Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciya. Duk da har yanzu y.husaini baice min komai ba akn hukuncin daya yanke a kaina. Idan na kirashi ina jinsa faram2 nasan babu matsala.idan ma akwai matsala ina addu'a allah ya kawar da ita ya tankado mana da alkhairai. Af ta marairaice ido tayi mrmsh tace, amin ya allah. Tana rufe bakinta sai taji an daka mata duka a baya ance,shegiya aisha umar zance kikeyi da yamman nan? Tayi sauri ta waiwaya cike da takaici sai taga ummi kawarta ce. Al'amarin ummi sai addu'a sbd ta zama abar a tausaya mata, kai kace sabuwar mahaukaciya ce sbd rashin kwanciyar hnkl da talauci ko zanin daurawar kirki babu a jikinta,ita da goyon bakikirin a cikin tsummokarai. Yadda dr s ya kaikaice yana kallon ummi sama da kasa shiyasa af jin kunya. Da kunya ta nuna ummi tace kawarta ce,dk da ba zaman karya suke yi ba ita dashi. Sai suru2 ummi takeyi barkatai babu nutsuwa idan tayi magana daya saita dakawa farida duka ta dauko ashar ta kwararo mata,ta dauka burge shuraim takeyi. Kokari take ta tonawa farida asiri dn harta fara cewa badai wannan mu2min an bane,yazo da kafarsa? Suna shiga dakin af sai ummi tace,aisha umar wanne malamin ne ya tsaya miki kika sami wannan tsalelen,nima ki raka ni? Kada dai kice min likitan nan ne da kikeso baya sonki,wanda malam yayi miki aiki a kansa. Kinsan aikin malamn nan fa yanaci,yanzu gashi naki yaci yazo har kfr gidanku,gsky mu2mn nan ya hadu nifa na zaci baya jin hausa,na dauka farar fata ne,mu2min nan kadara ne,ga kyau ga kudi harya fiki kyau fa. Daman banda aikin malami yaya za a yi mu2min nan ya kalle ki,kinga yadda yake sonki kuwa naga sai wani kallonki yakeyi. Nima dai ba laifi ina dan ganin cigaba a ckn ayyukan dana rarrabwa malamai kashi-kashi matsalar da ake samu ni inayi,budurwarsa ma tanayi,uwarsu ma tanayi dn su raba mu. Shiyasa bana ganin abubuwana suna tafiya dai-dai. Dadin dadawa bani da kudi,kin san aiki sai da siyen kayan sadaka,duk kayan dakina sun kare,yanzu ko kmen zanyi ma banida ko katifa dk na siyar. Kinga yanzu ma daga wajen wani nake a lungun sharifai makociyarmu ta hadani dashi,shima dubu 3 yace nakai za a yi aiki,sannan a yanka kaza,shiyasa naji dadin dubu biyun nan daya bani. Af tayi shiru dn takaici ko iya kallon fskrta batayi na,tacigaba da kirga himilin kudinta data iske a cikin ambulan din daya bata. Sababbin 'yan dubu dubu ne har guda ashirin,dubu ashirin ya bata hade da wani dan karamin kati (greeting card) mai dauke da kalaman soyayya dadada 2nda Allah ya halicce taba a taba yi mata kyautar kudi mai dimbin yawa ba irin wannan,dadin dadawa kyautar daga wajen masoyinta ne. Ta gama karanata katin, saita rungume shi a kirjinta, tace Allah srk likitana. Kai Allah kaine abun godiya ngd maka. Ummi tazo ta nanikewa af,tace,cafdi dk wannan himilin kudin,ke ya bawa? Daman ance ana yin asirin bada kudi sai kaga mu2m yanayi maka kyauta ba a hayyacinsa ba,irinsa nake so a yiwa yasar. Dn Allah farida ki raka ni wajen malaminki,kinga tsakaninmu dake babu boye-boye. Takaicin abn data ke fada da warin dattin bakinta,dana 'yarta ne suka addabi af,taji kmr zata yi amai,tmkr xuciyarta