Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta yi? Yana tafe sai faman sakin huci ta baki ya ke yi, yana tuna shi fa a kwanaki nan yana kai idanuwansa in dai bai kamata ya kai ba. Sai kwana ya ke yi acikin kuncin zuciya, haka yaje ya ga hotunta a shafin su na Karamchi Tv a Faceebook hotonta na barka da sallah wanda ta yi a madina. Ta saka bakar Abaya ta yane kanta da mayafi amman gabadaya hakoranta suna waje ne ta yi dariya. Karin bakincikinsa ma yadda ya shiga comments section ya ga ana yabawa da kyan da ta kara ita kuma har ta na ba da amsa tana dariya. Ranar bai iya barci ba saboda bakinciki da Kishi. Yanzu ma ya ƙara wani mugun gani, saboda haushin da yake ji yasa ya koma gida kuma sun yi waya da Makama ne za su haɗu. Saura kwana biyu bikin sa Mu'azzam sai gobe zai shigo garin. Yana saman mashin ya ji kiran wayarsa sai da ya isa gida ya duba ya ga makama ne. Sai ya kirasa daga baya, ce masa ya yi yana anguwan yana jiransa shi kuma ya ce ya koma gida. Makama bai yi fushi ba ya ce zai zo ya same sa su yi mgana. *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI   08066726866 Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z *Page 8* Sai da Makama ya zo ƙofar gidan sannan ya kira Aji ya ce masa gashi ya iso yana wajen get yana jiransa. Ba jimawa ko sai ga shi ya fito har ya sauya kaya zuwa wata jallabiya mai ruwan ƙasa. Hannu ya bashi suka yi musabaha da mirmishi kaɗan a saman fuskar Mansoor ya ce"Makama ango." Makama ya fashe da dariyan farincikin da yawanci angawaye a satin bikin su suke kasancewa kafin Ya ce" Aji namu, a waje zamu  tsaya ba za a bani izinin shiga cikin gidan ba ne?   Mansoor bai yi masa magana ya wuce gaba Makama ya biyo bayansa duk da ya taɓa zuwa tun ana aikin gidan ba a gama ba. Ya zagaye haraban gidan sannan ya ci burki a falon gidan yana faɗin. "Aji gaskiya ka tsara gida komai ya ji ban da abu ɗaya wlh." Yasan abin da zai ce shi ya sa ya yi masa banza ya isa ga ƙaramin firizan dake falon ya ɗauko masa ruwan gora guda ɗaya Sai ya haɗo masa da ƙaramin ƙofin dake saman firizan.   Ya kawo masa har gabansa ya ijiye yana faɗin"Ka sha ruwa Makama." Makama da ya yi rashe rashe a zaune ya ce"Zan sha ruwa, Aji ya kamata ace akwai mace a gidan nan gaskiya zai fi kyau." Ya kallesa a ɗage bai yi mgana ba sai ma ya kauda kai, shi kuma makama ya sha ruwa ya sauke kofin yana faɗin" Daman alfarma na zo nema a wajen ka." Sai ya juyo ya na kallonsa bai yi mgana ba Makama ya gyara zama yana fadin"Ba ku yi mgana da Mu'azzam ko Nasir ba? Sai ya girgiza kansa kafin ya ce"Ina Studio a gida na bar wayata ban sani ba ko sun kirani.". Ya faɗaa kai tsaye yana wani tsuke fuska shi fa baya son takura Allah yasa ba wani abu za su ce zai yi a bikin nan ba. Allah ma ya sani shi har addu'a ya riƙa yi Allah yasa ranar ma suna da wasa a wani garin ya bar garin sai bayan bikin sai ya dawo.   