"Damn it!, Kin raina ni ko?"
Ta girgiza mashi kai.
"Bakiga gown d'in da na ciro miki bane?"
"Yaya Khaleel wallahi ban gani ba."
"Kije tana nan saman gadon ki ' ki d'auka ki sa yanzun nan 5minutes na baki."
Cikin hanzari ta d'auki hijab d'inta ta wuce d'aki kai tsaye saman gadon ta nufa, Nan ta hau cire kayan ta ' sannan ta d'auki sleeping gown d'in ta saka a jikin ta.
Fadwa wajen madubi ta je ta tsaya ' tana kallon kanta.
"Tabdijam! Never in history! Wannan rigarce Yaya Khaleel zaice insa? Me ya d'aukeni to ' nasan ba wani abu bane amma gaskiya bazan iya sa rigar nan ba ' komai na jikina ya bayyana babu abinda ya b'oye , aiko abincin ma na hak'uri dama ba wani yunwa nakeji ba!!"
Zuwa tayi ta sa key a k'ofar ta sannan ta haye gado tayi kwanciyar ta da rigar a jikin ta.
Yaya Khaleel kuwa sai agogo yake kallo ' don ta haura lokacin da ya bata, Shuru yaji har yanzu ba zo ba.
"Lallai yarinyar nan ' ni zaki mayar d'an iska! Zanyi maganin stubborness d'in ki kuwa.!"
Zuba abinci yayi ' yaci sannan ya kashe kayan kallon ya wuce d'akin shi, Shirin bacci yayi cikin singlet da boxer ya kwanta ' tare da d'aga pillow ya d'auko wayar shi, Yayi dialing number d'in Lubna yaji switch-up ' nan yayi wulli da wayar gefen shi.
*AROUND 12:30AM*
Dukkan su babu wanda yayi bacci ' Yaya Khaleel juyi kawai yake yi saman gado sam ya kasa runtsawa, Tabbas yasan yana da buk'atar Fadwa a kusa dashi.
Fadwa itama kasa bacci tayi ' kasan cewar bata saba bacci ita kad'ai ba, tsoro ne ya lullub'eta ga uban yinwa data dame ta ' babu arzik'i ta sauko daga gado ta nufi parlor cike da tsoro, Plask d'in abincin ta gani a saman dinning table ' nan ta k'arasa wajen cikin hanzari ta bud'e abincin ta fara ci a yunwace.
Bayan ta gama ne ta fara tunanin yadda za'a yi ta kwanta ita kad'ai a d'aki, Mik'ewa tayi ta fara neman inda d'akin Yaya Khaleel ' wani d'aki ta murd'a taji a bud'e haka yasa ta shiga ciki kai tsaye.
Duhu Fadwa ta gani kasan cewar wutar d'akin a kashe take, Cikin duhu ta dinga lalube harta cinma gado ta haye ' Yaya Khaleel yana jin hawowar ta yayi shuru yaga iya gudun ruwan ta.
Bayan ta hau saman gadon ne ' ta ja blanket d'in da yake lullub'e dashi ba tare da ta sani ba, Yaya Khaleel yana jin haka ya sa hannu daidai saman kanshi ya kunna wutar d'akin.
Fadwa sai ganin haske tayi fauu ' tashi tayi ta zauna cike da tsoro suka had'o da Yaya Khaleel.
"Ke lafiya? Me kika zo yi a d'aki na?"
Yana maganar ya na kallon jikin ta ' ita kuwa ta ma manta kalar rigar da ke jikin ta saboda tsabar tsoro, Jin tayi shuru ne yasa shi janye blanket d'in shi da k'arfi.
"Oya! Fita mun a d'aki, Ko bakida naki ne?"
"Ina dashi..."
tayi maganar a sanyaye.
"To tafi d'akin ki, Ke zafin nan ma ko damun ki bayayi?"
"Yaya Khaleel don Allah ka barni in kwanta a nan! Please...."
"To bari in bar miki d'akin sai in koma parlor."
Nan idon ta ya cicciko da hawaye.
"Please Yaya Khaleel wallahi tsoro nakeji ' bazan iya kwanciya ni kad'ai ba."
Sauka yayi tare da d'aukan blanket d'in zai fita tayi saurin rik'e mashi riga.
"Yaya Khaleel please..."
Dawo wa yayi ya zauna ' tare da yin nazari sannan ya kalleta.
"Shikenan ba damuwa zaki iya kwanciya."
Dad'i taji sosai ' tare da yin ajiyar zuciya sannan ta kwanta shima ya kwanta, Fadwa runtse idon ta tayi gami da takure wa waje d'aya.
