Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ja kafin ta ce"Ai sai ya zama muna nan muna jira." Mu'azzam yayi dariya yana kallon Mansoor da hankalinsa ke kan karamar wayarsa ya na ɗan mirmishi Inna Meri ya kallah kafin ya ce"Hajiya na gaishe ki da gajiyar biki, yanzu daga can mu ke." Ya lalubo aljihunsa ya ɗauko Sweet da yawa  yana mika ma Bintu da har ta zuro kai yana faɗin"Anty Mami ta ce na kawo ma su Bintu."   Da gudu Bintu ta warce ta na ihun Murna Mansoor ya kalleta a karkace kafin ya ce"Ke ashe wawiya ce bansani ba? tana jin haka ta yi gum da bakinta ta na raba ido. Walida ta mika hannu ta na faɗin"ki ba ni Nawa " Bintu ta make kafaɗa kafin ta yi mgana Mu'azzam ya ce"Sai kin bata ko wlh ke ma ya haramta gare ki, yarinyar nan son kai gareta."  Hararansa ta yi kafin ta tura baki shi kuma sai ya mika hannu zai kwace da yasa ta kwashi uku ta mika ma Walida sauran kuma ta tura cikin sikat ɗinta ta mike da gudu zuwa cikin ɗaki. Mu'azzam ya girgiza kai kafin ya ce"Inna Allah yasa Bintu ta jiƙan ki wata rana." Inna na yar dariya ba ta ce komai ba illah kai da ta daga sama tana kallon taurari kafin ta dawo da kallonta kan Mu'azzam ta na fadin"Hajiyar tana lafiya ko? Allah Sarki Hajiya gobe zan shiryar takanas ba domin aiki ba na je na yi mata godiya." Mu'azzam ya ce" Ya kamata Inna Hajiya tana da kirki, duk abun Yayanmu sai da ya yabi kirkin Hajiya." Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba ita fa akwai wani abin da ke ba ta tsoro shakuwar bintar Hajiya da Baban Inna soyayya suke yi, tun tana ganin abun yarinta ne har dai yanzu ta yardan ma kanta da gaske ne. Ban da Baban Inna da rigima ina shi ina ƴar masu kudi, ai wannan jawo ma kai fitina da jidali ne.   Yarinyar nan kunyar surukan take yi mata in dai taje gidan ba ta iya haɗa do da ita, ita kuma Hajiya ba ta damu ba domin ta ce abunda Binta ke so shi ta ke so. Ba za ta taɓa  mantawa da sun taɓa  maganar da Hajiya saboda Hajiyar da kanta take ce mata yara nan fa da gaske suke son juna su ke yi.  A lokacin Dariya Inna Meri ta yi kafin ta ce"Haba Hajiya yarinta ne da shirme irin na Baban Inna sai kuma shakuwa amman ai ruwa ba sa'an kwando ba ne, kuma ina shi ina aure yanzu? Duka duka nawa yake? A lokacin sai Hajiya ta ce"To ai ko ba yanzu ba Meri sai iyaye su shiga mganar, kamar yadda ya ke son zama Sojan nan ya je can ya na karatunsa itama tana nan ta na yi sanda ya gama ya dawo itama ta gama sai su yi auransu ai ba wani abu, ni fa ba na ƙyamar zuru'arki Meri ke macece mai kirki da mutumci ya'yanki masu tarbiya ne, kuma maganar ruwa ba'a san kwando ba ne bai taso ba abin da Binta ke so shi nake so, matukar kuma ta ce Mansoor ta ke so ni kuma zan shige gaba wajen na ga ta samu abin da take so."   Tunda lokacin Maganar sai ta fara damunta ta turke Mu'azzam kuma ya tabbatar mata da gaske Baban Inna na son Mimi irin soyayyar da ba zai iya kwantatawa ba, in ba ta manta ba yana da kuma ra'ayin aure tunda ya na da ƙananun shekaru, ita abu daya ke damunta da shi nacin tsiya da kafiya sannan ga ɗauko fitinar da ta fi karfinsa in ba neman jawo zaune tsaye ba ina shi ina Binta yarinyar da Ubanta ma akan dole ya bar ta hannun mahaifiyarsa ita fa tana hango ma Baban Inna nadama kan wannan shegen kafiyar nashi.  