Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ikon kyautata maku. Ameen suka amsa a tare ' sannan Abba ya ce. "A Company din Abokina ka sami aikin ' gobe Insha Allah zan kaika. Cikin Farin ciki Ya tashi ya wuce d'akin shi ' nan ya dinga kiran Friends d'inshi suna Congratulating d'inshi. ya na gama wayar ya d'auki key d'in motar shi ya fita. *Around* *10am*... Fadwa ta farka daga bacci ' ta nufi bathroom tayi wanka sannan ta fito, Simple makeup tayi ta sanya doguwar rigar atamfa ' tukunna ta nufi parlor ta taradda Umma da Abba ta gaishe su sannan ta juya zata koma ciki Umma ta tsaida ita da cewa, "Fadwa yaya jikin naki? "Da sauk'i Umma. "To Allah ya k'ara sauk'i, Ameen ta ce sannan ta juya ta wuce. kai tsaye ta nufi Lambu ta zauna tare d'aga kanta sama tana kallon yadda Tsuntsaye keta safa da marwa a wajen, abun Yayi matuk'ar burge ta yasa ta tashi ta k'arasa cen cikin Lambun tana kallon tsuntsaye kala dabam dabam. Cikin ta ne ya fara mata k'ara sakamakon Karya wanda batayi ba, hakan yasa ta tsinki Tuffa(Apple) a wajen ta ci saida taji ta koshi sannan ta cigaba da kallon Cikin Lambun. Yaya Farook dawo wa gida yayi ' Ya shigo parlor babu kowa sannan ya wuce cikin gidan, d'akin su Fadwa ya fara lek'awa ganin bata cikine yasa ya tafi Lambun shima kai tsaye, A zaune Ya hangi Fadwa ita kad'ai Fuskar ta cike da Fara'a, Ya k'arasa wajen ' jitayi anrufe mata Ido. "Waye please? Ilham kece ko? Shuru yayi ya kyaleta ba tare da yace mata komai, "Mtsw Dalla malama ki sakemun ido na. sake mata ido yayi sannan ta juyo ta kalle shi, ganin shine yasa ta tsorata ta mik'e tsaye gami sakin k'ara, "Ahhghh, Yaya Farook kayi hakuri bansan kai bane. D'aure fuska yayi ya matso daff da ita, "Na sami Aiki Fadwa. "Wow! Alhamdulillah Yaya Farook naji dad'i kuma na tayaka Murna. Murmushi yayi Tare da tallabo fuskar ta da hannu biyu, "Fadwa ai kece yadace azo a tayaki Murna ' Domin Wannan samun aikin tamkar ke ce kika sameshi. Haka ya fad'a ya na k'ok'arin Kissing d'inta, "Yaya Farook what are you trying to do? Tayi tambayar gabanta na dukan uku uku, tana k'ok'arin Kub'uce wa ya k'ara matseta. "Yaya Farook please ka daina mana ' banajin dad'in hakan.... Cikin sauri ya saketa Tare da juya mata baya yana maida numfashi, itama ta juya tayi gami da dafe k'irjin ta hannunta na rawa ta ce, "Yaya Farook Am sorry but i just can't. "Yes bazaki iya ba ai ' saboda bakya sona Fadwa. Da sauri ta juyo ta kalle shi idanuwan ta sun kad'a sunyi jaaa. "Yaya Farook na dad'e da fara Son ka a cikin Zuciya ta , kad...... Bata kaiga k'arasa maganar ba Ya dakatar da ita da cewa, "Inhar kina sona dagaske ' to kije ki fad'awa Su Umma domin suyi mana Aure, Fadwa baxan iya jure rashinki a kusa dani ba. mamaki ne ya rufe ta ' yasa ta je Gaban shi ta tsaya, "Yaya Farook kada ka d'auramun nauyin da banice Ya dace insauke shi ba. Tana gama fad'in haka ta juya zata wuce yayi sauri ya rike hannun, "Fadwa bazan iya fad'a ma Umma da Abba ina sonki ba. Saurin fizge hannun ta tayi cikin bacin rai sannan ta juya ta wuce. D'akin su ta wuce direct ' tana shiga ta fada saman gado, wasu zafafan hawaye ke zubo mata a fuskar ta, "Wannan wace irin soyayya ce? Wannan wane irin azabtar wa ce? Dama haka Soyayyar take?.... Cikin kuka ta k'arashe maganar, tashi zaune tayi ta share hawayenta sannan ta wuce Kitchen ta daura