saurin kashe wayar tayi ' sakamakon ganin Umma da tayi ta shigo cikin d'akin, Hakan yasa Ilham mik'ewa tsaye.
"Ku bani waje inason inyi magana da 'yata".
Nan Ilham ta had'iye miyau dakyar, Sannan k'awayen suka fita daga d'akin zuwa parlor.
Umma ajiyar zuciya tayi ' ta k'arasa cikin d'akin ta zauna, Sannan itama Ilham ta koma ta zauna kusa da ita.
"Ilham?".
Ilham d'ago kai tayi ta kalleta, zuciyar ta na k'una ' amma sam batasan dalili ba.
"Nasiha zanyi maki ' kin kasance 'yata kuma jini na! Wacce ta tashi cikin *BABBAN GIDA!* mai cike da tarbiyya".
Umma hannun Ilham ta kamo ' da sauri Ilham ta d'ago kai ta kalle ta jin yadda hannun take rawa.
"Ki kasance mai yiwa mijin ki biyayya ' Ilham.....".
Umma kasa k'arasa maganar tayi ' saboda rad'ad'in da ke cinta a zuciya, Na zafin rashin 'yarta da zatayi a kusa da ita.
Hawaye ne suka zubowa Umma a ido ' tayi sauri ta goge don kada Ilham ta fahimci wani abu.
Ilham kuwa duk ta fahimci haka ' itama wasu zafafan hawaye ke fitowa daga idon ta, A hankali ta mik'e tsaye ta dawo saitin fuskar Umma ta zuk'unna.
"Umma na! Meyasa kike kuka?...".
Suna cikin haka ne ' d'aya daga cikin k'awayen ta shigo d'akin cikin sauri.
"Umma ' masu d'aukan Amaren ne suka iso".
Umma saurin share hawayen ta tayi ' sannan ta tashi tsaye tare da rufa mata mayafin ta akai.
"Kije kawai ' zamuyi waya".
Umma na fad'in haka tabar d'akin cikin sauri, Hakan yasa Ilham had'iye miyau dakyar ' sannan sauran k'awayen suka shigo d'akin cikin hanzari suka fara shirya ta.
Bayan sun gama ne ' suka fito daga d'akin tare da amarya, Ilham tsayawa tayi tana kallon harabar parlon.
"Haba Ilham lokaci na k'urewa fa! Sai kace ba'a gari d'aya ake ba?".
Haka suka fito waje harabar garege ' ta tsaya cak hawaye na zuba a fuskar ta.
Fadwa ji tayi kamar ance ta tashi ' haka tayi firgigit ta tashi, Cikin hanzari ta diro daga saman gado ' duk da tanajin dizziness a jikin ta, Hakan bai hanata zarcewa parlor inda Ige ke zaune.
"Ige?".
Ige juyowa tayi ' ta kalle ta.
"Na'am 'yan nan, Yaya jikin naki?".
"Amm...da sauk'i Ilham fa?".
"Ayya! Anya kuwa basu wuce ba?".
"Ina?".
"Ha'a gidan mijinta mana!".
Zaro ido Fadwa tayi ' gami da juyawa tabar parlon zuwa waje cikin hanzari.
Fadwa na fita ta iske ' k'awayen sai daga suke da ita akan suwuce, Amma sam Ilhan tak'i.
Nan take k'walla suka ciko idon Fadwa, Hakan yasa ta k'arasa har inda take tare da tallabo fuskar ta.
"Ilham...".
Ilham kallon Fadwa tayi ' da idanun ta da suka rine saboda kuka.
"Ni kike jira ko?".
Kai ta d'aga mata alaman Eh, Sannan Fadwa ta rungume ta cikin kuka.
"Please idan kinje ki kulamun da kanki! Kumayi biyayya a gareshi".
Tana fad'in haka taja hannun ta ' tai mata rakiya zuwa gaban mota.
Fadwa saka Ilham tayi a cikin mota ' tare da cewa.
"Sai nazo".
Sannan ta rufe ' suka koma kallon junan su ta glass d'in motar , Motoci bakwai ne suka zo wajen ' amma mota uku ne suka cika da Amare, Sai da ko waccen su ta gama shiga ' sannan gate man ta bud'e masu gate suka fito.