Kan nacin sa da zama Sojan nan har Mallam Sidi ta shirya ta je bikin yaron yalwa da shi ma taso tafiya ya ce shi ba zai je ba, ta ma ta zencen Babansa yakubu ya kira shi ya je can Bauchi ya same shi ya yi masa faɗa ƙo  ya ji Yalwa ta ce to in Yakubun yazo ko in sun yi waya tunda yanzu ya yi ƙarfi kasuwanci yake a Bauchi yana can shi da iyalansa.  To kila dai ba ta samu magana da shi ba ne, bai aiko ba kuma sannan ba ta kara ji daga Yalwa ba, ta so shi Yakubun ya kira shi ya matsa masa kila ya watsar da wannan ra'ayin na sa na zama Soja ya nemi wata hanyar. "Inna me kika dafa ne?   Mu'azzam ya katse mata tunani sai ta yunkura ta mike tana faɗin "Tuwo ne miyar yauki bari na zubo muku." Ta zubo musu kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya shigo gabaɗayan su suka yi masa sannu da zuwa ya amsa ya na ƙokarin sakin fuskarsa. Cikin ƴaƴan na shi ya zauna suka ci cin tuwon Mansoor ne ya fara ƙoshi ya tashi Baba Danjuma ya kallesa yana faɗin"Ka ƙosh ne Baban Inna? Yana nufar randar Inna ya ce"E Baba.!" ruwa ya diɓa a buta ya shiga makewayi ya kama ruwa sannan ya wanke hannunsa ya kuskure bakinsa.  Bayan ya fito sai ya zo ya durkusa gaban Baba Ɗanjuma kansa na kasa, Inna Meri na gefe tana kallonsa kafin ta yi mgana Baba Danjuma ya ce"Ya aka yi ne Baban Inna? da wata matsala ne." "Baba Aure nake so na yi.."   Gabaɗayan su suka kalleshi a tare Mu'azzam sai da ya ƙware da tuwo duk da ya san hakan zai iya faruwa amman bai tsammanci maganar da wuri ba, inna Meri ta yi tagumi kawai tana kallon Baban Inna yaro ƙarami na neman saka kanshi a wahala shekararsa fa duka duka ashirin da uku ne tsawon kafa ke jansa yake ganin ya isa ya yi aure har ya riƙe mata yana zaune ba shi da sana'a naira biyar ma na bashi sha'awa. Baba Ɗanjuma sai ya dakata da cin tuwo ya miƙe yana faɗin"Babban mgana, taho ka zuba min ruwa na wanke hannuna sai mu yi maganar sosai" Haka ko akayi ya zuba masa ruwa a bakin magudanar ruwa ya wanke hannunsa sannan ya koma ya zauna yana kallon Mansoor mirmishi ya suɓuce masa ai shima ya taɓa gaya masa haka tun bai kai haka shekaru ba. "Baba ni fa ba zan bari sai na fara tsufa zan yi aure ba, da wuri zan yi aure saboda ba na so ya'yana su taso su ganni ƙarfina ya ƙare."   Ko a lokacin da ya ce masa haka sai da ya yi dariya kuma yana da yaƙinin Baban Inna zai maimaita mganarsa lokaci kaɗan tunda shi baya faɗin abin da ba shi ne acikin ransa ba, Inna Meri ya kallah kafin ya ce"To ke fa Meri kin ji, za ma ai bai gan ki ba Baban Inna Aure yake so yayi" Inna Meri ta ja katon tsaki Mtsewwww kafin ta ce"Ai sai ya yi auran tunda auran faɗe ne a fatar baki, ban da shegen rigima kana yaron ka da kai ba ka ba wani ajiya ba, kai  ba ka ijiye mai ba ka ba sai kawai rana tsaka ka ce wai aure za ka yi? Anya Baban Inna..!" Ta faɗa tana nuna shi da yatsa kai tsaye ya ɗago yana kallonta kafin ya ce"Inna ina da gado na, a saida gonakin baba na Mallam Sidi ayi min aure da shi." Ai sai Inna Meri ta hau tafa hannu tana faɗin" Yai naji sheganta ka, zan ɓace ka Mansoor yanzu nan wlh." Baba Ɗanjuma da ya ga ranta ya ɓaci yayi saurin tare ta da faɗin" Kar ki yi masa faɗa ai ba laifi ya yi ba, kuma bai yi ƙanƙanta ba, waɗanda ba su kai shi ba ma su na yin aure  yanzu dai mu saurare shi mu fara sanin in da ya samu matar" Inna Meri gabanta na faɗuwa ba ta son ta ji ya kira sunan da zai ba ta tsoro. "Mimi ce, jikar Hajiya in da Inna ke zuwa aiki."   