da addu'a, To gaba d'aya zai iya mantawa da ita."
Fadwa hawaye ne ya zubo daga idanun ta, Ta sa hannu ta share.
"Na gode sosai Ige ' ban san meyasa ba kwata kwata banason in rasa shi."
"Ai bazaki rasa shi ba y'an, Amma auren had'i ne tsakanin ku?"
Fadwa ta d'aga mata kai alaman Eh, Sannan Ige tayi ajiyar zuciya.
"Lallai a gaishe da Umman ku da aiki ' gaskiya ta raya zumunci, Kuma auren had'i babu abinda ya kaishi dad'i."
Suna cikin haka ne Ilham ta shigo d'akin rik'e da plate a hannun ta, Ajewa tayi a harabar d'akin ta koma ta kama k'ugu.
"Wannan dambun Allah yasa karya rik'a shak'e mutane, Ige nina tab'a ganin dambu haka zak'o zak'o?"
"Kaji ja'ira, ke ce ta farko da zakiyi santi."
Dariya suka kwashe da shi ' dukkan su, Sannan Ige ta bar d'akin zuwa kitchen don ta zuzzuba abincin.
Nan su Fadwa suka sauko k'asa suka fara cin abinci, Cen Fadwa ta d'an daka ta.
"Ilham please taimako!"
"Taimakon me?."
"Ki kaiwa Yaya Khaleel abincin shi ' wallahi idan naje bazai barni in dawo ba."
"Cifd'i aiko babu inda zani! Ga matarsa a kusa ' sai nice zaki ce inkai mashi abinci? Ayya kuwa Fadwa kina kula da shi yadda ya kamata?"
"Dalla cen banson iskanci ' in bazaki je bane kawai ki fad'amun!."
"Eh bazan je ba d'in."
Ajiyar zuciya Fadwa tayi ' gami da yin fuskar tausayi.
"Haba mana Ilham! Don Allah ki taimake ni ' ki kai mashi."
"Hahah! Idan anaso a moreka ansan ta inda za'a b'ullo su Fadwa."
Ilham tashi tayi ' ta nufi kitchen ta iske Ige ta zuba masa nashi a plate, Sannan ta d'auka ta nufi part d'in nasu dashi.
Ilham bud'e k'ofar tayi d'auke da sallamar ta a baki, Yaya Khaleel dake zaune a parlor ya amsa sallamar ba tare da ya d'aga kai ya kalle ta ba.
"Yaya Khaleel ga abincin."
"D'aura mun a kai."
Nan gaban Ilham ya fad'a, A zuciyar ta tace.
"Maida wuk'ar, karka huce kaina."
Wajen dinning table ta nufa ' ta ajiye mashi abincin, Sannan ta juyo zata fita ya dakatar da ita.
"Tana ina?."
"Wace?"
Harara ya watso mata ' nan fa baki ya fara rawa.
"Oh Fadwa? Ta na cikin gida ' abinci take ci."
"Kice mata ina kiranta!"
To kawai tace sannan ta fice cikin sauri ' Ilham tana shiga cikin gida ta nufi d'aki direct, Sannan ta zauna a k'asa.
"Yace kije yana kiran ki."
"To me zan masa?"
"Ha'a niko ya za'ayi in sani? Nidai kije kawai please, Don karma kice ban fad'a miki ba."
D'an tsaki Fadwa taja ' sannan ta gyara zaman ta.
"Nikam babu inda zanje ' ina nan, Don nasan babu abinda zan mashi a cen d'in a toh."
Yatsine baki Ilham tayi ' suka cigaba da cin abincin su.
馃憚馃憚馃憚馃憣
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*69-70*
Tana shiga suka had'e da Yaya Khaleel yana k'ok'arin fitowa.
"Baby nah?."
Ta d'ago kai ta kalle shi ' sam ta kasa b'oye damuwar da ke bayyane a fuskar ta.
