Uban waye wannan.
Ya na gama fadin haka jefar da wayar a kasa, Daker ya iyayin bacci a wannan lokacin.
*Washe* *Gari* *Around* 4:00am
Yaya Farook Ya tashi ya wuce masallaci, Bayan ya dawo ne ya koma bacci.
Wajen 6:30 *Ilham* ta shi ' tashiga bathroom tayo Alwala sannan ta tada *Fadwa* daga bacci,
"Fadwa tashi muyi Sallah ' kada lokaci ya kure.
Cikin Magagin bacci ta tashi tafada Bathroom ita tayi Alwalan tukunna ta fito suka yi sallah, Bayan sun sallame ne Fadwa taga Ilham ta haye gado tare da Lullube wa.
"Ilham bazaki je School bane yau?
"Eh ' saboda bakida lafiya konaje school din bazaimun dadi ba.
Murmushi kawai tayi sannan ta mike tsaye tare da cire hijjab dinta,
"Allah yasa Yaya Farook ya gane cewa bazakije School ba.
Nan take ilham taji cikin ta ya murda,
"insha Allah haka bazata faruba.
Fadwa hayewa gado tayi ' bacci yayi awon gaba da ita. Basu suka tashi ba sai wajen 7:30, koda suka tashi Ilham kitchen ta shiga domin hada Breakfast. Yaya Farook ' farkawa yayi daga Bacci yashiga bathroom yayi wanka ya fito sannan ya shirya ' ya fita siyowa Fadwa Magungunan ta, Ba shiya dawo ba saida aka gama hada breakfast sannan ' Yana shigowa parlor ya iske su Umma a dinning suna shan tea.
Karasawa wajen yayi yasami waje ya zauna ' sannan ya gaida Umma cike da ladabi, Bayan ta amsa ne ya maida kallon shi akan Fadwa.
"Idan kingama breakfast din ' kizo Ki sameni a daki Kisha magana.
To kawai tace ' sannan Ya dauki tea dinshi ya sha, Yana gama wa ya mike tsaye gami da cewa.
"kiyi ki gama Kizo ina jiranki ' don akwai inda zanje,
"To wai Shi maganin dole saikai ne zaka bata?
Cewar Umma.
"Eh Umma ' Saboda Batason magani.
Yana fadin haka ya juya ya wuce dakin shi, Ita kuwa Fadwa Hankalin ta atashe yake ' Cikin Zulumi ta ajiye cup din da ke hannun Ta tashi ta bishi Dakin.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:49 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
7-8pages馃尮
Tana zuwa abaki kofa ta tsaya, Tayi Knocking gami da yin Sallama sannan ta shiga. A zaune ta ganshi ' yana dannan wayar shi,
"Yaya Farook gani!
dago kanshi yayi ya kalle ta ' tundaga sama har kasa sannan ya ce,
"Ni zan biyoki Nan wajen inbaki maganin ko?馃槧
cikin hanzari ta karasa cikin dakin, kusa dashi ta tsaya ' Yaya Farook ya aje wayar shi a gefe sannan ya duk'a inda ya jefar da Wayar Fadwa ya dauko, Gami da Tashi tsaye. Damko kunnen ta yayi Tare da murdabawa,
"Idan kika sake kikayi ihu ' Umma taji to abinda zanmiki sai yafi haka.
Kai Fadwa ta daga mashi alaman To, sannan Yaya Farook ya kunna wayar tare da Nuna mata Hoton da yagani.
"Uban waye wannan?
Ya fada yana sake murda kunnen,
"Yaya Farook Don Allah kayi hakuri ' Akwai zafi....
Cikin launi na kuka ta karashe maganar, Kunnen ta duk yayi jaaa duk da Kasan cewar Chocolate colour ce sai da yanuna.
"Oh akwai zafi kike cemun? Akwai zafi kike cemun?
Jikake timmm ' saukar duka a bayan ta, Cikin kuka tace.
"Yaya Farook, kayi hakuri ' wallahi zan fada maka.
Sakin kunnen yayi ' sannan ya sami waje ya zauna,
"daman wannan School friend dina ne ' Kuma ni banmasan shi na dafa ba .
Ta na fadin haka ya watso mata wata harara ' Cikin sauri ta,
"Wallahi Yaya Farook ' ka tambayi Ilham, babu wani abu tsakanina dashi.
Ta Na gama rufe baki ' Ya hada Wayar da bango, Ta fashe. 馃槺
"Idanma Akwai wani abu tsaka ninku, to na fasa Wayar ' Kuma bazaki sake yin Waya ba tunda abun naku iskanci zai koma, har itama Ilham din saina karba nata.