Fadwa kuwa idonta akan Ilham yake ' hakama Ilham, Har saida taga bata ganin komai a wajen tukunna ta koma sashen ta.
*DEDICATED TO MY FAN'S*
馃憚馃憚馃憚馃槝
[5/23, 2:58 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*#IG:* *_@Bae_Seema鉂*
*_I dedicated this page to my BESTY (ONE LOVE鉂�)_*
*87-88*
*WASHE GARI*
Da sassafe Fadwa ta farka daga bacci ' cikin matsanancin ciwon kai, Ga jikin ta yayi zafi rau.
A hankali ta tashi ' ta sauka daga saman gadon ta nufi d'akin ta.
Toilet ta shiga ' tayi alwala sannan ta fito tayi sallah, Bayan ta idar ne ta mik'e tsaye tare da yaye hijab d'in ta, Ta nufi side-drower d'in da ke wajen gado taja ta d'auko paracetamol (pain-reliever).
Fadwa fitowa tayi da maganin a hannu ' ta nufi kitchen tasha, tukunna ta dawo d'akin ta ta kwanta gami da jan blanket ' don zazzab'i zazzab'i takeji.
*AROUND 7:00AM*
Yaya Khaleel ya tashi daga bacci ' cike da mik'a, Shafa gefen shi yayi baiji Fadwa ba hakan yasa shi bud'e idon shi ' ganin bata d'akin ne yasa shi saukowa daga saman gadon cike da salati a bakin shi.
Yaya Khaleel saida ya shiga toilet ' tukunna ya fito ya shiga bathroom don yin wanka.
Bayan ya gama ne ya fito d'auke da alwala a jikinsa, Yayi sallah sannan ya fara shiri.
"Yau kam da wuri zan tafi office ' don ina da aiki sosai, Allah yasa Baby nah ba bacci ta koma ba".
Abinda ya fad'a kenan ya gama shirya wa, Sannan ya fito parlor cikin sauri.
"Baby nah!!".
Yaya Khaleel kiran Fadwa yakeyi amma bata amsa ba ' ganin haka yasa ya nufi bedroom d'in nata.
A duk'un k'une ya hango ta saman gado ' sai rawar sanyi takeyi da sambatu, Cikin sauri ya k'arasa kusa da ita ya zauna tare da tallabo ta.
"Baby nah! What's wrong?".
"Swe.. Sww... Sweetheart am feeling sick, Am not well".
Ta fad'a cikin rawar baki.
Yaya Khaleel rungume ta yayi ' yaji jikinta yayi rau da zafi, Cikin hanzari ya ciro wayar shi ' ya kira wata Nurse, Kasan cewar abokiyar shi ce sosai.
Bayan sun gama wayar ne ' ya maida wayar shi aljihu.
"Baby nah! Yanzu za'a zo a dubamun ke, Don't warry ok?".
"Ok".
Kwantar da ita yayi ' tare da lullub'e ta sosai.
"Bari inje in gaishe dasu Umma ' sannan in fad'a masu bakya jin dad'i".
"Uhm Hum".
Tashi yayi ya fita ' ya nufi part d'insu Umma, A parlor ya same su ' ita da Ige sai kuma Ilham wacce ke zauna a k'asa kanta a sunkuye.
Yaya Khaleel duk'awa yayi ya gaishe su ' sannan Ilham ta gaishe shi, Tukunna ya sanar masu da rashin lafiyar Fadwa.
"Subhanallah! Meke damun ta".
Cewar Umma.
"Wallahi Umma yau ne ta tashi da zazzab'i, Amma nadai kira nurse zata zo ta duba ta yanzu ' by the way Abba na nan kuwa?".
"Aiko bai dad'e da tafiya office ba".
"Ok".
Ilham ce tayi wuff ta tashi ' ta nufi sashen Fadwa cike da tausayawa, Tana shiga ta wuce d'akin ta kai tsaye.
Kakarin amanta taji a toilet kasan cewar babu komai a cikin ta ' hakan yasa Ilham ta nufi toilet d'in kai tsaye.
"Sannu Fadwa ya jikin?".
Fadwa d'ago kanta tayi ta kalli Ilham amma sam bata gani sosai.
"Ilham please ' jani ki maidani saman gado, Jiri nake gani".
Haka Ilham ta kama hannun ta ' ta maida Fadwa saman gado tare da ja mata lullub'i.
