Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sayayya ki kai min gida? Zaki jefa rayuwata cikin damuwa tsakanina da matata, da kuma iyayena. Na dinga tafiya a hankali ina kallonsu, a tsaye suke a jikin motarsa har ya bude mota zai shiga sai ta tsayar dashi. Ransa a bace yake magana cikin matsanancin fushi, sai ita ma ta fusata ta magana cikin kuka da fada. Dr shureim in har ni 'yar halak ce a cikin uwata da ubana na kyale ka, har abada ba zan sake nemanka ba. Ya fada cike da gadara yace shi yafi sauki, naji dadi sosai kuwa. Ta juya a fusace tana sharce hawaye, yayin da farin gilashin idonta ya fado kasa, ido daya ya fita. Na karaso da sauri na dauko mata na mika mata, sai ta dube ni jajayen idanuwanta ta karba gami da ce min thank u very much. Ta wuce da sauri. Dr shureim ya dube ni, ya sake bude ido ya kalle ni sosai, na tsaya cak kamar yadda yake tsaye kyam yana dubana. Na harare shi sama da kasa naja dogon tsaki na kada kai na wuce na bar shi nan a tsaye bai daina kallona ba, ni dai ban waiwaya ba. Na san ya cika da mamakina, ni dai burina ya cika tunda na fara ramawa kaina wulakacin da yayi min da sauran wahallalun mata da 'yan uwana masu sonsa. Na kudiri aniyar kallon arziki ya daina hada mu sabida na san ba zan same shi ba kamar sauran da suka fini haduwa, ga kyau basu same shi ba. Da na koma gida, dare yayi sai bacci ya gagare ni, na shifa zulumi da fargabar kallon da nyi masa. Naji kwata kwata ban kyauta ba, tausayinsa ya rufe ni, yayin da sabon sonsa ya tsatsafo daga cikin zuciyata. Na dora hannu aka ina fadinn na kashe kaina da kaina, me ya kaini yi masa wulakanci ni da nake addua, ina saka ran zan same shi watarana? Na shiga adduar Allah Ya sa baiji haushina ba. Gari na wayewa na shiga shiryawa, na tsaya na tsarawa fusakata kwalliya yadda zanyi kyau sosai. Nayi sauri na tare yaya hussaini zai fita aiki, nace ya bani lambar yaya yahaya wani abokinsa likita ne ta ke nema. Naci sa'a ya rubuta min akan wata 'yar takarda anan take ya miko min, ko karya kumallo ban tsaya na yi ba, na fice. Allah cikin ikonSa ina sauke kafata daya daga kan acaba ko dayar ban sauke ba a bakin gate din asibiti, sai ga dr shurim ya karyo zai shiga gate. Ya galla min harara sannan ya figi motarsa ya wuce, sai naji dariya ta subuce min, nasan dalilin hararar da yake min bai wuce don na hau acaba ba, ni kuwa ko a jikina. Acaba kuwa yanzu na fara hawa tunda ya tsani yaga mace akan acaba. Idan baya so mu hau sai ya saya mana motar hawa ni da 'yanuwana mata masu hawa acaba. Sai na tsinci kaina ina tafe ina farin ciki, ko babu komai dai yanzu ya fara sanina, hararar dana samu ma naji dadi, nafi wadanda bai san suna raye ba. Kai tsaye ofishinsu na bishi, kafin in isa har ya kai cikin ofis. Ina murda kofa sai ta wangale sai gani kicibus gabansa, bai amsa sallamata ba sosai a ciki ciki ya amsa kamar baya so, kallo daya yayi min ya dauke kai yaci gaba da dube duben littafin da yake kan teburinsa , yana tsaye. Na gaishe shi yayi kamar baiji ba, na fada cike da gatsali dr lukman nake nema. Ya fada cike da takaici, kuma aka ce miki nan ne ofishinsa ko? Na fada cikin tsiwa eh a nan na ganshi jiya shi yasa yau nazo nan nemansa. Sai ya dago da sauri ya dubeni cike da mamaki. Can ya dukar da idonsa kasa, yaci gaba da dube dubensa, bai bani amsa ba. Na