"Insha Allah.!"
Abinda Umma ta fad'a kenan ta sami kujera ta zauna, suka cigaba da kallo.
*** *** *** ***
B'angaren Yaya Khaleel kuwa ' zaune yake a office d'in shi, yana duba wasu takaddu.
Yana cikin haka ne wayar shi ta fara k'ara, D'aukan wayan yayi ' ya duba amma sam babu suna.
Yaya Khaleel receiving call d'in yayi.
"Hello who's on the line?"
Cewar Yaya Khaleel.
"Ka fito daga waje ' anbada sak'o ne a baka."
Yaya Khaleel muryar na miji yaji.
"OK! but waye?"
"Ka fito dai ' koma waye ai zaka gani, Muna sauri ne.!"
Ok kawai yace ' sannan ya kashe wayar tare da tashi ya fito daga office d'in, Sakatariyan shi ya iske a zaune ya sanar mata cewa ' zai fita karb'o sak'o.
Haka Yaya Khaleel ya saka kai ' ya fita, Wasu mutane ya hango jingine a jikin wata babbar mota ' wacce duk tasha tinted.
K'arasawa wajen yayi ' ya basu hannu suka gaisa.
"Kune ke son ganina?"
"K'warai kuwa!."
Wani dake sanye da bak'in speck ne ya bashi amsa ' tare da cuna mashi bindiga daga cikin shi.
"Subhanallah!."
Abinda Yaya Khaleel ya furta kenan ' cike da tsoro.
"Wannan ne sak'on naka, saboda haka shiga mota mu tafi!."
"Subhanallah! Bayin Allah menai muku?.
D'ayan ne ya bud'e baki ya ce.
"Kada ka sake ' kayi wata k'wak-k'warar motsi, inba haka ba zamu harbe ka ' so just get in."
Bud'e motar sukayi ' Yaya Khaleel cike da addu'a a bakin shi, Haka suka tunkud'a shi ciki.
Yana shiga ya iske wasu a zaune ' Yaya Khaleel bai ankara ba yaji anfesa mashi wani abu, Nan ya fara fita hayyacin shi ' take ya rasa inda yake suka ja mota suka wuce.
*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃憣
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*73-74*
*AROUND 1:00PM*
Su Fadwa suna parlor zaman jiran Yaya Farook ' yunwa duk ta ishe su.
"Ni dai Umma ' muci abinci idan ya iso sai yaci nashi, Umma yunwa nakeji Allah."
Cewar Fadwa.
Ilham ce tayi saurin taron numfashin ta ' da cewa.
"A'a Yaya Farook d'in guda? Gaskiya ki bari aci gaba d'aya."
Wani haushi ne ya lullub'e Fadwa, A zuciyar ta tace.
"Mtsw nikam ' yanzu ko sunan shi banson inji an fad'o, To meye ma dalilin shi na dawo wa?."
Umma ce ta katse mata tunani ' da cewa.
"A'a ba takura! Je ki zuba abinci kici ' nima dai naga kamar bazai shigo da wuri ba.
Fadwa tashi tayi tana ma Ilham dariya ' ta k'arasa wajen dinning table tayi zaman ta, Sannan ta zuba abincin ta fara ci cikin kwanciyar hankali.
Sai da Fadwa ta gama ' tukunna ta tashi rik'e da plates d'in ta a hannu zata shiga kitchen suka ji sallama, Cak Fadwa ta tsaya ' nan su Umma suka mimmik'e tsaye tare da amsa sallamar.
Fadwa juyowa tayi a hankali ' ganin Yaya Farook ne yasa ta amsa sallamar tare da bud'e hak'ora.
Sannu da dawo wa kawai suke mashi ' Ilham ta karb'i jakkar dake hannun shi cikin jin dad'i.
"Sannu da isowa Farooku."
Cewar Ige.
"Haba tun d'azu muke ta jiran shigowar ka ' har Fadwa tayi gajin hak'uri ta ci abinci."
Jin haka yasa Yaya Farook mai da kallon shi kan Fadwa ' wacce ke rik'e da plates a hannu, Had'a ido sukayi ta sake mashi dariyar yak'e tare da cewa.
