Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Sunana Aisha farida umar, 'yar asalin jihar katsina amma zama ya kai kakannina garin shagamu. Anan aka haifi mahaifi har yayi aure aurensa ya hayayyafa don haka babu garin da muka fi sani wanda ya wuce shagamu. Mahaifiyata ma 'yar garin shagamu ce. Yanzu shekaruna ashirin da uku a duniya, na fito daga dangi wadanda suke talakawa liki. Ilahirin dangina kakaf na wajen uwa dana wajen uba basu da hali. Koda yake akwai daidaiku masu rufin asiri amma ba za a kira su masu arziki ba amma dai sunfi wasu. Wannan dalili yasa bamu cika karatu mai zurfi ba wasu daga primary suke tsayawa, wasu sun shiga scondary amma talauci sai yasa a cire su basa karasawa. Masu dan gara gara ne ma suke kammala secondary amma fa jami'a ta gagaresu sai dai kallo. Danginmu suna da dimbin yawa mata da maza, yara da manya gamu da tsofaffi tukuf tukuf Allah Ya ara musu tsawon rai. Mahaifina yana daya daga cikin dattijan domin ya tsufa jagof, tun tashi na daman a tsohonsa na ganshi har ya makance saboda tsufa. Shine babba a cikin 'yan gidansu don haka yafi kannensa tsufa kuma yafi sauran 'yan uwansa talauci kasancewar yafi su tara mata har guda hudu da tulin 'ya'ya har guda arba'in da uku. Nice 'ya ta arba'in da biyu a wajensa, kanwata guda daya kacal mai suna munauwara. Mu biyu ne kadai muke uwa daya uba daya a gidan domin mahifiyarmu ce amaryarsa, ya aure ta tana kankanuwa yayin da yake tsohonsa. Sauran matansa ma duka sun tsufa wasu daga cikin manyan 'ya'yansa sun girme ta suma har sun aurar da 'ya'yansu suna da jikoki wadanda suka fini ma. Don haka ban mori dadin uba ba, sanda na fara wayo baya ganina kasancewar ya makance. Aikina shine kullum inzo dakinsa in riko hannunsa in fito dashi kofar gida sai in zaunar dashi akan kujerar katakonsa sannan ni kuma in zauna a gefensa ina sauraron hirar da sukeyi shida abokansa, makwabtansa da 'yanuwansa tsofaffi. Ina jin dadin sauraron tsofaffi labarai masu al'ajabi na mutanen da. Ina fahimta sosai kuma ina rikewa a kwakwalwata tas, babu abinda nake mantawa harma idan suka fadi wata kalma da ban sani ba sai in tambayesu su bani amsa. Idan babana ya aike ni dauko ruwa, fura ,koko ko kuma kurtun tofin yawunsa a dakinsa sai inji duk raina ya baci saboda za'a tsallake wani shashi daga cikin hirar. Sai in zura da gudu don inyi sauri in dawo kada a wuceni, idan na dawo kuwa na sa su dole su dawo da labarin baya. Anan na koyi iya magana mai ma'ana da jan hankalin mai saurarona da kuma fitar da lafazai masu girma da hikima tamkar wata babba. Daga nan na samo suna "Farida tsiri" inji kawayena haka suke kira na domin duk wanda na zauna dashi zaiyi tunanin wayona yayi yawa zan cuce sho ko zanyi masa dubara ko in yaudare shi. Duk sanda zanji labarin anyi gulmata bai wuce ace na cika iyayi ba da dadin zance rai-rai-rai kamar aku. Ko kuma ace na cika kissa da kisisina bana fushi ko ma za'ayi min, ga tsiri ina magana kamar wata tsohuwa wacce taga jiya taga yau. Ina jin dadin halayena kuma dashi nake cin ribar zaman duniya. Zan iya zama da kowanne irin mutum ne komai bakin halinsa da muguwar zuciyarsa, duk