Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Nan ya kashe wayar ba tare da ya tsaya yaji abinda zatace ba, Lubna shuru tayi ta tsaya tana kallon wayar cike da mamaki. "Me kake nufi da ' nida ita akwai banbanci? Kanaso ka cemin ita matar sunna ce ni kuma ballagaza?, hmm lallai sunana kawai kakeji Lubna ' zan baka mamaki." Yaya Khaleel k'ana nan kaya ya saka ajikin shi gami da d'aukan Car-key d'inshi ya fice. Kai tsaye ya nufi hotel ' ya kama d'aki sannan ya shiga ya zauna a bakin gado, wayar shi ya zaro cikin aljihun wandon shi yayi dailing number d'in Lubna. Ringing biyu tayi Lubna ta d'aga. "I thought bazaka sake kirana ba!" "Ba wannan na tambaye ki ba ' kizo yanzu hotel d'inda muka saba had'uwa, i want us to spend a night together." "馃槷What!?" Cike da mamaki take magana tana kallon wayar. "Kinji abinda na fad'a ai ' so am waiting for you!" Ajiyar zuciya tayi ' sannan tace. "To." Ta kashe wayar ' ta saka cikin handbag d'inta tare da ciro kayan baccin ta ta saka a ciki, Lubna yafa gele tayi sannan ta fito parlor ' ganin babu kowa ne yasa ta ajiyar zuciya sannan ta fice taja motar ta zuwa hotel. B'angaren su Fadwa kuwa ' bayan fitowar Ilham daga wanka ne sukayi shirin bacci cikin kayan bacci, sannan suka kwanta. *Dedicated To My Fan's* 馃憚馃憚馃憚馃槏 [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 www.Seemaluv.wapka.me *51-52* *Washe gari* Asuban fari Yaya Khaleel ya tashi daga bacci ' rungume da Lubna a hannun shi, zame jikin shi yayi a hankali ya fad'a bathroom donyin wanka. Koda ya fito ya isketa a zaune ' harta tashi hannun ta akan waya. "Kin tashi da wuri!." Abunda ya fad'a kenan yana k'ok'arin sanya riga a jikin shi "Eh wallahi my Love ' duk wahalar da ka bani ainayi k'ok'ari ko?" "Yes kinyi k'ok'ari atleast ke ba ragguwa bace!." Dariya ta d'an saki kad'an sannan ta sauko ta rungume shi. "Please My Love ' karka tafi yanzu kad'an tsaya, akwai sauran lokaci." "What! Yaufa za'aimun aure kinga kuwa yau ranata ce, dole zan nutsu." Nan ta sakeshi daga rungumar da tayi mashi ' cikin b'acin rai ta koma ta zaune tare da calming hannun ta. Yaya Khaleel ' murmushi kawai yayi mata, saida ya gama shiryawa tukunna yayi pecking d'inta a chick d'in ta sannan ya fice alamar gida ya wuce. Tsaki Lubna taja mai sauti ' tare da buga k'afarta k'asa. "Wannan yarinyar kina shiga mun hanci ' two days." Nan ta tashi itama ta fara had'a kayanta da suka watse a k'asa, Ta sanyasu a cikin handbag d'inta sannan ta fita tabar hotel d'in zuwa gida. Yaya Khaleel yana isa yayiwa mai gadi hone ' domin ya bud'e mashi, Bayan ya shigar da motar shi cikine ya fito zai shiga gida mai gadin ya tsaida shi da cewa. "Yallab'ai tafiya kayi ko? Don da alamun ba'a gida ka kwana ba." A fusace Yaya Khaleel ya dawo ya fuskance shi, cikin fushi yace. "Non of your business malam ' ba abinda ya dameka bane wannan." Yana fad'in haka ya juya ya shige cikin gida, Koda ya ratsa cikin parlor babu kowa ' don da alamun babu wanda ya tashi bacci. Haka Yaya Khaleel ' ya shige d'akin shi ya sanya key, d'auko diary d'inshi yayi ya nufi kitchen ' yasa mashi wuta. Yaya Khaleel na tsaye saidaya tabbatar komai ya k'one tukunna ya bar kitchen d'in ya koma d'akin shi ya kwanta, Wani wahalallan bacci ne ya d'aushi. Lubna bayan ta kai gida ne ' tayi packing sannan ta shiga ciki, a zaune ta iske Mummy da alamun jirar dawo warta takeyi. Lubna tana ganin haka ta had'iye miyau daker, wata zuciyar