"Sannu da dawowa ' babban Yaya!."
"Yawwa."
Kawai yace ' sannan ya cewa Umma.
"Umma ' kuna da bak'uwa bari in shigo da ita."
Nan ya juya ya fita ' cike da mama ki su Umma suke kallon juna.
"Bak'uwa kuma?."
Cewar Fadwa.
Nan ta yatsine baki ta juya ' ta wuce kitchen don ajiye plate d'in da ke hannun ta gami da wanke hannu.
Yaya Farook shigo da bak'uwar yayi cikin parlon biye a bayan shi, Wa ta kyak-kyawar mace ce chocolate colour ' wacce bazata wuce 22yrs ba, Yaya Farook introducing d'in ta yayi wajen su.
"Umma wannan sunan ta Safeena! Daga Bangladesh muka had'u da ita, A cen family d'in ta da kowa nata suke ' kuma...."
Nan Umma ta dakatar da shi ' da cewa.
"Haba Farook! A tsai tsaye haka? aiko ruwa ne kwa bari kusha ko?."
Murmushi Yaya Farook yayi ' wanda sai da kyan fuskar shi ya bayyana.
Umma jagora tayi musu ' zuwa wajen dinning table, Ige da Ilham na biye da su.
Bayan sun zauna ne Fadwa ta fito daga kitchen zuwa parlor ' idon ta na kan Safeena wacce ta bata baya.
Cikin hanzari Fadwa ta k'arasa wajen dinning table d'in don ta ga wace ce; Fadwa jan kujera tayi ta zauna ' suna kallon kallo sa Safeena.
"Umma wace ce wannan?."
Fadwa tayi tambayar ' idon ta akan Safeena.
"Tare da Farook suka zo."
"Sannun ki da zuwa.!"
Cewar Fadwa.
"Yawwa sannu."
"Meye sunan ki?."
Safeena harta bud'e baki zatayi magana Umma ta dakatar da ita ' da cewa.
"Haba Fadwa ' amma kya bari dai ta gama ko? Sunan ta Safeena."
Murmushi Fadwa tayi wa Umma ' sannan ta maida kallon ta kan Ilham, Wacce abincin ta kawai take ci.
"Ilham k'arfe nawa don Allah?."
"Babu waya a tare dani!"
Yaya Farook duba wristwatch d'in hannun shi yayi.
"2:22pm yanzu."
Fadwa na jin haka ' ta tashi tsaye zata bar wajen Yaya Farook ya tsaida ita da cewa.
"Me zakiyi?."
"Wallahi Yaya Khaleel ne ' naji shi shuru, Shine zanje in duba ko ya riga ya shigo."
"Ok."
Abinda ya ce kenan ta juya ' ta wuce sashen ta, Ta na shiga ta zarce d'akin ta ' wayar ta ta fara duba wa amma sam bata gani ba.
"Oh na tuna ' tunda nayi aure ban sake amfani da phone d'ina ba, Tabbas tana d'akin Ilham."
Tana fad'in haka ta juya ta koma sashen su Umma ' kai tsaye ta zarce inda Ilham take ta janyo hannun ta.
"Fadwa meye haka? Abinci fa nake ci!."
"Yes i know."
Fadwa janta tayi har zuwa d'aki sannan tace.
"Ilham don Allah! Waya ta zaki taya ni bincikawa."
"Tana nan ' na adana miki ai."
"Yawwa to d'auko min."
Ilham wajen drower d'in gado ta nufa ta bud'e, Sannan ta d'auko wayar ta mik'a mata.
"Thanks sis ' to bani number d'in Yaya Khaleel."
Ok kawai Ilham ta ce ' tukunna taje bakin gado ta hankad'a pillos ta d'auko wayar, Nan ta fara karanto ma Fadwa number d'in.
Sai da Ilham ta gama ' sannan Fadwa tayi dialling numbern, Ringing wayar tai tayi ba'a d'aga ba harta tsinke.
"I hope shikenan?."
Cewar Ilham.