"Yanzu na dawo daga masallaci ban ganki ba."
"Amm...Eh naje wajen su Umma ne."
Ta fad'i haka tare da k'arasawa ciki ta nemi waje ta zauna, Shima kusa da ita ya zauna yana kallon ta.
"Baby nah! Are you alright? Ko dai jikin ne?."
"No! Babu komai Sweetheart ' gajiya ce kawai."
"Ok ' to yanzu muci abinci tukunna ko?"
Kai Fadwa ta d'aga mashi alaman to, Sannan ta tashi gami da rik'e hannun shi suka nufi dinning table.
Sai da ya zauna tukunna ta juya ta wuce kitchen don d'auko abincin, Bayan ta fito daga kitchen d'in ne rik'e da tuwo da miya a hannun ta ' ta ajiye zata koma d'auko plates Yaya Khaleel yayi saurin rik'e mata hannu.
"Baby nah! Dawo ki huta haka nan ' ni sai inje in d'auko sauran kinga ba kyajin dad'i.
"No Sweetheart bara kawai in k'arasa ladar tawa."
"A'a kema kinsan bazan bari ba ' so kawai ki hak'ura ki dawo ki zauna."
Murmushi ta sakar mashi ' hakan yasa shi jin dad'i sosai, Ya tashi yaja mata kujera ta zauna ' tare da cewa.
"Yawwa Baby nah!."
Tukunna ya juya ya wuce kitchen d'in Fadwa ta bishi da kallo cike da murmushi.
Bai wani b'ata lokaci ba ya dawo parlor rik'e da plates a hannun shi da sarving spoon & spoon, Bayan ya zauna ne ' ya zuba tuwo da miyan a plate d'aya, Sannan ya fara kaiwa bakin shi.
"Ummm.... Yummy! Ashe dai na iya miya."
Da sauri Fadwa ta harare shi ' tare da turo baki.
"Na iya miya dai! Bayan kai burkawa kawai kayi? Kuma ma duk ka zubarmin da miyan!."
"Oho dai! Ai dai akwai hannu na aciki ko? To oya bud'e bakin."
Babu musu Fadwa ta bud'e baki ya fara feeding d'inta ' yana yi yana sawa a bakin shi shima, Sai da ya tabbatar ta k'oshi tukunna ya kyale ta.
"Baby nah! Nidai ban k'oshi ba tukunna sai na cinye tuwon tass."
"To ai gaka gashi ' daman don kai nayi shi ai Sweetheart, Kaga kuwa ai baza'ayi maka rowan shi ba."
"Baby nah ' kinsan mene ne? Gobe insha Allah zan kaiki hospital a dubamin lafiyar ki ' daga nan sai inkaiki saloon d'in ko?."
"To shikenan Sweetheart ' Allah ya kaimu."
Fadwa tashi tayi zata wuce d'aki ya tsaida ita.
"Ina kuma zakije?."
"Sweetheart ' rigar bacci zan sanya, zafi duk ya isheni."
"Haba Baby nah! duk da AC d'in nan?, Kuma ma aida kin bari sai anyi isha'i tukunna."
"Ok to bari ind'an watsa ruwan sanyi."
Fadwa d'akin ta tashige don yin wanka tukunna Yaya Khaleel ya had'a komai na wajen ya kai kitchen.
bayan ya dawo ne ya koma harabar parlor ya zauna, Nan wayar shi ta fara k'ara ' cikin hanzari ya cire ta daga aljihun shi ya duba, Ganin Lubna ce ke kiran shi yasa yayi rejecting call d'in cikin fushi ' tare da jan tsaki.
Lubna sake kiran shi tayi ' ganin zata dame shine yasa ya d'aga wayar.
"Wace irin mace ce ke?."
Daram taji gaban ta ya fad'i.
"Ni mace ce wacce ' mukayi rayuwa tare kuma muke k'aunar junan mu."
