yasa ta fara dar dar Dashi.
Shima lura yayi da yadda Fuskar ta ya sauya ' haka yasa ya ciji lips dinshi gami da yin Murmushi,
"Nina fasa Zuwa shopping din ma ' Bara kawai in sami taxi ya kaini gida.
Cikin damuwa tayi maganar ' har saida Ya nuna a fuskar ta, bude Kofar motar tayi xata fita ' yayi sauri ya rike Gelen ta cikin fargaba ta juyo ta kalleshi.
"Haba Fadwa, why are behaving like a kid? na lura tunda na taba fuskar ki ' yanayin ki duk ya cenja Why?
Nan take jikin ta ya fara rawa ' cikin rawar murya tace,
"Don Allah Taj ' ka sakemin gele na intafi, Please.
"Tor yanzu bazaki bari intaba abinda yafi fuskarki tsadaba?
馃槰, Da karfi ta fizge gelen ta ta fito daga motar ' cikin hanzari ta tare Napep, bayan ta zauna ne ta kalli wristwatch din hannun ta taga 2:30pm ' nan gaban ta ya sake Faduwa.
"Don Allah bawan Allah kayi sauri mana!
"To aibaki fadamun inda zan kaikiba hajia.
Cewar mai keke napep,
Nan ta fada mashi inda zaikai ta ' sannan suka dauki hanya. Ba ita takai gida ba sai wajen 2:56pm, Tana sauka ta mika mashi kudin shi sannan ta shige gida ' Saida ta tsaya a bakin kofa tayi Adduo tukunna ta bude ta shiga ciki.
Ta na shiga da Yaya Farook ' ta fara hada ido, Ya watso mata wata muguwar harara gami da Karkada kai ' Gaban ta ya fadi dakerr ta iya hadiye miyau, sannan ta waiga bata ga Umma a kusa ba haka zalika babu Ilham a kusa. Haka ta taka tare da yin sallama ' ta wuce ciki,
"Hmm Ba yanzu zan kama kiba tukunna!
A zuciyar shi ya fadi haka, ' ita kuwa sai jin dadi takeyi ganin bai tsaida ita ba, Cikin fara'a ta shige daki ' akwance ta iske Ilham ta na Assignment, Sannan Fadwa ta ajiye handbag dinta a saman Drower ta koma ta zauna a gefen Ilham,
"Ke! Ilham Yaya Farook ' baimin komai ba wallahi.
Ilham dariyar mugunta tayi tare da jan tsaki,
"saida ya tambaye ni ' ina kika tsaya nikuma na fada mashi duk abinda nasani,sannan ya ce yau jikin ki zai gaya maki kuwa.
"Na shiga ukku ' ni Fadwa banda ruwan wanke kai yau, inama ace Abba zai dawo yau.
Cewar Fadwa,
Tabe baki Ilham tayi ' sannan ta cigaba da abunda takeyi, Ita kuma Fadwa ta tashi ta cire kayan jikinta ta daura towel ' tukunna ta shige bathroom don Watsa ruwa. Bayan Shigan ta Bathroom ne Yaya Farook ya shigo dakin,
"Ina Fadwa?
Cikin tsawa yayi maganar ' haka yasa Ilham firgita, Ta yi saurin cewa,
"Tashiga wanka!
"Ok Tana fito wa kice tazo ta sameni ' kada kuma ta batamun lokaci..
To kawai ta ce sannan ta maida kanta akan Assignmenta dinta.
Bayan *5* *Minutes* Fadwa ta fito daga wanka, Ta na fitowa Ilham ta ce.
"*Yaya* *Farook* yazo da kansa kuma yace kina fitowa kije kisame shi ' yanzu.
Raras gaban ta ya Fadi ' Gami da zaro ido.
"Ilham please kicemun wasa kike!
Shuru Ilham tayi ta kyaketa ' aibabu shiri Fadwa ta baza a guje taje dakin Yaya Farook, saida tayi Knocking Sannan Ta shiga ' tama manta Towel ne a jikinta, Yana ganinta ya mike tsaye .
