Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
d'akin ne, ta fahimci cewa akwai abinda yake damun Fadwa. "Fadwa? " Juyowa tayi ta kalleta ' cike da sosa idanun ta. "Na'am Ilham." "Kamar kinyi kuka ' Fadwa, da abinda ke damun kine?" Nan ta matso murmushin k'arfin hali. "Laa! Wane irin kuka kuma? A'a babu abinda ke damuna, kawai kwaro ne ya shigar mun ido." Ok kawai Ilham tace ' sannan ta d'auki towel ta d'aura a jikin ta, ta shiga wanka. Ilham komawa tayi a kwanta ' abunda Yaya Khaleel, yayi mata ne ' yaketa fad'o mata a rai. *Around 8:00pm* Bayan Ilham tayi wanka ' harta gama shiryawa, cikin Riga da skirt ' atamfa, sannan ta zauna a gaban mirrow ' ta fara cab'a ado. Fadwa wacce ke kwance ' a saman gado ne tace, "Waike, wannan wace irin make-up kikeyi haka?" Ilham tsayawa tayi cak ' tana kallon ta cikin mirrow, "Ha'a to ina ruwanki? Nifa banason sa ido ' in kinji haushi kema kiyiwa Yaya Khaleel." Tsaki taja ' tare da saukowa daga saman gadon, cikin b'acin rai. "Ke dai kika sani!!" Ta fad'a gami da ficewa daga d'akin, ta nufi parlor kai tsaye. zaman ta keda wuya ' Yaya Farook ya dawo, sallama yayi ta amsa ' tukunna ya sami waje ya zauna. "ke kad'ai ce a parlon, ina Ilham tace?" "Ilham, tana d'aki." Ta fad'a ba tare da ta kalleshi ba. Yaya Farook ' zaiyi magana kenan yaji sallamar Abba, a cikin parlon ' cikin hanzari ta tashi, ta tunkari Abba. "Abba, sannu da dawowa." Fadwa ta fad'a gami da karb'ar jakkar shi , sannan ta kai mashi sashen d'in shi. Bayan ya zauna ne ' Yaya Farook yayi ma Abba sannu da isowa, tukunna ya koma k'asa ya zauna. "Ina Umman taku take?" Cewar Abba, "Nima shigowa ta ' kenan Abba, amma ina tunanin tana d'akin ta." "Alright! Naga sak'on ka ta Email d'ina, game da transfer d'inda akayi maka ' hope dai ka gama shiryawa?" Hakan yayi dai dai ' da dawo war Fadwa cikin parlon. "Eh Abba , na kammala shirina ' nan da next week Insha Allah flight d'ina zai tashi." Raras Fadwa taji ' gaban ta ya fad'i , a hakanli take saukowa ' daga saman steps tare da cewa, "Abba, nakai jakkar d'aki." Muryar ta na rawa ta fad'i haka, jin haka yasa Yaya Farook juyowa ' ya kalleta a tsorace. Ganin ta nufi b'angaren su ne ' yasa shi mik'ewa tsaye tare da cewa, "Abba , ina zuwa." Uhm-hum, kawai Abba ya ce ' sannan Yaya Farook yabi bayan Fadwa cikin sauri, hartasa hannu zata bud'e k'ofar d'akin su yayi saurin tsayar da ita. "Fadwa, Please.." A fusace ta juyo ' ta kalle shi, idon ta cike da hawaye. "Bana son ji! Yaya Farook, babu abinda zaka fad'amin, kamin k'arya kuma ka b'oyemin, and Insha Allah ' na hak'ura dakai for good, and if am where you ' zan had'a kaya na ne gobe gobe intaf...." Bata kaiga k'arasawa ba ' ya falla mata mari, jikake tasss ' nan take ta zuk'unna gami sakin k'ara. "Ahhhhgggh," "Fadwa, kinsan me kike fad'i kuwa? Kinsan wanene a gabanki kuwa?" Cikin kuka ta mik'e tsaye ' tare da cewa, "Kwarai kuwa, nasani ' kuma nagode!!!" Tana fad'in haka ta bud'e k'ofar d'akinsu ta shige, nan sukayi kicib'us da Ilham ' tana k'ok'arin fitowa. "Ke! Fadwa, harya iso." Fadwa banza tayi ' ta kyaleta tashige d'aki, Ilham lura tayi da Yaya Farook a bakin k'ofar ' ranshi a bace , a zuciyar ta tace. "Topha! Ashe takuce ' ta had'o ku!!" Saida ta tsaya ' ya wuce tukunna, itama ta wuce parlor ' gudun karya huce kanta. Ilham wacce ta fita ' ta shigo da bak'on ta mai suna Al'ameen, cike da fara'a ta zarce dashi ' parlon da bak'i ke zama. Bayan sun gaisa ne ' ya yaba da irin Kwalliyar da taimashi, "My baby, gaskiya kinyi kyau ' nawa za'a siyarmun da wannan kwalliyar?" Murmushi tayi ' sannan ta tashi, tare da cewa. "uhm ' bara in kawo maka ruwa!," Tana fad'in haka ta wuce ciki ' ta nufi kitchen kai tsaye, ta had'o mashi drinks da abubuwan da ta shirya mashi. Ilham, dawo wa tayi ' ta aje mashi a gaban shi, sannan ta bud'e drinks d'in ta zuba mashi a cup ' ta mik'a mashi cike da ladabi, ta koma ta zauna. Al'ameen, sau d'aya yasha ' sannan ya aje a k'asa, "My baby na gode ' da tarba mai kyau, But nace nawa ' zanbiya kwalliyar nan?" "Sweetheart, ai bazaka iya biya ba ' so kawai kabarshi." Nan suka cigaba da hirarsu ' ta soyayya, Fadwa kuwa na kwance a d'aki tana danna wayarta, taga an bud'o k'ofa ' ga dubanta saitaga Umma ce , "Fadwa! " "Na'am Umma?" Umma k'arasawa ciki tayi ' ta zauna a bakin gado, itama Fadwa ta ' tashi ta zauna. "Ki tashi ' kije Abban ku nason magana daku," To kawai Fadwa ' ta cewa Umma, sannan ta sauko daga kan gadon ' da niyyar fita, "Ina Ilham take?" Cewar Umma, "Amm, Umma ' tayi bak'one, suna k'aramin parlor." To Umma tace ' sannan Fadwa ta fita zuwa parlor, ita kuma Umma ' zarcewa tayi d'akin Yaya Khaleel ' da Yaya Farook. Bayan Fadwa ' ta isa harabar parlon ne, ta iske Abba a zaune d'auke da laptop a saman cinyar shi ' sai da ta gaishe shi tukunna, ta sami waje a k'asa ta zauna. "Fadwa, ke kad'ai ce ' ina sauran suke?" "Umma taje kiran su ne ' but ita Ilham, tana da b'ako ne shiyasa." Ok kawai Abba ya fad'a, sannan ya maida kanshi ' ga laptop. Ana a hakan ne ' Umma ta shigo cikin parlon ' su Yaya Farook ' da Yaya Khaleel, suna biye da ita. Umma zama tayi ' gefen Abba, tukunna suma suka zazzauna a k'asa cike da ladabi, Abbane ya ajiye ' laptop d'in nashi, saman hannun kujera ' sannan yayi gyarar murya. "uhm Uhm! Ammm... dalilin ' taraku anan wajen shine, Magana ce akanka ' kai Khaleeel." Nan Yaya Khaleel ' yaji rasras a zuciyar shi. Sannan Abba ya cigaba da cewa, "Tabbas ' duk naji abubuwan da kakeyi, a cikin gidan nan ' da kuma waje, da irin wulak'ancin da kake nunawa ' ita wannan yarinyar Fadwa, to inaso ka bud'e kunnuwanka sosai ' ka saurare ni, Fadwa ce ' zab'in mu a cikin gidan nan ba wataba ' kuma Aure tamkar an d'aurashi ne ' harkai ka isa kayi jayayya ' da zab'in mu?" Cikin tashin ' hankali Yaya Khaleel ke girgiza kai. "Kuma bari ' kaji in gaya maka, wani abinda baka sani ba ' aure kamar anyishi angama ne, domin nida Umman ku ' mun yanke shawaran Next week za'ayi auren ku, in Allah ya yarda." Maganar ce, taiwa Fadwa tsawa a kai ' da k'arfi ta d'ago kai ta kalli Abba, sannan ta maida kallon ta ' akan Yaya Khaleel, wanda shima ita yake kallo ' ranshi a b'ace, tukunna ta maida kallon ta ' zuwa k'asa.. "To amma Abba, bikin nan fa kamar yayi kusa ' da yawa...." Bai kaiga ' gama rufe baki ba, Umma ta daka mashi tsawa ' da cewa, "Rufe mana baki, ja'iri kawai ' wato kai har wuyarka tayi kwarin da zaka iya ' fad'a in fad'a da Abban naku? Lallai bakada kunya Khaleel." "Umma, don