"Lubna meyasa baki da tunani? for God sake ' bazaki kyaleni inyi rayuwa ta ba.?"
"Khaleel ni kake fad'awa haka? Ni ce fa Lubna! Kana so kace min zaka watsar dani kenan?"
"Eh inaso ne kema kije ' kiyi aure ki hutawa rayuwar ki, Lubna kid'au ka rayuwar da mukayi a baya munyi ta ne a bisa kuskure ' kuma yanzu ne yakamata mu fara istigfari."
"Am i dreaming?."
Ta fad'a cikin rawar murya ' tamkar zatayi kuka.
"No you are not! Lubna ina cikin kwanciyar hankali da mata ta ' and i love her so much, Please try to understand ko dama cen kece kika cusa mun sonki ' tun banaso har kika saba min."
"No!!! Stop it please! I have had enough ' Khaleel zan so mu had'u face to face, Don wallahi ban yarda wad'an nan kalaman daga bakin ka suke fitowa ba..."
Ta fad'i haka cikin kuka mai tab'a zuciya, Haka yasa yayi saurin kashe wayar ' gami da cilla wayar saman kujera.
Yaya Khaleel mik'ewa yayi da niyyar shiga d'aki yaga Fadwa a tsaye tana kallon shi.
"Baby nah ' har kin fito wankan ne?."
Da sauri Fadwa ta k'arasa ta rungume shi ' cike da jin dad'i, Shima matse ta yayi da hannun shi.
"Sweetheart ' naji dad'i sosai! Hakane ya nuna min cewa lallai kana so na."
Bubbuga bayan ta yakeyi a hankali ' tukunna ya rabata da jikin shi suka zauna."
"Baby nah! Kiyi hak'uri da abunda ya faru a baya ' tabbas munyi zaman haramun da bid'ala tsakani na da Lubna, Yanzu ne ya kamata mu gyara kuskuren mu ' and am willing to do anything just to make you happy!."
Fadwa pecking d'in shi tayi a kumatu馃槉, Sannan ta koma ta lafe a jikin shi.
"Thank you Sweetheart ' Yaya Khaleel d'ina na kaina!."
D'an ture ta yayi kad'an, Hakan yasa ta d'ago kai ta kalle shi.
"Bana ce ki daina cemin Yaya ba? Ai gara ki kira ni da Khaleel d'in ma."
"Ahhh! Haba ba ba ba...wane ni? Babu girma kenan Sweetheart."
Murmushi yayi ' tare da d'ago fuskarta zaiyi kissing d'in lips d'in ta tayi saurin mak'ale bakin.
"Meye haka kuma?."
Girgiza mashi kai kawai tayi ' tare da bazo mashi idanu.
"Wannan d'in ma? A'a baki isa ba kuwa!."
Nan ya fara mata cakulkuli ' ta fara ihu cikin dariya, Ganin tana neman sik'ewa ne yasa tayi saurin cewa.
"Ahh ahaha!.. Sweetheart ' wallahi ji nayi an kira sallah shiyasa, Kaje Mosque kada alwallar ta karye."
"Kin sha! Amma ki bari in dawo ' sai bakin ki yayi tsini."
Tashi yayi ya fita zuwa masallaci ' idon ta na kanshi har ya fice bata daina murmushi ba.
"Huh! Allah na gode maka ' daka misanya min da Yaya Khaleel, Wanda a yanzu shi kad'ai kawai zan iya kallo inji sanyi a raina."
Tana gama fad'in haka ta tashi ta wuce d'akin ta ' har ta sanya hijab sai kuma ta cire.
"Anya? Alwallar nan bata karye ba? Bari dai kawai in cenja wata."
Bathroom ta fad'a tayo alwala tukunna ta fito ' ta sanya hijab d'inta ta tada sallah.
Bayan ta idar ne ' ta mik'e gami da cire hijab d'in, Sannan ta nufi madubi ta jawo kwalbar turaren nan ' ta zuba a tafin hannun ta tukunna ta mutsits-tsika shi ta shafa a jikin ta.
