An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[5/23, 2:49 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
馃尮GODIYA馃尮
Dukkan Godiya Da Yabo Sun Tabbata Ga Ubangiji Mallakin Sammai Da Kassai, Wanda Ya Tsaida Ita Ya Kuma Shinfidata Ba Tare da Wani Majingi Ko Taimakon Wani Abin Halitta Ba. Tsira da Amincinsa Su Tabbata Ga Annabin Karshen Zamani Cikamakin Annabawa, Wanda Haskensa Da Kamshinsa Basa Gushe wa Daga Zuciyar Wanda Yafi Kowa Yi Masa Salati.
馃尮SADAUKARWA馃尮
Na Sadaukar Da Wannan Littafin Ga Marigayi Muhammad Abdulmumin Suraj Da Marigayi Lawal(Na Goggo )Allah Yaji Kansu Da Rahmarsa Ya Haskaka Makwancin su, Allah Ya Bamu Guzurin Ishesu Cikin Ni'imarsa Amin-Amin.
馃尮IYA YENA馃尮
Iyayena Alhaji Idris Musa Alhasan Da Hajiya Amina Ango Abdullahi, Allah Ubangiji Ya Biya Muku Dukkan Buka tunku Ya Kuma Yi Muku Sakayya Da Gidan Aljanna Kan Irin Tarbiyyar Da Kuka Bani Na Gode Kwarai, Allah Ya Kara Lafiya Da Tsawon Rai Amin Ya Allah.
馃尮KANNAI NA馃尮
-Hafsat Idris
-Alhassan Idris
-Fatima Idris
-Sa'adatu Idris
馃尮Allah ya bar Zumunci Yan Uwana.馃尮
-Aunty Bara'atu
-Aunty Mahadiyya
-Aunty Hafsat (Ummi)
-Aunty Khadija (Yarinya)
-Aunty Fatima (Gaje )
馃尮KAWAYEN ASALI馃尮
-Asiya Muhammad (Reality )
-Rabeeat Idris Baba (Slexy )
-Fatima Ango Abdullahi (Queenart )
-Zainab Abubukar (Sparkle)
-Zainab Ibrahim.
馃尮BAN MANTA DAKU BA馃尮
-MISS XOXO
-MELODY
-CUTE ZARAH
-ZAHRA BUKAR
-ILILEE
-MR SMILE
-RAHEEM
-ASY KHALEEL
-MAMAN USY
-SADNAF
-ANKA
-.........AND THE REST....
1-2page馃尮
Da Gudu Fadwa ta biyo Ta tana Fad'in,
"Allah ilham ki bani Waya ta bana so.
Fitowar Umma Keda wuya ilham taje bayan Umma ta Boye ' Umma ta ce,
"Ilham? Fadwa kika tsokana koh?
"Eh Umma duba fa Chatting takeyi da Wani Saurayin ta.
Ilham Zata Nunawa Umma Wayar kenan ' Fadwa tayi Sauri ta Fizge Wayar daga Hannun ta.
"Aunty Karya Ilham takeyi miki, ni banda Wani Saurayi.
Umma zatayi magana kenan Yaya Farook ya shigo parlon cikin bacin Rai ' Fadwa Da Ilham suna ganin shi suka sunkuyar da kai cike da Nutsuwa.
"Wannan wane irin iskancin banza ne ' bance maku idan ina bacci banason surutu ba?
A tare suka Amsa mashi da cewa,
"Ka ce!!!
Yaya Farook kallon wayar da ke hannun Fadwa yayi,
"Ke kuma ban wayar Nan ' nayi seezing dinta,
Nan Hawaye suka cika idon Fadwa jikin ta na rawa Ta mika mashi Wayar,
"Yaya Farook please am....
Tun Kafin ta Karasa fada ya daka mata tsawa da cewa,
"Yimin Shuru.
Yaya Farook Ansan Wayar yayi sannan ya juya ya Wuce Dakin Shi.
Umma Koma wa tayi ta Zauna ba tare da ta saka masu baki a Maganar su ba,
"To ai saiku dawo ku zauna tunda ya wuce.
Cikin Sauri suka dawo suka zauna ' Fadwa kuwa idanu cike Da Hawaye.
"Umma Don Allah kitayani bawa Yaya Farook Hakuri ' ya dawomin da Waya ta.
