Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne duk wani magani yana asibiti. Allah Ya yaye miki kowanne irin ciwo ne wannan. Na amsa da amin nagode. Na juya a sanyaye ina tafiya kamar kwai ya fashe min a ciki. Ina mai matukar mamaki da takaicin kallon wulakancin da yayi min. Na kasa tantance ni kuwa laifin me nayi masa a rayuwata da ya tsane ni, yaushe ma ya taba ganina banda sau daya shima a rubibi, yaushe zai ganeni? Aisha farida umar, karaf naji an kira sunana daga gefena. Nayi firgigit na juyo da sauri. Khadija sani ismail na gani ta tsaya da motarta hience 2008 ta sauke gilashin wundonta kasa, na tsallako inda take na bude gaban motar na shiga. Ina kokarin gaishe ta sai ta katse ni cikin murna take magana tace albishirinki? Na kira Dr shuraim imran jiya ya dauka, sai dai mun fara magana yace in bashi bane wanda nake newa wrong number ce, ya katse wayar. Sai na tura masa sako nace ni dalibarsa ce , na kira in gaishe shi. Kinga amsar daya bani. Sai ta miko min wayarta, sai hannuna ya hau kakkarwa, har sai da ta tsaya tana kallona saboda gaba daya jikina bari yake yi. Na duba na karanta sai naga ya runuta "thanks". Sai na lumshe ido don dadin ganin rubutunsa da lambarsa, naji dama nice nake yi masa waya da tura sako da ko amsar da ya bawa khadija na samu ya bani kadai na gama jin dadin rayuwata, ta isheni abin farin ciki. Na bude baki nayi magana da kyar, nace lallai kinji dadi. Tace dadi ka-n jiya ai jar da barci da munshari don samun kwanciyar hankalin dana ji. Dole in karawa malamaina kudi su sake dagewa da addua sosai. Nayi ajiyar zuciya nace ya san sunanki? Tace bai tambaye niba, ki kyale shi sai a hankali, dan wulakanci ne fa wannan da kike gani. Muka isa bangaren da muke,mun bar bangaren masu kuraje mun koma bangaren yara. Muna shiga ciki muka iske 'yan ajinmu a tsaitsaye kowannensu da dan littafinsa a hannu da biro, da alama matron ta fara bayani akan wannan yaro mai ciwon amai da gudawa. A tsaye nake ina kallon bakin yaron a hannun mahaifiyarsa yana tsala kuka, amma ban fahimci bayanan matron ba, ko kadan ban san me take cewa ba. Tunanina kawai daman ace dana ne wannan jaririn muka haifa tare da Dr shureim imran. Sai da ta gama bayani ta juya, naga an bi ta duuu a baya zuwa gadon wani yaron marar lafiya, shi kuma mai ciwon pneumonia ne, sai na ja birki na tsaya cak na ki bin su saboda kafafuwana da kwakwalwata sun gaji ba zasu iya daukar abubuwa guda biyu ba, tunanin dr shuraim imran shi yafi matsa min, gara in yi shi shi kadai, shi yafi muhimmanci a gareni don haka na juya na nufi ofishinmu inda muke zama mu huta da ajiye jakunkunan mu. Ina shiga sai naga maryam ahmad tayi kasake a zaune akan kujera tana matsa wayarta, fuskarta babu walwala. Nayi mata magana sai naji da kyar take amsa min. Na tambaya cikin damuwa maryam lafiya? Me ke damunki? Baki da lafiya ne. Ta girgiza kai tace lafiya kalau. Ni dai na dame ta da tambaya lallai sai ta fada min abin dake damunta. Ko a mafarki ban zata amsar da zata bani ba kenan. Budar bakin ta ke da wuya tace waye inba dr shureim ba? Sai naji gabana ya fadi daf! Na fada a gigice me yayi miki? Sai ta dube ni kwalla ta cika mata ido tace aisha farida na yarda dake shi yasa zan fada miki sirrina, na san kina da rike sirrin jama'a ba ataba fada miki