karki damu Insha Allah zata farfad'o, bari in shiga wanka kafin su Yaya su shigo. "
Kai kawai Umma ta d'aga mata sannan ta tashi zata wuce sai kuma ta tsaya,
"Umma ina Abba ne?"
"Abban ku yana masallaci,"
To tace sannan ta wuce d'akin su.
*Around* *7:00pm*
Abba da su Yaya Farook suka shigo gida cikin nutsuwa, bayan sun shiga ciki ne Yaya Farook yace.
"Abba i think ' ni kawai zan koma hospital d'in yanzu, don jiki na yabani Fadwa ta farfad'o kuma baza taji dad'i ba idan ta farka taga babu kowa."
A zuciyar Yaya Khaleel kuwa cewa yayi,
"Mtsww Don Allah ji Yaya kuma! To dama wane dad'i kuma akeso taji itada take a gadon Hospital? "
"To shikenan Farook , maganarka haka take ' to amma ka ci abinci kuwa?"
Cewar Abba,
"A'a Abba wallahi banajin yunwa.
"Haba Yaya yaza ai kace bakajin yunwa? Don Allah ka tsaya kaci abinci and beside likitocin nan suna iyakar yinsu ' am sure Fadwa zata sami sauk,"
Cewar Yaya Farook,
Yaya Farook kallon shi kawai yayi tare da cewa,
"Bani key d'in mota!"
sannan ya juya ya wuce ' ba tare da yace masa komai ba.
kai tsaye ya wuce hospital d'in, direct ya nufi d'akin da Fadwa take ' koda ya shiga a zaune ya iske ta hawaye kawai ke zubo mata a fuska, da sauri ya k'arasa kusa da ita tare da tallabo fuskarta gami da share mata hawaye.
"Ko kad'an bana son inga hawaye na fita daga idonki,
A fusace ta d'ago rinan nun idanun ta ' ta kalleshi cikin b'acin rai,
"Hawaye?!! Hawaye fa kace!"
Ya d'aga mata kai alaman Eh,
"Ko dayake a fatar bakin ka kawai ya tsaya ' saboda nasan duk duniya babu wanda ya kaika son ganin hawaye na!!..."
Ta k'arashe maganar cikin matsanan cin kuka,
"Subhanallah Fadwa meyasa zaki jefeni da wad'an nan kalaman? Nasani wannan hukuncin da su Abba suka yanke ' dole zai yi mana ciwo amma we just have to accept the fact, dole zamu yarda da k'addara kumm..."
Tun kafin ya gama rufe baki ' ta d'aga mashi hannu alaman dakatar wa sannan ta goge hawayen ta,
"K'addara? K'addara fa kace! Wannan ai ba ita ake kira da k'addara ba Yaya Farook, Yaya Farook ko a yanzu zaka iya warware komai ' kafad'a masu cewa ni kakeso ' ka fad'a masu cewa akwai soyayya tsakanin mu ple...."
Ba ta kaiga k'arasa maganar ta ba ya daka mata tsawa da cewa,
"Me kike nufi!!? Kina nufin inkoma ince masu zab'inda sukayi baiyi ba ko kuwa mene?
"Eh abinda nikeso kenan kayi ' idan kuma ba haka ba to Wallahi zan bijire , ba don komai ba sai saboda kwata kwata babu soyayya a tsakanin mu da Yaya Khaleel ' baka ganin yadda yake treating d'ina? Yaya Farook wallahi inasonka."
"Wai meyasa bazaki fahimci abinda nikeson fad'a miki bane? Fadwa inason ki amma haka nan zan hak'ura dake, hakuri kawai ya dace muyi baki d'aya."
Ya na gama fad'in haka ya juya zai fita tayi saurin rik'e mishi hannu,
"Please Yaya Farook ' meyasa baka sona? Amma shikenan naji kuma na hak'ura zan aure shi, amma Yaya Khaleel bazai tab'a jin dad'in aure ba wallahi. "
jin haka yasa shi juyowa ya kalleta cike da b'acin rai sannan ya fizge hannun shi ya fice, ya na fita suka had'e da su Umma a bakin k'ofar Ward d'in.
"Ina kuma zaka je?
