Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
addabarta a rayuwa, idan ta tuno rashin lafiyar abida sai taji jikinta yayi sanyi lakwas. Koda yaushe sai ta saka lambar dr shuraim a gaba tayi ta kallo, sai taji kamar ta kira shi ko ta tura masa sako, sai kuma ta fasa. Amma ranar juma'a ta tura masa sakon adduoin juma'a amma bai bata amsa ba. Ta fara shiga damuwa, amma sai tayi masa uzuri , watakila bai cika karanta sakonni ba kasancewar aiki yayi masa yawa. Ranar litinin da misalin karfe goma da rabi na safe aisha farida na kwance akan tabarmarta tayi shiru tana tunani, rashin lafiyra abida tana damunta matuka, musamman yanzu da tayi waya shagamu tayi tayi su ba wa abida waya suyi magana, aka ce bacci take yi. Sai take ganin kamar jikin ne yayi tsanani suke boye mata. Tana so ta tashi ta dora abincin rana, domin yara sun kusa dawowa daga makaranta, amma ta kasa tashi saboda damuwar da tayi mata yawa a zuciya. Wayarta tayi ruru tayi sauri ta dauka ta duba, sunan yaya hussaini ta gani, sai tayi matukar mmaamki da ganin kiransa, don bai dade da fita aiki ba ya bata kudin cefane. To me yasa ya kira? Ko mantuwa yayi ne a gidan? Take tambayar kanta da kanta. Tayi sauri ta dannan gami dayi masa sallama cike da tsananin fargaba, tayi shiru tana sauraron abin da zai fada mata. Yayi gyaran murya yace yaya kuke? Gidan duk lafiya? Yara basu dawo daga makaranta ba ko? Sai tace eh basu dawo ba. Ina gida kowa lafiya kalau. Yace to madallah, daman na kira ne naji halin da kuke ciki. Kada ki damu, ki cigaba da hakuri, kici gaba da kula da yara. Muyi wa abida addua, naga kin damu duk kin rame, kina yawan koke koke. Nima na damu har bana iya aiki yadda ya kamata, har 'yan ofis dinmu sun gane ina cikin damuwa. Yanzu na yanke shawara a raina idan yara suka yi hutu sai nima na dauki hutu mu tattara mu kaura shagamu. Idan hutuna ya kare sai na dawo, idan kuma na samu aikin yi a shagamu ko wata sana'a sai muyi zamanmu ba sai mun dawo kano ba. Rashin abida a kano ya zama tamkar tuwo gaya babu miya. Ni, ke da yara duk bamu jin dadin rayuwarmu. Ko abinci kika dafa babu wanda yake iya ci yadda kika kawo min haka kike zuwa ki dauke, haka na lura yara ma ba sa iya ci, kema haka. Tulin abinci ake juyewa almajirai kullum. Aisha farida ta rushe da kuka, yayin da shima kukan ya turnuke shi, sai yayi sauri ya katse waya. Ta kifa kai akan filo tayi ta rusa kuka tamkar idonta zai fashe. Tana ta addua Allah Ya yayewa abida wannan ciwon. Wayarta ce ta sake yin kara. Nan da nan ta katse kukan ta dauka ta duba sunan barr muazzam ne. Ta goge hawaye da sauri ta tashi zaune, sannan ta matsa waya da yin sallama. Barr muazzam yayi murmushi yace kanwata kwana biyu, kina nan kuwa? Tayi murmushi tace ina nan yayana, na sha kiranka baka amsawa, ko aiki ne yayi maka yawa? Yace kwarai kuwa, satittikan nan uku duk bana zama, daga bakwai na safe zuwa na dare. Alhmdlh abin da ake nema ya samu. Daman case din dr janan ne an tafka sharia na shawo kanta, ta bude baki tayi bayani, ta tonawa su izzuddin asiri, ta kuma fadi inda za a iya samunsa shi da abokansa. Aka yiwa 'yan sandan can garin waya don su kamo shi. Sun kawo mana shi kano, har ya bayyana a kotu, kuma ya amsa laifinsa. Yanzu haka kotu ta wanke janan, an tabbatar ba ta da laifi, an sake ta tana gidansu shi kuma yana daure. Farin ciki ya lullube aisha farida, tayi dariya tace alhmdlh, Allah Mai iko, amma yaya muazzam na taya ka