Sai dai addu'arsa ba ta karɓu ba sai ma watan gobe su ke da wasa kuma Kano pillars ne za ta zo wasan cikin gida za a buga, yana wannan tunanin ya ji makama na faɗin " Dama alfarman wajen kwana nake nema akwai abokai na ko na ce yan'uwa ne daga Zariya za su zo sh ine zan sauke su a gidanka sai sauran dai abokan mu na nan ai duk kasan su." Mansoor ya kallesa a karkace kafin ya ce"Ban san su ba." Daga haka ya cigaba da faɗin "Su nawa ne? Kasan ba na son takura kuma duk wanda zai zauna a gidana ina da dokoki." Makama ya ce" Ba za mu wuce mu goma ba." Mansoor ya kallesa cikin mamaki kafin ya ce"Ba ni da katifa, kuma  ɗakin da nake kwana ne kaɗai a gyare" Makama ya ce"Bakomai ga falo tunda akwai cafet sai ayi amfani da barguna., Ni da kai da Nasir da Ahmad da Mu'azzam sai mu yi amfani da cikin ɗakin naka." "Wani ɗakin kenan?   Har Mansoor na sauri wajen tambaya Makama ya nuna masa ɗakin da hannu kafin ya ce"Nan ciki mana ai muma gobe duk nan zamu kwana Aji." Mansoor ya yi shuru bai yi mgana ba yana jin Makama na sanar da shi Ahmad ma gobe zai shigo garin cikin zolaya ya ce"Gobe akwai kwanan hira za mu tuna baya ne Aji." Kallon Makama kawai yake yi ya ma kasa magana sai dakyar ya buɗe baki yace" Ni da Mu'azzam kaɗai zan kwana, ku sai dai ku kwana a falo." Ya faɗa  kai tsaye kuma da gaske yake yi Makama ya kallesa kafin ya ce"Ba ka isa ba, kai ko da yaushe sai ka nuna son kai wato Mu'azzam ƙanin ka ko? Ba ka isa ba Allah tare duk zamu kwana sai dai ka koremu in mu baka son ganin mu.". Ya karishe faɗa a kufule, Mansoor ya yi masa banza bai tanka sa ba sai cewar da ya yi" Ahmad da Nasir suna da mata fa to miye haka na wani zuwa su kwana a gida na? Mu fa ba yara ba ne mun girma Makama mu rika abu na masu Aji mana." Makama ya fashe da dariya har ya na dafa kafaɗan Aji kafin ya ce"Aji Aji! Aji namu  ba zaka taɓa sauyawa ba kai komai sai kace an yi abu na rashin Aji, Ahmad ai ya tafi da matarsa kaduna in da ya ke ɗinki Nasir kuma ya ce gamu za mu kwana waje ɗaya ba zai ware kansa ba"   Mansoor ya yi ƙaramin tsaki ya sauke hannun Makama daga kan kafaɗarsa yana faɗin " Ka ji ba, to shi yaro ne? Makama sai faman dariya ya ke yi, Mansoor kuma haushi duk ya kama shi, yaushe ne su Nasir za su girma su daina aikin yara ne?miye wani abun zuwa a cakuɗi a kwana waje ɗaya sai kace masu shiga itfikafi. Haɗe rai ya yi ba halin ya ce kada su zo ya san su mayu ne domin su kure shi ma Nasir sai ya ce su zo, kuma ya na da tabbacin Mu'azzam ya kasa gaya masa ne ya sa ya ce makaman ya zo da kansa. A rayuwarsa ta yanzu ya fi son ya zauna shi kaɗai ta fi yi masa daɗi in ka ganshi da mutane yan Club ɗinsu ne ko wani taro na buga wasa ko abin da ya danganci haka. Ko a baya da yake da sakin jiki da son mutane bai yi aikin yaran da su Nasir ke yi yanzu ba.   Sama sama ya ji Makama na faɗin"To yanzu dai ka amince mu zo ni da baƙina ko? Mansoor ya kallesa kafin ya ce"Ba na son mata a gidana, ko shaye shaye kai ko sigari na kama mutum na busamin sai na koresa, sannan 9pm nake rufe gidana in suna yawon dare ka faɗa musu su kiyaye sannan kwana nawa za su yi ne? Makama ya buɗe baki cikin mamaki kafin ya ce"Waɗanan dokikin kamar na shiga Villa? Mansoor yace" Gidan Aji ya fi Villa martaba da matsayi." Makama ya jinjina kai kafin ya ce" Ba shakka  kar ka damu iyakarsu kwana uku, kuma duk abin da ka zayyano ba sa mu'amala da ko ɗaya mu kuma ka san mu tun muna matasan mu in ma muna da wani halin banza za ka fi kowa sani." Kamar magana ce ya gaya masa, shi kuma bai damu ba sai ma kafaɗa da ya ɗaga masa ma'ana is better.   