sharrinsa ko alkhairinsa haka kuma duk in da ya kai ga masifa da zafin rai zamu zauna lafiya. Da kowacce irin kabira zan iya zama lafiya. Da bakar fata da inyamuri, hausa, babarbare, bafillatani, bayarabe, ibira ne, tangale ne, mumuye ne, margi ne, basayi ne, ba'are ne, dan niger ne ko kuwa adon dawo ne dan bur sudan duk na san yadda zan tafiyar dasu. Mahaifina yana da yawan magana ba zai iya zama shi kadai ba, ba tare da bakinsa yana motsi ba, sai na gado sho don haka tamu tazo daya sai mu hadu muyi tayi. Har baya so in matsa daga gabansa don haka ban cika zuwa makaranta ba, ko yayyena zasu korani sai in ruga da gudu dakinsa in labe a bayansa. Sai yace musu "inga mara kunyar da zai shigo ya banbare aisha daga bayan, baza taje makarantar ba nan dakin ma makaranta ce". Aji ne mai zaman kansa don darasi take duka na iya rayuwar zaman duniya. Ku fada min ko a jami'a wanne darasi ne za'a zaunar da dalibi a karanto masa rayuwa karara balle dan primary aji daya? To ku kyale ta ba in da zata je sai ta ga dama sannan zata je makarantar. Dalilin zuwanta makaranta don ta koyi rubutu ne kawai. Idan sukaji yana fada basa karasowa cikin dakin, su gama labe-labensu ina hango inuwarsu ta jikin asabari sai inki fita, sai sun gaji da jirana sannan su tafi. Idan hantsi yayi sai inje zaure in kinkimo kujerar katako in kai masa kofar gida, sannan in share wajen in shimfida tabarmi a kasa wasu tabarmin in shimfida akan wasu dakali biyu da suke kofar gida. Sannan in dawo dakinsa in mika masa sandarsa na riko hannunsa in fito dashi kofar gida wajen kujerarsa, sai ya laluba ya zauna sannan in koma gefensa in zauna sai ya fara bani labari ko tatsuniyoyi. Sannu a hankali sai 'yan majalisarsa su fara bulbulowa daga gabas wasu daga yamma wasu daga barin kudu, wasu daga arewa. Yawancinsu kannensa ne uwa daya uba daya, ko uba daya. Wasu kuma kakanni suka hada, wasu makwabtaka ce ta hada ko auratayya, wasu kuwa manyan abokansa ne da akayi kuruciya tare. Babu wanda yake da kasa da shekaru sittin a wajen. Anan na samu tarbiyar girmama babba duk kankantarsa, domin idan na gaishe su daga tsaye ko daga zaune ba zaus amsa ba ko kuma inji duka dal a bayana wai nayi rashin da'a. Sai kaji sun daka mintsawa suce inzo in durkusa har kasa sannan in gaishe su. Tun ina jin haushin inyi kuka har na daina, tun ina mantawa har na saba. Sannan na koyi durkusawa har kasa idan zan mikawa babba abu koda kuwa da kadan ya girme ni kuma da hannu biyu. Sun hana ni mikawa sa'ana ko yaron dana girma abu a wulakance ko da hannun hagu. Sun gargadeni ni da na guji wulakanta dan adam ko da kuwa almajiri ne domin babu kyau wulakanci da girman kai. Anan nakoyi daubarun cin jarabawa a makarantar boko ko kuma saurin haddace kur'ani a makarantar allao. Sunce in zamana mai yawan kallon bakin malamina ina sauraro, ina ganin yadda yake fitar da lafazinsa daga hanka, ganda, tantanin makwallato da kuma dumbarun bakinsa. Yin haka zai sa in dinga fitar da kalma yadda ake bukata a fada. Kada in dinga zama a bayan aji, ko da yaushe kujerata ta zamana a gaban malam saboda gudun yin wasa da yara. In zama mai yawan tambayar