"Mun bani, i thought d'akin Yaya Farook zai kwana ' innalillahi kenan yanada d'aki dabam wanda bamu gyara shi ba. "
Haka ta fad'a a zuciyarta jikin duk yayi sanyi, suna isa bakin k'ofar Yaya Khaleel yasa hannu ya bud'e d'akin ya shiga kai tsaye sannan itama tashiga, tsayawa yayi yana k'arewa d'akin kallo ranshi abace ' ganin haka tasan cewa lallai yau zasuci ubansu hakan yasa ta fara zubda hawaye tunkafin ya yanke hukunci.
"Yanzu haka ake gyaran d'aki agarinku??"
shuru tayi ba tare da ta ce komai ba ' jin haka yasa shi juyowa a fusace,
"Fadwa ba dake nak....."
Kasa k'arasa maganar yayi ganin yadda hawaye kebin fuskarta, cikin hanzari ya matsa kusa da ita tare da cewa.
"Fadwa are you Okey?"
"Yaya Khaleel don Allah kada kabigemu ' wallahi aikine yayi yawa shiyasa muka manta da gyara d'akin, kuma ni nad'auka tare da Yaya Farook zaka rik'a kwana....."
Tana gama rufe baki yayi saurin rungume ta ' tare da shafa bayanta,
"is Okay! Fadwa ki daina wannan kukan ' tunda banyi bugunba tukunna. "
Yadda take ta mutsu mutsune ' ya gane cewa batason Hugging d'inne, Raba jikin shi yayi da nata gami da cewa,
"Yanzu dai kije ki d'auko min bed sheet, sai kizo ki samun a gadon inkwanta kafin gobe sai ku gyara."
Ok ta ce sannan ta juya ta fice cikin hanzari ' bata wani b'ata lokaci ba ta dawo d'auke da bed sheet a hannun ta ' ta mik'a mashi ya karb'a gami dayin kissing d'inta a goshi hakan yasa ta zaro ido,
"is a normal thing ' so don't fall in love with me, don nasan halinku Y'an nigeria ' saboda haka zaki iya tafiya."
Yana fad'in haka ta kama hanya ta wuce d'aki ta kwanta, Kwanciyar ta keda wuya ta tuna maganar Yaya Farook ' da sauri ta tashi zaune, Ilham dake kwance ta na chatting ne tace.
"Lafiya kuwa ?"
"Lafiya kalau kitchen zanje don k'ishi nakeji."
Ok kawai Ilham ta ce sannan Fadwa Ta tashi ta nufi d'akin Yaya Farook, Handle d'in ta murd'a taji a k'ofar a bud'e yasa ta shige cikin sauri. Akwance ta hangi Yaya Farook hakan yasa ta kiran sunan shi,
"Yaya Farook"
Jin yayi shuru ne yasa ta k'arasa cikin d'akin tare da cewa,
"To ko yayi bacci ne?"
Hayewa tayi har tsakiyar gadon shi ' sannan ta sunkuya tana kallon fuskar shi, bata ankara ba taji ya jawo ta jikin shi, lips dinta daff da nashi ' haka yasa ya matse ta sosai yadda bazata iya Kuccewa ba ' nan fa ido Ya raina fata,
"Yaya Farook na d'auka ko kayi bacci ne shiyasa."
Ta fad'a tana k'ok'arin janye jikinta,
"Yau anan nakeso ki kwanta ' Inaso ki d'ebemun kewa Fadwa,"
"Yaya Farook please ka bari intafi ' kasan banason irin wad'an nan abubuwan."
Ta fad'a tare da yi mashi magiya,
"Ke ! Am serious fa ' Karma ki bari raina yab'aci."
Ya fad'i haka cike da d'aure fuskar.
Murmushi tayi mashi tare da kashe mashi ido d'aya (wink), Sannan ta sa hannu a k'irjin shi ta fara yinmashi waiwayi a Wajen, Nan take ya farajin launin jikin shi yafara sauyawa ' cikin wata murya yace,
"Fadwa stop it ' kidaina yimin wannan abun please,"
"A'a"
Ta fad'a saida ra bari ya sakan kance sannan tayi wufff ta sauko daga gadon ' cikin Sauri har tana had'awa da gudu tabar d'akin, Yaya Farook Sai ninshi yakeyi yana mutsu mutsu.