Makama bai ƙara wasu mintina ba, ya ma Aji sallama ya wuce gida saboda ya san ko ya zauna ba biye masa zai yi su tattauna ba tunda yasan hali, shi ko Mansoor Makama na tafiya ya ɗauko wayarsa ya kira Mu'azzam. Yana ɗauka ya fara masifa ta in da yake shiga ba ta nan ya ke fita ba. Faɗi yake yi" kai ne ka ce su zo su kwana a gidana  ko Mu'azzam? ka san me ka jawo ko? Mu'azzanm dai sai cewa ya ke yi"Ni fa ba ruwana ya yi min mgana ne na ce ya je ya same ka ya ji ta bakin ka." A Fusace Mansoor ya ce" Mu'azzam ka fara zama mara jin magana yanzu ko? Yaushe ka zama haka? To ka guji haɗuwarmu sai na saɓa maka." Daga haka ya katse wayarsa ya bar Mu'azzam da dafe kansa dagacan bangaren.   Hibba na gefensa daman suna cin abinci ne kuma a wayar akwai kara taji faɗan da Mijinta ya sha. Cikin kwantar da murya tace"Ka taɓo Baban Inna yau." Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ce" Na rasa me ya sa ya ke gudun mutane yanzu? Alhalin a baya ba haka Dan'uwana yake ba." Ya fad'a kamar zai yi kuka, Kansa take shafawa kafin ta ce"Ka yi hakuri mu cigaba da gayama Allah In sha Allahu komai zai wuce" Huci kawai ya saki ta baki wani abu na sukan ranshi. Hibba ita ta yi ta lallaahinsa har ya samu ya saki ranshi. Shifa Nasir ne ya matsa masa amman yasan haka za ta faru  bayan shi Mansoor ba ya son raɓar kowa ciki harda abokan da suka taso tare tun suna yara.   A bangaren Mansoor kuwa kwana ya yi ya na sakawa yana warwara, kamar ya gudu ya je Camp ɗin su ya kwana sai dai kuma ba ma evining training gare su gobe ba Morning ne haka kurum y ji baya son wannan haɗuwar, haɗuwar tana nufin tuna wasu abubuwan da suka shuɗe a baya. Da ace kafin ya sauya rayuwarsa ne ya san zai fi kowa murnan ganin sa a waje ɗaya tare da makama , da Ahmad da Nasir, saboda abokansa ne tun lokacin da Inna Meri aure ya kawo ta Gombe a kuma anguwan Arawa su ya fara sani bayan Mu'azzam. Har gari ya waye bai samu mafita ba hakanan ya shirya ya tafi Studio din su yana shiga wajen daman shi kaɗai ke jira sai ji kawai kake yi " Barka da safiya Captain"  shi kuma yana ɗaga musu hannu dukkansu suna sanye da yellow din riga da ƙannanun wanduna takalman kafarsu ma mai ruwan kwai ne, suna shirye waje ɗaya a layi dukkansu kowa ya harɗe hannayensa a bayan hannunsa sun kame waje ɗaya. Wajen Cauch ɗin su ya nufa shima yana Shirye da irin kayansu hannun ya bashi suka yi musabaha. Cikin yanayin maganarsa ya ce"Barka da safiya Coach." Shima ya amsa masa da cewa" Barka da safiya Captain." Nan da nan aka hura usir members suka fara gudanar da training ɗin su.   A gida ya bar wayarsa saboda ya san za a yi ta kiransa a waya  sai wajen sha biyu ya koma gida ya yi wanka ya ɗan kwanta kafin azahar sai a lokacin ya duba wayarsa ya ga an kira shi da yawa harda Mu'azzam sai Nasir. Kiran Mu'azzam ya bi, bayan ya dauka sun gaisa yace gashi ya iso yanzu ba da jimawa ba. Shi kuma sai ya ce yana gida zai huta sai zuwa bayan la'asar zai shigo anguwan, ko kiran Nasir bai bi takai ba ya share shi saboda tun a zamanin baya sun fi yawan samun saɓani da Nasir. Nasir akwai daɓa mgana ko kaji haushi ko ta yi maka daɗi  shi kuma Mansoor saurin hasala da zuciya da masifa ko magana za ka iya yi ya ce da shi kake shi ya sa suke saurin samun matsala da Nasir ko a baya. Bai yarda barci ya daukesa ba sai da ya je ya yi sallar azahar sannan ya dawo ya kwanta kuma ya samu barci sai uku da rabi ya tashi. Ya ji kuma zuciyarsa ta rage nauyi tunda daman ya daɗe ba ya samun barcin dare sosai.   