duk abin da ban gane ba anan take ba sai an wuce wajen ba. Sannan in dinga kwafar rubutu daidai in da ban gane ba ko ban gani ba in tambayi malam ko wani na kusa dani wanda nasan yasan abin da yake yi. Kada in sake in koma gida in yarda jakata ko allona ba tare da nayi bita ba. Sunce da zarar naci abinci na huta in samu lungu in shiga inyi ta tilawa zanji na fahimci abin da ban gane ba a a aji watakila saboda yunwa ko gajiya ta hana in gane a lokacin. Suka shawarce in yawaita yin aikin gidan (homework) tare da yayyena wadanda suke ajin gaba dani, kada in sake in dinga yi ni kadai ba tare da wani ya duba min ba. Duk abinn nan dana fada min na haddace sai dai anan nake zubarwa saboda bana kaunar zuwa makaranta, har gara ma makarantar allo dan itama a kofar gidanmu take dole inje. Idan rana ta bude sai majalisa ta yoye, ni kuma sai kama hannun tsohona in shiga dashi daki sannan inje in karbo masa abincin rana daga wajen matar da take da girki. Tuwo ne dai na masara ko na dawa, miyar kuka ce ko danyen karkashi. Shinkafa sai jifa jifa ake siyowa a dafa ko kuma idan an samu wani dan albarka cikin yayyena ko sirkiai su kawo mana a dafe ko danye. Da yamma sai in sake zuwa inyi shimfida in fito dashi, 'yan majalisarmu basa tashi basa manta lokacin sai kagansu daya bayan daya suna bulbulowa. Duk wannan zance da nake yi muku ina da shekara hudu ne zuwa tara, ban cika shekara goma ba a duniya Allah Ya karbi ran mahaifina. Mahaifina ya rasu a ranar wata juma'a da safe. Bazan taba manta wannan ranar ba saboda itace ranar dana taba makara ban tashi da karfe bakwai na safe banje wajensa ba, domin kullum karfe bakwai a dakinsa take min. Wannan kuwa ya faru ne a sanadiyar wata kasala da wani yanayi da jikina yake min ba dadi. Ni ba mai barci ba, haka ni ba ido biyu ba. Tamkar wani abu mai nauyi aka saka aka dirirritseni na kasa juyi. Sai dai kuma idona a rufe ba kamar mai tunani kamar mai mafarki domin abinda nake nanatwa hirar da mukayi da mahaifina ce a daren jiya kafin inzo in kwanta. Daga ni sai shi bayan 'yan majalissa sun watse muna labari kamar yadda muka saba. Ya laluba ya dafa kaina yace aisha ki zama mai rikon amana a rayuwarki yin haka zai ja miki farin jini a wajen al'umma. Ki kiyayi munafunci, ma'ana gulma shine yi da mutum yin haka zai zubar miki da kima. Ki guji sata duk rintsi kada ki taba abin wani yin haka zai zubar miki da mutunci ke da zuri'arki gaba daya za'a dinga yi muku gori. Ki guji yin zina, laifi ne a wajen Allah kuma rashin mutunci zai dasu a idon jama'a zaki zama abar zagi, kowa ya fada miki magana, sai ki zama ballagaza ko yaro karami ba zai girmamaki ba. Ki kiyayi kwadayin abin wani, ki nema naki na kanki duk kankantarsa ki hakura kiyi amfani dashi shine zaman lafiyarki da farin cikin rayuwarki. Kada ki raina baiwar da Allah ya baki, kada ki dinga ganini wadanda suka fiki. Kada zuciyarki ta mutu kice ba zaki shiga ku fafata ba, ki zama mai karfin zuciya da kudiri na alkhairi kada zuciyarki ta dinga karaya. Sannan ki zama mai godiya ga Allah a duk halin da kika tsinci kanki na dadi ko wuya. Ki zama mai yawan kyauta ko abinda kika mallaka