zata hautsuno ya fito waje. Ta daga ido tana kallon ummi dn takaici ta kasa ce mata komai. Ta mike tsaye ta daga labulen kofa dn iska ta shigo,ta kade kauri da karnin da dakin ya kidime. Ta wuce taje kwandon kayan wanke wanke ta dauko kwano da kofi ta zubo mata abnci da ruwan sha ta kawo mata. Taga alamar yunwa sukeji daga ita har 'yarta. Tana kawo musu suka hau ci hannu baka hannu kwarya tmkr wadanda suka kai azumi a lkcn rani. Af ta koma gefe taci gaba ga rangadawa masoyinta sakon gdy a cikin wayarta,ta tuttura masa. Ummi zata sake yi mata maganr bokaye af ta dakatr da ita da hannu. Tace ummi dn Allah kici abincinki kiyi shiru,kada ki kware idan kin gama kya yi mun tatsuniyar. Ummi ta maimaita, tatsuniya kuma? DUK KYAN TAKALMI 3* 6 Af tace,ai gara ma tatsuniya,yara suna karuwa sbd dk tatsuniya gargadi ce,amma wannan lbrn naki gara in saurari kidan garaya da in cigaba da sauraronki.allah ya shrye ki ummi. Ummi ta koma ta zauna tayi kulas tana ci tana gyada kai tana fadi a ranta,lallai dan adam, wulakanci aisha umar zatayi min dk irin halaccin danayi mata na rakata inda aka jawo mata hnklnsa yazo yana sonta,har yake cusa mata kudi,shine na zama abar kyara a wajenta? Da ummi da 'yarta suka gama con abinci aisha farida ta kwashe kwanunkan ta dawo ta zauna, ta dubi ummi wacce 2ni alamomin bacin rai sun bayyana fskrta. Af tace, ummi yaya su hjyrki? Ta tabe baki tace, suna na kalau. Keda naki sake nemana ba 2n ranar da muka rabu dake daga gidan malam. Ai kya zo kice min wannan bukata ta samu kiyi min godiya. Amma shiru babu ke babu labari. Koda yake ba zaki zoba dn kin fara samun daula,gashi harda waya a hannu kina daddannawa ai dole ki guje ni.af tayi mrmshn krfn hali tace, naje nemanki mana na tarar ba kya gidanki,facalarki tace an sake ki. Har kinyi rshn m2mci kala2 kince asiri sukayi miki ke ma saikin ga bayansu. Haba ummi me yake damunki ne,kina abu kmr baki taba shiga aji ba? Ummi ta fusata tace, dole mana kice haka,ai ke aiki yaci ni da baici ba sai in zauna in zura ido? Kina ganin har yassar yayi aurensa yaki ya mayar dani ko ganina baya son yi. Af tace, yayi min dai-dai gsky ba dn kin tako kinzo gidanmu ba har aba bana son ganinki,kuma koda kuskure bazan kara taka gidanku ba. Sbd kin kusa halaka ni,kin tozarta ni duniya da lahira. Ke ba kawar kirki bace ummi,dk mai yawo dake ma sai ya halaka. Ummi ta fusata tace, to naji kuma dk wulakancin da kika yimin nina tako nazo gidanku, dk ranar da kika ganni a gidanku kiiyi min dk wulakancin da kika ga dama. Ta zabura zata mike af ta riketa ta mayar da ita ta zaunar. Tace, yo hkr gsky nakeso na fada miki,ita kuwa gsky daci gareta. Ummi,fada miki ne ban yi ba amma jana gidan boka da kikaui kika zuga ni na ranto kudi,kin jawo min bakar masifa a rayuwata. Aikinsa bai min amfanin komai ba,har kulle ni akayi a ofoshin 'yansanda sbd wannan kudi,shi kuwa wanda akayi min asirin dn yasoni saima ya sake tsanata. Ummi bazan boye miki ba saida nayi kuka da hawayena,nayi allah wadai da halayenki. Ni mai yafiya ce, na yafe miki,amma fa kin cuceni. Ummi ta harari af tace me kike so kice min bayan nan kin samu,gashi nan yazo