Lubna Allah na rok'e ka haukan da Fadwa ke dashi akan ta, To karya sami sauran mutane."
Lubna ta fad'i haka tare da d'aga hannun ta sama.
Ilham ce tazo taja hannun Fadwa suka zauna ' tare da cewa.
"Fadwa please ' ki daina kula ta, Ki bari idan Yaya Khaleel ya dawo to koma mene ne ' sai ayi shi."
Hawaye ne ya zubo ma Fadwa a ido ' cikin sauri ta share hawayen.
"Lubna ki kira su please ' don asan inda suke, Nai waya da inspector d'in police d'in suna nan zuwa yanzu."
"Ok".
Abunda Lubna ta ce kenan ' tayi dailing number d'in 'yan daban, Akayi sa'a kuwa ringing d'ays tayi ogan nasu ya d'auka ' Lubna tayi sauri ta saka wayar a loudspeaker.
"A'a yau kuma kiran ki ne ' da sassafe haka?".
"Eh aiba abun mamaki bane ko?".
"Eh haka ne ' gani ga wannan mutumin, Har yanzu a d'aure yake tun jiya ya kasa cin komai ' amma hajiya ya kika sa wayar ki a loudspeaker?".
Nan Lubna ta zaro ido ' ta kalli su Umma wad'an da suke a tsaitsaye cike da fargaba.
"Wace irin tambaya ce wannan? Kaya nake sanyawa shiyasa ' ai kasan haka nan kawai bazan saba, A tak'aice dai kuna ina ne? Don inaso inzo yanzun nan ' inason in ganshi ne kuma zan taho muku da d'an kud'i."
"Hahaha Hajiya kenan ' to muna tsohon ginin dake bayan gari, Amma fa ko kinzo bazamu baki shi ba!."
"To shikenan ' sai dai nazo d'in."
Tana gama fad'in haka ta kashe wayar, Sannan ta juyo ta kalli Fadwa wacce hawaye ne kawai ke kwaranya mata a fuska.
"Sai ki kwantar da hankalin ' mijin ki ya kusa dawo wa gare ki, Kuma ina fatan laifina zai goge a idon ki ' don kuwa bazan so naje gidan miji na da zunubi a kai ba."
Fadwa kauda kanta kawai tayi ' tare da sanya hannu a fuskar ta ta share hawaye.
"Thank you so much! Lubna kinyi mana k'ok'ari matuk'a!"
Cewar Abba.
Umma kuka kawai takeyi mara sauti.
"Haba Umma aiba kuka zakiyi ba ' gode wa Allah ya dace muyi."
Umma samun waje tayi ' ta zauna kusa da Ige, Tana share hawaye.
Sallama sukaji anyi ' hakan yasa suka juya gaba d'ayan su..
Inspector ne ' ya shigo ciki sanye da kakin shi a jiki, Ya k'arasa har inda suke zaune ' Abba ya mik'e tsaye suka gaisa tukunna yayi musu jaje.
"Tare nake da yara na a waje ' hope a shirye kuke!".
"Insha Allah! Tare da wannan baiwar Allan zamuje ' don tayi magana dasu kuma sun fad'a mata wajen, Infact dai yaran ta ne".
"OK muje ko?".
Haka Lubna ta tashi ' har zasu wuce, Fadwa ta tsaida su da cewa.
"Abba ' nima zan biku."
Yaya Farook ne ya waigo ya kalle ta ' cikin b'acin rai.
"A gida zaki tsaya! Tare da su Umma, Kima daina wannan maganar banzan."
Koma wa Fadwa tayi ta zauna ' sannan su Abba da Yaya Farook da Inspector d'in suka juya suka wuce.
Lubna tana fita ta shige cikin motar ta ' suka bita a baya, Wajen waje ne mai nisa ' don sai da suka dad'e suna tafiya sannan suka kai inda tsohon ginin yake.
Suna gaf dasu k'arasa wajen ne Lubna taja burki ta tsaya, Sannan ta fito suma suka firfito.
"Bara in fara shiga tukunna".
Abinda tace kenan ' sannan ta k'arasa wajen da k'afa ta shige cikin ginin, Sai da tad'an jima sannan suka bi bayan ta ' Abba da Yaya Farook suna daga waje.