magana kin yada ba, na san zaki bani shawarar da ta dace. Ina matukar son dr shureim imran, har zuciyata sai naga da in tsaya labe labe shi ma mutum ne kamar ni, me zai hana in tunkare shi in fada maas tunda ni bazawara ce, kunyar me zanji? Duk inda mace ta kai na kai, ina da kyauna da ilimina da arzikina, gani 'yar asali karewa ma 'yar sarauta. Dazun nan na tare shi a bakin ofis dinsa yana ganina ya bata rai na gaishe shi ya amsa da kyar, ya bude kofar ofis dinsa ya shiga sai na bi bayansa. Muna shiga sai ya daka min tsawa yace lafiya? Nace nazo in gaishe shi ne. Ya fada a fusace yace to naji sai anjima. Nace kuma ina da magana da nake tafe da ita. Sai yace fadi maganarki ki fita. Nace so nake mu saba in karbi lambarka, ka karbi tawa. Ko rufe bakina banyi ba yace bana bukatar in saba da ke, haka bana son lambarki, sai anjima. Sai ta fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda na dora hannu aka ba nace mun shiga uku, Allah Ya jikaina. Maryam ta dago cike da mamaki tace aisha farida menene? Nayi sauri na gyara zancen nace ai da kika fada min abin da yayi miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in mutu, shine nace Allah yaji kaina. Tace meye shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi. Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata. Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a wahalar min da abin kaunata. Daga nan na kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min maganin ciwon nan. DUK KYAN TAKALMI 7 Sai ta fashe da kuka ta rungumeni. Bansan sanda na dora hannu aka ba nace mun shiga uku, Allah Ya jikaina. Maryam ta dago cike da mamaki tace aisha farida menene? Nayi sauri na gyara zancen nace ai da kika fada min abin da yayi miki sai naji kama zan hadiyi zuciya in mutu, shine nace Allah yaji kaina. Tace meye shawararki? Shawarar da na ba wa kaina ita nake kokarin in bata, itace tayi hakuri ta rabu dashi, taci gaba da addua. Allah ya yaye mata sonsa ya hadata da mai sonta wanda yafi shi. Sai tace a'a ai ba isa ba, sai ya san ita yayi ma wulakanci. Ai ko zata salwantar da dukiyarta kakaf sai ta rama abinda yayi mata. Sai tayi masa asirin da sai ya kwanta a kasa ta murje shi da takalmin kafarta. Ban sake magana ba na tsaya kawai ina kallonta, yayin da naji tausayinsa ya kama ni, bana so a wahalar min da abin kaunata. Daga nan na kara cire ran mafarkin samun dr shuraim imran a rayuwata. Naci gaba da jinya ina jiran ranar ajalina domin mutuwata ce kadai zatayi min maganin ciwon nan. Abida ta lura bana cikin walwata kullum ina cikin damuwa, ta tambayeni har ta gaji na kasa fada mata wannan badakalar cutar da zuciyata ke fama da ita, babu abinda nake boyewa abida amma wannan dai ba zai fadu ba. Na gwammace a dauki gawata a dinga tunanin fuju'an na mutu babu ciwo ni da Ubangijina munsan abinda ya kashe ni. Sai na shiga tunanin ko shi yasa ya dinga hararata saboda masu irin uniform dina ne suke damunsa ya zata nice? Haka ne ma babu tantama ya dauka khadija da maryam ce ni. Bansan takamaiman ofis dinsa ba, don haka kaina tsaye na tunkari ofishin dr lukman likitan kwakwalwa dauke da file din matron maryam ta umurce ni da in kai masa. Ofis na uku tace min daga hannun dama, don haka kaina tsaye nan na kwankwasa na shiga tun kafin a bani izini, saboda