Kai kawai Fadwa ta d'aga mata ' sannan Ilham ta juya ta wuce.
Nan Fadwa ta sami waje ta zauna ' ta cigaba da kiran wayar, A k'alla sai da taimashi 5 missed calls ' tana cikin na shidan ne taji anyi rejecting.
Nan take Fadwa ta mik'e tsaye gami da dafe k'irjin ta.
"To ko ansace wayar ne? Ko kuma yana meeting!."
Abunda ta dunga ayyana wa kenan ' ta baro d'akin ta dawo parlor, Gani tayi har sun gama cin abincin sun dawo suna kallo ' haka yasa ta zarcewa inda suke ta zauna cike da tunane tunane kala kala a ranta.
" 'Yan nan lafiya? Naga kinyi wani iri ne!."
Cewar Ige.
Hakan yasa kowa ya maida kallon shi akanta , Murmushin yak'e Fadwa tayi had'i da cewa.
"Wallahi! Number d'in Yaya Khaleel ne nake ta kira ' amma ba'a d'agawa k'arshe ma rejecting yayi, Kuma yace mun 2:00pm zai dawo."
Cike da damuwa ta k'arashe maganar.
"Ina ce yau ya fara zuwa office d'in?.".
Cewar Umma.
"Eh yaune ya fara."
"To k'ila aikin ne yayi mashi yawa, Kinsan dole yaje ya iske aiki sosai."
Kai kawai Fadwa ta d'aga ma Umma ' amma ita dai jikin ta yana bata kamar ba lafiya ba.
"Amm... Umma wannan dai sunan ta Safeena ' kamar yadda na fad'a, Kuma Umma ita ce wacce mukayi alk'awarin aure tsakanin mu.
Fadwa mai da hankalin ta tayi ' akan abunda Yaya Farook ke fad'a, Sannan ya ci gaba da cewa.
"Umma ba komai yasa ta biyoni ba ' illa yardar da tayi dani! Da kuma son ganin family d'ina da take so, Umma kuma bata taho nan ba sai da iznin iyayen ta ' kuma suka ce idan na tashi dawo wa inzo da wani nawa don ayi maganar aure, Kasan cewar sun gaji da zaman ta gida babu miji."
"To Alhamdulillah! Naji duk abinda ka fad'a Farook ' Allah ubangiji ya nuna mana ranar lafiya, Insha Allah idan Abban ku ya dawo zan sanar dashi komai."
Cewar Umma.
Safeena ba k'aramin dad'in kalamin Umma taji ba ' ganin yadda aka karb'e ta hannu bibbiyu babu tsangwama.
"Ilham tashi ki d'auki trolley d'in ta gata cen bakin k'ofa, Ki kai ta d'aki tayi wanka ta huta."
To Ilham tace ' tukunna taje d'auki trolley d'in kamar yadda aka umarce ta.
Fadwa tashi tayi ' ta wuce sashen ta jiki a sanyaye, Bayan wuce war tane Yaya Farook yake tambayar Umma cewa.
"Umma wannan kuma wacece?."
"Oh yaran zamani ' ai dama ba sanina zakayi ba."
Cewar Ige.
Abun ne ya bawa Umma dariya ta ce.
"To Ige ce dai ' daga k'auye take, Kuma abokiyar wasa ce a tsakanin ku."
*Dedicated To My Fan's.*
馃憚馃憚馃憚
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
#IG: @Bae_Seema鉂�
*75-76*
Fadwa tana shiga sashen ta ' ta zauna a parlor saman kujera, Dialing number d'in Yaya Khaleel ta sakeyi ' cikin sa'a aka d'aga wayar, Cikin muryar damuwa Fadwa ta fara magana.
"Hello! Sweetheart ' fisabilillahi haka mukayi dakai? Tun d'azu nake cikin damuwa wallahi, Kuma na kira ka baka d'aga ba why?".
Tana gama rufe baki ' taji an b'arke da dariya, Wata murya taji wacce bata Yaya Khaleel ba ' hakan yasa ta tsora ta matuk'a.
"Ke!!!."