girki. *** *** *** *** *** *AROUND* *1:56PM* Fadwa ta gama girkin ta zuba cikin Plask ' sannan ta kawo parlor ta ajiye, ta wuce sashen Umma ta fad'a mata cewa ta gama Abinci, koda ta dawo iske Yaya Farook tayi a dinning table a zaune ' yana kallon ta cike da murmushi, Kawar da fuskar ta tayi sannan ta k'arasa wajen cikin sauri ta Zuba mashi abinci, fuskarta babu annuri a cikin ta. Bayan tayi sarving d'inshi ne ta koma ta zauna Suna kallon kallo, "Bazaki zuba abincin bane? Shuru tayi ta kyaleshi sannan ta zuba ruwa a cup tasha, "Fadwa am i not talking to you? "Am not hungry! Abunda ta ce kenan ' ta mike tsaye da niyyar barin wajen yayi saurin tsaida ita, "Fadwa son da nake miki bashine zai hanani hukunta ki ba idan kikayi laifi. Cikin fad'a yayi maganar hakan yasa ta jin tsoro ' gudun kar jikinta ya dimamu ne yasa ta saki fuskarta tare da yin murmushi, "Yaya Farook don Allah ka barni ' wallahi banajin Yunwa. "Fadwa ban yarda ba ki dawo ki zauna,... Yana gama fad'an haka Umma ta shigo parlon cikin hanzari Fadwa ta boye a bayan ta, "O'o lafiya? "Umma, Yaya Farook ne wai dole sainaci abinci yanzu ' ni kuma banajin yunwa, "Ha'a Farook banason zalunci, antaba yin abune dole ne wai? sosa kai yayi Cikin fara'a Sannan ya ce, "Umma ni ban mata dole ba ni kawai... Tun kafin ya k'arasa Umma ta ce, "Yi tafiyar ki kinji ki kyaleshi, Saida tayi mashi gwalo sannan ta juya ta wuce. *2:00pm* Bayan sun gama cin abinci ' Umma ta dawo harabar parlor ta zauna' shi kuma Yaya Farook ya d'auki key din motar shi ya fita, Ilham ce ta shigo cikin parlon a gajiye ' Ta gaida Umma sannan ta nufi d'akin su, ta na shiga ta Iske Fadwa a zaune ta na duba handOut. Zuwa tayi ta jiye Handbag dinta sannan tace, "Ke baiwar Allah ya jikin naki? Ajiye handout din tayi a gefe ta d'ago kai ta kalle ta, "naji sauki kad'an Ilham. "To gwara da kika warke da wuri don gobe munada test din Anatomy. Cewar Ilham, "Tabb hmm Allah dai kawai ya taimake mu kawai. Ameen Ilham ta ce sannan ta dauki towel ta daura ' ta fada bathroom donyin wanka. *Dedicated* *To* *My* *Fan's* 馃憚馃憚馃憚馃槣 [5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_P.W.F_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluvv_*馃憚 @*JAMEESHA* *_wannan_* *_page_* *_d'in_* *_nakine_* *_i_* *_just_* *_feel_* *_like_* *_dedicating_* *_this_* *_page_* *_to_* *_you_* *_because_* *_of_* *_love_* *_and_* *_friendship_* *19-20* pages馃尮 Bayan wasu y'an lokuta k'alilan ne Umma ta ga kiran Yaya Khaleel ya shigo cikin Wayarta, Murmushi tayi gami da girgiza kai tukunna ta d'auka, "Sallamu Alaykum, " "Hello Umma!? Umma yau zan dawo gida in sha Allah." "Tor Khaleel Allah ubangiji ya tsare ' har jirgin naku ya tashi ne?" "A'a Umma But yanzun nan zai tashi ' shiyasa nakira!" Addua Umma tayi mashi sannan sukayi Sallama ta kashe wayar. Umma tashi tayi ta wuce d'akin su Ilham ' koda ta shiga Fadwa ce kawai tagani, "Fadwa Ina Ilham? " Cewar Umma, "Umma Ta shiga wanka ne," "To idan ta fito Kice mata ' kushiga kitchen ku shiryawa Khaleel Abinci, don yau zai dawo." 