ma Lubna izni data shiga su tafi ' seat d'in gaba ta bud'e ta shiga.
Tunda suka fara tafiya babu wanda ya ce Uffan ' kowa sak'e sak'e kawai ya keyi a ranshi.
A bakin gate d'in gida ya tsaya shi bai kaiga shiga ba,
"My love, restaurant d'in nan zaka mai dani, don mota ta tana cen."
Cewar Lubna,
"Ku kuma ku k'arasa ciki bara in maida ta,"
Ilham ce mai k'arfin halin cewa to, sannan suka fito suka shige gida ' shi kuma ya juya domin maidata restaurant d'in.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*39-40pages*馃尮
Yana shiga, ya iske ta a kwance ' duk'unk'une cikin blanket, sautin kukan ta kawai ke yi mashi zarya a kunnuwan shi.
Samun waje yayi ' ya zauna a bakin gado ' dai dai Fuskarta, sannan ya yaye bargon ' nan ne Fadwa tasan da mutum a cikin d'akin, hakan yasa tayi saurin d'aga kanta ' ta kalle shi,
"Meyasa kikeso ' kiyiwa kanki horo da yunwa? ko kinaso ' wani ciwon ya kamaki ne?..."
Yayi maganar cikin sanyin murya ' Fadwa tashi tayi ta zauna, tare da had'e kanta da gwiwa,
"Yaya Farook, zan cigaba da hora kaina da yunwa ' kuma zanyi k'ok'arin ganin ciwo ya kamani, ciwon ma na zuciya ' saboda na tabbata haka kake buk'atar gani, "
Ta fad'a tare da d'ago kanta, tana kallon cikin kwayar idon shi ,
"Fadwa, hak'uri shine abinda ya dace damu ' bayan wannan babu wani abunda zamu iyayi, kuma inaso daga yau ' ki d'aukeni a matsayin Yaya Farook d'in da kika sani ,"
Yana gama fad'in haka ya juya ' ya share hawayen da ke shirin zubo mashi a fuska, bai ankara ba ' yaji ta rik'o mashi hannu, a hankali ya juyo ' ya kalleta,
"Please Yaya na, promise me that ' bazaka tafi ka barni ba, zaka tsaya tare da ni ' a cikin *BABBAN GIDA*, "
Nan take ' yaji wani mugun tausayin ta ' ya kamashi, zuciyar shi rugugi kawai take mashi ' hakan yasa yayi saurin tallabo fuskarta.
"I promise you that ' k'anwa ta, insha Allah bazan tab'a barin ki ba."
Nan yasa hannu ' ya share hawayen da ke fuskarta,
"yanzu ' inaso ki tashi muje parlor, ki ci abinci kuma kiyi walwala kamar kowa."
To kawai ta ce mashi ' sannan ta hanzarta ' ta sauko daga saman gadon, suka fito d'akin a tare.
Kai tsaye ' suka zarce wajen dinning table, Fadwa ta zauna kusa da Ilham ' tukunna shima Yaya Farook ya sami waje ' ya zauna, sannan Ilham ta mik'e ta zuba mata abinci.
Tunda Fadwa, ta zauna ' Yaya Khaleel keta satar kallon ta, yana son tambayar ta dililin da yasa take kuka ' ita kuwa ko a jikinta, abin cin ta kawai takeci ' kasan cewar Yaya Farook ya tausasa mata zuciya.
Bayan sun gama ' cin abincin ne , ta tashi ta wuce d'akin su, Ganin haka ' yasa Yaya Khaleel shima ya tashi zaibi bayan ta,
"Ina zakaje?"
Cewar Umma,
Tsayawa yayi ' yana kallon plate d'inda ke gaban shi,
"Umma d'akina zanje fa!"
"Allah ya baka sa'a , kuma ka cigaba dayin abinda kaga dama Khaleel ' shigowar Abban ku kawai nake jira."
Had'iye miyau yayi dak'er, har ya juya ' zai tafi sai kuma ya tsaya,
"Umma, ko wani laifin akace nayi?"
"Khaleel, tambaya ta kakeyi?"
Nan ya sunkuyar da kai ' gami da sosa kanshi,
"A'a Umma kawai dai..."
