sannan ta juya ta nufi d'akin shi, bayan y'an lokuta k'alilan ne ta dawo parlon ta zauna tare da cewa,
"Yaya Khaleel na gama.
ok ya ce ba tare da ya d'ago kai ya kalleta ba.
*Around* *2:30pm*
Ilham ta gama jera abinci da duk wani abun buk'ata a saman dinning table , sannan ta haura sama ta yiwa Umma magana ' hakan yayi daidai da dawo war Abba daga wajen aiki, Fadwa da Ilham da sauri suka tunkari Abba tare da yi mashi sannu ' sannan Fadwa ta karb'a bag d'in hannun shi ta kai sashen shi, Yaya Khaleel ya tare Abba cikin ladabi ya zukunna a gaban sannan ya ce,
"Abba sannu da dawo,"
Yawwa Abba ya fad'a sannan ya nufa dinning ya zauna, tukunna Umma ta fito cike da fara'a a fuskarta ta zauna gami da yiwa Abba sannu da dawowa, Ilham ce ta tashi donyin sarving d'insu Fadwa tayi saurin karb'ar Spoon d'in tare da cewa,
"Ai Abba nane so kibari na zuba mashi,"
Nan Ilham ta koma ta zauna gamida balla mata harara ' Abin haushi ya bawa Yaya Khaleel yasa yaje ya zauna awajen ,
"Ke kiyi ki zuba min yunwa nikeji!"
Ya fad'a a gadaran ce ' Abba ya kalle shi,
"banson takurawa fa Khaleel ' hannu biyu gareta ba takwas ba.
Saida Fadwa ta zubawa kowa tukunna ta nemi waje ta zauna ta fara bawa ciki abinci , saida kowa ya kammala sannan Ilham ta tashi ta tattara plates d'in wajen ta wuce kitchen dasu.
Umma da Abba tashi sukayi suka tafi sashen su ' Yaya Khaleel kuma ya fita harabar gida don shan iska, fitar shi keda wuya Yaya Farook ya dawo ' shigowa yayi tare da yin sallama, Fadwa da ke a zaune ta amsa mashi cike da fara'a.
"Baby na ke kad'aice a parlon?"
Yayi tambayar a gajiye gamida zaunawa,
"Eh ni kad'aice Yaya, In zubo maka abincin ne?"
Juyowa yayi ya sakar mata wani kallo ' tare da yin murmushi,
"Yes, but ki zubomin ki kawomin d'akina."
To tace mashi sannan ta yunk'ura ta nufi kitchen kasan cewar Ilham ta tattara komai ta kai kitchen, koda ta je kitchen babu kowa har Ilham ta gama ta wuce d'aki.
Cikin hanzari ta zuba abincin d'an daidai a plate tare da d'aukar roban ruwan sanyi ta nufi d'akin Yaya Farook ta aje masa a saman side drower sannan ta juya zata fita ya turo k'ofar, a tsora ce taja dabaya ta tsaya Yaya Farook ya k'araso daff da ita gami dayin mata kiss tare da rungume ta.
"i missed you so fucking much Fadwa!!"
Nan take ta saki wani k'ara cikin sauri ya saketa gamu da tallabo fuskarta nan yaga idonta yayi jaaa Alaman daf take dayin kuka,
"Babyna lafiya? Ko dai bakida lafiya ne?"
Yayi tambayar yana kallon Cikin idonta,
"Yaya Farook ' ka famamin inda aka dakeni ne d'azun!"
Nan ya waro manyan idon shi ' cike da mamaki,
"What!!! Waye ya dakeki??"
Ranshi abace yayi tambayar ' sunkuyar da kai kawai tayi hawaye na d'iga a hankali......
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚鉁�
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*27-28* *pages*馃尮
Sake tambayar ta yayi cikin tsawa,
"Nace waye ya dake ki!!!?
Ranta abace ta d'ago kai ta kalleshi, "
"Waye zai dake ni idanba Yaya Khaleel ba!! "
Jin haka yasa jikin shi yin sanyi ' Cikin d'an k'ank'anin lokaci ya ce,
"hm Fadwa ai bakwajin magana ne ' ni nasan Bro ba zai dake ki haka nan ba, sai idan kinyi laifi."