murna, Allah ya kiyaye gaba. Yanzu a wanne hali kuke ciki kai da ita? Yayi murmushi ya lumshe ido yace komai ya daidaita amma dai ba dukka ba, kinsan komai sai a hankali. Kanwata na riki abubuwan nan guda uku, nayi addua, nayi hakuri matukar hakuri kuma naci riba. Naja mata aji, na nuna mata yanzu babu zancen soyayya a tsakanin mu, ina da wacce zan aura. Na nuna mata bani da wata alaka da ita face ta aiki. Ta bani hadin kai kawai in gudanar da aikina yadda ya kamata. Data tabbatar da haka, sai ta saduda ta ajiye wannan zaren da take ja na aji ta bude baki ta amsa duk abubuwan da na tambaye ta, sannan ta gudanar da duk abin da na umurce ta tayi a kotu. Na lura ashe daman tana sona, boyewa kawai takeyi, ko kuma nace yanzu ta fara sona da taga halaka. Ni daman bani da matsala da iyayenta, tun da can suna sona balle da suka ga irin taimakon da nayi musu. Ji suke tamkar su dauko ta su kawo min ita gidana. Ba soyayyar iyayenta nake nema ba, ina so janan ta soni da kanta ba sai wani ya tilasta mata ba, ko don wani dalili ba. Ta soni don Allah, muyi zaman so da yadda a tsakanin mu, ko babu ran mahaifanta. Aisha farida tace gaskiya ne wannan. Allah Ubangiji Ya tabbatar da alkhairi. Yace amin malamata, menene mataki na hudu da zan taka, kin san fa duk abin da kika ce dashi nake amfani, don kin fini wayo ke kuma anti abida ta fiki wayo. Ku dora min karatun. Aisha farida ta kyalkyale da dariya, tace uhmm yayana kenan, har ka bani dariya wallahi. To mataki na hudu da abida ta fada min shine tunda yanzu ta san da kai, ta kuma san abinda ake ciki, sai ka zama mai yawan kyautata mata, da haka zata so ka fiye da kowa. Barr muazzam yayi murmushi yace idan haka ne to ai na riga na haye mataki na hudu don ni mai yawan kyautata mata ne, har ita da kanta ta rubuto min sakon godiya a waya, ta yaba da hakan. Dazun nan ta rubuto min wannan sakon. Mene mataki na biyar kuma, ko baka taka shi ba? Aisha farida tace eh to inaga nima a mataki na hudun nake amma abida ta fada min mataki na biyar din tace ka nuna kama sonta tamkar kafi kowa sonta a duniya. Kamar kulawa da duk halin da take ciki, da kuma tattalinta, tamkar kwai, ka nuna ko kuda ba kaso ya taba ta. Idan ka yi mata haka ita ma zata so ka, zatayi kokarin ta mallake ka a rayuwarta, kaga sai ka aure ta. Barr muazzam yayi ajiyar zuciya yace kice min gangaro na kusa samun janan kenan? Zanje na dorawa baraka wannan karatun. Aisha farida tace af! Na manta ban tambaye ka baraka ba, ina take? Wanne hali take ciki? Yayi dariya yace mutuminki nurudden dai ya saduda daya ga ta share shi, sai yake shishige mata, ita kuma tana watsar dashi. Yanzu haka ya fara neman shawarata wai yana ga zai rabu da nafisa. Yace min baraka tace ta amince ta auro nafisa ya hada su, su biyu. Ita kuma nafisa tace sai ya saki baraka kafin ta aure shi. Shine yake cemin da ya saki baraka gara ya fasa auren, domin baraka ce mace ta gari da take yi masa biyayya. Aisha farida tace yawwa ka cewa baraka ta taka mataki na hudu shine taci gaba da kyautata masa fiye da na da. Sannan mataki na biyar ta nuna masa tsantsar soyayya kamar tafi kowa sonsa a duniya fiye da yadda nafisa ke sonsa. Brr muazzam yace lallai ke malama ce, ke kuma yaya naki gogan, me kuke ciki? Tayi murmushi ta lumshe ido tace alhmdl. Dr shuraim yasan dani yanzu, ya san sunana, har ya damu da halin da nake ciki. Ta kai ta kawo dr shuraim ya nemo lambar wayata ya kira ni a waya ya gaishe