kalilan ne kada ki makale hannu kice baki dashi, sai ranar da kika samu da yawa zaki dinga bayarwa. Ki nemi ilimi mai yawa, na muhammadiyya dana zamani komai wuya domin kada a barki a baya a rayuwar duniya da lahira. Allah Yace mu nemi ilimi a duk inda yake domin sai munsan shi zamu bauta masa. Allah baya karbar ibadar jahili, har baccin mai ilimai yafi jahilin da zai kwana yana sallah. Sai naji mahaifiyata tana girgiza ni tana ta ambaton sunana, idan na bude ido na dube ta sai in koma in kwanta har sai da ta daga ni zaune. Tace dani wanne irin bacci ne haka har tara da rabi tayi baki je kin kaiwa babnki koko ba, bayan kinsan baya jin dadin jikinsa? Cikin magagin bacci nace mata yau baba ya fita kofar gida da kansa, yayi shara yayi shimfida da kansa. Sai ta harareni tace karyar banza, a mafarki ko a ido biyu? Yaushe kika ganshi ke da na tashe ki dakyar? Sai na tuna ashe mafarki ne don haka na mike a firgice ko sallah banyi ba na fita kofar gida na hau shara, na fitar da kujerarsa da tabarmi kamar kullum. Sannan nazo na dauki koko a kwanon sha da kudaya na duma na nufi dakin tsohona. Wata irin al'ada ce matan gidanmu sukeyi wai mata mai girki bata shiga dakin miji saboda kada ayi gulmarta ace ta cika jaraba, tsohon Allah sai anje an nanike maka, makahon da yake ta kansa yau da lafiya gobe babu. Kina shiga dakinsa za'a fara lekowa ta lungu lungu ana kus kus, kina fitowa kuwa zaki hadu da harara , zumde, yafice da habaice habaice. Tsakanin shi dasu gaisuwa daga bakin kofa ya fadi abinda zai fada ki juya idan kin zuba masa abincin ki aiki 'ya'yanki ko jikokinki su mika masa. Daga baya ma da aka ga nice karama mai shiga wajensa kullum sai aka dora min alhakin kai masa abinci kullum, duk wacce ta gama sai ta kwalla min kira inzo in kai masa abinci. Na shiga dakinsa sai na iske shi a lullube kamar mai bacci, sai na zata lambo yayi ko fushi yake yi dani dan banzo da wuri ba. Nayi ta sallama shiru, sai nazo dai dai kunnensa na durkusa na gaishe shi bai amsa ba, sai na shiga yi masa bayanin abinda ya tsayar dani, shimfida nayi har su malam shehu sun fara zuwa. Sai naji yayi shiru bai motsa ba, sai kawai na bude lullubin sai ga idanuwansa a kakkafe yana kallon sama kamar mai murmushi. Nace lallai baba kana jina ashe kayi kasake kana kallon sama kana murmushi. Sai bai bani amsa ba! Ni kuma sai naji raina ya baci, sai nayi fushi na tashi na fita bakin kofar dakin na zauna ina kumbure kumbure. Matan gidan suka fara yimin tsiya suna cewa ke kuma me akayi miki? Ke da baban naki ne kuma yau ake jin kanku "yar lelensa wacce baya bari a taba ki. Sai nace dasu yana ji ina tayi masa magana yaki kulani, idonsa biyu yaki yi min magana idanuwansa suna kalllon sama kamar yana murmushi. Sai jikinsu ya fara basu tabbas akwai wata matsala domin suma sun leka suna gaishe shi bai amsa ba duk da dai anji motsin alwalarsa da asuba amma baya baccin safe. Sai matansa suka kutsa cikin dakin da sauri kuma a gigice. Kururuwa da lafazansu ne ya gigita ni, har yau ban kara jin mummunar kalma a kunnena irin ta ranar ba. Suka ce wayyo malam babu, malam ya mutu, munga ta kanmu, ihu mun shiga