"Yaya Gani!
Daf ita Ya matso ' sannan ya riko hannun ta yajata har cikin Dakin,
"meyasa Bakijin magana Ehe!!!!
SunkuYar da kai tayi ba tare da tace komai ba,
"Ba zaki fadamun inda kukaje ba saina mareki?
Hawaye ke zubo mata a fuska amma babu yadda ta iya,
"Yaya Farook, Tajuddeen ne yazo School dinmu Shineee....
Bata gama rufe baki ba ' taji saukan mari a fuskar ta Tasss....
"Ahhhgggg!!!!
Sauri Dafe wajen tayi ' cikin kuka,
"Fadamun Ubanwa ya gayyace shi wajen ' idanba ke ba!!!
Hannu biyu yasa ya dafa kafadunta gami da girgiza ta,
"Kinsan meyasa nadamu ke? Kuma kinsan meyasa nake miki haka? Hmm Saboda ina sonki!! Ina sonki Fadwa!!!
Jikinta yayi sanyi ' tsayawa Tayi ta na kallon shi cike da mamaki,
"nan *BABBAN* *GIDA* * NE!!* Kuma cikin shi kike ' Fadwa kinsan waye Taj dahar kika saki jiki dashi haka?
Ya fada gami da Girgiza ta ' da har sai da Towel din jikinta ya Kwance, Sauri Fadwa tayi ta rike Towel din ' cikin kuka ta ce,
"Yaya Farook don Allah kayi hakuri ' bansan haka abun yake, please kayi hakuri.
Harya daga hannun shi zai sake marin ta ' sai kuma ya fasa, ya sauke hannun tare da juya mata baya.
"Fita ki bani waje ' before i did something that you will regret it.
Juyawa tayi ta bar dakin' da gudu cikin kuka ' ta shige dakinsu. Saman gado ta fada ' kuka kawai takeyi tamkar ranta zai fita.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
*15-16* pages馃尮
Suna cikin Haka ne Umma ta shigo Parlon Ta sami Waje ta zauna Sannan Ta kalli Fadwa ' Ganin yadda jikin ta duk yayi sanyi,
"Fadwa ya naga duk jikin ki yayi sanyi? Ko Halan Farook ya dake ki?
Cewar Umma,
Saida Ta kalli Yaya Farook sannan Ta girgizawa Umma kai alaman A'a, Suna cikin Wannan ne Sukaji Sallama Abba ' Ilham ce tayi zambur ta mik'e tsaye tare dayin Ihu,
"ahhh!!! Yeee Abban mu ya dawo.
Gaba d'ayan su Mik'ewa sukayi tsaye cikin murna suka tunkare shi, Ilham ta karb'a jakar hannun shi tare da cewa.
"Abba sannu da dawo wa!
Amsawa yayi Cike da fara'a sannan ya kalli Fadwa wacce ta rakub'e a bayan Umma ita a dole ta na fushi,
"Haba Wa ya tab'amin Y'ata Fadwa?
Cewar Abba,
Nan ta saki Fuskarta Tayi murmushi sannan ta ce,
"Abba kaine Kaimin Laifi da baka dawo da Wuri ba ' amma Yanxu Tunda Kadawo shikenan.
Gaba d'ayansu dariya sukayi sannan suka nufi Dinning Table domin cin abin, Ilham kuma sashen Umma ta nufa Domin ta ajiye jakar Abba.
Bayan Sun zauna ne ' Fadwa ta fara Yimasu Sarving Abincin, Sai da tabbatar ta zubawa kowa sannan Ta koma tazauna itama Ilham ta zo ta zauna suka fara cin Abinci ' Abba kallon Yaya Farook yayi sannan ya kuma kalli Ilham da Fadwa,
"Fadwa??
Abba ya kira sunan ta cikin kamala ta d'ago kai ta kalle shi tare da cewa,
"Na'am Abba.