ni ya tambayi jikin antina abida. Ina ga yanzu zan taka mataki na hudu, zan cigaba da kyautata masa sosai har sai ya kaunace ni yaji sona tamkar ransa zai fita, sai ya saki jiki dani, don bana tantama ya fara sona. Sai in taka mataki na biyar shine ina nuna masa tsantsar kauna nima. Barr muazzam yace amma abu yayi kyau, Allah ya tabbatar da alkhairi, Ya zaba mana abin da yafi alkhairi a rayuwarmu. Har yanzu jikin anti abidar ne bataji sauki ba? Aisha farida ta marairaice tace ba za'a ce babu sauki ba, amma har yanzu ana nan ana fama. Babbar matsalar ma da 'yan uwanta suka zo suka dauke ta shine dr shuraim din yake fada min kada su jifga mata sassake sassake ya jawo mata ciown koda, domin ciwon yana da alaka da ciwon koda. Barr ya girgiza kay tace subhanallah! Allah Ya kiyaye, Allah Ya bata lafiya. Kiyi kokari ki kira su a waya ki fada musu abinda likita ya fada, kada su bata sassake. Yanzu zan turo miki katin waya don kiyi magana dasu yadda ya kamata. Aisha faida ta matse hawaye tace nagode da wannan hidima da kake yi min ko wani dan uwan nawa na jini ba yayi min abin da kake yi min.....sai ta rushe da kuka. Ya girgiza kai yace dadina dake saurin kuka kamar wata tsohuwa. Ki daina kuka kinji ko? Duk abin da ya samu bawa Ubangiji Yana sane, kuma Zai yaye masa. Sai kinga sakona sai anjima. Aisha farida tace sai anjima, Allah Ya saka da alkhairi. Ya kashe waya ba dadewa taji kara a wayarta, da alama sako ne ya shigo. Tayi sauri ta duba sai taga brr ne ya turo mata da kati. Data loda sai taga na 1500 ne. Ta kira shi har ta katse bai dauka ba, sai ya kirata daga baya. Tace dama godiya zanyi maka, naga kati na gode. Yace ba damuwa ba sai kin yi min godiya ba, don nabaki wannan dan kati. Ya kashe wayar ta koma ta kwanta ta dubo lambar dr shuraim tayi ta kallo tana shawara a ranta ta kira shi ko kada ta kira shi? Sai ta yanke shwarar ta kyale don ta lura baya son damu, idan ya kira da kansa zaifi kamar yadda rannan yaga dama ya kira da kansa. Sai ta jiye wayar a gefe zuwa jimawa sai ta sake jawo wayar ta fara rubuta masa sakon gaisuwa da fatan alkhairi. Har zata tura sai ta fasa ta goge da ta tuna ta tura masa na juma'a bai bata amsa ba, kuma bai kira ba. Ta duba agogo karfe goma sha daya da rabi 'yan makaranta karfe goma sha biyu zasu fara dawowa daga makaranta, gashi bata dora abinci ba, don haka sai ta mike tsaye zata je ta dora abincin sai taji wayarta ta dauki ruri. Ta dawo ta zauna da sauri ta jawo wayar ta duba, sunan dr lukman ne ya bayyana, sai farin ciki ya rufe ta, tayi murmushi tayi sauri ta danna, cike da fara'a tayi masa sallama gamu da cewa yayana ina ka shige ne kwana biyu naji ka shiru? Yayi dariya yace kaji marar kunya. Ni zan neme ki ko ke zaki kira ki gaishe ni ki samu lada? Ko baki kirani ba naga flashing ko pls call me ai zan kira ki. Amma baki neme ni ba. Ko da yake jan aji ne irin na 'yan mata ko? Yanzu muke maganarki da abokina dr shuraim. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido ta tambaya cike da zumudi, me yace? Dr lukman yace yanzun nan ya fice da yaga zan kiraki. Daman nace sai na fada miki ko baya so. Wai ya akayi kike burge abokina ne, ni tunda nake dashi a asibitin nan shekara da shekaru ban taba ganin macen da ya taba maganarta ba balle ya yabe ta, sai ke? Yace kina burge shi saboda kina da hankali. Ga ki da kunya, kara, kawaici, ga hakuri da shiga ta mutunci, uwa uba kin da aji ba ki cika shishigi da rawar kai irin na 'yan matan yanzu ba. Sannan haka kawai yake tausayinki musamman da ake ce ke marainiya ce. Sannan yace kina da matukar kirki da yaji ashe kace kike daho mana dambu da danwake. Kinsan da hannunsa ya dauki lambarki a wayata, yace zai kiraki ya ji jikin yayarki. Aisha farida tayi ajiyar zuciya tayi dariya. Tace Allah sarki, haka Allah Ya ke shirya al'amuran Sa duk yadda yake so. Dr lukman yace munafukai ne ke dashi, kunsan abin da yake tsakaninku. Ai idan tayi tsami zamuji. Shima sai kwana kwana yake yi min, idan na tambaye shi. Amma gaskiya na sha mamaki da naga yana yawan USA Novels BOOK DUK KYAN TAKALMI 2* 13 Damuwa dake, don ni nasan shi nasan ra'yainsa, nga yadda yake kushe mata. Ban taba jin ya yabi wata budurwa a duniya ba ma balle a cikin asibitin nan, shine na kiraki naji meye sirrrin? Aisha farida ta kyalkyale da dariya tace ba wani sirrri wallahi, Allah ne Ya hada jininmu, nima yana burge ni sosai. Dr lukman ya gyada kai yace gaskiya kanwata idan har wannan abu zai tabbata tsakaninki da shuraim zanfi kowa taya ki murna, don kinyi dace da mutum na gari, mai tsananin kirki da tausayi, mai kulawa. Aisha farida ta dafe kirji ta lumshe ido tace Allah yayana haka ne? Yace inayi miki fatan alkhairi, sannan ina taya yayarki da addua ta samin sauki. Zanje wajen marasa lafiya, sun taru suna jirana. Ya katse hiran. Aisha farida ta sulale ta kwanta, tayi shiru tana sake maimaita kalaman dr lukmann, mamaki ya rufe ta, tamkar a mafarki ba a ido biyu abubuwan suke faruwa ba. Anya kuwa itace, ko dai mafarki ne? Take tambayar kanta da kanta. Ta sake gasgatawa babu abin da yafi addua da hakuri a duniya. Ta dinga yi wa Allah godiya da Ya nuna mata wannan rana. T dinga kwararo addua tana rokon Allah ya karawa dr shuraim sonta, kuma Ya sa ya aure ta. Ta tuno abida taji daman abida tana nan taji irin wannan dadadan labari. Sai tayi wa abida addua Allah Ya bata lafiya. Tana zaune ta kasa tashi ta dora abinci bata ankara ba, sai taji muryar 'yan makarnata sun fara dawowa. Ta ji wani kara kwarakwacam anyi wurgi da jaka da robar abinci a bakin kofar dakinta, ta san gajiya ce da yunwa take addabarsu. Tayi wuf! Ta fito. Ta shiga llallabasu tana yi musu dubaru tana koda musu dadin garin kwaki da mai da yaji, ta aika su suka siyo ta kwada musu suka ci suna murna. Tace musu haka 'yan makarantar kwana suke yi, gara ku fara koyon ci kafin ku tafi sakandire ta kwana. AISHA SHURAIM HIMMA BA TA GA RAGO!!! BABI NA GOMA SHA BIYU Fiye da sati biyu dr shuraim bai kira aisha farida ba, itama bata kira shi ba. Don haka sai ta fara shiga kokonto anya kuwa dr shuraim yana sonta? Da yana sonta ai ba zai share ta haka ba, wata kila tausayinta kawai yake yi ba soyayya ba. Jikinta yayi sanyi, ta fara shiga damuwa, bata da walwala abubuwa suka taru suka yi mata yawa. Kowa ya kalle ta sai ya tambaye ta me yasa ta rame. Taci gaba da daurewa tana ta addua tana neman agaji daga Ubangiki Mai kowa, Mai komai. Son dr shuraim ya zame mata tamkar ruwan shanta, ya zame mata abincin cinta, kuma mayafin lullubarta. Duk da daurewa da tayi, sai da ta kai ta kasa cigaba da daurewa saboda ji take tamkar zuciyarta zata yi bindiga ta fashe don kunci. Tsananin son dr shuraim da kuma rashin abida abokiyar shawararta, itace mai bata shawara da kwantar mata da hankali. Tasan da tana nan da tuni ta fada mata abin da ya kamata tayi nan gaba. Ranar talata bayan yaya hussaini ya fita