uku, rumfa ta gaji da shirgin kaya ta rushe. Ire iren kalaman da suke fada kenan suna rusa kuka kururuwa. Sai naji zuciyata ta hau dukan uku, na dafe kirjina na fada a bayyane nace Innalillahi wainnailaihi rajiun. Allah Ya jikanka baba, Allah ya sa aljannah ce makomar ka. Allah da Ya karbi abunSa dan yafi mu sonsa, daga gareka muka zo kuma gare Shi zamu koma. Da ka tafi ba kayi gaggawa ba haka mu da muka rage ba muyi nawa ba. Sai manyan maza da mata suka jeru a kaina suna kallona babu wanda ya kara magana balle ihu. Mamaki marar iyaka zaka dinga hangowa daga cikin idanuwansu. Ina salati ina hawaye cikin natsuwa ba tare da kwarmato ba. Sai yaya hussaini ya fashe da kuka yace farida lallai baba ya shigar dake makaranta, ya saka ki a aji ya koyar dake darussan dako a jami'a ba za koya miki ba. Baba yayi gaskiya da yake hana ki tafiya daga wajensa har sai da kika koya ilimi wanda zai isheki zaman duniya da lahira. Ya juya ya duba iyayensa da 'yan uwansa yace wannan abinda farida ta fada ya zama darasi a wajenku, wa'azi ne, nasiha ce zuwa gare mu. Ihu da kwarmato da dora hannu aka kuna fadin mun shiga uku, ina zamu saka kanmu? Gatanmu ya fadi. Dawa zamu zauna a duniya? Rumfa ta gaji da shigi ta rushe. Dukka sabo ne, bata ne, jahilci ne, azaba kuke karawa mamaci. Tabbas idan ka saba da abu ranar da zaka rabu dashi akwai ciwo, kuka wajibi idan akayi mutuwa amma ba'a son ihu da kururuwa. Kamata yayi ayai ta karanta innalillahi wainna ilaihi rajiun sannan ayiwa mamaci fatan samun aljannan. Ku dubi karamar yarinya nan farida itace kusan wacce tafi kowa kankanta a cikin gidan nan amma ita kadai ce tayi abinda ya dace , itace wacce tafi mu shakuwa dashi, tafi mu sonsa, kuma itace tafi mu nuna masa kaunar da take yi masa shine data yi masa addua. Muyi koyi da ita don tafi mu ilimi, tafi mu sanin ya kamata. Sai suka daina ihu suka koma suna ambaton sunan Allah. Yaya hussaini ya tashe ni tsaye yasa gefen rigarsa ya goge min hawaye. Yace ki daina kuka 'yar karamar kanwata, kowa yasan ke aka yiwa mutuwar nan sai kuma kika fi kowa yin tawakkali haka Allah yake so. Ina mai yi miki albishir Allah ba zai bari ki wahala ba, da izininsa ba zakiyi kaskantaccen maraici a rayuwarki ba, duk da kin rasa mahaifinki a lokacin da kike da karancin shekaru saboda baki mance da Ubangijinki ba wanda shine gatan ki. Allah Yana tare da duk wanda yasan da Shi kuma wanda yake neman taimakonsa. Farida nayi miki alkawari zan dauki nauyinki, zan rike ki amana har izuwa ranar da zan aurar dake saboda wannan tawakkalin da kika nuna, zan rike ki tamkar 'yar dana haifa ta cikin. Wacce hakkin cinta, shanta, suturarta, tarbiyyarta, iliminta da suka wajaba a kaina har zuwa ranar da zan aurar da ita sannan nauyinta ta koma hannun mijinta. Ki shiga ciki wajen baba kiyi masa sallama, kiyi masa irin adduar da kika yi masa yanzu ta neman gafara da rahamar Ubangiji. Mutuwa ce kadai ta raba kaunar dake tsakaninku. Na juya da sauri na shiga wajen tsohona, durkusa a gabansa setin kunnensa na tofa masa kulhuwallahu ahad uku, sannan nayi masa adduar samun aljanna da neman hasken kabari. Nayi masa fatan Allah