Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zuciya. Farida tace in kyale ta bazata iya cigaba da son ba saboda babu ran abida. Dr lukman yayi tsaki yace wannan ai shirme ne, zafin mutuwa ne ya shige ta, zata dawo hayyacinta ta neme ka. Dr shuraim ya girgiza kai yace a cikin hayyacinta take magana ba zafin mutuwa bane. Na kasa gane abin da suke nufi. Yayanta yace min bata mutu ba, ita kuma tace min abida ta mutu. Abin da na fuskanta boye mata yake yi don yaga ta damu. Ga shagamu da nisa kar ta sume masa a hanya. Dr lukman yace nima na fi yadda ta mutu don yanzu yahaya ya turo min sako a waya ta yace inyi hakuri yana cikin mutane zai kira ni anjima. Dr shuraim yace idan ba zaka zo ba gani nan zuwa gidan naka muyi shawarar, don bansan yadda zan iya yini a cikin wannan halin ba. Dr lukman yace naga ka damu da yawa abokina, bari nayi wanka inzo tunda gidanka babu kowa zaifi dadin magana. Dr shuraim yace don Allah kazo da wuri ina jiranka. Suka kashe waya. Dr shuraim ya kame a zaune ko yatsarsa baya iya dagawa balle ya tashi yayi wani abu. Shi kansa yana tausayin kansa da kansa, halin da zai shiga idan ya rasa aisha farida. Ya rasa yadda akayi ya zurmuka cikin ramin kaunar ta wanda yayi zurfin da ya kasa fitowa. Ya fada a bayyane lallai karshen namiji a karkashin mace yake. DUK KYAN TAKALMI a kafa ake taka shi. Sai ya zubo da wani zazzafan hawaye daga idanuwansa. TABBAS DUNIYA RAWAR 'YAN MATA CE, NA GABA SAI YA DAWO BAYA IDAN AKAYI WANI JUYIN. ASUBA TA GARI LIKITAN AISHA FARIDA!!! BABI NA GOMA SHA BAKWAI Mako guda kenan dai-dai da tfyr su aisha misalin karfe 5 na yamma. Dandazon maza tsofaffi ne suka cika a majalisar hirarsu ta 2ntuni,wato kfr gdnsu aisha farida. Mahaifin abida shine ya gaji kujerar tsohon af shine kadai yake zaune akan kujera sauran dukka a zazzaune suke akan tabarmi a gefensa. Af ita kadai ce mace a cikinsu,tana zaune akan kujera, sauran dukka a zazzaune suke akan tabarmi a gefensa. Af ita kadaice mace a cikinsu,tana zaune akan dakali ta lanqwashe kafa,sanye take da bakr riga abaya ta yafa dankwalin a kanta. Ta jima tana kallon tsofaffin nan daya bayan daya,sai ta 2na da a lkcn da mahifinta yake raye,mahaifin abida ya juye shi sak! Kmrsu 1 a yanzu shine babba a cikinsu. Tabbas abida da mahifinta tayi kama sak! Sai taji hawaye ya cika mata ido ta grgza kai dn tausayi. Tace a ranta, Allah sarki, wata rana sai a shafe kowa kmr ba a taba yin mu2m a doron k'asa ba. Haka ake tfy daya byn daya. Baba iliyasu ne ya dubi aisha farida yayi mrmshi yace, kai girman dan mu2m babu wuya, kmr ba 'yar yarinyar nan bace, 'yar karama aisha, yanzu ga yadda ta girma. Af tayi dry tace,kaima aika tsufa inda zaka san an dade kenan. Sai suka hau hirar 2na baya,abun tausayi a jajanta,abn dry a kyalkyace Tsayuwar wata tsaleliyar mota baka mai duhun gilashi ce ta katse hirar,sai hnklnsu gaba daya ya koma kallon motar. Mazaje 4 ne suka bude kofofin moyar guda 4 suka fito. Af ta cika da tsananin mamakin data kasa boyewa,sai cimak ta mike tsaye, yayin da aka hau kallom-kallo a tsakaninsu. Dr s, Dr Lk, Dr Dayyab da yahya umar ne suka nufo inda su af suke. Suna isowa sai su duka suka zube a gaban tsofaffi suka kwashi gaisuwa. Nan da nan suka matsa musu waje suka umarce su dasu hawo kan tabarma su zauna sosai. Bayan kowannensu ya zauna sai af ta durkusa ta gaishe su ckn sanyayyar murya. A lkc guda suka amsa, yayinda Dr S ya kafa mata ido yana kallonta, ko ba a fada ba ansan yayi kewarta,sati guda kenan bai ganta ba. Cikkin kunya kanta a sunkuye