aiki, yara sun tafi makaranta, sai ita kadai a gida. A kwance take a daki ba tare da tana jin dadin kwanciyar ba. Ta yanke shawarar tunda ga dan kudi a hannunta bari ta harhada tayi musu danwake, ta kai musu asibiti ko Allah Zai sa ta dace ya ganta ya tuno da ita don tana tunanin ya manta da ita ne. Tayi zumbur ta miike ta shiga shirye shiryen yin dan wake. Kafin karfe goma na safe ta gama tsab, ta zubawa yara na su a flask. Ta shiga tayi wanka ta fito ta dauki fiye da mintina talatin tana kwalliya. Wata sabuwar atamfarta ta saka diamond mai kore da ja, aka dinka mata riga da skirt matsattsu, ta sami bakin gyale da bakin takalmi ta saka. Sai dai kash! Ta juya ta sake juyawa ta dubi jikinta sosai, sai taji ba zata iya fita a haka ba. Ta san shi kansa dr shuraim din ma ba burge shi zatayi ba. Don haka ta ajiye gyalenta ta dauko bakin hijabinta sabo dal ta siya kwanan nan naira dubu daya irin wanda ake siyarwa a dinke mai hannaye kamar riga. Ya shiga da takalminta mai dan tsini. Ta kullo kofar dakunan bayan ta debowa yara kayan makarantar islamita da flaski din abincinsu ta mika dakin uwani taroke ta arziki idan yaran sun dawo ta basu abincin su ci su sauya kaya idan lokacin islamiya yayi su tafi. Tace itama ba dadewa zatayi ba, zata kai wa marar lafiya abinci a sibiti. Uwani ta amsa mata cike da fara'a gami da alkwarin zata aiwatar da abin da ta umurce ta, ta hada ta yiwa marar lafiyar adduar samun sauki. Aisha ta dauki kwandon da ta saka flask din abinci da plates da cokula, bayan yaji dakakke a 'yar roba, da 'yar robar mangyada. Tana tafe cikin nutsuwa har ta fito daga lokonsu ta sami adaidaita sahu nan da nan ta haye. Ita kanta tasan tayi kyau, ko ba a fada mata. Jama' da dama sun dasa don samari suna ta binta sun kai su uku sunayi mata magana. Suna sonta bata kula su ba. Kuyi hakuri an riga an bada ni. Amsar da take ba su kenan. Tana isa cikin asibitin malam ta doshi ofishin dr lukman, sai taji kirjin ta ya fara dukan uku uku, don fargabar abinda zata tarar daga dr shuraim. Tana hawa kan barandar ofishin sai ta hango dr shuraim da wasu dattijai maza su uku sun tunkaro ta, ma'an suna fitowa ita kuma tana shiga. Sai taji wani mummunan faduwar gaba. Ya tsura mata ido sosai yana kallonta, har sai ta taji kunya ta sunkuyar da idanuwanta kasa. Suka wuce ita ma ta wuce, ta juyo a hankali zata dube shi, shima ya juyo sai gaba dayansu suka gaggauta juyawa da sauri. Ta shiga fargaba saboda ta dimauce, bata gaishe shi ba, kuma ya kamata ta gaishe shi din. Don haka ne ma yake ta kallonta har da waiwaye. Abin da zuciyarta ke zayyano mata kenan. Jikinta a sanyaye ta shiga ofishin dr lukman, taci sa'a yana nan shi da abokinsa dr mohd. Bayan ta gaishe su, sai ta ajiye kwandon abinci a gaban dr lukman. Tace ga danwake nayi muku. Yayi farin ciki, yayi godiya sosai. Dr mohd ta dubi dr lukman yace lukman zaka bani 'yar kanwar nan taka kuwa? Ina sonta tun ranar da na fara ganinta. Kirjin aisha farida ne ya burededen dukan uku uku har ta fara dana sanin zuwanta nan a yau. Ana wata sai ga wata, yanzu idan dr shuraim yaji ko da wasa dr mohd ya furta yana sonta, ai bar masa zaiyi ba zai kara nuna alamar so ba. Ta tsunduma cikin wannan dogon tunani, sai da dr lukman ya ambaci sunanta ta dawo da hankalinta gare su. Yace kanwata kinji wai in bashi ke? Tayi murmushin karfin hali tayi shiru. Dr mohd yaci gaba da kallonta, kallo mai cike da so da kauna. Ta sunkuyar da