wajenki? Af ta soko mata tata harara tace har yanzu baki saduda bako, ba zaki daina gasgata karairayin 'yan danfara bako? To bari na fada miki wannan mu2min da kika kaini wajensa macuci ne,kema kinsan da haka,tawada ce ya zuba a ruwa ya bamu sai laya aka rubuta alifun,ba'un da sauransu tsabar ya mayar damu jahilai. Ke bari ma na baki labarin dk abnda ya faru bayan rabuwata dake. Kinci sa'a anti abida bata nan, da yau saita wanke ki,sbd taki jinin taga mace mai bin bokaye. Habba ummi yanzu mai bin boka ya kara miki,kin kadar da dk abnda kika mallaka a duniya kina yawo a cikin tsumma keda 'yarki ko wanka babu. Mai yassar zaiyi dake a haka kmr tababbiya? Ai har abada ba zaki ga dai'dai ba idan dai baki daina bin bokaye ba. Ummi da nayi istigifari na mayr da gaba daya lamurana wajen Allah a saukake. Ya kawo min dr s cikin kwanciyar hnkl. Ina ma zaki bi hanyar dana bi dakin samu yassar cikin sauki ba tareda kin kashe ko sisi ba. Da rayuwarki ta gyaru duniya da lahira,hnkli ya kwanta,kin fita daga talauci dacin bashi. Ummi tayi sororo da alama jikinta yayi sanyi,ta fada cike da sanyin jiki. Aisha umar fada min yadda kika yi. Af ta gyara zama ta bawa ummi labarin dk abnda ya faru da ita,2n daga ranar da suka rabu da ita,har izuwa rana irin tayau. Ummi ta buga tagumi tana sauraron af daga dukkan alamu tana gasgata nasihohinta. Da af takai aya,sai ummi tayi ajyr zuciya. Tace,aisha umar kinyi gsky,to yanzu meye shawararki? Ta ina zan fara? Af tayi dry tace, ta inda na fara zaki fara,kum kema ki riki wadannan matakai biyar da abida tabani, ki riki kissar malamai nan da yasa matar na ta debo masa nonon bauna. Ki rabu da bin 'yan tsibbu ba sai wani ya fada miki ba,kema kin san babu riba. Ummi ta sharce hawaye tace, gsky ne, nima ina tsoron haduwata da ubangiji,sannan ga sunanan ya baci a garin nan dk wanda ya danni,yasan ina bin bokaye,har da 'yan ina da kare nake bi. Yanzu yaya zanyi aisha umar? Saita rushe da kuka. Af tace, laifin da kikayi tsakaninki da ubangiji zai yafe miki,idan kika tuba. Laifin da kikayi wa wani ne Allah bazai yafe miki ba saikin je kin nemi gafarar wadanda kika yiwa laifin. Wannan shine mataki na farko da zaki fara takawa. Kiyi ta istgifari da lahaula kiyi ta addu'a akan Allah ya juyo miki da hnklin yassar ya dawo gareki. Abu na biyu ki zamo mai tsananin hkr, karki ga idan kinga an sami jinkiri,bai kuyo gareki bada wuri. Na 3 ki kama mu2ncinki,kija ajinki kada ki sake binsa ko waninsa kina rokonsa ya mayr dake. Idan kika rike guda ukun nan zaki ga yadda Allah zai yi dake. Ummi ta zauna shiru tana 2nani,ta kasa cewa komai,canta dago ta dubi af. Tace, yassar fa ya tsaneni, ya tsani ya ganni ko a hanya. Sai naje nayi masa hayaniya nema yake aiko min da dubu 1 ko 2 a wata na abincin 'yarsa. Af tace,to saime? Bake kika jawa kanki ba? Ai halin mu2m ke sawa a tsane shi,ki gyara halinki ki gani idan baiso kiba. Ki dinga wanka kina tsaftace jikinki dana 'yarki,ki rage magana barkatai da yawo a gari,ki zauna a gidanku ki riki sallah da zumi da lazimi,kina ta addu'a kiga yadda Allah zai sauya ki. Ummi tace, insha Allahu zanyi duk yadda kik ce min, yanzu