Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zaro dukka kudin da yake jakarta, dubu daya da dari biyu ne kacal sai 'yan canji. Ta miko min naira dubu daya, na karba nayi ta godiya. Tayi ajiyar zuciya tace wallahi dr ya cuce ni, na kashe kudina a banza ko gezau baiyi ba. Na fada cikin marainiyar murya nace karki damu kaddara ce Allah Ya aiko mana. Sai nayi sauri na gyara zancen son naga tayi sauri ta dubeni, sai nace ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, tunda ya shafe ki nima ya shafe ni. Bakiji yadda zuciyata take tafasa ba don takaici. To shi dr dame yafi sauran likitoci su basa wulakanci sai shi? Khadija tace yafi sauran mana ke kuwa, shifaa a london yayi karatunsa, ke har pri sa secondary duk a can yayi rabin rayuwarsa, sai da yazo nigeria fisha ya tafi. Ance dai yayi aiki a asibitin nan shekara 2 a lokacin yana karamin likita. Sai ya koma ya sake shekaru hudu ya zama consultant sannan ya dawo kwanan nan. A bangaren ilimi addini kuwa a saudia yayi karatun kurani, larabawa suka koyar dashi, ance yafi kowanne likita sanin kurani. Don tun yana yaro yaje saudia sai da ya sauke ya dawo london, ya karasa primary kinga kuwa Allah Ya yi masa baiwar da ba kowa yake da ita ba. Gashi dan attajiri shima attajiri, ga ilimi dukkan bangarorin biyu, ga wani kyau tamkar sai da zaba aka bashi. Kowacce mace dole taso shi, sai dai idan ta ga ba ta samu bata hakura irina. Maryam ahmad ma na gano sonsa takeyi, har wani kishi takeyi dani, nace kije na bar miki in dai shureim ne zaki gaji ki kyale shi. Amma ke aisha farida naga bai dadaki da kasa ba, ko zancensa ma ba kya so. Kowa yana yabon kyawunsa, ke ko ki kula. Baiyi miki bane? Sai naji tamkar an saki bom a kahon zuciyata, saboda faduwar gaba. Nayi firgigit nace yanzu khadija ina ta kaina ina ni ina cusa kaina wajen irin wannan halitta? Ai sai ku kyawawa, masu mota 'ya'yan attajirai. Khadija tace kin hutawa kanki wallahi kina burge ni yadda kike tafiyar da rayuwa, ba kya jajubo wa kanki abun da zai wahalar dake. Nima nayi nadama ba zan sake shiga irin wannan hatsarin ba. Yanzu mun bata da malaman nan makaryata, wai yaga aurenmu har da haihuwar 'yan biyu. Shine ai na saki jiki nayi ta tura musu kudi suna cemin zai zo da kafarsa nemana ga mutum kamar zai yayyaga ni cikin waya don masifa. Bani ba wani malami ai yanzu na rufawa kaina asiri nace mohd ya aiko da iyayensa muyi aure. Ina laifinsa yaro matashi, yana da mota da gidan kansa da aikin bankinsa, nima da aikina ya ishe mu rayuwar duniya. Sai naji hankalina ya tashi, dana sani ta afko min. Na gyara zama nayi tagumi ina duban khadija na rasa in da zan saka raina, sai yanzu na fara gane kuskuren da na tafka a rayuwa. Ummi ta cuce ni. Na fada a cikin zuciyata yayin da hawaye ya cika min ido. Nace da khadija kina so kice min gaba daya asirin da malamanki suka sha zabgawa ko daya bai taba shi ba, asiri baya cinsa kenan? Tace baya cinsa tunda bai ci shi ba, babu abin daya yi masa. Malamina daya ne ya fada min gaskiya tun da farko naji haushinsa, daga karshe na gane gaskiya ya fada min. Yace dani yaron nan da kike so gaskiya ya rike adduar neman tsari dare da rana, da wuya a jefe shi ya taba shi, sai dai kawai kije kiyi addua in da alkhairi Allah Ya hada ku ta wata hanyar, a dadin rai yazo, kuma ina so ki sani ba'ayiwa Allah dole. Khadija tace aiki ma daina damuwa, Allah Ya ganar dani har na dade ina istigfari. Su maryam