kanta kasa, tana mai tsananin jin kunya hade da bacin rai. Dr lukman yayi dariya ya daki kafadarsa yace kai da kake min tsiya wai ba kanwata bace, bamuyi kama ba, sai inga wanda zai baka 'yar. Dr mohd yayi dariya yace yi hakuri don Allah, yaya na daina. Yana rufe bakinsa sai dr shuraim ya shigo. Nan da na hankalin aisha farida ya sake tashi. Ta fara addua kada Allah Ya sa acigaba da zancen soyayyar nan. Tayi sauri ta sulalo daga kan kujera ta gaishe shi. Ya amsa cike da far'a, sannan yaci gaba da kallonta. Can yace lukman dama kanwarka ce na hadu da ita a baranda nake mata kallon sani, amma ban gane ta ba. Naga ta sauya. Aisha farida ta dube shi a kunyace ta sunkuyar da kai. Dr lukman yace me ka ga tayi? Ta sake yin kyau ko? Ai an gama makaranta ana hutawa a gida. Dr mohd yace kai fa lukman yaya ne ka bari in fadi da bakina mana, sai kace tayi kyau, kai yayan kwabo ne ko? Su biyu suka tuntsire da dariya yayin da dr shuraim ya tsaya cak! Ya dubi dr mohd ya juya ya dubi dr lukman ya juyo ya dubi aisha farida nan da nan taji zuciyarta na dukan uku uku. Daga dukkan alamu dr lukman ma baiji dadi da dr mohd ya fadi haka a gaban dr shuraim ba, domin yana kyautata zaton dr shuraim yana son aisha farida, furatwa ne kawai baiyi ba. Dr shuraim ya gaggauta daukar ajiyarsa a loka ya fice da sauri. Aisha farida ta kame a zaune, yayin da numfashinta yake kokarin daukewa gaba daya, babu wanda yake magana a tsakanin su biyun, dr mohd ne kadai yake surutunsa. Haushi da tsanarsa suka bayyana a fuskar aisha farida. Ta dauke shi a matsayin tamkar mutumin da ya dauko wuka mai kaifi ya dubi cikinta ya burma mata, ma'ana ya kashe ta. Domin ya rugurguza mata walwalar rayuwarta duniya da lahira. Dr mohd yayi ajiyar zuciya, ya dubi aisha farida yace bani lambar wayarki aisha umar. Ta dago da sauri ta dube shi, duba na takaici ba tare da ta iya furta kalma gida daya ba. Dr lukman yayi sauri yace ita zaka tambaya ko ni yayanta zaka tambaya na ba izini ka karba? Ita ma na umurce ta ta baka? Tayi murmushin karfin hali ta mike tsaye a sanyaye ta yi musu sallama zata tafi. Dr mohd ya nemi ta kara zama suyi hira, tace gidan babu kowa sai ita kadai, don haka take so ta koma da wuri. Dr lukman ya ciro naira dubu daya ya mika mata, yace tayi kudin mota. Tace ya bari ba zata karba ba, tana kudin motarta. Dr mohd ya zabura yace ka bari kawai zan bata ko kuma ma marasa lafiyan da suke jirana suyi hakuri sai na kai matata gida sannan zandawo. Dr lukman yace wannan kyautata ce ta daban a matsayin na yayanta, kai da ita kuma daban. Kuma wallahi sai kin karba kinji ma na rantse. Aisha farida ta saka hannu biyu ta karba gami da yin godiya, cikin sassanyiyar murya. Dr mohd yace Allah sarki, kaji yarinya mai ladabi, gaskiya nifa da gaske nake. Lukman zanje in kai ta gida in dawo muyi maganar gaskiya ba wasa nake ba. Tayi wuf! Ta fice da sauri don bata so ya biyo ta, shima ya fita da sauri ya biyo bayanta ta, ya umurce ta ta jira shi su tafi tare. Wani babban tashin hankalin kuma sai ya tura kofar ofishin dr shuraim ya leka sai ga dr shuraim a zaune a kan kujerarsa yana danna laptop. Ya dagi da kyawawan idanuwansa ya dubi dr moh sannan ya sake daga ido ya hango aisha farida a gefensa. Sai ya sunkuyar da kai, yaci gaba da danne dannensa. Amma daga kallon fuskarsa kasan zuciyarsa a bace take. Dr mohd yace abokina zo muyi rakiya, wancan dan iskan lukman yaki yace shi a dole babban yaya ne. Ya