"Fadwa me kikaci to?".
"Bana jin cin komai Ilham ' ki kyale kawai".
"Allah shi kyauta in kyaleki a haka! ' meye amfani na kenan?".
Suna cikin haka ne ' su Umma suka shigo cikin d'akin tare da Yaya Khaleel d'in.
"Amma ya kamata ace ' nurse d'in nan ta iso".
Yaya Khaleel ya fad'a yana k'ok'arin kiran nurse d'in a waya, Ringing d'aya tayi ta d'auka.
"Idan baza ki sami damar zuwa bane ' ai saiki fad'amun in wuce da ita hospital kawai".
"Ayya! Afuwan ' ina kan hanyan zuwa yanzu, Na kusa iso wa".
Tana gama rufe baki ' ya kashe wayar.
Umma da Ige ' gaishe da Fadwa sukeyi da jiki.
"Umma bari inje ko ruwan lipton ne in had'a mata".
"To shikenan ' ai yakamata".
Cewar Umma.
Ilham bata dad'e da fita ba ' nurse d'in ta kira Yaya Khaleel a waya cewar ta iso yazo ya shigo da ita, Sai da ya fad'awa su Umma isowar Nurse d'in tukunna ya fita.
Nurse d'in shigowa tayi cikin garege ta tsaya, Yaya Khaleel ta hango yana isowa gare ta cikin sauri.
"Barka da isowa! Muje ko?".
Ya fad'a tukunna ya juya ta bishi a baya, Part d'in Fadwa suka shiga kai tsaye ya zarce da ita cikin d'akin.
Bayan sun gaisa da su Umma ne ' ta fara duba Fadwa wacce ke kwance jiki na rawa.
Saida ta gama ' tukunna ta rubuta musu magun gunan da zasu nema mata, Sannan ta sanar musu da cewa Fadwa na d'auke da ciki.
Yaya Khaleel baki ya saki ' yana kallon Fadwa wacce idon ta ke rufe, Amma itama zuciyar ta cike take da farin ciki.
Umma da Ige ' sun nuna farin cikin su matuk'a gami da yiwa Allah godiya.
"Alhamdulillah! Allah na gode maka, Friend kina da tukwaici mai tsoka ' karki damu".
Cewar Yaya Khaleel.
"Uhm! To ina nan ina jira ' yanzu dai kar abata komai har sai tasha wad'an nan magun gunan da rubuta inba haka ba zata cigaba da yin amai, Kuma zai galabaitar da ita".
Nurse ta fad'i haka tana k'ok'arin d'aukar jakarta don ta koma wajen aikin ta, Umma ta tsaida ita da cewa.
"To yanzu ko ruwan lipton bazata iya shaba? ' don batasa komai a cikin ta ba".
"Amm... Mama zaku iya bata ruwan lipton ba tare da milk ba a ciki".
Tana gama fad'in haka, Tasa kai ta wuce gami da yiwa Yaya Khaleel sallama.
Bayan wucewar ta ne ' Ilham ta shigo ciki rik'e da cup d'in lipton a hannun ta, Zama tayi a gefen Fadwa tukunna ta tasheta ' ta rik'a bata a baki.
"Khaleel ' ka tashi kaje ka siyo mata maganin, don yau akwai aiki sosai a gidan nan".
To yace ' sannan ya juya ya fice rik'e da car-key a hannun shi.
Umma ta maida kallon ta ga Ilham.
"Ke kuma! Idan kin gama ' kije ki shirya don nasan k'awayen ki suna kan hanya, Kuma *1:00pm* za'a d'aura auren ' Ige sai ta tsaya da Fadwa a nan, Ni kuma zanje in cigaba da duba masu aikin gyaran part d'in Farook, Don nasan amaren suma suna nan tafe".
To Ige tace sannan ta tashi ta nufi parlor tare da cewa.
"Ni bari inje inyi kallo kafin Ilham ta gama".
Tukunna Umma ta tashi ta wuce sashen su, Zuciyar ta cike da farin ciki ' don kuwa ta kusa ganin jikanta da iznin Allah.
Umma na shiga ' ta iske Yaya Farook zaune a parlor yana kallon news, Samun waje tayi ta zauna ' sannan tace.
"Farook ' Fadwa batajin dad'i ya kamata kaje ka duba jikin ta".