rike kugu nace ga sakonsa dan Allah ko zaka ajiye masa? Ya sake dagowa a fusace ya fada cikin fushi, ke an fada miki nan ba ofishinsa bane, kije ki tambayi inda ofis dinsa yake. Ko nayi miki kama da wanda zaki bawa sako? Na murguda baki nace saboda nan matron maryam tace min inzo in same shi jiya shiyasa yau ma nazo. Na juya a fusace na fice na ki rufo masa kofar sosai. Sai naga ya biyo bayana, ya dade a tsaye yana kallona ina tafiya har na fice daga harabar, na barshi zuciyarsa cike da takaici. Na fara samun sa'ida a zuciyata tunda na fara samun damar yin magana dashi, duk da ba maganar arziki bace. Dana dawo ofishin da rana, sai na sami dr lukman a ofishin dr shureim baya nan. Mun dade muna hira da abokin yayana, naki tafiya da wuri ina saka ran ko zai dawo sai bai dawo ba, takaici ya isheni. Na koma gida cike da tunaninsa da sonsa zokar a cikin zuciyata, ko rufe idona nayi suffarsa ce ke fado min. Ina matukar son abinda ba zan samu ba, sai inyi kuka inyi dariya ni kadai bana mantawa da addua, ina neman agaji daga wurin Ubangijina. Nafi adduar Allah Ya yaye min sonsa akan adduar Allah Ya karkato da tunaninsa kaina, saboda a ganina shi zaifi yi min sauki duk da babu abinda ya gagari Allah. Sai inyi ta shawagina cikin asibiti a satin nan ko Allah zai sake hada ni da dr shureim, ban ganshi ba ko a hanya, ni kuma bana so inje ofishinsu saboda zai gane akwai wani abu a zuciyata. DUK KYAN TAKALMI 9 Sai dai kash! Na rabu da karatuna har 'yan ajinmu sun gane hankalina baya kan abinda ake koya mana, ban ma cika tsayawa a wajensu ba, bini bini a neme ni a rasa. Nima na rasa kaina, duk likitan da naga ya wuce da bakar suit sai na bishi da kallo in zata abin kaunata ne, sai inga ashe bashi bane, raina yayi ta baci. Matron maryam ta lura da haka sai tayi ta tambayata, amsar dai ita ce babu komai, idan aka dame ni ince bana jin dadin jikina. Haka ma dai a gida amsar iri daya ce, data makaranta ga duk wanda ya dame ni da tambaya. Na zama tababbiya a cikin satin nan da ban ganshi ba. Addua nake Allah Ya yaye min amma tamkar sonsa karuwa yake a zauciya, ban taba sanin haka dacin soyayya yake ba a rayuwata ko a film da littafi ban taba ganin irin abin da ya faru dani ba. Haka kawai na fara son mutumin da bai san inayi ba. Shiyasa a rayuwa ba a so ka cika baki akan abu, muddin ka cika baki akan wani abu tabbas abun nan sai kaga ya same ka. Bazan manta ba shekaru hudu da suka wuce akwai wata kawata ummi, ajinmu daya a shekara. Allah Ya jarrabe ta da son wani malamin mu mai suna abdul yasar, shima danji da kaine kamar dr shureim. Duk sanda taje wajensa sai yayi mata wulakanci ita kuma tazo tana kuka tana fada min, takaici ya kama ni maimakon in bata hakuri sai inyi ta zaginta, ina Allah wadari da halinta. Kullum sai ince mata me akayi aka yi da namiji? Har zata je yana wulakanta ta, duk a cikin samarinta ma babu kassararre, talaka, bakauye ma irinsa, duk sunfi shi haduwa ta rabu dashi mana. Sai tace min ita dai shi take so bata son sauran. Kuma taci gaba da nace masa tanayi masa wahala bayan mun gama makaranta daga karshe ya aureta. Ranan wata asabar da hantsi na shirya naci ado da wata atamfata shudiya, tunda ranar babu makaranta saina zankadawa yayana da matarsa karya nace a asibiti ake nemanmu zamu yiwa yara allurar rigakafi, yayana ya zaro kudin