Ta ji an daka mata tsawa ' har sai da gaban ta ya fad'i.
"Baki ba mijin ki! Don bazai tab'a dawowa gareki ba!!, Zamu kashe shi ' bari ma kiji."
Nan mutumin ' ya ware hannun shi ya zubama Yaya Khaleel duka a ciki ' wanda yake a d'ad'd'aure, Haka Yaya Khaleel ya saki wani wahalallan k'ara.
Nan take Fadwa ta kama baki ' hawaye suka fara mata zarya a fuskar ta.
"Kinji ko?."
"Don Allah kayi hak'uri ka sakarmin mijina, Ko nawa kakeso ni zan ba..."
Bata kaiga k'arasa wa ba aka kashe ' Fadwa ihu ta saki mai sauti tare da sakin wayar a k'asa ta zuk'unna tana kuka.
"Wayyo ni Fadwa na shiga uku...!"
Su Umma ne suka shigo sashen nata a guje ' cikin tashin hankali, Su ka isketa a zuk'unne ta d'aura hannu biyu akai.
"Fadwa lafiya? Meyafaru?."
Cewar Umma.
Nan ta rik'a musu nuni da wayar ' cikin kuka.
Hankalin Yaya Farook kuwa ' inyayi dubu ya tashi, K'arasa wa kusa da ita yayi ' ya zuk'unna inda take.
"Meyasa bazaki bud'e baki kiyi bayani ba? ' don Allah ki fad'a mana meyafaru?.
"Yaya Farook zasu kashe mun miji! ' don Allah ka taimaka min karsu kashe shi, Ina son shi."
Nan ta juya ta kalli Umma ' wacce idon ta duk ya cicciko da hawaye.
"Umma ' Umma don Allah ' ki fad'a musu karsu kashe shi..."
Ige karan kanta abun tsoro ya bata sosai ' hakan yasa ta koma gefe ta takure.
Yaya Farook daka ma Fadwa tsawa yayi ' har sai da gabanta ya fad'i.
"Fadwa!!! Ki natsu mana ' ki fad'a mana abinda ke faruwa.!"
Cikin rawar baki Fadwa ta fad'a mashi duk abinda ya faru.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!."
Abunda suka furta kenan a tare ' Umma jiri ya d'ibe ta zata fad'a Ige tayi saurin rik'o mata hannu suka sami waje suka zauna.
Yaya Farook mik'ewa yayi ' yayi ta maza ya fita daga waje ' ya ciro wayar shi daga aljihun shi, Yayi dialing number d'in Abba.
Bayan Abba ya d'aga wayar ne ' Yaya Farook ya sanar mashi duk abinda ke faruwa, Nan take Abba ya rafka salati ' sannan ya ce.
"Zan kira commissioner of police in sanar dashi komai ' Insha Allah Khaleel bazai mutu ba, Kuma nima gani nan dawo wa."
Ok kawai Yaya Farook ya ce ' sannan ya koma ciki aka cigaba da lallashin ta.
*** *** ***
Bayan Safeena ta fito daga wanka ne ' harta gama kintsawa, Sannan ta fito parlor ' ganin babu kowa a parlon ne yasa ta koma ciki wajen Ilham ' wacce ke amfani da wayar ta.
"Ilham babu kowa a parlor ' ina suka je?."
"To k'ila suna waje ne ' yawwa bari ma mu shiga part d'in Fadwa."
Ilham ta fad'a tare da mik'ewa tsaye suka bar d'akin, Sashen Fadwa suka nufa ' nan Safeena da Ilham suka fara jin shesh-shek'an kuka.
Cikin hanzari suka k'arasa ciki da sallama d'auke a bakin su, Carko carko sukayi a tsaye ' ganin yadda fuskar kowa ke d'auke da damuwa.
"Farook ' is everthing alright?."
Safeena tayi tambayar ' ba tare da ya bata amsa ba.
Ilham wajen Umma ta je ta zauna ' tana kallon yadda hawaye ke zuba a fuskar ta.
"Umma ' don Allah meke faruwa?."
