Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kwalbati. Allah Ya kiyaye basu fada ba, ya tashi hayaki da kara mai tsanani, sannan ya zuga da gudu kamar zai tashi sama. Kunsan yarinyar nan ko a jikinta, mutane babu wanda bai dora hannu a ka ba ya dau salati don ni sankarewa nayi a zaune wallahi na dade a daren banyi bacci ba. Dr lukman yace to don wannan ne ma shine kaki fada a gabata, kaga ka tayar mata da hankali har tana kuka. Dr lukman yace to don wannan ne ma shine kaki fada a gabanta,kaga ka tayar mata da hankali har tana kuka. Dr shuraim yace kukan munafunci ne, tasan abinda nake nufi ai tana shigowa ta kalli idona ta dauke kai, tasan na ganta kuma da zata lura dani tasan na tsani hawan acaba to yadda kasan tsokanata take yi, ina yawan hango ta ta dane. Da ace tasan ni ta san ra'ayina akan tsanar mace ta hau babur da sai ince da gangan take yi, don inji haushi. To bata sanni ba, amma tana bani haushi wallahi. Dr lukman yace ni kuwa yarinyar burge ni take yi, tana da natsuwa. Dr shuraim yace tana da hankali amma da ace zata rabu da hawan acaba da tafi hankali. Aisha farida ta shafa kirji tayi ajiyar zuciyar jin dadi, ta daga idonta sama tayi wa Allah godiya, sannan taci gaba da kasa kunne tana sauraronsu. Bata damu da mutanen da suke wucewa suna ta kallonta ba, ko tantama babu sun san gulma take saurare. Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin hankalinta ma idan yau na sanar maka cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun nan da danwake wanda kake ci kana santi kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan zan fada mata ta daho mana gobe. Shine daga shigowarta kuka hau yi mata shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi, data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba, duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus bane. *nxt page din is damaged, bana ganin rubutun sosai* Dr lukman yayi dariya yace zaka sake ganin hankalinta ma idan yau na sanar maka cewa ita ce mai yi maka daddadan dambun nan da danwake wanda kake ci kana santi kullum. Yanzu ma kiran da nayi mata kenan zan fada mata ta daho mana gobe. Shine daga shigowarta kuka hau yi mata shakiyanci, har kuka sakata kuka, shikenan duk kun huta gobe ba cin dambu. Dr shuraim ya sankare, ya dade baiyi magana ba. Sai dr mohd ne yace ba ruwana wallahi, data gaishe mu ma ni kadai na amsa, dr shuraim ne ya share ta. Dr lukman yayi dariya yace kai ka fara iskantarta kake cewa wai ko kanwar zamani ce, alhali lallabata nakeyi, don kada ta zata mun mayar da ita baiwar mu. Ko kudin na bata ba ta karba, duk kyauta muke ci in dai ba dubara ba zata karba ba. Gashi daga dukkan alamu ba su da hali sosai, dole ce ma yake sawa ta hau acabar ba zata iya biyan shatar adaidaita sahu ba, inajin kuma gidansu ba hanyar bus bane. *nxt page din is damaged, bana ganin rubutun sosai* Dr shuraim ya ja doguwar ajiyar zuciya yace Lukman don Allah da gaske kake ita ce ke dafa ma dambun nan da kanta?dan iska kace kakarka ce ko kakarku daya ne? Dr L yayi dariya yace ka taba ganin dangina a kano balle in yi kaka? wallahi itace ta ke kawo min da farko ma ajiya ta kawo ta dahowa kawarta an kwantar da ita anan asibitin to bata san an sallameta ba nace mata za mu dandana tace mu cinye dukka" dr Sh yace to me yasa ka boye mana kace kakarka ce take