Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kunna, Mansoor ne ba shi da wani masaniya a kanshi sanin shi fa ba ka gane gabansa ballantana bayansa to kila har gwara shi ya kan tsaya su yi magana mai tsawo, wasu tuni ya yanke wannan alaqar a tsakanin su. Bai taɓa tunanin haka soyayya ke da zafi ba sai akan Mansoor a lokacin ma daga shi har Mimi suna da karancin shekaru shi ya ɗauka a shekarun da suka ɗauka ba sa tare soyayyarsu za ta disashe ashe ba haka ba ne, tana nan ta kara girma ne acikin zukatan su. Ba zai taɓa man tawa da ciwon da Mansoor ya kwanta a lokacin ba, da kukan da ya riƙe ƙirjinsa yana yi ba, bqasonta yake yi ba kaunarta yake yi sannan sun shaku sosai soyayya ta rufe musu idon da suka kasa gane bambamcin dake tsakaninsu har sai da komai ya kwaɓe sannan Mansoor ya fahimci abin da aka jima ana nuna masa. Tun Mu'azzam na zaman jiransa har barci ya ɗaukesa Mansoor bai fito daga tiolet ba. Sama da awa ɗaya sannan ya fito daga cikin tiolet ɗin jikinsa na faman ɗigan da ruwa. Tsaye kawai ya yi a tsakiyar falon ookaci ɗaya yana mai harɗe hannayensa a saman ƙirjinsa. Mu'azzam yake kallo yana barcin sa cikin salama da kwanciyar hankali ba shi da damuwan komai a cikin zuciyarsa. Yana jin dama shima haka yake ba shi da wata damuwa. Dama shima zuciyarsa ta sauke wannan nauyin abin da ya tokareta shekaru goma ya yi rayuwarsa cikin salama ba tare da damuwa da tunani ba. Duk lokacin da ya tuna abun sai ciwon da ke kirjinsa ya dawo sabo, saboda ita ne har gobe ya kasa kallon wata ƴa mace da sunan kallon soyayya. Saboda ita ce ya ji aure ya fita kansa kwata kwata ya ji a duniyan nan ba zai iya zaman aure da wata mace ba. Saboda ita ne ya sauya rayuwarsa da ga mai yawan hira da son mutane zuwa wani mutum mai son kaɗaici da son zama shuru, Saboda ita ne ya ji ya tsani masu kaki gani ya ke yi dukkansu haka suke marasa adalci da sanin ɗarajan ɗan Adam. A lokacin baya da ita ya yi mafarkin kasancewa har karshen rayuwarsa. Shi fa mafarkansa gabaɗaya ko ɗaya bai cika ba, duka ya rasa su sai wasu ya gina sabbi acikin duniyarsa. _*Bai tab'a tunanin Soyayyarsa da MIMI akwai wasu tarin bambamce bambancen da mutane ke hango masa wanda shi nashi hangen bai taɓa kawo masa ba. Ya ɗauka ita soyayya babu ruwanta da bambamcin jinsu ko hallita, ba ta kuma duba dukiya ko launin fata, ba ta kallon ilimin mutum ko kuma nasabarsa, ita ba zaɓan chanchanta take yi ba, ba kuma ba tasan ya kamata ba, in da ace Soyayya ta san ya kamata da tun farko yin soyayya da FATIMA SULAIMAN DABO bai kamace sa ba*._ _*A iya hange hangensa bai taɓa hango bingiren rayuwarsa ba tare da Mimi ba, sai ga shi rayuwar ta lula shi wata duniyar da babu Mimi a cikinta ta ɓace daga cikinta, shi ya saba mafarkan ga shi ga Mimi tare da kyakyawan ya'yansu da irin yadda suka gina kyakyawan rayuwarsu, ashe ashe matacaccen mafarki ne ba zai taɓa tabbata ba.Hannunsa da ya kasa CIZAWA shi ya kai sa ga duniyar da ya zama sai shi kaɗai babu MIMI a cikin ta. Ta yi nesa da duniyarsa domin tarin bambamci tare da tazara mai kimanin kilo tamanin da Ahalinta suka hango tsakaninsa da ita wanda shi nashi hangen ya kasa hango masa, saboda tarin soyayya da ta rufe masa jin sa da ganinsa a lokaci ɗaya.