Cewar Umma,
Komawa ciki yayi sannan suka bi bayanshi, Umma na shiga taje ta zauna gefen Fadwa cike da fara'a.
"Ina wuni Umma? "
"Lafiya kalau Fadwa yaya jikin naki?"
"Umma kada ku damu naji sauk'i ina Abba?
Murmushi Umma tayi ' zatayi magana Ilham ta tari numfashin ta da cewa,
"Haba wa ai Abba ya ce yayi fushi dake ' shiyasa ma baizo ba,"
"lalala Umma dagaske ne?"
Cewar Fadwa,
"A'a k'arya take miki Abban ku yana cen tare da Doctor suna magana."
To kawai Fadwa ta ce sannan ta ballawa Ilham harara, Yaya Khaleel kuwa yana gefe a tsaye rik'e da waya a hannun.
Abba ya shigo tare da doctor ' ya cirewa Fadwa canulla d'in hannun ta sannan aka sallame su sannan suka koma gida.
*** *** *** *** **
*Around* *8:00pm*
Suka koma gida ' basu wani zauna yin hira ba kowa ya tafi d'akin shi domin yin bacci.
*_babu_* *_yawa_* *_kuyi_* *_hak'uri_* *_da_* *_wannan_*
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*33-34* *pages*馃尮
Bayan shigarsu Fadwa d'aki ne Ilham ta sanya key a d'akin ta kulle tare da ajiyan zuciya sannan taje ta sami waje ta zauna a gefen gado, Fadwa kuwa tana tsaye tana k'ok'arin sanya rigar bacci,
"Alhamdulillah Fadwa watan mu ya tsaya! "
Fadwa tsayawa tayi cak ita bata sanya rigar ba ' ita kuma ba cire ba,
"Wane irin wata ne kuma ya tsaya?
"Eh mana kinga yanzu ' ni anbani damar in tsaya da duk wanda nikeso, ke kuma an zab'a miki Yaya Khaleel ' kuma wallahi Fadwa ba k'aramin dacewa kukayi ba."
Ya tsine baki tayi sannan ta sanya rigar baccin ta ' ba tare da tace mata komai ba ta haye gado ta kwanta gami da jan bargo,
"Ha'a Fadwa meye haka? Magana fa ni keyi kika shareni! Wai ma tsaya ko dai bakyason Yaya Khaleel ne? "
Nan take Fadwa ta matso murmushi a fuskarta ' tare da tashi zaune,
"Haba Ilham wace irin magana ce wannan? Aini su Umma sun gama min komai ' to donme zance banason Yaya Khaleel? "
Murmushi Ilham tayi har saida fararen hak'oran ta biyu suka bayya,
"Naji dad'in jin haka Fadwa,"
Kwanta wa sukayi a tare ' sukayi shuru nad'an lokaci sannan Fadwa tayi zambur ta tashi zaune,
"Ilham?"
Ilham ta amsa da "Na'am,"
"Ilham amma sai nake ganin kamar zansha wuya a hannun Yaya Khaleel ' saboda baya sona kuma kinga bawani sabawa mukayi dashi ba."
Ilham dafata tayi tare da cewa,
"Hmm Fadwa kenan ' karki bani kunya mana kamar ba'a *BABBAN* *GIDA* kike ba? Ai wannan lokacinki ne da zakiyi amfani da damarki ' ki tsigilgila mashi rashin kunya dole yayi hak'uri saboda ke zai aura! Kuma dole ki rik'ayin abubuwan da zai rik'a jawo hankalin shi gareki although dama ya riga yace ke bakida kunya ' so saiki nuna mishi haka."
Sakin baki tayi ta na kallon yadda Ilham keta zuba zance,
"Niko Ilham wai ina kikasan wad'an nan abubuwan?"
Cewar Fadwa,
"To ki zauna nan ' don wallahi Yaya Khaleel yana da y'an mata da yawa saikinyi dagaske am telling you this! "
Murmushi kawai Fadwa tayi mata sannan suka koma suka kwanta ' A zuciyar ta tace,
"Nifa Ilham ba son Yaya Khaleel nakeyi ba, amma da wannan shawarar taki zanyi amfani in nunawa Yaya Farook kuskuren daya tafka."