saurin da nake yi don inyi in koma wajen daukan darasi. Abin da nagani a cikin ofishin shi ya firgita ni har sai da kowa ya gane na tsorata, dr shureim imran na gani a zaune a kan kujera da laptop dinsa akan table yana danne danne, maimakon mai ofis din dr lukman. Wace wannan? Ya kika koma da sauri? Wa kike nema? Tambayoyin da na jiyo ana yi min kenan daga cikin ofishin ni kuwa tuni nayi waje. Na rufo kofar a hankali na fara sanda zan juya, jikina yana rawa ina gudun wulakancinsa. Wata murya naji an kira ni, har na kai kan barandar waje. Ina juyawa naga mai gadi ce (security). Tace inje inji doctor. Hankalina ya tashi kan kace kwabo na fara gumi tamkar ana gasa ni a garwashi. Ofishin dr lukman kuwa ta nuna amma ban ga kowa a bakin kofar ba, kuma har yanzu kofar a rufe. Ni kaina ban san ayoyin da nake karantawa ba har na isa bakin kofar, na tura kofar na shiga ina mai jan dan gajeren hijabina ina rufe rabin fuskata. Ina sauraron yadda Allahi Zaiyi dani kuma. Nayi sallama na shiga amma na kasa daga ido in dube shi. Yaya kika leko kika koma? Wannan karon kuma wata sabuwar murya naji daban ba irin ta dazu ba, sai na dago ido da sauro na dube shi. Dr lukman na gani zaune yana danna laptop dinsa ba dr shureim imran bane. Sai mamaki ya rufe ni a zahiti har ya fahimci haka, na tabbatar son dr shureim yayi min yawa da har ya fara yi min gizau. Nayi murmushi na dauka ba ofishin na shigo ba shiyasa na juya. Na matso na mika masa file din yana dubawa ya girgiza kai yace me yasa matron zatayi min haka, ni ba wannan nace ta aiko min ba. To iyakacin kalmar da na fahinta kenan daga nan na daina sauraronsa saboda dr shureim imran na gani ya fito daga bandaki da alama alwala yayi don jikinsa daruwa. Kallo daya nayi masa na zazzare ido sai na sunkuyar da kai kasa yayin da jikina ya hau rawa, zuciyata ta hau tsalle tana oyoyo ga abincin da na dade ina yunwarsa. Shine ma dai yayi min kallo sau biyu ya watsar ya shige lungu ya shimfida abin sallah. Kafin ya tayar da sallah dr lukman ya tsokano shi da ci gaba da hirar da suke yi. Yace wato dr shureim ka tsani ka ga 'yan acaba kenan? Yayi dariya yace yadda naki mutuwata haka naki inga mutum ya hau acaba musamman mace ina takaicin wannan abu, sai inga ba gara mutum yaje ya kwanta a sibiti ba yace a zuke jininsa gaba daya a rabawa marasa lafiya saboda ya mutu, gara yace a yayyanki duk sassan jikinsa a raba sadakatul jariya. Dr lukman ya kwashe da dariya har da buga kafa a kasa. Yace haba dai doctor har abin ya kai haka? Yace haka ne mana, saboda yadda zaka ga suna kutsawa a jikin tirela. Na fada maka fa acaba ne ya kashe san uwa na uwa daya uba daya, kuma ina tsaye ina kallo ya kutsa dashi karkashin tirela. Daha cewa dan acaba kai ni can in siyo batir motarmu ta mutu a hanya, shikenan ya warce shi sai karkashin tirela sai gawarsu aka kwakulo. Tun daga lokacin idan naga mutum akan acaba sai kaga na bar abun da nakeyi na rike kai, ina taya shi da addua har sai na daina hangensu. Musamman mace sai inji kamar in fasa ihu ince ga motarta nan zo ki hau na tafi da kafa. Wadanne irin maza ne zasu bar matarsu taje ta hau acaba, ko bashi da mota ai sai ya bata kudin drop har inda zata je a mota. Sai a lokacin na tabbatr da dalilin da yasa yake hararata rannan ashe, don na sauko daga