"Matso nan!"
Abinda taji ya ce kenan ' tayi banza dashi tamkar tana bacci..
"Bakiji ba ko? Shikenan tashi ki barmin d'aki na!"
Aiba shiri ta bud'e idon ta ' ta matsa inda yake.
"Ke wai da aljani kike kwance ne? Ki matso nace..."
Maganar ya k'arashe a sanyaye tamkar bashi ba, Bud'e ido tayi suna kallon juna ' ganin bata da niyyar yin abinda yace ne ' yasa shi janyo ta da hannun shi ya had'a ta da jikin shi yana jin d'umin jikin ta.
Sannan ya rufa masu blanket ' ya kashe wutar d'akin.
"Kince kinajin tsoro ko?"
Fadwa wata sassanyar murya taji yayi amfani da ita ' hakan yasa ta cewa.
"Uhm."
"Meye kuma Uhm? Ki amsamin da kyau!"
"Eh inaji."
"To sa hannun ki biyu ' ki rungume ni.."
"Na'am?"
Ta sake tambaya ' tamkar bata ji abinda ya fad'a ba.
"Kinji abinda na fad'a ai, so do what i say!!"
Fadwa hannu tasa ta rungume shi ' don tasan cewa bata da wata mafita bayan hakan, Yaya Khaleel rungume yayi sosai ' a haka bacci mai dad'i ya d'auke su.
*WASHE GARI!!!*
*_AROUND 8:00AM_*
Yaya Khaleel ' ya tashi daga bacci ' sauke idon shi yayi akan fuskar Fadwa ' wacce baccin ta kawai takeyi hankalin ta a kwance, Zame jikin shi yayi a hankali sannan ya yaye mata blanket d'in da ke jikin ta.
Yaya Khaleel sai da ya b'ata 5minutes yana kallon jikinta da irin rigar da ke jikinta, Sannan ya sauka daga gadon ya shiga bathroom yayo alwala.
Bayan ya fito ne ' ya ciro jallabiya ya sanya tukunna yayi sallah, Sallame warshi ce tayi daidai da farkawar Fadwa daga bacci ' jin ta tayi fayaya tamkar babu kaya a jikin ta ' hakan yasa ta bud'e idon ta a hankali ba tare da tayi kyakkyawar motsi ba.
Kallon jikin ta tayi ' sannan ta tuna da irin rigar da ke jikin ta, Wuf tayi ta tashi zaune a tsorace ' ji tayi an mata magana kamar daga sama.
"Ki tashi kije d'akin ki kiyi sallah."
Kunya ce ta rufe ta ' tayi sauri ta janyo bargo ta rufe jikin ta, Fadwa sauko wa tayi daga gadon a hankali zata wuce d'akin ta ya dakatar da ita.
"Ina zakije mun da blanket? Come on dawo ki aje mun abuna!"
Kwata kwata Fadwa jitayi bakin ta ya kulle ' babu abinda zata iya cewa, Haka ta yaye blanket d'in daga jikinta ta ' ta cilla mashi saman gado sannan ta juya ta wuce.
*_Kuyi hak'uri da wannan page d'in babu yawa, Don ba'a nan naso tsayawa ba kamawa tayi!!!..._*
*_Dedicated To My One And Only JAMEESHA!!! ' She mean alot to me!!!..._*
馃憚馃憚馃憚
[5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*57-58*
Yaya Khaleel binta yayi da kallo har ta b'ulle zuwa d'aki, Bayan Fadwa ta shiga d'aki ne ta fad'a bathroom tayo wanka tare da yin alwala ' sannan ta fito tayi sallah , Mik'ewa tayi nufi gaban mirror ta zauna ta fara gyara jikin ta.
Bayan ta gama ne ta tashi ' ta bud'e wardrope d'in ta ta ciro riga da skirt d'inki mai kyau ta saka a jikin ta gamida kashe d'auri, Tana cikin hakan ne taji ana k'wank'awasa k'ofa ' cikin hanzari ta bar d'akin ta nufi parlor ta bud'e k'ofar.
Ilham ce rik'e da kayan breakfast a hannun ta, Shigowa tayi cikin parlon cike da sababi.
"Kinyi aure amma mutum bazai huta ba?"
Murmushi kawai Fadwa ta bita da shi ' sannan suka zauna Ilham ta mik'a mata ledar da ke hannun ta.
"Gashi ' Milk ne da bread da sauran su aciki, inji Umma."
Mik'ewa Ilham tayi zata wuce Fadwa ta tsaida ita da cewa.