dahowa? Lukma yace kawai don inji dadin bakina ni ma kun koya min shakiyanci ne ai? Dr sh yayi shiru can yace kuma yarinyar ta tabbatar maka da hannunta take dafawa ko dai mamanta? Lukman yace eai kai me ye abun mamaki ta tabbatar min ita take dafawa zata min karya ne?Shuraim yace ashe alkawarinmu ya tashi ke nan da muka saka ran zuwa gaishe da tsohuwa mai dambu,ashe karyarka ce? Lukman yace ga yarinya mai dambu ta gaishe ka ka ki ka amsa ka yiwa kanka"shuraim yayi murmushi yace Daman ai don kai take yi ba don ni ba idan ka yi mana bakin ciki don kada mu ci to ai shi ke nan don ta ni mai sauki ne don kada mu ci to ai shi ke nan don ta ni mai sauki ne .kada yake Abbana fa ya kamu da son dambun nan jiya ma ya tambaye ni yaushe zan kawo masa dambun nan mai dadi inda ya sake son dambbun ma da nace ba na gidan sayarwa bane a gida ake yinsa na musamman ga tsafta" Lukman yace ka ci albarkacin abba bari in kirata ta zo in ce ta yi mana"dr shuraim yace kada ka bari ta san mune muke ci kasan abun da zaka fada mata"Dr L yace ban iya karya ba ko karyar kuma zaka koya mani? Ya dauko wayarsa ya lalubo sunan Aisha farida ba ta ankara ba ta ji wayarta tana kokarin daukar kara alhali ga ta a jingine a jikin kofarsu sai ta falla da gudu ta fita daga farfajiyar ofisoshin sannan ta matsa dr Lukmn ya ce kanwata kina kusa ne ki zo mana ina da magana dake"Aisha ta amsa masa na da yi nisa yayana sai nan da minti 30 zan karaso"yace babu komai sai kin zo tana ganin Dr Shuraim da Dr Mohd suka fita daga ofishin Dr Lukmn don kada ta zo ta same su ita ma saboda su din ne ta ki zuwa da farko da suka fice sai ta yi wuf ta fada ofishin.Dr L yayi murmushi da ganinta yace a'a ai ko minti 5 baki yi ba kika zo?ta ce Ashe zamu gama da wuri na dauka zamu dade kasan tafiya shi ne muka dan harhada kayayyakinmu"yayi dariya yace mata dai duk inda kuka je sai an barbaza shirgi wato dan zaman da kukayi asibitinmu har kun baza mana shirgi kenan? Aisha Farida ta yi dariya tace Wallahi kuwa don wasu jaka guda cika a nan suke cire kayan makarantasu wata ma jakar kayan siyarwarta a nan take bari duk a ofishin metron Maryam. Doctor ina so inyi muk dambu da danwake gobe, ina fatan kana gari ko? Yayi dariyar farinciki yace kai haba! Kina wahala da kanki, ki bari kawai. Aisha farida tace a'a ai nayi niyya ba a mayar da hannun kyauta baya. Dr lukman yayi dariya yace koda yake na bankwana ne ko? Gashi zaki tafi ba ganinki zamu dinga yi ba. Aisha farida tace haba yayana ko kasar ka bari inda hali ai zan ziyarce ka balle nan da nan. Ai duk sanda kake da bukatar dambu ko ba kai bane, ko abokanka ne kada kaji komai, kayi min waya kawai. Dr lukman yayi godiya yace to amma abin da yasa zaki sage min gwiwa idan na baki kudi ba kya karba, ni kuwa banga dalilin da tika tika damu mun daukar albashi mai tskoka zamu zauna muna tsotse dan alawus din dalibarmu. In kina so mu shirya to duk abin da na baki ki karba, idan da ciko na yadda ki cika mana idan babu yawa, idan kudin sunyi yawa ki rike canjin. Haka ake rayuwa, sai muma mu sami kwarin gwiwar cewa a kawo mana gobe. Aisha farida tace to yayana amma banji dadin kudin da zan dinga karba ba, adduarku manyanmu muke nema. Dr lukman yace kaji uwar iya magana, kin cika wayo kanwata. Baki tambaye ni laifin da abokina yake zarginki dashi ba. Kin fita kina kuka, na