Tana gama ayyana haka a zuciyar ta ne bacci yayi awon gaba da ita.
*** *** *** *** ***
*Around* *6:30am*
Alam d'in wayar Ilham ya fara k'ara haka yasa Fadwa tashi a firgice,
"Haba don Allah wane irin abu ne wannan? Kinsama mutane Alam kamar wasu yara!"
Cikin magagin bacci Ilham ta tashi ' tare da yin mik'a,
"Ke dai kika sani!! "
Cewar Ilham,
Ilham shigewa Bathroom tayi tayi wankan ta tare dayin Alwala ' sannan ta fito ta iske Fadwa sai sharar bacci takeyi,
"Oh Fadwa wato bacci kika koma ko? To tashi zakiyi wallahi yanzun nan!"
K'ara sawa wajen gadon tayi ta yaye blanket d'in sannan tahau bubbuga ta,
"Ke dalla ki tashi ' kinsan ko k'arfe nawa yanzu,"
Ba arzik'i Fadwa ta tashi cikin b'acin rai sannan ta shige bathroom itama. Ko da ta gama wanka ta fito ' ta iske Ilham harta idar da Salla, sannan itama tayi Sallar a gurguje suka shirya don ganin kada lokaci ya k'ure masu.
*Around* *7:00am*
Suka gama kammala had'a breakfast, Fadwa ta shirya komai a saman dinning table ' sannan suka zauna ita da Ilham, haka yayi daidai da isowar Yaya Farook da Yaya Khaleel cikin parlon ' hakan yasa Ilham kashewa Fadwa ido d'aya (Wink馃槈) alaman tayi wani abu. Bayan sun zauna a wajen ne Fadwa tayi wuff ta mik'e tsaye gami da cewa,
"Let me serve! "
Zubawa ko wanen su tea tayi a cikin cup ' suka fara sha, sannan ta dafa hannun Yaya Khaleel tare da cewa,
"Dear? A k'wai wani abunda kake buk'ata ne bayan wannan?"
Yaya Khaleel zaro ido yayi ' cike da mamaki tare da sakin baki ' hakan yasa Yaya Farook sark'ewa,
"A'a babu abinda nike buk'ata!"
"Oh i see ' ai kamar Yaya Farook ne ma ke buk'atar ruwa a kusa dashi!"
Cewar Fadwa,
Nan take ta zuba mashi ruwa a cup ta mik'a mashi tare da cewa,
"Sannu,"
Ko kallon ta beyi ba ya karb'a ruwan tare da balla mata harara, sannan ta koma ta zauna. Bayan sun gama karya wane Umma da Abba suka shigo parlon ' tukunna su kuma su Ilham suka tashi da niyya wuce wa School,
"Har kun gama karya wanne?"
Inji Umma,
zukunna wa sukayi ' dukkansu suka gaishe su sannan suka mik'e tsaye,
"Umma zamu tafi School yanzu."
Cewar Fadwa,
"To Allah ya kaiku lafiya ' ya kuma baku sa'a!"
Ameen suka ce sannan suka nufi d'aki domin d'aukar handbag d'in su. Bayan shigarsu d'aki ne Ilham ta ce,
"Fadwa ki cewa Yaya Khaleel shi zai kaiki School yau!"
Zaro ido tayi ' ta tsaya tana k'arewa Ilham kallo cikin tsoro,
"kinsan me kike fad'i kuwa?"
Ta d'aga mata kai alaman Eh ' sannan Fadwa ta girgiza mata kai gami da cewa,
"A'a wallahi bakisan me kike fad'iba, so kike ranmu ya b'aci da sassafen nan ko Ilham?"
"Ko kad'an kawai k'ok'ari nike inga ya fara sabawa dake, kafin Aure!"
Girgiza mata kai kawai tayi ' sannan ta jawo handbag d'inta zata fita ' Ilham tayi saurin rik'eta,
"Please ki gwada don Allah, "
To kawai ta ce sannan ta fice itama ta bi bayanta, saida suka kai tsakiyar parlor sannan Fadwa ta tsaya.
"Ammm... Mhm Yaya Khaleel please zaka d'an kaimu School yau?"
Cikin bacin rai ya juyo ya kalleta ' sannan ya kalli su Abba dake karyawa,
"What!!?"