"Tsaya! Mu tafi tare ' ingaida Umma da Abba."
To kawai Ilham ta ce sannan suka fita zuwa sashen su Umma ' Ilham a parlor tayi zaman ita da Ige sannan Fadwa ta haura wajen su Umma ta gaishe su.
Bayan ta gaishe su ne ' ta dawo parlor ta zauna sannan suka gaisa da Ige.
"Y'an nan harkin gama cin amarcin naki ne?"
Cewar Ige,
"Hmm me kika gani?"
"Gani nayi harkin fara fitowa!"
Nan ta sunkuyar da kai ' Ilham tashi tayi ta matsa kusa da Ige.
"Ai Ige ' daga gani babu wani amarcin da sukaci, Ige Yaya Khaleel fa bak'in rai ne dashi wallahi."
Nan Ige tayi zuk'u tana kallon Fadwa.
"Y'an nan abinda Ilham ta fad'i gaskiya ne?"
Fadwa d'aga kai tayi alaman Eh, Sannan Ige ta sauke ajiyar zuciya.
"Lallai wannan shine daidai lokacin da ya dace tsarabar da nai miki ' ki fara aiki da ita."
Nan Fadwa da Ilham suka had'a ido, A tare su kace.
"Kamarya?"
Ige ta bud'e baki kenan zatayi magana Abba ya shigo parlon ' cikin hanzari.
"Fadwa tashi kije ki cema Khaleel ' ko ya manta akwai inda zamuje yau ne!"
To tace ' sannan ta tashi ta bar sashen cikin sauri, Ta na shiga sashen su ta iske shi a zaune a parlor cikin shadda blue yayi kyau sosai ' waje ta samu ta zauna ba tare da ya d'aga kai ya kalle ta.
"Ina kwana Yaya Khaleel?"
"Lafiya!"
"Amm... sorry na d'anje sashen su Umma ne na gaishe su ' so shine Ige ta tsareni."
Banza yayi ya kyale ta ' ya cigaba da kallon shi.
"Yaya Khaleel ' Abba ya ce na fad'a maka wai ko ka manta akwai inda zakuje ne?"
Jan tsaki yayi kad'an sannan ya mik'e tsaye ya fice, Fadwa bin shi tayi da kallo.
Tashi tayi ta d'auki kayan tea d'in ta nufi dinning table da su, Sannan ta wuce kitchen ta d'ebo ruwan zafi a plask ta ajiye ' nan ta zauna ta had'a nata tea d'in ta na sha kafin ya dawo ta had'a mashi nashi.
Fadwa ta na cikin haka ne ' Ilham ta shigo rik'e da y'ar k'aramar kwalba a hannun ta, Zama tayi tukunna Fadwa ta aje cup d'in tea d'in ta zo harabar parlor kusa da Ilham ta zauna.
"Yaya Khaleel ya fita ko?"
Cewar Ilham.
"Eh."
"To ga wannan ' inji Ige."
Ta mik'a mata kwalbar turare ' Fadwa ta karb'a.
"Ta ce duk idan lokacin kwanciya bacci yayi ne ' zaki shafa shi kad'an a saman k'irjin ki."
"To meye amfanin shi?"
"Oh my God! Nikam aida kin bari na gama bayani na ko?"
"Uhm! Shikenan ina jinki!"
"Yawwa, Bayan kin shafa shi ' to muddin yaji k'amshi turaren zaiji babu wacce yake sha'awa saike, Gaba d'aya zaiyi sanyi ' zaiji babu wacce yake so kamar ki!"
Ajiyar zuciya Fadwa tayi ' tare da juya kwalbar turaren cike da tsoro.
"Amma Ilham ' ni gaskiya inajin tsoro fa!, Kinga ance ba k'aramar wuya mutum ke sha ba ' kema kanki kinsani."
Wata harara Ilham ta watso wa Fadwa.
"Ke wai meye haka? Anaso a taimake ki ' kina wani butsarewa haba Fadwa."
"A'a nidai bana so ' karb'a ki maida mata abunta, A hakan nina son Yaya Khaleel yana sona."
"Oh Allah? A hakan ko? Amma karki manta fa ' yana da budurwa a waje, Saboda haka anan zan aje shi ' idan kinga dama kiyi amfani dashi ' idan kuma kinso ki yar."
Nan Ilham ta tashi ta kama haryat fita ' har ta kai bakin k'ofa ta juyo ta kalle Fadwa wacce ke ta nazari.
"Kuma banma sake shigowa sashen shi."
Fadwa murmushi kawai tayi ' sannan Ilham tayi wuce warta.