Fadwa babu abinda takeyi inba kuka ba ' Yaya Farook mikewa yayi ya dauko mata magun gunan, ya cire mata wanda zatasha yanxu Ya bata tare da bata cup din ruwa ta rike a hannu.
"In kinga dama kiyimin Amai a daki ' Jikin ki kuma yagaya maki.
Daker ta iya shanye Maganin ' Aje mashi Cup din tayi sannan ta juya da niyyar tafiya,
"ke!!! Na sallame kine?
Tsayawa tayi gami da Juyowa ta kalleshi ' Lemon sweet ya dauko daga cikin drower din shi, Ya bata.
"Bude kisa abaki yanzu, Saboda maganin da kikasha Akwaisu daci.
Babu musu tayi yadda yace '
"Oya Share hawayen ki '
Fadwa Share hawayen fuskarta tayi ' sannan ta kalleshi.
"And Yanzu kinsan me nakeso kiyi?
Ta girgiza mashi alaman A'a.
"Murmushi nakeso kiyi yanzu ' saiki wuce.
Don dole Fadwa ta matso murmushin karfin hali ' tayi mashi, Shima Murmushi yayi mata gami da cewa.
"Good gurl, kokefa ' yanxu kina fita ki wuce daki ki kwanta, ki huta.
Juyawa tayi ta wuce ba tare da tace mashi komai ba, Ta na fita taja tsaki.
"Mtsweee!!! Wai adaki mutum ahana shi kuka, Nidai Wallahi sai Allah yasaka min.
Dakin su ta shige ta kwanta kamar yadda ya Umarce ta'.
Yaya Farook Fitowa yayi ' ya nufi Parlor ya iske Ilham,
"Ke! Babu School ne yau?
Cewar Yaya Farook.
Nan take ta mike tsaye Ta tako har inda yake cikin Dingishin kafa,
"Yaya Farook, targade nayi dazun ' shiyasa.
Tayi maganar gami da nuna mashi kafar, Harara ya watsa mata sannan Ya fice. Ta ganin fitar shi ' takoma wajen Umma ta zauna,
"*Umma* don Allah cewa Yaya Farook ' ya rika shan Ruwan Buta, Seriously Umma ya cika fushi da yawa matar shi zatasha wuya.
"allah ko? to bari yazo sai infada mashi ' abinda kikace game dashi.
馃槰"No Umma kada ki fada babu ruwa na walkahi, Ban shirya shan duka ba.
Tashi ilham tayi zata wuce sai kuma ta dawo ta zauna tare da cewa,
"Yawwa *Umma* please ki bamu izni nida Fadwa mu fita.
"Ina kuma zaku je? Kinsan dai Fadwa batada lafiya koh?
"Haba Umma Shopping mu keso muje ' kibarmu kawai , ai ta sami lafiya.
Cewar Ilham,
Umma dogon Numfashi taja sannan ta ce,
"A'a Ilham kidai bari Yayanku ya dawo sai kuje,.
To kawai Ta ce sannan ta tashi ta wuce dakinsu ' Jikin sanyin jiki. A kwance Ilham ta iske Fadwa ' tukunna ta sami gefen gado ta zauna,
"Fadwa? Ki tashi kishirya muje ' Shopping.
Cewar Ilham,
Zanbur Fadwa ' tayi ta tashi zaune cike da fara'a.
"Wow! Aikam yanzu zan tashi inyi makeup, but yanaga jikinki a sanyaye?
"Umma ce tace wai saimun jira Yaya Farook,.
Ajiyar zuciya Fadwa tayi ' gami da mikewa tsaye,
"Shine duk zaki wani damu? Ki dai tashi ki shirya.
Ilham itama mikewa tayi ta shirya ' suka caba ado sannan suka nufi Parlor suka zauna zaman jiran Yaya Farook.
*Around* *2:30pm*
Yaya Farook Ya shigo gida ' Cikin sallama sanan suka amsa tare da Mikewa tsaye,
"Lafiya? Kuka mimmike tsaye kamar soldiers?
sunkuyar Da kansu sukayi ' sannan Umma dake gefe ta ce,
"Cewa sukayi ' wai zasuje Shopping shine nace subari kadawo, tukunna.
Watsa masu harara yayi ' ya wuce gami da cewa,
"Babu inda zakuje.
Kallon junan su sukayi ' sannan suka koma daki cikin kunkunai. zama sukayi gami dayin shuru nadan lokaci,
"Nidai gaskiya, xanje inroke shi ' don seriously inada abinda zan saya, Idan ba haka ba kuwa Gobe daga school zanje.