馃槺To kawai Fadwa tace sannan Umma ta juya ta koma parlor ' nan wajen ta tsaya tana kokwanto akan Maganar Umma, "Kai Kardai Yaya Khaleel dinda Ilham ta bani labari? Wayyo ' shikenan mumbanu " Cikin hanzari ta mike tsaye ' Ba tare da tasan abinda zatayi ba , kai da komowa kawai takeyi ' tana cikin hakan ne Ilham ta fito daga bathroom dauke da karamin towel a hannun ta tana goge gashin kanta, ganin yadda Fadwa keta yawo a dakin ne yasa ta tsaya cak ta na kallon ta. "I hope ba wani laifin kika kara Daukowa kanki ba?" Cewar Ilham, Tsayawa tayi ta kalleta with sad face ' sannan tace, "Kin fito kina wani Goge gashi ' verysoon zaki manta da wannan ai!!" "Me kike nufi?" "Eh Umma tace Mu shiga kitchen Mu shiryawa Yaya Khaleel abinci ' don ya kusa dawo wa, "What!!?" Cikin tsawa da muryar tsoro tayi magana ' Hakan yasa ta samu waje ta zauna a sanyaye tare da cewa, "Shikenan, ya dawo Lafiya ' basai na shiga harkar shiba sannan zansha wuya?" Shuru sukayi nadan lokaci sannan Ilham ta ce, "Please Fadwa kije kifara Kafin Ingama shiryawa ' koma mene ne sai indaura daga baya." Ok kawai Ta ce mata sannan ta fita daga Dakin Zuwa kitchen. *Around* *3:00pm* Bayan Fadwa da Ilham sun kammala Komai sun jera a dinning table ne ' Abba ya dawo Gida, "Anata preparation din dawo war Khaleel ne?" Yayi magana cikin sauri ya na k'ok'arin wuce wa sashen shi, Ilham ta d'ago kai ta kalle shi cikin sanyin jiki. "Eh Abba wai haka aka ce." Komawa sukayi suka zauna a harabar Parlor suna kallon, Yaya Farook ya shigo d'auke da leda Guda biyu a hannun shi ' Wurgama ko wannen su yayi Fuska a daure ya sami waje ya zauna. Cikin sauri Fadwa ta bude ledarta da kwalin waya ta fara hada ido ' xambur ta mike tsaye cike da murna, "Wayyoo Yaya Farook..." Juyowa tayi ta kalleshi cike da Fara'a, ganin ya daure fuska ne yasa Ta koma a zaune jiki a sanyaye. Itama Ilham bude nata tayi taga wayace ' sannan tayi mashi godiya, kai kawai ya daga Mata alaman Yaji ' sannan yace, "Yau Khaleel zai dawo Hope ' kun kammala komai." A tare suka amsa da cewa Eh, Sannan kowannen su ya mik'e tsaye d'auke da wayarshi a hannu suka wuce d'aki. Shima Yaya Farook tashi yayi ya wuce d'akin shi, yana shiga ya ciro wayar shi ' yayi dailing wata new Number. Fadwa na zaune bayan sun kunna wayan ' cikin jin dadi Itada Ilham sai taga kira ya shigo Wayar, "Kai!! Ilham harda Sim a ciki." Abunda ta ce kenan ' tayi saurin yin recieving call din, Sai jitayi ance. "It's Me Farook, kizo d'akina Yanzun nan." Yana gama fad'in haka ya kashe wayar, kallon Ilham tayi Cike da mamaki. "Wane ne?" Cewar Ilham, Smilling tayi mata ba tare da tace mata komai ba ' ta tashi ta bar d'akin, kai tsaye ta wuce dak'in Yaya Farook ' saida tayi knocking sannan ta shiga tare dayin Sallama, "Yaya Farook gani! Juyowa yayi ya kalleta ' sannan ya jawo hannun ta ya zaunar da ita a saman gadon shi, "I hope kinji dad'in Gift d'inda na baki?" Ya fad'a yana k'ok'arin zaunawa kusa daita, "Eh Yaya Farook na gani ' kuma na gode sosai" "Fadwa you completely changed my life ' koda nayi niyyar yin wani abun saboda Soyayyar ki sai inji nakasa, because i love you so much." Yana gama fad'in haka yayi kissing d'inta a goshi, "Tashi ki wuce d'aki, bazan iya jore ganin ki a nan wajen ba ' komai zai iya Faruwa Fadwa!!" Cikin Sanyin Murya yayi Maganar ' hakan yasa taji wani Yarrrrr a jikinta, da sauri ta mik'e sannan ta bar d'akin cikin hanzari. parlor ta wuce kai tsaye ' Suka had'e da Umma zataje kitchen, "Lafiya Fadwa? Naganki kamar Wacce aka biyo ne?" Had'd'iye miyau tayi daker, tare da zurowa Umma idanu tana tunanin k'aryar da zatayi mata. "Fad'amin mana, Don Fuskarki ta kasa boye tsoron da take d'auke dashi, " "Amm...well Umma babu