Bayan ta shiga daga ciki ne ' ta sake kiran ogan 'yan daban, Yayi mata kwatance da inda suke ' kasan cewar cikin ginin k'usurwa k'usurwa sunyi yawa.
Haka Lubna tabi kwatan cen da yayi mata ' tashige wani d'aki, Tana shiga ta fara sauke idanun ta akan Yaya Khaleel ' wanda yake zaune saman kujera a d'aure idanuwan shi duk sun kumbura saboda duka.
Cikin hanzari Lubna ta k'arasa inda yake ' ta zuk'unna idon ta cike da k'walla, Shi kuwa uku uku kawai yake gani ' don baima san wanda ke kanshi ba.
Cikin kuka Lubna tace.
"Khaleel... haka suka maida mun kai?".
"Hajiya! Muna fatan dai ke kad'ai kika shigo wajen nan!".
Lubna mik'ewa tayi tsaye gami da share hawayen ta, Sannan tace.
"Ni kad'aice mana! Kuma don Allah na rok'e ku ' ku barni in tafi dashi gida."
Ogan umurtan d'aya daga cikin yaran nashi nayi, Da yaje ya lek'a ya duba yagani.
"Hajiya ' inhar aka gano cewa bake kad'ai kika zo wajen nan ba to zan kashe ki daga ke har shi, Kuma maganar kud'in da kika ce zaki kawo mana kenan k'arya ce kawai kikeyi!".
"Wallahi a'a, Kunsan ai bantab'a yi muku alk'awari na sab'a ba ko?".
"Eh haka ne hajiya! Amma don me zaki damu dashi haka? Bayan kin fad'a mana baya son ki! ' kuma inda 'yan uwan shi sun damu dashi ai bazasu kyale shi haka ba".
Lubna juya wa tayi ' ta kalli Yaya Khaleel, Zuciyar ta cike take da tausayin shi.
Yaran da Ogan ya aika ne ' ya dawo a guje yana haki!.
*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
*_#IG: Bae_Seema鉂*
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*#IG:* *_@Bae_Seema鉂*
*77-78*
Fadwa wuf tayi ta mik'e tsaye cike da mamakin shigowar ta cikin gidan.
"Me ya kawo ki gidan nan?."
Fadwa ta fad'a tana share hawayen da ke fuskarta, Kallon uku saura kwata Lubna ke mata ' hakan yasa Fadwa k'arasa wa har gaban ta, Ta d'aga hannu ta sharara mata mari a fuska.
A gigice Lubna ta dafe fuskar ' cikin wani irin k'ara.
"Ahhhhgh."
Nan Ilham ta taso tazo ta rik'e Fadwa, Su Ige da Yaya Farook tasowa sukayi sukai kansu.
"Ke baki da hankali ne? Ya zaki mare ta haka? ' ku bari muji da d'aya mana!."
Cewar Yaya Farook.
"Kad'an ma ta gani wallahi ' inda ba'a raba ba kashe kine kawai bazanyi ba, Banza kawai karuwa mai bin mazajen mutane."
Nan Fadwa ta sakeyo wani kukan kura ' zata sake marin ta Yaya Farook ya rik'e hannun.
"Meyasa ba kyajin magana ne waike! ' ashe b'atan mijin ki ma bata dame kiba kenan?."
Fadwa fincike hannun ta tayi daga nashi ' ta maida kallon ta kan Lubna, Wacce har yanzu rik'e take da fuska ' Umma da Abba kuwa suna gefe a zauna abun duniya duk ya ishe su.
"To kwartuwa! Ai saiki fad'i abunda ya kawo ki."
Safeena ce taja hannun Fadwa ' suka koma suka zauna.
"Haba! Fadwa ' ai fad'a ba naki bane yanzu."
Wata harara Fadwa ta watsama Safeena ' aiba arzik'i ta fita harkar ta.
Yaya Farook da Ilham ' suma komawa sukayi suka zauna.
"Baiwar Allah ' muna sauraron ki."
Lubna k'arasa ciki tayi ' ta sami waje ta zauna, Sannan ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya.