D'akin su tashige a guje ' har saida Ilham ta razana,
"ke kuwa ina kika shiga? Don na je kitchen ban ganki ba,"
Fadwa kwanciya tayi gami da jan blanket ' sannan tace,
"Well, Ilham lambu naje."
"lambu da daddaren nan Fadwa?"
"yes ' fruit naje nasha, A tsorace na dawo shiyasa Ma kika ganni a haka."
"ke kika sani dai."
Abunda tace kenan ta maida kanta akan waya ' nan bacci yayi awon gaba dasu.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
*23-24* pages馃尮
*Washe* *gari*....
Da sassafe around 6:22Am ' Fadwa da Ilham suka tashi sukayi Sallah, Bayan sun idar da sallah ne Ilham tayi wuff ta tashi tana k'ok'arin d'aura towel a jikin ta,
"Ilham kada kiyi wanka yanzu ' saboda gyaran d'aki yana jiran mu."
Cewar Fadwa,
Ilham tsayawa tayi tana kallon Fadwa d'auke da alaman tambaya a fuskar ta,
"Gyaran d'akin ina kuma? "
"Gyaran d'akin Yaya Khaleel kuwa, domin kuwa ya ce yau da safe zamu gyara shi ' Ai auna arzik'i mukayi jiya don wallahi da jikinmu ya gaya mana."
Tsaki Ilham taja ' tare da jan kwafa,
"To wallahi ' babu wani gyaran d'akin da zamu tsayayi, don kuwa test garemu yau ' shi ya gama nashi karatun mu zaizo ya takura mAna, "
"Tab!! To aini mantawa nayi banyi mashi bayani ba tun jiya d'in."
Ya tsine baki Ilham tayi gami da buga cinyar ta,
"ke kika sani, wallahi ki zauna nan harkisami Carryover ' shine na farko wanda zai jibge ki, "
Fadwa mik'ewa tayi tsaye tare da yaye hijab d'in jikin ta,
"To yanzu yaza'ayi kenan mu fita ba tare da kowa ya sani ba? "
"Yanzu dai kibari inshiga wanka ' infito saike ma ki shirya. "
Ilham harta juya zata shige bathroom Fadwa tayi saurin dakatar da ita da cewa,
"Ilham Amma kinsan dai bazamu fita ba tare da ' mun shirya musu breakfast ba ko?"
"Fadwa wai wane breakfast kuma? Bayan kinsan muddin muka tsaya tofa ' gyaran d'akin nan tamkar mun gama yin shine, kawai mubar musu Umma idan ta tashi saita had'a kokuma d'aya daga cikin su."
Ta na gama fad'in haka ta shige bathroom ba tare da ta jira abunda Fadwa zata ce ba. A bakin gado ta zauna Tayi jugum ' babu abinda take tunowa sai irin marin da Tasha wajen Yaya Khaleel.
"Anya kuwa Ilham zan iya bin shawarar ki kuwa?
Haka ta fad'a idanuwan ta cike da tsoro. "
*Some* *Minutes* *Later*
Bayan Ilham ta fito daga bathroom ne Fadwa ta shige cikin sauri ' Tukunna Ilham ta fara Shiryawa.
Yaya Farook saukowa yayi daga gado ' gami dayin mik'a sannan Ya fad'a bathroom cikin Sauri yayi wanka tare da yin Alwala, sannan ya fito yayi sallah. Bayan ya idar ne yaji cikin shi tamkar anyi mashi yasa aciki, Hakan yasa yayi saurin mik'ewa tsaye.
"Ashhh wace irin yunwa ce da sanyin safiya haka? "
Fita d'akin yayi cikin sauri, ya nufi kichen ' lipton ya fara nema baigani ba, ganin haka yasa Ya nufi d'akin su Ilham cikin sauri,
"Ke zo ki had'amun Tea insha yanzun nan Yunwa nakeji, "
Jitayi maganar ta daki zuciyar ta ' kallon shi ta juyo tayi, cikin k'unk'uni tace.
"To, "
Yaya Farook juyawa yayi ya koma d'aki ya cigaba da shiryawa, Ilham bayan ta kammala shirin tane ' ta je ta tsaya bakin Kofar bathroom,
"Fadwa dalla kiyi sauri, inba haka ba wallahi Tafiyata zanyi ' kinga har Yaya Farook ya sani aiki ko? "
Cewar Ilham,
"Ke naji ' yanzun zan fito dalla, "
Tsaki taja sannan ta wuce kitchen ' cikin d'an k'ank'anin lokaci ta had'a mashi ta kai mashi d'aki,
"Yaya Farook ga tea d'in nan, "
Nuni yayi mata da yatsa ' alaman ta aje saman side drower, Bayan ta ajene Ta juya ta wuce ' tana komawa d'aki ta iske Fadwa a zaune ta na Shafa mai,
"Wai ke Fadwa kanki d'aya kuwa? amma kinsan dai sauri mukeyi ko?"