"A'a babu ruwa na a maganar ku, Aikune dun bakwajin Magana.
Fadwa maida kallon ta tayi ga Ilham wacce itama jikin ta dar dar yake saboda tsoro.
"Ai duk Ke kikaja gashi nan ya Anshemun waya.
Harara Ilham ta watsawa Fadwa,
"Ke inda kinsan tsoron da ke jikina da bakimin wannan Maganar Banxan ba.
Shuru sukayi nad'an lokaci sannan Fadwa tayi Zanbur ta mike tsaye tare da dafe kanta,
"Nashiga uku ilham ' na manta ban sanyawa wayata security ba, gashi Yaya Farook zai iya shiga wani wajen dabam.
Umma tashi tayi tare da cewa, "Ni yaran nan kuna neman kusamin ciwon kai wallahi ' bakin bazai ta'bayin shuru ba.
Ta na gama fad'in haka ta wuce sashen ta.
"Nifa Fadwa duk fa laifinki ne ' ke ce da kike yawon fito da wayar ki parlor gashi nan tsautsayi ya Afka mata.
Cewar ilham.
Fadwa koma wa tayi ta zauna tare da zuba tagumi,
"Don dai Abba yayi tafiya ne Amma dashi zai kwatarmin wayata.
Ilham najin haka tayi saurin toshewa Fadwa baki,
"Ke wai bakisan duk Abinda muke fada Anaji ba? To nidai karki jamun duka ' kinsan halin Yaya Farook sarai don ya jibge mu bawani abu bane Awajen shi.
"To yaji din mana ni ina ruwa na?
Cewar Fadwa.
Ilham mikewa tayi tsaye tare da yiwa Fadwa kallon Naman kaza.
"Lallai kuwa jiki zaiyi tsami ' ni kinga tafiyata... 馃毝
Ilham juyawa tayi a guje ta wuce dakinsu ' nan wajen Tabar Fadwa rai abace.
Wacece Fadwa, 'yace Ga Alhaji Aminu Muktar ' kuma yace Ga hajiya Amina Shehu, Allah yayi masu rasuwa ne sakamakon Goborar da suka ' gaba daya suka kone. Fadwa ce kadai ta tsira, A lokacin Fadwa Tana da shekara Goma sha tara 19 ' Hakan yasa Alhaji Sulaiman wato Aminin Mahaifin Fadwa, Ya amince shi zai rike ta da Amana kuma zai saka ta cikin Y'ay'an shi ' tamkar shine Ya haifeta.
Alhaji Sulaiman Mahaifine awajen Yaya Farook da Yaya Khaleel da kuma Ilham, haka zalika 'ya'yane Awajen Hajia Maimuna, wacce suke kira da Umma.
馃憚馃憚馃憚馃槣
Dedicated To My Fan's.
漏ONLINE HAUSA WRITERS.
[5/23, 2:49 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
3-4page馃尮
Fadwa na Zaune ' sai ga Yaya Farook ya shigo parlon, Ta na ganin shi ta mike tsaye.
"Yaya Farook kayi hakuri don Allah.
Ko kallon ta biyi ba ' ya Wuce. Ta na ganin ya fita ta nufi Dakin shi kai tsaye,
"Yanxu zan sami damar Daukar wayata ' kuma inyi mirsisi .
Tana gama Fadin haka ' ta hau yimashi bincike A dakin, gaba daya ta birkice dakin ' Fadwa ta du'ka zata bude Drower kenan taji magana kamar daga sama.
"Kinyi ajiya a wajen ne dazaki dauka?
Da sauri Fadwa ta dago kanta har tana Bige goshin ta ' Fargaba da tsoro ya hanata juyowa,
"zaki juyo ki kalle ni, ko sai kinji saukan duka? Cewar Yaya Farook.
馃槰 Nan Fadwa ta hauyin adduoi kala kala ' saboda tsabar tsoro, A hankali ta juyo ta kalle shi.
"Me kike nema a dakin?
"Yaya Farook ' Don Allah kayi hakur....
Tun kafin ta gama rufe baki ' ya dauke ta da mari tasss.... Nan take Fadwa ta Dafe kumatun ta tare da Dukawa kasa, cikin kuka. Cen bata ankara ba taji saukar Hauri a jikinta,
"Ahhhhgg!