"Nidai suna na Lubna ' kuma ni budurwar Khaleel ce ada, Yana sona kuma nima inason shi."
Had'a ido sukayi da Fadwa ta kalle ta ' ta watsar sannan ta cigaba da cewa.
"Wato a tak'aice dai nazo ne akan maganar kidnapping d'in Khaleel da akayi.
Nan Umma da Abba ' suka mik'e tsaye a tare suka ce.
"Kinsan inda yake ne?."
"Yes ' har mutanen ma nasani."
Gaba d'ayan su mik'ewa tsaye sukayi, Idanun Fadwa kyar akan Lubna.
"Baiwar Allah su waye? Ki fad'a mana don Allah."
Cewar Umma.
Nan Lubna ta kwashe duk abinda ya faru ' ta fad'a masu.
"Kun gani ko? So take ta raba ni da miji na ' duk abinda ya faru da miji na itace sila, Don Allah ku barni inyi k'asa k'asa da ita anan wajen."
Fadwa ta fad'a haka cikin kuka.
"Umma don Allah ku zazzauna abi komai a hankali."
Cewar Yaya Farook.
Bayan sun zauna ne ' Yaya Farook yace.
"Yanzu ke basu fad'a maki inda suke a b'oye ba?."
"Basu fad'amun ba ' amma idan na nemi nasan hakan wannan abune mai sauk'i."
"Lubna ko?."
Ta d'aga mashi kai alaman Eh, Sannan ya ce.
"Zamu so ki taimake mu akan hakan ' don nasan dama taimako ne ya kawo ki."
"K'warai kuwa, Amma kasan cewar yanzu dare yayi *8:30pm* zamu bari sai gobe da safe ' don zanje gida yanzu."
Yaya Farook zaiyi magana kenan ' Fadwa ta tari numfashin shi.
"Mtsw! Wai don kinga ana neman taimakon ki? ' ko kuwa don miji na ne?, Idan da mijin kine fisabilillahi ya zakiyi?."
"Fadwa ' can't you be patient? Zamu iya jira har goben muddin wani abu bazai same shiba."
Cewar Abba.
Fadwa shuru tayi ' idanuwan ta na zubar da hawaye.
"Lubna zaki iya tafiya ' Allah ya kaimu goben.!"
Lubna tashi tayi zata wuce ' har ta kai bakin k'ofa, Fadwa ta tsai da ita da cewa.
"Inaso ki sani cewa ' ni Fadwa wallahi bazan tab'a kyale ki haka ba, Saboda duk wannan abun da ya faru da miji na ' ke ce sila."
Lubna girgiza kanta kawai tayi ' tare da jan tsaki, Sannan tace.
"Da zakiyi ' hak'uri nima biki na saura kwana uku, So kinga kuwa babu abinda zanyi da mijin ki ' kawai zan taimaka maku ne don har yanzu akwai sauran tausayin sa a cikin zuciya ta".
Tana fad'in haka ta fice.
"Haba Fadwa! Bakya tunanin wad'an nan magan ganun zasu iya sawa ta cenja ra'ayin ta?.
Cewar Yaya Farook.
Banza tayi ta kyale shi ' tukunna yaja tsaki gami da cewa.
"Abba ' muje masallaci muyi sallah, don bamu sami magrib ba ' ga isha'i ma."
Ok Abba yace, Sannan suka tashi suka fita zuwa masallaci.
Bayan fitar sune Umma da Ige suka haura sama ' don yin sallah, Fadwa da Ilham da Safeena kuma ' d'aki suka nufa suma suyi nasu sallolin.
Bayan sun idar ne ' Fadwa ta haye saman gado, Ta sake dasa wani sabon kukan ' Ilham da Safeena suka shiga lallashin ta .
Ko da su Abba suka dawo cikin gidan ' kowa d'akin shi ya zarce cike da fargaban abinda gobe zata haifar.
Haka suka kwanta babu wanda ya sanya komai a cikin sa, Fadwa kuwa bacci? ai sai dai b'arawo.