Cikin hanzari ta tashi tasa kayanta sannan Tasha powder sama sama ' tukunna ta d'auki gelen ta yafa a kirji,
"Tow Am done. "
Ta fad'a rik'eda k'ugu ' sannan Ilham ta d'auki gelen ta itama ta yafa, suka fito parlor cikin sand'o har suka fita cikin garage ' Fadwa ce ta kwankwasa wa driver kofa,
"Ka fito mun shirya!
Cewar Fadwa, "
Ba tare da wani b'ata lokaci ba driver ya fito, ya bud'e motar sannan suka shiga ' tukunna yayi hone mai gadi ya bud'e gate d'in suka fice.
Bayan wuce warsu ne ' Yaya Farook ya fito rik'e da key d'in shi a hannu ya wuce Office,. Yana fita Umma ta fito daga sashen ta ita da Abba ' kallon dinning table tayi taga babu komai,
"ha'a inasu Fadwa ne? Ya haryanzu basu Had'a breakfast ba?"
Abba zama yayi a kujerar harabar parlor,
"Kila basu gama bane da wuri, "
Cewar Abba,
Umma d'akinsu ta nufa ganin basa cikine yasa ta wuce kitchen domin duba, nan ma haka ' cikin hanzari ta Koma parlor,
"Wallahi basa gidan, kardai sun tafi School ne yaran nan."
"Kinga bara kawai in wuce wajen aiki ' zan karya acen, tunda kikaga haka to sunda uzri ne a gabansu."
Yana gama fad'in haka ya tashi ya fita, Haka yai daidai da shigowar Yaya Khaleel parlor , a tsaye ya iske Umma tayi folding hannayen ta ' sannan ya zukunna cike da ladabi,
"Umma ina kwana! "
"Lafiya k'alau Khaleel ya gajiyan jiya? "
"Lafiya lau Umma ' Umma lafiya na ganki haka?
Yayi tambayar tare da mik'ewa tsaye,
"Hm Khaleel al'amarin yaran nan ne yabani mamaki, School suka wuce ba tareda sun had'a breakfast ba."
Cikin yanayi na mamaki yace, "what!! Lallai ransu zai b'aci yau, nasan wannan iskanci Wannan yarinyar ce Fadwa jikinta zai gaya mata. "
Umma zatayi magana yai saurin taren numfashin ta da cewa, "Umma karki damu nima gwani ne a kitchen ' da lafiyata da komai bazaki shiga kitchen ba ina kallo. "
Murmushi yayi mata sannan ya juya ya nufi kitchen ' indomie ya dafa cikin d'an k'ank'anin lokaci sannan ya kawo Ya aje a dinning table.
Umma na zaune a harabar parlor ' tana kallon kai da komo wanshi, saida ya gama jera komai sannan ya dawo ya zukunna inda take zaune.
"Umma ga abun karya war nan na kammala, "
To Umma ta ce sannan ta tashi ta nufi dinning table ta zauna ' cikin hanzari yayi sarving d'inta sannan shima ya zuba,
"Amm Umma Yaya ya tashi kuwa?"
"Gaskiya banji motsin shiba Khaleel,"
Tashi yayi ya nufi d'akin Yaya Farook, ya murd'a kofar yaji a kulle sannan ya juya ya koma parlor.
"Farook d'in na nan kuwa?"
Cewar Umma,
"a'a Umma k'ofar shi a kulle. "
"Ohh Hakane yaune zai fara shiga Office,"
OK kawai yace sannan ya maida kallon shi a kan plate d'in indomie d'inshi ya cigaba da ci.
*** *** *** *** ***
*Around* *11:30am*
Su Fadwa sun fito daga exam hall ' rik'e da handbag d'insu a hannu.