"Naga kin rame mun ne, A kwai mai takura maki ne?
Abba na fad'in haka ta kalli Yaya Farook taga shima ita yake kallo ko zata ce wani abu,
"A'a Abba babu mai takura mun, nayi rashin Lafiya ne.
Ta na gama rufe baki Umma tayi sauri ta ce,
"Karki wani boye mashi ' babu mai takura maku inbanda Farook.
"Haba Umma ki barta ta fad'a Da bakinta mana , ai ita tasan babu abinda nake mata.
cewar Yaya Farook,
Shuru kawai Fadwa tayi ta sunkuyar da kanta.
"Hmm aini dama Nasan za'a rina Wannan zaman gidan naka wasane? Ainasan duk wannan bak'in halin kansu zai kare.
Abba na gama fad'an haka Fadwa ta mik'e tsaye da niyyar wuce wa d'akin su.
"Ina kuma zakije?
Cewar Ilham,
"Wallahi bacci nakeji sosai ' shiyasa zanje in kwanta.
"Tohm nidai bacci ba yanzu ba,
Fadwa d'aukan plate d'inta tayi tare da yiwa Umma da Abba sallama , sannan ta kad'a kanta ta wuce d'aki.
Bayan Wuce warta ne da y'an mintoci, Yaya Farook shima ya tashi gami da yimasu sallama ' kai tsaye ya wuce d'akinsu Ilham, Ko sallama bai yiba yana shiga ya iske Fadwa har tayi shirin bacci rigar bacci ne ma a jikin ta ' tana zaune a kujerar Madubi.
Ganin mutum kawai tayi a tsaye a bayanta, hakan yayi matuk'ar bata tsoro ' a firgice ta mik'e tsaye tana shirin yin ihu yayi saurin Toshe mata baki,
"Are you out of your sense? Akwai wanda zai shigo d'akin nan bayan nine?
Girgiza mashi kai tayi sannan ya sake mata baki ',
"Yaya Farook Lafiya?
Tayi tambayar ta na kallon idon shi,
"Fadwa meyasa bakiyi sallama dani ba kafin Kije ki kwanta?
Yayi maganar a sanyaye ' ita kanta saida tayi mamaki,
"Am sorry Yaya Farook.
"Ba kya tunanin halin da zan shiga?
Zaro idanu tayi cike da Mamaki a zuciyar ta tace,
"Oh ni Allah Yau kuma Yaya Farook ni yake fad'awa haka.
K'ara matsowa yayi dafff da ita suna shak'an numfashin junan su, sannan ya riko habar ta.
"Am totally in love with you Fadwa ' am in love with your dress,
Abun ne ya bata tsoro ganin yadda ya sauya lokaci d'aya gashi kuma su biyu a d'akin hakan yasa ta cewa,
"Yaya Farook please Kaje kada Ilham ta zo ta sameka a nan wajen kaji.
Saurin sakin ta yayi tare da cewa,
"Tor Promise me that we will Always be together.
Kai ta d'aga mashi Tare da cewa,
"I promise you that i will always be with you!!
Tana gama fad'in haka Ya juya Ya fita daga d'akin ya wuce d'akin shi.
Bayan fitan shine Ilham ta shigo d'akin a tsaye ta sami Fadwa,
"Kinyi wani tsaye kamar soldier ' ya akayi.
ta fad'a tana kokarin cire rigar jikinta don sanya ta bacci, Murmushi kawai Fadwa tayi sannan ta ce.
"I think am in love with him.
ta fad'a tana k'ok'arin Hayewa saman gado, Cikin sauri Ilham ta sanya rigar bacci itama ta d'are saman gadon Tare da zurawa Fadwa ido,
"In love with who ' Fadwa?
"No lokaci baiyi ba tukunna Ilham ' kibari sai lokaci yayi sai in fad'a maki.