"To Umma".
Abinda ya fad'a kenan ya mik'e ya nufi sashen ta, Nan suka ci karo da Yaya Khaleel ya dawo zai shiga ciki.
"Khaleel ashe Fadwa batajin dad'i?".
"Eh wallahi Bro ' amma mu shiga daga ciki ku gaisa".
Haka suka k'arasa ciki ' har d'akin ta, Sannan Yaya Farook ya gaishe ta da jiki ' har ya juya zai wuce yaji tace.
"Sweetheart ' babu Injections a ciki ko?".
"Haba! Baby bah ' tsoron allura kikeyi?".
Yaya Farook ne yayi saurin taron numfashin shi ' da cewa.
"Eh Khaleel ' tana da tsoron allura sosai, Hope babu!".
Fadwa tsayawa tayi tana kallon shi cikin mamaki ' duk da batajin k'arfin jikin ta hakan bai hana ta magana ba, b'ata rai tayi gami da cewa.
"Not really, Gaskiya sanin da akaimun ' amma banda yanzu".
Yaya Farook yana jin ta fad'i haka ya juya ya bar d'akin, Kai tsaye ya nufi garden yayi zaman shi ' zaman jiran amarya.
Bayan Ilham ta gama bawa Fadwa ruwan lipton ne ' ta tashi ta nufi kitchen don d'auko ruwan da zata sha maganin dashi.
"Sweetheart ' muga magun gunan to".
Yaya Khaleel mik'a mata ledar yayi ' ta duba taga babu injection ko d'aya aciki, Hakan yasa tayi ajiyar zuciya.
"Baby nah ' karkiso kiga yadda nak'agara cikin nan ya fara girma".
Murmushi tayi tare da jinginar da kanta jikin gado.
"Karka damu ai kamar gobe ne".
Suna cikin haka ne ' Ilham ta shigo d'akin rik'e da robar ruwa a hannun ta, Ta mik'awa Yaya Khaleel sannan ta juya ta fice tare da cewa.
"Fadwa bari inje inshirya ' a wuni da sauk'i".
"To Allah yasa".
Tana fita ' Yaya Khaleek ya b'alli magun gunan da zata sha yanzu ' ya bata ta sanya a baki, Sannan ta kora da ruwa.
Fadwa bata wani jima ba ' bacci yayi awon gaba da ita, Kasan cewar cikin maganin akwai maganin dake hana amai ' wanda kuwa shike sanya bacci.
Yaya Khaleel gyara mata kwanciya yayi ' sannan yaja mata lullub'i ya koma gefe yana kallon ta.
*DEDICATED TO MY FAN'S*
馃憚馃憚馃憚
[5/23, 2:58 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*#IG:* *_@Bae_Seema鉂*
_@...Am sorry fan's for not posting on time!, Wannan page d'in naku ne ' My besty (Jameesha) and (Rufaida Yusuf) thank you for caring, Loving and Support... 鈾モ櫏鈾*
*91-92*
Fadwa zuwa tayi ta zauna kusa da Ige ' tare da cewa.
"Ige baki fito kinyi sallama da Ilham ba!".
"Zamuje gidanta ai ' nan da kwana biyu".
Fadwa ajiyar zuciya tayi ' ta jinginar da kanta jikin kujera, Cen kuma ta tashi tare da yunk'ura wa da gudu ta nufi kitchen, Hakan yasa Ige tashi tabita cikin sauri.
Ige iske Fadwa tayi tanata amai.
"Subhanallah! Zazzab'in ne kuma ya dawo?".
Ige k'arasawa tayi har inda Fadwa take ' ta d'iba ruwa a hannun ta ta shafa mata akai, Sannan ta rik'o hannun ta suka dawo parlor.
"Sannu kinji?".
Cewar Ige.
"Ige ina Khaleel yaje?".
"Ya tafi wajen aiki ' ai bazai dad'e ba".
Kai kawai ta d'aga mata alaman to, Sannan Fadwa ta koma ta kwanta saman kujera.
Umma ce ta shigo sashen rik'e da waya a hannun ta, Ta zauna kusa da Fadwa.
"Fadwa yaya jikin naki?".
"Da sauk'i Umma".
Sannan Umma ta maida kallon ta akan Ige.