girgiza kai yace nima yaya ne, ba zanje ba. Kaje sai ka dawo. Aisha farida tayi wuf! Ta bar wajen, tafiya take ba tare da tasan inda take jefa kafarta ba. Kawai wani lungu ta samu ta dinga kutswa cikin asibitin maimakon ta nufi bakin gate sai tayi ciki. Kafin dr mohd ya waiwayo sai yaga wayam! Bata nan. Ya fito da sauri ya dudduba hanyar gate ba ta nan. Ya duba kudu da arewa, babu ita babu dalilinta. Sai ya cika da mamaki, ya shiga kokonto da wasi wasi don haka ya koma ciki da sauri don ya shaidawa yaya lukman. Dr lukman yayi dariya yace kunyarka takeji, kuma tana da tarbiya bata so a ganta da namiji , ni nasan halin kanwata. Dr mohd ya takura sai an kitay a waya yaji inda take. Aisha farida ta isa ofishin matron maryam ta iske bata nan, sai sababbin dalibai da aka turo daga makarantarsu. Yawancinsu ma duk sun santa. Bayan sun gaisa ta tambaye su matron sai suka ce ta fita. Aisha ta jawo kujera ta zauna tana huci, nan da na suka hau tambayarta bata da lafiya ne? Tace gajiya ce kawai, tana so ta huta sannan ta tafi. Bata rufe bakinta ba sai wayarta ta dau kara. Ta bude 'yar karamar jakar da ta saka kudin motarta da wayar ta zaro wayar, sunan dr lukman ne ya bayyana. Sai taki amsawa har ta katse. Tana katsewa ya sake kira, don haka ta tabbatar kiran yana da amfani, sai ta amsa. Tambayar da ya fara mata itace kina ina? Tayi inda inda sannan tace ina cikin adaidaita sahu hanyar komawa gida. Yace toh shikenan. Allah Ya kaiki gida lafiya. Ya kashe wayar tana jiyo muryar dr mohd amma bata gane abin da yake cewa ba. Anan zan dakata mu hadu a DUK KYAN TAKALMI 3 kuji yadda zata kasance. Daga 'yar uwarku JUT. See Translation January 10, 2015 at 7:26pm · Public 35 DUK KYAN TAKALMI 3* 1 Tayi ajiyar zuciya mai karfi.sannan ta kwantar da kanta akan teburin da yake gabanta don ta rasa abun da yake yimata dadi innalillahi wa inna ilahi raji`un,ta ke ta ambato,sai da ta dauki tsawon mintina 20 bata iya dago waba,ta mike tsaye da kyar yayin da idanuwanta suka yi ja,alhalin kuma ita ba kuka takeyi ba daliban dai har yanxu tambayarta sukeyi,anya kuwa lafia? tace lafia kalau kawai dai gajiya ce. Tayi musu sallama tabar musu sako su gaishe da metron maryam sannan ta tafi,ta cikin lunguna ta kurkurda ta fito gate,tana fitowa taci sa`a ta sami A dai- daita sahu babu kowa a ciki,don haka tayi wuf ta shigo batare da ta fada masa inda zai kai ta ba balle suyi cinikin kudin da zai karba,tana shiga ta zauna tana daga kanta, sukayi ido hudu da dr shuraim cikin tsaleliyar motarsa discussion continues,shi ma kallonta yake yi alokacin da yake kokarin tsallakawa titi,ta sunkuyar da kanta da sauri,yayin da shikuma ya tsaya cak yana kallonta,daga dukkan alamu yana mamaki da ya ganta yanxu,mai adaidaita sahu yaja ya tafi yayin da aisha farida ta rike kai,saboda nauyin da taji kan yanayi mata sai da mai adaidaita sahu yayi da gaske sannan ta bashi amsa, ta fada masa inda zai kaita tana shiga gida sallan azahar kawai tayi ta shiga lungun ta kwanta ba tare da ta san a duniyar da take ba,taji dadi da ganin yara a zaune a dakin uwani,sunci abinci suna hutawa,don haka tace suyi zamansu a nan zatayi aiki idan lokacin makarantar islamiyya yayi su tafi,saboda kawai bata son damu da magana cikin wanan hali da ta riski kanta Allah sarki soyayya ruwan zuma tayini tana duban numbr dr shuraim,sai taga kamar shi take gani,koda yaushe kunnenta da idanuwanta ta suna yi mata

Chapter 15 of 23