komai ' and please don't worry about me, tsaka nagani a kitchen shiyasa naji tsoro." "To shikenan Allah ya kyauta." Ameen Ta ce sannan ta k'arasa Parlor ta zauna ' zamanta keda wuya taji ana Knocking K'ofa, tashi tayi taje ta bud'e. Cikin izza ya shigo Cikin parlon ' Fadwa baki ta saki ganin yadda ya shigo kai tsaye, "Malam lafiya? Kuma wa kake nema? " Juyowa yayi ya kallet ta cikin b'acin rai da jin haushin tambayar da tayi mashi, yasa ya dawo daff da ita ya tsaya tare da k'are mata kallo. "Ke? .." Kasa k'arasawa yayi saboda haushi, sannan ya juya zai k'arasa cikin gidan tayi sauri ta rike mashi riga. "Malam magana nakeyi ai...." Ji kake Tasss ' tun kafin ta gama rufe baki ya sharara mata mari, "ke!! Wace ce dazaki yimun irin wad'an nan tambayoyin, Koda yake dama haka y'an aiki suke ' To nine Khaleel kuma idan kika cigaba da Yimun tambayoyi dukan banza zakisha." Zukunna wa Fadwa tayi rik'e da fuskarta hawaye na gangaro mata ' Lallai ta tausayawa kanta jin Yadda sukayi Arba da Yaya Khaleel for the first time, Haka nan Ta share hawayen ta tare da mik'ewa tsaye. "kayi hak'uri Bansan kaine Yaya Khaleel ba... Tsaki ya ja gami da zama a saman kujera, "Naji kije ki kiramun mutanen gidan." Juyawa tayi ta nufi d'akin su ta iske Ilham a zaune, Ilham d'ago kai tayi ta kalle Ganin fuskarta babu annuri ne yasa tayi saurin mik'ewa tsaye, "Fadwa? Ya dawo ko?" "Hmm ya dawo mana ' tunda harya watsamin mari" Zaro ido tayi sannan ta fita d'akin cikin sauri ta nufi kitchen ta fad'awa Umma, sannan ta zarce d'aikin Yaya Farook shima ta sanar dashi ' ita dai Fadwa zama tayi a bakin gado ' cike da jimamin marin da tasha. *Dedicated* *To* *My* *Fan's* 馃憚馃憚馃憚馃槣 [5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluvv_*馃憚 *21-22* pages馃尮 Umma kai tsaye ta baro kitchen Ta nufi parlor Ilham da Yaya Farook suna biye da ita ' Suna Isa cikin Parlon suka iske Yaya Khaleel a zaune ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya yana kallon TV, Jin Sallamar su ne yasa yayi saurin Juyowa ya kallesu tare da mik'ewa tsaye cike da Farin ciki, Cikin sauri ya rungume Yaya Farook Cike da jin dad'i, "Yaya! Nayi kewar ku sosai wallahi" Cewar Yaya Khaleel, Murmushi yayi sannan suka sami waje suka zauna ' Yaya Farook yace, "Khaleel kenan ai muma haka ' and Yanzu ai Kewa ya k'are tunda gaka a gida," "Hakane Yaya!" Umma ce ta katse masu ' magana da cewa, "O'!! Hanta da jini kenan, To ai saiku tashi Aje aci abinci ' don nasan Khaleel da yunwa ka shigo." Dukkan su Dariya sukayi sannan suka mik'e tsaye da niyyar Zuwa dinning table Yaya Khaleel yaja kunnen Ilham gami da cewa, "Ke haryanzu rashin kunyar ki tana nan ko? Bakisan kimun sannu da dawo wa ba ko?" Saida ya bari Umma tafarayin gaba tukunnan ya zungure ta ' har saida ta fad'a saman kujera tukunna ya k'ara gaba. Cikin hanxari ta tashi kamar zatayi kuka sannan ta nufi dinning d'in. Bayan zauna wansu ne Ilham tayi Sarving d'insu , ta zubawa kowa sannan ta zuba nata ' saida suka fara ci sannan Umma ta lura Fadwa bata wajen, "Ilham me Fadwa takeyi ne ' da bazata zo taci abinci ba? " "Bara inkira ta Umma." Abin da Ilham ta ce kenan ta tashi ta bar wajen domin kiran Fadwa ' Yaya Khaleel kuwa Mamaki ne ya cika shi, "Fadwa kuma? To bakuwa mukayi a gidan?" Abinda ya ce kenan A zuciyar sannan ya cigaba da cin abincin. "Kaii!!.. Umma abincin nan yayi dad'i wallahi