dauka kina shigowa abin da zaki fara tambaya ta kenan. Aisha farida tayi murmushi ta langabar da kai kasa tace bana son in cika tambayar manya, amma tambayar tana raina. Dr lukman yace uhmm aisha tsiri kenan, ko ba haka bane sunanki, don naji haka yahaya yake kiranki. Kina da hankali sabanin 'yan matan zamanin nan. Dr shuraim yace kina da hankali amma da zaki daina dane bayan acaba da sai kinfi hankali. Suka tuntsire da dariya su dukka. Dr lukman yace ai baya son yaga mutum akan acaba, musamman ma mace. Aisha farida tace a zuciyatya ni da acaba kuwa har abada, tunda yin haka zai jawo min samun kaunar wanda nake kauna. Kudin da dr lukman ya miko mata ne jimus dashi ya firgita ta, ta dafe kirji tace na meye wannan kudin? Karbi mana. Ya fada cikin tsawa a lokacin da yake zunguro mata kudin gabanta. Ta girgiza kai tace dr kudin yayi yawa fa. Yace nawa ne kike tunani? Naira dubu uke ne fa kawai, ba yawa don dai 'yan dari bibbiyu ne shiyasa kika gansu da yawa. Nifa bana son mu dinga irin wannan abun, ke fa ni yayanki ne. Bana son ina baki abu kina kin karba. Aisha farida tasa hannu biyu ta durkusa ta karba sannan tayi masa godiya tayi masa sallamaa ta tafi. Yau farin cikin da yake lullube a cikin zuciyarta Allah ne kadai Ya sani, saboda ta sami canji da yawa daga wajen masoyinta. Ba ta da wani buri wanda ya wuce ta ganta a wajen abida ta bata labarin abubuwan da suka faru tsakaninta da dr shuraim a yau. Ai kuwa tana isa gida ta iske abida a zaune ita da matan gida dankar suna hira, suna ta soya awarar siyarwa. Aisha farida ta kasa daurewa ta bari har sanda abida zata gama ta shiga daki sannan suyi hira don haka sai ta damko hannunta. Tace maman farouk zo muje ciki in baki sakonki daga shagamu. Abida na biye da aisha farida har cikin daki. Suna shiga aisha farida ta jefar da jaka. Tace Allah Shine Allah, Allah Shi ne mamallakin duniya da lahira, Shine mai yawan kyuta ba Ya gajiyawa. Tsarki da yabo sun tabbata ga Ubangijina, sarkin sarakuna. Bai haifa ba, ba a haife shi ba. Abida ta runguma aisha farida yayin da ita ma farin ciki ya lullube zuciyarta tun kafin taji abin alherin da ya sami aisha farida, ko ba a fada ba tasan akan dr shuraim ne. Tace alhmdl farida me ya faru? Dr shuraim ko? Aisha farida ta jawo hannun abida suka zauna ta jawo jakarta ta zaro kudin da dr lukman ya bata ta mika mata. Tace inji dr lukman suna son dambu da danwake gobe. Abida ta karba cike da murna, ta kirga ta daga ido ta dubi aisha farida ta harare ta. Tace na dauka dr shuraim ne ya baki kudin da kansa yace a yi masa? See Translation DUK KYAN TAKALMI 2* 10 Aisha farida tace antina kin cika gaggawa, karkade kunnenki kiji labari. Aisha farida ta zazzagewa abida labarin abin da ya faru yau a asibiti tsakaninta da dr shuraim babu dadi babu kari. Daga karshe ta zurawa abida ido. Tace kinji abin da ya faru, meye shawararki kuma meye abinyi nan gaba? Abida tayi dariya tace Ikon Allah kenan, farida kinga faidar addua ko? Kinga banbancin madanfaran bokaye ko? To duk abin da kike so ki nema a wajen Allah Shi kadai, kuma ki yarda Zai baki. Aisha farida ta gyada kai tace na yadda da haka na dade da yin imani da wannan. Abida tace a yanzu da Allah Ya sa shuraim ya sanki, yasan kina raye, yasan sunanki, yasan kina da amfani a wajensa, ya fara damuwa da rayuwarki, ya fara gane halayyarki, ya