anmad ne suka rage suma Allah Ya ganar dasu. Shiyasa aka ce wani kyau bala'I ne, sai a dilmiyar da kai in bakayi taka tsan tsan ba. Yanzu dr shureim in ba don Allah Ya sa nutsatte bane da mata sai sun halakar dashi. Haka ma mace mai kyau idan baatayi a hankali ba maza su halakar da ita, su rude ta da kudi tabi su koda kuwa tana da aure. Ke dai Allah Ya sa mu gane gaskiya. Sai naji khadija ta burge ni, tafi ni gaskiya. Ina ma a llokacin da naje neman shawara wajen ummi khadija na samu ta fada min abinda ta fada yanzu, da ba wa zuciyata hakuri, da ban je na jefe kaina a rigima ba. Yanzu gashi komawa gida ya gagareni. Da me zan biya wannan dimbin bashin na kaina gashi babu alamar nasara a aikin malamin. Khadija ta katse min tunanina tace duk inda ya kai da takama da kwalliya, da yanga karshen alewa dai kasa. Dole mace zai aura, ba auri kansa da kansa ba. Kuma dole yayi 'yar murya kafin a bashi ita, dole ya kashe kudi ya bauta mata saboda Allah Ya wajabta masa ciyarwarta, sutura, kula da lafiyarta, muhallinta da duk wata dawainiyarta. Daman dai ance DUK KYAN TAKALMI dole kafa ce zata saka sannan a taka kasa. Lallai zanso inga irin macen da zai aura, karshenta fa ya kare a mummuna, baka, 'yar talakawa, kinsan karshen irinsu kenan. Nace yana da mata fa har da 'ya, kema kinsan dr shuriem ba zai auri kucaka ba. Khadija tace ke aisha farida wa ya fada miki wannan? Nayi murmushi nace matarsa ma baturiya ce a london suka hadu, a london take zaune. Da bakinsa naji yana fada. Kuma a gabana sukayi waya da ita cikin harshen turanci ko hausa bata ji. Khadija ta gyara zama tace don Allah da gaske kike? Ni da kin fada min haka tuntuni ai da ban wahalar da kaina ba wallahi. To wai ina kika ganshi ne har kika ji yana waya, nifa tun ganin nan nasa da mukayi yana motarsa ban sake ganinsa ba. Ko dai ba shi kika gani ba? Nace shine wallahi, abokin dr lukman ne, likitan kwakwalwa wanda matron maryam take aikena wajensa. Kinsan tana da kanwa mai matsalar kwakwalwa, to yana duba to ko ba ranar clinic ba. Khadija tace lallai ba zai saurari kujari-kujari irinmu ba, mai mata baturiya mai zaiyi damu? Naji zuciyata tana kokarin bugawa, sai na mike na tayar da sallar la'asar daman da alwalar azahar dina bamu dade dayi ba. Nayi sallama nayi addua, Allah Ya biya min bashin da yake kaina. Na yunkura zan mike in tashi, sai khadija tace dani aisha farida gaskiya akwai abinda yake damunki, saboda duk jikinki yayi sanyi, yanzu ko yanayin sallarki ya canza ba irin na da ba, ba kya samun nutsuwa wajen yin sallh, kin daina doguwar addua bayan kin idar da sallah. Nayi shiru ina tunani nace a raina yanzu son dr shureim har addinina zai taba, bayan karatuna da ya tava ga zaman lafiya dana rasa. Sai na zuba wani zazzafan hawaye nayi sauri na boye fuskata don kada ta gane. Na dauki jakata na rataya nace mata zan tafi gida. Ta rako ni har bakin titi na hau acaba na tafi, ita kuma ta koma gida. Sai a hanya na fara tunanin halin da zan fada idan naje gida, don haka nace dan acaba ya kai ni zango gidan ummi kenan. Ina isa cikin gidan na tarar da kofarta a kulle alamar bata nan, sai naji banji dadi ba don haka na leka bangaren faccalarta na tambayeta. Tace min bata nan tun jiya ta tafi. Sai naji zuciyata ta buga na dafe kirji na tambaya kafiya? Ta tafi unguwa tun jiya bata dawo ba? Amsar da ta bani itace babu komai. Na sami kujera na zauna nace da ita ki fada min gaskiya, ummi