ya sa ya tashi a cikin gafartattun bayi a cikin alummar manzon Allah (SAW). Sannan mahifiyata ta jawo hannuna muka fito waje, cikin kuka mai tsanani tace dani farida na yafe miki duk abin da kika yi min. Allah yayi miki albarka a rayuwarki ta duniya da lahira. Alhamdulillahi nayi dace da 'ya ta gari, mai jin kan iyayenta. Ina fatan nima zakiyi min irin wannan adduar idan na riga ki tafiya. Muna zazzaune a tsakar gida maza suka shiga sukayi masa wanka, suka hada shi suka fita da shi akayi masa sallah. Aka dauke shi aka tafi dashi gidansa na karshe, gidan da ba'a fitowa unguwa, gidan da ba'a leke, gidan da ba'a jiyo motsinka balle a gaishe ka ka amsa wato kabarinsa. Bakina bai gushe da karanta masa kulhuwallahu ba da inna a'adaina kalkausar har karshe. Shi ya bani adduar yace ita ake so a dinga karantawa mamaci. Da akayi sadakar bakwai sannan aka watse, lokacin mutuwa ta dawo min sabuwa fil, idan aka tashe mu daga bacci za'a tura mu tafi makarnatar boko sai in nufi dakinsa zan buya sai in ga a rufe sannan in tuna ashe ya rasu, dole a tura keyata zuwa makaranta raina baya so, da yamma ma sai a tura ni makarantar allo. Ina tuna nasihohin da tsohona da abokansa sukayi min na dabarun samun nasarar karatu, sai nake bin duk yadda suka umurce ni sai naga ina ganewa kuma ina cin jarabawa don haka saina fara jin dadin makarantun da nake zuwa, na dawo ina zuwa makaranta da kaina ba sai an tura ni dole ba. Ranar asabar da lahadi muna zuwa makarantar allo da safe da yamma amma ranar alhamis da juma"a da yamma ba ma zuwa koina don babu makarantar allo, sai na fitar da kujeran babana in shimfida tabarmi kamar yadda na saba. Sai inga tsofaffin nan suna zuwa daya bayan daya suna zuwa suka taru kamar yadda suka saba da, don har sun daina taruwa tun bayan da ya mutu. Baba ahmadu ne ya maye kujerar babana shine babba ina gefensa koda yaushe, duk sanda suka kalle ni sai inga suna hawaye suna tausayina da alama suna tunawa da yayansu, abokinsu, amininsu, makwabcinsu, abin kaunarsu. Zaman majalisar yakoma ranar alhamis da juma'a ne kawai da yamma. Kuma munci gaba da hirarrakin mu kamar yadda muka saba. Bayan rasuwar mahaifinmu da shekara guda yaya hussaini yayi aure, ya auri 'yar kanin babanmu mai suna abida dai dai lokacin daya sami dan karamin aiki a union bank, da certificate dinsa na secondary a matsayin masinja a branch na kano dan haka kano ya kauro damu. Da zamu tafi mahifiyata ta hada min kayana kakaf tana kuka ina kuka, kanwata munauwara ma tana kuka, 'yan gidan kacokan suka fito suna mana fatan Allah Ya kiyaye hanya da fatan Allah Ya bamu zaman lafiya, Ya hada mu da abokan arziki a can. Muka tare masu babura biyu muka hau da jakunkunan kayanmu muka nufi tasha, muka hau doguwar mota mai zuwa kano. Kano ta dabo tumbin giwa, mai mata da motoci ko da me kazo an fika. Rabona da shagamu kenan har yau ban sake komawa da sunan zama ba sai dai inje da sunan ziyara. A wata unguwa a cikin kano mai suna sharifai zauran tudu, yaya hussaini daman ya kama mana haya tun kafin muzo, a gida mai dakuna bakwai muka kama dakuna biyu. Don haka mutane ne da yawa a cikin gidan, bandakin