ma daga nan gidan sirikata zanje na nemi gafararta da facalata dashi kansa yasar din,nace kuskure nayi dana biyewa zancen malamai. Sai in koma gida in zauna in daina yawo in dinga sana'a ina biya dimbin bashin dake kaina. Aisha umar ngd,madalla sai kin ganni kuma. Ta tashi ta dauko 'yarta ta goya a baya,jikinta sanyi kalau. Af ta bude jakar kayanta ta tsinto mata atamfofi kala biyu tsofaffi ta bata,ta sake zaro nairi dubu 1 daga cikin kudin da dr s yabata ta hada mata. Sai gdy ummi keyi tana murna. Ta rakata har bakin titi ta hau acaba ta tafi. Af ta dawo gida cike da tausayin kawarta mayi mata addu'ar Allah ya shirye ta, Allah ya sa abunda take fada a bakinta ya shiga har cikin zuciyarta ASUBA TAGARI UMMIN YASIR BABI NA GOMA SHA SHIDA Yaya husainai ne yaketa shige da fice tsakanin dakinsa zuwa kfr dakin 2n kafin gari ya karasa wayewa. Da duku-duku af ta tashi dn tayi sallah ta kuma kai yara fitsari kasancewar lahadi ce babu mkrnta,in yaso bayan sunyi sallah saisu koma suci gaba da bacci. Tayi mamaki da ganin y.h a tsakar gida yana tsaye cak kmr mai 2nani. Mamakinta ya sake karuwa alkcn data fito daga bandaki har tayi alwalla bai koma daki ba,dai kai kawo yake tayi tsakanin dakinsa zuwa zaure. Ya shiga ya fita. Bayan tayi sallah yaran dk sunyi sallah,saita sake kwantar dasu sannan tayi wuf! Ta fito dn taga y.h yana nan? Ta iske shi a tsaye daf da kfr dakinta ya sakale hannayensa a bayansa ya sunkuyar dakai kasa kmr mai 2nani. Saita dafe kirji dn bugawar da zuciyarta keyi. Yaya lfy? Ta tmbyeshi. Ya dago jajayen idanuwansa ya dubeta da kyar ya iya bude bakinsa yace,lfy? Ta tsaya a jkin kofa tana kallonsa babu abnda zuciyarta bata aiyana mata akan abida ba. Tasan tabbas wannan damuwar tasa tana da alaka da abida. Yace, aisha yaushe ne zaa yiwa yara hu2n mkrnta? Muryarta na rawa tace, gobe litinin zasu fara jarabawa, ranar juma'ar kuma za a yi musu hutu. Lafiya? Sai yayi shiru, can ya dago sai taga idanuwansa sharkab da hawaye, yace, ina ganin su hkra da jarabawar ki hada muku kayanku mu tafi shagamu yanzu. Ta sulale ta durkusa ta dora hannu aka ta fasa kuka mai tsananin sauti da gigitar da mai sauraro. Tace, Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Wayyo Allah anti abida,wayyo antina, Allah ya jikanki,Allah yayi miki gafara. Sai y.h ya fisgota ya toshe mata baki ya grgza ta fadi yace, rufe min baki,waye yace miki abida ta mu2? Kan kace kwabo yaran abida suma sun fito daga daki da gudu,suna kuka. Mutanen gidan yaransu da manya,maza da mata sun firfito a gigice suna tmbyrsu ko lfy? Af dai bata ji bata gani,ba kuma ta gane dk abubuwan da jama'ar da suka taru akanta suke fada ba. Kuka take,faduwa take ana riketa bata kakkautawa. Abida bata mutu ba. Kalmar da y.husaini keta ambato,amma fa shima din kuka yake yi haikan. Mutanen gida maza da mata sai suma suka dinga hawaye dn tausayawa su AF. Af ki hada kayanku a babbar jaka da dk wani abu mai amfani ki shiga dakina ki harhada kayana dana abida kakaf gara mu kaura shagamu meyi jinyarta 2nda har yanzu bata warke ba,ni bance miki ta mutu na. Bari naje na nemo mana tasi wacce zata kaimu tasha. Ba dn ma tfyr ba