Inna Meri ta ɗora hannu a saman kanta lokaci ɗaya tana faɗin"Na shiga uku ni Merama, da gaske daman son yarinyar nan kake yi baban Inna? Me ya sa ka cika fitina ne? Ina kai ina wannan yarinyar? Kai tsaye ya ce"Inna tana sona itama, kuma Hajiya ai ta sani kuma ta amince da hakan."   Inna Meri ta aika masa da dakuwa lokaci ɗaya tana faɗin"Ka ga naka nan, In Hajiya ta sani Hajiya ce ta haifeta, babanta Soja ne kuma ko Hajiyar ba ya jin maaganarta wlh ba zai aura maka ƴarsa kana zaune ba ka da wani tunani ba, ko a addini mai sana'a aka ce ba mai burin banza ba, ka fita idona da wannan mganar na ma gaya maka." Daga haka ta tashi ta shige ɗaki tana ta faɗa, shi kuma Mansoor yana gayama Baba Ɗanjuma ai ya na neman karatun Soja in ya samu zai iya rike Mimi, Baba Ɗanjuma ya samu ya lallaɓashi yace za su yi mgana da Safe.   A can ɗakin su ma Mansoor Mimi ya kira a waya yana faɗa mata ya faɗa ma su Inna zai aueta, tunda itama yanzu tana da waya da ta saka Hajiya ta sa Daddy ya siya mata mai kyau da ita yar yayi. Mu'azzam bai isa ya ce ma yayansa wani abu ba, amman shi kanshi ya na hango ma kansa ya yi gaggawa sannan Soyayya ta rufe mishi ido ya kasa gano abunda Inna ke hango masa.  A daran shima Baba Ɗanjuma yayi ta fama da Inna Mari ta sauka daga fushinta su yi mgana ta ce in ta sauka sai Baban Inna ya bar maganar Jikar nan ta Hajiya, shi ko Baban Inna ya yi nisa da ba ya jin kira yadda yake jin Mimi a zuciyarsa in ya rasa ta sai ya iya mutuwa. Kuma shi ya gayama Mimi da kansa cewa Inna Meri ta ce ta fi ƙarfin shi. Kuma su sun tsara rayuwarsu da cewa zai tafi makaranta Sojoji kafin nan za'a ɗaura musu aure sai ya barta wajen Inna ta cigaba da kararunta.    Mmi kuka reras ta riƙa yi ma Hajiya akan abin da Inna Meri ta ce, Hajiya ta ce za ta aika a kira mata Merin ta ji me ya sa ba ta son jikarta ta zama surukan ta? Ba ta ma kai ga aikawa ba sai ga Inna Merin ta zo ma Hajiya Godiya domin 100k ta ba ta da bikin nan bayan ƙananun alherinta a gareta sannan ta bata hutu ta ce har sai gajiyan Biki ya sake ta sannan ta dawo. Tana zuwa da niyar yi ma Hajiya godiya sai tace su shiga cikin ɗakinta ta na son mgana da ita. Tana jin haka tasan kwanan zencen, illai ko Hajiya ta tsareta akan me ya sa ba ta son alaqar Mansoor da Binta?   Inna Meri sai ta saka kuka cikin kukan take faɗin"Haba Hajiya ban da neman rigima ina Baban Inna Ina Bintar ki? Hajiya tace"To Ubangiji ya haɗa sai mu ce a'a tunda suna son junan su sai kuma mu hana su kudirin alheri." Inna Meri ta ce"Hajiya Baban inna yaro ne yarinta ne ke damunsa shekaransa ashirin da uku ne da wattani, da me zai riƙe Binta? Sojan da yake ta ƙulafuci har yanzu bai samu ba kuma ya ki sauya ra'ayinsa don Allah Hajiya a bar mganar nan shakuwa ce kawai ba wai soyayya ba."   Hajiya ta ce"Duk na fahimci tunaninki, kina da gaskiya abin da za'ayi ai shima kabirun Soja ne zan kira shi mu yi mgana sai a zauna ko shi sai ya ne ma Mansoor ɗin makarantar Sojjojin a yi alkwari in Mimi ta gama karatu su yi auren su ba shike nan ba." Inna Meri dai ta kasa mgana amman tana hango wani abu da ba zai tafi dai dai ba amman gudun kar Hajiya ta ga kamar tana gudun maganar sai ta amince da hakan, Kuma Hajiya da kanta ta kira Mansoor ta zaunar da shi ga shi ga Binta ta ce ya faɗa mata gaskiya yana son Binta?   