Ya tsine Fuska tayi gami da jan pillow,
"Kyadaiji dashi kuma idan tayi wari aizanji.
Cewar Ilham,
smilling Fadwa tayi sannan suka kwanta.
*** *** *** *** ***
*Washe* *Gari* ...
Da sassafe Fadwa ta farka daga bacci ' Jitayi tamkar an d'ora mata dutse a marar ta saboda Azabar Ciwo,
"Ahhhghh Ilham don Allah ki tashi ki taimaka min,
Cikin Magagin bacci Ilham ta farka , Ganin yadda Fadwa keta hawaye ne yasa Baccin idon ya washe.
"Meke damunki?
"Menstrual cramp, ke damuna Ilham please... ki bani pain reliever please.
Cikin hanzari Ilham ta diro daga gado taja side drower ' ta ciro Paracetamol ta bata, sannan ta nufi Kitchen ta d'auko ruwa ta kawo mata. Bayan ta sha maganin ne ta tashi cikin dabara Ta sanya Pad (Always) a jikin ta sannan ta koma ta kwanta , bacci yayi awon gaba Da ita.
Ilham Bathroom ta shiga tayo wanka tukunna ta fito ta shirya ' Sannan ta wuce Kitchen don ta had'a Breakfast, Cikin Sauri ta had'a tea tazuba cikin Plask takawo parlor ta ajiye, Su Umma da Abba suka shigo cikin Parlon Suka zauna sannan Ilham ta gaishe su.
"Ina Fadwa??
Cewar Umma,
"Umma Tana daki batajin dad'i Menstrual cramp ke damunta.
"Subhanallah to tasha magani daiko?
Cewar Abba,
Kai Ilham ta d'aga mashi Alaman Eh sannan ta zuba masu Tea din Ta basu, Itama ta cigaba da shan nata tea din. Bayan ta gama breakfast d'inta ne ta wuce d'aki domin tayi shirin wucewa School, Tana shiga ta d'auki Handbag d'inta sannan ta juya ta fito daga d'akin.
Ta na fitowa suka had'e da Yaya Farook, ta gaishe shi sannan ta juya Zata wuce Yayi saurin dakatar da Ita da cewa.
"Ita Fadwa bazata je School d'in bane yau?
"Eh Batada Lafiya ne!
Ok Kawai ya ce mata sannan tayi tafiyar ta.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
@ *_I_* *_Honestly_* *_Dedicated_* *_this_* *_page_* *_to_* *_All_* *_Members_* *_of_* *_PWF_* *_Group_* ' *_you_* *_Gurls_* *_are_* *_simply_* *_Amazing_* *_in_* *_Anyway_*!!!
*13-14* pages馃尮
Kukan ne Ya dami Ilham yasa tayi saurin Rufe Littafin ta,
"Haba don Allah Fadwa, Sai ka ce wata karamar Yarinya? And beside ke fa kika jawa kanki.
Cewar Ilham,
Fadwa tashi tayi ta d'auki Hijab ta sanya sannan Ta bar D'akin da gudu, bata tsaya ko ina ba sai a harabar Lambu. Numfashi taja nadan wani lokaci ' sannan ta share hawayen fuskar ta Gami da cewa,
"Tabbas Taj baida hali mai kyau, to Amma aishima Yaya Farook d'in mugune ' Ta Ya zaayi yace yana sona? Kilama dai Banji dai kyau bane.
Juyawa tayi cikin sauri ' ta nufi d'akin Yaya Farook, Bud'ewa tayi gami dayin Sallama. Akwance ta ganshi saman gadon shi yana kallon Fanka,
Tsoron tambayanshi taji ' yasa ta juyawa zata koma inda ta fito,
"Fadwa???
Ji tayi ya kira sunan ta ta wata irin sigarda bazata iya Fayyace wa ba ' Haka yasa ta juyo ta fuskance shi, sannan ya Sauko daga gadon ' ya tako har inda take ya riko hannun ta gami da murza gannun,
"Is Everything Alright?