ta shiri bace, aida motar ofis zan aro in zuba mai mu da kayan mu kakaf mu tafi, to ba shiri. Af ta tsh tsaye daga kasan datake burgima jikinta yayi bududud yayin da fskrta ta hadu ta damule,bayan hawaye da yayi face- face,idanuwan da fskr dk sun kumbura luhu-luhu. Ta kade jikinta ta dubi yayanta tace,yaya ina da magana dakai. Saita suce daki, ya biyo ta a baya. Ta jawo jkrta ta binciki,sai ta damko himilin kudi ta mika masa har naira dubu goma sha takwas. Ya karba cike da mamaki ya tmby,af waye ya baki wadannan makudan kudi? Ta matse hawaye tace, dr s ne ya bani dubu ashirin wancan satin da yazo. Ya kalmashe ya zura a aljihu yace,ki nutsu ki hada muku kayanku a tsanake ni bance miki abida ta mu2 ba. Ta fashe da kuka tace,haba yaya nima fa musulma ce,kuma mai hnkli nasan tawakkali. A gabana babana ya mutu ba a dade ba uwata ta mutu,me yasa zaka boye min mu2war abida? Yace,ni dai bance miki ta mu2 ba. Ya ficce yabarta a drksh ta jawo wayarta da sauri ta kira lmbr goggo mahaifiyar abida taji a kashe. Ta kira lambobin mutanen gdnsu har su 3 babu mutum 1 data samu,dk sun kashe waya. Wannan ya tabbatar mat abida ta rasu. Saita kira kanwarta munawwara a lagos taji muryar knwrta rangadau cikin fara'a take magana. Af cikin kuka tace,baku da labarn mu2war abida ne? Sai taji munauwara ta kwalla ihu ta wurgar da wayar tana salati. Aisha farisa ta tabbata lbrn mu2war bai isa garesu ba. Ta kira yaya yahya sai tci sa'a bugu daya ta shiga,nan da nan ya amsa. Ta rushe da kuka,tace, yaya ka fada min gsky,abida ta rasu ko. Hello,hello kawai yake cewa,kasancewar yana cikin hayaniya baya jinta. Yace aisha zan kiraki bana jinki. Saiya katse wayar. Ta mimmike kafa ta ske bude wani sabon shafin kuka. Kukan dako a mu2wa iyayenta batayi irinsa ba. Bata manta da ambaton innalillahi wainna ilaihi rajiun ba. Babu anda tafi 2nawa sai irin gudunmuwar da abida ta bata wajen yakin neman soyayyar dr s. Allahu akbar,allah mai yadda yaso,ga dr shuraim ya samu ita kuma ta tafi. Tace a ranta, tabbas rabuwa da dr s shine kwanciyar hankalina 2nsa babu abida, muddin na kasance da shuraim babban fami zai dinga yimin ina tunowa da ita. matan gida suka biyo ta daki suka zagayeta suna bata naki, su ma sun shiga rudani kasancewar husaini yace bata mutu, to idan bata mutu ba mai yasa xai tashi tfy a yau, gashi kuma yana rusa kuka shima uwani ta matse hawaye, tace AF tashi ki hada muku kayan kafin yayanki ya dawo don ya tafi ya samo mota" AF ta girgixa kai , tace"baxan iya ba ku kyaleni kawai" taci gaba da rusa kuka baji ba gani. nan matan gida suka shiga hada musu kayayyakinsu suna durawa a jakunkuna da buhuhunan kama daga kayan sawarsu takalmansu da kwanukansu. faruk ne yake ta jawo akwatinan mamansu da babansu daga cikin dakinsu yana fitowa dashi tsakar gida,matan suna ta harhadawa. himilin kaya dauri dauri aka kawo zaure aka himila, katifu ne kawai basu dauka ba amma babu abinda ba'a harhada ba. ha yanzu AF na zaune a daki ta hada kai da gwuiwa, kukan da takeyi yaki ya kafe sai ita tasan abinda takeji a cikin zuciyarta, kuna ,suya da tafarfasa duk sun tabbata a kirjinta. ta fada a baiyane" Abida.....abida