Fadwa sai da tabi ko ina na jikin ta ' ta shafeshi tass da turare, Tukunna ta bud'e wardrope ta ciro rigar bacci 'yar k'arama dai dai gwiwa ta sanya.
Sai da ta gama shirya wa ' sannan ta fito parlor kai tsaye taje ta kunna TV ta dawo ta zauna, Bata dad'e da zama ba Yaya Khaleel ya dawo daga masallaci ' sallama yayi Fadwa ta d'ago kai ta kalle shi tare da amsawa.
"Sannu da dawo wa!."
Ta fad'a tare da mik'ewa tsaye zata nufi kitchen.
"Duk ki gama rara gefen ki ' yau bazaki iya k'watar kanki ba."
A tsora ce ta juyo ' ta kalle shi tare da yin innocent face.
"Sweetheart kana magana ne?"
Sai da ya sami waje ' ya zauna sannan ya ce.
"A'a da kaina nake magana!."
Yaya Khaleel ya fad'i haka tare da watso mata wani irin kallo, Fadwa juyawa tayi ta wuce kitchen d'in gaban ta na d'ar d'ar, Fridge ta bud'e ta d'auko roban youghout mai sanyi ' sannan ta juya ta dawo parlor tayi zamanta suka fara kallon kallon.
"Baby nah ' inzo ki bani?."
A tsora ce ta kalle shi ' don tasan ba komai ke jan shi haka ba, Illa turaren da ta sanya.
"Ko bazaki bani ba?."
Fadwa kasa magana tayi ' sai dai ta tsinci kanta da girgiza mashi kai.
Murmushin mugunta Yaya Khaleel yayi ' tare da mik'e wa tsaye yana takowa a hankali inda take zaune, Hakan yasa Fadwa tayi wuff zata tashi gudu ' ya dank'ota da hannu d'aya.
"Sweetheart bacci nakeji.?"
Waro idon shi yayi' cike mamaki.
"Bacci? Haba! Aiba yanzu ba tukunna."
Juyawa yayi ' yaje ya sanya key a k'ofa, Sannan ya dawo ya d'auke ta cak tamkar wata baby ' yayi d'akin shi da ita a hannu.
Yaya Khaleel a saman gado ya a jeta ' tare da cewa.
"Ki fara addu'o'i kafin in kashe TV in dawo."
Had'iye miyau Fadwa tayi da kyar don kuwa duk tsoro ya gama cika ta ' sannan ya fice, Bai wani b'ata lokaci ba ya dawo ' a zaune ya iske ta kanta a sunkuye.
Yaya Khaleel k'arasa wa yayi kusa da ita ya zauna ' ya fara sunsunar ko ina na jikin ta, ganin hakan ba zaiyi satisfying d'inshi bane yasa shi kwantar da ita saman gadon ' sannan shima ya haye.
Fadwa hannu biyu tasa ta tallabo fuskar shi ' cikin sanyin murya tace.
"I love you so much ' Sweetheart..."
"love you more Baby nah..."
Ni *Seemaluv* hannu naga Yaya Khaleel yasa ya kashe wutar d'akin, Hakan yasa na tattara 'yan komatsai na ' na koma parlor na yada zango kafin gari ya waye.
*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:57 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*_@Dedicated To All Members Of PURE MOMENTS OF LIFE WRITERS, I like you gurls so muah馃拫, And To My Dearest JAMEESHA ' ban manta dake ba..._*
*71-72*
*Washe gari*
*AROUND 6:30AM*
Yaya Khaleel ya tashi ' zame jikin shi yayi daga jikin Fadwa wacce baccin ta kawai takeyi.
Bathroom ya shiga yayi wanka tare da d'auro alwala tukunna ya fito ' yayi sallah.