"Ige amare fa sun iso Nigeria ' don yanzu suka kirani suka sanar dani cewa suna airport, Khaleel nake k'ok'arin kira yanzu ana cemin line busy".
"To amma kin fad'awa Farooku?".
"Eh na sanar dashi ' domin ya zauna cikin shiri, Kinga kuma dole sai Khaleel ya dawo ' ko kuma kawai in tura musu driver.
"Eh Umma kawai ki tura driver d'in tunda kinga Yaya Khaleel yana office, A tura driver kawai ' nasan dai bazasu rasa kayayyaki ba! So ya kawo su sai ya koma ya d'auko masu kayan".
Cewar Fadwa.
A zuciyarta tace.
"Bazasu mayarmun da miji boyi boyi ba!".
Maganar da Umma tayi ne yasa tayi saurin dawo wa cikin hankalin ta.
"Eh tabbas abinda zanyi kenan! Bari in tashi ' intura masu driver kawai".
Umma na gama fad'in haka ta tashi ta nufi wajen driver ' ta sanar dashi, Sannan ta fad'a mashi da motar daya dace ya tafi da ita.
Haka driver yaja mota ya fice zuwa airport.
B'angaren Ilham kuwa ' tunda aka kaita d'akin ta 'yan uwan mijinta wato Al'ameen keta kai da dawo wa cikin gidan, K'annan shi kuwa sai zuwa sukeyi suna gabatar da kansu ' Haka gidan ta ya cika tam da 'yan uwa!.
Ilham taji dad'in yadda suka karramata matuk'a.
*AROUND 3:00PM*
Mutane suka fara watse wa ' a gidan Ilham, Ya rage daga ita sai k'awayen ta sai kuwa 'yar autar su Al'ameen mai suna Suhaila.
Suhaila mace ce wacce ta cika mace ' daka ganta kasan yarinya ce k'arama wacce bata wuce tsarar Ilham ba a shekaru, Wannan shine dalilin da yasa jinin Ilham da Suhaila ya had'u.
"Auntyn mu gaskiya ' naji dad'in kasance warki matar Yaya".
Ilham murmushi kawai tayi mata ' sannan Suhaila taci gaba da bata labarin yanayin yadda gidan su yake.
Umma na sashen Fadwa ' suna zaman jiran amare ne sukaji tsayawar mota a cikin garege, Hakan yasa Fadwa tashi ta lek'a window ganin wasu jajayen fata tayi suna fitowa daga motar, Sai ita Safeena wacce take a gaban mota taci ado ' hakan yasa Fadwa juyowa ta kalli su Umma.
"Umma sune suka iso".
Nan take Ige tayi zambur ta mik'e tsaye tare da cewa.
"To ai sai muje mu tare su ko?".
Hakan yasa Fadwa tayi sauri ta fita ' su Umma kuwa na biye a bayan ta.
"Sannun ku da zuwa!".
Cewar Fadwa cike da fara'a a fuskar ta.
Saida suka gama fitowa ne Safeena ta fito daga motar tayi hugging Fadwa ' tukunna suka rik'e hannu taja ta zuwa part d'in ta, Har k'awayen ta sun biyita Umma ta dakatar dasu tare da mik'a musu key d'in part d'in Safeena.
"Ga key d'in gidan ta nan! Kamata yayi ku shiga kuga yanayin gidan da kuma tsarin da zakuyi mashi".
Ansar key d'in sukayi, Sannan Umma tayi musu nuni da sashen suka nufi wajen.
Kasan cewar Safeena tare da mahaifiyar ta sukazo ' hakan yasa Umma da Ige suka ja mahaifiyar Safeena zuwa sashen su, Domin ta zauna ta huta ta kuma ci abinci.
Bayan sun zauna ne Umma suka fara hira da Mahaifiyar Safeena ' suna cikin hakane Ige ta tashi ta kawo mata abinci sannan ta kaiwa k'awayen amarya nasu abincin, Bayan hakan ne Ige ta kaiwa Safeena nata abincin ta.
Sannan ta koma sashen Umma sukaci gaba da fira.
Yaya Farook ne ya fito daga d'akin shi ' yazo suka gaisa da Mahaifiyar Safeena.