acaba naira dari biyu kamar yadda ya saba bani kullum. Na nufi gidan ummi domin inji hanyar da ta bi ta samu mai gidanta abar kaunarta abdul yasar. A kofar nasarawa gidanta yake duk da na dade banje gidan ba, amma naci sa'a na gane, rabona da gidan tun ranar da muka kai ta, haka da ta haihu ma a gidansu muka same ta muka yi mata barka, 'yar unguwar zango ce. Cike da fargaba na shiga gidan don kada ace min bata nan inyia asarar kudin babur din da na kashe nazo, ga na komawa gida. Sai naci karo da maigidanta a zauren gidan. Nayi sauri na duka na gaishe da malamina, ya amsa a gaggauce ko kallon kirki baiyi min ba, da alama dama ya tsane ni. Nasan dadin soyayya yasa ummi ta zazzage masa shawarwarin da na sha bata cewar ta rabu dashi bakauye ne, bai hadu ba. Babu wanda ya fada min haka, na lura tun a lokacin bikin yana kula sauran kawayenmu nice kada baya son yiwa magana. Na wuce cikin gidan sadan sadan don banga fuskar da zan tambaye shi tana nan ko bata nan ba. A tsakar gida na ganta ta buga tagumi da alama akwai damuwa a tattare da ita. Tana ganina sai ta mike da sauri ta rungume ni, na dauka dariya takeyi, sai naga hawaye. Na cika taf! Na tumbatsa da mamaki na rike ta ina tambayarta ko lafiya? Taja ni zuwa cikin dakinta muka zauna a gfen gado tana magana cikin kuka. Tace aisha farida wulakancin da yassar yake min ya isheni, don kawai yaga bazan iya rabuwa dashi bane. Nayo shiru na kasa magana, yayin da na shiga hankalina na fasa tambayar abin da nazo tambaya. Ashe har yanzu da sauran rina a kaba, ko a yanzu na auri dr shureim ashe idan naje gidan ma wulakanci yana nan zokar. Zuciyata ta fara yimin fada tana cewa farida ki yi ta kanki, ki cire son dr shureim imran idan ba kin zabi ciwon zuciya ya zama ajalinki ba. Na tambaya cikin sanyin jiki wai ke ummi yaya aka yi ma tun farko ya amince ya aureki bayan baya sonki? Tace ashe ba dake muka je ba, da maijidda lawan mukaje wajen wani malami a kurna. Sai na dafe kirji na fada a gigice, na shiga uku ummi! Malami kuma? Ta gyada kai tace shine yayi min aiki yace dole sai yasar ya zo ya aure ni ko ba a hayyacinsa ba. Kuma yazo din ya aure ni, har nake juya shi yadda nake so, sai bayan da na haihu ban koma ba. Kinsan ance idan mace ta haihu duk wani sihiri da tsarin da yake jikinta karyewa yake yi, sai tayi sabon shiri. Kuma kin san halin malaman zamanin nan sunfi so ka dauwama kana zuwa wajensu kana kai musu abin da ka kwakwala daga wajen mazan, idan ka dauke kafa bayan bukata ta biya sai su karya maka aikin, komai sai ya cakude dole sai ka dawo. Sannan yanzu bani da waya, bama magana dashi ta waya, daya fada min irin sadakar da zanyi dan duk ranar laraba yanayi min waya yace nayi sadakar sukari ko nono na aljanar da take kula da soyayyar da yasar yake min, kinga na dade banyi sadakar ba. Hankalina ya tashi, abin da nake gani a film yazo har gida. Nace ummi tsafi kenan fa? Tace haba dai tsafi, babban malami ne fa ya iya jan aya, baki ga matan manya da masu kudin garin da suke layi a gidansa ba, talakawa irina kadan ne. Ya iya aiki fa. Zuciyata ta fara rabuwa gida biyu, inje ko kar inje? Amma fa jikina bari yake yi, naji tana ambaton aljana a cikin al'amuran. Daga karshe zuciyata ta yanke min, kawai inje ni ma ayi min asirin da dole zaizo ya so ni ko da daga baya asirin ya karye ai dai