*._ Kirjinsa ya fara tasawa yana faman sama da ƙasa, yaji kamar iskar ɗakin ya fara yi masa kaɗan sai kawai ya buɗe kofa ya fita zuwa falo ya goya hannayensa a bayansa ya fara tafiya yana zagayen falon gaf gaf! ana jin karan takun sa da karfi kamar wani namijin zaki. Zuciyarsa ke zafi tana wani turiri daga ciki iskar bakinsa yake fitarwa ya na jin zafin har a saman fuskarsa. Ba zai taɓa mantawa da tun a lokacin baya Nasir ya taɓa so ya ankarar da shi bai saurareshi ba, ba laifin shi ba ne soyayya ce ta rufe masa ido da ya kasa hango wannan bambamcin dake tsakaninsa da Mimi sai daga baya. _Aji tsakani ga Allah yarinyar nan ta fi ƙarfin ka, naga kana sonta da yawa kar nan gaba iyayenta su hana ka auranta_ A lokacin dambe ne kaɗai ne ba su yi da Nasir ba sai da su Makama suka shiga tsakanin su, Shi a lokacin yana ganin ga Hajiya ta ba shi dama har cikin falon gidan yana shiga su yi hiran su da Mimi, ya manta ita kakarta ce sannan ya manta sanadin haɗuwarsa da Mimi sanadin aikatau ɗin da Inna Meri ke yi a gidan Hajiya ne. "Ni? Kamar ni major Kabir My daughter ta auri yalaka agolan da ubansu har ya mutu a can wani ƙauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran ƙasakancin ba ta isa ba, ko za ta Mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyawam makoma ko anan gaba_ Sai da ya saka hannunsa guda ɗaya ya daki bangon falon, yana ji kamar a lokacin ake gaya masa kalaman ta ya ya ake so ya manta da wannan cin mutumcin? a kira sunan mahaifin shi a kabari aci zarafinsa sannan aka kira mahaifiyarsa da yar aiki aka zage ta sannan shima a ka kirasa da mara kyakyawan makoma shi ko zuciyarsa ba ta yi masa adalci ba da har take tunawa da wannan yarinyar da aka gama kare ma zuru'ar sa tanadi a kanta. Shi ba dukan da aka yi masa ke damunsa ba, ya fi jin zafin irin kalaman da Mahaifin Mimi ya jefe shi da shi.wai shi ne mara kyakyawan makoma? Shi ne saboda shi Inna Meri ta duka ita da Baba Ɗanjuma suna kuka suna roƙon a yi masa afuwa a sake shi. _Ku ja ma ɗan ku kunne, naga alaman Tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ƴata domin ruwa ba sa'an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na ɗaure shi da kakin jikina.._ _Abi ka yi hakuri. Abi ina son shi don Allah kada ka rabamu da juna.._ _Sai dai ki mutu, amman ba za ki aure wannan talakan yaron ba, ba shi da makoma mai kyau, na tambayi Hajiya kwalin karatun shi tana gayamin iyakarsa Secondary school. Kuma shima soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya._ _Abi ina son shi._ _Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba_ _Abi Ina son shiiiii...!