kan acaba ne. Ya tayar da sallah, dr lukman ya miko min file biyu da wanda nazo dashi da wanda yayi cike cike yace in mayar mata ince bashi ba, koren file din zata bayar. Na durkusa na karba na fito da sauri, yayin da zuciyata ta cika da murna saboda yau taga abinda take muradi. Sai ya sake burge ni dana ga yana sallah, naji dadi danaji dalilin hararar da yayi min rannan ba tsana ta yayi ba. Sai na fara tunanin hanyar da zanbi in shiga harkarsa ba tare da yayi min wulkanci ba. Naci sa'a kuwa ina zuwa nayi mata bayani sai ta miko min koren file din da yace ta bani in kai masa. Na taho hanya ina farin ciki hade da fargabar abun da zanje in tarar. Na isa ofishin sai faduwar gaban da nake ji ta karu, na fara karanta ADDUAR WANDA YAJI TSORON MUTANE "Allahummakfinihim bimaa shi'ita" (Ya Allah Ka isar mini dasu da abin da kaso). Ina tura kai sai nayi sallama. Dr lukaman ne ya amsa, har yanzu gogan nawa yana kan abin sallah ya idar amma yana jan carbi. Na dago ido na dube shi a hankali, sai muka hada ido ni dashi, bansan wanda ya fara kawar da kai gefe ba. Na matsa lungu ina jiran dr lukman ya gama dubawa sai da na tabbatar lungun da na shige ko ya daga ido ba zai ganni ba. Na nutsu kai kace a gaban sarki nake, yadda nake sanda kai kace da kayan sata aka kamani, za'a yanke min hukunci. Wayar dr shuraim imran ce take ruri, kidan ringing tone din yana tashi a hankali, wakar soyayya ce ta celen dion mai taken come bake to me, sai ya danna amsa. Kalmar da ya fara ambato a cikin harshen turanci ita ta gigitani, tasa na dimauce sai na tsinci kaina har da kwalla mai radadin fita saboda kishi. Daga ji ba sai an fada min ba da matarsa yake magana, wacce yake tsananin so da kauna fiye da kowacce 'ya mace a duniya. Tunda nake a rayuwata ban taba jin namijin bahaushe da ya fadawa matarsa wannan kalma, ko da yake ni 'yar gargajiyace na tashi cikin 'yan gargajiya tsakanina da matansu sai ke zo nan, dauko, dafa, wanke, goge. Kullum sai hantara dube ki ballagaza, kazama, kwadayayyiya. Haka na saba ji tun tashina tsakanin miji da matarsa. Amma dr shuraim imran yace da abar kaunarsa, salam my dear, my heart, my life how are you and how is your trip? Hope cool. Duk da ban jiyo abinda zata fada ba itama da daddadar kalma ta mayar masa. Ya juye harshe sai turanci yake zazzagowa ya tambaya kuna ina yanzu? Sai ta bashi amsa, banji amsar ba sai yace ok kun bar london yanzu kuna amsterdam? Awa nawa zaku yi transit din? Ta fada masa, sai yace karfe goma dai dai zaku iso kano, ni kuma karfe tara a airport zata yi min da izinin Ubangiji. Ina kewarki, ina babyna? Can sai naji ya fara magana cikin muryar yara yana yiwa yaro wasa, sai na tabbatar 'yarsa ce itama da turancin yake mata magana. Kalmar da ya fada ta karshe daga ita ya kashe waya itace "I love u baby, I miss u too, I am eager to see ur beautiful face. Take care bye". Na dinga dauki ba dadi da zuciyata don so take ta tsinko fado kasa ta ragargaje don tashin hankalin da ta shiga. Dr lukman ya dube shi yayi dariya yace madam ce? Ya lumshe ido tace madam ce ita da baby sun taho yanzu suna amsterdam sun baro london. Kaji matar da take makaranta shine ta bar karatunta ta biyo ni. Dr lukman yace ah da gaskiyarta, yaushe zata zauna a can mijinta yana nan? Dr shureim imran yace toh ai