Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
to kasancewar asabar ce babu banki, lahadi ma babu aiki ba za a iya fitar da kudin ba, sai ranar litinin. Shine tace in ranto mata zuwa litinin zata biya. Uwani tace a'a aisha farida kinsan halin mutane kayi musu rana suyi ma mutum dare. Ki zo ki taimake su suki biya, ko kuma ni in taimake ki, kiki taimakona. Kinsan dai kudin nan da kika gani kudin cizo ne, bana kashewa bane da masu shi. Gobe haj rabi ce zata dauki adashen nan dubu talatin. Mace dayace bilki bata saka mata ba, na aika tace gobe zata aiko yana aikowa sai in hada in aikawa haj rabi daukarta. Yanzu idan na baki aka zo aka sami matsala yaya zanyi? Kinsan bani dashi, lada suke bani duk wata dubu daya dan tarawar da nakeyi. Niko ikon sgiga adashen ma bani dashi dan bani dashi. Nace na sani uwani, idan Allah Ya yarda babu matsala, ranar litinin da sassafe zanje bankin da kaina in karbo miki. Tace to shikenan gashi nan. Ta kirgo dubu goma sha bakwai tabani, na karba na kirga sun cika cas, nayi godiya. Sannan na roki arzikin ta rufa min asiri kada ta fadawa kowa ko abida kada taji, salin alin zan dawo mata da kudinta. Tayi min alkawari babu wanda zaiji. Na shiga daki na hada kan kudina na adana a jaka. Naira dubu ashirin. Farin ciki fal a zuciyata, har sai da abida ta fuskanci haka a daren, a da bana iya cin abinci sosai, amma a daren taga har da kari nayi. Da bana son magana sai taji na isheta da labari a ranar. Ta san na daina fara'a amma a ranar na ishe ta da kyakyata daria har da wake wake. Saboda na riga na sami kudin da bana tantama na gama samun dr shureim imran. Gari na wayewa na shiga tunanin karyar da zan shiryawa yaya hussaini wacce zai bari in fice, domin ranar lahadi ce babu aiki, kuma kulle yake min. Na shirya tsaf na kira abida gefe na shirga mata karyar cewa zanje asibiti yau ma, ana yiwa wata nurse bikin gama aiki, tayi retire ance kowa sai yaje kuma da kayan gida. Na santa da wayo ta san yadda zata fadawa maigidanta ya aminta da ita. Ta shiga daki ta tsaro shi sai ga ta da dari biyu kudin babur. Naji tausayinsu ya kama ni saboda nafi su kudi yanzu, da sun san kudin da yake jikina da basu rabu da dari biyunsu ba. Nayi godiya na karbe na tafi, abida ta rakani har zaure tana yi min fatan alkairi. Tana jaddada min in ragowa 'ya'yanta kayan walima. Na amsa mata da zan rago musu da yawa ma kuwa. Ina fita na hau acaba sai gidan ummi kawata. Da yake sassafe ne mijinta ma bai fita ba yana daki, tajani zuwa falonta muka zauna muna magana cikin sirri. Ta tambaya yaya ake ciki, na samo kudin kuwa? Na ciro mata himilin kudin daga jakata sai ta rike baki tace lallai kinyi kokari, nima na hada dubu goma sha biyar bari inje inyi masa karya inzo mu tafi. Yau lahadi ba zai fita da wuri ba, gara muyi tafiyarmu. Ta shiga daki ba dadewa ta fito a shirye da goyonta muka nufi kofar fita, har mun kai zaure faccalarta ta biyo mu da sauri. Tana cewa ummi unguwa zakije baki fada min ba mu fita tare? Yau ne sunan mariya 'yar jummai, ki tsaya in shirya mu fita gaba daya mana. Ummi ta doka mata harara tace dani aisha faida da Allah muje, dole ne sai mun fita tare. Myka kada kai muka fice muka bar ta a tsaye tana kallonmu har abin tausayi. Muna fita nace da ita haba ummi ya za ayi kiyi mata wulakanci? Ai sai ki bata amsa mai dadi ko ba kya so tabimu. Ummi ta tabe tace ai na daina raga