tace. "Aiki shiga kawai kinsan babu abinda za'a miki so kici duniyarki da tsinke kawai." Nan ta k'arasa cikin harabar parlon, ta nufi d'akin ta Mummy ta dakatar da ita. "Daughter daga ina kike?" Lubna dawowa parlon tayi ta zauna. "Hm... Mummy wata friend d'ita ce ' jirginta ya sauka d'azun a round 4:00am, to shine ta kira awaya inzo in taimaka mata ' bak'uwa ce batasan ko inaba." "Kinyi k'ok'ari Lubna ' to ina k'awar taki?" "Hotel ta kama saboda tazo bikin wata k'awar mu ne." Kai Mummy ta d'aga sannan Lubna ta tashi ta shiga d'akinta gami da dafe k'irjin ta. *** *** *** *** *** *** *AROUND 8:30AM* Su Fadwa suka tashi bacci cike da mik'a, d'aya daga cikin k'awayen ne tashiga bathroom donyin wanka. "Yau Amarya ita ce k'arshen wanka a d'akin nan." Cewar Ilham, "Nidai Ilham kamar a d'aga bikin nan nakeji ' jikina yana bani zansha wahalar aure!!!." Ilham jitayi kamar an buga mata dutse a k'irjinta. "What!? What are you trying to say? Fadwa kin bani mamaki fad'amun hakan da kikayi!, ban kuma tab'a zato ba!" Cikin fushi Ilham tayi maganar. D'aya daga cikin k'awayen ne ta d'an dafa kafad'an ta. "Kiyi hak'uri Fadwa ai komai nufine na Allah, balle ma ke! Aikowa yasan cewa kinyi dacen miji." Hawaye ne yafara yiwa Fadwa zarya a idanun ta, Ta tashi taje kusa da Ilham wacce ta juya banta ' tana fuskanta mirrow. Hannu Fadwa tasa ta juyo da ita suka had'a ido, ganin hawayen da ke fuskar Fadwa ne ya d'agawa Ilham hankali. "Ilham ke y'ar uwata ce kuma dukda ' a cikin *BABBAN GIDA* zan tare still inaji kamar zan rasa wani b'an gare na jikina, Ilham idan na wuce d'akina nan d'akin zai miki fad'i zaki waiga kiga ke kad'ai ce babu ni!!... zaki..." Bata k'arasa ba Ilham ta fashe da kuka, tare rungume junan su ' k'awayen su suma kansu abun tausayi ya basu. "Bazan tab'a bari wani abu ya cutar dake ba Fadwa, ni takice har kullum." Ajiyan zuciya dukkan su suka sauke ' sannan wacce ta shiga wanka ta fito. "Yawwa aiko yanzu zan shiga ' don so nake in rigaki wanka." Cewar Ilham, *** *** *** *** *** *Wajen k'arfe 10:56am* Su Fadwa ko wannen su yayi wanka ' amma babu wanda ya shirya cikin su, Don kuwa sai wajen 1:00pm za'a d'aura aure a babban masallacin da ke layin. "Kaii haba ninasan da walaki! Ashe bamu karyaba shiyasa naji cikina na zafi." Cewar Ilham, "Ilham ki dafa mana indomie mana ' zaifi rik'e ciki." Inji Fadwa. Suna cikin hakane ' saiga Umma ta shigo dakin, Dukkan su gaisheta sukayi cike da ladabi. "Fadwa kun karya kuwa?" "A'a Umma amma yanzu Ilham zataje ta dafa mana Indomie." "Yawwa gara dai a hanzarta." Fita Umma tayi daga d'akin ta basu wajen. "Yawwa Ilham please ki dafa da Yaya Khaleel ' nasan babu abinda yaci kuma kinsan yanada Ulcer." "To naji." Abinda Ilham ta fad'a kenan ta nufi kitchen. Bayan wucewar Ilham ne Umma ta dawo cikin d'akin rik'e da robar youghout a hannun ta amma sai dai ba youghout d'in bane a ciki , wani abunne dabam. "Fadwa karb'a wannan inaso ki shanye shi tas, bayan kinci abinci ' kuma ki kawomin robar d'aki." Fadwa karb'a tayi sannan ta maida kallon ta kan Umma. "Umma miye wannan?" "Banason tambayoyi ' zan baki abunda zai kashe kine? To kisha tsumi ne zai k'ara miki kuzari ne." To kawai Fadwa tace ' sannan Umma ta juya ta fita, tana fita Fadwa ta ajiye robar a k'asa. "Ni aiba saina sha tsumi ba! Ahaka na inada kuzari ai." D'aya daga cikin k'awayen ne tace. "Kai Fadwa ashe haryanzu kina nan da rashin jin ki! To wallahi saikin