matsalar ba zata iya zaman bane a nan, tana yin sati biyu a daddafe zata fara magiya inzo mu koma london, ita ba ta zauna tayi karatunta ba a can, ita bata bar yarinya tayi karatunta ba. Dr lukman yace ai da ta dinga barin yarinyar a gidan iyayenta ba suma a london din ba gidansu yake? Sai iyayenta su rike muku 'yar kai da ita ku karaci walagiginku tsakanin london da Nigeria. Dr shureim imran yayi dariya yace toh ai yarinyar harta fi uwar damuwa ai ita tace take so uwar tace sai an kawo ta ta ganni, sai tasa uwar tayi min waya fiye da sau goma a rana ace min ga baby tana kuka, wai tana son magana dani. Ina daukar wayar kasan abinda zata ce min? Daddy I miss you, sai ta kashe waya shikenan. Su dukka suka kwashe da dariya, dr lukman yace gaskiya ku canza tsari, ko kai ka hakura da zaman nigeria ka koma can ku zauna, daman a can kuka hadu. Dr shureim imran ya rike baki yace cafdi! Ai ba zai yiwu ba, ka manta halin babana ai ba zai bari inyi aiki a can ba, kasan shi da kishin kasar nan, babu dansa da bai dawo nigeria ba yanzu. Karatu kadai ya amince muje muyi, aiki kuwa dole mu dawo mu bautawa kasarmu, mu taimaki alummar hausa, fulani, musulmai 'yan uwanmu, bai damu da yawan albashin can ba. Dr lukman yace haka ka fada min, gaskiya ya burge ni. Ina ma za'a sami dattijan arewa irinsa masu kishin YARENSU DA ADDININSU da kasar nan, da kasar nan ta gyaru. Dr shureinm yace ai kuwa sanda zanyi aure hana ni yaso yi, dana dage ina so ni da ita ya shimfida mana sharudda masu tsauri. Tace taji ta gani zata bi duk abinda yace. Sharadi na farko da ya shimfida mana shine dole ta biyo ni nigeria mu zauna dindindin idan munje london hutu muka yi da zarar hutu ya kare mu dawo. Sannan dole ta bar shigar dan siket da wando ta saka atamfa ko leshi da mayafi don shi ya tsani english wears. Tace ta yarda yanzu ma zaman da ya bari tana yi na dan shekaru ne saboda karatu, ta kusa kare makarantar da zarar ta kare yace ta hado kayanta kakaf ta kaura kasar nan, dole anan kasar zatayi aiki ba a can ba. Tags : Itama kuma bata iya zaman kasar na, tsoron sauro takeyi, ko kuda ta gani sai ta hau kuka ta tashi da gudu. Baby kuwa tana burge ni babu abinda ba taci, kuma babu in da bata shiga ta zauna lafiya a kasar nan, bata damuwa da duk wani canji kuma itama a can aka haifeta kamar yadda aka haifi uwar a can. Dr lukman yayi dariya yace ah wannan ita ta biyo kakanta alhaji, komansu na gargajiya , babu zancen cewa ma kai ta biyo, don kai ma bature ne. Dr shureim imran yace ai kuwa baka san bature ba, ai ni ko a gidanmu sun san nina biyo alhaji sak, saboda ko wajen abinci bana cin su shinkafa, taliya , cake, macaroni da sauransu. Idan aka ga naci irin wadannan toh a london nake, ko abj don babu yadda zanyi. Nifa har kwano nake bawa direbana ya dauka ya tafi cikin gari unguwar su wani abokina neman danwake, dambu, ko gurasa mai kulikuli. Dr lukman ya kwace da dariya yace har da yawon neman dambu kake sawa ayi? Lallai dagaske kake. Ni kuma abinda ba'aci kenan a gidana ko tuwo zasu yi sai dai suyi min abincina daban, haba ai an wuce wannan lokacin ina yaro in nadi dambu da tuwo, yanzu da wayona da 'yan canjina a aljihi inci dambu? Ko ba haka ba 'yar boko, har yanzu kina cin dambu? Ya tambayeni, sai nayi sauri na dubi dodona dr shuriem, domin