mata tunda bincike ya nuna bata kaunata. Ni da mutunci da ita har abada. Nace to amma ai maganar malamai ce, babu tabbas zaiyiwu kirkira yayi. Ta harare ni tace lallai kina wasa da aikin malamin nan. Idan yayi miki duba tabbas zaki ga komai a hankali daya bayan daya. In bai gani ba zai fada ne ko da ya taba ambato sunanta in ba yanzu ba, kuma nima na lura tun sanda muka sayi generator ta canja min, taga mun cigaba a rayuwa. DUK KYAN TAKALMI 11 Bansake magana ba dai har muka isa gidan malam. Yana ganin mu ya fara washe baki, fara'ar yau tafi ta jiya. Muka zazzage masa kudaden jakarmu kakaf domin bayan dubu ashirin da dayan da ya karba sai da ya sake kwakwalo min wasu kudaden daban daban har dubu biyar da dari biyar. Kuma na harhada na bashi, a takaice dai har cikon dubu daya da dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita ma ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta tashi cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba, goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin komai zai daidai ta. Muka fito muna murna, ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta koma gidanta, na sake shirgawa abida wata karyar tunda ban taho da kayan walima ba, naso in siyo musu lemo da biskit amma na juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban damu da himilin bashin dake kaina ba, burina aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana. Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare- dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna tafe muna hirar soyayya. Na dade ina tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa zuciyata na sami dr shureim na gama kamar yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na shirya na karbi kudin babur a wajen abida. Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku na fara zullumin inda zan nemo wadannan makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi da dr lukman suna fitowa medical students suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya (ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana biyu, rannan har yahaya umar yace in baki waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne sanda yake magana, har yakai barandar waje banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe. Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba. Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na shiga gidan mu har sai da abida ta shiga damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce. Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai dai wannan abincin bana lasa bane, yafi karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya yana kamshi amma aka zazzaga masa guba kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na amshi wata galleliyar harara daga gareshi. Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce tafi ta dazu wulkilewa. Sai nayi sauri na juya na fara tafiya ba tare da nasan inda zanje ba, sai gani a bakin gadon marasa lafiya nayi wuki wuki suna kallona ina kallonsu. Sannu likita, zoki duba cikinsa ki gani ya kumbura. Inji wata tsohuwa mai zaman jinyar danta. Na girgiza kai nace ki kira likita ni ba likita bace. Nayi saurin barin wajen na dawo bakin kofar ofis din na tsaya, nayi kamar in tura kofar in shiga sai na fasa. Na hakura na tafi ba don zuciyata tana so ba. Ina zuwa ofishinmu na iske