_ _Murja ki ɗauke min Mimi kar raina ya ɓaci na fasa kanta da bindigata._ Ba zai manta da wannan kukan da ta riƙa yi lokacin da mahaifiyarta ke riketa ba, har gobe yana jin sautin wannan kukan acikin ƙirjinsa. Ya tuna ta na miko hannunta mahaifiyarta da yayarta suka rike ta suka tafi da ita zuwa cikin wani ɗaki Kafafunsa sun kasa ɗaukansa dole ya koma ya zauna Jagab a tssakiyar Falon yana sauke numfashi sama sama. Hawaye ya cika kwarmin Idanuwansa, Dakyar kuma siririn hawayen ya gangaro ta wajen idanuwansa hawayen so ne, Hawayen son abin da ka haramta ma kanka har Abada. Zafi ya ji jikinsa duka ya ɗauka kuma yana zufa har ta saman goshinsa. Shi ya sa ya miƙe yana jan kafa ya koma cikin ɗakin cikin Tiolet ya ƙara komawa ya kara yin wanka. Yana fitowa nepa suka kawo wuta sai ya kure fanka sannan ya kara kunna ta kasa dai dai saitin Mu'azzam ganin kamar yana jin zafi. Gyara masa kwanciya ya yi yana tuna baya yadda ya ke kula da rayuwar ƙaninsa kafa kafa kamar ba shi da wani kani a duniya sai shi. A fili ya furta" Bani da kamar Mu'azzam bani ni kuma da wami ƙani kamar sa." Shima gefensa ya koma ya kwanta bayan ya kashe hasken ɗakin Ya kuma ɗauki wayar Mu'azzam ya saka masa chaji da chager ɗinsa. Shi kuma wayarsa sai ya sauketa a kasan cafet din da ke cikin ɗakin. Ya daɗe bai yi barci har biyu na dare barci ma barawo ne ya sace shi. Da asuba da suka dawo daga masallaci Mansoor ya shirya ya tafi camp yace za su haɗu a gida in ya dawo. Mu'azzam sai da ya yi barci ya koshi sannan ya tashi ya yi wanka ya sauya kaya ya ɗauki motarsa ya bar gidan bayan ya kulle gidan tunda ya ga key din gidan anan cikin bedroom din. A wajen Inna Meri ya je ya karya da waina da Miya Inna Meri da kokari da Safen nan ta toya ta miyar kuma Walida ta yi shi kafin ta ta fi makaranta Mansoor bai zo gidan ba sai da rana sai kuma a lokacin shima ya karya da waina da miya, daga nan Mu'azzam ya je tudun wada ya ga kwanan Hibba daga nan ya taho ma da Mansoor Junior. Tunda kuma ya ɗauke shi suka fita a mashin sai yamma ya dawo da shi akwai wani team ne da suka gayyace shi kallon wasan su, Bacerlona sunan Team ɗin anguwan Jekadafari ne, can ya je kallon buga wasan su tsakaninsu da Mesi team na anguwan Tudun wada. A hanya ya ga ana saida kayan wasan yara ya siyan masa jaka guda ya kawo sa wajen Inna Meri, yana ma gidan Mu'azzam ya kira shi ya ce suna tare da Nasir ya ce yana gida su zo su same shi. Sai ga Nasir har ɗakin Inna Meri, daman ai sun saba zuwa lokaci bayan Lokaci ko ba su Mu'azzan suna zuwa gaida Inna Meri. Nasir ya mika ma Mansoor hannu suka tafa lokaci ɗaya yana faɗin "Aji aji manyan gari." Mansoor ya ce"Nasir kana nan a gari abin ka" Nasir ya ce"Karyan tsiya kake yi baka neman mutane, ya wasa? Aji ka kusa haurawa waje fa duk garin nan hiran irin taka ledan ka ake yi, ranar muna gaddama da wani a wajen aikinmu na ce ai Aji tun a Nasara Team kowa yasan guru ne a taka leda na gaya masa lamba goma kake bugawa ya ko san duk wanda ke buga lamba goma ya kware a sanin ƙwallo." Mirmishi ya