yabe ki da bakinsa. To anzo gangara, lokaci yayi da zan fada miki mataki na hudu da zaki taka. Aisha farida ta gyara zama ta dafe kirji da hannayenta biyu taja doguwar ajiyar zuciya tace Allah Ya sa zan iya. Abida tayi dariya ta dafa kafadar aisha farida tace kada ki damu, ba abu ne mai wuya ba, guda ukun na farko sun fishi wahala. Ai abin bi da bi ne, na daya yafi na biyu wahala, na biyu zai fi na uku wahala, na uku zai fi na hudu wahala, na biyar duk yafi su sauki. Har yanzu dai ajiyar zuciya aisha farida take yi, zuciyarta sai dukan uku uku takeyi don fargabar abin da abida zata fada, so take taji mai yiwuwa ne ko ba mai yiwuwa bane? Abida tayi shiru kamar mai tunani, can dagao ta kalli aisha farida tace idan na fada miki wannan mataki na hudu, ba wai ina nufin ki zubar da matakai uku na baya ba, a'a duk zaki hada kici gaba. Kici gaba da addua sosai ki ma kara wata akan ta da. Haka hakuri sai kin sake ci gaba sannan ki hada da na ukun ki rike mutuncinki sai na hudun da zan fada....saboda kaguwa aisha farida ta katse ta tace fadi na hudun wannene? Abida tayi murmushi ta gyada kai tace ki zamo mai yawan biyayya da ladabi a gare shi. Jikin aisha farida sai ya dauki rawa ta rike abida cike da rudani tace antina ban fahimce ki ba, ta yaya zanyi masa biyayya ni da ba ganina zai dinga yi ba, musamman ma mu da zamu bar asibiti? Abida ta mike ta dube aisha farida tayi murmushi tace haba farida bafa na son rikicewa, kina tsoron shuraim kamar wani malaikan da zai dauki ranki alhali TAKALMIN da zaki sura ne ki saka a kafarki. Ki dauki wannan ruguntsumin da ake ciki tamkar wasan 'yar tsana ne da yara suke yi, ki dauka tamkar wasan kwaikwayo ne don nishadi, ki dauka tamkar cartoon din tom and jerry ne da yara suke kallo a talabijin, sai ki daina fargaba. Ko kin manta DUK KYAN TAKALMI KAFA CE MAI TAKA SHI? Nace ki saka a ranki daurin dan kwalin da kike yi a kanki yafi wahala akan samun dr shuraim. Abu ne sassauka dalilina kuwa shine kince yana da ilimi, yana da wayewa, yana da tausayi uwa uba yana da riko addini, ma'ana tsoron Allah ne. To sai kibi duk hanyoyin nan da kika san yana so kiyi kane kane. Abin nufi ki zama mai amfani da iliminki duk abinda zakiyia agabansa, ki zama mai wayyayyen kai, idan yana wajen. Ki zama abar tausayi don ya tausaya miki, sannan ki nuna masa kinfi shi rikon addini, sai kiga hankalinsa ya karkato gare ki. Aisha farida ta dora hannu biyu aka tace anti kin sake rudani, don Allah yi min misalin yadda zanyi. Abida ta girgiza kai tace bazan fada miki yadda zakiyi ba, saboda ke mace ce, kuma nayi imani kowacce mace an haife ta da irin tata kissar a jikinta. Musamman ke aisha tun kina yarinya kin kware da iya zama da mutane da lafazai dadada. Haba kin manta zamanki a cikin tsofaffi ne? Kin manta halinki na kissa wanda ko zaginki akayi sai kiyi dariya ki ba wa mai zaginki hakuri? To shine wannan. Kije Allah Ya baki sa'a, sai mun hadu a mataki na biyar in kinci nasarar cinye wannan jarabawar. Abida ta juya zata fita, aisha farida ta lngwabe kai tace anti mataki na hudu yafi na daya dana biyu dana uku wahala. Abida tace hakuri yafi komai wahala, tunda kikayi hakuri zaki iya wannan. Idan baki gane biyayya ba, to bansan yadda kike so nace miki ba. To bari dai in baki misalain abin da nake nufi, ki durkusa har kasa ki gaishe dashi a