naci riba tunda bani da buri a rayuwata irin in ga na same shi yayi min magana ma kawai, balle ace yazi gidanmu har anyi maganar aure dashi, ya aure ni na tare gidansa, ai ba karamar riba bace a rayuwata. Kuma idan haka ne in anyi auren ai sai in ringa komawa wajen malamin ina kara masa kudi yana cigaba da sona, yana fada min abinda zan bayar sadaka ina yin sadakar yadda son ba zai tafi daga zuciyarsa ba. Tunda kafin lokacin bikin na gama makaranta na fara aiki, ko da albashina na dinga biyan malam ko bai bani kudinsa ba. Sai na gyara zama nace ummi nima fa matsalar da take tafe dani kenan, nima irin naki ne ta same ni. Allah ya jarrabe ni da son wani likita a asibitin da nake attachment, amma fa likitan yafi ni haduwa nesa ba kusa ba, gashi daji da kai da wulakanci, har yafi malam yasar dinki. Na rasa yadda za'ayi ya saurareni ma balle ayi zancen soyayya. Baki ga yadda hadaddun likitoci mata suke binsa ba yaki sauraronsu. Kawayena biyu suke yi masa asiri dan ya sosu amma bai kama shi ba, ina jin ya shirya kansa asiri baya cinsa. Wani babban tashin hankali ma yana da mata ina jin ma baturiya ce a london suka hadu sukayi aure, ita ma yanaji da ita, nasan ta fini kyau nesa ba kusa ba. Ya zanyi? Ummi ta daki kafada ta tace ke dalla wawuya daman ke irin wannan mutumin kika samu amma zaki bari ya subuce miki? Lallai kin cika wawuya baki da wayo. Ai kawai kije a zuba miki aiki tuntuni zaiji ya tsani baturiya ya biyo ki, balle mai kudi ne, kina shiga zaki fanshe kudafen da kika kashe a kansa. Na girgiza kai nace babu ruwana da taba matarsa, suyi zamansu ni dai yaso ni kawai, tunda ina sonsa. Idan kuma akwai abin da malamin zai yi min na daina sonsa ni nafi son haka, saboda nayi iyakacin adduar da zanyi don na daina jin sonsa na kasa dainawa kullum karuwa yake ma. Ummi tace yaya za'ayi kice a cire miki sonsa ai shirme kenan. Ace yaji abin da kike ji koma ince fiye da yadda kike ji don an fi son namiji yafi na mace sai afi zama lafiya. Ke ban da abinki wata budurwar ba irin wannan take nema ba ma ta kai shi wajen malami a rike mata sai ko ta wanne hali, ko ba komai ai ka tsira da kudi ko babu soyayyar. Na girgiza kai nace ai ni ba kudinsa nake so ba, shi nake so. Ni na yadda ya so ni kada ma yabani kudinsa, na yarda idan na fara aiki in ciyar da kaina ba sai ya ciyar dani ba. Ummi ta rike baki tace Aisha farida haka kike sonsa kamar ki cinye shi? To ko asiri yayi miki irin wannan son dai bana lafiya bane. Na girgiza kai nace ko kadan, Allah ne yayi masa baiwar kyau, ilimi, arziki, da jan aji dole mata suke sonsa. Shi kansa baya son haka. Bai ma san inayi ba balle ace shi ma yana sona har yaje yayi min asiri. Jarraba ce kawai ta afka min, nima ba don ina so ba, haka Allah ya tsaro min. Sai na fashe da kuka. Ta rungume ni tace taso muje in kai wajensa yanzu, nima daman ina shawarar zuwa yau ko gobe, al'amarina ya cabe ni da yassar. Na mike tsaye ina goge hawayena yayin da ita kuma ta canja kayan jikinta ta saka wata jar atamfa riga da zani ta goya 'yarta da take barci akan gado, muka fito ta kullo dakin. Ta leka tayi wa matar kanin mijinta sallama wacce katanga ce kadai ta rabu tace da ita zamuje bakin asibiti zata raka ni inyi sare sare. Muka fito muka kama hanya tun a hanya na sanar mata ko kudin mota bani dashi, tace babu komai zata biya