Bintu ce fa, ga Walida."
Ta faɗa ta na nuna Walida Hajiya ta rike baki cikin mamaki kafin ta ce"Ikon Rabbi. Bintu ke ce haka? Sai kuma ta kalli Walida lokaci ɗaya ta na faɗin"Ba shakka shekarun da yawa Walida an zama yan mata, to waɗannan yaran fa?
Inna Meri ta tura mata su Husaaini gabanta tana fadin"Jikokin ki ne Hajiya, yaran wajen Bintu ne yan biyu ne ga su nan Hassan da Husaini."
Hajiya ta riƙesu kusa da ita ta na faɗin"Ba shakka , yara nan Allah ya raya ku kun ji ko?
Ta fada ta na shafa kawunan su duka biyu, su kuma suna ta kallonta.
Kara gaisawa suka yi Inna Meri ta kara yi mata gaisuwa Hajiya ta ce"Uhm ke dai bari Meri Kabiru ashe ba'a deɓo da yawa ba."
Inna Meri ta ce"Allah ya sa an huta Allah ya kyautata tamu bayan ta su.".
Hajiya ta yi ta amsa da Amin Amin, ganin mutane sun yi yawa a falon ya sa Hajiya ta kalli Inna Meri lokaci daya tana faɗin"Meri ko za ku shiga ciki ku jirani na sallami baki na? Daman ina neman ki kuma ko ke ba ki neme ni ba wannan karon ni zan neme ki." Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"To bakomai Hajiya, Ina Binta ne? Ina so itama na yi mata gaisuwa su Bintu ma suna son su ma su yi mata gaisuwa."
Hajiya ta ce bari ta saka a kaisu ɗakin Binta
Baaba Uwani da ke kitchen ta ƙwalama Kira ta na zuwa tace ta raka su Inna Meri ɗakin Binta itama ga ta nan zuwa duk da ita Baaba Uwanin ba ta taɓa ganin Inna Meri ba tunda lokacin da ta zo gidan tuni Inna Meri ta daina zuwa shi ya sa ba su san juna ba Amman da Hajiya ta ambaci Meri sai da ta so ta ɗauki sauna tunda in dai suna hiira da Hajiya tana yawan ambaton sunan Meri din da kuma irin kyautatawar da ta yi mata lokacin da ta yi aiki a gidanta.
Har ɗakin Mimi Baaba Uwani ta raka su, Mimi na kwance saman gadonta da ya sha shimfiɗar alfarma da kyakyawan zanin gado na kamfanin FHB CLOTHING Phone no 08034109622
Wtsapp no.08080266674 Zannuwan gadon su masu kyau ne da inganci ka daɗe kana mora kamar yau ka siye shi.
Ta yi kwamciyar ruf da ciki Rukky ne ke zaune a gefen gadon tana laatsa wayarta jefi jefi suna hira da Mimin da ba'a jin muryanta sanda ma Baaba Uwani ta shigo ta ce baƙi ne Hajiya ta ce a shigo da su Mimin ba ta iya tashi zaune ba a tunaninta tunda ta ji Hajiya ta ce a shigo da su har cikin ɗakinta sai ta yi tunanin kila bakin na gida ne.
Dukkansu a tsaye suka tsaya tunda mai ɗakin ba ta ko tashi ba, Rukky ce ta kallesu lokaci ɗaya tana faɗin " Sannun ku, Mimi ki tashi an zo miki gaisuwa."