Tsayawa tayi tana kallon cikin kwayar idon shi cike da mamaki,
"I know that Yaya Khaleel d'an uwanka ne and ni ban fad'i haka da wata manufa ba and beside kai ne ka nemi kasani. "
fuuuu ta juya zata fita yayi saurin rik'e mata hannu,
"I know that you're hurt Fadwa ' but ki kiyi hak'uri bazan iya cewa Khaleel komai ba. "
"Is OK, na fahimta. "
Fizge hannun ta tayi ta fice daga d'akin , har ta nufi d'akin su sai kuma ta juya ta nufi d'akin Yaya Khaleel ' kasan cewar tasan cewar baya d'akin yasa ta bud'e Kofar a hankali gami da yin sand'o, ta na shiga ta tura ta rufe. Ciki ta k'arasa cikin izza ' ta hango Album a saman gadon shi tare da diarry d'insa a gefe.
Cikin sauri ta hau saman gadon ' gami da d'aukan Album d'in ta d'ora a cinyarta, ( *Ohh* *Ni* *Seemaluv* *kodai* *Fadwa* *ta* *mance* *d'akin* *da* *shiga* *ne*?)
Budewa takeyi a hankali ta na kallon hotunan shi da abokanan shi mata da maza, haka taita kallon hotuna daga wanda zai bata dariya sai wanda zai bata haushi ' a haka har ta bud'o wani hoto, ganin hotun yasa gabanta fad'uwa.
"Dama Yaya Khaleel haka kake? Daman abunda kake tsina nawa a American kenan? Wannan kuma wacece to!!. "
Hoton cikakkiyar mace ce kyakkyawa ' haihuwar Uwarta, wacce babu kaya ajikinta ta na zauna. Cike da tsoro Fadwa ta rufe Album d'in tare da jan dogon tsaki,
"Mtsww wannan wace irin rayuwa ce? Yanzu shi kuma Yaya Khaleel me yakeyi da wannan picture d'in?"
Ta fad'a cike da takaici ' sannan ta jefar da Album d'in a gefe ta d'auki Dairy d'in. Bayan ta bud'e ne taga An rubuta, (Dear Diary...) A America ; ranar Litini ce na tafka babban kuskuren da ban tab'a tunanin zan tabka shiba a rayuwa ba, haka yasa duk idan na tuna dashi nakan zubda Hawaye.....
Fadwa bata kaiga k'arasawa ba taji an bud'o k'ofa bamm , da k'arfin tsiya hakan yasa ta razana ta mik'e tsaye cikin rawar jiki rik'e da Dairy d'in a hannun ta, Yaya Khaleel tsayawa yayi cak yana kallon ta cikin mamaki cen ya hangi Dairy d'in shi rik'e a hannun ta hakan yasa shi k'arasowa wajen ta cikin zafin nama da b'acin rai,
"Uban me kike min a d'aki? Ke wane irin stubbornness ke damun ki?"
Ya fad'a tare da kama kunnen ta,
"Ahhhggh Yaya Khaleel please am sorry ' zaka ciremun kunne!!!"
Ta fad'a Idonta cike da hawaye, Yaya Khaleel ya fizge diary d'in nashi gami da cewa,
"Bincike kike yimin dama? Da kikayi binciken ubanme kika binciko fad'amin, Iyee fad'amin nace!!!!"
Ya k'arashe maganar cikin tsawa, hakan yasa ta fashewa da kuka ' don kuwa tasan idan har tayi wasa to kuwa wani dukan zata sake sha,
"Yaya Khaleel don Allah ka tsaya kaji ' wallahi Allah ba bincike nake yi maka ba Yaya Farook ne ya ce inje in nemo masa biro, shine nazo nan ina dubawa....."
Ta na gama rufe baki ya d'auke ta da mari tasss, a gigice ta dafe wajen tare da sakin k'ara,
"Ahahhgg..."
"Ke!! Ni zakiyiwa k'arya da rainin hankali? Kaff d'akin ku babu mai Biro sai kin shigo nan? Iyeee ba tambayar ki nakeyi ba??"
Kwata kwata kasa magana tayi saboda kukan da yaci k'arfin ta, girgiza kai kawai takeyi Alaman a'a.
"In banda ke kin gama raina mutane ' Diary na a hannun ki sannan ki dubi tsabar idona kice Biro kikazo nema, Kakkarya kine kawai yau bazanyi ba Fadwa."
