Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Cikin tsoro ' ta d'auki tissue d'in ta zara ta goggoge bakin ta. "Na share." "Ke am not joking ' ko sokike in tashi maki?" Ta girgiza mashi kai ' sannan ta matsa gaban mirrow d'in tana gogewa, ganin yak'i goguwa ne ta gane cewa lallai 24hrs ta shafa a bakin ta ' cikin fargaba ta juyo ta kalleshi suka had'a ido. "Yaya Khaleel ' yak'i fita amma don Allah kayi hak'uri bazan sake sawa ba." Nan take ya diro daga gadon ' gami da cewa. "No ai saiya fita yau d'in nan." A hankali yakeyo kanta ' tanaja da baya, Sai da yaji ya k'ureta a bango tukunna ya kamo k'ugunta. Ganin haka yasa Fadwa tsorata sosai ' k'ok'arin k'wacewa takeyi amma ta kasa ' Yaya Khaleel kuwa k'ok'arin kissing d'inta yakeyi amma tak'i bashi had'in kai. "Ke!" Ya daka mata tsawa ' cikin tsoro ta d'ago kai ta kalleshi. "Bazaki daina wannan fizge fizgen ba?" Hawaye kawai ke tsiyaya a fuskarta. " Ya Khaleel ' kayi hak'uri don Allah, ka barni in wuce ' bazan sake sawa ba i promise." Jikinta rawa kawai yakeyi ' hakan yasashi sakin ta cikin sauri, gami da juya mata baya. "Get out!" ya fad'a cikin tsawa, Fadwa sauri tayi ta fita cikin rawar jiki ' ta koma kitchen tana maida numfashi. Sunan ta taji ankira ' haka yasa tayi saurin juyowa, don ta duba waye. "Are you Okay?" ganin Yaya Farook ne yasa tayi saurin share hawayen ta ' tare da cigaba da had'a tea d'in. "Of cause." Ta fad'a a tak'aice sannan ta cigaba da abinda takeyi. Abin ne yabawa Yaya Farook haushi ' yasashi k'arasowa kitchen d'in cikin fushi. "Bazaki fad'amin abinda ke damunki ba!" Fadwa banza tayi ta kyaleshi ' ta zuba tea d'in cikin plast, sannan ta d'auka zata wuce ya rik'eta. "Ki fad'amun abinda ke damunki mana Fadwa.!" Nan ta d'aga kai ta kalleshi ' tare da ajiyar zuciya. "Ya Farook ' ni babu abinda ke damuna, kuka kuma da kaga inayi wannan tsakani nane da wanda zan aura." Tana gama fad'in haka ta fizge hannun ta ta wuce, ba tare da ta tsaya ko inaba ta wuce parlor ' ta ajiye plast d'in, sannan ta koma d'akin su don sanarwa Ilham. Tana shiga suka cikaro da Ilham tana k'ok'arin fitowa. "Thought ko baki gama shiryawan bane," Cewar Fadwa. Juyawa Fadwa tayi suka tafi parlon a tare, suka zauna a dinning table. Zaman su keda wuya ' su Umma da Abba suka shigo parlon, sai da suka zauna sannan Fadwa da Ilham suka gaishesu. "Yawwa Fadwa idan kin tafi School ' ki nemi permission subaki hutu, don yau nakeson a fara shirye-shiryen bikin nan." To kawai Fadwa ta iya cewa ' don kuwa sai yanzu ne takejin damuwa a cikin zuciyarta. A gaban idonta Umma ta d'aga waya ta fara kiran dangi tana sanar dasu bikina ' wata kunya ce tazo mata had'e da bak'in ciki, yasa tayi zambur ta tashi tsaye. "Ilham tashi haka nan ' wallahi lokaci ya k'ure mana yau." Tashi Ilham tayi ta d'auki cups d'inda sukayi amfani dashi sannan ta zarce kitchen ita kuma Fadwa ta wuce d'aki don d'aukar handbag d'inta da gele. Su Fadwa basu wani b'ata lokaci ba suka fita driver ya d'aukesu suka bar gidan zuwa school. Bayan driver ya sauke su a school ne ' suka shige class cikin sauri, duk d'aukan su akwai lecturer a cikin. Saida suka shiga suka iske aji kowa sharholiyar shi yakeyi, tukunna suka sami waje suka zauna. "Ilham kince zaki fad'amin yadda kukayi da Abba jiya." "Hm aikedai bari kawai ' Abba cewa yayi in fad'awa Al'ameen cewa yanason ganin shi, don idan akayi bikin ki da one-week za'ayi nawa." "Toh