Nan take ta fara Aman Wahala ' a galabaice,
"Zaki sake shigowa daki na ba tareda iznina ba? Zaki sake? Fadwa inbanda girgiza kai babu abinda takeyi Alaman A'a.
"Good! Tashi ki fice mun a daki kuma ki dauko Mopper ki goge aman da kikayi!!
A guje ta tashi ta fita ' cikin hanzari ta dauko Mopped ta goge Aman, Yaya Farook na kwance saman gadon shi yana kallon ta '
"idan kuma kingama ki dauko Perfume ki sa awajen ' don banason Karni yadame ni.
To kawai Fadwa ta ce sannan ta je ta dauko turare ta sanya ma wajen. Da sauri ta fice donma kada ya tsaida ita, kai tsaye ta wuce dakinsu ' Ta iske Ilham akwance ta nata sharar baccin ta, Fadwa zuwa tayi ta zauna a gefen gadon ta kafa wani sabon Kuka tamkar yanxu ne Yaya Farook ya mareta.
Kukan ta ne ya dami Ilham ' yasa ilham farkawa daga baccin da takeyi, Ganin Fadwa a cikin wani hali ne yasa tayi hanzarin gangarowa kusa da ita.
"Fadwa? Me yafaru?
Da sauri Fadwa ta share hawayenta '
"Babu komai Ilham ' kawai na tuna da Iyayena ne...
Ilham rungume Fadwa tayi cike da tausayi,
"ayya kiyi hakuri Fadwa ' kedai kirinka masu addua kawai, kuma duk abinda kikeso a Abbanmu na nan ko?
Kai Fadwa ta daga mata alaman Eh, Sannan Ilham ta lura da shedan yatsu a fuskar ta, Alamun mari.
"Subhanallah! Fadwa Waye ya mareki haka?
Cewar ilham.
Fadwa shuru tayi bata Ce mata komai ba, sannan Ilham ta ce.
"Hmm Kinje daukan wayar ki dakin Yaya Farook ko?
"Ilham na dauka yayi nisa ne sabida naga fitarshi, Amma ina shiga ya ritsani aciki.
"Aikin gani Allah yakara ' yanzu ai jikinki ya gaya maki, Kina abu kamar bakisan wanene Yaya Farook ba.
"ilham Yaufa tsawon Shekara Biyu kenan ' da zuwa na gidan nan Saidai inji Kuna labarin Wani Yaya Khaleel, wai waye shi.
Ajiyar zuciya Ilham tayi gami da Zuba ta gumi,
"Meyafaru naga kinyi ta gumi?
cewar Fadwa.
"hmm, Dole inyi Ta gumi domin kuwa Inhar Yaya Khaleel ya dawo ' to zaman parlor ma sai ya gagaremu.
馃槰Zaro ido Fadwa tayi cike da mamakin wannan Alamari,
"To wai wanne yafi zafi cikin su?
Cewar Fadwa.
Nan Ilham ta gyara zama tare da kama Hannun Fadwa,
"hmm Fadwa ai inhar Yaya Khaleel ya dawo to Yaya Farook dan kallo zai zama.
Wani ihu Fadwa ta Saki ' cike Da Zulumi,
"Ahhh馃檰 to yaushe zai zawo?
Cewar Fadwa.
Dariya Ilham ta yi cike da buga kafa,
"What are you eating nabaka is falling dawn?' abba ya ce mun Next month Yaya khaleel zai dawo, Kuma zai gama School din shi gaba daya.
馃槰馃槰馃槰馃槰
Ilham nagama fadin haka , Fadwa ta ruga da gudu ta fada Toilet...
Sai da Tayi 5 minutes sannan ta fito ' tana fitowa suka hada ido Da ilham, Babu abinda ilham keyi inba dariya ba.
"Ke ni bazan biye maki ba ' duk kinbi kin gama tsorata mun ciki, Ni yanzu ma bacci xan.
Fadwa na gama fadan haka ' ta haye gado ta fara bacci, ita kuwa Ilham ta Dauki wayae ta ta hau chat.
*AROUND* *7pm*
Ilham Da Umma suka fito parlor Domin suyi Dinner dinsu, Shima Yaya Farook Fitowa yayi daga dakin shi yaje Yayi joining dinsu a Dinning table ' bayan Sunfara cin Abinci ne Umma ta ankara bata ga Fadwa a wajen ba,
"ilham? Ina Fadwa take ne?