yi bai yi mgana ba, sai Mu'azzam da Nasir suka koma hiran ƙwallo Jefi jefi Mansoor na tsoma musu baki. Daman Mu'azzam mafarkinsa ne kwallo, Shi ma Nasir haka in suka haɗe hiran su kenan ƙwallo. Sun fi awa a ɗakin Inna Meri sannan suka fito kofar gida sun jima suna hira kafin su yi sallama akan sai sun haɗu da sallah. Nasir ya tafi ya na yi ma Mansoor tsiyan da azumin nan sai yasa yara sun kiɗaa masa gwuro. Mu'azzam na ta dariya shi kan shi Mansoor din sai da ya yi mirmishi. Daga Mansoor har Mu'azzam nan suka yi mangariba da isha'i bayan Mu'azzam ya maida Junior wajen maman shi tare kuma da Baba Ɗanjuma suka ci tuwon masaran Inna da miyar kubewa. Bayan sun gama kuma suka zauma suna ta hira, yau Inna ce ke da turaka shi ya sa suka samu zama da Baba Danjuma sosai. Sai wajen goma suka baro gidan suka koma gidan Mansoor suka kwana washegari Mu'azzam da iyalansa suka koma kano. Duka duka sun tafi da kwana goma aka fara azumin Ramadana. Kamar yadda suka saba haɗaa hannu shi da Mu'azzam duk azumi su siya komai buhu a raba nan cikin gida da kuma makota. Sannan kowannen su ya aika da kuɗi danginsa, Shi Mansoor ya tura sakon kudi a can kwami shi kuma Mu'azzam nan Anguwan bolari inda aka haifi mahaifiyarsa. Inna Meri ba ta yi sakacin da suka manta dangin su ba, sannan kaf ƴan'uwansu mata sun samu siga da gero na kayan azumi. Bintu kuma 50k Mu'azzam ya tura mata Mansoor kuma ya siya mata firiza da ta ce ta na so zata fara saida Zobo da ruwan sanyi da azumi. Sannan ya ba ta jarin kayan zobon ranar Bintu ta tiki rawa abokiyar zamanta ta sha habaici da Bashir ya yi magana ta ce ya kyaleta itama in taji haushi yayyenta su siya mata. ****** Hajiya da Mimi a na saura kwana huɗu a fara azumi suka ɗaga umra, Hajiya ce daman duk Azumi can ta ke yin azumin ta wannan karon kuma ta matsa tare da Mimi za ta tafi sai Daddy ya niya musu suka tafi tare aka bar ma Baaba Uwani amanar gida. Hajiya ta je ƙara yi ma ɗanta Kabiru addu'a tare da Binta ita kuma Mimi ta je yin ma Abin addu'an Allah ya bashi lafiya duk da ta taɓa zuwa Umra sau biyu. Hajji kuma sau ɗaya ta taɓa zuwa lokacin da ta gama bautar kasarta ne kafin ta koma kano ta yi master ɗinta. Tunda suka je ibada kawai suke yi, kuma daman ba ta da matsala da wajen aikinta tunda Umra ce, ba ma ita kaɗai ta je ba har news manaja din su yaje shi da iyalansa sun haɗu da shi acan, sannan har Madiha sun gani ta je ita da mijinta da ƴaƴanta amman su ba acan suka yi sallah ba. Tun suna Umra Rukky ke damun Mimi a chart da mganar bikin Bibi sai da Mimi ta yi mata alkwarin in da ta dawo ba zata ja baya ba da ita za'a yi komai a gama in sha Allahu. Acan kuma ta siya ma Bibi zanin gado mai kyau na guddumwa. Ranar salla ta yi Hoto ta ɗora shi a status ɗin ta mutane suna ta cewa yaushe za ta dawo? Gidan karamchi Talabijin na kewarta. Daman tunda suka tafi ba ta cika amfani da waya ba sai jefi jefi ta dukufa addu'an Allah ya cire mata Soyayyar Mansoor acikin ranta ko