Yayi tambayar ya na kallon cikin kwayar idonta, hakan yasa ta kasa Cewa komai ' sai dai ta tsinci kanta da cewa,
"Yaya Farook ' dama hakuri nazo in baka.
Nan ya saki hannun nata tare da juya baya ' Yayi Murmushi sannan ya ce,
"No Fadwa idan har akan maganar Taj ne ' to bazan hakura ba.... Har sai kince min....
sai kuma yayi Shuru ' bai k'arasa maganar ba.
"Yaya Me kakeso in fad'a? I promise you duk abinda ka ce inyi to zanyi shi ' Inhar zaka yafemun.
Da sauri ya juyo ya kalle ta,
"Fadwa ki ce kina sona!
馃槰zaro ido tayi cike da mamaki , ganin haka yasa Yaya Farook ya d'aure fuskar.
"Meye kika wani zaro ido ' ko na fad'a abunda bazaki iya bane?
Sunkuyar da kai tayi gami da girgiza kai,
"Yaya Farook Ina sonka.... .
Ta fad'a Tare da rufe Fuska ' k'o k'arin Juyawa tayi zata fita Yayi saurin fizgota, Har sai da tad'an tokare shi.
"ina zakije? Mun gama magana ne dazaki wuce?
Yayi maganar cikin Fad'a, Mamaki ne ya cika ta ganin yadda ya sauya cikin k'ank'anin lokaci.
"Ba Dake nake magana ba?!!
Cikin tsawa Yayi maganar ' nan take idanuwan ta suka ciko da hawaye,
"Yaya Farook kayi Hakuri, nakasa....
bata k'arasa maganar ba ya dakatar da ita da cewa,
"Come on, yimin shiru ' yar wannan maganar ce zaki cemun kinji kunya? Dama tuncen kina Sona...
D'ago kai tayi ta kalleshi ' Cike da mamaki, harta bud'e baki zatayi magana yayi saurin taron Numfashin ta da cewa.
"Karki fad'amun wata maganar Banza Anan wajen, Kuma zan gayawa Umma tayi maki Aure tunda Shi kikeso.
"Yaya Farook Hakuri don Allah...
Dariya taso ta kwace mashi yayi saurin Juya mata baya ' ya ce,
"Oya fita kibani waje!!!
Jiki a sanyaye ta bar d'akin, Kitchen ta nufa ta bud'e fridge ta d'auko ruwan sanya tasha, sannan ta wuce dakin su. Tana shiga ta iske Har Ilham tayi wanka ta shirYa,
"Hm Harkin shirya nikuwa ko Mai banshafa ba!
Cewar Fadwa,
"Ke kuwa kina mene?
Ajiyar Zuciya tayi ' sannan ta sami waje ta zauna,
"Hm Babu komai ' Ai tunda kika koreni d'azun Daga d'aki nawuce Lambur.
OK kawai Ilham ta ce , sannan ta wuce Parlor ' cikin sauri Fadwa ta sanya kaya Cikin shigar Tamfa tukunna tayi makeup, itama ta fito parlor ta zauna tana Kallo.
*AROUND* *4:32PM*
Umma ta fito daga sashen ta zuwa Parlor, Cikin hanzari tazo ta sami su Fadwa da Ilham a zaune.
"Ku tashi maza, Ku shiga kitchen don Abban ku yacemin jirgin su ya kusa sauka.
Jin haka yasa Fadwa tayi zambur ta mik'e tsaye cikin Fara'a ta ce,
"Wayyoo Allah na Abbana Zai dawo ' Umma naji dad'in wannan Good news d'in.
Nan suka fara gardama ita da Ilham akan Abunda zasu dafa, Hayaniyan sune yasa Yaya Farook fitowa Daga D'akin shi, Kai tsaye ya tunkaro inda suke hayaniyar ya tsaya yana kallon su. Ilham ce ta fara ganin shi ' tayi saurin Tab'a Fadwa, Amma inaa... ta riga tayi nisa.