Allah ya kaimu ' but ninaso ace tare za'a aurar damu wallahi." Wata uwar harara Ilham ta watsama Fadwa ' haka yasa Fadwa darawa kad'an, sannan tad'an bigi kafad'anta. Suka cigaba da surutun su ' kafin wani malamin ya shigo. *** *** *** *** *Around 1:54pm* Fadwa ta mik'e tsaye daga seat d'inta ganin lecturer na ciki ne yasa ta d'auki permission d'in fita. Kai tsaye ta wuce Office d'i shugaban school d'in ta sanar da ita komai, sannan akayi signing wata takarda ' aka bawa Fadwa. Koda ta fito daga Office d'in ta iske antashi duk an watse, sai Ilham ne kawai dake tsaye a k'ofar class take jiranta. Cikin sauri ta k'arasa wajen ' ta karb'i handbag d'inta sannan suka nufi inda driver ke tsaye yana jiransu. Shiga motar sukayi a gajiye ' tukunna yajasu ya maidasu gida, saida sukaji yayi packing ' sannan suka fito daga motar suka nufi cikin gida. Fadwa na bud'e k'ofar parlon taji wani shock a jikinta cak ta tsaya a wajen ' don ganin yadda mutane suka cika parlon , Ilham abinne ya bata mamaki ganin yadda Fadwa ta tsaya awajen. "Ke don Allah meye haka ' ji yadda kikasa mutane sunata kallon mu," Ilham gaishe su tayi da hanya ' sannan itama Fadwa ta gaishesu, Ilham ganin Fadwa tak'i tafiyane yasa ta kama hannunta ta jata suka wuce d'akin su. Bayan shigarsu d'akine Fadwa ta fad'a saman gado cike da gajiya. "ai kwanciya bai gankiba tukunna." "Kamarya?" Fadwa tayi tambayar ta k'ok'arin gyara kwanciya. "eh tashi zakiyi muje mu gyara d'akin saukan bak'i , don nasan ba wani datti yayyi ba k'urace kawai, don wallahi bazan iya sharing toilet ba ' kina gani harda mutane k'auye akazo, yoo koma mutanen birnin nefa?!" Fadwa ajiyar zuciya ta sauke ' tare da cewa. "To nidai yanzu ki daure kije ki farayi ' don wallahi agajiye nake." "to naji." Har Ilham ta tashi zata bar d'akin, sai kuma ta tsaya gamida juyowa. "Yawwa Fadwa ya kamata fa ' muyi arranging yadda za'ayi KAMU." "Eh jeki dawo dai ' koma menene saimuyi magana akai koh." Ilham ficewa tayi daga d'akin don zuwa gyarawa bak'i inda zasuyita kara kainan su, Fadwa kuwa nan bacci mai dad'i ya d'beta. *Dedicated To My Fan's* *_Seemaluv the brave馃挭_*馃槣 [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 www.Seemaluv.wapka.me *47-48* *Around 4:00pm* Fadwa ta farka daga bacci ' tashi tayi cike da mik'a da hamma, a zaune taga Ilham tana karanta english novel. "Ilham bak'in nan sun tafi ne? Naji banji hayaniya ba." "Eh basu dad'e da wucewa ba amma zasu dawo gobe." Fadwa saukowa tayi daga saman gado ta nufi bathroom da niyyar yin alwala ' Ilham ta tsaida ita da cewa. "Fadwa guess what?" Juyowa tayi ta kalleta cike da tambaya a idonta. "Meye?" "Anan zaku tare!" "Kamarya?" "Yes ' Abba yasa a gyara muku d'ayan part d'in nan." Nan Fadwa tayi shuru nad'an lokaci sannan tace. "Koshh!" "Kosh kamarya ' ke wallahi don dai bakije kin duba bane, yafi wannan part d'in kyau." "Zan duba." Abinda Fadwa ta iya cewa kenan ta shige bathroom, Ilham ta cigaba da karatun ta. Umma ce ta shigo cikin d'akin nasu ta sami waje ta zauna sannan tace. "Ina Fadwa?" "Ta shiga bathroom." "To dama Yayan kune Farook ' yace kuyi masa addua jirgin shi zai d'aga yau." "Laaa Umma ' tun yau ya wuce d'in? Allah sarki Yaya Farook, aikam zamuyi ta yimashi addu'a. "Idan Fadwa ta fito ki sanar ita." To kawai Ilham tace cike da murmushi ' sannan Umma ta bar d'akin. Cikin d'an lokaci k'alilan Fadwa ta fito daga bathroom, Saida Ilham ta