kawata ce bata boye min komai. Sai tace to kiyi mata waya mana sai ta fada miki da bakinta tunda aminiyarki ce. Na jikina a sanyaye nace to sai anjima na tafi. Sai naga ta bini da kallo alamar tausayawa tace dani gaskiya ummi tana gidansu mijinta ya sake ta. Kuna fita shekaran jiya ya kai mata takardar sakinta gidansu, ashe bai bata izinin fita ba ta biki kuka fita har ina cewa ku jirani in shirya kuka ki. Na dawo na tsuguna a gabanta nace innalillahi wainna ilaihir rajiun. Yanzu yassar saboda dan wannan dalilin ya saki ummi? Tace a'a ba wannan kadai ba, daman akwai wata kasa. Ummi bata da kunya, ga ta da bin bokaye da 'yan tsubbu kowa yasani, mijinta ya sani saboda yana tono binne binnen da takeyi, da kuma barbade barbade da takeyi masa a abinci. Da zarar sun fada mata karya sai ta zai tana habaici ta bata da kowa, har uwarsa da ta haife shi bokanta yace uwar mijinta bata sonta. Yanzu ya dace ace ummi tazo ta zazzageni? Jiya ita da kannenta da kyar aka fitar dasu daga gidan nan wai sai sun dake ni. Har da cewa yadda na raba zamanta da mijinta nima zamana da mijina sai ya kare, sai in babu malamai a kano. Kinga kenan malaminta ne ya fada mata ina yi mata asiri. Ta tabe baki ta harareni tace to ai fitar da kukayi gidan boka kuka je, saboda yassar yabiku a baya har yaga inda kuka nufa, shi yasa ya kai takardar sakinta gidansu. Ko kin dauka ban gane ki bane munafuka kin san inda take. Aiko ki tayi kizo ki barbada min wani abu ko? Na zabura na mike tsaye na dafe kirjina nace ni?? Wallahi bansan ummi ba ta nan ba da bazan zo ba. Ba na irin wadannan halayya kuma ba da wata manufa nazo ba. Tace dani fita daga gidan nan kafin in tara miki jama'a. Kuma duk ranar da kika kuskuara kika hadu da yassar yace sai ya balla miki kafa, tun a sakandire kike yi mata hudubar tsiya, yasan kin tsane shi, shine kika biyo ta har gidan aurensu kika kai ta gidan boka, wato a kashe shi kuci gado ko? Tunda nake a duniya ba a taba yimin cin mutunci, kazafi da wulakanci irin na wannan ranar ba. Duk irin gulmace gulmacen nan da ake yi a lungunmu tun ina yarinya ba ataba cewa ga abin da aisha farida tace ba. Lalli na jefa rayuwata cikin wani mawuyacin hali saboda son dr shureim imran. Na gaggauta ficewa daga gidanta kafin ta tara min jama'a kamar yadda ta fada, kuka nake wiwi na hau acaba ba tare da nasan inda na nufa ba. Sai da dan acaba ya tambaye ni sau uku hajiya ina zan kaiki? Sannan nace ka kaini gadon kaya. Gidansu maryam ahmad kenan. Ita ma inje inji halin da take ciki da dr shureim dinta. Duk da haka ban daina sonsa ba. Maryam ahmad tayi mamakin ganina, amma ganin ina fara'a ta san lafiya kalau kenan. Tace dani shegiya aisha farida umar daga ina kike, ba ki koma gida ba ne har yanzu na ganki da uniform a jikinki? Nace ke dai bari, yau bana jin komawa gida da wuri, zumunci nake ji, zuwa nayi in gaishe da su mamarki. Sai taji dadi taja hannuna har dakin mahaifiyarta muka gaisa, na gaisa da kannenta da 'ya'yanta biyu wanda Allah Ya yiwa mijinta rasuwa ya barta dasu amma fa da dimbin dukiya. Muka koma dakinta muka zauna akan wani makeken gado, ta kunna mana AC yayin da ta dinga kwallawa 'yan aikin gidansu kira suna kawo min abubuwa kala kala kamar su juice, kayan marmari, cincin da cake. Sai taga duk na kasa ci sosai, ina yawan yin shiru idan tana magana kamar hankalina baya tare da ita. Sai ta zungureni nake dawowa hankalina, na rasa yadda zan dauko mata