*** *** *** *** *** *** ***
*WASHE GARI*
Da sassafe Fadwa ta tashi ' ta riga kowa tashi, kai tsaye ta wuce sashen ta ' wai ko a tunanin ta zata ga mijin ta, Amma ko da ta shiga tsit taji ' babu motsin komai.
"Sweetheart?."
Ta fad'a kamar zatayi kuka ' haka ta shige d'akin shi ta fad'a bathroom tayo alwala, Sannan ta fito tayi sallah.
Bayan ta sallame ne ' ta tashi tsaye tana k'arewa d'akin kallo.
"Allah ka taimake ni ' Yaya Khaleel d'ina ya dawo lafiya."
Ta fad'i hakan gami da d'aga hannun ta sama.
Fadwa barin d'akin tayi ta dawo parlor ' tayi tsaye tana tuna irin wasan nin da suka rik'ayi tare da shi, Nan da nan k'walla ta ciko mata ido.
Hakan yasa ta barin sashen nata cikin hanzari ' ta nufi sashen su Ilham, Fadwa tana tafiya tana share hawaye ' ko da ta shiga iske Ilham tayi wajen dinning table tana jera cups d'in da za'a sha tea wato breakfast.
Wajen dinning table d'in Fadwa ta nufa ' taje ta zauna tare da sunkuyar da kanta k'asa.
"Fadwa in zuba miki tea d'in ne yanzu?."
Girgiza mata kai tayi ' tukunna Ilham ta sami waje ta zauna.
Umma da Ige ne ' suka shigo parlon suma suka zauna a wajen, Fadwa da Ilham suka gaishe su ' sannan Ilham ta zuba musu tea d'in su a cup ta ajewa kowa a gaban shi.
Bayan su Umma sun fara karyawa ne ' Yaya Farook da Safeena suka shigo parlon suma a tare suka ja kujera ' suka zauna, Kai zakace a d'aki d'aya suka kwana.
Safeena gaishe da su Umma tayi ' tukunna Ilham ta tsiyaya masu nasu tea d'in a cup ita da Yaya Farook, Safeena ta b'alli bread ta mik'a mashi shima ya b'alla.
"Aww! Ilham na manta ' zubawa Abban ku tea d'in shi a cup ki kai mashi."
Cewar Umma.
To tace ' sannan tayi yadda aka umarce ta.
Ilham bayan ta kaine ta dawo ' ta cigaba da breakfast, Yaya Farook lura yayi da Fadwa ' don tunda yazo baiga tana breakfast ba.
"Fadwa! Ke kin gama naki breakfast d'inne?".
Kai ta girgiza mashi ' tare da cewa.
"A'a bana jin yunwa."
"What do you mean by ' bakya jin yunwa? Come on ki zuba tea kisha."
D'ago kai tayi ta kalle shi ' idanuwan ta cike da hawaye.
"Yaya Farook kawai bana jin cin komai ne."
Zaiyi magana Umma ta dakatar dashi ' da cewa.
"Farook ' ka kyaleta , Ai tamayi k'ok'ari dole a d'aga mata k'afa don tana cikin damuwa!".
"Amma Umma ai ya kamata tayi breakfast ' for her own health".
Yaya Farook kallon ta yayi ' yayi k'wafa, Sannan ya tashi ya wuce d'akin shi ba tare da ya gama breakfast d'in ba.
Safeena kuwa kishi ya riga ya gama turnik'e ta yadda ya nuna damuwar shi akan ta sosai, Don kuwa ya riga ya bata labarin rayuwar shi ' da wadda sukayi tare da Fadwa a baya.
Hakan yasa Safeena jan tsaki ' tsakin da batasan zai fito fili ba, Da sauri Ilham ta kalle ta.
"Lafiya Safeena?".
"Me kika gani?".
"Tsaki kika yi!".
"Well.. am just worried about Farook's health too, Don ya tashi ba tare da ya gama breakfast ba."
"Oh! Ayya!."
Abunda Ilham tace kenan ' ta ajiye cup d'in hannun ta, Ta rik'o hannun Fadwa tana tausar ta akan ta daure tasha tea d'in ko kad'an ne.
Suna cikin haka ne ' sukaji anyi sallama, hakan yasa Fadwa yin saurin juya wa don taga waye.