jira ta idar da sallah tukunna. "Fadwa kinsan kuwa Yaya Farook ya tafi?" Wani abune ya cokari k'irjinta ta rasa ko menene, Cike da mamaki ta juyo ta kalli Ilham. "Ya tafifa kikace! Zuwa ina?" "Bangladesh mana." Nan gabanta ya sake fad'uwa, nan take hawaye suka fara yimata zarya a fuska. "He left without even calling me! He left without telling me!! Ilham ki fad'amin wasa kikeyi please." Ilham tashi tayi tare da kamo hannunta suka zauna, Sannan Fadwa ta yaye hijab d'in jikinta. "Komai yai zafi ' to maganinsa Allah Fadwa, meyasa bazaki zama mai tawakkali ba?" "Ilham na yarda da k'addara kuma nina yarda cewa Yaya Farook ba mijina bane, amma Ilham meyasa zai tafi bai fad'amin ba? Meyasa?" Ilham sharewa Fadwa hawaye tayi ' cike da tausayawa." "Is okay Fadwa ' ni banga abin kuka ba anan, may be yanada reason d'in yin haka." Kai kawai Fadwa ta daga mata ' alaman Eh. "Hakane ' to yanzu kinsan me za'ayi Ilham? Mu tashi driver ya kaimu ' muje musa a fara buga mana invitation card d'in, hope dai akwai abinci?" "Eh akwai ' don naga bak'in nan sunyi kuma zaikai har dare." Yawwa Fadwa tace ' sannan suka tashi tare da rufe jikinsu da gele, suka fita wajen garage. Anan suka iske Yaya Khaleel a zaune yana shan iska da waya a hannu ' baima lura da suba, sannan suka nufi wajen driver kai tsaye. "Yawwa don Allah taso zaka kaimu wani waje." Cewar Ilham, Cikin hanzari ya tashi ' rik'e da car-key a hannun shi, ga bud'e motar suka shiga. Bayan shigar sune ' suka fad'a mashi inda zai kaisu. Basu suka dawo gida ba ' sai wajen *7:30pm*, sakamakon tsayawan da sukayi aka gama musu nan take. Bayan driver yayi packing ne suka fito, Ilham ta farajin fargaban shiga gida. "Wai don Allah miye haka kikeyi Ilham? Mun riga mun girma fa! Mu shiga kawai ninasan abinda zan fad'a tunda dai ga invitation cards a hannun mu." Haka nan dai Ilham ta yarda suka shiga cikin gida, shigar su parlor suka iske Umma da Yaya Khaleel ' a zaune ya wani had'e rai. Sallama sukayi a tare cike da ladabi. "Sannu da gida Umma." Cewar Fadwa, Yawwa Umma tace ' sannan suka d'auki hanya zuwa d'akin cike da fiskewa馃槑, Yaya Khaleel ya tsaida su. "Daga ina?" Fadwa ce ta juyo cike da tsoro ' sannan ta koma wajen Umma ta zauna gamida nuna mata invitation cards d'in. "Umma ' kinga abinda ya tsaida mu nan, inba haka ba wallahi da tuntuni mun dawo." Murmushi kawai Umma tayi ' cike da fara'a tace. "Amma ko kinyi dabara Fadwa ' za'aje a rabawa k'awaye kenan?" "Eh Umma' da yake muna so muyi wani event ne (*KAMU*), shiyasa." "To shikenan Allah ya kaimu." "Ameen.!" Abinne ya k'ufule Yaya Khaleel, cike da b'acin rai yace. "Babu wanda zai had'a wani party a gidan nan, Walima kawai za'ayi." Salati Fadwa ta shiga a cikin zuciyarta ' suka had'a ido da Ilham. "A'a bazaka hanasu yiba Khaleel, kaidai idan bakkada ra'ayi shikenan ' amma su zasuyi." Cewar Umma, Yaya Khaleel ' tashi yayi tare da cewa. "Umma ke kike goya masu baya ' suna raina mutum." Sannan yasa kai zai fita waje ' Umma ta tsaida shi. "Ina zakaje? Ko ina zakaje aikabari kaci abinci ko ' kafin ka fita." "A'a Umma ' akwai wacc..infact ma a restaurant zanci a binci." "Toh ai shikenan." Abinda Umma tace kenan ' sannan yasa kai ya fita, ita kuwa Fadwa a zuciyar ta cewa. "Ahab! Wajen wannan ballagazar zaije ' wai ita Lubna." Tana gama ayyana hakan ta mik'e tsaye da niyyar wucewa, Umma tace. "Fadwa ki kawomin abinci inci ' na farajin yinwa." To