Allah kuyi hak'uri." Abinda ya iya fad'i kenan, sannan ya sunkuyar da kanshi k'asa. Fadwa kuwa ' mamakin kanta ' ta rik'ayi ganin yadda idonta ' ya k'enk'eshe sam babu hawaye a cikin sa. Shi kuwa Yaya Farook ' komai baice ba game da maganar, sannan Abba ya ce. "Ku tashi ' ku tafi." Fadwa yunk'urawa tayi zata wuce, Abba ya tsaida ita. "idan Ilham ta gama ' ki sanar da ita, ina neman ta." To kawai ta ce ' sannan ta wuce d'akin su, ta haye gado ' a cigaba da danna wayarta. *Dedicated To My Fan's* 馃憚馃憚馃憚馃槣 [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 www.Seemaluv.wapka.me *43-44* Yaya Farook kuwa ' yana shiga d'akin shi, ya hau shirya kayan shi ' cikin trolley, daga bisani ya tsaya ' don kuwa yarasa meyasa yake sanya kayan shi aciki. Komawa yayi ' ya zauna tare da goge zufar goshin shi, sannan ya tashi ' ya shiga bathroom yayo alwala, yayi sallah raka'a biyu(Nafila) ' gami da rokon Allah yazab'a mashi mafi alkairi. B'angaren Yaya Khaleel kuwa, gaba d'aya ranshi ya riga ' ya gama b'aci. Nan ya d'auki wayar shi ' da take kan mirrow d'in d'akin, cikin sauri yayi dailing number d'in Lubna, harta shiga ' yayi saurin yanke call d'in gami da dafe kanshi, "Oh my God, what the hell ' is wrong with me!, meyasa su Abba zasuyi min haka? Yes inason Fadwa ' but is just that ita ba ajita bace, and besides she's not my choice." Ita kuwa Lubna ' cike take da mamaki, yadda taga flashing d'in Yaya Khaleel a cikin wayar ta ' girgiza kai kawai tayi, sannan tayi dailing number d'in shi itama. Yaya Khaleel ' yana cikin wannan tunanin ne, yaga shigowar kiran Lubna ' cikin hanzari yayi recieving. "My love!" "Yes baby ' ya kike?" "Lafiya kalau my love!' I was surprised dana ga missed call d'inka." Nan ya tuna cewa ' eh tabbas yayi dailing numbar ta, "Oh yes baby, it was a mistake ' bansan na kiraki ba ma. " Yana yin ' yadda yake magana ne, ta fahimci cewa ' akwai abinda yake damun shi. "but my love ' is everything alright? " "Of cause, baby zamuyi magana ' anjima Okay?" Bai jira ' yaji abinda zata fad'a ba ' ya kashe wayar, sannan ya koma ya zauna a Sofa. Yaya Khaleel ' cike yake da tunani iri ' iri, a cikin zuciyar shi ' jinginar da kanshi yayi a jikin kujera, zuciyarsa na maimaita mashi ' maganar da Abba yayi. "Subhanallah!" Abinda ya iya furtawa kenan ' ya tashi ya shiga bathroom, domin watsa ruwa. Ita kuwa Fadwa ' pictures taketa kallo cikin wayarta, don kuwa duniya taimata dadi ' tana cikin haka ne Ilham ta shigo cikin d'akin. Zambur Fadwa tayi ta zauna ' fuskarta d'auke da murmushi. "Har Al'ameen d'in ya tafi?" "Eh ya tafi ' kuma yayi fushi, tunda bakizo kun gaisa na." Uhm ' kawai Fadwa tace wa Ilham, Ilham lura tayi ' Fadwa ta sauya ba kamar yadda ' ta barta ba. "Fadwa akwai labari ne mai dad'i?" "Uhm ' ai dama abinda naketa jira ki tambaya kenan." Nan ta fad'a mata duk abinda ke faruwa, da kuma hukuncin da Abba ya yanke ' sannan kuma ta sanar da ita cewa Abba yana nemanta. Miyau Ilham ta had'iye dak'er, gaban ta na dukan uku uku. "Shikenan ' nima za'a badani, Allah dai yasa nawa ba kusa ' kusa bane haka." Ta fad'a tare da dafe k'irjinta, abinne ya bawa Fadwa dariya matuk'a. "Haha! Lallaima Ilham ' to ba gwara kawai a had'a mu ' mu biyu ba?" Girgiza