Lubna ce ' a tsaye cikin pink d'in atamfa rik'e da wayar ta a hannu mai riga pink ' komai nata pink ta saka, Cikin hanzari Fadwa ta tashi ' ta k'arasa har inda take.
*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槡
*IG* *_@Bae_Seema鉂*
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*81-82*
Ogan ne ya nufo shi cikin sauri.
鈥淵a? Lafiya ka dawo a haka?鈥�.
Yaron nuni kawai yake yi da hannu ' dakyar ya iya bud'e baki ya ce.
鈥淲allahi Oga police ne a ciki鈥�.
Cikin tashin hankali ya juya ya kalli Lubna ' wacce ita ma duk a tsorace take, Zaro bindiga yayi ya nuna mata.
鈥淜in yaudare mu! ' kuma bazamu barki ba kema!鈥�.
Cikin tashin hankali Lubna tace.
鈥淓h na yarda ku kashe ni ' amma ku barshi da rai, Wallahi yana da mata...鈥�
Nan ya dage ya buga mata kan bindiga a goshi ' Lubna zube wa k'asa tayi cike da azaba ta dafe goshin jini kawai ke zuba.
Nan take yayi setin Yaya Khaleel ' zai harbe shi, Lubna ta d'ago da sauri tace.
鈥淣ooo! Please don't ' don Allah karka kashe shi pls...鈥�
Ko kafin ta gama rufe baki ' taji tassss!, Alaman harbi.
Police ne suka k'arasa cikin wajen da sauri ' Lubna ganin sune sukayi harbin hakan yasa tayi ajiyar zuciya, Tare da k'arasa wa wajen Yaya Khaleel tana k'ok'arin kwance shi.
鈥淜u ajiye bindigogin ku ' kada wanda ya motsa!.鈥�
Cewar inspector.
Yaran duk ajiye bindigan sukayi a k'asa ' shi kuwa ogan nasu rik'e yake da tasa yana setin Yaya Khaleel.
鈥淜afi k'arfin ka aje ne?鈥�.
Ganin yak'ine yasa ya harbeshi a k'afa , hakan yasa shi durk'ushe wa k'asa bindigan ta sab'ule daga hannun shi tare da sakin wani k'ara.
鈥淎hhhhhagghh鈥�.
Nan sauran police d'in da ke tsaye a wajen suka kwashe bindigogin ' sannan suka tarka ta 'yan daban waje ciki kuwa harda ogan nasu.
Lubna k'ok'arin taimaka wa Yaya Khaleel takeyi wajen ganin cewa ya mik'e sun fita daga wajen ' amma ta kasa kasan cewar yafi k'arfin ta.
Inspector d'in ne ya taimaka mata suka d'aga kafad'un shi suka jashi zuwa waje, Don kuwa Yaya Khaleel a wahale yake.
Abba da Yaya Farook ' da suke waje ne, Suka ga anata fito da 'yan daban hakan yasa su jin dad'i sosai, Cen suka ga an fito da Yaya Khaleel cikin hanzari suka nufo kansu.
Abba ganin halin da Yaya Khaleel ya shiga ne ' yasa k'walla ta zubo mashi a ido, karb'ar shi sukayi suka nufu mota dashi ' suka saka shi a ciki.
Lubna kuwa dake ta tare tare da goshin ta ' da yake jini ne ta cire d'ankwalin kanta ta d'aure wajen sannan ta nufi wajen motar ta.
鈥淏aiwar Allah! Bazaki iya driving da wannan ciwon ba yanzu! Ki shigo motar mu ' mu nifu asibiti baki d'aya鈥�.
Cewar Abba.
Haka ko akayi ' Lubna ta mik'awa d'aya daga cikin police d'in nan key d'in motar ta don ya buyota dashi.
Haka ta shige ta zauna tare da Yaya Khaleel ' suka ja motar suka nufi hospital, Su kuma police suka zarce station d'insu ' sai wanda Lubna ta bawa key d'in mota ne ke binsu a baya.