maganar dr shureim domin kada ta zargi wani abu ta gano saboda zancensa na zo gidansu. Domin ban taba zuwa ba gidansu haka kawai ba, sau daya na taba zuwa kuma daga makaranta muka zo muka yi mata gaisuwar mijinta, da yake gidanta na kallon gidansu ne. Muka shigo nan ma muka yi mahaifiyarta, to anan na san gidansu. Da kanta ta dauko min hirarsa tace baki tambayeni likitana ba dr shureim. Sai na zauna dai dai nace yaya akayi? Ki bani labari, akwai cigaba ko? Tace wanne ci gaba ni da tun kafin aikin da na rabawa malami bai je ko ina ba abu ya dagule gaba daya, nace to su daina adduar yafi karfina. Dr shureim yafi karfin ya kwanta in taka shi da takalmin kafata, kinji. Anya mutumin nan haifarsa akayi ba tikowa yayi daga sama ba? Ace mutum ya hadu ta ko ina babu aibu a tattare dashi? Sai naji na kara tsanar kaina, na fada cikin shamulalliyar murya, me ya faru? Tace mutuminki na same shi a ofis dinsa wancan sati, malamina ya bani laya na kunshe a karkashin harshena wai in dai da layar nan duk abin da nace masa ya zauna babu musu. Bayan turarukan da na dume jikina da goshina dasu, wasu masu wari kamar na 'yan bori, ni kaina sun isheni da wari balle shi dan gayu. Ina shiga kaina tsaye ko fargaba banayi saboda an bani tabbaci, ni kuma na yarda da cewar na same shi na gama kamar yadda suka bani tabbaci. Shi da wata likita mace ina jin dai daliba ce, bata gama ba. Ta cika tayi taf kamar zata fashe saboda fushi. Ta wani galla min harara nima na harare ta saboda abin da ya kawo ta shi ya kawo ni. Da na gaishe su babu wanda ya amsa sai na sami kujera na zauna a kusa da ita, shima yana zaune a kujerarsa. Ya juyo ya dubeni sarai sannan ya dukar da kansa yaci gaba da rubuce rubucensa. Ya gama ya mika mata takarda, gami da cewa Allah Ya sawake jeki. Ta tabe baki ta dubi takardar da alama magani ya rubuta mata sai tace inje in sha wannan kenan? Ya ce eh In sha Allah kurajen zasu warke. Sai tace doctor muje ka kaini chemist din mana, nina fi so ka tabbatar masu kyau ne. Sai ya bata rai yace ba aikina bane in rubuta miki magani, kuma in raka ki zabar miki wanda zaki saya ba, komai a rubuce yake zasu karanta su baki. Tace kaki zuwa ka duba ni a gida, kwanana biyu ban fito ba har waya nayi na fada maka. Na turo maka sakon adireshina kaki zuwa. Sai ya harare ta yace bani da lokacin zuwa duba dalibaina don basu da lafiya. Ta sake turo baki tace amma ai daliban daban daban ne, ba daya nake da sauran ba. Ya daka tsawa ya zazzare mata ido yace dalibaina dukka daya suke, daidai kike da wannan. Ya nuna ni, ita kuma ta wurgo min harara, nayi murmushin jin dadi nima na harare ta sama da kasa. Yace idan baki da abin da zaki fada min mai ma'ana game da karatunki ki tashi ki tafi, kada ki kara shigo min ofis. Ta fice sai ya juyo wajena ya tambaye ni cikin fushi, ke kuma fa? Menene? Ina fitowa na kira malamin da ya bani laya da turaren nan mai daga hankali don wari kamar na 'yan bori. Yana daukar wayar sai yace malama an sami nasara kuwa? Nace nasarar me mutum kamar zai mare ni? Sai yace to an sami kuskure ne daga wajenki ina ganin baki yi yadda nace ba. Nace komai daidai nayi banyi kuskuren komai ba. Yace yaushe zaki zagayo sai in sake bincikawa muga ta hanyar da zamu sake bullowa kuma? Nace Allah Ya sawake in sake kashe wani kudin bayan wanda na tula maka na baya har da yankan rago amma a banza..... Kafin in rufe bakina ya kashe wayarsa, nayi ta kira har yau a