Bayan ya idar ne ' ya tashi ya fara shiri cikin manyan kaya shadda milk colour, Fadwa bud'e ido tayi gami da tashi zaune cike da murza ido.
"Sweetheart ' ina kuma zaka je kake ta shiri da sassafe haka.?"
"Baby nah ' zan lek'a office ne yau, am sorry ban fad'a miki jiya ba!."
Nan ta sauko cikin sauri ' ta rungumo shi ta baya.
"Good morning!."
"Morning Baby nah!."
"Yanzu bari inyi sallah ' sai muyi breakfast ko?."
Ok kawai ya ce ' ya cigaba da sanya battle d'in wuyar rigar shi, Sannan Fadwa ta juya ' ta wuce d'akin ta.
Tana shiga ta cire rigar baccin jikin ta ' ta sanya towel tukunna ta shige bathroom don yin wanka ' tare da yin alwala.
Bayan ta fito ne ta sanya T-shirt ' tare da d'aura zani cikin sauri ta wuce kitchen ' ta fara had'a musu abinda zasu karya dashi.
Sai da ta kammala ne ' ta fito daga kitchen d'in rik'e da cup guda biyu a hannun ta, Tea ne a ciki mai kauri ta ajiye a dinning table ' sannan ta juya ta nufi d'akin Yaya Khaleel.
Fadwa shiga tayi cike da sallama ' ya amsa rik'e da waya a hannun shi, Sannan taje kusa dashi ta zauna.
"Sweetheart ' gafa breakfast d'in cen."
Ok ya ce ' tare da duba wristwatch d'in hannun shi ya ga 7:00am, Tukunna ya tashi tare da rik'e hannun ta suka k'arasa parlor.
Yaya Khaleel kujerar dinning table d'in yaja ma Fadwa ta zauna sannan shima ya koma ya zauna.
"Baby nah? "
Ta d'ago kai ta kalle shi ' cike da fara'a.
"Tea haka zalla? Ko bread babu?."
"Sorry Sweetheart! Kaga ai laifin ka ne ' inda ka sanar mun tafiyar ka office yau aida tun jiya da daddare na aiki mai gadi ya siyo bread d'in."
"Haka ne fa!!."
"Tea d'in da kauri ai, zai iya rik'e maka ciki har ka dawo.!"
Murmushi kawai yai mata ' sannan ya d'auki cup d'in tea d'in ya fara kaiwa baki.
"Sweetheart k'arfe nawa zaka dawo?"
Fadwa tayi tambayar ' tare da kurb'a tea a bakin ta.
"K'arfe 6:00pm zan dawo.
Nan take ta sark'e, Cikin hanzari Yaya Khaleel ya taso daga kujerar shi ' ya yo kanta gami da tallabo ta yana hura mata fuskar ta da bakin shi.
"So sorry ' Baby nah, me yayi zafi haka?."
Da kyar Fadwa ta sami damar cewa.
"Kaine ai!."
"Nine me?."
Cewar Yaya Khaleel.
"Kai kasa na sark'e!."
"Baby nah ' am sorry to, Ko sai na kawo ruwa ne?"
Girgiza mashi kai tayi ' sannan ya koma ya zauna.
"Nifa gaskiya ' 6:00pm, yayi yawa."
"Wasa nake miki ' 2:00am zan dawo, Saboda haka maida wuk'ar."
Murmushi tayi cike da jin dad'i, Suka cigaba da shan tea d'in.
A tare suka gama breakfast ' tukunna Yaya Khaleel yasake duba lokaci yaga wajen 8:30am, Nan ya mik'e tsayi tare da cewa.
"Baby nah ' zan makara da yawa."
"Alright Sweetheart..."
Fadwa tashi tayi gami da kama hannun shi ' suka nufi bakin k'ofa, Yayi pecking馃槉 d'in ta.
"Am blushing, Sweetheart hope baka manta komai ba."
"A'a, Phone d'ina na jiki na ' documents kuma suna office."