Kai tsaye yake kallon Hajiya kafin ya ce" ba sonta nake yi ba, kaunarta nake yi Hajiya." Itama Hajiya ta tambayeta lokacin Mimi an zama yan mata shekaranta sha tara, ta rufe fuska ta ɓoye bayan Hajiya tama yar dariya. Hajiya ta ce kar su damu za ta yi mgana da baban Binta.  A lokacin ita Mimi soyayya ta makantar da ita kamar yadda ya makantar da Mansoor dukkansu suka kasa gano abunda mutane ke hango musu. Hajiya kuma ta manta waye Kabiru ta ɗauka haihuwarsa da ta yi ya isa ya sa ya bi abin da take so.   Major Kabiru bai san halin da ake ciki ba, Brr Murjanatu kaɗai ta sani tunda ita macece kuma yaran sun fi sabawa da ita shi kullum fuska ba fara'a tsoro tsoron sa ma suke ji, kuma Mimi in ta zo hutu daga baya nan tana yawan kamata suna waya da wannan yaron da ta ce Mimi ta bar maganan sa, ta yi ma Hajiya ƙorafi Hajiya ta ce ta kyaleta tunda har Binta na son wannan yaron to sai a zauna a ga abunda Ubangiji ya tsara, ita ba wai talauci ko yanayin rayuwa ba ɗaaya ba, abu daya take dubawa sun yi yarinta da yawa da maganar aure, sannan ta san waye mahaifin Mimi ba shi da tsarin aurar da ita yanzu to ko Madiha karatu take yi bai saka maganar auranta ba, ballantana Mimi da ta ke just 19 tabbas ta san akwai kura. Ita Hajiya ta fara kira akan maganar Saboda suna da kyakyawan alaqa na mutuntawa a matsayinta na surukarta, Mommy ta ji tsoron da Hajiya ta ce ta fara tuntuɓar Major da mganar cikin firgici ta ce"Hajiya wlh ba zan iya ba, kina ganin ko madiha wani yaron yayata na sonta da Major ya ji ba ki ji yadda yake ta masifa ba ya ce ba yanzu zai aurar da ita ba sai ta gama karatu ta fara aiki."  Hajiya ta yi tsaki kafin ta ce"To ai wannan tsarinsa ne ba tsarin Ubangiji ba, karatun ya fi auren daraja a wajensa ne? ya bar yara sun zama manya bai aurar da su ba da an yi magana sai ya ce ba yanzu ba shi Sulaimanu ai ya na can cikin jajayen fata har yanzu bai dawo kasar ba." Mommy ta ce" Hajiya karatun likitanci yake yi, sai nan da shekaru biyu zai dawo in sha Allahu." Hajiya tace"To dama dama shi tunda namiji ne amman matan ne ya le neman kashe musu rayuwa da tsatauran ra'ayinsa na banza, zan kirasa da kaina na yi masa mganar."    Ranar a tsure Mommy ta dawo daga wajen aiki, fargaban ta ɗaya ta san komai ya je ya dawo ita zai sauke ma bala'in zai ce tana sane da komai bata gaya masa ba sai da abu ya yi girma. A ranar da dadadde  bayan ya dawo daga office Khadija na ɗakinta tunda ita a nan Abujan ta ke karatu Madiha ce ke BUK kano ta na karatun ta acan, Mommy duk jikinta ba daɗi Sai fama take da faɗuwan gaba tana Allah Allah ta ji ya ce Hajiya ta kirashi sai ta ji har sun gama cin abinci bai ce haka ba sai ta samu yar salama.   Sai dai bayan sun koma falo suna hutawa yake ce mata Mimi zata dawo nan ta yi jarabawa so ya ke yi ta ta fi Jami'a mai kyau ta yi karatun likitanci akan abin da ya Shafi mata tunda Sulaiman ya na karantar fannin zuciya, Mommy ta kasa magana sai zufa ke yanko mata duk ko da sanyin Ac dake falon. Kallonta ya yi cikin mamaki kafin ya ce"Honey lafiya? Ko baki da lafiya ne? Da sauri ta ce"No am fine." Saboda ya ga duk ta firgice sai ya yi dariyan basawa kafin ya ce" ko case ɗin dake hanunki ne ya ba ki tsoro.? Dakyar ta yi yaƙe ta kasa mgana.   