Harara Ilham ta watsawa Fadwa,
"I think you're very stubborn right? Fadwa kinfiso Kici dukan banza ko? Alright Allah yabaki Sa'a.
Ameen Ta ce tare da mikewa ' ta wuce Dakin Yaya Farook, Knocking tayi sannan ta shiga ciki ' A tsaye ta iske shi ya na kokarin cire rigar jikin shi, hakan yasa Tayi saurin juya mashi baya.
Hakan yasa Yaya Farook yin Murmushi cike da cije leben shi, ya daure fuska.
"Ke!!! Lafiya kika juyamin baYa? Dalla juyo ki fuskan ceni.
Cikin tsawa yayi maganar ' Haka yasa tayin hanzarin Juyowa ta Fuskance shi.
"Yaya Farook ' daman nazo ne Innemi izni awajenka.
"For What?
"Yaya Farook ' Please kadan barmu Mu tafi shopping nida Ilham i really want to buy something.
"No!!!,
Ya fada cikin tsawa!
Nan take Idon ta ya ciko da Kwalla,
"Yaya Farook, don Allah....
"banace A'a ba? Ko so kike sai nayi kwallo dake?
Juyawa tayi ta fita daga dakin cikin bacin rai' a zuciyar ta tace,
"Lallai kuwa gobe After School zanje'...
Ta na gama Ayyana hakan a ranta ' ta wuce parlor ta yi zamanta wajen Umma.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:49 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
*9-10* page馃尮
*Some* *minutes* *later*
Yaya Farook ' ya shigo cikin Parlor Ya iske Umma da Fadwa suna kallo,
"Fadwa Kiramin Ilham.
Jin maganar tayi kamar daga sama' don batasa da shigowar shi parlon. Cikin hanzari ta tashi ta kira Ilham na dan wani lokaci, sannan suka dawo parlon tare.
"Yaya Farook gani!
"Indomie zaki dafamin ' yanzun nan, kuma *30Minutes* na baki.
Babu musu ko wani alaman damuwa a fuskar ta ' ta fada kitchen, A cikin wannan *30minutes* ta gama ' ta zuba a plate sannan ta kai mashi Parlor.
"Yaya, Gashi nan.
Ansa yayi ya fara ci ' cikin sauri, Tukunna Ilham ta koma Ta zauna.
Yana gamawa yayi Hamdala ' gami dayin gyaran murya,
"Mhnm, Ilham da Fadwa ' tashi zakuyi Yanzu Ku shiga kitchen, Ayi lunch da wuri domin akwai Abokina da zaiyi joining dinmu.
Cikin hanzari suka tashi suka bar Parlon zuwa kitchen ' Jellof rice with chicken sukayi preparing yi. cikin *1* *hour* Suka kammala komai sannan suka jera Abincin Saman Dinning Table.
Yaya Farook kira ne ya shigo cikin wayar shi ' yayi recieving dinshi,
"Hello Taj? Harka iso ne? To shikenan ganinan zuwa.
Abunda sukaji ya ce kenan sannan ya tashi ya fita ' cikin *5* *minutes* suka shigo tare da Abokin nasa.
Bayan Isowar su parlon ne ' Abokin nashi ya duk'a ya gaida Umma ta amsa cikin kamala, sannan Ta tashi tare da cewa.
"Fadwa biyoni da Abinci na Daki.
Cike da ladabi ta zubawa Umma abincin ta a plate ' Ta bita da shi, ita kuwa Ilham zama tayi A dinning sannan Yaya Farook ya Umarci Abokin sa da suje su zauna domin suci abinci. Bayan zaman sune Ilham ta yiwa Abokin nashi sannan da zuwa sannan tayi serving dinsu Abinci '
"Wannan ce kanwar ka?
Yayi tambayar ya na kallon fuskar Yaya Farook,
"Eh ita ce Kanwa ta.
maida kallon shi yayi kan Ilham wacce take cin abinci,
"Well, sunana Tajuddeen ' amma zaki iya kirana da Taj.
Ko kallon shi Ilham ba tayi ba ' tace,
"Am Ilham by name.
Ta na gama fadin haka ne ' Fadwa ta shigo parlon tunda ta shigo Taj ya ke kallon ta ' kai tsaye ta wuce inda Ilham take, bayan ta zauna ne ' ta Zuba abinci ta faraci, still idon shi na kanta.
"Farook? Wannan kuma wacece? Kuma mene sunan ta. Cewar Taj,
"Ai gaka gata ' ka tambaye ta mana.
Fadwa Kallon Taj tayi ' tare da yimashi Murmushi,
"Sunana Fadwa ' kuma nima kanwar shi ce, Kaima meye sunan ka?
