ni ko sai na ga Jaheed ba laifi, Mimi ce matsalan kusan halinta kowa sai ta ce ba ta so kuma in aka biye mata sai dai kila ta mutu ba ta yi aure ba a take taken ta wlh."
Khadija ta faɗaa lokaci ɗaya ta juya tana mai kallon Mimi ta ke ta hararanta.
Sulaiman ya kalleta ya na yar dariya kafin ya ce"Sisto taho nan naji me ya sa baki son Jaheed din? Mimi ta tura baki kafin ta mike sanye ta ke da doguwar riga mai santsi ta na da buɗewa ta kasanta sannan ba ta kama Jiki sosai ba.
Har gabansa ta zo ta tsaya ya kama hannunta yana faɗin"Me ya sa ba ki ba ma Jaheed dama ba Mimi?
Mimi ta yi shuru ba ta yi mgana ba kuka ke son taso mata sai dai ta danne amma taki mgana.
Khadija ta ce"Ba ta da wani dalili fa, Saboda tasan ba shi da makusa, haka abokin Dee ya ce yana sonta nan ta wulakantashi ni nasan abin da take yi ma ƙulafuci wannan yaro shi ke cikin ranta har yau ta kasa cire shi."
An so so mata in da ke mata ƙaiƙayi kawai sai ta fashe da kuka har da jiniya, Abi na kwance faɗi yake yi" Dr. Kyaleta ku kyaleta Mimin Abi taho nan taho nan wajena."
Sa gudu ta haura gadon ta faɗa gefensa ta na kuka shi kuma ya saka hannunsa guda ɗaya yana shafa kanta cikin lallashi yake fadin"Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki tunda baki son shi ba wanda zai ce dole sai kin aure shi Ok?
Sai ta gyaɗa kai kafin cikin kuka ta ce"
Abi ba na son shi, ni wlh ba na son Jaheed"
Ta karishe faɗaa ta na gunjin kuka kamar wacce aka daketa. Mommy da Hajiya suka kalli juna ba su yi magana ba.
Abi ya ɗago idanuwansa ya na kallonsu kafin ya ce"Kar a ƙara takura ma Mimi da mganar kowa tunda ta ce ba ta so a kyaleta, shima Hamzan zan kira shi a bar wannan mganar tunda Mimi ba ta so period."
Khadija ta buɗe baki ta ce" Amma Abi..'"
"Na ce tunda Mimi bata so a bar mganar nan, abin da Mimi take so ko bayan raina shi za ku yi mata wanda kuma ta ce ba ta so kar ku ce za ku matsa mata don Allah.."
Abi ya katse Khadija, ya na mgana kamar zai saka kuka da sauri Sulaiman ya ce"Abi ba wanda zai takura mata kan abin da ba ta so tunda tace ba ta ra'ayi nima ina goyon bayan a bar mganar."
Hajiya ta ce" Ni kaina ba zan ce a yi ma Binta fole ba Kabiru, Yaddiko ce da Hamzan suka matsa da zamanta haka ba aure shekaru talatin ai ba kwana talatin ba ne."
Mommy ta yi shuru ba ta yi mgana ba wani abu da ya faru a shekarun baya suna dawo mata, duk abin da ke faruwa da rayuwar Mimi ba kowa ya ɓata komai ba sai shi.
Ba'a maida hannun agogo baya tasan da ana maidawa da tuni Major Kabir ya maida lokacin ya gyara kuskuren da ya tafka a zamanin baya da ya ke ji da duniyar a saman kansa.
Mimi jin a bar mganar Jaheed sai ta daina kuka ta tashi ta fice daga 'ɗakin ta koma Bedroom ɗinta na gidan kwanciyarta ta yi ta na sharan kwallah, Jaheed ɗin fa da gaske ba shi da makusambSai dai ita kawai ba ta son shi ne, sannan shagwaɓaɓɓe ne ko ita mace albarka ta zauna tana wannan shagwaɓan Mama boy ne. Jaheed babban yaron Daddy Hamza ne yana Lagoa can ya ke aiki a wani babban kamfanin sarrafa Karafuna.