tace sannan sannan ' ta yaye gelenta ta mik'awa Ilham tare da Invitation cards d'in. "Don Allah wucemin dasu d'aki, ni bara inzarce kitchen kawai." Ehem ' Ilham tace sannan ta karb'a ta wuce dasu d'aki ita kuma ta shige kitchen. *** *** *** *** *** A kwana a tashi ' gashi yau saura kwana d'aya kacal, bikin *Fadwa&Yaya Khaleel*. Fadwa ce ke zaune a parlor ' tare da mai lallee, k'awaye zagaye da ita ' Ilhan kuwa tana gefe tana video Covering d'inta. K'awaye ko wacenta da shirinta tazo ' don kuwa *Around 4-5:00pm* za'a tafi KAMU. Haka aka gyara Fadwa ' tayi kyau sosai, sannan Ilham ta kira makeup artist ta zo taimasu kwalliya ta gani ta fad'a. *4:00pm* Lokacin tafiya wajen kamu yayi ' har wasu daga cikin k'awayen sun fara tafiya, Fadwa ta tashi ta nufi d'akin Yaya Khaleel. Bud'e k'ofar tayi without any tension, ta shiga tare da yin sallama ya amsa ba tare da ya kalleta ba ' ganin shi tayi daga shi sai singlet sai boxer. Fadwa tsayawa tayi daidai wajen k'ofa ' ita bata k'arasa cikin d'akin ba ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da y'an yatsunta. Jin shurun yayi yawa ne yasa ya d'ago kai ya kalleta ' Wow ya furta a cikin ranshi don ba k'aramin kyau tayi. "Lafiya?" "Yaya Khaleel ' dama lokacin tafiya wajen kamu d'in ne yayi, ti shine...." Ya dakatar da ita cikin fad'a,. "Karma ki k'arasa, angaya miki banda aikin yine? Nan k'walla ta ciko mata cikin idanuwan ta. "Yaya Khaleel please!!" "Fitarmun daga d'aki please hutawa nakeson yi." Juyawa tayi ' ta fita ba tare da tace komai ba, turo mashi k'ofa tayi sannan ta share hawayen ta ' ta wuce d'aki. Yaya Khaleel murmushi yayi har saida hak'aran shi biyu suka fito. Sannan ya fad'a bathroom don yin wanka. *Dedicated To My Fan's* 馃槣馃槣馃槣馃挭 [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 www.Seemaluv.wapka.me *49-50* Bayan ta shiga d'akine ta iske Ilham da wata cikin k'awayen nata ita kawai suke jira. "Yawwa sai muzo mu tafi ko?" Cewar Ilham, Nan suka sanyawa Fadwa mayafinta mai kama da net, sannan suka fito wajen garage ' dangi da y'an uwa kowa idon shi na kanta. Haka suka shige mota driver yaja ' suka tafi, Ilham kuwa sai aukin d'aukan hotuna take kamar ba gobe. "Wai ke baki gajiya ne Ilham?" "Tab ya za'ayi nagaji da d'aukar amarya hoto? K'awata, y'ar uwata, bugu da k'ari ma matar Yaya na!" Smilling kawai Fadwa tayi gami da girgiza kai. "Yawwa Fadwa ' kinsan gudun mawarda Abba ya bada kuwa?" "A'a." "Tow Abba ' ya zuba securities a wajen, sai wanda aka gayyata zai shiga wajen." "Wow, gaskiya naji dad'i kuma ina yiwa Abba godiya sosai." Suna cikin hakan ne aka isa wajen ' babban fili ne ankewaye shi da decoration gunun ban sha'awa, sannan suka fito daga mota suka k'arasa ciki. Haka aka kunna wak'a kala kala k'awaye suka kewaye Fadwa, ita kuwa babu abinda takeyi sai fara'a. Wuri yayi wuri ' Fadwa sai tashewa takeyi cikin k'awaye tare da Ilham. Suna cikin hakane ' Yaya Khaleel ya iso wajen dashi da ayarinshi maza, Yayi kyau sosai cikin milk d'in shadda da hula k'ube. Fadwa sauke idon ta tayi akan shi ' mamaki ya lullub'e ta, haka ya k'araso tsakiyar filin ba tare da yaje ya zauna ba ya rik'o hannun ta, nan kid'i ya cenja salo ' haka Yaya Khaleel ya rik'a juya Fadwa son ranshi, rawa sukayi sosai irin rawar turawa. Ita kanta Fadwa abin ya burgeta ' da yadda suka burge mutane, Ilham kunyace ta lullub'e ta yasa taja gefe ta koma ta zauna aka bawa Amarya da Ango