min, gakudin cefanenta nan yau ko cefanen ma bazatayi ba. Ce masa zatayi dan aiken ya zubar da markade. Ta juyo ta dube ni tace to ke yanzu da baki da kudi yaya za'ayi miki aiki? Dole fa sai kin kashe kudi idan kina son aiki yace. Tafiya mai nisan gaske mukayi a motar bus mai zuwa kurna, sai da muka hau acaba muka niki tafiyar kafa saboda babur ma ba zai iya shiga lokon ba, wahala iri iri muka sha kafin muka isa gidan. Nace muje dai muji, na san yadda zanyi. Sai na fashe da kuka. Ta rungume ni tace taso muje in kai wajensa yanzu, nima daman ina shawarar zuwa yau ko gobe, al'amarina ya cabe ni da yassar. Na mike tsaye ina goge hawayena yayin da ita kuma ta canja kayan jikinta ta saka wata jar atamfa riga da zani ta goya 'yarta da take barci akan gado, muka fito ta kullo dakin. Ta leka tayi wa matar kanin mijinta sallama wacce katanga ce kadai ta rabu tace da ita zamuje bakin asibiti zata raka ni inyi sare sare. Muka fito muka kama hanya tun a hanya na sanar mata ko kudin mota bani dashi, tace babu komai zata biya min, gakudin cefanenta nan yau ko cefanen ma bazatayi ba. Ce masa zatayi dan aiken ya zubar da markade. Ta juyo ta dube ni tace to ke yanzu da baki da kudi yaya za'ayi miki aiki? Dole fa sai kin kashe kudi idan kina son aiki yace. Tafiya mai nisan gaske mukayi a motar bus mai zuwa kurna, sai da muka hau acaba muka niki tafiyar kafa saboda babur ma ba zai iya shiga lokon ba, wahala iri iri muka sha kafin muka isa gidan. Nace muje dai muji, na san yadda zanyi. Munci sa'a babu layi sosai, mun tarar da maza uku a kofar gida, mata biyu a cikin gida. Muka gaishe su muka bi layi. Gabana sai faduwa yake tamkar zuciyata zata fito sarari, sai in zunguri ummi ince na fasa ta tashi mu tafi. Sai ta mintsine ni tace ba inda zamu je sai mun shiga. Na daure har layi yazo kanmu, muka shiga ciki. Daga sanda naga kasar duba da dogon carbi sai na tabbatar na kauce hanya, domin nasan makomar masu bin 'yan tsubbu masu duba, in har kaje wajen mai duba ya fada maka gaibu ka yarda dashi, to baka da sallah har tsawon kwanaki arbain. Allah ba zai karba ba. Ya san ummi sosai, ya san matsalolinta don haka sai ya hau mata bayani. Tace malam a bincika min dai. Sai ya jawo farantin kasa yayi zane zanensa ya hau yi mata bayanai kamar wanda ke karantawa. Na dubi kasar naga babu rubutu babu alamarsa na rasa inda yake karanto wadannan labarai, sannan na dubi sama da kasa banji motsin wanda yake fada masa ba. Yace ummi wannan tsohuwar budurwar nan tasa da yake so itace take raba ku, ta tashi tsaye tana asiri sai ta fitar dake ta shiga gidan, sannan faccalatki matan kanin mijinki da kuke gida daya, itama tana saka miki hannu saboda mijinki ya fi nata zuciyar nema, kin fi ta hutawa, don haka take so ta raba ku. Tags : Ummi ta fusata ta hau bayani. Lallai biri yayi kama da mutum, domin tun sanda mijina ya siyo mana generator sai ta yini a daki baata fito tsakar gida ba, haka ma zance tsohuwar budurwarsa ba su rabu ba suna tare har yanzu, naga sakonta a wayarsa. Yanzu malam yaya za'ayi? Sai naga ya karkace ya zayyano mata abubuwa kamar su turarruka na wuridi, kaji, dan akuya ja, farin kyalle da kudin yaran dazasu zauna aiki, dubu ashirin da biyar. Ko ta nuna damuwa ma batayi ba sai kawai ta ce gobe zan kawo dubu goma sha biyar a fara, don Allah malam ka