mutunce. muyane nagari basu cika dadewa a duniya ba. sai yanzu na cika marainiya nayi rashin yar uwata garkuwar jikina. dama in mutu a yau in huta da takaici rayuwa. bani da sauran farin ciki a rayuwata kuma.... U.khairi ta rushe da kuka ta durkusa a gaban af tace,ki yafe min, abida ta yafe mana abubuwan da muka dinga yi muku a zamanmu daku a gidan nan,hakika mun zalunce ku,kullum muna cikin gulmarku,yi muku kazafi,makirci kala2 ku baku sani ba. Allah ya jikan abida mace mai hkr,sai a zageta a gabnta ta juyo t kallemu tayi mrmshi ta wuce ba zata rama ba,kuma bazata tabayin gaba damu ba. Ban san abida idan ta tafi ba zata dawo ba, dana nemi gfrarta a ranar da za tafi da ita. Farida, ki yafe min koke ma idan kin tafi kin tafi ba zaki sake dawowa kano ba. Tabbas nice nayita hada makirci a wajen mahaifiyar musbahu dn kada ya aureki. Laure,uwani yaya ku kayi shiru bayan daku mukeyi musu komai. Suma sai suka gyara zama sukace haka ne farida ki yafe mana, mun zalunce ku, mun zalunci kanmu. Zazzafan hawaye ne ya dinga tsattsafowa daga idanuwanta. Ta tsura musu ido tana kallonsu kawaita kasa furta kalma 1 sbd tsananin data ke ciki. Kalamansu tmkr ruwan wuta suke fesa mata,saita daga hannu ta dakatar dasu. Tace,ya isa, dn Allah kubar fada min, dk nasan abunda yake frauwa,kuma abida ta fada min komai. Naji abnda kukace,kuma na yafe muku,na tabbatar abida ma ta yafe muku,dn bata taba kwana da wani a ranta ba. Su dukka suka cigaba da koke. Muryar yaya hussaini suka jiyo a zaure dashi da maza suna ta jidar kaya a zaure ana kaiwa mota ana lufgawa. Har sai da aka kwashe kayan tatas ya leko dakin yace aisha farida da yara su fito su tafi. Sai da su uwani suka daga ta tsaye wannan tana taro mata zaninta zai fadi, wannan tana gyara mata hijabi. Takalmi silifas sai da aka tura kafarta a ciki don ta manta yadda yake sawa saboda tsabar kidimewa. Wayarta ce kawai a hannunta don ko kofofin dakunan sai da yaya hussaini ya datso, kanta tsaye ta fice ba tare da ta iya waiwayowa baya ba. Bata iya amsa adduoin ta'aziya da fatan Allah Ya kiyaye hanyar da jama'ar gida da makota suke yi mata ba. Tafiya take tamkar kwai ya fashe mata a ciki. Bata ma san inda take jefa kafarta ba, 'ya'yan abida na nanike da ita, idan ta kalle su sai taji wani gagarumin tashin hankali ya sake taso mata. "Faridah!!" Tattausar murya taji a gefenta don haka ta waiga da sauri. Musbahu ta gani idanuwansa sharkab da hawaye, itama sai hawaye ya fara kwaranyo mata. Tayi sauri ta sunkuyar da kanta kasa ta dinga tafiya wurin mota. Yace Allah Ya jikan abida, naji ance kun kwashe kayan ku kakaf kun kaura shagamu. Yanzu shikenan ba zan sake ganinki ba? Ki sani har abada ba zan daina sonki ba, babu yadda zanyi ne. Sai ta sake rushewa da kuka, shima haka yana biye da ita har ta shige mota ita da 'ya'yanta. Yaya hussaini ya shiga gaba shi da direba, su kuma a gidan baya. Kaya kuwa suna can baya irin motar nan ce mai kama da na 'yan sanda bayanata kamar a kori kura. Cincirindon mutanen unguwa ne suka firfito yara da manya, maza da mata suna ta daga musu hannu har suka ja motar suka tafi. Sabon kuka ne ya sake sarkewa