shashi ' ai tunda kikaga ta baki to yanada amfani, kuma ai bata tab'a baki ba sai yau saboda haka kisha kawai ' inba haka ba wallahi yanzun nan inje kiran ta." "Ke! Rufamin asiri ' to naji zansha amma ai saina ci abinci ." Suna cikin hakane Ilham ta shigo d'akin rik'e da plates dai cooler a hannun ta, sai da ta aje sannan ta zubawa kowa nashi. "Kin kaiwa Yaya Khaleel nashi ne? Cewar Fadwa, "Ke kinfa fara isata ' saikace akanki aka fara yin miji! Na kaimashi mana." Murmushi Fadwa tayi sannan suka fara breakfast ' bayan ta gama ne ta d'auki abunda Umma ta bata ta shanye tass ta wullar da robar. "Meye wannan? Ilham tayi tambayar, "Umma ce ta bani ' tace in shanye tass zai k'aramin kuzari." Okay kawai Ilham tace sannan ta d'aga kai ta dubi agoge. "Shikenan wata ta kusa zama matar aure ' yanzu k'arfe 12:57pm." Harara Fadwa ta watsa mata ' tukunna suka fara haramar gyara jikinsu. Yaya Khaleel kuwa shiri yayi cikin fararen kaya shadda ' yayi kyau sosai, Abokanan shine suka dame shi da kira ' hakan yasa ya fita zuwa Babban masallaci. Zuwa yayi ya iske mutane mak'il a wajen abokan Abba da abokan shi ' suka cika wajen gunun sha'awa, Wakilan Ango dana Amarya duk sun hallara a wajen. *1:00pm dot* Aka d'aura aure ' haka Abba ya kira Umma a waya ya sanar mata cewa aure ya d'auru. Haka gidan ya cika da shewa da gud'a . Nan cikin sauri su Ilham suka shirya Fadwa ' sannan wata tsohuwa daga cikin dagin ta shigo d'akin. "To kud'an bamu waje!" Abinda ta fad'a kenan k'awayen suka bar d'akin, ita kuwa Ilham tana zaune ta kaso kunnuwa. Haka tsohuwan nan ta dunga yiwa Fadwa nasiha ' yi nayi bari na bari, Nasiha sosai mai shiga jiki takewa Fadwa. Saida ta gama sannan ta tashi tare da cewa. "Zaku iya kaita d'akin ta yanzu." Abinda ta fad'a kenan ' Ilham tahau gud'a, da gudu k'awayen suka shigo d'akin suma suka d'au gud'a. *** *** *** *** *** Haka y'an uwa da k'awaye suka yiwa Fadwa rakiya zuwa d'akin ta Ilham ce kan gaba, Saida suka kaita bedroom d'inta sannan suka ajeta a saman gado ' suka juyo. Aka barta daga ita sai Ilham sai k'awayen ta. B'angaren Yaya Khaleel kuwa ' Yana tare da abokan shi sai murna ake tayashi. *Dedicated To Sadnaf* 馃憚馃憚馃憚 [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 www.Seemaluv.wapka.me *53-54* *AROUND 4:00PM* Yaya Khaleel ya dawo gida ya iske duk mutane sun watse ' sai wata y'ar tsohuwa wacce ta manyan ta zaune a parlor. kai tsaye ya wuce sashen shi ya cire babban rigarshi, sannan ya fito parlor suka had'e da Umma wacce dama shi take jira. "Khaleel daga ina?" "Amm Umma yanzu nake dawo wa ' daga wajen abokai na, zanje sashe na.." Ya fad'a yana sosa k'eya. "Ai indai da kunya to anjita. Cewar tsohuwar da ke zaune a wajen, Yaya Khaleel juyawa yayi ya kalleta ' sannan ya maida kallon shi kan Umma. "Umma wannan wacece kuma?" "Sunan ta Ige ' akwai wasa a tsakanin ku, zata cigaba da zama damu ne anan ' tana d'an taya Ilham aikin da ba'a rasa ba." Ok kawai Yaya Khaleel ya ce ' sannan yasa kai zai fita Umma ta dakatar dashi. "Ina kuma zakaje? Bata tare da mun gama magana ba? Duk zumud'in ne haka?" Murmushi kawai yayi. "To kaje sashen Abban ku yana nemanka yanzun nan." Kai tsaye Yaya Khaleel ya nufi sashen Abba ' a zaune ya hange shi saman kujera, Yaya Khaleel sallama yayi sannan ya shiga. Abban ya amsa cike da fara'a. "Sami waje ka zauna!" Yaya Khaleel k'asa ya zaune cike da ladabi. "Khaleel ' Alhamdulillah yau aka d'aura auren ku