shi nake tsoro. Gogan nawa sai yayi dif bai sake magana ba, yaji an dako dani a zancensu. Jikina ya sake yin sanyi, nayi murmushi nace bana cin dambu nima. Dr lukman yace yawwa ashe bani kadai ne na gaji da cin tuwo ba, muna da yawa. Daga lokacin hirar ya koma ni da dr lukman kadai, dr shureim yaki tsoma baki. Dr lukman yace dani ke 'yar gidan matron maryam ce, naga kuna kama? Wannan karon ne ma naga dr shureim ya dubeni kasa kasa, sai yayi wuf ya mike tsaye yana nade abin sallah, ya linke ya ajiye sannan ya shiga daura neck tie a wuya, ya saka bakar suit dinsa. Cikin sanyi jiki nace a'a ni ba 'yarta bace, malamata ce kawai, muna shiri sosai. Dr lukman yaci gaba da rubutu yana magana yace ke ba 'yar gezawa bace kenan. Tunda matron maryam 'yar gezawa ce. Nayi dariya nace a'a ni ba 'yar kano nace ba ma, ni 'yar shagamu ce. Sai ya tsaya da rubutun ya dube ni ta cikin gilashinsa yace da gaske kike, ko kanwar yahaya umar ce? Babban abokina ne, ajinmu daya a sakandiren da muka yi a yobe. Sai nayi caraf nace yayana ne, babanmu daya. Sai ya fasa rubutun ya ajiye biro yace yanzu dan Allah yahaya umar yayanki ne? Na gyada kai nace yayana ne. Yace llallai kuwa naga kama, kina cewa ke 'yar shagamu ce sai naga fuskarku iri daya daman tun sanda na fara ganinki na rasa wanda kika min kama. Yana ina yanzu? Yana nan lagos yana aiki a tasha dan union ne. Yace subhanallah! Yanzu duk kokarin nan na yahaya umar bai cigaba da karatu ba a aikin tasha ya kare? Kinsan fa ni dashi muka kudiri niyyar sai munyi karatun likita. Tunda muka gama makaranta a. Yobe na dai ganinsa, naje gidansu a nan yobe nemansa ban same shi ba aka ce ya koma garin babansu shagamu, ashe dangin mahaifiyarsa ne a yobe ko? Shikenan rabuwarmu dashi, sai dai duk sanda aka ambaci shagamu sai na tuno shi, saboda dan shagamu muke ce masa. Mun shaku sosai dakinmu daya, ajinmu daya. Nayi murmushi nace eh dangin mahaifiyarsa ne suka rike shi a yobe, tun yana yaro, daya gama sakandire sai ya koma gida shagamu, bai cigaba da karatu ba kuma. Ina rufe bakin dr shureim ya shirya tsafa, ya dauki jakar laptop dinsa ya dubi abokinsa dr lukman. Yace ni na tafi sai kuma gobe. Dr lukman yace aini ma na tashi, ka jira ni yarinyar nan zan sallama kawai, ka ga ashe ma ni kanwata ce, haba tun sanda nake ganinta nake ganin kamar na san fuskar, ashe kanwar abokina ne childhood frnd yahaya umar. Ya tabe baki yace a'a ni dai nayi gaba, sai ka taho kawai. Ya fice ya bar mu. Bai ma bada amsar labarin da ya bashi ba saboda a kaina ne ba zai tsoma baki ba, sai na fara dankarawa zuciyata zagi akan ko taki ko taso sai ta rabu da son wannan marar mutuncin. Me yayi zafi? Dan kawai Allah yayi masa baiwa kala kala, yayi masa farin jini, ana sonsa sai ya dinga wulakanci, shi waye? Namiji ne fa kamar kowanne namiji, gasu nan birjik a titi suna bin mace tana musu yanga kafin ma ta kula su. Suna 'yar murya suna yi mata wahala, don ta saurare su. Haka na dinga kushe shi a zuciyata don in samu sukuni, duk yadda zanbi in raba zuciyata da sonsa bi nake yi don shine samun saukina. Dr lukman ya rufe file ya bani, tambayi lambar wayar abokinsa yayana yahaya. Nace bani da waya, amma zan karbo masa lambar a wajen yayana hussaini gobe zan kawo masa. Sai yayi mamaki don nace bani da waya, sai ya tambaye