aisha farida. Sun fita daga kano kenan sai dr shuraim ya kirata, da farko tayi kamar ba zata dauka ba, sai dai ta daure ta amsa. Magana yake cikin shaukin soyayya. My love kin tashi kalau? Jiya kuma muna magana sai kikayi bacci ki ka barni ko? Ta runtse ido dan tsananin tashin hankali yayin da hawaye ya dinga tsartuwa daga idanunta. Bata iya bashi wannan amsar ba. Yayi murmushi yace banji kinyi magana ba tun dazu, ko baki jina ne? Tayi magana cikin sansanyiyar murya tace dr muna hanyar shagamu. Abida ce ta mutu. Innalillahi wa inna ilaihir rajiun dr shuraim ya sake maimaitawa har sau uku. Yayin da kuka ya barke mata. Dai dai lokacin kuma yaya hussaini ya hasala ya juyo a fusace ya fizge wayar, ya murtsike ya kashe ya rufe ta bambamin fada. Waye yace miki mutuwa tayi har kike yadawa a waya? Wai ke wace irin yarinya ce mara jin magana? Cikin kuka tace haba yaya me yasa kake boye min mutuwar anti abida? Ya ja dogon tsaki ya girgiza kai ya juya ya cigaba da kallon haya, ya saka wayar ta ta a aljihunsa. Dr shuraim yayi ta gwada kiran aisha farida ji wayar a kashe , sai hankalinsa ya kara tashi matuka. Yasan duk inda take yanzu bata cikin hayyacinta, kuka kuwa yau ko kogin maliya sai haka. A gigice ya tashi zaune ya fizge bargon da ya lulluba ya diro daga kan gadonsa yafito falonsa ya zauna ya cigaba da kiran wayarta a kashe. Ya kira dr lukman shima har sau uk bai amsa ba ,sai na hudun ne ya dauka yana magana cikin magagin bacci. Dr shuraim ya fada a dimauce, lukman ka wartsake daga baccin nan ka saurareni. Farida ce take cikin wani hali gashi kuma na rasa ta waya. Ka kira yayanta yahaya umar ka tambaye shi dan inji halin da take ciki. Dr lukman yayi firgigit ya tashi zaune yace ban fahimce ka ba, meya samu farida? Yace yanzu na kira ta tana kuka ta shaida min suna hanyar shagamu Allah Ya yiwa antinta abida rasuwa, mara lafiyar nan. Dr lukman ya zabura ya dauki doguwar salati yace kashe wayar ina zuwa barin kira yahaya umar. Bayan mintuna 15 dr lukman ya kira dr shuraim yace ka kara hakuri dai zuwa anjima don yanzu nayi ta kira ba dauka ba. Daya dauka ma sai naji shi a cikin hayaniya yake, yace na kashe zai kira ni anjima. Kaga kenan suna makabarta ko wajen zaman makoki. Dr shuraim ya dafe kai ya cije lebe yace halinda farida zata shiga shine babbar matsalata. Idan ka duba yadda kullum take kuka saboda rashin lafiyar nan inaga idan ta mutu? Lukman yaya za'ayi kenan? Dr lukman yayi ajiyar zuciya yace babu abinda sai dai muji ra zuwa anjima muji ta bakin yayan nata tukunna. Nayi maka alkwari yana kirana zan kiraka kaji halin da ake ciki. Dr lukman yayi godiya suka kashe wayan. Har yanzu kiran wayar aisha farida yake yi taki shiga. Sai ya tuno yana da lambar yaya hussaini don haka ya cire kunya ya kirashi. Yaci sa'a kuwa yana kira ta shiga, nan da nan yaya hussaini ya amsa. Ya ambaci sunan shi tangararau dr shuraim ne? Caraf aisha farida ta dago ta dubi yayanta. Dr shuraim yace sannu yaya, ya akaji da hakuri? Sai yaya hussaini ya gallawa aisha farida harara yace af! Kai ma ta fada maka anyi mutuwa ne? To wannan fadarta ne kawai, ni dai nace ta shirya mu tafi shagamu