zata samu sauki acikin ranta, ba ta san cewa Na Misau ya dauki hoton ta ya je shafinsu na Faceebook ya ɗorata tare da cewa. " Fatima kabir sulaiman dabo(Mimin karamchi) na yi muku barka da sallah daganan Birnin Madinatul munnahwara." Ita ba ta man san ya saka ba sai da daddare da zata kwanta ta buɗe data ta gani ta sha comment har wani na faɗin" Hajiya Mimi Madina ta karɓeki har kin kara jan kumatu." Sai da kalamansa ya sa ta yi dariya har ta yi masa reply da cewa" Zama waje ɗaya ne, kafin na dawo manaja ya rika sani fitar dafiya." Shike nan sai aka fara cecekuce ana ta hira ta jima online ta na yi ma masoyanta reply ita kanta ai ta yi nishadi sai da Mommy ta kirata Vedio call sannan ta koma suna waya da ita tare da Abi da duk ya kara ramewa ya tsufa saboda ciwo. Hajiya har ta fara barci ta tashe ta suka yi mgana da Mommy da Abi. Su ma suna ta shirin dawowa gida nan da sati mai zuwa. **** Mu'azzam da matarsa da ɗansu duk anan suka yi salla sati ɗaya suka yi suka koma kafin komawarsu sun haɗu kan bikin Makama amman babu Mansoor ba ya nan sun tafi Bauchi buga wasa su kansu ba su damu da shi ba sanin ba zai shiga wannan hurumin ba, ta bakinsa ku riƙa yin abu na masu Aji mana. Tun ana washegarin sallah ya tura ma makama 150k guddumuwa kuma ko da ya kira shi a waya ya yi masa godiya bai ɗauka ba. A chart kuma ya yi masa mgana bai buɗe sakonsa ba, ya yi ma mu'azzam korafi ya ce kada ya damu ba ya son ya yi masa godiyar ne shi ya sa bai ɗauki kiransa ba. Sun tattauna yadda za su shirya dinner da sauran bukatun amarya Nasir suka bar ma komai a hannunsa tunda shi ke zaune a gari. Kuma shi ake ba ma jagoran zama da amarya domin ya ji tsarinta. Bikin zai kama 28 Ga watan April, tunda an ƙara sati ɗaya. Nasir ya je gidan su Bibi sun haɗu da Rukky tunda kamar ita ce ja gaba kan komai sun yi mgana, Nasir irin mutanen nan masu maagana kai tsaye ba su tauna ta Sai da ya yi ma makama mganar yayar matarsa ce za ta ci ma kanwarta ƙawa ne? Makama yace to in ma hakane ina ruwansa. Nasir yace"Shi fa na gani babu ruwana ai da din kallo ne da shi." Bayan guddumuwar da suka ba ma Ango sun ba ma Amarya kuɗin gyaran jiki da na abinci ɗinkunan kuma da aka sanya a acikin akwati Ahmad ya ɗinko su duka ya aiko da su da yazo sallah daman ya ce Makaman ya bashi zai ɗinka ma amarya kayan fitan biki. Kala goma ya ɗinka mata kaya masu kyau da yarari ga su sun haɗu da tela ƙwararre sai kayan suka fita sosai. Ana saura kwana goma biki aka kawo kayan aure akwati bakwai da ghana Must go. Mimi da Rukky daga wajen aiki suka zo tare ta ga kayan sai dare ma ta koma gida. A yadda Rukky ke ba ma Mimi labarin abokan angon da Angon kanshi sun yi kokari sosai ba su yi ƙwaron hannu ba. Dinner daman su suka ce a bar komai a hannunsu za su shirya daga bangarensu. Saboda Rukky Mimi ta shiga bikin kuma Bibin ma ta ce"Don Allah Anty Mimi kune yan gayu ki tsara min bikina." Har sai da tayi dariya, da ta kawo mata zanin gadon da ta