ragargaza min su kamar yadda suke son su raba ni da mijina suma a rabasu da mazansu, ni kuma mu zauna daram ina so a kama min shi don wulakanci yake yi min kwanan nan har da cewa bai san inda yake kallo ba ya aure ni, don ni ba irin tsarin rayuwarsa bace. Sakacinki ne inji malam. Ya juyo ya dube ni sai na takure a lungu kirjina yana dukan ukuk uku. Yace ke fa meye matsalarki, ko baki fada ba zan iya ganin asiran da akayi miki a jikinki, ki tashi tsaye wajen neman tsari. Ummi ta kwanto da 'yarta daga bayanta ta gyara zama tace malam, aisha farida kawata ce, a taimaka mata. Matsalarmu kusan iri daya ce, ayi mata bincike tukunnan. Ta bukaci ina saka abin sadaka kafin ya fara, sai ummi ta zaro dari biyu zata mika masa na rike hannunta nace ba sai an bincika min ba malam zan fada da bakina. Na koro masa bayani tas, sai yayi dariya ya kyakyata yace wannan karamin aiki ne a wajena, idan har zaki sayi kayan aiki na baki kwana biyu inda dr shureim imran ne kim gama samunsa. Ina jin haka sai naji farin ciki ya lullube ni nayi dariya, na tambaye shi me dame za a siya? Sai yayi min zancen abubuwa daban daban, wasu na sansu wasu ban sansu ba. Aka hada kudin ya kama naira dubu ashirin da daya. Sai na dafe kirji nace malam bani da kudi ko zaka yi min bashi idan komai ya kankama sai in biya? Ya dubi ummi cike da bacin rai yace ina kika samo min wannan yarinyar? Baki fada mata dokar aikina bane? Sabon shiga ce ko? Toh ni bana fadar farashi a nemi ragi balle ace inyi a bashi, a cikin kudin nan babu sisi nawa, duk na rauhanai ne. Ummi tace ayi hakuri malam, laifina ne ban fada mata dokokinka ba zamu dawo gobe tare zamu nemo kudin mu kawo. Mun goda. Banyi godiya ba na kada kai na fito, hankalina ya gama tashi. Muna fita kofar gida ummi ta hau yi min fada tana cewa me yasa ban bari anyi min bincike ba inji bayani dalla dalla ba, sannan me yasa nace ayi min aiki bashi alhali tun a kan hanya na baki labarinsa? Nace to bani da kudi ko naira hamsin ta kaina bani da ita. Me zance? Tace ki sayar da kadararki mana. Nace ai bani da ko barimar gwal balle dan kunne. Ta tabe baki tace ni dai shawarar da zan baki itace kije kisan abinyi don nima nan da kika ganni bashi zanje in ciyo in kai masa idan aiki yaci da kansa zai baki kudi kije ki biya. Malamin nan fa aikinsa kamar yankan wuka, sha yanzu magani yanzu. Kije kiyi tunani zuwa gobe ki samo kudi, kizo mu kai don ni ma daga nan gari zan shiga neman bashi. Ta bani kudin mota mukayi sallama na shiga motar unguwarmu, ita kuma ta shiga motar dawanau ban san inda ta nufa ba. Ina zaune a mota tamkar gunki ina tunani, sai da kondasta yyayi ta magana sannan na gane dani yake, na mika masa kudin mota. Haka da aka zo inda zan sauka ma na manta har aka wuce dani, sannan na ankara nace a sauke ni. Saida na dawo baya. Na shiga gida a cakude, narasa inda zan saka raina, tunanina gaba daya ya koma wajen inda zan samo rancen kudi in kaiwa malam gobe. Cikin unguwar nan da batsewarta babu matar da zata iya fitar da dubu biyar ma kai tsaye saboda talauci. Da yamma na shirya na fita neman kudi gida gida, da kyar na hado rancen dubu biyu. Na zarce kai tsaye shagon da musbahu yake sana'a. Sai yayi matukar mamakin ganina ya tambayeni lafiya ya ganni a hargitse haka? Na fada masa cewar matsalar kudi ce ta taso min, bani da lafiya. 