kawayena suka hau min surutu. Wai aisha farida ina kike shiga ne aka nemeki aka rasa kullum har anyi test jiya ba kya nan? Nayi shiru na koma gefe na zauna na rasa abun da yake min dadi. Naci sa'a khadija sani tace inzo in rakata ta siyo ruwa zata sha magani. Ashe itama ta kunso labarai kala kala take so mu kebe ta fatsar. Ta dube ni ta tabe baki tace baki tambayeni dr shureim ba. Sai naji gabana ya fadi, sai na zargi kaina ina ganin kamar kowa yasan halin da nake ciki. Na zabura nace kamar yaya ban tambaye ki dr shureim ba? Tace kin manta inda muka kwana na nuna miki sakonsa a wayata? To in fada miki an gasa minshi da addua, ba adadi har sai da yaji ba dadi. Ina kiransa ya amsa, yace dani wacece? Sai na fada masa sunana khadija sani ismail. Ni daliba ce a schl of nursing tanan aminu kano, kuma ina attachment a nan cikin asibiti, sai yace yayi kyau lafiya? Nace lafiya so nake yayi saving lambata zan dinga kira muna gaisawa. Na dafe kirji nace yayi saving lambar? Tace kwarai kuwa, don da na sake kira sai da ya ambaci sunana. Sai naji kwalla ta cika min ido, kishi ya kamani, jikina yayi sanyi kalau. Taci gaba da cewa da na sake kira sai yayi tsiyar. Na tambaya a sanyaye meye tsiyar? Tace wulkanci yayi min kamar zai zageni, wai kada in sake kiransa. Kuka wiwi nayi da hawaye na hakura dashi ma ni yanzu. Allah Ya sa bai san fuskata ba, na goge lambarsa na daina kiransa yanzu. Dadi ya rufeni, amma fa na kara tausayawa kaina. Na bata shawarar tayi hakuri taci gaba da addua, Allah Ya musanya mata da abin da yafi alkhairi. Ta amsa min da ameen. Da aka tashi daga makaranta sai na kasa komawa gida, sai nacewa khadiji sani ismali zanbi ta gidansu somin 'yan gidanmu ba sa nan sun tafi unguwa sai dare zasu dawo. Khadija tayi farinciki da jin haka, sai muka dunguma muka tafi har yanzu labarin dr takeyi min. Ban cika bata amsa ba, tamkar tana min famin gyambon da yake damuna da zugi ne. Kwakwalwata ta cunkushe na rasa abin da yake min dadi, na kasa tantance abin da zanyi. Abinci kala kala aka jera min a gabana, amma na kasa ci da yawa saboda damuwa. Khadija sani ta dube ni tace wai don Allah aisha farida me yake damunki ne kwana biyu kin susuce tamkar bake ba. Ba kya son magana, ba kya son karatu gashi ba kya son cin abinci tundazu dan abincin da kika zuba kin kasa cinyewa, bakiga yadda kika rame ba, kika kwanjale ba. Kin cika zurfin ciki, ba a jin sirrinki daman. Wai me yake faruwa ne? Nayi murmushi nace haka kowa yake ambata, malaria ce ke cin jikina. Tace toh kisha magani mana, yaya zaki zauna da ciwo kina malamar asibiti, ko in saya miki babu kudi hannunki? Ta soso min inda yake min kaikayi, na gyara zama nace kamar kinsan satin nan cikin matsalar kudi muke, kinga yanzu haka yayana ne aka bashi ajiyar kudi, ya kawo gida aka shiga har daki aka sace, ya rasa yadda zaiyi. Mai kudin yana ta damunsa har da zai kai shi police station yake ambato. Khadija tace a garin yaya aka shiga har daki aka yi muku sata, babu mukulli ne? Nace maso abinka ya fika dabara, kinsan rayuwar cikin gari, gidan yawa aka shiga aka dauke. Khadija tace babu dadi, Allah Ya kiyaye gaba. Shi kuwa mai kudin bai san kaddara bane? Yayi hakuri mana sai ya samu ya biya shi. WaLlahi nima a cikin matsala nake, domin na karbi kudi a wajen abba yayi dubu hamsin kwanan nan haka ma a wajen mama. Har sun gane ba'a makaranta nake kashewa ko