duk inda kika ganshi, zaki fita daban daga cikin 'yan mata a idanuwansa, don 'yan matan yanzu basu da wannan tarbiyar. Ki rabu da hawan acaba tunda baya so, sauran kuma kinfini sani. Aisha farida tayi ajiyar zuciya tace sai yanzu na fahimce ki, godiya nake. Abida ta fice yayin da aisha farida ta daka tsalle ta rungume pillow gami da cewa waYyo shuraim dina. Da tazo kwanciya ta jima tana juyi, don tunanin shuraim yayi mata katutu a rai, ta rasa dalilin da yasa ta tsinci kanta tana cikin farin ciki yau. Ta kagu gari ya waye ta dauki dambu ta kai masa da alama hadin da sukayi wa dambun nan zaiyi dadi. Daga barci ya soma wartarta sai tayi firgigit ta bude ido ta jawo wayarta ta duba agogo tana gudun kada asuba ta shude su makara ba ta tashi ta dora dambu ba. Karfe uku saura ta mike taje tayi alwala tazo ta fara sallah. Rakaoi ba adadi, doguwar sujjada take yi tana zayyanowa Allah yadda take so ta kasance a cikin zuciyar shuraim. Karfe hudu da rabi ta fita ta fara kokarin dora dambu don ya turara sosai, bayan ta dora da jimawa sannan taji motsin fitowar abida daga daki. Abida ta shigo dakin ta dube ta tayi dariya. Tace kaji mai himma, wato kin daura dambun tun kafin assalatu tayi, koda yake aikin shuraim ne babu bata lokaci. Aisha farida tayi murmushi ba tare da ta bata amsa ba, saboda tana wuridi. Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen food flask guda 2 manya,daya a shake da hadadden dambu daya a shake da danwake sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya man gyada zaryan aka soya da albasa sai kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka shi kanana da tumatir da albasa da kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa da wuri ba. Karfe 8 saura kwata a babur din a daidaita sahu ta yi wa aisha Farida ita da kwandunan abincinta har guda 2.ba ya ga kayataccen food flask guda 2 manya,daya a shake da hadadden dambu daya a shake da danwake sai farantunan tangaran 3 sai cokulla sai wasu robobi 3 yan kanana masu murfi daya yaji ne mai dadi gaske ya sha maggi daya man gyada zaryan aka soya da albasa sai kamshi yake dayar kuwa salad ne aka yanka shi kanana da tumatir da albasa da kokunba.ta isa ofishi kanta tsaye babu shajja ba tsoro,don ba ta ga motar gogan nata ba tasan bai iso ba don bai saba zuwa da wuri ba. Ta kwankwasa kofa sai ta murda ta tura kai dauke da kwandunan abinci riki-riki a hannunta ta yi sallama ta shiga sai ta ga wayam babu kowa a ofishin.babu tantama ko ya shiga bandaki ne don haka sai ta daiki gwandunan ta tura lungun da take ganin yana ajiyewa dan ta kawo masa.tana tsaye a gaban teburin tana jiran ya fiti amman shiru kuma abun da ya bata tsoro ba ta jin motsin komai a bandakin. Motsi ta ji an turo kofa da karfi yayin da ta waiwaya da sauri fuskarta cike da fara'a tana murna da ganin yayanta.tace a ranta ashe ba'a bandaki yake ba yana waje"sai dai kash da ta hada ido da mai shigowar ba fuskar Dr Lkman ta gani ba tayi matukar firgita gami da razana a bayyane wanda shi kansa wanda aka yi razanar dominsa ya gane. Kallonta yake yi a nutse har sai da ya shigo cikin ofishin ya mayar da kofar ya rufe ya fara tafiya a hankali zuwa gaban teburin kusa da inda take a tsaye. Numfashinta ne yake kokarin daukewa, idanuwanta kuwa sai suka kasa tsayawa a waje guda suka dauki farfari yayin da ta nemi yawun