'Yar karamar tiyata za ayi min gobe a asibitin ana neman naira dubu ashirin. Sai ya dafe kirji yace aisha farida babu inda zan sami dubu ashirin a yau. Ai ko bashi babu in da zan samu. Ko idan anyi wa likitan bayani zai yarda yayi miki aiki a bashi karshen wata sai in biya shi. Na girgiza kai nace babu zance bashi kuma dole in hada kudin daga yau zuwa dare. Yace to inje gida zai aiko yaro ya kawo min abin da ya sauwaka. Zaije ya fita ya nemo abinda ya samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa guda banyi ba da shiga gida sai ga dan aike da dubu uku har da doguwar wasika yana mai bani hakuri abin da ya samo kenan. Amaa zaici gaba da nemowa zuwa gobe. Ya jero min kalaman soyayya ko gama karantawa banyi ba na yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan in kai. Ina zaune a mota tamkar gunki ina tunani, sai da kondasta yyayi ta magana sannan na gane dani yake, na mika masa kudin mota. Haka da aka zo inda zan sauka ma na manta har aka wuce dani, sannan na ankara nace a sauke ni. Saida na dawo baya. Na shiga gida a cakude, narasa inda zan saka raina, tunanina gaba daya ya koma wajen inda zan samo rancen kudi in kaiwa malam gobe. Cikin unguwar nan da batsewarta babu matar da zata iya fitar da dubu biyar ma kai tsaye saboda talauci. Da yamma na shirya na fita neman kudi gida gida, da kyar na hado rancen dubu biyu. Na zarce kai tsaye shagon da musbahu yake sana'a. Sai yayi matukar mamakin ganina ya tambayeni lafiya ya ganni a hargitse haka? Na fada masa cewar matsalar kudi ce ta taso min, bani da lafiya. 'Yar karamar tiyata za ayi min gobe a asibitin ana neman naira dubu ashirin. Sai ya dafe kirji yace aisha farida babu inda zan sami dubu ashirin a yau. Ai ko bashi babu in da zan samu. Ko idan anyi wa likitan bayani zai yarda yayi miki aiki a bashi karshen wata sai in biya shi. Na girgiza kai nace babu zance bashi kuma dole in hada kudin daga yau zuwa dare. Yace to inje gida zai aiko yaro ya kawo min abin da ya sauwaka. Zaije ya fita ya nemo abinda ya samo. Nayi godiya na tafi. Ko awa guda banyi ba da shiga gida sai ga dan aike da dubu uku har da doguwar wasika yana mai bani hakuri abin da ya samo kenan. Amaa zaici gaba da nemowa zuwa gobe. Ya jero min kalaman soyayya ko gama karantawa banyi ba na yayyaga na zubar, burina in hada kudin nan in kai. Uwani uwar adashe ita kadai na tabbatr zan iya samun rancen kudi a wajenta ko nawa ne saboda itace naga koda yaushe mata suna aiko mata da zubin kudin adashe, ina hango shigarsu da fitarsu daga windon dakina domin dakinta na kusa da dakina. Ina idar da sallar magriba na tabbatar abida tana daki tana wuridi ba zata fito tsakar gida ba, sai tayi sallar ishai kamar yadda ta saba. Sai nayi sanda na fito dakina na fada dakin uwani, sai tayi mamakin ganina a wannan lokaci, naci sa'a maigidanta bai dawo ba. Ta saka fitilar kwai a gaba tana kirga kudi kashi kashi. Farin ciki ya rufe ni da naga kudin nan sai na shiga marairaice mata inayi mata dadin baki cewar ta ranta min dubu goma sha bakwai zan biya ta gobe da yamma. Ta tsorata matuka har da dafe kirji ta tambaye ni, me zakiyi da kudi haka? Na shaida mata kawata ce zata haihu a asibitinmu ance ba zata iya haihuwa da kanta ba sai an yi mata tiyata. Ga mijinta ba ya gari yana lagos. Amma ya sako kudin ta banki,

Chapter 5 of 23