Wanka ya sake yi ya shirya cikin wata Riga ta kwallo ce an saka MESSI a jikin rigar saboda shi Mansoor allon ƙwaikwayonsa a kwallo tun a zamanin baya Messi ne har kuma yanzu da yake cikin kwallon dumu dumu bai sauya gwani ba, sai ya saka bakin wando mai kamawa ta kasa kaɗan ya yi zanzanro sannan ya saka wani bakin takalmi mai rufi ya kuma gyara gashin kansa da ya tara sai ya ɗora P.Cap saboda ba ya so Inna ko Baba su gani su yi masa faɗan rashin aski. Ranar har da fesa turare abon da ya jima bai yi ba. Key din mota ya ɗauka da ita yau ya ke fita tunda zai kai ta gareji a yi juyen baƙin mai ya jima bai kaita an duba ta ba. Shifa ba domin Mu'azzam ya matsa masa ba bashi da ra'ayin siyan mota mashin ɗinsa ta ishe sa, farko mashi ɗin da ya siya Baba Danjuma ya ba ma wa, ko wata ba ta yi ba aka tare shi aka karbe mashin ɗin Allah ya sa ba su yi masa rauni ba sun dai dake sa, sai yanzu ya ke tunanin zai ba shi wannan mashin din sai ya siya babba mai kama da mota.   Daga anguwarsa ta Tunfere gareji ya je da yake kanukawan sun waye shi yana zuwa suka fara kiran sunansa "Aji Aji.! Shi kuma yana ba su hannu suna gaisawa anan ya ɓata lokaci har wajen biyar na yamma Nasir ya kara kiransa ya ki ɗauka sai ga Ahmad ya kirasa shi kam daman sun jima ma ba su yi mgana ba. Shi ya sa ya ɗauka sun  fara gaisawa kenan Nasir ya karɓe wayar yana faɗin "Aji ni kake yi ma wulakanci ko? Duk abin ka dai yau a katifarka zan kwana." Bai gama sauraransa ba ya katse wayarsa Nasir dai ba zai taba sauya hali ba.   Sai da aka gama duba motar ya ba su kuɗinsu sannan ya baro garejin zuwa gida, ya je ya iske Inna Meri ita kaɗai a bangarenta Walida ba ta nan ta tafi islamiya. Ya zauna suna gaisawa ta ce masa yanzu su Mu'azzam suka fita suna ta jiransa. Shuru ya yi bai yi mgana ba, Inna Meri ta je ta kawo masa ruwa da abinci kamar ta san ya na jin yunwa. Shinkafa da wake ne da manja ya na son dahuwar Inna wake ya dame da shinkafa. Yadda ta ga yama cin abincin ne ya sa ta san ya daɗe bai ci abinci ba. Cikin Tausayin shi ta ce" Baban Inna ka rika cin abinci don Allah, zama da yunwa babu amfani ka tattala lafiyarka tun kafin ta kubce maka." Kai ya gyaɗa mata kafin ya ce'" To inna." Daga haka ya cigaba da cin abincin sa, tana lura da shi ana ta kiran wayarsa yana kashewa. Kuma tana jin  Nasir kafin su fita  dazu yana  faɗin baya ɗaga kiransa, sannan Mu'azzam ya ce"Don Allah Inna ki roki Baban Inna kar ya ce zai ja baya a sha'anin nan na Makama kin san halinsa."   