Sannan kuma a America ya yi karatunsa na Engeniaring har na tswon shekara biyar, yana da wayewa har ta yi masa yawa kuma ita a tunaninta ba sonta yake yi ba kawai yana sonta ne saboda tana aikin gidan Tv asan fuskarta a duniya sannan tana da kyau domin ya sha faɗa mata shi bazai iya auran macen da bata da kyau ba, shi komai nashi ya na son harka da abu mai kyau
Yaddiko ta matsu ta yi aure kamar a saman kanta take zaune shi kuma Daddy saboda Jaheed ne shi ya ke matsa masa tunda ta ki ba shi dama kuma yasan har yanzu bai samu karɓuwa. Ba ko da yaushe take ɗaukan wayansa ba sai ta ga dama, a chart kuma sai ya yi mgana da wajen sati sannan ta ke dubawa. Ita fa Namiji kwara ɗaya ta taɓa so kuma har abada shi kaɗai take so.
Tunda Abi ya ce a bar mganar tasan mganar ta mutu. Saboda a baya ne Abi ke girmama ra'ayinsa saman na kowa, amma yanzu zai iya girmama nata ra'ayin sama da na kowa ba na shi ba ma. Saboda yana tuhumar kanshi da komai ya faru da rayuwar Mami shi ne silar hakan.
Tana jin shigowar Khadija ɗaakin sai ta yi kamar ta yi barci tana jinta ta kira Anty Madiha a waya tana faɗa mata duk abin da ya faru da yadda Abi yace a bar mganar.
Abu ɗaya ya fi bata haushi irin in da Khadijan ta ce"Ni fa nasan me ya sa Mimi ta kin sauraran kowa, wannan yaron ta kwallafara rai akansa wanda ba ta san isalinsa ba, tuni ya yi auransa ma ya manta da ita, itama ai ya kamata ta manta da abin da ya faru a baya ta gina wata sabuwar rayuwar."
Tana da tabbacin khadija ba ta san menene SO..! Da ace ta taɓa ɗanɗana shi ta ji ya ya raɗaɗinsa yake da ba ta yi wannan mganar ba. Da ace tasan ya ya zafin dafin so ya ke da ta yi mata uzuri, ammh itama ta yi ma lta uzuri saboda wanda take so ba ta sha wahala a kansa ba ta same shi. Shi ya sa ba za ta san zafin dafin ka rasa wanda zuciyarka ta aminta da shi ba, ba ta san ya ya zafi da raɗaɗin raba ka da wanda kake so ba. Duk ba ta san wannan zafin da raɗaɗin ba so khadija tana bukatar a yi mata uziri ko da uzurin ya kai kimanin sau saba'in ne. Saboda wannan dalilin ya sa har suka koma Gombe ita da Hajiya ba ta kara walwala a gidan ba. Haushi Khadija take ji, itama Khadijan haushinta ta ke ji Sulaiman kuma ranar oahadi suka bi jirgi zuwa Kano shi da matarsa da ƴayansa. Mimi kuma sai washegarin litini suka bi jirgi ita da Hajiya zuwa Gombe nan suka bar Khadija tunda ita sai mijinta ya so za su koma tare.
Ko bayan dawowarsu Hajiya ma ba ta kara ta da mganar ba, sai dai kwana uku tsakani ta dawo daga wajen aiki ta iske Yaddiko a gidan ta na ganinta sai da gabanta ya faɗi domin tasan akwai mgana.ilai kuwa kan mganar jaheed ne tana ta ma Mimi faɗan da ta ki ɗan uwanta so take yi ta zauna ta cigaba da fita aiki tana nuna fuskarta a duniya bata da niyar aure.
Daga karshe ta gatsa ma Mimi mgana da cewa" In ma wannan yaron kike ta jira to kin yi a banza, a gabanki a gaban mu mahaifinki ya ce ko bayan ransa kika auri wannan yaron bai yafe miki ba."
Mimi ta fashe da kuka wiwi Hajiya ta fara yi ma Yaddikon faɗan me ya sa take haka ne? Ita kuma ta ce ai gaskiya gwara ma ta rufa ma kanta asiri ta karɓi ɗan uwanta yadda ma tun lokacin yaron bai kara nemanta ba zata fahimci da gaske yake yi abin da ya faɗa da ya ya ce ko su kaɗai suka rage a duniya sai dai su mutu ba aure ba zai aureta ba."
Cikin faɗa Hajiya ta ce"To miye na sai kin ta do da abin da ya wuce Yaddiko, ko Kabirun da kike magana ya yi sanyi kuma shi da kansa ya ce tunda Binta bata so a bar mganar ba shi kenan ba."