Sai Mimi ta yunkura ta mike tana gyara zaman rigan jikinta wata doguwa mai ruwan hoda kanta ba ɗankwali tunda daman hula ce ta kuma saɓule kanta, har ga Allah ba ta gane Inna Meri da farko kamar Hajiya ba, ta ji sanda ta yi mata sannu sai ta ce cikin dashewar murya"Ku kariso ku zauna mana, Rukky hayo gadon ki ba su waje" Sai Inna Meri ta ce"Bari mu zauna anan ya isa." Ta faɗa tana zama saman cafet din da ke makeken bedroom din Mimi. A cikin ran Inna Meri tana faɗin an sauya komai na ɗakin da ba haka ta san shi ba yanzu ko cike yake da kayan alatu na more rayuwa kamar ba ɗakin budurwa ba, to budurwa ce yar gata wacce ta san kanta Dole ɗakinta ya kasance abun kallo haka Bintu ke ta sakawa a cikin ranta nan da nan taji makeken gadon Mimi ya gama tafiya da Imaninta taji kamar ita ce ita, a cikin ranta taji in sha Allahu sai ta yi irin gadon nan itama.
Inna Meri ta san Mimi ba ta gane ta ba har suka yi mata gaisuwa kuma har su Bintu ba ta gane ba, ta dai kallesu kamar tana so ta ji ta san fuskarsu amman halin da take ciki ya hana ta tsayawa ta gane su, sai ta koma ta kishigiɗa kawai tana jin Rukky na faɗin"An zo miki gaisuwa kina ta kwanciya kuma? Cikin wani yanayi ta ce"Na amsa su Rukky ki barni kaina ke ciwo."
Inna Meri ta bi Mimi da kallo wato a kwalban nan ta zamani ana rage mata ma kyau a fili tafi haka kyau da hasken fata.
Inna Meri ganin kawar Mimi na ta kallonsu ga su Hassan sun fara kiriniya ya sa ta ce"Hajiya ta ce mu jira ta gata nan zuwa."
Sai Mimi ta muskuta kafin ta ce"Laa bakomai ku jira ta ɗin." Sai ta koma tana kallon yan biyun Bintu da suke neman yin wasa Walida ta yi musu jan ido, sai suka burgeta da ganinsu yan biyu ne kuma ma su kama sosai sannan sun ci gayunsu da kaya iri ɗaya.
Rukky ma su take kallo acikin ranta ta ji ta na sha'awar yan biyu, amman wahalansu ne ke ba ma mutane tsoro Walida kuma Bintu ta ke yi ma raɗa da cewa"Gaskiya Anty Mimi ta fi kyau a fili."
Bintu ta yi dariya kafin ta ce"Gaskiya kam."
Dai dai Lokacin da Hassan ya ture Hussaini ya kusa faɗuwa sai da Rukky ta mike ta rike shi da Sauri Bintu ta daka ma Hassan tsawa Lokaci daya tana faɗin"Kai ba na son mugunta, in ka turesa ya ji rauni fa?
Kawai sai ya saka kuka Inna Meri ta kirasa da hannu tana faɗin "Taho nan kyale Mamanka kai da kake da ni ina kai ina kuka Megidana". Take faɗa tana masa dariya jikinta ko ya zo ya lafe yana sharen kwallah Hussaini kuma na ganin haka shima sai ya kwace daga rikon Rukky ya dawo ya kwanto a jikin Inna Meri wai shima sai an ɗauke shi.
Rukky ta fashe da dariya Mimi na taya ta ganin Inna Meri ta haɗa duka ta ɗauka saman jikinta tana faɗin "Ya na iya? Ni mai mazaje har guda biyu."
Rukky ta koma ta zauna tana faɗin "Ina jin ana yawan labarin suna da kishi sai yau na gani, wace ce mamansu hala.?
Ta faɗa ta na kallon su Bintu sai Walida ta nuna ta, Rukky ta ce"Ma sha Allah Allah ya raya miki su, Sun samu jikin kaka sun yi luf Allah dai ya kara tsawon kwana."
Kafin Inna ta samu zarafin Magana Hajiya ta shigo dakin ganin su Inna Meri zaune a kasa ya sa ta kalli Mimi tana faɗin"Ba ki gane su ba ne hala Binta?
Mimi da kanta ke Sara mata ta dafe shi tana yamutsa fuska kafin ta yi mgana Hajiya ta yi saurin cewa"inna Meri ce fa, tare da Bintu da Walida fa, ni kaina ban ganeta da farko ba sai daga baya."