Shiyasa yana gama cin abinci ya sha ruwa ta kalle sa kafin ta ce"Su Nasiru sun fita suna ta neman ka, ka kira su kaji in da suke Baban Inna." Ba musu ya ce To Inna ya ɗauko wayarsa ya Kira Mu'azzam sai yace suna kofar gidan su Ahmad. Sai ya ce yana gida su kariso, Bayan sun gama wayar Inna Meri ta kalle shi tana fadin" ka saki jikin ka bikin abokin ka  ake yi ba na wani ba, Don Allah ka zama aboki nagari ban san kana zille zille nan." Sai da kalaman Inna su ka bashi dariya sai ya girgiza kai kafin ya ce"Mu'azzam ne ya kawo miki ƙara ta ko Inna? Inna ta ce" ba ruwa Ɗan Inna ni na haife ka ai na san halin ka." Mirmishi kawai ya yi bai yi mgana ba Inna Meri ta zauna ta na ta masa nasihanta na kullum ya yi hakuri ya manta baya ya dawo da rayuwarsa kamar ta baya. Jin ta kawai ya ke yi, shi fa bai ga wani Sauyawar da ya yi ba, ya na dai guje ma wasu abubuwan ne saboda gudun tuno da abjn da ya wuce a baya. Kiran wayar Mu'azzam ya ƙwace sa ya mike ya ce bari yaje waje suna jiransa.   Yana fita ya gansu gabaɗaya Makama ne kawai babu Ango kenan, yana fitowa Nasir ya ɗauki dutse ya jefe dashi ya caɓe dutsen Ahmad na dariya ya ce"Ka ga Ajin ƙwallon kafa akwai iya kama saiti." Mu'azzam na jikin Motar Mansoor ɗin shi da Ahmad suna dariya. Nasir faɗi ya ke yi" yau fa sai mun raba hali ni da kai Aji."   Aji ya kallesa kafin ya ce"Nasir ka yi aure ba ka girma ba? Sai yaushe? Ahmad yace" Sai matarsa ta haihu, daman tsohon ciki gareta." Mansoor ya yi mirmishin saman fatar baki bai yi mgana ba, ya isa wajen Ahmad ya bashi hannu suka yi musababa Ahmad ya jinjina hannunsa yana faɗin"  Aji an daɗe ba'a haɗu an gaisa  ba." Aji ya ce"Wallahi ya rayuwa.? Ya amsa ma sa da Alhamdulillah.   Mu'azzam ya mika masa hannu suka gaisa ya tambaye shi ya hanya? Ina su Junior ya ce duk suna gaishe su. Nasir ne ya warce hulan kan Mansoor ya ɗora bisa kansa Mansoor ya bisa da kallo kafin ya bata rai lokaci ɗaya yana faɗin. "Nasir ka rika yin abu cikin Aji don Allah mana." Gabaɗayansu suka fashe da dariya, Ahmad da Nasir suka haɗa baki wajen faɗiin " Da girman Kujeran Aji Allah ya kara lafiya." Mu'azzam nata dariya, shima Ajin sai da ya Murmusa kafin ya mika hannu ya warce hulansa daga kan Nasir yana faɗin"Kai yaro ne har yanzu Nasir na kara samun tabbacin tsawon kafan ka ne, ya ruɗeka ka yi saurin aure." Nan ma suka kara kecewa da dariya Mu'azzan na ta mirmishin jin daɗi  ganin ɗan uwansa na hira har da mirmishi.   Makama ya tambaya Mu'azzam ya ce ya karbi motarsa ya je ya dawo, suna faɗa masa wai akwai kamu a gidan su Amarya kuma ana bukatar ganin Ango da abokansa. Aji ya kallesu a kaikace kafin ya ce"kamar wasu mata sai ku je kuma? Ahmad ya ce"Ni kaina na ce ba za mu je ba." Aji ya ce"Kana da girman ka Ahmad gwara ka kama kanka da harkan yara." Ya faɗaa ya na nuna Nasir, Nasir kuma ya ce shi in ba za su je ba zai raka makama, Mu'azzam ma ya ce shi yanzu Tudun wada zai je ya kai wani sako saboda jibi ya ke so ya koma saboda aikinsa. Nasir kuma ya kira Makama ya ce ya shirya zai raka shi su tafi kamun tare da sauran abokan shi. Nan ya barsu ya wuce gida su kuma suna nan kofar gidan suna ta hira har aka kira mangariba. Abun mamaki Mansoor ya saki jiki suna ta hira da Ahmad.   Duk dai yawancin hiran ta ƙwallo ce daga nan suka aika cikin gida aka ba su butoci suka yi alwala suka wuce masallaci. Daga nan Mansoor ya ɗuke su a mota zuwa Tudun wada gidan su Hibba ya kai mata sakon da ta ba da, daga nan dakyar ya roki Mansoor ya biya da su Bolari can gidan su mahaifiyar Mu'azzam kakarsa Innayi ta na nan da ranta da ta ga Mansoor sai da ta ce shiyasa ta ga an sha iskar rahama ashe shi ne zai zo.   