"Yanzu inda munsan zamu gama da wuri ' aida mun sanarwa Driver, "
Cewar Fadwa,
"ai bari kawai in kirashi ' don naga inada Number d'inshi. "
Ilham ciro wayarta tayi daga handbag d'inta tayi dailling number d'in Driver,
"Hello, kazo ka d'auke mu daga school ' don munyi closing. "
To kawai driver ya ce ' sannan ta kashe wayar, cikin hanzari driver yaje ya d'auko su daga school ' ya kawosu gida haka yayi daidai da fitowar Yaya Khaleel cikin Garage domin shan iska. Bayan su Ilham sun fito daga motor ne suna k'ok'arin shigewa gida, Yaya Khaleel ya dakatar dasu da cewa.
"Where did you think you're going to????"
Yayi maganar cikin yanayi na fad'a , a tsorace suka tsaya tare da juyowa suka kalleshi.
"Yaya Khaleel ciki zamu shiga,"
Cewar Fadwa.
"ciki ko? To kushiga!! Aike dama daga ganin kwayar idonki to baza kiyi kunya ba!!!. "
Fadwa kallon Ilham tayi suka had'a ido sannan ta sunkuyar da kanta k'asa,
"Ubanwa kuka mayar y'an iska??? Umma? Kokuwa Abba?? Ko kuma nida Yaya Farook?"
"Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri ' zanyi maka bayani,"
Cewar Fadwa.
"Zakimin shuru ko sai nazo na tattaka ki? To bari kuji infad'a maku, da zarar kun shiga ciki kun aje wannan kima kiman handbags d'in naku ku zarce d'akina ku jirani. "
Tsoro duk ya gama cika Ilham idanuwan ta kuwa ' gabb suke da zubar da hawaye, d'ago kai tayi ta kalleshi gami dayin fuskar tausayi.
"Yaya Khaleeel please....
Bata kaiga k'arasawa ba ya daka musu tsawa,
"zaku b'ace mun da gani kokuwa?"
Da gudu suka shige cikin gida ' cike da tsoro.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
@ *_I_* *_proudly_* *_dedicated_* *_this_* *_page_* *_to_* *Jameesha* & *Husna*
*_Good_* *_Friends_* *_Are_* *_Hard_* *_to_* *_Find_* *_Difficult_* *_to_* *_Leave_* *_Impossible_* *_to_* *_Forget_* *_Nikam_* *_babu_* *_abinda_* *_zance_* *_sai_* *_godiya_*...*_dana_* *_sameku_* *_a_* *_matsayin_* *_Friends_*
*25-26* *pages*馃尮
Suna shiga cikin parlor suka iske Umma a zaune tana kallo ' basu san lokacin da suka tsugunna a k'asanta idanuwan su ciccike da hawaye,
" Umma don Allah kicewa Yaya Khaleel karya dake mu!
Cewar Ilham,"
Umma rage k'arar TV d'in tayi da remote sannan ta kalli Ilham,
"Ai bansan bakida Kunya ba sai yanzu Ilham ' inbanda kun raina mutane kwatafi ba tare da kun had'a mana abin karya waba? "
Sunkuyar da kai Ilham tayi Hawaye kawai ke zubo mata,
"Umma don Allah kiyi mana Hakuri ' wallahi Uzri mukeda shiyasa amma insha Allah haka bazai maimaita kanshi ba, "
Cewar Fadwa,
"Au kema zaki nunamin taki rashin kunyar kenan ko? Ai Fadwa koma wane irin Uzri ne daku ' ai kamata yayi Wani cikin ku yazo yaimun bayani, bawai ku kad'a kanku ku fita ba."
Umma na gama rufe baki Ilham taji saukar dundu a bayan ta, a kid'ime suka waiga domin suga waye ' Haba ido hudu sukayi da Yaya Khaleel, haka yasa suka tashi a guje tare da cillar da handbags d'insu zuwa d'akin shi.
Suna shiga d'akin shi suka zube a k'asa Cike da tsoro, Yaya Khaleel kwafa yayi gami da girgiza kai sannan ya biso.
"To banda mugun duka dai ' don nasan halinka. "
Cewar Umma,
Kai tsaye ya zarce d'akin shi ba tare da yacewa Umma komai, Cikin zafin nama ya bud'e k'ofar ganin su yayi a zukunne kowan nen su da hawaye sharkaf a fuskarshi, fuskar nan tashi a d'aure ya nufi wardrope dinshi ya zaro belt ' da Fadwa ya fara had'a ido sannan ya nufo kanta, ganin haka yasa tayi zambur ta mik'e tsaye.
"Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri ' Karka dakemu please...."
Cikin kuka ta k'arashe maganar ta cike da shash shek'a,
"Ohhh Kokowa xamuyi koh? Aike dama nasan babu abinda bazaki iya ba.... "
Jikake zafff zafff ' saukar belt a bayan ta, Da gudu ta nufi wajen gadon shi ta rakub'e cikin kuka tace.
"wayyo!!! Yaya Khaleel don Allah kayi hakuri please forgive us....."
Komawa kan Ilham yayi wacce ko ina najikin ta rawa yakeyi,
"Ke dan ubanki ' da hankalin ki da komai, zaki biyewa wancen tsageran? saboda kin manta wanene Yaya Khaleel ko? To jikinki zai fad'a maki kuwa."
Sai da ya sauke mata belt shida a jikin sannan ' ya k'ara mata da hauri a jikin ta, saboda tsabar kuka Ilham ko hawaye ya daina fita daga idonta.
"Tashi ki fita ki bani waje ' idan ba haka ba saina kakkarya ki a wajen nan. "
Da gudu Ilham ta bar d'akin jin haka yasa Fadwa mik'ewa tsaye Cikin sauri zata fita, ya cafko ta A gigice ta juyo ta kalle shi.
"ina kike tunanin zaki? Ba tareda jikin ki ya gaya maki ba? Mara kunya!!!"
Jin saukar belt tayi a k'afa funta ' yasa tayin tsalle cikin rad'ad'i ta k'ank'ame shi jikinta sai rawa yakeyi,
"Ya..Yay. Yaya please kaimin afuwa ' wallahi zan iya mutuwa...."
Wani zirrr yaji tundaga k'afar shi har saman kanshi, shuru yayi nad'an lokaci sannan ya finciko ta da karfin tsiya har saida ta fad'a k'asa, a hankali yake takowa inda take ' ganin ya nufo ta da belt d'in ne hankalin ta ya k'ara tashi ,
"Yaya wallahi wannan ba plan d'ina bane Ilham ce tace muyi haka, please karka kasheni.
Jin haka yasa shi tsayawa cak ' tare da wullar da belt d'in a saman gado,
"Tashi ki fice mun da gani ' gobe idan Ilham tace ki shiga wuta sai ki shiga...."
Da sauri ta mik'e tsaye gami da had'awa da gudu ta fice daga d'akin, ba ta tsaya ko ina ba sai a saman gadon su.
Saida ta gama dawo wa normal sannan ta lura da Ilham rik'e da bucket d'in ruwan d'umi a hannunta tare da K'aramin towel tana gasa jikinta,
"Ilham?"
A gajiye Ilham ta juyo ta kalli Fadwa,
"Ya akayi?"
Fadwa tashi tayi ta zauna cikin jin zafin jikin ta,
"Meyasa Yaya Khaleel ya tsane ni?"
"Mtsww wannan wace irin banzar tambaya ce ' ni dalla ki kyaleni naji da d'aya mana aida kinsani kin tambaye shi kafin ki fito.!"
Ya tsine baki tayi sannan ta tashi ta fada bathroom don yin wanka da ruwan d'umi, ko da ta fito bata iske Ilham a d'akin ba nan ta d'aga kai ta kalli a goge,
"Ok! Lokacin girka lunch yayi 2:00pm Ilham na kitchen yanzu.
Bayan ta zauna agaban mirror ne ta fara gyara jikinta ' wayar ta tayi k'ara, cikin hanzari ta d'auka ganin Yaya Farook ne yasata yin picking cikin sauri.
"Hello Yaya.."
"Baby na yakike? Hope kina lafiya?"
A wahale ta ce, "lafiya kalau Yaya"
"Meyasa meki naji kamar bakida lafiya Fadwa!"
Jitayi kamar ta fad'a mashi abinda ya faru sai kuma ta fasa,
"Well, Yaya Farook babu komai ' is just that nad'an sami bacci ne d'azun. .
Ok yace tare da yinmata sallama sannan ya kashe wayar ' a tsanake ta tashi ta sanya kaya ajikin ta doguwar riga atamfa, sannan ta fito ta nufi parlor ganin Yaya Khaleel tayi a zaune ' nan take cikin ta murd'a ta juya xata koma ya dakatar da ita da cewa,
"Kije ki gyaramun d'aki na yanzun nan kuma ke kad'ai.
To tace
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 20