Ya fad'a a tsawa ce ' hakan yasa k'afafun ta suka fara rawa, Ilham tayi saurin tab'ota tare da cewa,
"dalla ki dake!"
Fadwa kallon Yaya Farook tayi ' ta ga idon shi nakan wayar shi, haka yasa ta saki murmushi sannan ta maida kallon ta kan Yaya Khaleel ' wanda ya had'e rai kai kace mutuwar shi ya gani,
"Yes! Cewa nayi kad'an zo ka kaini School, "
"Driver d'in aikin uban me yakeyi?"
Sunkuyar da kanta tayi ' cikin shagwab'a tace,
"Nidai kai nikeso ka kaimu yau ' please Swe..."
Yaya Farook ne yayi gyarar murya ' tukunna Yaya Khaleel ya ce ,
"To shikenan muje!"
Ya fad'a cikin sanyin jiki ' sannan suka fita ya bi bayansu.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*35-36* *pages*馃尮
Bayan fitarsu ne daidai bakin k'ofa ya finciko ta cikin zafin nama ' Ganin haka yasa Ilham yin sand'o ta shige mota,
"Don't you think kin cika zak'ewa da yawa? Ko cemiki akai ina..."
Nan yayi shuru ba tare da ya k'arasa ba ' ita kuwa tsoro ya gama cika idon ta ' Nan tayi k'arfin hali ta fizge hannunta tare da cewa,
"Yes ainasan cewa baka so na ' haka zalika nima bana sonka don baka tab'a shiga raina ba Yaya Khaleel..."
Ta na rufe baki ya d'auke ta da mari tasss ' nan ta dafe wajen wasu zafafan hawaye ke zuba mata a fuska,
"Kamar kin manta wanene a gaban ki ko?! To bara in tuna miki ' kina magana da Khaleel ne, bana d'aukar raini Fadwa harni zaki kalla kice bakya sona?"
Nan ya ja hannun ta zuwa gaban mota ' ya bude seat d'in gaba cikin b'acin rai ta shiga sannan ya rufe bamm, ya shiga ya ja motar.
Fadwa kuwa tunda ta shiga babu abinda take in banda kuka ' kukan ne ya ishe shi yasa shiyin packing a gefen titi tare da cewa,
"Zaki min shuru ko saina k'ara miki? Idan kuma bazaki yi shurun ba to ki fitarmun a mota,"
Aiba arzik'i tayi shuru don tasan halin shi babu abinda ba zai iya ba. Bayan sun kai School d'in ne yayi packing Ilham ta fita ' Fadwa bud'e mota tayi zata fita ya tsaida ita, sai da yayi shuru nad'an lokaci sannan ya ce,
"idan kuma kika sake ' kika fad'awa Umma ko Abba cewa na dakeki ' to wanda zan miki sai yafi haka!,"
Sunkuyar da kai tayi ta had'e rai ba tare da tace Uffan ba,
"And ' anjima ni zan dawo na d'auke ku,"
Yayi maganar cikin sanyin rai ' ya na kallon ta,
"A'a ka barshi zan kira driver sai yazo ya d'auke mu,
"What!! Ina magana kina magana? To idan na dawo d'aukar ku ' kice bazaki shiga ba! Fita ki bani waje, "
Da sauri ta fita tare da rufe mashi k'ofa sannan ya ja motar shi ya koma gida. Ko da ya koma gida ' Umma kawai ya iske a parlor, Abba da Yaya Farook duk sun wuce Office ' samun waje yayi ya zauna,
"Ina kaje ne?"
Cewar Umma,
"Umma na kai su Ilham School ne,"
Umma murmushi tayi sannan ta cigaba da kallon ta ' suna cikin hakan ne wayar shi tayi k'ara Alaman kira, cikin hanzari ya d'auka.
"Ok to gani nan zuwa ' just give me some minutes Ok?"
Abunda ya fad'a kenan sannan ya kashe wayar gami da mik'ewa tsaye,
"Umma zan fita ' amma bazan dad'e ba zan dawo!"
