso rana.sai na ga abida ta shigo tana dariya tace da ni "af ashe wanka zaki yi da labari zan baki mai dadi kuma marar dadi." Na ajiye kwandon wanka na jawo hannunta muka zauna.Na ce bani in sha ai na fasa wanakan,me ya faru? Ta yi dariya tace labarin musbahu tsohon saurayinki da matarsa lubabatu zan baki daman,aure dai yaki dadi har ya yi mata saki daya dazun nan aka yi rigimar. Lungun nan ya cika da mutane mahaifiyarsa dai sai a taya ta da addua don ta cika naci,ce masa tayi idan ya sake furta kalmar saki sai ta tsine masa dole sai ya zauna da lubabatu tasan akan aisha farida yake yi mata wulaqanci kala- kala. Tayi rantsuwa tace ko bayan ranta idan ya saki lubabtu ya aure ki Allah ya isa. Kin ji wata kiyayya sabuwa ko? Na yi murmushin karfin hali nace,Allah ya kyauta,ta ma daina kokarin tsinewa danta a kaina tuntuni na yi masa sallama nace ya bi mahaifiyarsa don ya sami rahama. Ya na aiko min da kudi tun ina karba sai na daina karba daga baya idan ya aiko sai in mayar da dan aiken in ce bana so don zaman lafiya. Abida tace haka ya fi,ai gara da kika yi. Masa haka kin taimake shi. Ni na dauka ma zancen kika ji tun daga zaure da na ga kin shigo ranki a bace. Amma fa ki godewa Allah AF saboda kin samu kyakkyawon yabo a ung nan. Ba kiji. Yadda kowa yake yabonki ba,ake ta tsine mata ita kuma. Kowa ya dinga cewa me ye laifin AF har da bata so danta ya aura? Yarinya mai nutsuwa da hankali mai ilimi da fara'a tana gaishe da mutane. Ta zo ta tauyewa yaro rayuwarsa ta cusa masa dakalkalalliyar macen da ba ta da tsari. Nace au daman an sanni da yawa a ung nan haka? Abida tace "ji ki da Allah da neman magana waye bai sanki ba,musamman da kika shiga skul of nursing kina karbar haihuwa kina allura a cikin ung sai ki ji kowacce mata tana cewa wajen aisha likita zan je ta rubuta min magani. A nan dai muka tashi muka rufe hirar nan zuciyata cike da tausayin musbahu ba don mahaifiyarsa ba ta sona ba da na aure shi mun zauna mun rufawa juna asiri,in huta fadawa cikin hatsarin da nake shirin jefa kaina. Bayan na yi wanka na ci abinci sai na wartsake na shiga cikin matan gidan muna ta hira har ma na ji na fara mantawa da abunda yake damuna a zuciyata. Sai da kowa ya shiga barci dare ya fara nisawa sai tunanin Dr shureim imran yace da wa Allah ya hada ni in ba da ke ba,sai na ji gaba daya daya zuciyata ta kasa sukuni. Da zarar na rufe ido sai in ganshi tamkar a zahiri. Sai na yi ta yaki da zuciyata ina ture shi daga tunanina.kai in takaice maka a cikin satin nan ban gane kaina da kaina saboda tsananin tunaninsa. Idan na je asibiti bana walwala haka idan na dawo gida ba na jin dadin zuciyata kada ma dare ya ji labari sai ka ga idona ya wartsake garau na burma tunanin DR shureim imran. Da gaske sonsa nake,so ba da wasa ba.tun ranar kuma ban sake ganinsa ba sai dai kullum sai khadija ta yi min labarinsa.Albishir din da ta yi min shi ne ta sami lambar wayarsa amma tana tsoron kira don tana ganin zai yi mata wulaqanci. Ta shaida min ta rabawa malamai kudi ana ta ragargaza mata addu'a ta koina,a kalla ta raba musu zunzurutun kudi ya kai N25,000 so take sai an gama addua tas sannan ta kira shi dolensa ya amince. Sai na sake jin jikina ya yi sanyi na sake yi wa zuciyata fada da ta yi ta- ka tsan- tsan ta daina cusa abunda zai iya kasheta.idan da khadija. Zata lura duk sanda ta fara yi min zancen Dr shureim sai jikin yayi sanyi kuma na kan rasa amsar da zan bata ko shwara. Kallonta kawai nake tsayawa ina yi yayin da zata iya ganin hawaye yana cika min ido sai inyi sauri in mayar da shi ina tauisayinta na fi tausayin kaina domin na san zuciyata ta fi tata shiha hatsari kuma ta fini sanin yadda zata yi da kanta. Ni ko wayar ma bani da ita babu kudin saka kati balle in saka rai ko zan karbi lambar in kira inji dadi. Na zama na rasa walwala ta ko abincin kirki bana iya ci na dukufa da adduar Allah ya yaye min don sonsa ya zame min ciwo.naji duk na tsani kaina karfi da yaji nake fisge tunaninsa daga cikin zuciyata.amma abu ya ci tura sai ma karuwa yake yi. Idan naki tunaninsa karfi da yaji a ido biyu da zarar na kwanta sai nayi mafarkinsa, sai gani cikin dare ina kuka wiwi ina sallah da adduar Allah Ya yaye min, Allah Ya kawo abin da zai sa inji na tsane shi ma. Duk satittikan nan da nayi ina jinyar sonsa ko a hanya ban hadu dashi ba balle ma in ji dan sanyi a raina, ina so ina kara ganin suffarsa don in kawata tunanina domin kamanninsa suna kokarin disashe min. Ranar talata da sassafe ina dirowa daga kan acaba a kofar shiga gate din asibitin aminu kano sai na yi kicibus dashi a cikin wannan tsaleliyar motar tasa. Na waiwaya da sauri na dube shi yayin da shi ma yake dubana har da rage tafiya amma fa duban da yake yi min bana kauna bane, hararata yake yi game da nuna tsana mai yawa a bayyane. Sai yayi tsaki ya girgiza kai ya kada sitiyarin motarsa yayi wucewarsa. Sai na dankare a tsaye ni ban ciro kudin mai acaba na biya shi ba, ni banyi gaba ba balle ace mantuwa nayi. Bani kudin mana, inji zalamamman dan acba. Na ciro kudin na mika masa ya karba yana shirin ya miko min canjina naira ashirin sai na girgiza kai nace kayi min sadaka, ku taya ni addua don bani da lafiya. Sai ya tsaya yana kallona cike da tausayi yace to ko gida za a mayar dake idan ba zaki iya aikin ba? Ai komai sai da lafiya akeyi. Nayi murmushin karfin hali nace ciwona addua yake bukata ba hutu ba, ko shan magani. Sannan maganin ciwon yana cikin asibitin nan, idan na koma gida ai babu maganin a can. Yace gaskiya

Chapter 3 of 23