"To ka bari ' sai Abban ku ya dawo, sannan kaji laifin da ka aikata ' kuma ka wuce ka bani waje,"
Tana gama fad'in haka, Yaya Khaleel ya nufi d'akin su Fadwa kai tsaye, Yaya Farook kuwa fita yayi ' ya shiga mota yayi tafiyar shi.
Jin gidan babu dad'i ne yasa ' Ilham kunna TV donyin kallo. Bayan shigan ' Yaya Khaleel d'akin ne ya iske Fadwa tsaye, wajen window ta na kallon waje ' daka ganta zaka fahimci cewa lallai tana cikin damuwa,
"Meyasa meki Fadwa?"
Maganar ce tazo mata ' zuwan bazata, haka yasa tad'an razana kad'an, sannan ta juyo ' ganin Yaya Khaleel ne yasa ta b'ata rai, ta juya ta cigaba da fuskantar window.
Murmushin gefe yayi ' sannan ya tako har inda take, tare da tallabo fuskarta ' da hannu biyu, suna fuskantar juna.
"Why are you ignoring me? Ko nayi wani laifin ne ' ban saniba Fadwa,"
Harara ta watso mashi tare da kauda ' fuskarta daga hannun shi, sannan ta ja tsaki ' ta juya zata wuce, yayi saurin janyo ta cikin zafin nama ' tare da had'a ta da bango, nan ta saki wani k'ara.
"Ahhhggh,"
Matse ta yayi sosai ' ga irin rik'on da yayi mata a hannu, nan da nan ' idanun ta suka ciko da hawaye,
"Yaya Khaleel, you're hurting me.."
"Ni zakiyiwa tsaki?
Cikin kuka ' tace,
"A'a.."
Nan ya saketa ' suka koma suna maida numfashi, daga bisani ya juyo ' ya kalleta.
"idan kin gama kukan ' kizo d'akina ki sameni,"
Fita yayi ' ba tare da yajira abinda zata fad'a ba, Fadwa komawa tayi ' ta zauna gefen gado, ta share hawayen ta ' sannan ta tashi ta d'aura towel, ta fad'a bathroom donyin wanka.
*** *** *** *** ***
*Around 5:30pm*
Fadwa ta fito parlor ' cikin doguwar riga, english wears ' gown ce a jikin ta, ta zauna a jikinta sosai ' don shape d'in jikin ta gaba d'aya ya fito.
Ganin babu kowane a parlon ' yasa ta nufi kitchen kai tsaye, tare da kwala wa Ilham kira.
"Ilham!!!"
"Na'am Fadwa, ina kitchen." Haka yasata k'arasawa cikin kitchen d'in cikin sauri,
"Me kike girka mana ' don nasan dai akwai abincin dare."
"Kin manta ' nace miki yau zanyi bak'o Fadwa?"
"Ayya! sam na manta ' to k'arfe nawa yace miki zaizo? "
"Zaizo around ' 8pm,"
OK kawai Fadwa tace ' sannan ta bar kitchen d'in, ta nufi d'akin Yaya Khaleel ' knocking k'ofar tayi taji shiru, kawai ta bud'e ta shiga .
Shigarta yayi daidai ' da fitowar shi, daga bathroom d'aure da towel a jikinsa ' da alama wanka yayi, ganin haka yasa tayi saurin juya mashi baya.
"Am sorry ' I didn't know that you were naked!"
Ta fad'a, haka yasa shi juyowa ' a 360 cike da mamaki, sakin baki yayi yana kallon ta ' sannan ya maida kallon shi ga jikinshi,
"Naked???"
Nan ya b'ata rai, a zuciyar shi yace,
"lallai ' wannan yarinyar y'ar rainin wayo ce, wato tsirara ma nake ' a haka kenan, Lallai zan koya miki hankali."
Ya fad'a a zuciyar shi tare da jan tsaki ' sannan ya kalleta,
"Sai yanzu kikaga damar zuwa?"
"wanka nayi shiyasa..."
Nan ya tsaye yana k'arewa halittar ta kallo, sun b'ata minti 5 a haka sannan yayi gyarar murya.''
"Ke! Wane irin iskanci ne ' wannan? Bayanki nakeson gani kokuwa gabanki?"
Maganar ce tayi mata wani ' ga tsaitsai,
"Yaya Khaleel, nifa ba y'ar iska bace ' taya kakeso in kalle ka, bayan babu riga a jikin ka?"