Mimi ta yi kasaƙe tana kama sunan da Hajiya ta ambata ai sai ga ta ta zaro ido da sauri ta diro daga kan gadon ta tsaya kan kafafunta tana kallon Inna Meri da su Bintu sai a lokacin ta shaida su ɗazun ba ta wani kallesu sosai ba duk da dai suka sauya mata gaskiya, kunya ta kamata Inna Meri na yar dariya ta ce"Shekarun da yawa Hajiya ba lalle ta shaidamu kai tsaye ba."
Jikin Mimi sai ya fara rawa sai ta rarumi mayafin Rukky ta saka sai gata gaban Inna Meri ta durkusa tana faɗin"Inna Meri ki yi hakuri wlh ban gane ki ba ne"
Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce"Bakomai Binta ya ƙarin hakuri kuma? Allah ya jikansa da Rahma.". Mimi ta amsa kanta na kasa tana jin wani irin kunya na kamata. Mamaki ya kama Rukky ta kalli Hajiya tana so ta yi mgana sai ta fasa jin Mimi na faɗin"Bintu. lalle Bintu an zama uwa ke ce haka?.
Bintu ta saka dariya kafin ta ce" Auran wuri su Inna su ka yi min, amman har gobe Bintu na nan da yan matan cinta."
Ba Mimi ba har Hajiya da Rukky sai da su ka yi dariya, Mimi ta ce"Kai Bintu kina nan dai da halin ki" inna ta ce"Wannan ai ba za ta taɓa sauyawa ba."
Mimi tace"Walida an zama yan mata Eyee, Ina su Yaya Amina da Yaya Halima?
Walida tace" Suna gidajen su, da Inna ta ce zata aika musu su zo mu zo nan gaisuwa tare sai kuma ta sha'afa."
Mimi ta kaɗaa kai kafin ta ce"Allah Sarki ki ce don Allah ina gaishe su."
Walida ta amsa ma ta da in sha Allahu za ta gaya musu , Yan biyun Bintu Mimi ta kira abun mamaki ba su yi mata kiyuwa ba, Hajiya kuma ta kara ficewa ta ce bari ta sallami bakin Kumo za su tafi.
Rukky kuma ta ga Mimi ta manta da ita sai hiran ta ta ke yi, amman tun ɗazu da ta zo kwance ta yi mata tana mgana dakyar ba ta kawo komai ba ta ɗauka kila cikin yan'uwansu ne, ganin haka ya sa ta yi shirin tafiya tace Mimi ta ba ta mayafinta za ta wuce gida. Sai ta ba ta nata ta ɗauko wani karamin hijabinta iya gwiwa ta saka ta ce ma su Inna Meri bari ta raka kawarta, su ma su ka yi sallama da Rukky har 500 500 hundred ta ba ma su Hassan su ka karɓa suna faɗin sun gode ko domin hararan da suke sha a wajen uwar ta su.
Sai da su ka fito haraban gidan sannan Rukky ta kalli Mimi kafin ta ce"Wai su waye waɗanan da kina ganinsu kika mike tsaye? Ko ƴan'uwan ku ne? Mimi ta yi mirmishi kafin ta ce" Surukata ne da ƙannen saurayina." Rukky ta saki baki tana kallonta kafin can ta ce"U Mean maman Aji ne da ƙannensa?
Mimi ta lumshe ido jin sunan rabin ranta da aka kira kafin ta buɗe su akan na Rukky sannan ta jinjina mata kai alamun hakane.
Rukky ta riƙe baki ta ce"Ikon Allah dalilin mutuwa yau sai ga shi sun zo, ko da yake ai kin ce ƙaninsa ɗin nan ya yi miki gaisuwa da sauran abokan su Usman to shi baƙin masifaffan Ajin ya kira ki ya yi miki gaisuwan kuwa? na ga mahaifiyarsa da ƙannensa babu ruwansu amman shi kam wlh ba shi da mutumci ai ko Allah ma gafurin Rahimunun ballantana shi ɗan Adam ba kowa ba."