Sakin ta yayi ya nufa Wardrope d'inshi ganin haka ya bata damar fallawa a guje ta bar d'akin , kai tsaye ta wuce d'akin su cikin tsoro ta tura k'ofar ta rufe da key. Ilham wacce keta waya tun d'azu ne ganin halinda Fadwa ke ciki yasa ta yanke wayar ta cillar da ita saman gado, tayo kanta cikin hanzari.
"Lafiya Fadwa? Meyasa meki?"
Tayi tambayar tare da d'ago fuskarta, nan ta ga shedar hannu Alamun mari.
"Subhanallah meya sameki? Waya mareki! Halan Yaya Khaleel?"
Nin shi kawai Fadwa keyi sama sama ' saboda azabar da takeji a fuskar, Ilham rik'e hannun Fadwa tayi sannan tajata zuwa gado.
"Fadwa idan akwai wanda ya dace ki fadawa damuwar ki to ni'ce, "
d'ago kanta tayi ta kalleta da rinan nun idanun ta,
"Ilham d'akin Yaya Khaleel na shiga ni karan kaina bansan meya kaini ba, Bayan na shigane ya iske ni aciki shine yayi mun wannan mugun marin ' Ilham wai meyasa Yaya Khaleel ya tsane nine? Meyasa kokad'an baya d'aukata amatsayin k'anwar sa?"
D'an k'aramin tsaki Ilham taja sannan ta rungume Fadwa tare da bubbuga mata bayanta ,
"Amma dai Fadwa kinsan ko wajen Abba za'aje kece bakida gaskiya ko? Kuma tunda kinsan cewa ya tsaneki ai sai guji fad'awa tarkon shi, kuma sanin kankine gidan nan babu mai nuna miki banbanci ' yadda akemun haka kema ake miki.."
Saurin share hawayen ta tayi tare da cewa,
"Nagode Ilham ' lallai kin cika y'ar uwa, "
Ilham tashi tayi ta wuce parlor, Fadwa kuwa a zuciyar ta tace .
"Naji duk abinda kika ce Ilham ' amma ni gaskiya koda zai kakkarya nine kamar yadda yace, to fa saina binciko abinda Yaya Khaleel ke b'oyewa a diary d'innan. "
Nan ta tashi ta fad'a bathroom ta wanke fuskarta sannan ta wuce parlor, suka ci gaba da kallo.
*** *** *** ***
*Around* *4:30pm* ...
Su Fadwa na zaune a parlor suna kallo Umma ta shigo parlon ' bayan ta zauna ne ta ce,
"Aikin ku kenan kallo ' to kun d'aura girkin yamma ko?"
Fadwa cike da fara'a ta juyo ta ce,
"A'a Umma ai d'azu tare muka had'a mukayi,
"yawwa aiko kun kyauta, yanzu ku tashi kuje ku kira Farook da Khaleel ' Abban ku keson magana daku gaba d'aya. "
To sukace a tare, sannan suka tashi suka tafi ' ba tare da wani b'ata lokaci ba suka iso parlon, Umma na ganin sun iso ta tashi ta haura sashen su don kiran Abba.
Yaya Farook da Yaya Khaleel a k'asa suka zauna cike da ladabi, su kuwa su Ilham suna saman Kujera don ita Fadwa ma harda hard'e k'afafu d'aya kan d'aya Yaya Farook ya d'ago kai ya kallesu,
"Wane irin iskancin banza ne? Ba ankira mun nan don su Abba zasuyi magana damu bane? Shine kuke zaune d'are d'are a saman kujera?"
Jin haka yasa Yaya Khaleel juyowa ya watsa masu wani irin kallo ' ai tuni suka sulale k'asa cike da nutsuwa.
*Dedicated* *To* *My* * Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*29-30* *pages*馃尮
Suna cikin haka ne Umma da Abba suka shigo parlon ' cikin kamala suka sami waje suka zauna daga bisani Abba yayi gyaran murya,
"Ba komai ne yasa nace ku hallara anan ba ' illa maganar da zanyi wacce bata wuce uku zuwa hudu ba, wacce kuma ta k'unshi had'in kanku baki d'aya."
Abba gyara zama yayi sannan yace,
"Zan fara da kai Farook! Well Alhamdulillah yanzu ka sami aiki ' to me kuma ya dace kayi yanzu?"
Sai Umma tace,
"Aure!!"