siya mata da ta je Umra har Babansu Rukky sai da ya yi mata godiya. Hajiya ma ta ba da 20k ta kaima Mamansu Rukkaya. Duk Lokacin da Angon da abokonsa za su so Mimi ba ta nan ko suna wajen aiki kuma da daddare sukan zo lokacin ta koma gida. Ana saura sati ɗaya biki suna mota ita da Rukkya daga wajen aiki za su shiga kasuwa Rukky tana ta mita da tsaki. Mimi ta ce"Wai me aka yi miki ne? Kin ishe ni da mita" Rukky ta ce"Ni da abokin Usman ne da suke zuwa tare ba shi da mutumci shekaran jiya kallo na fa ya yi yana cewa wai Amaryan nan ba ta da ƙawaye ne sai ke? Mimi ta fasjhe da dariya kafin ta ce" Gaskiya ya faɗa kina Yaya kin zama ƙawar ƙanwarki." Rukky ta ce"To ina Bibi ta ga wasu kawaye Allah na tuba, ai na yi ta jaraba Usman ya bani hakuri da cewa haka yake nace to ya saita bakinsa." Mimi ta kara saka dariya kafin ta ce" Baby Rukkaya." Rukky ta yi dariya kafin tace"Zai ga ƙawaye in ana gobe biki da ranar biki amman yanzu duk mu za mu shirya komai." Mimi dai faman dariya take yi sanin halin Rukky ita so ta ke yi a biki na nuna sa'a shi ya sa take so su shiga su shirya komai da kansu. Sun jima a kasuwa saboda sauran siyayyan kayan kitchen sai Atamfar yinin biki da suka siya tunda Mimi na dinner kaɗai ta turama Rukky kudin ta siya mata less ta ba da ɗinki a waje ɗaya tare da nata. Na yinin bikin kuma Atamfa ce gold itama Rukky ta ce ɗinki iri ɗaya za su yi saboda haka waje ɗaya za ta kai musu ɗinki. Mimi ta bar mata, tunda Rukky dai ta dage sai sun zama ƙawayen Bibi. Satin bikin kaf ba su zauna ba tunda tana da mota mai kawai take sha suna shiga gari. Ko a wajen aiki ma bini bini Rukky ta ja ta sun fita Har Na misau sai da ya yi magana yace" Ke dai Rukky kina da son kuɗi, ki rage ciki ki siya mota ki daina lafe masu mota ana miki ɗani. Rukky ta rika hararan shi Mimi na yi musu dariya. Sai dai shima yana zolayanta ne, tunda ai su san ƙawaye ne, kuma ga bikin Kanwar Rukkaya da kowa a an bashi katin gayyata. Zirga zirga ya yi musu yawa ba ta komawa gida sai dare har Hajiya sai da ta ce Rukkaya yar gaban goshin Mimi ce da har take iya janta suna faman zirga zirga. Itama Mimin ta gaida matsayin Rukkaya a zuciyarta ita da ba ta yarda ta je ko'ina daga wajen aiki sai gida fita nan da Rukkaya ta matsa mata suke yi duk jikinta ciwo yake yi. Ana saura kwana uku biki suka je kunshi aka yi ma Mimi lallin Sticker a kafanta ja ya yi maroon a hannun ma an yi mata jan sai aka sirka mata da bakin zane. Ya yi kyau sosai abun ka ga farar fata a can gidan kunshi ma ana ta santin kunshin saboda Mimi ta manta rabonta da kunshi tun bikin Auran yayarta Khadija in za ta iya tunawa. Ita kanta haka ta riƙa kallon kunshin tana jin daɗi ana gobe jibi kuma gyaran kai suka je sun yi kuma yamma saboda sai da suka je kasuwa ita da Rukkaya sannan suka tsaya shagon Salloon suka yi gyaran kai Amarya Bibi tana tare da wasu kawayenta guda biyu yan makarantar su sai wata ƴar'uwansu da suka zo daga Bauchi. Tunda su Rukkaya