bakinta ta rasa, balle ta samu damar fitar da lafaxi guda daya. Ya dauke kansa daga kanta ya zagaya ya jawo kujera ya zauna yaci gaba da bincike wani file. Da taimakon addoui aisha farida taji numfashinta ya daidaita, ta sami nutsuwa a cikin zuciyarta. Ta dube shi cikin kunya hade da ladabi ta sunkuyar da kai kasa, sannan ta kaskantar da muryarta kasa ta zakaka makoshinta, ta duka har kasa ta gaishe shi. Dr shuraim ya daga ido ya dube kasa kasa da alama yaji dadin yadda ta gaishe shi, sai ya amsa cikin sakin fuska. Ya kara da cewa kina neman lukman ne ko? Ta gyada kai ba tare da ta iya hada ido dashi ba, tace eh. Ya dube ta da gefen ido yace ai bai karaso ba, sai anjima nine na bude ofishin. Aisha farida ta duka tace nagode. Sannan ta juya zata fita. Kamar a mafarki taji yayi mata magana. Babu abinda za'a ce masa? Ta juyo a nutse ta dube shi sannan tayi masa wani dandasheshen murmushi, wanda ta tabbatar an sha tabbatar mata idan tayi shi yana kara mata kyau. Siririyar wushiryarta ta bayyana yayin da kumatunta gefen dama ya lotsa, fararen hakoranta sai su sake haske. Tace dama sakonsa ne na kawo masa, gashi can na ajiye masa. Sai ta nuna lungun data ajiye kwandunan. Ya wurga dara dara idanuwansa ya kalli wajen sannan yaci gaba da dube duben file dinsa. Har yanzu aisha farida tana tsaye a jikin kofa ta rike kofa ita bata fita ba, ita bata dawo ciki ba. Ya dago da kai a hankali ya dube ta, yayin da ita kuma ta sunkuyar da kanta kasa a hankali. Yace okay zan fada masa. Tace kace masa kanwarsa ce aisha farida umar. Ya dago da kai ya dube ta da alama yaso yayi mata wata tambaya ya fasa, sai ya gyda kai yace idan nace masa kanwarsa mai hawan acaba ai ya sani. Sai ta ya danyi murmushi lokacin da yake karshen maganar. Ta langwabe kai ta marairaice ido kamar mai shirin fasa kuka. Tace yaya lukman ya fada min laifina jiya, nayi kuskure bazan sake ba, nima nayi tunanin naga ban kyauta ba. Sai ya kalle ta kawai ya ci gaba da rubutu, can yayi magana ba tare da ya sake dubanta ba. Yace hakan dai zaifi, ki yiwa kanki fada, don ke mace ce, a addinance ma bai dace ba. Dan wasu 'yan acaba ba su da hankali. Ta duka tayi masa godiya ta murda kofa ta fita. Ta jawo kofar a hankali ta tafi. Taji kamar ta fasa ihu, ko ta daka tsalle ta dire don murna. Ta shaki iska ta lumshe ido ta daga ido sama tayi wa Allah godiya gami da yiwa alkawarin zata yi ma Sa azumi gobe don godiya, da Ya fara karkato da hankalin dr shuraim kanta. ALLAH ABIN GODIYA!! BABI NA GOMA Nan da nan aisha farida ta ajiye aikin ta take yi ta jawo gyalenta da sauri ta biyo dan aike ta fito don taga mai sallama da ita da yammacin nan. Tana fitowa sai taga muazzam ne. Sai ta ji farin ciki ya rufe ta, tayi sauri ta durkusa har kasa ta gaishe shi, yayin da ta nemi izini a wajensa zata shiga ta dauko sallaya ta shimfida masa akan dakali. Sai ya dakatar da ita, yace ta bari kawai daman daga wajen aiki yake hanya ta bullo dashi tanan, shine yace bari ya karaso su gaisa. Aisha farida tayi murmushi ta lngawabar da kai tace sai in rasa harshen da zanyi amfani dashi wajen gode maka yayana. Allah Ya saka maka da alkhairi da wannan zumuncin da kake gudanwarwa a tsakanin mu, nagode. Ai na sayi waya da wannan kudin da ka bani, ashe ban karbi lambarka ba, na rasa inda zan nemo ka, dole na hakura. Na kagu inji halin da