To kawai Umma ta ce sannan Yaya Khaleel fita , wajen motar shi yayi ' ya bud'e ya shiga sannan mai gadi ya bud'e gate tukunna ya fita.
kai tsaye ya wuce wajen wani k'aya taccen restaurant, sannan ya d'aga wayar shi yayi kira tukunna ya k'arasa ciki.
Wata kyakkyawar mace ce zaune a kujera ' daka ganta kasan cewa kud'i sun zauna mata kuma ba y'ar k'ana nan mutane bace. Ganin shi yasa tayi saurin mik'ewa tsaye ta tare shi cikin murna ta rungume shi,
"i missed you so much ' my Love, "
Ta fad'a tare da k'ank'ame shi sosai,
"I missed you more baby,"
Rabata yayi da jikin shi ' sannan suka koma suka zauna , "jiya na sauka Nigeria ' na biyo kane akan wannan maganar,"
Nan ya had'e rai tare da cewa , "wace magana kenan?"
"Ha'a don't tell me cewa dawo warka Nigeria ' harka manta maganar dake tsakanin mu !"
"To basai ki tuna min ba! Ko aibune don kin tunamin?"
Sunkuyar da kai tayi cikin takaici ' tukunna ta d'ago idanun ta ta kalle shi,
"Khaleel ' maganar Auren da ke tsakanin mu mana, ka fad'amun cewa dazarar na gama school na dawo gida zaka turo!"
Shuru yayi nad'an lokaci sannan yayi gyaran murya,
"Lubna, ba zan Aure ki ba!"
Nan take gabanta ya fad'a, cikin tashin hankali ta mik'e tsaye,
"What? Me kake nufi? Bayan ka riga ' ka gama lalata mun rayuwa ta sannan ka ce bazaka Aure ne niba, impossible wallahi ba ka isa ba Khaleel..."
komawa tayi ta zauna ' cikin b'acin rai take kallon shi,
"Baby ba laifina bane ' su Umma ne zasu Aura mun wacce bana So, amma kema kin san inason ki "
"Kar kayimun wani dad'in baki Khaleel , kuma ka sani bazaka tab'a samun kwanciyar hankali ba inhar baka Aure ni ba."
Hannu yasa ya tallabo fuskarta,
"Haba Baby! Ki kwantar da hankalin ki, kinga wannan Auren da zanyi ' zanyi shine kawai don faran'tawa Umma da Abba, Amma i can assure you that bayan na Aureta da wata d'aya ke kuma zan Aure ki."
Murmushi tayi har saida dimples d'inta suka fito sannan ta ce,
"Da gaske kake?"
"Kwarai kuwa baby na!"
Kallon wristwatch d'in hannun shi yayi yaga *1:56pm* ,ya tuna da zaije d'auko su Fadwa daga School sannan ya maida kallon shi akan Lubna.
"Lubna zakiyi mun rakiya ' zuwa wani waje?"
Kai ta d'aga mashi sannan suka tashi ' suka bar wajen, wajen mota suka nufa ' ta zagaya ta bud'e ta shiga tukunna shima ya shiga.
Kai tsaye suka nufi School d'in , bayan isar shi cikin makarantar ne *2:00pm* ya cika daidai, Nan Fadwa da Ilham suka fito ' Ilham ce ta fara hango Yaya Khaleel tare da wata,
"Ha'a to wacece ita?"
Ta fad'a cike da mamaki, haka yasa Fadwa saurin tambayarta.
"Ita wa?
Ilham nuni tayi mata da yatsa ' sanin Fadwa ta fahimci abunda take nufi,
"Kin gani ko? Daman na fad'a miki sai kinyi da gaske!"
Girgiza kai kawai tayi sannan suka k'arasa wajen motar, Ilham sauri tayi ta shige mota ' nan Yaya Khaleel ya tsaida Fadwa,
"Baby , wannan itace Fadwa ' wacce Abba da Umma suka zab'amin don na aura, "
Nan Lubna ta tsaya ta na k'arewa Fadwa kallo, tamkar zata had'iye ta.
"Gashi kamar bata iya gaisuwa ba ma!"
Fadwa girgiza kai kawai tayi gami dayin Murmushi,
"Sannu!"
Abinda ta ce kenan ta shige mota ' cike da takaici a zuciyar ta, nan shima Yaya Khaleel yai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 20