Yaddiko ta yi shuru ba ta yi mgana ba sai can ta ce"Ai shike nan ta share kafa ta ci gaba da zama, daga karshe su kansu in da take aiki ta na fara tsufa za su nemo wata domin suma da kyanta da Kuruciyarta suke amfani da zaran shekaru sun ja sai dai kuma ta dawo zaman gida." Kalaman sun yi ma Hajiya ciwo sai dai bata nuna ba cewa kawai ta yi"To mun gode sosai."
Alamun ranta ya baci da Yaddikon ta ga haka ne sai ta koma kawo ma Hajiya illar zaman Mimi haka ba aure tunda tana da maneman ba wai babu ba ne.
Hajiya ta yi mata bakam har ta gama maganganunta ta kira Jikanta yazo ya ɗauke ta ya maida ta gida.
Mimi kuma ranar kwana ta yi kuka sai dakyar Hajiya ta lallasheta tasha Tea ta kwantar da kanta a saman cinyar Hajiya tana na hawaye tana faɗin " Hajiya ko wa ya ƙi ya fahiimceni ko wa yaƙi ya fahimci ta inda na ke jin ciwon abun, Hajiya ta nan ne, anan ne na ke jin wani irin nauyi a kirjina ta nan wajen ne." Take faɗi tana kai hannun Hajiya saitin wajen zuciyarta.
Cikin damuwa Hajiya ke faɗin "Ki yi hakuri Binta komai mai wucewa ne In sha Allahu."
Tana kuka Hajiya na share mata hawaye, Kukan da ta yi jiya yasa washegari da safe tana karanta labarai haka ta je wajen aiki fuska duk a kumbure. Ta sha tambayoyi sai dai tace idanuwanta ke ciwo sai aka koma bin ta da sannu Allah ya sauwake.
Rukky ta zo ta sameta a restroom tana hutawa ta riƙa damunta da mgana.
Ta gaji ta kalleta cikin wani yanayi kafin ta ce"Baby ƙyaleni yau bana jin daɗi ne kwata kwata."
Baby ta kalleta kafin ta ce"Daman tunda na ganki na fahimci haka, ki faɗa ma Manaja sai kije gida ki huta in kin warke sai mu yi mganar bikin Biba ne daman"
Shawaran Rukayya ta bi, taje ta sanar Manaja nan da nan ya ce ta koma gida daman yau da safe duk wanda ya kalli labaran Safe yasan wani abu na damun Mimi. Idanuwanta da fuskarta sun kumbura sannan ba ta da fara'a ko kaɗan shiyasa da ta ce ba ta jin daɗi ba wanda ya karyata hakan. Dakyar ta iya tuka kanta zuwa gida sai dai Hajiya ta ga ta dawo ta ce mata kanta ke ciwo zata huta, Hajiya ta ce Allah ya sauwake ta kwanta zuwa azahar in ta tashi sai taci abinci ta sha mgani.
Ɗakinta ta shige ta kwanta a saman gado ta na sauke numfashi.
Ba kanta ke ciwo ba zuciyarta ne ke ciwo amm tunda zuciyar tana rufe ne ba wanda ya sani ballantana ya fahimci halin da take ciki.
Aji.
Aji.
Aji.
Shi ne ciwonta, shi ne kasarwata shi ne kuma rauninta shi ne ciwon da ya yi shekaru ya na cinta acikin zuciya.
Ta yi addu'an har ta gaji ta bar ma Allah lamarinsa. Wasa wasa sai da shafe kwanaki uku ba ta je wajen aiki ba.
A fuskar labarai Salim Bunza aka yi ta gani ba ita ba sai a ranar na ukun da ta dawo ne ta cigaba da kawo labaranta a yadda ysarin yake tun Farko.
Sai dai kowa in ya kalleta sai ya ce ta rame idanuwanta sun zurma ciki sannan ta rage karsashi da fara'a.
_Haka so ya ke ɗiba ya maida kai bawa. Matsayin ka bai dubawa, balle yasan kai waye,ya saka ka yi jinya. Ka sauka kan Hanya ka manta alƙaarya ka yi kalan wawaye._
*******
*1rd March 2022*
Anguwan Arawa da misalin karfe 8:30pm na daren ranar Alhamis.*
Jiya ya dawo daga can kauyen mahaifin shi wato garin kwami cikin garin hedikwatansu na Mallam Sidi, gajiya ce jiya ta rufe shi ya sa ya wuce gidansa ya kwanta da rana kuma yana camp ɗinsu tunda evening training suka yi. Sai da suka tashi ne ya koma gida ya yi wanka ya ɗauko tsaraban da suka matsa masa sai da ya ɗauko, kifi ne da su dankali doya da sauransu.