mamansu ce yar Gombe Babansu kuma ɗan Bauchi ne. Ranar kuma ita ke da karanta labaran duniya na yamman dole daga Saloon Rukkaya ta wuce gida, ita kuma sai ta koma gida ta shirya ta wuce wajen aiki, ga shi ta zuba kunshinta ga gyaran kai goshi nan ya yi raɗau haka ta rika karanto labarai cikin zaƙin muryanta. Ranar ta sha magana su kansu ma'aikantan kowa ya ganta sai ya ce ta yi kyau. A lokacin da ta gama karanta labaran cikin harshen hausa sai ta koma na harshen turanci, a dai dai lokacin Mansoor ya shiga bangaren Inna Meri ba a anguwan ya yi sallar mangariba ba daga Studio yake ya tsaya ya yi sallar acan sai kawai yana shigowa anguwan ya shigo gidan kai tsaye. Ya ɗaga labulen ɗakin Inna Meri kenan lokaci ɗaya yana faɗin" Innar m..." Sauran kalamansa sun maƙale a fatar bakinsa lokacin da ya yi arba da ita. Ba shiga ta yi mara kyau ko wanda ya saɓa mata addini ba, tunda doguwar riga ta saka mai ruwan kasa mai faɗii ba ta ma kama jikinta ba. Sai dai ras kunshinta ya fito tunda hannayen ta suna waje ne. Kamar ya ga mutuwarsa haka ya ji, gabansa ya faɗi ras!.Haka ya ji kirjinsa na wani irin Dif! Dif! Kamar ya na da ciwon asma. Inna Meri na ɗakii ta jin muryansa dai dai ta fito tana faɗin "Murya wa nake ji kamar ta Baban Inna" Sai dai ta hangi bayansa ya na sakin L labulen ɗakinta ya wuce. Walida ke tsakiyar falon tana sallah inna Meri ta leka daga wajen kofar ɗakin sai ta ga da gasken dai ya fita. Sai ta dawo dai dai lokacin da Walida ta sallame salla. Inna Meri ta kalleta tana faɗin"Ba Baban Inna ba ne ya shigo yanzu? Walida ta ce"Shi ne yana ɗaga labule kuma na ga ya juya da sauri ya fita." Inna Meri na gyaran hijabin jikinta rike da casbaha ta koma cikin ɗakinta tana faɗin" Walida ki rage karan talabijin ɗin nan, a haka kika yi salla da shi ƙara ya yi yawa." Walida ta juya ta na kallon Mimi tana karanto labarai cikin turancinta mai kyau kamar ba'amurkiya. Sai ta fara tunanin ko ita Baban Inna ya gani ya juya. Zai iya zama gaskiya saboda akwai wata rana da ya taɓa zuwa yaga sun kamo tashar kuma ita ce ke karanta labarai da safe. Da kanshi ya saka hannu ya tuge soket ɗin talabijin ɗin har ya yi ma Walidan tsawa da cewa su daina barin Tv a kunne in babu kowa a falon. Ajiyar zuciya ta sauke duk da bata santa ba koma me ya faru ta na ƙarama ya faru. Amman ta ga dacewar Yayansu da wannan yar gayu. Kuma Inna ta ce gidansu na can cikin Gra, inna ta gaya mata ta yi zaman yi ma kakar mai kyau da iya turancin aiki wacce ake kira da Mimi mimin karamchi. Shiko iskar bangaren Inna Meri ne ya fara yi masa kaɗan saboda yadda yake jin zuciyar na zafi, ko tunanin tsayawa bai yi ba ya hau mashi dinsa ya bar anguwan. Yana tafe iska na kaɗashi amman kuma acikin zuciyarsa babu wannan iskar sai wani irin tukikin zafi da yake ji. Kishi ya ke ji a kasan ranshi, me ya sa ta yi kunshi ta bayyana adon ta a duniya? Maza nawa suka kalleta? Sannan maza nawa suka yaba da wannan kunshin da

Chapter 10 of 26