kashe. Ko yau ma na gwada a kashe, yaga na gane shi dan damfara ne babu abin da ya iya. Haka nabi duk sauran malaman naci musu mutuncu sukayi ta kame kame, sai yanzu na gasgata cewar malaman zamanin nan sun raina wa mata wayo, sun mayar dasu jahilan karshen zamani. Idan kura tana maganin zawayi tayi wa kanta, ke kina ganin malaman kinga wahalallu masu matsala sun kasa maganin matsalarsu, wai suce zasuyi wa wani maganin matsalar su, sai suyi ta canke canke don basu ma san ya ake duban ba. Ai ni na dawo daga rakiyarsu na goge lambar kowannensu, ko sun kira ni tsuye su nakeyi, sai su waya da sauro. Ko wata na gani zata bata lokacinta wajen bin malamai zan hanata sai dai idan taki yadda in kyale ta, idan taje taga uwar bari zata dawo da kanta tayi min bayani. Duk wadannan bayanai da maryam keyi tuni sun ragargaza min zuciya, kwakwalwata ta riga ta dau gobara, na rike kai kawai tamkar mai ciwon kai yayin da na sulale na kwanta akan gadonta tamkar sumammiya. Na yarda da cewar komai ya sami bawa rubutacce ne, in ba haka da ya za'ayi tun farko inji wadannan labarai akan malamai kuma in dauki zunzurutun kudi in kai wa wani? Nace a raina me yasa na fara zuwa gidan ummi neman shawara banzo wajen khadija da maryam sun fada min halin malaman zamani ba? Tun daga lokacin na tabbatar kudin sun mula kuma ba zan sami dr shureim ba. Maryam labari take bani kala kala, amma bana fahimta ina can ina tunanin abin da zanje in tarar a gida, haduwata da uwani mai adashe da sauran makoftan da na ciyo bashi, sannan bayanan da zanyi wa yaya hussaini in da naje na kai dare bayan tun karfe biyu na rana muka tashi. A gidan su maryam nayi sallar magriba, na yi ishai muka ci abincin dare. Taga bani da niyyar tafiya sai ta fara mamaki, tana jero min tambayoyi iri iri kasancewar ta sanni ba mai bin gidan kawaye bane kwata kwata balle tace na saba daman. Sai da na fuskanci har ta fara gyangayi , tara da kwata na dare sannan na fara haramar tafiya gida ba don naso ba, saboda niyyata sai karfe goma sha daya na dare zan koma gida kafin nan kowa yayi bacci. dole na fito ta raka ni kofar gidansu na hau babur na tafi. Ina tafe ina adduoi har na isa unguwarmu, daga nesa da gidanmu nace mai acaba ya sauke ni, don bana so 'yan gidanmu suji karar babu na san idonsu yana kan hanya suna zuba idon dawowata. Na biya dan acaban kudinsa yayin da nake tafiya tamkar hawainiya ina yi ina waige waige tamkar barauniya. Da sanda na shiga zauren gidanmu naci sa'a babu 'yan matan gidan masu zance a zaure da samarinsu. Sai na leka tsakar gidan, nan ma ban ga kowa ba. Sai na cire takalmana na rike a hannuna ina sanda dana zo giftawa ta windown dakin uwani sai na tsugunna nayi duku duku na wuce don kada taga giftawata, najiyo motsin mutum a daki ina kyautata zaton ba ta yi bacci ba. Da yake babu wuta sai hasken fitilar kwai da kyandira zaka dinga hangowa a dakunan don haka na hango kyallin kyandir a dakin abida ina hango inuwarta a tsaye jikin labule, sai dai ba zan tantance abin da takeyi a tsaye ba. Na duba kofar dakin sai naga takalman yaya hussaini da alama ya dawo, nan da nan tsoron da nake ciki ya karu. Nayi maza na tura kofar dakina na shiga na iske ta shimfidar da 'ya'yanta ta rage hasken fitilar kwai a gefe. Shiga ta dakin ke da wuya ko jakata ban ajiye ba naji motsi a kofar dakinmu, nan da nan na tsuguna na takure a lungu. Sai na sankare saboda firgici. Abida ce ta shigo hankalinta