Mimi ta rausayar da kai kafin ta juya tana faɗin" Sai anjuma Rukky ki gaida Mama."
Rukky ta taɓe baki tana faɗin "Uhm Mimi Allah ya yaye miki wannan makahon son da kike yi ma wannan gayen."
Mimi na jin ta amman ba ta tsaya ba ta yi shigewarta cikin gida, itama Rukky ta juya ta fice daga gidan ta na tunanin ita ba ta ga abulin da zai saka har a wannan lokacin Mimi ba ta daina son wannan masifaffan gayen ba, ga bakin fuska ga bakin rai da faɗin rai Allah dai ya sauwake.
Ko da Mimi ta koma a falo ta tsaya saboda Anty Sadiya babbar ɗiyar yaddiko ta ja ta da hira daga ita har Hajiya ba su samu kansu ba sai da bakin Kumo suka tafi sannan su ma su Anty Sadiya suka tafi.
Sannan Hajiya ta koma wajen Inna Meri Baaba Uwani ta sako abinci sai Hajiya ta saka a kai ma Inna Meri na ta a ɗakin Hajiyar daman tana so su yi mgana, Hajiya dai ta saka a gidan su ka yi sallar azahar kuma ta matsa ma Inna Meri sai da ta ci abincin da aka kawo mata.
Lokacin da ta ce a ƙoshe take sai da Hajiya ta ce mata" Nan fa gida ne Meri, kar ki manta har abincin nakan saka ki ɗaukan ma yara kada rayuwa ta sa ki sauyamin don Allah." Jin haka ya sa ta saki jiki ta ci doya da miyar ƙwai ɗin da Baaba Uwani ta yi bayan ta gama ta sha ruwa. Hajiya ta zaunar da ita su ka fara labarin bayan rabuwa da rayuwa.
Hajiya ta kalli Inna Meri tana faɗin "Meri ina ɗan Inna? Ina shi Baban Inna? Ina fatan duk suna nan lafiya"
Inna Meri tace"Suna nan lafiya, ɗan inna na kano yana aiki ɗan Sanda ne yanzu. Ya yi aure da matarsa Hibba da ɗansu mai sunan Mallam, Baban Inna dai bai yi aure ba yana nan yana buga ƙwallon kafa auren dai har yanzu lokaci bai yi ba."
Hajiya tace"Allah Sarki haka Binta ta gaya min kila ki kinsan kwanaki sun haɗu wajen bikin ƙanwar ƙawarta ɗin nan Rukayya da ta fita ko?
Inna Meri tace" Ɗan Inna ya gaya min kinsan dai uban gayyar ba zai taɓa faɗa min ba."
Hajiya na dariya ta ce"Ikon Allah Mansoor manya hali dai na nan an girman ma ba'a daina ba."
Inna Meri ta yi wani mirmishi kafin ta ce" Wasu abubuwan sun ragu amman wasu kam kamar an kara ingiza su ne, fatan mu dai Allah ya shirya mana gabaɗaya."
Hajiya ta amsa da Amin Amin, tana so ta dauko mganar amman kuma kunya da nauyi sun hana ta fara maganar sai kame kame take yi. Dakyar ta iya karfin halin cewa" Meri ki yafe ni don girman Allah ni nasan mai laifi ce a gare ki tun akan abin da ya faru a baya"
Inna Meri ta yi saurin cewa" Ba komai Hajiya ni ban rike ki a raina ba, ko yanke hulɗa da na yi dake na yi hakan ne saboda samun mafita ba domin ina jin haushin ki acikin raina ba."