Ta fi kowa sanin waye Major ba shi da kyau ko ya yi wanka ko acikin Sojojin shi mugu ne sannan ba shi da uzuri ballantana ragowa ga ra'ayin riƙau ne da shi  ita fa yanzu haka ba ta isa ta yi ba dai dai ba sai ya ce da gangan ta yi da farko ba haka yake ba daga baya lamarinsa ya kara ta'azzara. Daman can halinsa ne sai kuma ya zo ya haɗe da kakin dake jikinsa sai takamarsa ta yi yawa. Daman shi fa ya tsani ace za'a haɗa ƴaƴansa da komai, yadda yake kaunar ƴaƴan to kila sai aikinsa ne za su iya gogawa. kuma ya ci burin akan su da sai ya gina su zai aurar da su ga wanda ya dace in ya ji wannan labarin na Mimi ai sai ya harbeta daga ita har Mimin.   "Kin ga ko na manta Ina Office Hajiya ta kirani ta na son yi mgana dani, na ce ma ta sai na koma gida, miƙo min wayata na kirata in har ma akan Mimi ne sai dai ta yi hakuri zan karɓi  ƴata  bazan iya kara barin ta a garin nan ba yanzu."   Can a sama Mommy ta ji Abi na mgana duk sai ta kara ruɗewa,  ba ta tashin ba sai da ya ƙara mata mgana sannan ta mike ta ɗauko masa wayar wajen rawan jikin  wayar ta faɗi ƙasa haka ta duka Jiki na rawa ta tattaro masa wayar ta mika masa  ya karɓa lokaci ɗaya yana faɗin" Murja are u ok? Sai ta gyaɗa mai kai, kasa tsayawa ta yi da sauri ta shige ɗaki ya bi ta da kallo, bai ɗauka wani abu ba sanin shi da ita akwai ta da saka dmuwar Case in dai ya na hannunta acikin ranta. Lambar Hajiya ya lalubo ya kirata, bayan ta ɗauka sun gaisa ya ce"Hajiya ban jima da dawowa ba, ina fatan lafiya? Hajiya ta gyara zama tana faɗin. " Lafiya ƙalau, daman akan maganar Binta ne? Kai tsaye ya ce" Eh daman ina shirin miki maganarta  nan zata dawo ta yi jarabawa so nake Bintar taki ta zama likitan mata Hajiya."   Ya faɗa cikin yar dariya Hajiya ta haɗa rai kamar yana ganinta kafin ta ce" Eh to za ta iya zama likita amman daga baya yanzu dai aure take so." Ya ɗauka wasa Hajiya take yi sai da ya yi dariya kafin ya ce"Haba Hajiya aure kuma? Mimi ai ba ta san me ake kira aure ba." Hajiya ta ce"Ai ba jaririya ba ce shekaranta sha tara  da gaske nake yi Akwai wani yaro ɗan wajen Meri dake min aikace aikace sun shaku da Binta kuma yana  sonta da gaske itama Bintar na son shi.." "Wait Hajiya kika ce yaron waye?   Ya katse Hajiya cikin mamaki shi fa gani ya ke yi kamar ta tsuniya Hajiya ke karanta masa Hajiya tace"Eh yaron Meri ne matar dake taya ni zama." Mamaki ya hana shi magana Hajiya na son gayamasa wai yaron ɗan wajen mai aikinta ne ke son Mimi, Shi haka ya yi sakacin da ƴarsa ta za ma a arha da wani yaron talakawa zai ganta ya ce ya na so. Ai bai gama mamaki ba sai da ya ji Hajiya na faɗa masa Mimi na son yaron kuma ta yarda ta aure shi kuma yaron iya sakandiri ya gama ya na son ya zama Soja to shi ya taimaka masa ya samu sojan daga baya komai menene sai ayi.   Huci kawai ya ke yi ya kasa mgana, daman Hajiya ta matsa ya bar mata Mimi ne saboda ta bari wani yaron talakawa mara tarbiya su hore ma ƴarsa kunne lalle ko idon sa idon yaron nan sai ya harbe shi. Kuma sai ya taka wuyan Mimi da har da bakinta take faɗin za ta iya auran wani banzan yaron da bai da wata makomai mai kyau nan gaba. Kawai amsa ma Hajiya ya yi da Toh ko gama mganar ma ba ta yi ba ya katse wayar Hajiya da sauri ya kira ɗan uwansa Alhaji Hamza. Cikin masifa ya fara gayamasa yana garin har ahaka ya faru wai Mimi ke faɗin tana son auran wani yaron talakawa? Alhaji Hamza ya ce bai sani ba nan Major ya sanar dashi abin dHajiya ta ce ya kara da cewa"Hamza ka je ka samu Hajiya ina bukatar sanin tarihin yaron nan tun daga farko har ƙarshe, sai  na ji waye mai wannan tsautsayin da zai hure ma ƴata kunni." Daga haka ya kashe wayarsa ya miƙe a fusace kamar ya yi bindiga tun daga falo ya ke ƙwalama Mommy kira. "Murja.." "Murja.."   