"Umma tana daki a kwance ' wai zazzabi take ji,
Yaya Farook ajiye spoon dinda ke hannun shi ' tare da cewa,
"Zazzabi? And she is too big tazo ta fada abata magani ko? Umma bara inje induba ta,
Kai Umma ta daga mashi alaman Tor, sannan Yaya Farook ya tashi ya nufi dakinsu Ilham.
Koda ya shiga a Dukunkune ya iske ta acikin Blanket ' Ta na kuka, Yaya Farook karasawa yayi ciki ya zauna a gefen gadon tare da yaye Blanket din. Ganin yadda take rawan sanyine tausayin ta yakamashi,
"Bakida Lafiya meyasa Bazaki fada ba?
Fadwa shuru tayi bata ce komai ba,
"Ki tashi ki shirya inkaiki Hospital yanzun nan.
Har Yaya Farook ya mike tsaye da niyyar bata waje, yaji ta riko hannun shi.
"Yaya Farook don Allah idan Munje kace Masu ' karsumin Allura please!!!
Tausayin ta yasa ke shiganshi ' yayi sauri ya cire hannun ta daga Jikin shi,
"Is Ok! Ki dai tashi ki shirya ' kafin kuma Raina ya baci yanzun nan.
Ya na Gama Fadin haka ya juya ya fita cikin Sauri, Ya wuce dakin shin domin ya dauko key din mota.
馃憚馃憚馃憚馃槣
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
[5/23, 2:49 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
5-6page馃尮
Har saida Yaya Farook Yaje ya dauko key din ya dawo parlor, ya zauna zaman jiran Fadwa.
sai da ta Bata Minti 30,sanan Ta fito Parlon.
"Yaya Farook gani!
Cewar Fadwa.
Tashi tsaye yayi tare da saka hannun shi cikin aljihu ' gami da yimata Wani mugun kallo,
"Na dauka ko ' kinji sauki ne ai.
"Don Allah nidai Farook ka kaimin yarinya aduba ta.
Cewar Umma dake zaune a dinning table ta na kallon shi.
Yaya Farook fitane yayi Fadwa na biye dashi a baya har suka isa wajen motan, Ya fara shiga sannan itama tashiga cikin hanzari mai gadi ya bude gate din ' tukunna Yaya Farook Yaja motar.
Ba tare Da wani bata lokaci ba suka isa cikin Hospital yayi packing A gefe sannan suka fito, ganin Fadwa ba ta sauri yasa ya kama hannun ta ' Haka ya dunga janta har suka kai Office din Doctor din. Sannan likitan ya duba ta Ya rubuta mata magun gunan da za'a siya, Cikin jin Dadin Fadwa ta Ansa takaddar magungu nan don ganin babu allura ko daya aciki.
Har ta mike tsaye Likitan ya tsaida ita da cewa,
"Ki tsaya Akwai Allurar da za'ayi yanzu guda biyu, Data amai da kuma Wanda zata rage maki zafin jiki.
Ta najin haka ta juyo ta kalli Yaya Farook, Suka hada ido ' Ganin Ya hade rai ne yasa ta sunkuyar da kanta ba tare da tace komai.
"Idan kin shirya sai ki juyo.
Cewar doctor,
Jin haka Yasa ta juya ta mika mashi baya kamar da gaske ' Daya matso sai ta matsa haka suka dungayi da Dr din, Abin ne yabawa Yaya Farook haushi ' A fusace ya mike tare da finciko Fadwa ' ya rungumeta sosai ta yadda bazata iya motsi ba,
"Doctor yi mata Allurar ' don sauri nakeyi.
Cewar Yaya Farook,
Fadwa bata ankara ba taji shigar karfe ajikin ta ' jin haka yasa tasaki ihu cike da kankame Yaya Farook,
"Wayyo Allah Yaya Farook!!!
"Shhhh, kiyi hakuri saura guda daya kinji ko?
Cewar Yaya Farook.
Fadwa ta naji tana gani aka sake tsira mata wani allurar, Sai da aka gama sannan Yaya Farook ya zaunar da ita.
"Yanzu Zaku iya tafiya ' but saika dan rike ta saboda akwai Allurar da akayi mai sanya jiri.