"Inma baki shigo ba ' aini zaki ganni ne ai."
Fadwa tashi tayi ta bar turaren anan wajen ta koma dinning table ta cigaba da shan tea d'in ta.
*AROUND 12:00PM*
Yaya Khaleel suka dawo gida ' shi da Abba, Abba ya wuce ciki ' shi kuma ya shige sashen shi, A zaune ya iske Fadwa ta na kallo TV.
Ganin shigowar shi ne ' yasa tayi saurin mik'ewa tare da yi mashi sannu da dawo wa, Yaya Khaleel bayan ya zauna ne ' Fadwa ta je ta had'o mashi tea don tasan yau kam ya wuni da yunwa.
"Yaya Khaleel ga tea d'inka ' kayi hak'uri ban had'a da wuri ba sabo..."
Bata kaiga k'arasawa ba ya katse ta da cewa.
"Banason dogon surutu plaese."
Karb'a yayi ' Fadwa ta koma ta zauna ' sama sama ya sha tea d'in tukunna ya aje a k'asa, Sannan ya jingina da jikin kujera.
"Amm... Fadwa Abba ya bud'e mun Company, Kuma Alhamdulillah yau ya kaini wajen na gani ' Amma sai nan da 1week zan fara aiki."
"Wow! Alhamdulillah! Yaya Khaleel gaskiya naji dad'i sosai kuma Allah yasa rai a kaiwa."
Amin ya furta ' sannan ya tashi zai wuce d'aki tayi saurin tsaida dashi.
"Yaya Khaleel to yaushe zaka kaini inga wajen?"
Tayi maganar a shagwab'e cikin sanyin murya.
"Bazaki je ba!"
Nan ta tashi ido cike da k'walla.
"Yaya Khaleel ' inaso inga wajen ne please!"
"To shikenan naji ' kar kuma ki dameni!"
Ya na fad'in haka ya wucewar shi d'aki.
Fadwa koma wa tayi zauna ta cigaba da kallon ta.
A ranar haka Fadwa ta k'arashi wunin ta ' bata sashin su Umma bata sashen ta.
*** *** *** *** *** *** ***
*WAJEN K'ARFE 6:30 NA YAMMA*
Bayan Yaya Khaleel ya dawo daga masallaci ne ' ya zauna parlor tare da ciro wayar shi yayi dialing number d'in Lubna, Yayi sa'a ringing d'aya tayi ta d'ago tamkar ta na da k'ishin shi.
"Baby!."
"Hm i was shock and surprise!"
"Well...don't be, Lubna you know that i missed you so much right?"
"Bawani nan! Bayan kanata cin angon cin ka ' ko zaka cemin baka kwanta da ita ba?"
Fadwa da ke bedroom d'in taji kamar motsin mutum a parlor ' haka yasa ta fitowa daga d'akin nata zuwa parlor don ta duba waye.
"Haba meyasa zaki rik'a fad'amun haka? Kema kinsan Lubna ba zab'ina bace and she's not my class really..."
Haka yayi dai dai ' da isowar ta parlor, Cak ta tsaya jin abinda yake fad'a haka yasa ta fahimci da Lubna yake waya.
Sai da ta jira ya gama wayar ' tukunna tayi gyaran murya, Da sauri ya juyo ya kalle ta.
"Dama kina ciki ne?"
"Eh."
Juyawa tayi ta koma d'akin ta ' ta zauna a bakin gado.
"Ni nasan dama ba sona kakeyi ba Yaya Khaleel ' amma insha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe."
Turaren nan ne ya fad'o mata a rai ' haka tayi zambur ta tashi ta nufi parlor, Sam ta manta da akwai Yaya Khaleel zaune a wajen ' kai tsaye ta nufi wajen inda ta san cewa nan ta saki turaren.
Ta na ganin shi tayi ajiyar zuciya ' tukunna ta d'auka ta juya ta zata koma d'aki ya tsaida ' haka yasa ga banta yayi mugun fad'uwa ta juyo ta kalle shi a sanyaye.
"Meye ne wannan? ' kika zo zaki wuce kamar baki ga mutum ba?"
"Babu komai ' fitsari nakeji shiyasa na ke sauri."
Tana fad'in haka ta juya ' ta wuce cikin sauri harda k'arawa da gudu, Tana shiga d'aki ta sa key ta kulle ' nan ta cire kayan jikin ta ta fad'a bathroom don yin wanka.
B'angaren Yaya Khaleel ' text yayiwa Lubna da Address d'in Company d'in shi don anan zasu koma suna had'uwa.