kai kawai Ilham tayi ' daka kalli idon ta ' zaka gane cewa akwai fargaba a cikin su, Ilham juyawa tayi ta nufi sashen ' Abba. Bayan Yaya Khaleel ' ya fito wanka ne, d'aure da towel a jikin shi ' ya zauna a bakin gado, ya hankad'a pillow ' don d'aukan diarry d'inshi, Hankalin shine yayi matuk'ar tashi ' don ganin babu diarry babu alamar sa. Nan yayi zambur ' ya tashi tsaye, gami da bud'e drowers d'in wajen ' duk da yasan bai aje a wajen ba. "Ha'a to a ina na aje shi?" Yaya Khaleel ' saida yabi ko'ina ya bincike, amma kwatakwata ' bai gani ba. Fadwa ce ta fad'o mashi a rai ' don kuwa yasan babu wacce zata iya d'aukar mashi diarry ' sai ita. "Oh my God ' this gurl is so stubborn, ni bansan yadda zanyi ' da yarinyar nan ba wallahy, mtswww." Ita kuwa Fadwa tashi tayi ' tayi shirin bacci cikin rigar bacci transparent ' iyakarta gwiwa, sannan ta haye gado ' gami da janyo handbag d'inta, tana k'ok'arin cire diarry d'in Yaya Khaleel ' domin karan tawa. Yaya Khaleel ' abin duniya ne ya isheshi, ya ga bazai iya hak'uri ba ' hakan yasa yafito daga d'akin shi ' daga shi sai towel a jikin shi, ya nufi d'akin su Fadwa. Yaya Khaleel ' bankad'o k'ofar yayi ' haka yayi daidai, da cirowar Diarry d'in nashi ' daga hannun Fadwa. A tsorace ta d'ago kai ' ta kalleshi, tsoro ne yasa tayi saurin yin wurgi da diarry d'in k'asa ' cikin rawar baki tace. "Yaya Khaleel ' are you looking for something?" Ta fad'a tare da yin saurin rufe jikinta ' da blanket ma'ana bargo. Cikin fushi ya k'arasa cikin d'akin cike dayin huci tamkar zaki, finciko ta yayi ' har sai da hannun ta ya ansa, a tsiyace ya fizgota zuwa k'asa. "Ke!! Where is my diary?" Had'iye miyau tayi dak'er , sannan tace. "Yaya Khaleel ' babu diary d'inka a wajena!" Yaya Khaleel ' maida kallon shi yayi zuwa k'asa, sannan ya tuna lokacin da ' take wurgi dashi zuwa k'asa, Fadwa cikin tsoro ta kalli diary d'in ' sannan ta maida kallon ta kan Yaya Khaleel suka had'a ido. "Well ' am so sorry Yaya Khaleel, am just trying to..." "trying to do what!!!" Ya daka mata tsawa ' sannan ya duk'a ya d'auki diary d'in. "For Goodness sake ' why are you so stubborn? Fadwa!" Sunkuyar dakai tayi ' ita dai tsoron ta shine, kada ya tab'a lafiyan jikin ta. Fadwa jitayi yayi shiru ' yasa tayi saurin d'aga kai ta kalleshi, ga duban ta sai taga ' ashe k'irjin ta yake k'arewa kallo, kasan cewar rigar jikinta shara shara ce. Da sauri tasa hannu d'aya ' ta kare wajen ' don kuwa yana rik'e da d'ayan hannun, ganin haka yasa Yaya Khaleel dawo wa cikin senses d'in shi. Ganin yadda tsoro ya kamata ne ' yasa shi yin murmushi tare da tallabo hab'arta. "What? Meye kike karewa? Aren't you stubborn enough? And besides ' kin kusa zama matata duk da bakida mu halli a zuciyata." Nan ya fara k'ok'arin kissing d'inta ' tak'i yarda, jin tafiyar Ilham ne ' yasa yayi saurin wulli da ita ' ta fad'a saman gado, sannan ya juya ya fice ' suka had'e da Ilham a hanya, saida ta jira ya wuce sannan ' ta k'araso cikin d'akin. "Fadwa ' meyafaru ne?" "Me kika gani?" Ilham K'arasawa ciki tayi ' ta nemi waje ta zauna. "gani nayi ' daga ke har shi ' kunyi wani iri." "hmm ke kuwa ' akwai ki da sonjin kwakwaf, babu komai fa kawai zuwa yayi ' yayi abinda ya saba." Ya tsine baki Ilham tayi ' sannan ta shiga cire kayan jikinta, donyin shirin bacci. "Baki bani labarin yadda kukayi da Abba ba." "Ke nifa wallahi ' yanzu bacci nakeji, ki bari sai munje school." Ok kawai Fadwa tace mata sannan ' ta maida kallon ta kan wayarta *Dedicated To My Fan's* *_Seemaluv馃憚 ' the brave!!