Bayan sun isa harabar asibitin ne ' d'an sandan nan ya fito ya mik'a mata key d'in sannan ya tari keke napep ya wuce, Yaya Farook ne keta kici niyar fito da Yaya Khaleel daga motar Abba ya shiga cikin hospital d'in yayi magana aka had'o shi da nurses guda biyu tare da keken da marasa lafiya ke zama akai.
Haka suka taimaka aka ciro Yaya Khaleel daga mota ' aka d'aura shi saman keken , Sannan suka tura shi zuwa ciki Lubna tana biye dasu.
Suna shiga aka basu d'aki anan ciki aka kwantar da Yaya Khaleel ' ita kuma Lubna suka tura ta d'akin wanke ciwo.
Bayan wuce warta ne likitan ya shigo ' suka gaisa da Abba cike da girma mawa , Sannan ya fara duba lafiyar Yaya Khaleel.
Sai da ya kammala tukunna ya juyo ya fuskan ci Abba da Yaya Farook.
鈥淎mma! Meyasa meshi haka? Kamar yayi dambe?鈥�.
Nan Abba ya fad'a mashi duk abinda ya faru ' haka likitan tayi mashi jaje, Sannan ya ce.
鈥淵anzu bari inje ' inturo azo a d'ibi jinin shi domin akwai buk'atar yin test鈥�.
Ok kawai Abba yace ' sannan likitan ya juya ya fice.
Motsi Yaya Khaleel yayi kad'an tare da cewa.
鈥淎 ina nake?鈥�.
Jin abunda ya fad'a ne yasa hawaye suka zubo wa Yaya Farook ' yayi sauri ya share, Sannan yace.
鈥淜haleel ' kana hospital ne yanzu haka, Allah ya tsiratar da kai鈥�.
Ajiyar zuciya Yaya Khaleel yayi ' ya ce.
鈥淚na Fadwa?鈥�.
鈥淜arka damu Khaleel ' bari yanzu inje in d'auko su鈥�.
Cewar Abba.
Haka Abba ya juya ' ya fice zuwa d'auko su Umma dake gida.
Bayan fitar shi ne ' Lubna ta shigo cikin ward d'in tare da Nurse d'in da zata d'ibi jinin Yaya Khaleel.
Lubna a tsaye ta tsaya ' saitin wajen gadon shi, Saida nurse d'in ta d'ibi jinin ta wuce ' tukunna Lubna tace.
鈥淚na Abba? ' ya kamata a sanarwa su Fadwa da Umma鈥�.
Ta fad'a tana kallon Yaya Farook.
鈥淓h yaje kiranshi鈥�.
鈥淥k! Ni zan wuce gida yanzu ' insha Allah zan dawo nan da 1week, bayan nayi aure kenan鈥�.
鈥淭o Lubna ' Allah ya kaimu, Gaskiya kinyi halacci ' kuma munji dad'i鈥�.
Smilling kawai tayi sannan ta juya ta wuce.
Bayan wuce warta tane da d'an mintoci Nurse ta shigo wajen rik'e da drip a hannun ta, Sai kuwa sakamakon gwajin jinin da akayi ta mik'awa Yaya Farook.
鈥淪aka makon gwajin da mukayi ' an gano cewa yana da malaria, Gashi nan yanzu zamu d'aura shi akan anti-biotics ' sannan kullun safiya za'a rik'a mashi gashi ma'ana za'a rik'a gasa mashi jikin shi da ruwan d'umi鈥�.
鈥淥k ' shikenan babu damuwa鈥�.
Nurse d'in juyawa tayi ' ta fara neman jijiya tukunna tayi setling d'in drip d'in a jikin shi, Ta juya ta wuce.
Tana fita ne su Abba suka iso cikin harabar asibitin ' cikin hanzari Fadwa ta bud'e motar ta fita ' ta falla a guje ta shige cikin hospital d'in.
Tana shiga ne aka tsare ta .
鈥淏aiwar Allah wa kike nema?鈥�.
鈥淒on Allah inane aka kwantar da wani ' yanzun nan mai suna Khaleel?鈥�.
Nan nurse d'in tayi mata kwatan ce, Haka Fadwa ta k'ara kwasa a guje ta shiga d'akin, Yaya Farook ganin yadda ta shigo ne tana haki ' yasa shi ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 20