Tajuddeen yaji dadin yadda Fadwa ta saki jikinta,
"Sunana Tajuddeen ' Fadwa you have a nice name.
Jin Haka yasa Yaya Farook ya kalle shi, cikin bacin rai.
"Meye haka kakeyi Taj?
Cewar Yaya Farook,
"Me nayi kuma yanzu?
yaya Farook kallon Fadwa yayi ' haka yasa ta sunkuyar da kanta kasa,
"Ku tashi ku dauki abincin ku , ku shiga daga ciki.
turo baki sukayi ' sannan suka mike tsaye, suka bar wajen cikin kunkuni.
"Farook naga Alaman Kana takura wa yaran nan ' meyasa?
Taj yayi tambayar gami da Ajiye spoon din hannun shi.
"look, idan ka koshine mutashi ' mukara gaba, don nalura kacika shirme!
"No Farook, ba shirme nakeyi ba ' wallahi tunda naga kanwar ka naji inason ta.
馃槰, Gamm ' gaban Yaya Farook ya Fadi,
"Wace Kanwar ta wa?
*Taj* murmushi yayi gami da gyara zafi,
"Kanwar ka nakeso, Fadwa!!! And I hope bazaka hana niba?
Yaya Farook is totally speechless ' yama rasa abinda zaicewa Taj, haka yasa shi mikewa tsaye tare da Sanya hannun shi a aljihu.
"Ya naga ka mike tsaye ' kuma kayi shuru?
Cewar Taj,
"Saboda kazo abu mafi wahala.
"Meyasa?
"Saboda bazan iya baka Fadwa ba ' Taj ka nemi wata kawai.
Ajiyar zuciya yayi ' sannan ya ce,
"hmm, Farook kodai inada wani mugun hali ne?
"Taj, Bakada wani mugun hali ' Kawai dai...
"Kawai dai me?
Yaya Farook shuru yayi ya kyaleshi ' don kuwa zuciyar kemashi zafi,.
"Hm shikenan Farook, Yanzu inaso ka bani Damar yiwa Fadwa magana ' na *30* *minutes* kawai.
OK kawai Yaya Farook ya ce ' sannan ya kwalawa Fadwa kira, Cikin sauri ta iso Parlon.
"Yaya Gani.
"Tajuddeen ne yakeso ku gaisa.
Kallon Taj tayi ' cike da fara'a, Taj Mika mata Card dinshi yayi.
"Ga card dina nan, Zaki iya nema na ta wannan Number din.
Murmushi tayi gami da Kala kanta alaman to ' sannan sukayi sallama ta koma daki. Yaya Farook da Tajuddeen, fita sukayi Don suga gari.
Bayan Shigar Fadwa daki ne ' tayi tsalle ta fada saman gado cike da jin dadi,
"Wai ke lafiyan ki kuwa?
Cewar Ilham,
mika mata Card dinda yabata tayi ' tare da cewa,
"Kinga Card din da abokin Yaya Farook ya bani ' kuma yace In nemeshi.
"Ke kuma shine kiketa wani zumudi kinma kasa kama kanki gaba daYa.
Tashi Fadwa tayi ta zauna ' Tareda cewa,
"Ilham nidai guy din yaymun ne wallahi, Shiyasa gashi kyakkyawa .
Yatsine Ilham tayi ' sannan tace ,
"Kudai kuka sani ' daga ke harshi din.
Komawa ilham tayi ta kwanta abinta.
*AROUND* *6:00PM*
Da yamma Yaya Farook ya maida Taj gida, sannan ya tsaya yayi Sallah a masallaci tukunna ya dawo gida. Bayan shigo warshi ne ya iske su Ilham suna cin abinci,
"Ilham ina Umma?
"Umma ta na dakin ta,
Waje ya samu ya zauna ' sannan yace,
"Amma taci abinci kuwa?
"Eh ta ci abinci.
"Tor yanzu ' Kinsan me nakeso dake?
Ta girgiza kai alaman A'a,
"Kije Ki dauko min wayar ki kikawomin yanzun nan,
馃槰, zaro ido tayi gami da cewa,
"Yaya Farook Menayi?
wata mugun harara ya watsa mata, batasan lokacin da ta ruga aguje taje ta dauko wayar ta bashi ba ' itadai Fadwa ta na Gefe ta kallo. Ilham dawo wa tayi Parlon tare da wayar ta ahannu ' ta mika mashi,
"Yawwa, kema Babu ke bayin Waya daga yau Ilham.