a tashe, tana ambaton subhanallahi, yaya zanyi yau. Tana rufe bakinta sai muka hada ido yayin da zaka dinga hango mamaki a cike da fuskarta gami da firgici. Ni kuma ina tsugunne ina kokarin daidaita numfashina domin na shide, don tsoron yaya hussaini da uwani a tunanina daya daga cikinsu ne. Aisha farida lafiya? Yaushe kika dawo? Ina kika shiga yau tun safe? Abida ce ta jero min wadannan tambayoyi masu wuyar amsawa. Na mike tsaye a sanyaye ba tare da na san abinda zance mata ba. Ta sakke kallona tace da ban ganki ba yanzu da kin jawo min masifa yau, saboda yanzun nan yayanki ya shigo ko minti biyar baiyi da shigowa ba, ya shigo da ciwo a kafarsa sun fadi akan babur shine yace in taso ki, ki rubuta masa allura ko maganin da zai sha ko ki dauko akwatin taimakon gaggawa (first aid box) ki zo kiyi masa dressing. Na kasa ce masa bakya nan, shine na shigo nan ina tunanin abin da zance masa. Ina kika shiga kika sa hankalina ya tashi ko abincin dare banci ba? Me yake faruwa tsakaninki da uwani tayi ta zuwa nemanki ranta a bace tunda rana? Na zazzare ido nace me tace miki? Abida ta girgiza tace nayi nayi ta fada min dalilin nemanki din da takeyi, sai tace inkin dawo in tambayeki ita ba zata fa. Ranta fa a bace har zage zage nake jiyowa tanayi daga dakinki. Ke kuwa aisha farida me ya hadaki dasu uwani ke da ba a zama a yi gulmar wani dake, me ya kai ki tsoma baki a maganarsu? Nasan wata gulma suka hado aka ce dake a ciki, to ni shawarar da zan baki gobe da sassafe kafin ki fita kije ki samu uwani ku sulhunta, idan kinsan kin fada ki basu hakuri, idan baki fada ba ki wanke kanki tun kafin yayanki yaji abinda yake faruwa yaci miki mutunci, kinsan halinsa. Duk kin susuce a kwanakin nan kin canja halinki sai kiya ta nuku nuku kamar mara gaskiya. Nayi shiru ina sauraronta yayin da na cire kayan makaranta na saka doguwar rigar baccina na saka katon hijabi na dauko 'yar akwati na wuce gaba, tana tsaye tana kallona cike da mamaki da takaici. Nayi sallama a kofar dakinsu, yayi min izini na shiga, na durkusa na gaishe shi yayin da ya miko min kafarsa naga ciwon nayi masa sannu da adduar Allah Ya kiyaye gaba. Sannan na bude akwatin na shiga aikin saka iodine da auduga. Ita kuwa abida tana can tana kinkimar 'ya'yanta daya bayan tana kai su fitsari. Naga gama masa yayi min godiya na fito. Har yanzu abida na dakina tana jirana bata gama jero min tambayoyin da suka cika zuciyarta dam! Ta dube ni ta yatsune fuska tace baki fada min ba fa in da kika je ko daman kinsan da maganar su uwani shiyasa baki dawo gida da wuri ba? Na bata rai na turbune fuska nace ni ba wannan bane ya tsayar dani, bayan mun tashi daga asibiti aka ce mu dawo za'ayi mana darasi daga karfe hudu zuwa shida, wani sabin likta ne zai gabatar da wata sabuwar cuta shine naga ba zan iya dawowa gida ba in sake komawa da yamma ba, sai nabi khadija sani gidansu da yamma muka koma, bamu baro asibiti ba sai da karfe bakwai ana sallar magriba, tace inzo gidansu idan nayi sallah sai in wuce. Shine kuma muka zauna muna hira bansan dare yayi haka ba. Abida ta tabe baki da alama ba ta yadda da bayanai na ba. Ta sake dubana tace aisha farida me ya hadaki da musbahu kuma shima ya dinga aiko wani yaro da wasika, zuwansa biyu. Nayi nayi ya bayar a ajiye mike yace a'a, ance hannu da hannu zai baki. Sai na sake gigivewa na hau kame kame nace musbahu kuma? Meye hadina dashi? To ina jin bani aisha faridar