Kodon na dad'e banci abincin ki bane? " Cewar Yaya Khaleel, Murmushi Umma tayi ' Cike da fara'a ta ce, "Uhmm.. Khaleel kenan aibani nayi wannan abincin ba dakake ta zuba santi. " "To Umma wane yayi? Kardai kice Ilham ce tayi abincin nan." Tambayar ne ta bawa Yaya Farook dariya, "To mai ka maida Ilham ' ina gidan nan ace bata iya abinci ba? Aiko da taci najaki." Cewar Yaya Farook, "Ai Ilham da Fadwa sune sukayi maka wannan girkin." Tana gama rufe baki Fadwa da Ilham suka k'araso parlon ' cikin sauri bayan sun zauna ne Yaya Khaleel ya d'ago kai ya kalleta, "Umma wannan ce Fadwa d'in? Ita kuma wacece? Na d'auka y'ar aiki ce ai." Yayi maganar ya na kallon Umma, Nan Umma ta bashi labarin duk abinda ya faru ' da yadda akai ta dawo gidan da zama. Nan take tausayin ta ya kamashi ' cike dayin dana sanin Marin ta da yayi mata, Fuskewa yayi馃槑 sannan yace. "welcome to our house Fadwa," "Yaya Khaleel aini ba bak'uwa bace kai zan cewa haka ai," b'ata rai yayi ya maida kallon shi ga abinci, Shi kuwa Yaya Farook Ita kawai ya ke kallo cike da shauk'i, Umma ta na gamawa ta tashi ta wuce sashen ta ' ganin haka yasa Yaya Farook mik'ewa da niyar Wuce wa d'aki tare da cewa, "Dare yayi 8:00 yanzu ' idan kin gama kizo ki gyaramun gado na, don inaso inyi bacci ne. " D'ago kai tayi ta kalle shi suka had'a ido tasan cewa da ita yakeyi, Sannan ya juya ya wuce. Ilham cikin hanzari ta kammala cin abincin ta tashi da niyyar tafiya ' Fadwa tayi sauri ta rik'eta, "Please Ilham ki tsaya kid'an jirani na kusa gamawa. Yaya Khaleel d'ago kai yayi ya kalli Fadwa, " "A'a tunda kina zaune da aljani ai dole kice ta tsaya ta jira. " Maida kallon shi yayi akan Ilham wacce duk ta gama tsorata ' cikin tsawa Yace, "Come on ke kuma ki wuce kije ki kwanta ' tun kafin inb'ata maki rai a wajen nan. " Da gudu ta k'arasa d'akin, Fadwa kuwa kasa cin Abincin tayi ta tsaya tana kallon plate d'in. "Look! Idan kin k'oshi ne to ki tashi ki kwashe plates d'in don nagaji da ganin ki. " Cikin sauri ta tashi ta hau hahhad'a plates d'in wajen, tana cikin haka ne ta ture Cup da ruwa aciki ' sam batasan ma tayi ba, haka ruwan nan yadinga malalewa har ya sauka a jikin Yaya Khaleel ' shigar ruwa yaji a jikin sa yasa yayi sauri mik'ewa tsaye, "Kutma!! " Jin haka yasa ta juyo ta kalle shi a razane, "Fadwa jik'ani kikayi? Lallai jikin ki zai gaya maki." "Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri ' bada sani na nayi haka ba." Matsowa yayi kusa da ita ya d'aga hannu zai sharara mata mari kenan Abba ya dakatar dashi da cewa, "Karka kuskura , Koda wasa kada kasake ka mareta ' Au ashe muguntar taka tana nan ko? " Abba ya fad'i haka yana k'arasowa wajen, Yaya Khaleel sauke hannun shi yayi Sannan ya watsa mata harara ' tare da cewa , "zamu had'u ai. " Bayan Abba ya sami waje ya zauna ne ' yace, "Me kika masa? " "Abba Ruwane ya zuba a jikin shi by mistake ' shine yace... " Bata k'arasa ba ta sunkuyar da kai, "Kyaleshi ' karki damu dashi, Yanzu dai zo ki zubamun abinci na ' don yau na wuni ina aiki. " To kawai ta ce sannan ta zuba abincin a plate ta aje mashi ' Tukunna tayi mashi sallama don bacci takeji, har ta kama Hanya zata wuce Yaya Khaleel ya ce. "Ki biyoni da trolley d'ina d'akina" Babu musu taja trolley d'in nashi tabishi dashi ' tafiya yake ta na binshi abaya, ganin sun wuce d'akin Yaya Farook ne yasata mamaki.

Chapter 4 of 20