Cewar Yaya Farook,
"Yaya Farook don Allah kayi hakuri, wallahi....
Tun kafin Ta gama rufe baki ' Yaya Farook ya tashi ya wuce dakin shi tare da cewa,
"Ki biyoni ki karba.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槤
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
*11-12* pages馃尮
Nan Wajen Ilham ta zauna ' kusa da Fadwa, Idanuwan ta cike da hawaye.
"Karki damu Ilham ' ninasan meyasa ya karbe maki waya, Saboda Taj Yace in neme sane shiyasa.
Cewar Fadwa,
"To ni meyasa abun zai shafeni?
"Hm kada kidamu ' Bari Abba ya dawo mu fada mashi.
Da sauri ta kalle ta ' cikin fuskar mamaki,
"Lallaima Fadwa ' to nidai wallahi babu ruwa na, Idan kika fadawa Abba kinsan dai ' Yaya Farook kanmu zai rama ko?
Ajiyar zuciya Fadwa tayi sannan ta ce,
"Tor Allah ya kyauta ' nidai xanje in kwanta don banajin yunwa, kuma inaso in tashi da wuri gobe.
Tana gama fadin ta tashi ta wuce Dakin su ' itama Ilham tabi bayanta.
*Washe* *Gari*
Da sassafe Su Fadwa suka tashi ' cikin hanzari suka shirya sannan sukayi breakfast, Suka wuce School.
Bayan shigan su cikin Class ne ' lecturer ya shigo Yagama lecture sannan ya fito, Haka Yasa Fadwa ta sami wayar wata friend dinta ' Ta kira Tajuddeen ta hanyar yin Amfani da Card dinda ya ba ta. Ringing Uku yayi ya dauka,
"Hello Who's this?
Cewar Taj,
"It's me Fadwa.
Jin haka yasa yayi murmushi ' tamkar yana ganin ta.
"Wow! Fadwa Yakike ' kina Ina ne haka? Naji surutu.
"ayya! Ina School ne yanzu.
"Zan iya zuwa School din domin mu gaisa?
Murmushi tayi har sai da yaji ' Sautin shi, sannan ta ce.
"Eh Zaka iya ' But kazo 2:00 lokacin munyi closing.
Ok kawai ya ce ' sannan ya kashe wayar, ita kuma ta maidawa mai wayar ' wayanta. Ilham na zaune A seat dinta ' fadwa tazo ta zauna kusa da ita tare da cewa,
"guest What!!!
"Fadwa you know that am not good in that ' so kawai ki fadamun menene?
Cewar Ilham,
"Taj, ne yace min zaizo School din nan Anjima ' Domin mu gaisa.
"wanene Taj kuma?
"Tajuddeen mana ' Abokin Yaya Farook,
馃槰 a tsora ce Ilham ta mike tsaye tare da cewa,
"What!!? Fadwa? Keko? Amma shikenan Allah ya baku sa'a,
"Ke miye? Duk kika wani tsora ta? Aidama na fada maki ' zanje Shopping yau so After closing Idanma driver ya zo bana nan, kawai ki wuce.
"Ok ' ai dayake ma ba jikina ne zaiyi tsami ba.
Harara Ta watsa mata sannan ta tashi ta bar wajen.
Bayan anyi closing ne ' suka fito daga school suka tsaya abakin gate, Don jiran driver.
"Yanzu Fadwa ' bazaki hakura da wannan Shopping din ba?
Cewar Ilham,
"Nifa gaskiya Ilham banason haka ' ni idan kina fadim haka banajin dadi, Kawai addua zakimin kada Yaya Farook ya gane cewa bana gida.
Suna cikin haka ne driver yazo ' Ilham ta shige mota ta bar Fadwa anan wajen. Bayan wuce warsu ne ' nadan wani lokaci Tajuddeen yazo da motar sa yayi Packing daidai inda take tsaye, sannan ya sauke glass din motar.
"Kiyi hakuri na bata maki lokaci ko?
Murmushi tayi ' Tare da Girgiza kai Alaman A'a.
"To yanzu dai ki shigo mota sai muyi magana,
Shiga motar tayi kamar yadda ya umarce ta, Bayan zaman ta ne ta ce.
"Nifa dama shopping nakeso inje ' Saboda sauri nakeyi banaso Yaya Farook ya gane.
Shuru Taj yayi nadan lokaci ' sannan ya ce,
"Yayan ki yana takura maki ko?
Ta daga kai alaman Eh ' Sannan yasa hannu ya shafa kumatun ta,
"kiyi hakuri ' Ai muna tare ko?
tsoro taji ganin yadda ya shafa fuskar ta ' hakan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 20