Bayan ya gama ne ' zai tashi ya wuce Ilham ta bud'o k'ofa rik'e da cooler d'in abinci.
"Yaya Khaleel Fadwa fa?"
"Tana d'akin ta."
Ok kawai ta ce ' sannan taje ta ajiye abincin saman dinning table ta zarce d'akin Fadwa.
Murd'a handle d'in tayi taji a kwulle.
"Kome takeyi oho!"
Ilham juyawa tayi ta koma sashen su.
*Dedicated To Seemaluv Novel Group 2*
馃憚馃憚馃憚
[5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*@I Proudly Dedicated This Page To My Sweet Bestie鉂�(JAMEESHA馃憚) "JAMEESHA! I Just Want You To Remember That ' You Will Forever Be In My Heart!!!" Jealous One's Can Die!!...*
*59-60*
Fadwa bayan ta fito daga wanka ne ' ta zarce gaban mirrow ta na taje gashin kanta, Sai da ta gama ne ta fara gyara jikinta ' ta hanyar shafa turaruka iri iri, Sai da ta kammala gyara jikin ta tsaf tukunna ta d'auko turaren da Ige ta bata.
Fadwa harta bud'e zata shafa sai kuma ta maida ta aje.
"Ba yanzu ba tukunna!"
Abinda ta fad'a kenan ta tashi ta nufi wardrope d'inta ta ciro rigar bacci Cotton ta saka ' iya gwiwa rigar ta tsaya sai dai kuma rigar armless ce (wacce ba dogon hannu ba).
"Duk rigunan babu na k'warai mtsww!"
Ta na cikin haka ne ' Yaya Khaleel ya k'wala mata kira, Cikin sauri ta amsa da na'am! ' sannan ta fito daga d'akin zuwa parlor.
Ta na isa harabar parlon ta ganshi zaune a dinning ' da alaman abinci yake so suci.
Fadwa k'arasawa wajen tayi ' cike da kunyar shigan da tayi, Sannan ta sami waje ta zauna.
"Yaya Khaleel gani!"
"Yunwa nakeji ' ki zo ki samun abinci."
Fadwa mik'ewa tayi ta zuba mashi nashi ta mik'e mashi, Sannan ita ma ta zuba nata ta fara ci.
Suna cikin cin abincin ne ' wayar shi ta fara ringing, Zai d'aga wayar kenan Fadwa ta rigashi d'aukar wayar.
"Lubna ko?"
Ido kawai ya zuba mata ' ba tare da ya ce mata komai ba.
"Toh ta bari saika gama cin abinci tukunna."
Yaya Khaleel abun d'aure mashi kai yayi ' ya tsaya ya na kallon ta cike da mamaki.
"Yaya Khaleel please eat your food! And stop bothering yourself about her."
Tana fad'in haka ta fiske ' tayi kamar ba ita tayi maganar ba.
"Fadwa kinsha wani abu ne?"
D'ago kanta tayi ta kalle shi ' sannan ta maida kanta k'asa ba tare da tace mashi komai ba ' tashi tayi zata wuce d'aki ya dakatar da ita .
"Ina zaki je? Kin gama cin abincin ne?"
"Yaya Khaleel ' kawai na k'oshi ne, Don naga kafi d'aukan Lubna da muhimman ci akaina ' ni da nake matar ka."
Jikin shine yayi sanyi ' jin abinda Fadwa ta fad'a sai duk yaji tausayin ta ya kamashi ' kuma tabbas bai kyauta ba.
"Well Ok je ki kwanta d'in."
Juyawa tayi ta wuce d'akin ta cikin sanyin jiki, Ta na shiga ta fad'a saman gado ' tunani kawai takeyi yadda ta zata samo kan Yaya Khaleel.
Fadwa tashi tayi ta nufi gaban madubi ' don ta sha turaren nan ajikin ta, Bayan ta d'auki turaren ne jikin ta na d'ar d'ar d'in shafawa ' ta fara kici niyar bud'e kwalbar ba ta ankara ba duk turaren ya gama watse mata a jiki.
"Subhanallah ' gashi ance kad'an ake shafawa!"
Abinda ta fad'a kenan ta aje kwalbar a saman mirrow ' ta janyo towel cikin sauri ta fara goggoge wa don rage turaren, Fadwa na cikin haka ne taji an rik'o hannun ta ' cikin tsoro ta d'aga kanta don taga waye.
Yaya Khaleel ne ' tsaye a kanta suna kallon kallo.
"Me kikeyi? inata kiran ki baki amsa ba?"
Fadwa had'iye miyau tayi da kyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 20