Ok kawai Yaya Farook ya ce ' sannan Ya rike hannun Fadwa suka fita daga wajen ' daker Fadwa Take jan kafar ta Yaya Farook ya lura da haka,
"Zaki daga kafa kimin sauri Ko saina dauke ki tukunna?
Dago kai tayi ta kalleshi a gala baice ,
"Yaya Farook bazan iya bane!
Bata gama rufe baki ba ' taji ya dauketa cakk tamkar wata jaririya, Fadwa Kara lafewa tayi a jikin shi don kuwa batada wani karfi a jikinta.
Haka ya ratsa cikin Hospital din da Fadwa a hannun shi ' mutane kuwa sai kallon shi sukeyi, kai tsaye ya nufi wajen Motar shi yasa key ya bude sannan ya zagaya ya saka Fadwa A seat din baya,
"Saura kuma ki 'ki kwanciya.
Abinda ya fada kenan sannan ya shiga mota yaja suka koma gida A cikin *30* *Minutes* .
Horn Yaya Farook ya yiwa Maigadi yazo ya bude ' tukunna ya karasa ciki. Packing yayi cikin hanzari ya fito gami da Jan hannun Fadwa,
"kokarta ki fito don Yanzu dai ' nima nagaji bazan iya Daukanki ba don nauyine dake!.
Jin haka yasa Fadwa taja jikin ta fito daga motar cikin sanyin jiki, har suka shiga cikin parlor ' A zaune suka Iske *Ilham* tana Danna waya, Ganin su Yaya Farook ne yasa tayi saurin sake wayar a riga.
"Ina Umma?
Cewar Yaya Farook.
"Tana Sashen ta,
"Tor ki kawowa Fadwa Dinner dinta yanzu taci a gaba na.
Cikin hanzari Ilham ta tashi ta nufi Kitchen,
"Ke kuma bazaki sami waje ki zauna bane kokuwa?
Cikin sanyin jiki ta zauna ' Gami da kallon kasa, don batamaso su hada Ido dashi.
Cikin dan kan kanin lokaci Ilham ta dawo da plate a hannun ta, Jellof rice ce a ciki sai naman kaza cinYa daya.
Fadwa ansan abincin tayi tare da toshe hanci '
"Aiko zaki amayar da Hanjin cikin kine ' saikin cinye abincin nan tass, bakina wani toshe hanci ba.
cewar Yaya Farook,
Tun da ta ansa abincin ' sai kollon shi takeyi, takasa sawa abaki. Ganin haka ne Yaya Farook Ya Ansa abincin daga Hannun ta tareda diban spoon daya,
"Oya Ansa ' dakaina zanba ki ' kinayin Amai kuma kiji saukan duka.
Ba musu Fadwa ta bude bakin ta Yasa ka mata Abincin ' daker ta iya haddiyewa. Ilham na tsaye a wajen Ta na kallon su ' Dukka dukka Spoon uku kawai Ta ci, ta fara Kakarin Amai ' Bata Ankara ba Taji saukan dundu tiim Abayan ta haka yayi Dai dai da Shigowar Umma Parlon,
"Subhanallah ' Wai kai Farook mekakeso ka maida kanka? Mugu ko mene?
Umma zuwa tayi taja hannun Fadwa, ta zauna a kusa da ita.
"Ya jikin naki?
Cewar Umma.
"Umma da sauki ' Amma Umma na koshi da abincin haka bacci zanyi.
Kai Umma ta daga mata tare da cewa,
"Shikenan, *Ilham* rike ta ku tafi daki.
Hannu *ilham* ta kamama *Fadwa* sannan suka tafi daki. Yaya Farook kallon wristwatch din hannun shi yayi yaga ' 9:20pm dare yayi sosai, sannan ya maida kallon shi wajen Umma.
"Umma sai da safe , ni zan kwanta.
"To Allah ya tashemu lafiya!
A tare suka tashi kowannen su ya wuce sashen shi. yaya Farook na shiga daki ya cenja kayan jikin shi zuwa na bacci, sannan ya Haye gado tare da ciro Wayar Fadwa a drower gado ' ya shiga Gallery ya fara kallon pictures dinta inbanda smilling babu abinda yakeyi, Cen sai ya cikaro da wani hoton da tayi itada wani namiji A School ta dafa shi. Nan fa Zuciyar shi tafara mai radadi da zafi,.
"Allah ya kaimu gobe saikin Fadamin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 20