"Tohm here you go...Allah ya kare min kai."
Ameen yace ' sannan ya juya ya wuce, Yaya Khaleel har ya kai bakin mota ' ya laluba aljihun shi babu key, Hakan yasa shi juyawa ya koma.
Fadwa k'ok'arin d'aukan cups d'in da sukayi using dashi takeyi ' Yaya Khaleel ya shigo.
"Baby nah!."
Juyowa tayi ta kalle shi ' cike da mamaki.
"Duba min key d'in mota a d'aki na."
Cikin hanzari ta juya ta nufi d'akin nashi, Fadwa bata wani b'ata lokaci ba ' ta kawo mashi key d'in.
"Thanks ' and ki kulamin da kanki."
Ok Fadwa tace ' Sannan Yaya Khaleel ya fice yaja mota zuwa office.
*** *** *** *** *** ***
Bayan Fadwa ta gama kintsa parlon ne ' ta shige d'akin ta ta shirya cikin red atamfa ' riga da skirt d'auke da makeup a fuskar ta.
Turare ta fesa mai suna *MISS HOT* ' Sannan ta fito zuwa sashen su Umma, Fadwa shiga tayi d'auke da sallama a bakin ta ' Ige ta amsa kasan cewar ita kad'ai ce a parlon.
"Ina kwana Ige?"
Cewar Fadwa.
"Lafiya k'alau 'yan nan."
"Ige ' Umma da Abba fa? sun tashi kuwa?."
"Eh Umman ku dai ' yan zun nan ta haura d'akin ta, Amma Abban ku nina kwana biyu banji motsin shi ba!."
"Ok! Bara inje ' in gaishe ta."
Fadwa d'akin Umma ta nufa ' Ige na binta da kallo, Bayan shigar ta ne ' ta iske Umma a zaune a bakin gado tana waya, Sai da ta tsaya Umma ta gama wayar ' sannan ta duk'a k'asa ta gaishe ta, Umma amsawa tayi cike da kamala.
"Amm... Umma Abba na nan kuwa?."
"Aff! Bakisan yayi tafiya ba ko?."
"A'a."
"Jiya yayi tafiya zuwa garin bauchi ' next week zai dawo."
"To Allah ya dawo dashi lafiya!."
"Ameen."
Abinda Umma tace kenan ' Fadwa ta juya ta wuce zuwa d'akin Ilham.
Fadwa bayan ta sauko k'asa ne taga Ige still kallon ta takeyi ' hakan yasa ta nufi d'akin Ilham kai tsaye, A zaune ta iske Ilham tana waya ' daga ji kasan da Al'ameen take waya.
Fadwa samun bakin gado tayi ta zauna ' har sai da Ilham ta gama tukunna tace.
"Ilham ni banga ana preparation d'in komai ba!."
"Na d'aura tafashen shinkafa ne ' ke kuma sai kiyi miya.!
"Ok! Ai tashi zakiyi muje kitchen d'in."
"To naji muje ' ni karkuma ki takura mun."
Harara Fadwa ta sakar ma Ilham ' cikin zolaya suka tashi suka nufi kitchen.
Fadwa blending kayan miya tayi ta d'aura sanwan miyan, Sannan Ilham ta sauke shinkafan ta wanke ' ta sake maida ta saman electric.
Bayan sun gama ne ' suka suka koma parlor suka zauna tare da Ige ' suna kallo.
*AROUND 12:00PM*
Su Ilham suka kammala komai ' sai da Fadwa ta d'aban ma mijin ta nashi tukunna, Suka jera abincin a dinning table ' suna zaman jirar dawowar Yaya Farook.
Suna cikin haka ne Umma ta sauko parlon ' ta same su zaune suna a harabar parlor.
"Har kun kammala ne?"
"Eh Umma ' mun kammala komai shi kawai muke jira, Hope dai da wuri zai shigo!."
Cewar Fadwa.
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 20