a kasa ta yunkura zata tsh ta shige gida. Yahya umar yace ta daawo ta zauna zaiyi magana. Sai taji zuciyarta ta harba, a ckn ranta ta hau addu'a ALlah yasa alkhairi zai fada. Numfashinta ya fara cikewa,yayin da da babu abnda tafi bukat irin ta shige gida kada ayi maganar nan a gabanta,tasan koma dai me za a ce ya shafe ta. Ta fada cikin ladabi,ruwan sha zan kawo muku. Yahya yace munan ea kika ganmu a koshe muke,su kuma basa shan ruwan randa irin naki, sunada ruwansu na rba a mota. Sai dukkansu sukayindariya. Af ta dawo jikin dakali ta rabe kmr marar gsky. Ahya yagyara zama ya dubi tsofaffin yace, baba, wadannan gudaukun da kuke gani baki netun daga kano,kuma gaba dayansu likitoci ne a asibitin aminu kano. Sai tsofaffin sukasuka hautsine da maganasuna cea, likita bokayen turesai,ai da ga gani babu tmby gasu nan a nutse kowanne cikin kyakkyawan shiga. Wasu shaddoji ne suka saka masu kyau,kowacce tsasaddiya ce sai daukan ido takeyi. Farare sol sol anyi musu dinkin surfani dinkin boda,rigar iya gwiwa. Su shuraim dai dry kawai sukeyi. Yahya ya cigaba da byani,ya nuna DR LK yace wannan sunansa dr lk, babban abokina ne tun. Una yara a yobe tare mukayi sakandire. Ya nunaDR S yace ga shuraim babban liktan fatar da akeji dashi a kano shima aminin lukman ne, kuma shine yake so r AIsha FArida. Sai gaba daya suka juyo suna suka dubeta,tayi sauri. Ta sunkuyar kkasa yayi akwakalra tsg aito m da y yanaa,tmakr lma. Tana tmbyr zuciyarta ''ANya kuwaa mafarki nakeyi ba,yau shuraim ne ya fara mgnr aure na. Allah mai ikobabu abndaya gagari ubangiji. Dr shuraiam har yanxxu kallon aishaa f yakeyi kasa kasa yana soyaga yanayinta da taji mgnr aurensu. Ya fusknci ta cika da mamkikuma yaga annuri a fskrta yya karu, dn haka ya sake csamun kwari. Gwiwar tana sonsa. Tsofafi sai suka shiga jan dogayen addu'oi. B.Sule ya dubi farida yace,ja'ira ashe kin ruso miji kyakkyawa daa kano haka kikeboyewa. Yanzun nan ika gama cewa bakidasaurayi. Sai su dukka suka tintsire da dry,harda ita. Yahya umar ya nuna dayyan yazxe,wannan sunansa DR Dayyabu shima a sibitin m. Aminu kano yake aiki sunaji dashi ko kuma ma ince a arewa anaji dashi. Reumatologist ne,likitan daya shafi ciwon cikin kashi da jijyoyi. Shine likitan daya shafi ciwon abida,dn haka nema suka tzho dashi. Sai gaba daya suka zabura suna kalonsa,musamman ma aisha f. Mahaifin abida ya grgza kai, yace, ciwon abidaaiba naasibiti bane kada ma ku wahalar da kanku. Dr lk yayi gyarsan murya yace, baba ni babu waniciwo da za'a ce babu maganinsa a asibiti. Kada ku hana shi gwadawa,abunda ya karanata kenan,aikinsa ne shiyasa muka tahho dashia. Baban abidaya grgza kai yaxe, me likta zaiyi mata, yarinyar da htta gashin knta ya kde dukka,kan nan kmr anyi mata kwal-kwal,I wannan aikin kowa yasan iska ne. KYAN TAKALMI 3* 8 Dr dayyabu yayi murmushi yace ciwon ya gaji haka, yana zubar da gashi, yana saka ciwon ido, yana sa mutum yayi ta zabura, kuma da kumburin gabobi, wani lokacin da yawan jin sanyi. Idan ciwon ya tsananta zai iya taba dukkan kayan cikinta kamar koda, zuciya, mahaifa da kuma kurajen baki. Allah dai Ya kiyaye. Nan da nan tsofaffi suka fara gamsuwa da bayanan dr dayyabu, domin ya zano duk abubuwan da abida take ciki. Ya kara da cewa kurajen suna iya feso mata a kirjinta, baya, wuya, da kuma fuskarta. Na fuskar zai zagaye kumtunta da kuma kan hancinta. Zai yi siffar malam buda mana littafi a turance muna kiransa butterfly rashes. Aisha farida ta dafe kirji tace likita wannan wane irin ciwo ne? Yaya sunan ciwon? Kuma