K'arasowa yayi kusa da ita, sannan ya juyo da ita ' da k'arfin tsiya, take ta runtse idon ta gam gam.
"Zaki bud'e idonki kokuwa saina miki abinda zaki dad'e kina tuna shi, acikin ranki!"
Banza tayi ta kyaleshi ' ba tare da ta bud'e idon ba,
"Kinaso kicemin ' kwalliyar dama ba donni kikayi ba, ko kuwa mene?"
"Yaya khaleel, nidai kayi hak'uri but i can't..."
Bata k'arasa maganar ba ' taji saukar lips d'inshi a kan bakin ta, hakan yasa ta bud'e idanun ta cike da tsoro, k'ok'arin kwace wa takeyi ' amma ya riga yaci k'arfin ta.
Jin jikin ta na rawa ne ' yasa shi kyaleta, amma sam bai yarda ya rabu da jikinta ba ' ninshi kawai takeyi sama sama,
"what? Don't you love me? Didn't you feel me? Fadwa ' nasan kina sona ai ko, but ni bana....."
Jin haka yasa ta dawowa hayyaci ta ' cikin d'an k'ank'anin lokaci,
"Yaya Khaleel, abinda kaimun ' Allah ne kawai zai sakamin, kuma inaso ka sani cewa ' wannan maganar ' da kayi Insha Allah saikayi dana sani, "
Nan ya ture ta ' ta zube a k'asa.
"Wai don nayi kissing d'inki, shine kike fad'amin wannan magan ganun ' to bari kiji in fad'a miki, nayi kissing d'in y'am mata da dama, wad'an da suka fiki, kuma daga k'arshe sukemin godiya ' why not kema kiyi godiya , and stop pretending!"
Nan ta tashi ' cikin sauri ' ta bar d'akin, kai tsaye ta wuce d'akin ta fad'a saman gado, wani wahalallan kukane yazo mata mai sauti ' cike da tausayawa kanta.
*Dedicated To My Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_PERFECT_* *_WRITERS_* *_FORUM_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
*_I_* *_dedicated_* *_this_* *_page_* *_to_* *_all_* *_members_* *_of_* *SEEMALUV'S* *NOVELS* *GROUP*
*37-38* *pages*馃尮
Suna shiga ciki ' suka iske Umma a zaune saman kujera tana kallo, bayan sun gaishe tane suka juya da niyyar wuce wa d'aki Umma ta tsaida su,
"Ina Khaleel d'in? "
Ilham ce ta kalli Fadwa ' wacce kanta yake a sunkuye,
"Ha'a wai baku nake tambaya ba?"
"Umma yaje maida budurwar sa gida, "
Cewar Fadwa,
"Wace irin budurwa kuma ' babu dad'in ji, "
Nan Ilham tayi saurin shiga maganar ,
"Eh Umma budurwa! Umma wallahi ba kiga yadda ya wulak'anta Fadwa ba, harda cewa wai zab'in kune amma bashi ya ce yana sonta ba...."
Nan Umma ta dakatar da ita cikin fushi ,
"Naji, ya kuma isheni haka nan ' kuma shi Khaleel d'in zai dawo ya same ni, ku tashi ku shiga ciki."
Mik'ewa sukayi a tare suka wuce d'aki, bayan shigar su ne Fadwa ta sami waje ta zauna ' sannan ta maida kallon ta kan Ilham,
"Ilham dama akwai maganar da nakeso in fad'a miki, amma please kada kid'auke ta da wani fuska daban."
Cikin zumud'i Ilham ta ce,
"No wait! bari in fara fad'a miki wani albishir tukunna,"
To kawai Fadwa ta ce ,
"Fadwa yau zanyi bak'o na musamman, "
"Wow! Kardai kicemin dashi za'ayi,"
"Kwarai kuwa , Insha Allah shine mijin Aure na."
Girgiza kai Fadwa tayi cike da dariya ,
"Ameen, to meye sunan sa?"
Wara idanu Ilham tayi gami da juya su ' tukunna ta ce,
"Sunan shi Al'ameen."