Sai kawai Hajiya ta fashe da kuka cikin kukan take faɗin "Wlh Allah ɗaya ko Meri tun bayan abib da ya faru yaro nan Mansoor ke raina ina ta so na zo na duba shi amman kunya da nauyi suka hana ni, har ga Allah ban san abunda Kabiru ya shirya ba kenan da ban yarda na tura su wajensa ba, ki yafe min shima Kabirun ku yafe masa Wallahi tallahi kafin rauwarsa ya yi nadaman abin da ya aikata muku."
nna Meri ta riƙe hannayen Hajiya da sauri tana faɗin " Da gaske na ke Hajiya ban riƙe ki a raina ba wlh, kuma komai ya wuce tun a wanchan lokaci maganar kuma wanda ya rasu ai ba komai tsakanimu sai fatan Allah ya sa ya huta."
Hajiya na jan majina ta ce"Amin Amin Meri na gode. Wlh ina gaya miki ana gobe za su taho nan shi da Murja a daran ya rasu, kuma da niyar yazo ya roke ku gafara tare da neman afuwan Mansoor sai dai Allah bai nufa ba, bai wayi gari da rai ba."
Inna Meri ta hi tausayin Hajiya Itama kamar ta yi kuka ta ce"Allah Sarki ai Allah ya ga niyarsa, bakomai wlh Allah ya jiƙan sa da Rahma daman can Allah ya kaddara sai hakan ya faru."
Hajiya ta saki hannun Inna Meri ta na tsane hawayenta da hannu ta ce" Kabiru ya rasu da sunan Binta a bakinsa ya na matukar tausaya mata tun bayan abin da ya faru Binta ba ta kara ba ma wani namiji dama ba, da gaske ya ke yi kafin rasuwarsa Murja ta ce ya ce har azumin kaffara zai yi in har Mimi na son Mansoor har yanzu to shi ya saki ya kuma ba ma Mimi dukkan daman rayuwa da wanda take so."
Hajiya ta karishe faɗa tana kallon yanayin Inna Meri wacce ta yi jim kaɗan tana nazari, ita fa ta ga ya ma Hajiya komai ya wuce Baban Bintu ma haka amman babban matsalan shi ne uban tafiyar duk da itama za ta iya rantsuwa ta ba da shaidan har gobe ya na son Binta kuma dalilinta ne yaki ba ma rayuwarsa haske ko kaɗan sai dai in ina ita ina taran Baban inna da wannan maganar? Ai wannan bakar zuciyar tasa kamar ta kafuran farko ba za ta barshi ya baiwa zuciyarsa abin da take so ba.
"Kin yi shuru Meri, ko kina ganin da matsala ne?
Hajiya ta faɗa ta na kallon Inna Meri, ita kuma sai ta rausayar da kai kafin Ta ce" Hajiya da gaske nake yi da nace komai ya wuce kuma har abada bazan ƙi Binta a matsayin Surukata ba, sai dai abu ɗaya ne matsalan Baban Inna a gaban ku ya yi rantsuwan ko zai mutu bai yi aure ba ba zai iya auranta ba, Hajiya kin san wasu daga cikin hallayarsa kafiya da naci ga zuciya da riko har gobe Baban Inna ya kasa manta abunda ya faru tun daga lokacin rayuwarsa ta sauya ya daina shiga mutane ya koma rayuwa shi kaɗai, ya daina nuna ya na jin daɗin duniyar nan ma Hajiya mun yi mun yi akan ya daina tuna baya ya fuskanci gaba amman har gobe ya kasa gina ma kansa wata rayuwar, kina ganin a wannan halin da ya ke ciki zai karɓi maganar Binta a karo na biyu.?
Inna Meri ta karishe faɗa tana kallon Hajiya itama sai ta kalleta cikin tunani da nazari, Inna Meri ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce"Shi ne hanzarina Hajiya, da kamar wuya gurguwa da auren nesa wannan zuciyar ta Baban Inna ni kaina ta na bani tsoro bansan adadin sallar daren da na yi a kan sa ba, ina rokon Allah ya ya ye masa wannan bakar zuciyar ko ya samu shima ya yi rayuwa irin ta kowa" Yadda Inna Meri ta karishe a raunane ya sa Hajiya taji itama jikinta ya yi sanyi sai ta kasa mgana.