na tambaya basa bani. Sai tambayata suke me nayi da kudi a cikin satin nan, naki fada, ai ban isa ince malamai na kaiwa ba sai a kusa kashe ni. Tags : Bansake magana ba dai har muka isa gidan malam. Yana ganin mu ya fara washe baki, fara'ar yau tafi ta jiya. Muka zazzage masa kudaden jakarmu kakaf domin bayan dubu ashirin da dayan da ya karba sai da ya sake kwakwalo min wasu kudaden daban daban har dubu biyar da dari biyar. Kuma na harhada na bashi, a takaice dai har cikon dubu daya da dari biyar nan gaba zan ciko masa. Ita ma ummi ya kara mata wasu kudin, idan ta tashi cikowa ba dubu goma zata ciko masa ba, goma sha uku zata ciko. Yace ya bamu kwanaki uku mu dawo, ranar laraba kenan kafin komai zai daidai ta. Muka fito muna murna, ummi tana tabbatar min komai zai daidaita in kwantar da hankalina. Na tafi gida ita ma ta koma gidanta, na sake shirgawa abida wata karyar tunda ban taho da kayan walima ba, naso in siyo musu lemo da biskit amma na juyewa malam kudin dukka, da kyar ma na karaso gida, sai da kudi ya kare. Ko kusa ban damu da himilin bashin dake kaina ba, burina aiki yaci in mallaki dr shureim shine a gabana. Na yina ina hidindimuna da 'yan gidanmu cikin walwala da farin ciki. Da dare yayi na shiga barci sai na tsinci kaina na canza tunanina ba irin na da bane. Yanzu tunani nake gani a gidansa har mun zama ma'aurata, gani dare- dare a cikin hadaddiyar motar nan tasa muna tafe muna hirar soyayya. Na dade ina tunaninsa sannan nayi bacci, na dora da mafarkinsa mai dadin gaske. Na sa wa zuciyata na sami dr shureim na gama kamar yadda malam ya bani tabbaci. Naso in makara saboda dadin mafarki, na tashi a gaggauce na shirya na karbi kudin babur a wajen abida. Yayana ya bata ta bani donshi yana riga ni fita ma. Sai uwani ta biyo ni zaure da sauri ta tsayar dani tace yanzu zaki karbo kudin daga banki? Ko sai kin taso zaki taho dashi? Bilki ta kawo zubinta jiya na wajenki kawai nake jira in aikawa haj rabi na fada mata yau da rana zan aiko mata. Sai zuciyata ta hau dukan uku uku na fara zullumin inda zan nemo wadannan makudan kudi. Na hau rawar murya ina kame kame, nace sai an taso zan taho da kudin. Ina kan babur ina tunanin yadda za'ayi idan na dawo gida babu kudin? Ina shiga cikin asibiti naji farin ciki ya lullunbe min zuciyata saboda ko ba komai an fara aiki, zuciyarsa ta fara bugowa gare ni. Sai kuwa naci sa'ar a ranar an tura mu bangarensu dole zan ga ofishinsa ko ba ma wajensa aka mu tura mu ba. Muna shiga kuwa dakin darasin muka ci karo dashi da dr lukman suna fitowa medical students suna biye dasu zasu je zagayen marasa lafiya (ward). Na tare su da sauri na gaishe su, sai naji caraf ya amsa hadda kallon fuskata, ba murmushi yake ba haka bai bata rai ba. Dr lukman ne yake dariya, har yake yi min wasa yace ke 'yar shagamu ina kika shiga kwana biyu, rannan har yahaya umar yace in baki waya ku gaisa, nace ba kya kusa. Nayi dariya nace to yaushe zanzo ka kirawo min shi a wayar muyi magana? Da yake yana tafiya ne sanda yake magana, har yakai barandar waje banji abin da yace ba. Sai wani dalibi ne yake bayansu ya juyo yace min cewa yayi kizo gobe. Na yini ina farin ciki saboda naga canji wajen amsa gaisuwata da kuma kallon mutuncin da dr shureim ya min. Ban fara fargaba ba sai da aka tashi daga makaranta na tunkaro hanyar gida. Na shiga zullumin karyar da zan gina wacce ba za'a rutsoni ba, dakin uwani na nufa kai tsaye sai ta fara murna tana gyara hannu zata karbi kudi ta kidaya. Sai na zube a gabanta ina marairaice murya ina bayani. Nace wallahi tun safe ban huta ba muna ta kai kawo a cikin asibitin saboda matar bata da jini, don haka ba za'a yankata ba dole sai an kara mata jini. 