ba. Abida tayi murmushin takaici tace kila na fara zama kurma har a ambaci aisha farida inji ba daidai ba. Babu abinda zance miki tunda boye boye kike yi min tun yanzu. Sai dai kiyi hankali da mutane, ki kuskuri bin shawarar batattun kawaye, ki rike mairaici da talaucinki. Ta juya ta fice ta rufo mana kofa. Na sulale na kwanta na dora hannu aka ina juye juye, sai dai ban fasa karanto innalillahi wainna ilaihir rajiun ba. Yadda naga rana haka naga dare, barci ya gagareni. Fargaba da tunanin haduwata dasu uwani ta gallebe ni. Haka na kwana ban rintsa ba saboda tashin hankali, don haka da asuba kiran sallar farko na mike na shiga bandaki nayi wanka, duk da sanyin ruwan ban damu da saina dumama ba, na fito nayi sallar asuba na kakaba kayan makaranta. Na dauki jakata na dauko biro da takarda na rubutawa abida wasika na ajiye takardar a bude akan tabarmata yadda zata gani daga shigowarta. Na fita daga dakin ina sanda tamkar barauniya nayi sauri na fice, da yake kofar gidan a bude take maza masu zuwa masallaci sun bude. Na rufe fuskata saboda kada inci karo da mazan gidanmu, duk da banji motsin fitowar yayana ba, daga dukkan alamu kafar ta matsa masa da ciwo tunda bai fito sallar asuba ba, dan baya fashi in dai lafiyarsa kalau. Sai nayi ta tafiya da kafata sabida rashin babura kasancewar gari bai waye ba duku duku ne. Na dade ina takawa da kafata sannan Allah Ya jeho min mai babur na hau, mun dade da fara tafiya ba tare da nasan inda zance ya kaini ba. Ya sake tambayata malama ina zan kai ki? Da farko nace masa asibitin aminu kano, har munyi nisa na canza shawara nace ya kaini jakara, umguwarsu ummi wato gidan iyayenta. Muka isa kofar gidan na sauka daga kan acaba sannan na biya shi kudinsa. Abinka da cikin gari 'yan gargajiya basu san baccin safe ba kowa ya tashi ya shiga safgoginsa. Mai kosai ta ta fara suya, masu waina suna danawa. Haka masu koko da masu shayi da biredi sun fara tafasawa. Duk inda ka waiga yara ne dauke da 'yan kwanuka a kansu an aiko su sayan abin karin kumalllo. Na shiga cikin gidansu ummi cike da fargabar abinda zanje in tarar, ummin na iske a tsakar gida ita kadai ta saka buta a gaba da alama alwalla za tayi, tunani da damuwa sun hana ta sukuni. Ta buga tagumi kamar mai tunani yayin da idanuwanta sukayi luhu luhu. Tayi matukar firgita data daga ido ta dubeni , ta cika da mamakin ganina a daidai wannan lokacin. Ta fada cikin firgici aisha umar lafiya? Sai na fara zubar da hawaye shar shar shar daga idanuwana. Ta mike tsaye da sauri taja hannuna zuwa dakin da take kwana, a cike yake da yara daga dukkan alamu kannenta ne, yara 'yan kuci kuci da masu dan wayo. Kowannensu barci yake da munshari yayi da zarnin fitsarinsu da warin daudar jikinsu suka daki hancina. Kamar inyi amai, na dai daure na zauna akan wata dakwalkwalalliy ar katifa da ummin take kwana don naga 'yarta a shimfide a gefe. Anan tace in zauna bari taje tayi alwala tayi salla sai tazo mu zauna. Kallonta kawai nakeyi tamkar gunki na kasa magana, na dubi yaran da suke linkaya a cikin fitsari babu abinda ya dame su. Naji dama nice su nake linkaya a cikin fitsarin nan da irin wannan rayuwa da na jefe kaina. Ba jimawa ummi ta shigo sanye da hijabi da alama ta idar da sallah ko addua batayi ba sabida rashin mutuswar dake tattare da ita. A firgice ta shigo tana sauri kamar zata ci da kai, ta goya 'yarta duk da himilin fitsarin da ta ci a

Chapter 7 of 23