Illah kai da ta kaɗa tana faɗin "Kafin rasuwar Kabiru Murja ta jaddaddamin ya ce a yi ma Binta duk abunda ta ke so, ni kuma nan duniya ban ga abunda Binta ta jima ta na so da kauna tare da bege irin Mansoor ba."
inna Meri ta ce"Ikon Allah! A cikin ranta kuma sai tace ai shima har gobe bai daina begenta ba, Hajiya duk sai gwiwanta ya yi sanyi sai dai ta cigaba da gaya ma Inna Meri irin wasiyar da Kabiru ya bari kafin ya rasu har acikin ran Inna Meri ta tausaya kuma ita ba ta da matsala mai yin shine matsalan da kansa. Sai ga Inna Meri sai a'asar su ka bar gidan Hajiya shima Baban Inna ke ta faman kiran wayar Inna Walida ta ɗauka cikin muryansa ta koda yaushe ya ce"Ina Innar ? Lokacin tana ɗakin Hajiya sai ta yi masa ƙaryan tana sallah.
Cikin yanayin maganarsa Ya ce"Ina kuka je na zo bakwa nan gabaɗaya.?
Sai Walida ta rasa bakin mgana Binta na yi mata raɗan ta ce sun je gaisuwa dakyar ta iya ce masa suna cikin gari sun raka Inna gaisuwa amman ga su nan zuwa.
Lokacin Mimi na ɗakin amman hankalinta na kan waya ne, Walida na sauke wayar Bintu ta ce"Da kin sake kin gaya masa in da mu ka je da yau sai yayi biji biji dake."
Walida tace"Ina sane shi ya sa na rasa abin da zan ce."
Allah ya taimaka sai ga Inna Merin ta ce su zo su tafi, Hajiya ta ji daɗi ita da Mimi har bakin get suka rakasu Hajiya na jadaddama Inna Meri sai ta zo da kanta har gida in sha Allahu. Sai a hanya ne suke faɗama Inna Meri Baban Inna ya kira.
Cikin faɗuwar gaba ta ce"Allah ya sa dai ba ku ga ya ma sa in da mu ka zo ba ko?.
Bintu ta ce"Wa zai je ya yi karo da Kura? Ce ma sa walida ta yi muna cikin gari gaisuwa."
Inna Meri ta ce"To gwara hakan, ba na son fitinarsa da yamman nan."
Adaidaita suka hau saboda su Hassan suna zuwa Kofar gidan Wanzamai suka ci karo da shi tare da Baba Danjuma sun fito sallah. Suna ko ƙarisowa wajen su su Bintu na rige rigen gaishe da Mansoor ita da Walida sau ɗaya ya amsa, yana sanye da riga da wando baki da fari a jikinsa. Kansa da Pcap kamar ko da yaushe.
Shi Baba Danjuma bai san Mansoor bai san inda su Inna suka je ba kawai sai ya kalli Inna yana faɗin"Na ga kun jima ne? Ko Hajiyar ce ta tsaida ku? Inna Meri ba ta kawo zai iya cewa wani abu ba kawai sai ta ce"Eh wlh shiyasa mu ka jima." Mansoor ke yi ma Inna barka da zuwa, Sai kawai Baba Ɗanjuma ya kallesa yana faɗin"Daga gidan Marigayi sulaiman Dabo su ke, da yake Mu'azzamu ya yi waya da ita Innar taku ya ce sun dawo shi ne ta ce za ta je ta yi musu gaisuwa na ce hakan na da kyau an yi zaman amana a baya Allah dai ya jikan sa."
Ba su Bintu kaɗai suka tsure ba har Inna Meri, shi ko tun kafin Baba Ɗanjuma ya gama mgana sauran rahaman dake saman fuskarsa ta gushe bai kara mgana ba.