'Yan uwanta ne suka zo maza da mata muna ta auna jinin har a sami wanda ya dace da nata shi yasa ban samu fita daga asibitin ba naje banki, amma gobe da sassafe zanje in karbo. Uwani ta bata rai, yadda ta amsa min a ciki ciki na san bata so haka ba, ta bini da kallo har na fice daga dakin. Ina cin abincin rana na fice wajen musbahu ban same shi ba, na bar masa doguwar wasika. Nazo giftawa ya makoftanmu nayi ido hudu dahare ta leko kenan ta ganni, ita ma dari takwas ta ranta min kudin dinkinta zata kai domin ta kusa haihuwa, ita ma ranar litimin din nace zan kawo mata. Dole na shiga gidan na tsara mata karya iri iri na ce gobe zan kawo mata. Itama ta nuna min bataji dadi ba, har mijinta yayi fada da yaga kayan dinkin a ajiye bata kai ba. Naji hankalina ya sake tashi na fito a gigice na shiga gidan mu har sai da abida ta shiga damuwa ganin yanayin da na shigo. Tayi ta tambayata ko lafiya? Nace lafiya kalau. Idan naji damuwa ta gallabeni sai in tuno menayi da kudin, kuma nan gana me zan samu. Sai inji sanyi a raina. Washe gari talata na fita zuwa makaranta, kai tsaye ofishin dr lukman na wuce. Ina shiga na iske shi zai fita. Yace dani ke kuwa baiwar Allah ai ba da sassafen nan zaki zo ba, sai da rana in aiki ya lafa ko? Nayi turus banji dadin amsar daya bani ba, ya wuce abinsa ya barni a tsaye. Sai ga gogan nawa yau kuma shigar hausa yayi, shadda ruwan bula tazarce ya dora hular da ta dace da kalar kayansa. Ya ratayo laptop dinsa a kafadarsa sai naga ya kara yin kyau matuka babu wacce zata kalle shi bata sake kallonsa ba. Ya tari dr lukman sukayi magana, sannan kowa ya wuce. Sai naji zuciyata na tafarfasa saboda shaukin so, kai kace zakanya ce mai tsananin jin yunwa ta ga nama haka zuciyata ta dinga zillo tamkar ta ballo ta fito da taga abincinta. Sai dai wannan abincin bana lasa bane, yafi karfinta. Tamkar soyayyen nama ne aka soya yana kamshi amma aka zazzaga masa guba kaga duk kwadayin mutum doke ya kalla ya wuce ko da kuwa marmarin naman zai kashe shine. Na fara takawa a hankali na matsa daga bakin kofar kafin ya karaso. Tun daga nesa na amshi wata galleliyar harara daga gareshi. Daya karaso bakin kofa kafin ya lalubo mukulli ya bude kofar sai da ya waiwayo bayansa inda nake a tsaye ya wurgo min wata hararar wacce tafi ta dazu wulkilewa. Sai nayi sauri na juya na fara tafiya ba tare da nasan inda zanje ba, sai gani a bakin gadon marasa lafiya nayi wuki wuki suna kallona ina kallonsu. Sannu likita, zoki duba cikinsa ki gani ya kumbura. Inji wata tsohuwa mai zaman jinyar danta. Na girgiza kai nace ki kira likita ni ba likita bace. Nayi saurin barin wajen na dawo bakin kofar ofis din na tsaya, nayi kamar in tura kofar in shiga sai na fasa. Na hakura na tafi ba don zuciyata tana so ba. Ina zuwa ofishinmu na iske kawayena suka hau min surutu. Wai aisha farida ina kike shiga ne aka nemeki aka rasa kullum har anyi test jiya ba kya nan? Nayi shiru na koma gefe na zauna na rasa abun da yake min dadi. Naci sa'a khadija sani tace inzo in rakata ta siyo ruwa zata sha magani. Ashe itama ta