me yake kawo shi? Dr dayyabu yayi dariya har sai da kyakkyawar wushiryarsa ta bayyana. Ya girgiza kai yace bazan iya tantancewa ko me yake damunta ba har sai anyi gwaji. Gwajin ciwon kuma ba a yinsa a kasar nan, sai a south africa ko a beiruit. Aisha farida ta dafe kirji yayin da kake iya ganin gigicewa a fuskarta. Tace likita yanzu dai sai an kaita can sannan a gano ciwon? Sai ta fara hawaye saboda tunawa da tayi basu da wannan gatan. Dr shuraim yayi sauri yace kada ki fara koke koken nan. In Sha Allah komai yazo karshe tunda kika ganmu da likita. Sai ki shekara a AKTH baki samu damar ganinsa ba, amma gashi mun kawo muku shi har gida. Kuma zaiyi mata duk abin da ya kamata har sai ta ji sauki in sha Allah. Dr dayyabu ya girgiza kai yace ba sai an dauke ta an kai ta south africa ba, za dai mu tura jininta wani lab a abj su zasu aika jinin can idan anyi gwajin sai su turo mana da sakamakon online. Idan na duba sai in tantance takamaimain matsalarta, sai in bata magani. Amma bayan wancan gwajin mu ma anan akwai gwaje gwajen da zamuyi mata kala kala muga ko akwai matsala a cikin jikinta kamar su koda, zuciya, hanta da dai sauransu. Kowa yayi tagumi yana kallon bakin dr dayyabu zuciyarsu cike da fargaba da tausayin abida. Yayi murmushi yace kada ku damu, ba wani abu bane na daban. Anayi kuma ana warkewa sai dai don masu irin ciwon basu da yawa ne a duniya. Yaya hussaini ne ya fito daga cikin gida, baba ahmadu yace yawwa hussaini zo ka zauna kaji da kunnenka, likitoci ne suka zo daga kano suna bayani akan ciwon matarka. Yaya hussaini cike da mamaki yake kallonsu, bai san sauran biyun ba amma ya gane dr shuraim. Yazo ya mimmika musu hannu suka gaisa, ya samu waje ya zauna ya cigaba da sauraron bayanin dr dayyabu. Dr dayyabu yace daga yadda yahaya umar ya min bayani yadda ciwon nata yake yayi min kama da Systemic lupus erythramatosis (SLE). Sai kowa ya gyara zama suka mika tunaninsu gaba daya kan likita dayyabu. Yaya hussaini yace me kenan? Me yake kawo ciwon? Dr dayyabu ya lankwashe kafa yace SLE ciwo ne wanda yake samuwa jikin wanda Allah Ya dorawa. Lupus is an auto immune disease characterised by acute and chronic inflammation of various tissues of the body. Auto immune disease are illness that occur when the body tissues are attacked by its own immune system. Bansan yadda zan fassara muku ba, amma dai ba a gado, kuma ba'a daukar ciwon. Ciwon yafi ga 'yan america bakaken fata (africam americans) da kuma 'yan chinese da japanese. Anfi samun SLE a jikin mata fiye da jikin maza. Kuma yafi kama masu shekaru ashirin zuwa arbain da biyar. Malam ahmadu yayi dariya yace likita bokan turai, ai ni wannan bayanin naka kamar tatsuniya nake ji, mu nan 'yan chinese ne da zai zo ya kama 'yarmu? Ai ciwon abida sammu ne, daman ance tana da makiya a kanon nan, musamman da awararta tafi kowacce dadi suka jefe ta. Aisha farida ta girgiza kai tace a'a baba ahmadu, ka bari ku bari ya bata magani. Yau wata nawa kuke yin na sammun amma babu alamar sauki sai ma ciwon gaba yake ci. Yahaya yace gaskiya fa tunda yazo a dakatar da duk wani hayaki a zuba masa ido. Da yawa daga cikin tsofaffin suka kushe maganin asibitin har da mahaifin abida. Kadan ne suka goya bayan likita. Daga karshe yaya hussaini yayi magana yace ya yadda likita yazo ya duba abida ko Allah zai sa a dace. Gidan su abida da gidan su aisha farida babu nisa, don haka aisha farida, hussaini, yahaya, da likitocin guda 3 suka dunguma gidan su abida. A zauren gidan aka iskesu an daukota tamkar tsumma , wata mata mai maganin gargijiya ta shafe jikinta sharkab da man shanu ta tilo mata itatuwa a leda tace ayi ta jika mata a sabuwar kwarya. Hankalin likitocin ya tashi da ganin irin wannan kwabe kwaben. Yaya hussaini yayi wa surukarsa bayanin likitocin, tashin farko taki amincewa ita da mata mai magani, tace ba'a hada aikinta da na asibiti. Yaya hussaini dai ya takura sai likitoci sun duba matarsa. Mahaifiyar abida da mata mai magani suka yi fushi suka bar wurin a fusace daya ta shiga gida, mai magani ta fice dauke da buhunta a kai. Hakika abida tana jin jiki matuka, kamar ba ita ba, gaba daya halittarta ta sauya, yanzu ko magana bata iya yi saboda azaba. Sai gyada kai, sai hawaye kawai zaka ga yana zuba saboda tsananin wahalar da take sha. Aka kawo musu tabarmi suka zazzauna yayin da dogon turanci ya hautsine tsakanin likitocin uku, likitan fata, likitan kwakwalwa da likitan kashi da jijiyoyi. Dr dayyabu ya bude jakarsa (brief case) ya jawo allurar intramuscular injection wacce ake kira dexamethasone 8mg start. Ya umurci aisha farida tazo ta juya masa ita. Yayi mata allurar sannan ya debo wasu magungunan kala kala har kala biyar ya mika ma maigidanta yace lallai a dinga bata magungunan nan, kuma akan lokaci har tsawon sati biyu za aga canji In sha Allah kafin a gama gwaje gwajen jininta, idan an gama tantance takamaiman ciwon. Dr dayyabu ya dubi aisha farida yace matso kusa nayi miki bayanin yadda za a dinga bata maganin. Ga prednisole nan ta sha kullum guda uku HOQ daya da safe, daya da dare, calcium kuma kullum tasha daya. Sai kuma methothroxate ranar asabar zata sha 10ml. Ranar lahadi kuma ki bata folic acid guda 2. Yanzu zan dauki jininta kashi kashi in tafi dashi, wasu a kano zamuyi gwajin wasu kuma a abj zamu aika lab suna harhada jinin mutane da yawa, su tashi mutum a kai south africa a gwada. Yaya hussaini ya langabar da kai yace nawa ne kudin maganin? Kuma nawa ne zamu bada na wannan gwaje gwajen naji har da wanda za aika kasar waje. Dr dayyabu yayi murmushi ya girgiza kai yace kada ka damu da wannan, abokina shuraim ya gama shirya komai. Dan yanzu ma lagos zanje in hau jirgi cikin dare in isa abj in bada wannan jinin, kwana goma zaiyi sannan ya fito, to sauran gwaje gwajen ma sai inyi a national hospital abuja don yawo da jini babu dadi, duk dr shuraim zai biya. Gwajin jinin wanda za'a aika south africa ma dubu sittin za a biya, yace shi zai biya. Sai aisha farida ta fara hawaye haka itama abida hawaye ya fara kwaranyo daga idanuwanta dan tana jin duk abin da ake cewa. Yaya hussaini ya hau godiya yana shi albarka. Dr dayyabu ya zaro sirinji da kwalabe ya zuzzuki jinin abida ya ciccika. Ya dauko wata 'yar akwati ya jera su ya mayar ya rufe. Suka mike suna yiwa abida sannu da fatan Allah Ya bata lafiya. Aisha farida da yaya hussaini ne suka kinkimi abida suka shiga da ita cikin gida. A take yaya hussaini yace aisha farida ta dibo ruwa ya bata magani, bayan ya bata ta sha sai yace aisha farida ta boye maganin a wurinta. Sanda zata sha tazo ta bata kada ta barsu a fili goggo ta zubar dan bata yadda da maganin asibiti ba. Yaya hussaini ne kadai ya dawo wurin su dr shuraim suka dunguma zuwa kofar gidan su aisha farida wajen tsofaFfi. Babu abinda yaya hussaini da yahaya umar sukeyi sai godiya da shi albarka. Yaya hussaini ya yiwa tsofaffin bayanin duk abubuwann da ya faru da irin zunzurutun kudin da dr shuraim ya kashe da wanda zai kashe nan gaba. Sai suka kacame da yi masa godiya da shi albarka, shi da abokansa sauran