Nan Fadwa ta buga uban ihu ' cike da jin dad'in sunan ,
"Insha Allah ' sunan d'a na kenan na fari, "
Murmushi kawai Ilham tayi tace,
"To fad'amin abunda zaki fad'amin yanzu, "
Nan Fadwa ta d'anji jikin ta yayi sanyi, sannan ta rufe ido ta fad'a mata duk abinda ke tsakanin ta da Yaya Farook. Ajiyar zuciya Ilham tayi ' cike da tausayawa soyayyar su,
"Fadwa ba laifinki bane ' laifin Yaya Farook ne da baiyi saurin sanarwa ba, kuma inaso kiyi hak'uri ki cire shi amatsayin masoyi ' don na tabbata bazai aure kiba, kuma yanzu dole zaki jajirce don ganin kinsamo kan Yaya Khaleel ' don kuwa shine mijin auren ki.!"
Ajiyan zuciya tayi nad'an lokaci,
"Ilham , Insha Allah zan k'ok'arta duk da nasan zansha wahala a wajen shi,"
"A'a kar kice haka ' Fadwa ni zan taimaka miki wajen yak'ar wannan budurwar tasa dayake ik'irari, "
Nan sukayi smilling ' sannan suka tashi suka nufi kitchen, shirye shiryen abunda za'a ci na lunch sukeyi cikin hanzari, nan Diary d'in Yaya Khaleel ya fad'owa Fadwa a rai.
"Amm Ilham , ki bani 5minutes zanje indawo yanzu ' and please karki tsaya jirana, "
Ok kawai Ilham ta ce sannan Fadwa ta nufi d'akin Yaya Khaleel kai tsaye, bud'e k'ofar tayi a hankali ta shige cike da sand'o.
Ta na shiga tahau yin bincike ' gami da bud'e drowers d'in d'akin, ganin bata sami komai bane yasa ta koma gefe tare da cije yatsa ' tukunna ta haye saman gadon shi, tana d'aga pillow taga Diary d'in, nan tayi ajiyar zuciya sannan ta d'auka cikin sauri ta diro daga saman gadon ' ta baro d'akin.
D'akinsu ta nufa direct ta bud'e handbag d'inta ta saka ciki, sannan ta koma kitchen ' tana shiga ta iske har Ilham ta gama d'aura sanwa,
"Har kin d'aura sanwan kenan?"
"Eh na gama ' yanzu kuma kece da zarya cikin kitchen, don na gama nawa. "
Ya tsine baki tayi ' gami da cewa,
"To naji dai ' aini ba raguwa bace ' balle kice bazan jure ba !"
A tare suka bar kitchen d'in suka nufi parlor ' Umma suka iske a zaune ita kad'ai tana kallo, sannan suka sami waje ' suka zauna,
"Fadwa kun d'aura sanwan ne?"
"Eh Umma mun d'aura,"
Tana gama fad'in haka Yaya Farook ya shigo cikin parlon cike dayin sallama ' suka amsa, sannan ya sami waje ya zauna gami da sauke ajiyar zuciya.
"Ke Ilham kawomin ruwan sanyi, "
Cikin hanzari Ilham ta tashi ' ta nufi kitchen, ta d'auko mashi robar ruwan sanyi da cup ' ta kawo mashi. Bayan ya shane yayi gyarar murya,
"Umma ' na sami transfer daga wajen aiki na, "
"Farook transfer kuma?"
"Eh Umma yanzu haka ma tare da transfer letter d'in nake, "
Hankalin Fadwa in yayi dubu ya b'aci, cikin damuwa taketa k'ok'arin had'a ido dashi, shi kuwa yak'i yarda don kuwa yasan tabbas tana cikin damuwa,
"Yaya Farook ' ina ne suka maida ka yanzu?"
Cikin rawar muryar tayi maganar ' hakan yasa Ilham tayi sauri ta rik'e mata hannu,
"Bangladesh suka tura ni, sun bani nan da 3days ' infara shirye shirye, "
Nan ta rafka salata ' salatin da batasan ya fito fili ba,
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,"
Da sauri Umma ta kalli Fadwa ' hawaye ne kawai ke fitowa daga idanun ta,
"Fadwa lafiya? Bafa tafiya zaiyi gaba d'aya ba! zai rik'a zuwa yana ganin mu,"
Girgiza kai kawai takeyi cikin kuka ' ganin haka yasa Umma cewa,
"Ilham jata ku tafi d'aki ki lallashe ta, "
Kwallane cike a idon Yaya Farook ' kasa danne zuciyar shi yayi yasa yayi saurin tashi ' ya wuce d'akin shi.