kunso labarai kala kala take so mu kebe ta fatsar. Ta dube ni ta tabe baki tace baki tambayeni dr shureim ba. Sai naji gabana ya fadi, sai na zargi kaina ina ganin kamar kowa yasan halin da nake ciki. Na zabura nace kamar yaya ban tambaye ki dr shureim ba? Tace kin manta inda muka kwana na nuna miki sakonsa a wayata? To in fada miki an gasa minshi da addua, ba adadi har sai da yaji ba dadi. Ina kiransa ya amsa, yace dani wacece? Sai na fada masa sunana khadija sani ismail. Ni daliba ce a schl of nursing tanan aminu kano, kuma ina attachment a nan cikin asibiti, sai yace yayi kyau lafiya? Nace lafiya so nake yayi saving lambata zan dinga kira muna gaisawa. Na dafe kirji nace yayi saving lambar? Tace kwarai kuwa, don da na sake kira sai da ya ambaci sunana. Sai naji kwalla ta cika min ido, kishi ya kamani, jikina yayi sanyi kalau. Taci gaba da cewa da na sake kira sai yayi tsiyar. Na tambaya a sanyaye meye tsiyar? Tace wulkanci yayi min kamar zai zageni, wai kada in sake kiransa. Kuka wiwi nayi da hawaye na hakura dashi ma ni yanzu. Allah Ya sa bai san fuskata ba, na goge lambarsa na daina kiransa yanzu. Dadi ya rufeni, amma fa na kara tausayawa kaina. Na bata shawarar tayi hakuri taci gaba da addua, Allah Ya musanya mata da abin da yafi alkhairi. Ta amsa min da ameen. Da aka tashi daga makaranta sai na kasa komawa gida, sai nacewa khadiji sani ismali zanbi ta gidansu somin 'yan gidanmu ba sa nan sun tafi unguwa sai dare zasu dawo. Khadija tayi farinciki da jin haka, sai muka dunguma muka tafi har yanzu labarin dr takeyi min. Ban cika bata amsa ba, tamkar tana min famin gyambon da yake damuna da zugi ne. Kwakwalwata ta cunkushe na rasa abin da yake min dadi, na kasa tantance abin da zanyi. Abinci kala kala aka jera min a gabana, amma na kasa ci da yawa saboda damuwa. Khadija sani ta dube ni tace wai don Allah aisha farida me yake damunki ne kwana biyu kin susuce tamkar bake ba. Ba kya son magana, ba kya son karatu gashi ba kya son cin abinci tundazu dan abincin da kika zuba kin kasa cinyewa, bakiga yadda kika rame ba, kika kwanjale ba. Kin cika zurfin ciki, ba a jin sirrinki daman. Wai me yake faruwa ne? Nayi murmushi nace haka kowa yake ambata, malaria ce ke cin jikina. Tace toh kisha magani mana, yaya zaki zauna da ciwo kina malamar asibiti, ko in saya miki babu kudi hannunki? Ta soso min inda yake min kaikayi, na gyara zama nace kamar kinsan satin nan cikin matsalar kudi muke, kinga yanzu haka yayana ne aka bashi ajiyar kudi, ya kawo gida aka shiga har daki aka sace, ya rasa yadda zaiyi. Mai kudin yana ta damunsa har da zai kai shi police station yake ambato. Khadija tace a garin yaya aka shiga har daki aka yi muku sata, babu mukulli ne? Nace maso abinka ya fika dabara, kinsan rayuwar cikin gari, gidan yawa aka shiga aka dauke. Khadija tace babu dadi, Allah Ya kiyaye gaba. Shi kuwa mai kudin bai san kaddara bane? Yayi hakuri mana sai ya samu ya biya shi. WaLlahi nima a cikin matsala nake, domin na karbi kudi a wajen abba yayi dubu hamsin kwanan nan haka ma a wajen mama. Har sun gane ba'a makaranta nake kashewa ko na tambaya basa bani. Sai tambayata suke me nayi da kudi a cikin satin nan, naki fada, ai ban isa ince malamai na kaiwa ba sai a kusa kashe ni. DUK KYAN TAKALMI 12 Sai naji hankalina ya tashi, har na fara nadamar katobarar da na tafka. Ta bude jakarta ta

Chapter 6 of 23