Tunda Allah ya albarkaci garin mallam Sidi da amfanin gona da kifin Kifin bushasshe ne, shi ba ya cin kifi tun da ya ji labarin sanadin kayar kifin ne ajalin mahaifinsa ya tsani kifi a rayuwarsa.
A msallacin kusa da gidansu ya yi sallar isha'i yau da Motarsa ya zo shi ya sa matasan anguwa suka ɗauki Ihu ga Aji ya zo, Aji yara da manya sunan Aji na bakinsu.
Tare da su Baba Sani yau ma suka yi sallar har da Baba Ɗanjuma. Tsaraban da ya zo da shi yara ya sauke a kofar gida ya ce su shiga da shi shashen Inna Meri.
Mansoor mutum ne mai kyauta hannunsa ya na sake ne, shi ya sa in dai yazo anguwan nan ya riga ganin mutane kenan. Ta bakin Inna Meri ta ce Baban Inna jama'a fa Rahma ne ka cigaba da aikin alheri wata rana in ka mutu wallahi da wannan shedar za'a tuna ka. Kuma tunda Allah ya rufa mishi asiri ai ya na da halin taimakawa. Bayan ya gama sallaman jama'an garin ya zo ya sallami gidansu.
Tunda tun bayan da ya yi karfi a ƙwallon kafa ko ya ce tun bayan da ya cike takardan Kontiragin ɗin da ya yi da kungiyar ƙwallon kafa ta Gombe United rayuwarsa ta sauya.
Duk watan duniya nan ya na kwasan albashi mai tsoka, sannan kuma ga alawus in sun fita gari sun buga wasa.
Ya fito ma ya faɗi irin kuɗin da yake samu sai ma a karyata sa. Shi ya sa ya ɗauki nauyin abincin gidansu duk wata sannan kuɗin makaranta Mariya da Walida da duk wasu bukatu na shashen su.
Bangaren su Baba sani ma yana siya musu kayan abinci duk wata wani lokacin kudi ya kan ba su, ko kuma ya wakiltan Auwalu tunda in aka ba su kudi sokewa suke yi suki siyan kayan abincin.
Auwalun ma daman ya kirashi tun shekaran jiya yana can kauyensu ya ce ya bari ya dawo, to shima anan gida suka haɗu shima dai yana masa bayanin matarsa ke da tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe ba shi da kuɗin ragon suna ballantana kuɗin hidiman suna. Kuma daman gini yake yi kuma yanzu aikin sai a hankali.
Bai damu ba ya ce zai tura masa kuɗi ta asusun bankinsa ya cire kudin hidimarsa sauran ya siya ma su Baba sani kayan abinci. Anan kuma take ya ba su kowanne dubu ashirin na cefane. Suna ta saka albarka duk da yasan a bayan idon shi sai sun raina.
In da zai rike abin da suka yi masa a baya ko kallo ba su ishe sa ba. Ba zai manta yadda suka ware shi ba, a cewar su shi Agola ne.
Sai dai alherin Baba Ɗanjuma yake kallo a gareshi shi ya sa yake musu komai baya nuna bambamci.
Ko gyaran gidan da ya yi kaf ɗakunan matansu ya sa an sassake an saka musu tayels da kuma fentin zamani.
Dakin Inna Meri da magajiya kuma ya maida musu shi kamar na yaran mata.
Bai nuna bambamci ba duk abin da ya saka ma Inna Meri shi ya saka ma Magajiya.
Amma bata taɓa godewa ba, sai ma masifa da ta ke yi a bar mata ɗakinta ɗan ta Auwalu zai gyara mata, yaron da ke fama da kansa ammh fa da aka gyara ɗakin ta ji daɗi ba ta dai nuna ba har ya'yanta da a shekarun baya sun sha su nuna bambamci kiri Kiri tsakaninsa da Mu'azzam.
Tunda shi sun haɗa uba shi kuma zuwa da shi Inna Meri ta yi agola ne mara galihu.
Tare suka shiga gidan da Auwalu Magajiya na ƙofar ɗakinta tana tatan nikan geron kunun safe da za ta dama suka shigo.
Auwalu ya fara gaisheta ta amsa cikin fara'a amma Mansoor na cewa" Barka da dare Magajiya." Ƙim amsawa ta yi shi kuma ko ajikinsa ya tsallake zuwa shashen Inna Meri.