Tunda ya daɗe rabon shi da zuwa a baya dai duk zuwa shi da kansa zai raka Mu'azzam gidan ya gaida kakaninsa. A gidan suka ɗan jima shi ya sa ba su baro anguwan ba sai da suka yi sallar Isha'i. Daga nan suka koma anguwan Arawa Ahmad ya ce zai ɗauki sako a gida suma sai suka shiga gida suka gaida Baba Danjuma. Magajiya ba ta nan ta je kauyen su wani kawunta ya rasu. Tare da Mariya ta tafi duk yadda Baba Danjuman ya so ta kyaleta tunda akwai makaranta ta ce da ita za ta tafi. Mariyan ma ba ta so hakanan ta shirya suka tafi. Suna ɗakin Inna Meri tare da Baba Danjuma da Innar suna ta hira Walida ta zuba musu tuwon da Inna ta yi da yamman nan suka ci a kwano ɗaya tare da Baban su.   Ba su bar gidan ba sai goma lokacin da Ahmad ya kira su ya ce yana jiran su a waje, su daga nan suma wuce gidan Mansoor, a nan ne ma Mansoor ya ga kayan da Mu'azzam ya siya musu Shadda mai ruwan kasa su huɗu  Ahmad ya dinka musu daman shi ya tura ma kuɗin ya siya musu shaddar. Daman shi ba'a iya masa sai da ya kalli Mu'azzam kafin ya ce" Sai kace wasu yara mu saka anko? Tunaninka ya koma na yara ne Mu'azzam". Shi dai dariya kawai ya yi Ahmad ke faɗin. "Haba a baya ai muna ɗinka kaya iri ɗaya Aji ka manta ne" Kai tsaye ya ce"Yanzu mun girma mun zama magidanta kai da matarka da yarka, Mu'azzam da matarsa da ɗansa Nasir ma haka ga shi Makama zai yi aure ace duk ba ku fita sahun yara kun fara halin manya ba? Ahmad na yar dariya ya ce"Kuma fa hakane to daga wannan shike nan da bikin ka kowa kalan na shi zai saka." Banza ya yi masa kamar bai ji ba suka haɗa ido da Mu'azzam suna dariya. Su Nasir ne ba su dawo gidan da wuri ba megidan ya riƙa masifa yana faɗin"Ku kira su Nasir ku dawo kar na rufe gidana ya zageni, yana magidanci yana yawon dare"   Ahmad ya ce"Ba sun je kamun Amarya ba." Aji ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce" kamun amarya ko kamun shirme." Mu'azzam ya kira Nasir a waya ya ce ga su nan a hanya. Sai wajen sha biyu saura suka dawo Mansoor ya yi ta masifa yana cewa da sun kara mintina zai rufe gidansa ne. Nasir na rungume da katuwar jakar kayansa ya shigo yana fadin"Mun ji to megida mun ji to." Ya faɗa yana ture Mansoor ya shige falon. Makama tare da wasu maza su uku biyun bai san su ba amman yasan ɗayan abokin makama ne Nura suna ga gida ga gida ne. Hannu suka bashi dukkansu suka yi masabaha, daman da motar Mu'azzam suka dawo sai da ya fita ya rufe get sannan ya dawo. Allah ya taimaka nepa suka kawo wuta sai fanka ta fara kaɗaawa. Makama da abokinsa Nura da sauran ƴanwansa suka kwana a falo. Nasir da Ahmad da Mu'azzam da mai gidan suka kwana a ɗakin Mansoor.   Dolensa ya bar katifa nan ya kwana a ƙasa saboda yana kwanciya Nasir yazo ya shige tsakiyar su shi da Mu'azzam yana faɗin "Ni fa na saba da katifan matata ba zan iya kwanan ƙasa ba." Mansoor ya yi ta tsaki ya na faɗin" Nasir sam ba ka da Aji." Ya na dariya ya ce"Na ji Aji mai Aji ba." Karshe kasa ya kwana shi da Ahmad da Asuba shi ya ta da su suka yi alwala zuwa masallaci daurin auren na safe ne misalin sha ɗaya ne. Shi duk haushin su yake ji wannan abun fa sai ya yi kamceceniya da abin da mata suke yi. Ko a baya da yake cikin su ba haka halinshi yake ba yana komai da class ne shi ya sa ma a

Chapter 11 of 26