Tayi musu 'yar tak'aicecciyar nasiha, Yaya Farook godiya yayi mata tare da nuna farin cikin shi a fili ' sannan ya tashi ya fita zuwa part d'in shi a zaton shi Safeena tana ciki.
Yana shiga ya iske k'awayen ta a ciki sai jera kayayyaki sukeyi ' kasan cewar driver ya d'auko masu kayan dankin dake airport, Yaya Farook waje ya samu ya zauna saman kujera ta gaishe su da hanya tukunna yace.
"Ina fatan dai kunci kun k'oshi!".
D'aya daga cikin sune ta bud'e baki tace.
"Yes mun k'oshi! Amma muna fatan dai Ango ba Amarya ya biyo ba!!".
Yaya Farook dariya yayi ' har sai da hak'oran shi biyu suka bayyana.
"To inba ita na biyo ba ' wazan biyo?".
"Taw Amaryar ka ' bata iso ba tukunna!".
Yaya Farook tashi yayi ' ya fice cikin fara'a, Ya zarce wajen driver ya mik'a mashi 3,000.
"Kaza zaka siyo ' please yanzu...".
To kawai driver yace sannan ya shige mota yaja ya wuce ' inda aka aike shi.
Har Yaya Farook yasa kai zai koma wajen Umma ' yaji muryar Safeena a part Fadwa, Da alama fira sukeyi.
Yaya Farook harya nufi wajen sai kuma ya juya ' ya wuce sashen su.
Driver bai wani b'ata lokaci ba ya dawo musu da sak'on da Yaya Farook ya bayar, kai tsaye ya kaima su ' don yasan cewa nasu ne.
*AROUND 4:00PM*
Mahaifiyar Safeena da k'awayen ta suka fara shirye shiryen komawa gida, Umma da Ige da kuma Mahaifiyar Safeena harabar garege suka fito ' nan ma k'awayen suka fito gaba d'ayan su.
Fadwa da Safeena waje suma suka fito ' don suyiwa junan su sallama.
Haka aka shiga yiwa Safeena nasiha ' da jan kunne, Bayan ta gama ne ta shige mota tukunna k'awayen suma suka shige, tare da d'agowa Safeena hannu.
Nan take idanun ta suka ciko da hawaye ' amma sai dai basu kaiga zubowa ba.
Tanaji tana gani ' Mahaifiyar ta da k'awayen driver yaja su suka tafi zuwa airport.
"Fadwa ki kaita d'akin ta domin ta huta, Kuma ki lallashe ta".
Cewar Umma.
Kai kawai Fadwa ta d'aga sannan taja hannun Safeena donta kaita d'akinta.
Bayan sun wuce ne ' Ige tace.
"Kai nidai kam zanje in huta ' don wallahi agajiye nake".
"ai akwai gajiya kam ' ni sallah zanyi tukunna sai ind'an mik'e".
Cewar Umma.
Haka suka shiga daga ciki ' sukayi sallah sannan suka kwanta suna sauke gajiya.
Fadwa saida ta tabbatar Safeena ta manta da komai ' tukunna ta baro sashen nata, Ta dawo sashen ta ' haka yayi daidai da fitowar Yaya Farook daga sashen Umma.
Kallon shi kawai Fadwa tayi ' sannan ta juya ta nufi nata sashen, Shi kuma ya shige ciki.
Fadwa waje ta samu ta zauna saman kujera ' ta d'auki 'yar k'aramar wayar ta tayi dialling number d'in Yaya Khaleel.
Saida ta kirashi wajen sau biyu ' tukunna ya d'auka.
"Babyna? Kiyi hak'uri ina driving ne, Gani nan dawo wa gidan yanzu".
Tanajin haka ta kashe wayar ' ba tare da tace uffan ba.
*4:30pm*
Yaya Khaleel ya dawo gida ' sai da yayi packing motar shi a packing space, Tukunna ya fito.
B'angaran shi ya nufa kai tsaye cikin sauri, Shiga yayi cike da sallama d'auke a bakin shi.
Ganin Fadwa yayi a zaune ' fuskar ta na kallon TV babu walwala sam, Hakan yasa shi k'arasawa harabar parlon ya d'auki remote ya kashe TV, Sannan ya koma kusa da ita ya zauna.
"Babyna sallama fa nakeyi!".
Fadwa maida kallon ta tayi akan shi ' idanu suka cicciko da k'walla.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 20