da Fadwa kuma ina fatan zaka rik'ayin adalci a tsakanin ku." "Insha Allah Abba." "Kuma inayi maka albishir da cewa ' na bud'e maka company naka na kanka, domin ka rik'a sarrafawa." Yaya Khaleel bud'e baki yayi yana kallon Abba ' cike da mamaki. "Kuma na sama maka ma aikata ' wad'an da zasu rik'a aiki a k'ark'ashin ka yanzu kana zuwa sai dai ka hau aiki, Amma gobe insha Allah zan kaika domin ka ga wajen." Wani ihu Yaya Khaleel ya saki mai kama da kuka ' ya tashi ya rungume Abba cike da jin dad'i. "Abba na gode ' na gode sosai Abba ban tab'a jin dad'i irin na yau ba Abba." "To sakeni mana Khaleel ' so kake ka k'arasa ni?" Cikin sanyin jiki Yaya Khaleel ya koma ya zauna. "Yanzu ka tashi kaje ' dama kiran kenan!" "To shikenan Abba na gode ' Allah ya kaimu goben." Ameen Abba ya ce ' sannan Yaya Khaleel ya tashi ya fita, Parlor ya shigo d'auke da fara'a a fuskar shi zai wuce Umma ta tsaida shi. "Ina zakaje?" "Umma zanyi packing kaya na ne ' zuwa gidana!" "Yayi kyau masu gida!!!" Harya juya zai wuce Ige ta tsaida shi da cewa. "D'an samari naga kana ta fara'a ne! D'an fesa mun inji me aka samo mana." "Company Abba na ya bud'emun." "Ohh shi dama kanunfarin bud'e shi akeyi?" "Hahaha! Kinga illar zama a k'auye kenan, ki tambayi Umma ta fad'a miki ' ni inada abunyi." Wuce wa yayi ya kyaleta ita da Umma ' tana ta k'ok'arin fahimtar da ita. Bayan ya d'auko trolley d'in shi da duk wani abu nashine ya nufi part d'inshi. Karo yaci da k'awayen Amarya zasu koma gida. "Haba kardai har zaku koma!" Dariya sukayi dukkansu sannan d'aya daga ciki tace. "Ango kenan kasha mai ' to ai mun dad'e anan kuma kai kawai Amarya take jira." Murmushi kawai yayi sannan ya kira driver d'in gidan ya umarce shi ya kaisu gida. Godiya sukayi mashi sannan ya shige cikin gidan shi, D'akin shi ya fara shiga ' ya ajiye kayan shi sannan ya nufi d'akin da Fadwa take. Suna cikin hira ne da Ilham sukaji anyi gyaran murya ' hakan yasa Fadwa tayi saurin maida gelenta ya rufe mata fuskar ta. Yaya Khaleel k'araso wa yayi cikin d'akin fuska a d'aure sannan Ilham ta tashi ' ta fita cikin sauri ta wuce sashen su. Ita kuwa Fadwa gabanta dukan uku uku kawai ya keyi ' saboda tsabar fargaba. Yaya Khaleel gefen gadon ya zauna ' ya na kallon irin kyan da tayi cikin gele, Hannu yasa ya yaye gelen ya cigaba da k'are mata kallon. K'ara matsowa yayi kusa da ita yana k'ok'arin sunsunar wuyan ta, tayi saurin matsawa. "Me hakan ke nufi?" Banza tayi ta kyaleshi ' abun yayi matuk'ar b'ata mashi rai sosai, tashi yayi fita daga d'akin ta bishi da kallo. Parlor ya je ya zauna ' ya kunna TV ya na kallo, Haka Fadwa ta k'araci zaman ta a d'aki ita kad'ai har aka kira sallar magrib ta tashi ta cire mayafin ta ' ta shiga bathroom. D'auro alwalar ta tayi ' ta shinfid'a dadduma ta fara sallah, Yaya Khaleel shima tashi yayi ya shiga d'akin shi don yin sallah. Bayan Fadwa ta idar da sallah ne ' ta koma ta zauna a kujerar d'akin Sofa, ji tayi gaba d'aya batajin dad'in zama ita kad'ai hakan yasa ta tashi ta nufi parlor da niyyar fita zuwa sashen su Umma. Suka had'e da Yaya Khaleel zai shigo cikin d'akin, tsayawa cak yayi yana kallon ta yadda surar jikinta suka bayya. "Ina zakije?" "Ammm Yaya Khaleel dama inaso ne inje wajen Ilham in karb'a phone d'ina." "What!? Phone? Saboda ke dama kunya bata ishe ki ba ko? Yau yau da tarewar ki ' zaki kama hanyar yawo ko?" Nan ta sunkuyar da kai ' ba tare da tace komai ba, Sannan