daya ne kacal, kicin daya da tsakar gida daya ake amfani dasu mata da maza, yara da manya. Abunka da gidan yawa, kazanta ba'a magana. Gashi daman gidan ya tsufa ya farfashe ba gyara sai warin bola da kwata kowa kyashi ya hana shi gyarawa. Idan ka share cikin dakinka da kofar dakinka ka gama shara babu wanda zai share tsakar gidan da zaure balle kofar gidan. Ga gida a lungu ko mota bata shiga lokon, ga wata tafkekikyar kwalbati da ta cinye fadin lungun, kowa a tattakure babu sakewa, yara basa iya wasan guje guje su more sboda matsi. Haka kowacce mace ta baza kayan san'arta a cikin gida, cikin zaure ko kofar gida saboda sai an taimakawa mazan rayuwar zata tafi dai dai. Daman mazan da yawansu buga buga sukeyi, wani sai ya dawo gida babu abinda ya samo, da dan kudin sana'ar natar za'a yi cefane kuma ta bawa yaranta kudin makaranta. A gidan ma har gara yaya hussaini tunda yana daukar albashi duk tsiya dai karshen wata zai samu duk da dai dan albashin bashi da yawa kuma rabin kudin a acaba yake tafiya, kafin wata ya kare sai anci bashi dole kafin a biya an jigata. Duk da haka dai munfi sauran, muna dan cancanawa dai muna rayuwa. Ni da abida muka fara sana'a, muna soya wainar fulawa a kofar dakinmu, kuma ana saya ba laifi duk da cinikin naira biyar biyar ne, duk da haka muna samun na sayan maggi, gishiri, a ciki ake bani kudin makaranta da kudin dinkin tsummokaran mu idan sun yayyage. A makarantar bokon cikin unguwa aka saka ni, kamar sauran yaran unguwar haka aka saka ni a makarantar allo da yamma ta islamiya da daddare. Bana fashin zuwa makarantar kullum saboda ina tsoron yaya hussaini sosai, baya yi min wasa koda yake matarsa ma baya sakar mata fuska , mutum ne mai zafin zuciya. Lallaba shi muke kamar kwai. A daki daya nake zaune babu komai a ciki daga 'yar karamar katifa sai 'yar jakar kayana ta buhu a gefe ko ledar daki ba'a shimfida ba sai tsurar ragargajejjen siminti da wani yagulallan labule. Dakin su abida da mijinta ne mai labule mai kauri, an shimfida leda a kasan da katuwar katifa sai akwatin kayansu a gefe. Kayan kitchen da danyan abinci suna dakina wasu a dakinsu. Haka muke rayuwa amma muna farin ciki saboda mun sami ci gaba fiye da a garinmu tunda daman can a cikin talauci aka haife mu. Bayan kaurowar mu da shekara daya mahaifiyata ta tara kudin motarta da guzurinta tazo ganina sabida tun kaurowarmu bamu je shagamu ba, saboda matsalar tattalin arziki sai ita tazo dan taga yadda muke rayuwa don koda yaushe magana ta takeyi don tana sona sosai har fiye da 'yar autarta. Nayi murna matuka da ganinta har ita ta fini murna, yaya hussaini da matarsa ma sunyi murna da ganinta kuma sunji dadin tsarabar da ta kawo mana. Ni da abida atamfa dai dai ta kawo mana, yaya hussaini ta kawo masa yadi, sannan ta kawo mana doya, dankali, ayaba da lemo jifgi guda. Allah cikin ikonsa cikin daren data zo muna kwance da ita a dakina ciwon ciki ya turnuke ta kafin in bugawa yaya kofa ya fito don a kai ta asibiti rai yayi halinsa. Ummata ta mutu a gabana ina kallonta ban isa in hana ta tafiya ba, Ubangiji ya nemi kayanSa. Sai na tuna wasiyyat da ta bar

Chapter 1 of 23