Yaya Farook yana jin haka ya d'ago kai ya kalli Fadwa, ya ga itama shi take kallo cike da fara'a sannan Abba ya cigaba da cewa,
"nayi tunanin in had'a ku kai da Fadwa aure amma sai Umman ku ta ce had'in baiyiba ina ma laifin a had'a Khaleel da Fadwa? Dana duba sai naga Eh shawarar da ta kawo tayi, Amma nan da Two weeks kai Farook mukeso ka kawo mana wacce zaka aura!."
Jin haka gaban Yaya Farook ya fad'a, ita kuwa Fadwa idanuwanta cike suke da hawaye ' Yaya Khaleel kuwa ai abun ba'a magana don kuwa zuciyar shi tuk'uk'i kawai takeyi.
"Ke kuma Ilham yanzu kina iya bawa samarin naki damar zuwa domin ku fahimci juna ' amma mind you ba kowane zaki kawo cikin gidan nan ba!"
Bayan ya gama ne Umma ta ce,
"Ko kunada abun cewa game da wannan zabin?"
Yaya Farook gyara zama yayi tare da kai zuciyar shi nesa ya ce,
"Umma & Abba, bamuda abin cewa illa mu gode maku domin kuwa farin cikin ku shine farin cikin mu ' bak'in cikin ku kuwa! Shine namu, saboda haka wannan zab'in yayi."
Abinda Yaya Farook ya fad'a yayi matuk'ar tab'a zuciyar Fadwa, hakan yasa ta farajin jiri na d'ibarta. Abba da Umma sunji dad'in kalaman Yaya Farook sosai ba kad'an,
"Allah yayi maku albarka ' Allah kuma yasa naku y'ay'an suyi maku biyayya,"
Ameen suka ce sannan Umma tayi musu umarni da su tashi su tafi, bayan sun tashi Fadwa taji jiri na d'ibarta harta kaiga babu abinda take gani a gabanta face duhu ' hakan yasa ta yanke ji zata fad'i Ilham tayi saurin rik'eta.
Cikin tashin hankali Umma da Abba suka yo kanta,
"Innalillahi lafiya Fadwa? Meke faruwa ne?"
Cewar Umma!,
Yaya Farook ne yayi saurin sanya yatsun sa guda biyu wajen hancin ta,
"Subhanallah bata numfashi, Khaleel yi maza kaje ka tada mota akaita hospital. "
Cikin hanzari Yaya Khaleel ya fice ' Abba kuwa duk ya gama rud'ewa domin daka ganshi zaka gane cewa yana cikin tashin hankali,
"Fadwa don Allah kada ki mutu ' banason rasaki amatsayin y'a kamar yadda Allah ya d'auke min mahaifinki amatsayin amini!"
Cewar Abba,
"Don Allah mai gida ka kwantar da hankalin ka ' insha Allah Fadwa rayayya ce in Allah ya yarda,"
Yaya Farook d'aukar Fadwa yayi cen caka kaff d'aukar jarirai, yaje ya sata a mota sanna ya dawo ciki ya Umarci Ilham taje ta d'auko gelenta, bata tare da wani b'ata lokaci ba tadawo rataye da gele a k'irjin ta sannan suka fice ita da Yaya Farook , har Umma zata bisu Abba yayi saurin rik'ota,
"Bazakije a haka ba! Ki kintsa tukunna sai mufita tare . "
Ya fad'a tare da samun waje ya zauna sannan Umma ta haura sashen ta domin kintsawa, cikin hanzari ta Umma sauko parlon sanye sa hijab d'inta a jiki,
"A'a ki dakata tukunna harsai sun dawo sannan mu tafi baki d'aya,"
To kawai tace masa sannan ta sami waje ta zauna gami dayin tagumi.
Bangaren su Yaya Farook kuwa tunda Khaleel ya tada mota suka wuce gudu kawai yake zabga wa ' cike da tausaya wa Fadwa.
Cikin d'an k'ank'anin lokaci suka isa asibiti, bayan sunyi packing ne Yaya Farook ya fito cikin zafin nam ya d'auki Fadwa sannan suka shiga ciki, suna shiga ne sukayi kicib'us da Doctor zai shiga wani Ward d'in Yaya Khaleel ya tsaidashi,
"Doctor!!! Please wait you have client here!!."
A tsanake likita ya juyo ya kalle su sannan ya kwalawa Nurse kira ' cikin hanzari tazo wajen,
"Yes Sir!