"Ohh ikon Allah ' shak'uwa kenan, Allah dai yak'ara sanya shak'uwa a zuciyoyin ku. "
Cewar Umma,
Nan itama ta tashi ta wuce kitchen don duba ' girki.
Ilham lallashin Fadwa kawai takeyi ' amma sam tak'i daina kukan,
"Fadwa hak'uri fa zakiyi ' Yaya Farook ko ya tafi na tabbata zai rik'a dawowa yana dubamu, "
"Ilham wallahi inason shi sosai ' zuciyata ta kasa hak'ura kibarni kawai inyi kukan ko zansami sauk'i, "
Sake fashewa da kuka tayi ' cike da tausayawa,
"Fadwa, amma dai kinsan kukan nan bazai ammafana miki komai ba ko? Yes nasan kina son shi sosai ' amma kinsan dai bazai aure ki ba yanzu!"
"Ilham, please ki daina tunatar min da haka ' its hurting me, i have a stronge feelings that Yaya Farook shiya nemi wannan transfer d'in da kansa. "
Rik'e hannun Ilham tayi ' tare da cewa,
"Ilham, am pretty sure Yaya Farook ya na sona haryanzu a cikin zuciyarsa ' Ilham kawai bayason ganin biki nane dawani shiyasa ya nemi Transfer, "
Ilham d'aura kan Fadwa tayi a kafad'an ta gami da bubbuga mata bayanta,
"Kiyi shuru ki bar kukan nan ' and zuwa anjima idan zaki kwanta ki tabbatar kinyi *istik'ara* domin neman zab'in Allah,"
Ajiyan zuciya tayi ' sannan tace to tukunna Ilham ta tashi ta tafi kitchen.
*Around* *3:00pm*
Yaya Khaleel ya dawo gida, Ilham ce d'auke da plates a hannun ta nufi dinning table da shi, haka yayi daidai da shigowar Yaya Khaleel cikin parlon ' ganin har an gama abinci ne yasa ya doshi wajen dinning table d'in kai tsaye. Samun waje yayi ya zauna sannan ya tsayaya ruwan sanyi a cup yasha, itadai Ilham tana tsaye ta jera abubuwa.
Umma ce ta shigo cikin parlon ' ta Umar ceta dataje ta kira Yaya Farook ya zo ya ci abinci, Bayan Wucewar Ilham ne Yaya Khaleel ya gaida Umma da cewa,
"Sannu Umma!"
Umma ko kallon shi batayi ba ' balle ta amsa sallamar shi, ta sami waje ta zauna , hakan yasa hankalin shi ya tashi ' Yaya Farook ne ya shigo parlon Ilham na biye da shi , sannan suka sami waje suka zauna Tayi sarving d'insu.
Bayan sun fara cin abincin ne ' Umma ta umarce Ilham taje ta kira Fadwa ,
"Umma tund'azu naimata magana, tace batajin yunwa ' inbanda kuka babu abinda takeyi, "
Yaya Khaleel ne ' ya d'ago kai ya kalleta,
"kuka kuma? Me akayi mata take kuka, "
Yunk'urawa yayi zaije d'akin Umma tayi saurin dakatar da shi,
"ina zakaje? D'akin nasu zakaje domin kasake k'unsa mata wani bak'in cikin kokuwa me?"
Komawa yayi ya zauna ' tare da girgiza kai Alaman A'a,
"Umma zanje induba ta ne!"
Tsaki taja ' ba tare da tace komai ba, sannan Yaya Farook ya tashi ya wuce d'akin nasu domin duba halin da take ciki.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_Pure Moment Of Life writers_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
www.Seemaluv.wapka.me
@*_I want to use this opportunity ' to thanks everyone of you, for the birthday wishes ' gaskiya naji dad'i sosai, kuma na gode ' Thank you so much guys, you really make my day...thank U once more.馃槝馃槝馃槝_*
*41-42pages*馃尮
Jin tafiyar Ilham ne ' yasa tayi saurin share hawayen ta, tare da saukowa daga saman gadon.
Bayan shigowar Ilham ' cikin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 20