ni, yace faduwa wayar taki tayi ne? Kuma baki hadda ce lambarsa ba? Na amsa da eh faduwa tayi. Saboda sauri nake in fice daga ofishin saboda abin kaunata baya nan, daman saboda shi naji tsayuwar da nake yi bata isheni ba tun dazu, yana barin ofishin sai naji duk ofis din ya gindure ni. So nake in fito inga in daya nufa, kuma da wacce irin mota yazo yau. Nayi wa dr lukman sallama na fito bakin barandar da sauri, na waiga kowacce kusurwa sai ban ganshi ba, ko alamunsa babu, sai naji haushin dr lukman ya rufe ni, da bai bari na fito da wuri ba, gashi nan har ya tafi. Sai zuciyata tace ke da kike yi min fada in rabu dashi, ina ke ina takaicin don baki gan shi ba? Nayi ajiyar zuciya mai karfi naci gaba da tafiya maimakon inbi doguwar baranda sai na sauko na dinga kutsawa ta kasa cikin motoci. Ban sa ran ganinsa ba ko kadan amma dai nasan dole ta nan ya bi, idan zai dauki motarsa ko sawun takalmansa na taka ai naji sa'ida a raina. Kamar daga sama naji wata murya mai shige da tasa daga gefena, abin da yake fada kuwa shine "wait, wait dr hidaya, na fada miki na sake fada miki don Allah ki daina damuna da waya cikin dare, yau matata zata zo kasar na, bana so ki jawo mana matsala. Aiki ne ya hada mu anan idan an tashi daga aiki to ban sanki ba kowa ya kama gabansa. Wanne irin abu ne haka, ina zan saka raina? A asibiti a dame ni har gida ma kun fara bina? Yaya akayi kika nemo gidanmu har kika ba mai gadinmu sako ya bani? A wanne dalile zakiyi min sayayya ki kai min gida? Zaki jefa rayuwata cikin damuwa tsakanina da matata, da kuma iyayena. Na dinga tafiya a hankali ina kallonsu, a tsaye suke a jikin motarsa har ya bude mota zai shiga sai ta tsayar dashi. Ransa a bace yake magana cikin matsanancin fushi, sai ita ma ta fusata ta magana cikin kuka da fada. Dr shureim in har ni 'yar halak ce a cikin uwata da ubana na kyale ka, har abada ba zan sake nemanka ba. Ya fada cike da gadara yace shi yafi sauki, naji dadi sosai kuwa. Ta juya a fusace tana sharce hawaye, yayin da farin gilashin idonta ya fado kasa, ido daya ya fita. Na karaso da sauri na dauko mata na mika mata, sai ta dube ni jajayen idanuwanta ta karba gami da ce min thank u very much. Ta wuce da sauri. Dr shureim ya dube ni, ya sake bude ido ya kalle ni sosai, na tsaya cak kamar yadda yake tsaye kyam yana dubana. Na harare shi sama da kasa naja dogon tsaki na kada kai na wuce na bar shi nan a tsaye bai daina kallona ba, ni dai ban waiwaya ba. Na san ya cika da mamakina, ni dai burina ya cika tunda na fara ramawa kaina wulakacin da yayi min da sauran wahallalun mata da 'yan uwana masu sonsa. Na kudiri aniyar kallon arziki ya daina hada mu sabida na san ba zan same shi ba kamar sauran da suka fini haduwa, ga kyau basu same shi ba. Kamar daga sama naji wata murya mai shige da tasa daga gefena, abin da yake fada kuwa shine "wait, wait dr hidaya, na fada miki na sake fada miki don Allah ki daina damuna da waya cikin dare, yau matata zata zo kasar na, bana so ki jawo mana matsala. Aiki ne ya hada mu anan idan an tashi daga aiki to ban sanki ba kowa ya kama gabansa. Wanne irin abu ne haka, ina zan saka raina? A asibiti a dame ni har gida ma kun fara bina? Yaya akayi kika nemo gidanmu har kika ba mai gadinmu sako ya bani? A wanne dalile zakiyi min

Chapter 4 of 23