Umma kasa cewa komai tayi ' sannan Ilham ta maida kallon ta ga Ige.
"Ige don Allah ki fad'a mun meya faru?."
"Ilham Khaleel ne aka sace ' kuma sunce kashe shi zasu yi."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."
Nan Fadwa ta sake fashewa da kuka ' da sauri Ilham ta juyo ta kalle ta, Yaya Farook dafe kanshi yayi ya tashi da sauri ya bar wajen ' hakan yasa Safeena juyawa zata bishi ' yayi saurin dakatar da ita tare da mata nuni da hannu alaman ta tsaya.
Ilham tashi tayi ' ta sauko k'asa inda Fadwa ke zaune dirshen tana kuka.
"Sis?."
A hankali Fadwa ta d'ago kai da rinan nun idanun ta ' ta kalli Ilham.
"Am here for you! Kiyi hak'uri ki bar kuka, Insha Allah Yaya Khaleel zai bayyana ' kuma babu abinda zai same shi."
Ilham ta fad'a tare da kwanta da kan Fadwa bisa cinyar ta, Ta na bubbuga bayan ta a hankali ' tukunna Safeena ta sami waje ta zauna.
*** *** *** *** *** *** ***
*AROUND 4:00PM...*
Lubna na zaune a parlor ' tare da Mummy da Daddy suna fira, Wayar ta ta fara k'ara alaman kira ' da sauri ta kalli wayar number ce babu suna, Nan ta tashi cikin sauri ta wuce d'aki tare da receiving call d'in.
"Hajiya! Mutumin nan fa na hannun mu ' yanzu haka ma a d'aure yake!."
Ya fad'a yana dariya!.
"What!? Khaleel d'in? Amma haka mukayi daku? Inace na fad'a muku cewa ku barshi ni na hak'ura?.."
"Haha!.. Haba hajiya! Karfa ki manta kin riga kin fad'a mana address, Kinga kuwa dole muje mu yagi namu kason ko?."
Rik'e baki Lubna tayi ' tana furta Innalillahi.
"Kar ki damu hajiya! Bazamu kashe shi ba ' wahalar dashi kawai muke, Har mu samu mu sami abinda mukeso!."
"A'a kaga! Nidai ku sake shi please ' duk nawa kuke buk'ata nizan baku."
Dariya ya sakar mata ' sannan ya kashe wayar ba tare da yace mata komai ba.
Lubna wulli tayi da wayar saman gado ' ta kama bakin ta da hannu biyu, Ta fara zagaye d'aki.
"Na bani ' ni Lubna! Zan sa kaina cikin matsala, Insha Allah gobe zanje gidan su Khaleel na fad'a musu komai."
Lubna a bakin gado ta zauna ' tana nazarin irin halin da Khaleel ke ciki, Kila ma babu abinda yaci ' nan tayi zambur ta mik'e tsaye cike da damuwa bayyane a fuskar ta.
"Bazan iya bari har gobe ba! ' Yau zanje gidan su insanar."
*** *** *** *** ***
B'angaren Fadwa kuwa har yanzu kuka takeyi ba k'auk'auta wa.
"Ilham kama ta ' mu koma cen sashen zaifi."
Cewar Ige.
Nan suka tashi gaba d'ayan su ' Ilham ta rik'ewa Fadwa hannu ita kuma Ige rik'ewa Umma hannu suka koma sashen su, Yaya Farook kuwa yana garege yana zaman jirar isowar Abba.
Abba ba shi ya iso gidan ba ' sai wajen 6:30pm, Haka Abba yayi packing motar shi ya fito ' Yaya Farook ya tareshi.
"Sannu da isowa Abba."
"Yawwa Farook."
Abba ya amsa tukunna suka k'arasa ciki, Sallama Abba yayi ma su Umma suka amsa ' tare da mik'ewa tsaye, Umma ce ta tako har inda yake cikin kuka.
"Alhaji! Kaji abinda ya faru da Khaleel ko?."
"Ki kwantar da hankalin ki ' police suna nan suna aiki akai.