Khadija na ɗakinta tana karatu sanda ta ji wannan kiran sai da hantar cikinta ya kaɗa domin a muryan Abi ta fahimci yau akwai bala'i a gidan nan, Mommy kuma tana jin yana kiranta tasan rufa rufa kuma ai ta kare. Shi ya sa ta sadakar ta fito da sauri tana gyara ɗaurin ɗankwalinta lokaci ɗaya tana  faɗin"Ga ni nan Habib...' "Da sanin ki Mimi ta fara soyayya da wani banza yaron talakawa?  da sanin ki Murja Mimi take son ta bijirema tunanina?  da sanin ki na ce.? Ya faɗa a fusace kamar ya kai mata  duka sai ta kauce cikin rawan jiki ta ce,"Ban ban sani.." "Sai na harbe shi, ko waye wlh sai na ga da abin da yake takama da shi. Ko madiha ban saka maganar auranta a kaina ba, sai Mimi? Mimi fa? Hajiya ba ta kyautamin ba wlh zan yi abin da zukata ba za su ji daɗi ba.". Ya ke faɗa ya na huci cikin ƙara daka  wata tsawa ya hau kiran sunan Khadija. "Khadija.." "Khadija.." Mommy jikinta na rawa ta ce"Khadija ba ta san komai ba Habibi." "Murja zan miki tijara na ce, ƙarya kike yi kin san komai, Hajiya zata gaya miki kuma Mimi yarki ce kina sane da abin da ke faruwa, Wlh tallahi in har da saka hannun ki a abin da ke faruwa zan iya sakin ki a kan haka." Khadija ta ɗora hannu akanta san da ta fito ta ji maganar Abi Mommy kuma sai kawai ta juya tana kuka ta shige ɗakinta acikin zuciyarta tana fadin" Inna lillahi wa'inna ilaihirraju'un.."   Khadija ya kallah da ke tsaye tsuru tsuru, tsawa ya daka mata kafin ya ce"Ke ma kin fara soyayya ne? za ku tsallake umarnina ne? Jikin Khadija na rawa ta duka tana faɗin "Abi karatun ka ce za mu yi kuma shi nake yi, wlh ban taɓa soyyayya da kowa ba."   Yana faman sakin huci ya saka kafa ya daki tuberin gabansa kayan ciki suka watse da karfi yake taku zuwa cikin ɗakinsa Khadija ta zura da gudu zuwa ɗakin Mommy tasan bindiga Abi zai fito da shi ai su yau sun shiga uku. *Janafty,* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:JamilaUmar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka. *Zumar Matsi Guarantee 3500* *Maganin sanyi komai nacinsa 4k* *Zumar kacha kacha 2500* *Zumar kiba 4k* *Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki* *Dahuwar kaza ta manyan mata 8k* Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0 *Page 14* Mommy na zaune a gefen gadota tana sharan hawaye daman abin da take gudu kenan, da gudu Khadija ta faɗo ɗakin tana faɗin "Mommy mun shiga uku bindiga ina ga Abi zai ɗauko." Ta faɗa lokaci ɗaya  tana hawa saman gadon ta lafe a bayan Mommy, tana ta haki tare  da sauke numfashi. Mommy ta yi ajiyar zuciya kafin ta ce"Allah ya duba mu, yau sai abin da Allah ya yi." Khadija ta ce"Mommy me ya faru ne? me Mimi ta yi ne?   Nan Mommy ta karanta mata abunda ta sani sai Khadija ta zaro ido kafin ta ce"Mommy ke ma me ya sa ba ki hana ba? Mimi tana hauka ne? Wani yaro ƙarami da bai wuce a wanke masa kashi ba ne za ta jawo ma na bala'i muna zaman zaman mu? Mommy ta karɓe da faɗin "Hajiya ce ta mara mata baya,

Chapter 17 of 26