Ya bar Auwalu tsaye ya a faɗin "Magajiya kina jin Mansoor na gaishe ki kika amsawa?
Sai ta masifa tana faɗin"Ban amsa ba sai kuma na yi laifi? Ba ka ji irin gaisuwan na shi ba ne wai barka da dare kamar wata sa'arsa ai in uwarsa ce meri ba haka yake gaisheta ba."
Auwalu yace"Magajiya tsakani ga Allah ko Inna Meri haka yake gaisheta ko Baba ne kuwa shi haka yanayin gaisuwarsa yake"
Sai ta fara balla masa harara ta na faɗin "Ta fi can sakarai mara kishin kai kawai."
Saboda yadda ya ji tana faɗa yasa ya fasa ma shiga ɗakinta kawai sai ya Juya ya fice.
Tun tasowarsu wannan halin na magajiya da shi suka ganta. Kowa hakuri yake yi da ita musamman ma Baba.
Ba domin yana hakuri ba tuni ya jima da sakinta tunda ta daɗe cikin zamanin rashin mtumci acikin gidan nan ba adadi.
Shi ko Mansoor yana can ɗakin Inna Meri suna ta fira ya na bata sakon gaisuwan mutaanen can da suka ce suna gaisheta.
Ya iske ma Yaya Amina a gidan ta zo tun ɗazu har ta na yi masa tsiyan ta fi wata biyu ba ta ganshi ba. Mirmishi kawai ya yi batare da ya yi mgana ba.
Inna Meri ta kallesa kafin ta ce"Ya ka samu Goggon naka Yalwa? jikinta da sauki ko?
Mansoor yace"Eh ta samu sauki, amma na bar mganar a kaita asibitin cikin gari a dubata, na ba ma jikanta ɗin nan lambata na ce in da wani abu ya kirani."
Inna Meri tace"Allah Sarki yalwa mace mai son zumumci ba'a wata biyu ba ta zo garin nan ta duba ka ba, sannan ba ta zuwa hakanan mata nan ta na son zumunci kwarai bata manta da ɗan dan uwanta ba."
Yaya Amina ke faɗin ko itama ta san lokacin da ta ke zuwa ta zo mu su da kifi da dankalin hqusa. Inna Meri na kara faɗa mata kirkin ƴanuwan mahaifin Baban Inna da suka yi mata karamcin da ta kasa mantawa.
Shi dai yana gefe yana jin su ya yi shuru bai saka baki ba. Yana tunanin zuwan da ya yi yadda Yalwa ta matsa masa da mganar aure wai sa'aninsa har da masu mata biyu.
Ya je Bauchi gidan Baba Kabiru ya duba cikin ya'yansa suma yan boko ne irin sa tunda baya son yan kauye.
Sai da ya yi mirmishi shi tun bayan da ya rasa Mimi ko da wasa bai kara kallon wata mace da sunan so ba.
Tun lokacin rayuwarsa ta sauya ya cire babin aure a tunaninsa.
A tunaninsa ba zai iya kallon wata mace da sunan so ba, to so guda ɗayan da kaunar gabaɗaaya ita ya damkawama kuma da ta tashi tafiya sai ta tafi da abin ta gabaɗaya.
Zuciyar Mansoor yanzu babu sararin da zata iya samar ma soyayya matsugguni ba.
Ko Inna ya ka sa faɗa yadda suka yi da Gwggon nasa, ya dai ce mata ta bari in ya kara dawowa sai su yi mgana. Su ma ya yi raban kudi sosai a garin ƴauwansa ne bayan nan Gombe ba shi da kamarsu tunda nan ne tushen mahaifinsa.
Yaya Amina ce zata ta fi mijinta ya dawo daga aiki ya zo ɗaukanta sai Mansoor ya daukan mata kullin buhunta da Inna Meri ta ɗibar mata tsaraba zuwa waje, suna tafe ta na ba shi labarin Bintu ta zo gidanta da yadda ta ce ya je gidanta ya yi mata faɗa gaban Kishiyarta. Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba ya na can ma ta kirashi suka gaisa kuma yasan ma'anar gaisuwarta daman ya na da tunanin barin mata sako a wajen Inna ko Walida sai ta aika mata da shi. Sai da suka gaisa da mijin nata sannan suka yi sallama ta hau mashin din suka bar Kofar gidan Baba Danjuma kuma na can gefe shi da Mallam Hashimu suna ta mgana, Mansoor ya rasa menene suke tattaunawa haka tun ɗazu suke tsaye suna mgana ba ta kare ba. Har ya Juya zai koma cikin gida saboda tuwon Inna yake son ya ci a camp yau zai kwana gobe suna da morning training.