sai ta dau kuka da ihu. Dr shuraim ya cika da mamaki kafin yace wani abu yaya hussaini ya mikawa aisha farida wayar. Tayi ajiyar zuciya tayi sallama cike da sansanyar murya. Dr shuraim ya fara magana cikin tattausar murya. Yace farida meyasa kike da rudewa ne haka? Ga yayanki yyace bai fada miki ta mutu ba. Ta fashe da kuka tace haba dr nifa ba karamar yarinya bace nagane komai, meyasa za'a boye min? Ni nasan anty abida ta rasu, ko an fada min me zanyi, dole in dangana. Yaya hussaini ne ya sake yi mata tsawa yace kada ya sake ji tayi maganar rasuwan nan. Ta rushe da kuka mai tsanani, hankalin dr shuraim ya sake tashi ya shiga damuwa, yace yi shiru baby, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne , dukkanmu nan zaman jiranta mukeyi. Kiyi mata addua Allah Ya yi mata rahama. Ki kunna wayarki mu dinga magana. Tace wayar bata wajena yaya ya karba ya kashe tundazu da muke magana. Dr shuraim yayi yace to anjima zan kiraki a wannan layin. Idan anyi bakwai zaku dawo ko? Ta girgiza kai kamar tana gabanshi, ta zubo da hawaye masu yawa. Tace dr shuraim ina ganin wannan wayar da muke da kai itace rana ta karshe da zaka a duniya ballantana ka ganni. Kuka ya barke mata. See Translation KYAN TAKALMI 3* 7 Yayi zumbur ya mike tsaye ya dafe kirji yace farida me kike so ki fada min? Kina so kice min zaki kashe kanki ne saboda anti abida ta mutu? Ta girgiza kai tace bazan kashe kaina ba, saboda nima musulma ce. Rashin anti abida babban ciwo ne a zuciyata wanda bazan taba warkewa ba har abada, kuma duk sanda na ganka ko naji muryarka zaka zama min fami a wannan ciwon nawa. Ba lallai bane ka gane abin da nake nufi yanzu ba, kuma ba zan iya fada maka yadda zaka gane din ba. Ni kadai nasan abin da nake nufi da hakan. A sanadiyyar anti abida nasan ka, da ba zaka sanni ba ma balle ka fara sona, nima haka ba donn yakin da tayi ba da tuni na manta da shuraim a rayuwata. Abida itace silar hada soyayyarmu, naso ace abida na raye ta ganmu tare. Ta mutu ba tare da burinta ya cika ba, komai ya fita a raina tunda babu abida. Ya daka mata tsawa domin ya gigice gaba daya da jin kalamanta. Yace farida kin kuwa san abinda kike fada min? Anya kuwa kina cikkin hayyacinki? Ta fashe da kuka tace nasan abinda nake fada likita. Nayi sallama da kano ko hanya bana so ta biyo dani ta kano , tunda babu abida. Kayi hakuri ka yafe min, nasan irin ciwon da zaka ji a zuciyarka saboda nina fara shiga ciwon so kafin ka shiga. Sai ta mutsike wayar gaba daya ta rike a hannunta ba tare da ta mikawa yaya hussaini ba. Ya juyo ya dube ta cike da mamaki ba tare da yasan abinda zai fada mata ba. Dr shuraim yayi ta gwadar wayar, ya kira yaji an kashe mudik , sai ya sulale ya zauna akan doguwar kujerar falonsa yana sosa kai. Yace innalillahi waiinnna ilaihirajiun. Meyake shirin faruwa dani ne? Dama wannan shine cutar son da ake fada a gari? Ashe ban taba sanin so ba sai yanzu? Inama zan iya hakura da son farida in huta. Ya jawo wayarsa a sanyaye ya kira dr lukman. Cikin sanyin murya yace abokina kazo muyi magana ka bani shawara , don ina cikin masifa wacce zata iya kaini da kamuwa da son

Chapter 18 of 23