ya matso kusa da ita. "Bazaki fita ko nan da cen ba ' har sai nan da 2weeks, kuma babu mai shigowa ya katse mun jin dad'i." D'ago kai tayi ta kalle shi ' da y'ar kwallar ta a cikin ido. "Yaya Khaleel please ' wallahi bazan iya zama ni kad'ai ba shiyasa." "Nidai kinji abinda na fad'a miki." Nan ya juya ya wuce parlor ' yayi zaman shi. Koma wa cikin d'akin tayi zata cire kayan jikinta ta shiga wanka ' taji sallamar Ilham, Abinci ta kawo musu cikin plask Yaya Khaleel ya ansa sannan ya umarce ta data koma inda ta fito ' da gudu Fadwa ta nufo parlon. Ta na isa taja burki ta tsaya ' ganin babu Ilham a wajen sai Yaya Khaleel wanda ke rik'e da plask d'in abincin ya na kallon ta. "Yaya kamar naji muryar Ilham ko?" "Na ce ta koma inda ta fito! Wata matsala ce?" Tsayawa kawai tayi tana mashi kallon mugu ' sannan ta ce. "A'a." Ta juya ta koma d'aki, ta hau cire kayan jikin ta sannan ta d'aura towel ta shiga wanka. Tana cikin wanka ne ' taji an bangad'o k'ofar bathroom d'in, cikin tashin hankali da tsoro Fadwa ta rarumi towel ta rufe k'irjinta k'ok'ari take ta d'aura amma jikinta rawa kawai yake yi. Yaya Khaleel cak ya tsaya a bakin k'ofar yana k'arema jikinta kallo ' ita kuwa babu abin jikin ta keyi sai rawa. Sai da suka kwashe 5minutes a haka ' sannan ya juya ya rufo mata k'ofa ya koma gefen gado ya zauna ' yana sauke ajiyar zuciya. Ji yayi tana shek'a ruwa a jikinta alaman tana gab da fitowa ' haka yasa yayi saurin bud'e wardrope d'inta ya ciro mata wasu fitinan nun sleeping gown shara shara ya ajiye mata su saman gado sannan ya bar d'akin. *Dedicated To Seemaluv's Novel Group*馃憣馃憣 *_Love you Gurls So Much_* [5/23, 2:51 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮 馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮 *_Pure Moment Of Life writers_* 漏 ```Written```聽聽 聽 聽 By *_Seemaluv_*馃憚 www.Seemaluv.wapka.me *_@JAMEESHA! JAMEESHA!! JAMEESHA!!!, Hmm I Just Want All My Followers ' To Know That This Name Means A lot To Me, And The Person Own The Name Means Everything To Me. My Sweet JAMEESHA have a Wonderfull馃憣馃憣 day!!!_* *55-56* Bayan ta gama wanka ne jikinta na d'ar d'ar d'in fitowa, Saboda sam ita bata son su had'a ido da Yaya Khaleel ko kad'an. Haka nan ta bud'o k'ofa ta lek'o gani tayi babu kowa a d'akin hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta fito daga bathroom d'in, Bata tsaya ko ina ba sai gaban mirror ta zauna ' ta fara gogawa jikinta turaruka kala kala masu k'amshi. Bayan ta gama ne ta nufi wardrope ' ta d'auki rigar bacci mai d'an kauri riga da wando ta sanya, Sannan ta d'auki dogon hijab d'inta ta saka a jikin ta ' ta nufi parlor da niyyar cin abinci. A zaune ta hangi Yaya Khaleel a dinning table yana kallon shi ' da alama ita yake jira, Cike da sallama ta k'arasa wajen ' Yaya Khaleel juyowa yayi ya kalleta tare da amsawa, Ganin hijab d'in da ta kima ne yasa shi b'ata rai gami da maida kallon shi a TV. Bayan ta zauna ne zata zuba masu abinci ' ya watsa mata wani mugun kallo hakan yasa tayi saurin sunkuyar da kanta k'asa tare da barin abincin. "Cire min hijab d'in jikin ki!!" D'ago kai tayi da sauri ta kalle shi. "Au irin ban isa d'in nan ba ko?" Ta girgiza kai. "To ki cire mun hijab d'in jikin ki right now ' don ba wasa nakeyi da ke ba." Mik'ewa tsaye tayi ta yaye hijab d'in ta barshi daidai wuyan ta. . "Ba kiji abinda nace ba ko?" Da sauri ta aje gefe tare da maida kallon ta zuwa k'asa.

Chapter 11 of 20