Inna Meri ta tasa jikokinta gaba za su shiga gida da sauri Bintu ta ce"Inna bari kawai mu wuce yamma ta yi"
Sai da dariya ta kusa kama walida wato ta san abin a zai biyo baya dole ta gudu in gari banza ne Bintu sai Inna ta yi mata jan ido take tafiya.
Ita kanta Inna Merin a sanyaye ta shiga gidan suna shiga da Magajiya suka fara cin karo, Mariya ba ta nan ta na gidan Zuwaira, Inna na yi mata sannu da gida dakyar ta amsa Ita walida ma wucewarta ta yi, ita kanta Innar yau ba tsaya bin Magajiyar kamar uwarta ba ta biyo bayan Walida.
Suna shiga ɗakin Walida ta juyo tana faɗin"Inna yau mun shige su mun yi ma Baban ki laifi"
Inna Meri na rataye hijabinta saman Kofa ta ce"An yi masa laifin sai ya zo ya dake ni."
Innar ta faɗa a kufule sai Walida ta ja bakinta ta yi shuru ta yi ciki ita kuma Inna sai ta fara zuba ruwa a buta ta shiga ta kama ruwa daman Hajiya ta yi ta yi su tsaya su yi sallar la'asar Inna Meri ta ce sun sai sun isa gida. Ta fito kenan ta fara alwala sai gashi ya shigo da gif gif da ɗin tafiyarsa kafin ma ta ɗago kanta ta ji maganarsa a masifan ce a saman kanta.
"Inna fisabillahi me kuka je yi gidan nan?
Tana shafan kai ta ce"Gaisuwar mutuwa."
Ta faɗa itama kai tsaye, wani abu ne ya ji ya taso mai cikin kokarin danne abun ya ce"Inna har za ki iya zuwa gaisuwar wannan mutumin?
Inna ta ce"Eh mana ai musulmi ne ɗan uwana ko?
Ta katse shi cikin gajiya da maganarsa zai kara mgana ta ɗaga masa hannu cikin kosawa kafin ta ce"Ka ga na je gaisuwa gidan maƙiyanka sai ka dakeni Mansoor haba don Allah, kai kenan shigen bakar zuciya ko a baya da ka ga na daina hulɗa da Hajiya wlh ba saboda abin da ya faru ba ne, saboda kai ne ba na so in dawo maka da abin da ya wuce ne amman ba domin tsoron fininarka ba."
Ta faɗa kai tsaye kafin ta juya ta cigaba da wanke kafarta, shi kuma takaici ya hana shi mgana. Kirjinsa ke wani suya yana jin hucinsa na fita ta bakin hancinsa.
Sai kawai ya juya yana faɗin"Shike nan Inna ai shike nan kawai."
Gif Gif kamar wani damisa haka ya juya ya fice Inna ta rakasa da harara Ina dalili da sanyin la'asar zai zo ya tada mata da hankali. Ta kuma san tunda ya fusata ya fita an yi yaji sai ranar da kuma aka huce.
Tsab ta idar da alolanta ta shiga ɗaki tana kiran sunan Walida wacce ta leko tana faɗin "Ya ta fi ne Inna?
Ƙaramin tsaki ta ja kafin ta ce" Lokacin sallah ya kure Walida ki fita zuwa alola."
Daga haka ta shimfiɗa sallaya nan tsakar falon ta tada sallah.
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
Ina iyayem yara kuke kuzo MAIDALILI LACE AND THRIFT takawomuku ingantattun overralls bodysuit da longsleeves domin inganfa lapia dakuma kawara suturun yaranku.kamar yanda kuka sani damuna saida overall kisaqa bebynki ki sinkumeshi bakinki alaikum baruwansa da kamuwa da sanyi.akwai na yammadatan yara kamar yan 3yrs dabasan lulluba da sanyinnan kiyuta rufe yaro yana budewa tokizo kisaya musu overrall kawai dare nayi kizura yaro ciki kisamasa sock da saf wannan shi ake kira blanket huta🥰kiyi kokari ki killace yaranki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 26