kake ciki, kai da janan. Muazzam ya lumshe ido yace alhamduliilahi kanwata, naga falalar addua da hakuri, kuma na rike mutuncina yadda kika ce. Naje mata da siyayya iri iri na kaimata, ko kallona takiyi. Sai na sami waje na zauna nace mata janan ina so ki saurari bayanina kiji dalilin zuwana wajenki yanzu. Ada na soki ba kya sona, a yanzu naso ki bakya sona, don haka na hakura ba a dole a soyayya. Allah Ya sauya min da wacce take sona har ma an saka mana ranar aure. Kiyi hakuri da takura miki dana yi a da. Ina so a yanzu ki saki jikinki dani, ki dauke ni a matsayin yayanki, kuma lauyanki bayan nan babu wata alaka tsakanina dake. Ina gama fada naga alamaun jikinta yayi sanyi. Kullum naje sai inga tana yawan kallona tana kuma bude baki tayi min magana, duk tambayar da nayi mata. har na hada baki da wata matar yayan, sai tayi ta kirana a waya a dai dai lokacin da nake tare da jana, sai na dinga amsawa kamar da budurwata nake magana. Sai inga fuskarta kamar bata jin dadi. Aisha farida ta cika da mamaki tace duk a kurkukun ake wannan? Barr muazzam yace eh ai ana bari na in shiga sai a kirawota a hado ta da maikaciyar kurkukuk daya,ta kawo ta inyi mata tambayoyi saboda neman hujjojin da zan bayar da kuma nemo shaidu a kotu. Aisha farida tace lallai ni abin da na lura janan tanan sonka, tsabar jan aji take yi maka don ta tabbatar kana sonta, kuma baka fushi duk wulakancin da zatayi maka. Muazzam yace haka ne wallahi, sai yanzu na yadda da haka. Ai nuna mata nake bata gabana kwata kwata yanzu. Baraka ma ta samu sauyi na fada mata duk yadda zatayi, kuma ta aiwatar tana addua kuma tana hakuri, sannan kuma tana jan ajinta tana yi masa girki, ta tsaftace gida, ammma ta fita harkarsa bata bari ma su hadu a gidan, kwana biyu ko uku tana gidan bata bari ya ganta. Sai gashi yana fada min wai baraka ta sauya halinta yanzu ta daina damuwa dashi, in bashi ya leka dakinta ba, ita ba ta fitowa. Sai na kalle shi na watsar nace au har dakinta kake takawa ita da kake korarta da idan ta shiga dakinka? Sai yace ai dole in leka inga halin datake ciki, kar inje ta shiga daki ta kashe kanta ko ta hadiyi zuciya ta mutu. Nace masa ashe kasan kana kuntata mata har zata iya hadiyar zuciya ta mutu ko? To kaji tsorn Allah. Sai yayi shiru bai ce komai ba. Itama barakar take cemin wallahi ya fara sauyawa, yanzu da kansa yake dawowa gida yaci abinci, dga lokacin cin abinci yayi, da kuwa har kifarwa yake yi a gabanta idan ta matsa masa yaci. Aisha farida tayi dariya tace alhamdulillahi, Allah Ya kara yi mana jagoranci. Barr muazzam ya dube ta yace ni naga duk kin rame, lafiya kuwa? Ko dai shuraim din ne ya taba min ke? Aisha farida ta girgiza kai tace babu ruwansa bawan Allah, wlhi antina ce abida bata da lafiya sosai, gabobinta gaba daya tun daga kafa har wuyanta duk inda mahadar kashi take ta kumbura suntum, tana yi mata ciwo, da kyar take tafiya. Shien muke ta sunturi asibitin kashi na dala (autopeadic). Anyi xray da gwaje gwaje sunce basu ga komai ba, ciwo kima sai karuwa yake. Yanzu da kyar take iya takawa komai sai anyi mata. Shiyasa kaga duk na susuce. Subhanallah, Allah Ya bata lafiya. Inji barr muazzam. Aisha farida tace amin ai munyi sati biyu da barin asibiti, rabona da dr shuraim kenan amma akwai cigaba sosai. Ta zayyanowa barr muazzam labarin abubuwan

Chapter 13 of 23