fili. Zamanta keda wuya ' taga kiran Al'ameen d'in ta ya shigo cikin wayar, haka yasa ta mik'e ta matsa daga wajen tayi recieving call d'in. "Hello!" "My beauty kizo ki shigo dani ' ina inda kuke event d'in yanzu." "To" Kawai ta ce mashi sannan ta kashe wayar. "To waye ya fad'a mashi muna nan?" Abinda tace kenan ta tashi ta fita domin shigowa dashi. Tana kaiwa bakin gate d'in taja burki ta tsaya cak. "Wow!!" Ta furta a hankali cike da k'are mashi kallo, Al'ameen k'arasowa yayi kusa da ita gami da hura mata iska a ido ' tayi firgigit ta dawo hayyacin. "My beauty wannan kallo haka?" Murmushi kawai tayi mashi ' sannan suka koma ciki suka zauna. Ango da Amarya sunyi rawa kamar ba gobe ' saida suka gaji sannan suka koma suka zauna, aka fara basu hannun. Anfara shirye shiryen rufe wajen ne ' Ilham taja hannun Al'ameen suka keb'e. "Inaso muyi magana." "Okay." "My dear kaje ka sami Abba kuwa?" Murmushi kawai yayi mata sannan ya juya zai wuce ' ba tare da yace komai ba tayi saurin rik'e mashi hannu. "Kafad'amun." Juyowa yayi ya kalleta gami da kashe mata ido d'aya. "Karki damu, gwada ki kawai nayi ' naje kuma mun gama magana, Insha Allah nan da 1month za'ayi bikin mu." Ajiyar zuciyar tayi tare da yin murmushi kad'an. "Alhamdulillah!" Ta fad'a sannan suka koma wajen hole d'in, gani sukayi duk an watse babu kowa sai masu gadi. "Don't worry, muje in maidaki gida." Abinda taji ya fad'a kenan tabi bayanshi suka shiga mota ' suka bar wajen. *Around 5:56pm dot* Suka isa gida ' saida sukayi sallama da Al'ameen sannan Ilham ta shige cikin gida. Yau ma kamar jiya ' don kuwa mutane ne mak'il a cikin parlon, cikin su kuwa harda masu kwana. Saida ta gaishe su tukunna ta nufi d'akin su, k'awaye uku ne a d'akin wad'anda sukazo da niyyar kwana, Ilham waje ta samu ta zauna tare da masu ban gajiya ' saiga Fadwa ta fito daga bathroom d'aure da towel a jikinta rik'e da k'aramin towel tana goge gashin kanta da alama wanka tayi. "Ilham ' ina kika shiga ne d'azun mukaita neman ki babu ke?" Harara Ilham ta watsa mata ' tare da fincike d'ankwalin kanta ta aje agefe. "Kaji ta! To ina zanje kuwa? Meyasa to baki jira ni ba?" Ya tsine baki Fadwa tayi sannan ta wullar da towel d'in hannun ta saman gado. "Dad'in abun madai Yaya Khaleel ne yace a tafi a barki." "Ahh馃槷! Masu miji kenan! Nima ai nakusa yin nawa!" Nan gaba d'ayan su suka hau dariya, sannan Ilham ta mik'awa k'awayen nasu Camera d'in don suyi kallo ' itama ta tashi ta fad'a bathroom donyin wanka. B'angaren Yaya Khaleel kuwa ' sanye yake da towel shima, da alamun daga wanka ya fito direct wajen wardrope d'inshi ya nufa da niyyar ciro k'ana nan kaya wayar shi tafara ringing. Zuwa yayi ya duba ' sai yaga Lubna ce cike da murmushi ya d'aga wayar. "Hello babe how far?" "Don't baby me please ' Khaleel meka d'aukeni? Me kakeso ka mayar dani? Duk da baka gayyace ni zuwa event d'inka ba amma ai ankawomin video d'in har gida." "Wait let me explain!" Ya fad'a tare da samun waje ya zauna. "Explain what? Don Allah bana sonji Khaleel ' har kana wani mak'ale mata kana sunsunar wuyanta, for godsake what is all this? Ko kanaso ka cemin duk tsanar ce wannan?" "Lubna ki fahimce ni mana! Just inayi mata haka ne saboda yau ranar tane ' and she deserves to be happy." "To ni kuma fa?" "Please ki bari zamuyi magana zuwa anjima ' kar kisa komai a zuciyan ki, because ke da ita akwai banbanci yanzu."

Chapter 10 of 20