"Haha Tunda har kikayi Shuru ' to da magana ta za'a amfani.....
Cewar Fadwa,
Ta narufe baki taji anyi gyaran murya ' Haka yasa tayi saurin juyawa domin Ganin waye, Ido hudu sukayi Da Yaya Farook ' nan take cikin ta ya murd'a saboda tsoro,
"Surutun Ubanme kukeyi?
Ilham ce tayi k'arfin hali ta ce,
"A'a dama Abba ne Umma tace zaidawo yau, shine nida Fadwa Muke Magana Akai.
Harara Ya watsa masu ' dukkansu suka sunkuyar dakai, sannan ya ce.
"Allah Ya dawo dashi lafiya ' inji wani ya bud'e baki ya kai k'arata wajen shi kuga yadda zanyi daku.
Ya na gama fad'in haka ya Koma d'akin shi. Bayan ya wuce ne Ilham ta ce,
"Hm Kadaiji dashi, Kinji Fadwa Mutafi Kitchen domin musan Abunyi.
Jan hannun ta tayi suka nufi kitchen suka fara preparing girke girken Abinci kala Uku, Cikin *2hours* da y'an mintoci suka kammala komai, sannan suka jera a dinning table cike da Fara'a. Yaya Farook fitowa yayi daga d'aki cikin hanzari ya wuce masallaci , Acen yayi Magrib sannan Ya dawo. Fadwa tsayawa tayi a bakin kofa Tana jirar isowar Abba ' bud'e k'ofa taji anyi hakan yasa tayi saurin jan handle din gami da cewa,
"Oyoyo Abb....
kasa k'arasa maganar tayi ganin Cewar ba Abba bane ya dawo Yaya Farook ne ya shigo, Cikin tsoro da sanyin jiki tace.
"I thought Abba ne ya dawo shiyasa....
Harara ya balla mata tare da jan tsaki ' sannan ya je wajen dinning table yayi zaman shi, Itama komawa tayi ta zauna Ilham kuwa babu abinda takeyi inbanda dariya.
*Dedicated* *To* *My* *Fan's*
馃憚馃憚馃憚馃槣
[5/23, 2:50 PM] Jameesha: .....馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
馃尮馃尮 *BABBAN...GIDA*馃尮馃尮
馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮馃尮
*_P.W.F_*
漏 ```Written```聽聽 聽 聽
By
*_Seemaluvv_*馃憚
*17-18* pages馃尮
Bayan wucewar ta yayi sauri ya shiga cikin d'akin nasu, A kwance ya iske Fadwa rungume da pillow ta na bacci ' zuwa yayi ya zauna a gefen ta setin fuskar ta, a hankali yasa hannu ya shafa saman goshin ta tare da kissing d'inta a goshi.
Sannan ya tashi ya wuce parlor, a zaune ya sami Umma da Abba suna hira ' zuwa yayi ya tsugunna ya gaishe su sannan ya koma ya zauna.
"Ka karya kuwa Farook?
Cewar Umma,
"A'a Umma ban karya ba tukunna.
Yaya Farook maida kallon shi yayi akan Abba ' sannan ya ce,
"Ammm... Abba dama nazo ne natuna maka ' maganar Neman Aikin.
"Kaga Farook na manta aigwara daka tunamin ' kaje d'akina zakaga Wani envelop ka d'auko min.
Cikin hanzari ya tashi ya nufi d'akin Abba ' cikin minti Uku ya dawo d'auke da Envelop d'in rik'e a hannun shi, Sannan ya mik'awa Abba cike da ladabi.
"A'a rik'e a wajenka domin nakane, Wannan itace takardar samun Aikin naka Farook.
Murmushi yayi Har sai da hak'oran shi suka bayyana saboda jin dad'i ' cikin fara'a ya ce,
"Thank you so much Abba, nagode sosai Abba ' Allah ya bani
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 20