likitoci. Hussaini ya gyara zama ya dubi tsofaffin nan ya nuna shuraim yace shine mai son farida, da farko naki amincewa saboda ko ba a fada ba shi ba sa'an aurenta bane, mu talakawa ne kuma baki. Toh a haka muka rabu. Yahaya umar yace kayi kuskure hussaini tunda kayi wannan tunanin, ai al'amarin soyayya ba a ayin ta don kudi, shi ya ganta yana so, itama tana sonsa kayi garaje da ka tarki raba su. Ba 'asan inda rana zata fadi ba, haka baka san wanda zai yi maka amfani a rayuwa ba. Ga shi dai yanzu ya taimake mu a lokacin da bamu zata ba, kuma bamu da matsayin samun wannan. Dr lukman ya fada min komai daga haduwarsu har zuwa tahowar aisha farida. Naji ra'ayin shuraim akanta alkhairi ne kuma aurenta yake so yayi. Yanzu wannan tahowar da sukayi sunzo dan su duba abida su bata magani kuma su nemi auren farida ayi magana daya. Hussaini ance ka kauro gida kacokan zaka bar aiki, to zamanka a shagamu ba zai yiwu ba, ko ba dan aisha da shuraim ba, kuma ba dan karatun 'ya'yanka ba , don lafiyar matarka da rufin asirinka aikinka sai ka koma kano don abida yanzu dole ta kasance kusa da likitanta dr dayyabu yawan yawan bincikar lafiyarta. Yaya hussaini yayi shiru yana gyada kai don ya gasgata maganar yayansa. Can ya dago ya dubi yahaya yace tabbas ka fadi gaskiya, dama ni ban gama tsayar da shawarrar barin aikin ba, na dauko hutu ne na shekara. A cikin hutun ne dama nake so naga yadda halin zaman namu a shagamu zai kasance idan na samu abinyi sai in zauna. Idan ban samu ba in koma kano iyalina in barsu a nan. Yahaya yace to iyalinka ne ma zaman a kano ya kamasu saboda lafiyar matarka, wannan likitan da kake gani babu inda zakaje a kasar nan ka samu iirinshi , su biyu ne kadai rheumatologists , daya na kudu shi yana arewa. Saboda masu irin ciwon basuyi yawa ba. Saboda haka hutunka na karewa ko bai kare ba ka hada su ku koma dan naji yace sati biyu zai gama hada sakamakon gwaje gwajen sannan ya gano kan ciwon. Yaya hussaini fadi yake gaskiya in sha Allahu zamu koma nagode. Tsofaffi ma suna bayan yahaya, shawara suka ci gaba da bawa hussaini su hada su koma kano. Dr lukman ya gyara zama yace toh mu dai yanzu munzo a shirye tafi da gidanka mukayi, ma'ana muna neman auren aisha farida. Yahaya ya dubi tsofaffi yace toh me za a jira tunda gaku kacokan kun hallara? Mutumin nan sananne ne tunda ga lukman nasan gidansu yasan gidanmu. Farida na son shuraim shima yana so, ayi magana kawai. Dr shuraim ya sunkuyar da kai kasa yace saboda rashin lafiyar nan ne ta abida bamu san yadda zamu tarar da jikin bane yasa bamu taho da iyayena ba. Amma tunda komai yazo da sauki idan an amince mana sai mu bada kudin aure, sai kuyi magana da mahaifina a waya ya lamunce in nemi auren. Su dukka suka ce babu damuwa ai. Dr shuraim ya dakko wayarsa ya kira tsohonsa , bayan sun gaisa ya shaida masa gashi a gaban iyaye da kakannin aisha farida kakaf sun hallara , kuma sun amince zasu karbi kudin aurensa. Abban shuraim yace masa ya basu wayar, daya bayan daya abban shuraim ya dinga gaisawa dasu suna yi masa fatan alkhairi, shima yana yi musu har suka kashe wayan. Dr lukman ya tashi yaje mota sai gashi ya dawo da bakar jakar leda yazo ya zauna, sai ya mikawa yahaya umar. Yahaya ya bude yaga damin kudi dauri biyu 'yan naira dubu daya-daya. Kowanne dami dubu dari ne, dami biyu dubu dari biyu kenan. Dakata yahaya. Inji baban abida. Kowa yayi carko carko yaji abin da zai fada. Yace ba himilin kudi ba, haka ba wayar da mukayi da tsohonsa bane aure. Shin an tambayi yarinya tana sonsa? Don