"Aji."
Ya ji an kira sunanshi, ya ji muryansa shi ya sa ya juyo yana kallonsa yana karisowa kusa da shi.
Cikin dariya ya ce"Shege Aji motarka na gani sai kuma na hango ka daga nesa."
Hannu ya bashi suka tafa lokaci ɗaya yana faɗin"Makama ya garin? Kwana da yawa"
Wanda aka kira da Makama ya ce"Aji gaskiya ka sauya rayuwarka, shiken an ka janye jikin ka daga na mutane yaushe rabon da mu haɗu da kai?. Muna gari ɗaaya Aji ammh sai mu yi wattani bamu haɗu ba."
Mansoor ya ce"Rayuwar ne sai a hankali makama."karamin tsaki ya ja kafin ya ce"Ba wani rayuwa, Mu'azzam da ba garin nan ya ke aiki ba duk zuwa sai ya kiramu mun haɗu amma kai kana garin nan ko an kira sai ka ce baka da lokaci an ya Aji ba za a manta baya rayuwata ta yi kyau ba"
Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba Makama ya dafa kafaɗarsa kafin yace" har fa group mu ka buɗe namu mu biyar ko tari baka taɓaa yi ba har abubuwan biki na da ake tattaunawa ba ka ma san halin da ake ciki ba." Mansoor ya ce"To yanzu tunda ka zo ba sai ka faɗa min ba."
Makama ya ce" To ya na iya, biki fa ya zo saura wata biyu yanzu."
Mansoor yace"Allah ya nuna mana."
Makama ya amsa da Amin Amin.
Tsiya ya fara yi masa wai duk sun yi aure shi ya zauna sai ya zama tuzuru.
Mirmishi ya yi masa bai yi mgana ba shi kuma ya kallesa lokaci ɗaya yana faɗin"Ka ma saki jiki mallam wallahi da kai za'ayi komai a bikina baka isa ka tsame jikin ka ba." Mansoor ya ce"Allah ya sa muna raye za a yi, kuma ka yi fatan ba ni da wasa a lokacin."
Makama ya harzuka cikin fusata ya ce"Na bi wasan da gudu na taka da takalmin kafata" Har yana bubbuga kafa da ya sa sai da Mansoor ya yi yar dariya yana faɗin"Makama ba za ka canza ba."
Cikin yar dariya ya ce"Ina fa zan canza, ni fata na Allah yasa a wajen bikina ka samu cikin ƙawayen amarya wata ta yi wuf da zuciyarka."
Ido ya saka masa kafin ya ce" kana ganin akwai wacce za ta iya?
Makama ya buga kafaɗarsa lokaci ɗaya yana faɗin"Tsab kuwa mutum ne fa kai ba robot ba." Sai kawai ya jinjina kai kafin yace"To sai mu gani in za su iya."
Cigaba da hira suka yi duk dai rabin hira daga bakin makama ne.
Har Baba Danjuma ya kariso suka gaisa ganin haka ya sa ya ce bari ya shiga ciiki ya gaida Inna Meri. Tare suka shiga ya gaida Inna Meri taji daɗi sosai har ta na dibar masa Kifin da Baban Inna yazo da shi ta ce ya kai ma baabarsa.
Da zai tafi ma Mansoor ya rakosa har waje sun ka ɗan jima kafin su yi sallama.
Shi Makama gidansu na can Tudun wada ne yazo Arawa ne gaida wani abokin babansu.
Yadda suke hiran za ka fahimci sun jima da sanin juna.da kuma yadda ya ke labaran wasu abokan na su da Aji ya daɗe bai haɗu da su ba kuma suna gari ɗaya kamar irin su Shamsu, wanda ko a baya ba abokinsu ba ne amman abokin faɗan Aji ne.
Shi fa rayuwarsa gabaɗaya ta sauya ko a baya da yake da miskili ammh yanzu sai ya fi miskili iya miskilanci a baya yana shiga mutane ammh yanzu ya daina shiga jama'a kwata kwata ya koma yin rayuwa shi kaɗai kamar ba shi da kowa abokinsa kawai ƙwallon kafa ne.
*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
💃💃💃
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT
SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA
HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU
INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 26