馃挭_* [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 & *_Sumeeluv_* www.Seemaluv.wapka.me *_@Assalamu Alaikum, ina mai mik'a godiya ta agareki RUFAIDA YUSUF. Naji dad'i sosai matuk'a da yadda kika nuna soyayyarki ga JAMEESHA ' bama JAMEESHA kad'ai ba hardani, gaskiya munji dad'i sosai JAMEESHA tana godiya sosai..._* *45-46* A haka bacci yayi awon gaba dasu. *Washe gari* Da sassafe ' su Fadwa suka tashi, sai da sukayi sallah tukunna sukayi wanka ' Fadwa ce ta fara shiryawa sannan ta shiga kitchen domin had'a breakfast, Ta na cikin had'a tea ne Yaya Khaleel ya shigo . Cikin muryar rashin lafiya ' yayi mata magana, "Fadwa ' please ki had'a mun Coffee yanzu, ki kawomin d'akin...." Bai kaga k'arasawa ba ' amai ya taso mashi, cikin sauri ya k'arasa wajen sink d'in kitchen ' yaita kakarin amai. Cikin hanzari ' Fadwa ta d'ibi ruwa a cup, ta tsiyaya ruwan a tafin hannun ta, ta fara shafa mashi asaman kanshi. "Sannu Yaya Khaleel." Yawwa kawai yace ' sannan yabar kitchen d'in ya wuce d'akin shi. Nan tayi sauri ta had'a mashi Coffee d'in ba tare data k'arasa had'a masu kayan breakfast d'inba. Fadwa barin kitchen d'in tayi ' ta nufi d'akin Yaya Khaleel rik'e da cup a hannun ta, ciki ta shiga ta iske shi kwance saman gado ' rik'e da cikin shi, sannan ta sami waje ta zauna a bakin gadon. "Yaya Khaleel ' gashi na kawo." Tashi yayi ya zauna ' tukunna ya karb'a Coffee d'in ya rik'e a hannun shi. "Ki bud'e wancen drower d'in, zakiga Cimetadine ki d'auko min." Yayi mata nuni da yatsar shi ' haka yasa ta doshi wajen kai tsaye, ta d'auko maganin sannan ta dawo ta mik'a mashi. Harta juya zata wuce ya tsaida ta cewa, "Ina kuma zakije Fadwa?" Yanayin yadda yayi maganar ne ' yasa tajin tausayin shi sosai, hakan yasa ta juyo ta kalleshi tare da cewa. "Na'am?" "Baki bani ruwa ba ' zaki wuce kuma." "Bari in kawo ma." Juyawa tayi zata fita ' da niyyar wucewa kitchen, ya tsaida ita. "Ina zakije kuma? Bayan ga robar ruwa anan," Babu musu ta dawo ' ta d'auki robar ruwan ta mik'a mashi, sannan shi kuma ya b'alli maganin yasa a baku ta zuba mashi ruwan ya kora, Fadwa wani yarrrr takeji ' tsigar jikin sai tashi takeyi, don kuwa batason magani a rayuwar ta kokad'an. Yaya Khaleel ' sai a wannan lokacin ya kalli kwalliyar da ke fuskar Fadwa, a wannan lokacin ne yaji kishinta ya fara shiga cikin zuciyar shi 'Fadwa kam harta juya zata wuce yasake tsaidata, sai da ta yatsine fuska sannan ta juyo. "Dama a haka kike tafiya school d'in," Nan ta tsaya tana duba jikinta. "A'a zan sanya gele ai." "Nup! Ba dressing d'inki nake nufi ba, kwalliyar da kika cab'a nakeso ki gogeta yanzun nan." Sunkuyar da kai tayi ' tare da turo k'aramin bakin ta. "Ga tissue cen ' ki d'auka ki share wannan janbakin dake kan lips d'inki." Kallon wajen da tissue d'in yake tayi, sannan ta sake sunkuyar da kanta. "Yaya Khaleel plea..." Bata k'arasa ba ya daka mata tsawa. "Bakiji abinda nace maki bane?"

Chapter 9 of 20