idan yayana umar yana da rai zai iya yiwa kowacce 'yarsa auren dole banda aisha farida. Don yana matukar sonta, baya son abinda zai bata mata rai. Hankalin dr shuraim ya tashi, sai yayi ta zungurar dr lukman wai yayi magana. Hussaini yayi murmushi yace wallahi tana son shi, matukar so kuwa. Don nine shaida saboda ni ta tara tace min ina kokarin raba ta da shuraim, to in sani kamar ina kokarin raba tane da rayuwarta, don tanayi masa tsananin son da zata iya rasa rayuwarta. Babu wanda bai kyalkyace da dariya ba a cikinsu, yayin da dr shuraim yayi ajiyar zuciyar jin dadi. Salati goma ga annabi (SAW) suka fara kawowa, sannan dr lukman ya fara warware kudade yana bayani. Naira dubu 100 shine kudin na gani inaso, naira dubu 50 gaisuwar uwa da uba, sai naira dubu 50 kudi ne kyauta a rarrabawa dangi , wani a siya alawa da goro shaidar an bada ita. Sai tsofaffi suka rike haba don mamaki da jin wadannan makudan kudi tunda suke aurar da 'ya'yansu da jikokinsu babu wacce ta taba yin tsadar da farida tayi. Sai wasu suka barke da kukan dadi don ko naira ashirin babu a aljihunsu. Wasu kukan tunawa da mahaifin farida sukayi. A lokacin malam sule ya shiga yiwa farida kirari irin wanda baban yake yi mata tun tana karama. "Aisha sarauniyar mata, fara mai farar aniya, kinfi mata dubu". Kowa yana ta adduar fatan alheri da fatan ayi auren cikin sa'a da zaman lafiya. Dr dayyabu ne zai tafi a yau, dr shuraim da lukman zasu kwana sai washe gari zasu koma, da mota suka taho don haka yahaya zai raka su masauki. Wani tsadadden hotel zai kaisu, sai suka yi musu sallama suka shiga mota suka tafi. HAUSA Novels BOOK DUK KYAN TAKALMI 3* 9 Aisha farida tana zaune a gefen katifar abida tayi shiru tana sauraron bambamin fadan da goggo keyi, saboda an kawo likitoci sunzo sun korar mata mai magani da suka kashe kudi sannan ta yadda tazo. Tana shiga tana fita, ta na fada ita kadai, babu wanda ya tanka mata a cikin gidan saboda ranta yayi matukar baci. Ko hakuri aka bata sai taji tamkar an zage ta. Abida ta dubi aisha farida tayi dan murmushi yayin da itama ta dube ta tayi murmushin. Abida ta yi magana a hankali sai da aisha farida ta dora kunnenta a kusa da bakin abida sannan taji abinda take cewa. Cewa tayi allurar nan da akayi min naji dadinta, yadda kika san yawo takeyi kusurwa kusurwa duk inda ciwon yake tana wanko shi. Gashi ina iya daga hannaye sama. Dadi ya rufe aisha farida tayi dariya tace mungode Allah, Allah Ya karo sauki. Abida tace amin, naga shuraim, Allah Ya sa ayi auren nan. Aisha farida tayi dariya tace samun lafiyar ki shine fatan mu , kafin ayi wata magana antina......bata rufe bakinta ba saiga maimuna ta fado cikin dakin budik! Ko sallama babu kai kace jeho ta akayi. Sai haki take daga gani tasha gudu. Cikin sheshekar gudu ta rirrike aisha farida tace albishirinki? An bada ke, yanzu aka kawo kudin aurenki dubu dari biyu. Kallon rashin fahimta aisha farida da abida sukeyi wa maimuna. Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah abin godiya. Wai nice yau ake maganar aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta danna da sauri sai taji muryarsa cike da farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira wayarki taki shiga sai da na aika yara suka fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko? Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta mutu ne shine muka dungumo, muna nan dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu an samu rabin warakar ciown, tunda an samu likita da ya gano matsalar. Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji dadi ba. Aisha farida ta rike baki da daya hannun ta dafe kirji ta dinga fadin Allah mai iko, Allah abin godiya. Wai nice yau ake maganar aurena da dr shuraim? Maimuna ta fice ta barsu suna mamaki. Wayarta ce ta hau karan sai tayi sauri ta duba ta zaci rabin ranta ne, sai taga sunan barr muazzam ta danna da sauri sai taji muryarsa cike da farin ciki. Yace gani a kofar gidanku, na kira wayarki taki shiga sai da na aika yara suka fito suka ce min wai kun tashi, kun kaura shagamu. Ance anyi muku mutuwa ko? Yanzu yara suke fada min. Aisha farida tayi murmushi tace kai dai bari yayana, tafiyar ce babu shiri, a kidime muka taho jikin anti abida ne ya matsa har ta suma an zaci ta mutu ne shine muka dungumo, muna nan dai a shagamu har zuwa wani lokaci. Kafin muga yadda Allah zaiyi damu. Amma yanzu an samu rabin warakar ciown, tunda an samu likita da ya gano matsalar. Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace har naji sanyi a raina, ai tuni hankalina ya tashi da naji ance anyi mutuwa. Sai na kawo anti abida ce, Allah dai Ya bata lafiya. Albishir nazo miki dashi sai gashi ba kya nan banji dadi ba. Aisha farida ta dafe haba tayi dariya tace albishir din meye? Yace alewar saka aurena da janan na kawo miki. An bani ita har an kai kudi da kayan sa rana , nan da wata uku za a sha biki. Alewarki ta musamman ce, bounty na kawo miki har jaka biyu saboda matsayin ki a auren nan, sai gashi ba kya nan. Ko 'ya'yan yayanki suna ciki a kirawo mun su na basu? Aisha farida tayi dariya tace Allahi abin godiya, amma na taya ka murna yayana. Kuma na gode da karramawar da kayi min. Babu kowa a 'yan gidanmu, dukka muka taho. Nima kuma yanzu zan zankado maka nawa albishir din. Dr shuraim yana shagamu yazo da likita an duba anti abida, ya siya mata magunguna , ya biya makudan kudi za a kai jininta kasar waje a gwado. Sannan daga karshe ya kunso kudin aurensa ya kawo yanzu yanzun nan nima labari yazo min, suna can a kofar gida shi da yayyena da tsofaffin maza. Barr muazzam ya cika da farin ciki da mamaki, ya kyalkyale dariya yace ikon Allah, Allah mai yadda yaso. Wato auren namu ma tare za'ayi kamar yadda muka fara nema tare. Na taya ki murna kanwata. Baraka ma komai ya daidaita, ita da mijinta suna cikin farin ciki, ya rabu da nafisa , hankalinsa kacokan akan baraka. Ciki ne ma da ita, sai ririta cikin yake yi. Tace in gaishe ki da kyau, kuma tana matukar yi miki godiya, tana so ta ganki a rayuwarta. Tace in gayyato ki suna idan ta haihu. Aisha farida tayi dariya tace Allah Ya kaimu , idan dai ina kano zanje. Sukayi sallama ya kashe waya. 3 missed calls din dr shuraim ta gani a wayarta a lokacin da take waya yake kira, sai ta fara kokarin kiransa, shima ya kirata. Ta amsa sallamarsa cikin nutsuwa kafin ta gaishe shi ya jero mata tambayoyi guda uku, ta rasa wacce zata fara amsawa a cikinsu. Farida da wa kike waya nayi ta kira har sau 3 naji call waiting? Meyasa da kika shiga gida dazu baki fito ba mun gaisa har na tafi? Meyasa kwana biyun nan naga alamar kin daina damuwa dani? Sai ta lumshe ido tayi ajiyar zuciya sannan tayi murmushi. Tace bari na fara amsa maka tambayarka ta uku, sannan a gangaro ta biyu, sai in gangaro ta daya. Zancen na daina damuwa da kai wallahi ba haka bane, tunda ina tuna ka a rana sama da dubu. Sannan tambayarka ta biyu ina shiga gida na bawa anti abida magani sai na zauna ina saurarom fadan da goggo keyi mana ni da yaya hussaini, wai mun kawo likitoci sun duba

Chapter 19 of 23