"Ki hanzarta ki basu Ward ' kafin inzo yanzu!
OK tace sannan tayi masu jagora zuwa d'akin, bayan Yaya Farook ya kwantar da ita Nurse d'in ta fita zuwa kiran Doctor ' Ilham na zaune a gefen Fadwa,
"But Yaya baka tunanin Zab'in nan dasu Umma sukayi ne yajawo wa Fadwa wannan abin?"
Cewar Yaya Khaleel,
"What!!!? Karda insake jin wannan maganar daga bakinki Khaleel!! Ai duk abinda su Umma suka yanke shine daidai, "
"But nifa Yaya gaskiya bana son ta,"
Yana gama rufe baki ya d'auke shi da mari tasss,
"Ashe bakada hankali Khaleel?"
"Kayi hak'uri Yaya, nayi kuskure insha Allah bazan sake ba!"
Ya na fad'in haka ya tashi ya fice ya nufi wajen mota yayi zamansa, bayan fitar shine likita ya shigo ward d'in kai tsaye ya zarce inda Fadwa ke kwance ' stethoscope yasanya a k'irjin ta domin sauraron Numfashin ta, sai da ya kammala sannan ya cire ya juyo ya fuskanci Yaya Farook.
"wato tayi doguwar suma ne, Amma insha Allah nan bada dad'ewa ba zata farfad'o." . "To likita thank you so much,"
"You are welcome ' yanzu zan turo Nurse tazo tayi mata settling IV fluid, "
OK kawai Yaya Farook yace sannan Likita ya fita, cikin d'an k'ank'anin lokaci Nurse tazo tayi mata settling drip, sannan ta fita.
*Around* *6:42pm*
Yaya Khaleel ya shigo cikin ward ' ya sami Yaya Farook zaune a kujera,
"Yaya wai har yanzu bata farka ba?"
"Eh wallahi Khaleel,"
"Yaya yanzu kamata yayi mutashi ita Ilham a maida ita gida ' don taje ta d'an shiryowa Fadwa abinda zataci , bayan Munyi sallah sai mu taho da su Abba gaba d'aya ' nasan kafin nan ta farka."
"Hakane Khaleel muje!!
Yaya Farook mik'ewa yayi suka fita Ilham ta bi bayansu, fitarsu keda wuya Fadwa ta bud'e ido cike da kasala haka yayi dai dai da shigowar likita.
"Alhamdulillah ina y'an uwan naki?"
Yayi tambayar tare da dafa k'arfen gadon nata, kai kawai ta girgiza mashi sannan ya ce.
"Oh may be lokacin da kika farka basu nan ' bari inje sallah in dawo,
Abinda ya fad'a kenan ya juya zai wuce tayi saurin tsaida shi da cewa,
"Doctor!! Please meke damuna?
Juyowa yayi ya kalleta tare da sanya hannun shi a aljihu,
"A yadda na fahimta ' kamar kinsami wani bad news ne wannan ne kad'ai zai iya samar da shock a jikin d'an adam harta kaishi ga suma,"
"haka ne doctor tabbas bad news ne nasamu ' but please doctor can you do me a favor?"
Tayi tambayar tana kallon kwayar idon shi,
"For what?
"Doctor please ' idan y'an uwana sukazo kace masu na suma ne saka makon ciwon kan da yasami cikin d'an k'ank'anin lokaci please."
"is Ok i can do that for you ' akwai wannan sirrin tsakanin Doctor da patients d'insa, so you don't have to worry about that."
Murmushi tayi masa tare da cewa thanks ' sannan ya fice.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*31-32* *pages*馃尮
Bayan sun Isa gida ne ' Yaya Khaleel yayi packing motar Ilham ta fito sannan su kuma suka wuce masallaci, Ilham tana shiga ciki ta iske Umma a zaune ' jin motsine yasa Umma d'ago kai ta kalle ta a razane,
"Haba Ilham ki shigo haka babu Sallama? Yaya jikin Fadwa?"
Ilham samun waje tayi ta zauna ' sannan tace,
"Umma Fadwa insha Allah zata sami sauk'i, likita ya ce zata farka bada dad'ewa amma mudai har muka baro ta bata farka ba馃槩."
Umma hannu biyu tasa ta rufe bakinta, tare da yin salati.
"Umma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 20