Abinda ya fad'a kenan yaja hannun ta suka koma suka zauna ' Fadwa wacce ke zaune kasa cewa komai tayi sai dai hawaye da keta kwaranya a idanun ta.
"Fadwa?."
Abba ya kira sunan ta ' ta sigar tausayawa, Ta d'ago kanta ta kalle shi.
"Na'am Abba."
"Kar kisa damuwa a ranki kinji ko? Insha Allah Khaleel zai dawo."
Girgiza kai Fadwa tayi cikin sark'ewar murya tace.
"Abba ' how sure are you cewar zai dawo? Abba inhar suka kashe shi ' to nima bana tunanin zan iya rayuwa."
Abba girgiza kai kawai yayi ' alaman tausaya wa, Sannan Ilham ta cigaba da lallashin ta.
Yaya Farook waje ya samu ya zauna ' yayi dailing number d'in Yaya Khaleel amma a kashe.
Yana cikin haka ne ' suka ji sallama, A tare suka juya don suga waye.
Lubna ce ' a tsaye a bakin k'ofa rik'e da handbag d'inta a hannu.
*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槝
Follow #IG @Bae_seema鉂�
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*#IG:* *_@Bae_Seema鉂*
*79-80*
Sannan su Umma suka amsa sallamar ta ' Fadwa tsayawa tayi a gaban ta suna kallon kallo nad'an lokaci, Tukunna ta ce.
"I hope kinzo min da labari mai dad'i."
Lubna k'arasawa tayi daga ciki ' ba tare da tace wa Fadwa uffan ba, Ta sami waje ta zauna.
Bayan sun gaisa ne ' ta ciro wayar ta daga handbag d'inta tace.
"Umma! Jiya ban samu damar kiran su ba ' amma yau insha Allah zan kirasu agaban kowa."
Fadwa ce ta dawo ta zauna ' cikin b'acin rai tace.
"Aiba mijin ki bane ' kuma bakisan halin da yake ciki ba, Shiyasa baki damu da ki kira wad'an nan k'artan naki ba ' domin su sakar min mijina."
Wani mugun kallo Lubna ta sakar wa Fadwa ' gami da cewa.
"Fadwa ba don ke nazo wajen nan ba ' soyayyar Khaleel ce da har yanzu take d'awainiya dani, And let me warn you! Karki sake fad'amin maganar banza ' because i can change my mind at any time."
Fadwa har ta yunk'ura zata kai mata duka ' Umma ta daka mata tsawa.
"Fadwa! meyasa ke baki jin magana ne!! Ke bazaki tab'a kwantar da kai kibi komai a hankali ba?".
"Umma ' ki bari in koya wa wannan 'yar barikin hankalin, Harni zata kalla tace ' soyayyar shi ne a ranta?!".
Ige ce ' ta taso tazo har inda Fadwa take ta kamo hannun ta, Suka koma suka zauna waje d'aya tana lallashin ta.
"Ilham je ki kiramun Farook ' ni kuma bara inkira Abban ku."
To Ilham tace ' sannan suka sa kai ita da Umma suka tafi kiran su.
"Lubna! Please ki rik'a hak'uri da ita, Kinsan dama sai irin haka ta faru ' tunda taimako zakiyi kawai ki taimaka, karki saka wani haushi a ranki."
Cewar Safeena.
Fadwa yunk'urin tashi tayi Ige tayi saurin rik'e ta gami da girgiza mata kai.
"No Ige just let me talk!".
Kasan cewar Ige bata san abunda Fadwa ta fad'a bane, Hakan yasa ta sake ta ' Fadwa taje har gaban Safeena tare da tsira mata hannu.
"Baki san wacece ita ba! So please don't involved yourself in this matter!, besides ke da kike bak'uwa ma! Ina ke ina shish-shigi?".
Hakan yayi dai dai ' da shigowar Yaya Farook da Ilham, Umma kuma da Abba cikin parlon.
"Meke faruwa anan wajen?".
Cewar Abba.
"Rashin kunyar da take min ne ' a gaban idon ku, To yau shine take wa wannan baiwar Allan ' ni
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 20