Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
raga.   Rumgume hoton ta yi tana ji zuciyarta na bugawa sama sama. Tunaninta kuma ya tafi akan shin kamar yadda take bibiyan rayuwarsa shima ya na nibiyanta haka? Tsintar Aji a duniyar kwallon kafa ya sa ta sare ta yarda da mganarsa ya sauya mafarkinsa tuni. Ita ce shaidan yadda Aji ya so zama soja ƙwallo ma ra'ayin Mu'azzam ne ba ra'ayin Mansoor ba, kuma ko a baya ƙwallo  bata burgeshi duk ya na buga ƙwallo amma tasan ya na zuwa kallon ƙwallo sosai. Sai gashi rana tsaka ta ganshi tsamo tsamo acikin ta, duk me ya faru bayan rabuwarsu? Shi ne ba ta da wannan amsar ta jima Rumgume da hoton tana kuka kafin ta gaji ta nannade hoton ta kuma maida shi ma'ajiyarsa. Sallar isha'i ta yi yunwa take ji har ta fara ganin jiri.   Shi ya sa bayan ta idar da ta ji Baaba Uwani na buga mata Kofa taje ta buɗe Abinci ta kawo mata sai ta ce ta koma da shi ta haɗo mata tea ne. Sai ta Juya ta na fadin"Binta ki fito falo Hajiya fa ta damu." Cikin dashewar murya ta ce"Ki faɗa mata kar ta damu da ni ina lafiya." Daga haka ta juya ciki ta koma ta zauna ta yi tagumi. Tana tunanin makomar rayuwarta anan gaba, ko ta amince ko kar  ta amince rabuwarsu da Mansoor ta har Abada ce kuma da gaske yake yi da ya ce zai gogeta daga tunanin sa da mafarkin sa gabaɗaya. ***** *08 Feb 2022.* 6:00pm Yana studio ɗinsu yau sun yi afternoon training ne ya samu wayar mijin Bintu Bashir yana faɗa masa tun safe Bintu ta rufe Kitchen ta kuma ɓoye makulli ta ce ta ga wanda ya isa ya dafa abinci ya ci acikin gidan nan, Bashir ɗin ya ce ya yi ta roƙonta bata saurare shi ba, sai yaji ransa ya ɓaci daman ya na ta so yaje gidan sai kuma wasu abubuwan suka ɗauke masa hankali. Amma tunda abun har ya kai ga haka ai shike nan zai je gidan yaji ta inda iskancin na Bintu ya fara.   Coach ɗin su ya sanar ma zai je gida ana nemansa daman da mashi  ɗinsa yazo sai ya sauya wandonsa jikinsa daga gajere zuwa dogo tunda gidan surukai zai je kuma a matsayin sa na babban yaya ya rike girmansa. Cikin lokaci ƙankani ya iso gidan tun da nan anguwan Arawan ne daga can baya ba su da nisa daga gida. A kuma Kofar gidan ya ci karo da Bashir ɗin yana jiransa. A yadda ya gansa duk ya yi wani firgai firgai sai ya fahimci Bintu na iskanci kala kala acikin gidan nan tunda har mijinta na tsoronta.   Gaisawa suka yi bayan sun yi musabaha Bashir ɗin ya fara faɗin "Wato yayanmu lamarin ne ya fara fin karfina. Wajen sati ɗaya gidan nan ba ma zaman lafiya." Mansoor ya kaɗa kai kafin ya ce"Ka yi min izini mu shiga gidan tare." Ya na jin haka ya fara sosa kai yana Faɗin"To to shike nan Yayanmu ammh don Allah kar ka ce za ka yi mata faɗa a bi ta a sannu." Takaici yasa ya wuce yana faɗin"Kai dai ba ta gagare ka ba?  to ni ba za ta gagare ni ba don ubanta." Ya na faɗin haka lokaci ɗaya ya yi sallama acikin gidan. Bashir na binsa a baya jikinsa na faman rawa..   Uwar gidan Bintu ce a tsakar gida ita ta amsa masa sallamansa, ba saninsa ta yi ba domin bata ta taɓa  ganinsa a gidan ba amman ganin yadda ya shigo gidan ga Bashir a bayansa yana wani sunne kai. Kafin ma ta yi mgana ya yi saurin tare ta da cewa"Hadiza. Yayan Bintu ne" Kai tsaye ta kallesa tana faɗin"Ayya ina yini? Bai kalleta ba ya ce"Barkan mu da yamma, ina ne ɗakin Bintun? Ya faɗa ya ma kallon Bashir saboda shi dai yasan gidan ammh bai taɓa shigowa ba, shima abin da ya sa ya sani saboda Mu'azzam sun ne taɓa wucewa ta kofar gidan ya nuna masa ya ce ga gidan da Bintu ke aure. Da dai Mu'azzam ne shi kam kamar wani mace gida gida na mata ya iya shiga.   Bashir na gaba yana bayansa har ɗakin Bintu Hadiza ta bi su da kallo, ko shi ne yayanta ɗin ɗan ƙwallon kafa wanda a kace zuwa da shi garin aka yi?  domin ta san ɗayan yayan nata ɗan sanda ne tun da yana zuwa gidan in yazo garin, kuma ga dukkan alamu wannan bashi da wasa, kuma sai yanzu ta ga kamansu abu ɗaya ne ya bambamta su ita Bintu fara ce shi kuma baƙi ne. Taɓe baki ta yi domin ita abun ya isheta  Bashir ya zama sallamame tsoron Bintu yake ji, bai iya wani kuzari in tana wajen shi ya sa take yin abin da ta ga dama. Ita dai ta faɗa masa ta gaji, ko ya ɗauki mataki ko ta bar masa gidansa ya zauna da yar so Bintu.   Duka duka s haihuwanta ɗaya ne ya karo mata kishiya da fitinanniyar yarinyar nan tunda ta shigo gidan ta daina barin su cikin sukuni. Tana kokarin shiga ɗakinta bata san mai ya faru ba taji muryan yayan Bintu cikin tsawa yana faɗin"Ina za ki je kuma?  dawo nan ki zauna munafuka." Kuma ta ji ko motsin Bintu bata ji ba, a ranta tace kila dai wannan ne mai maganinta. Tana yar dariya ta shige ɗakinta.   Abin da  kuma ya faru shine suna shiga ɗakin nata, Mansoor ya zauna a falo Bashir kuma har ya mike jikinsa na rawa zai je ya kirata sai ga ta fito. Sai dai jikinta ya yi sanyi da ta ga Baban Inna ai ta shiga uku. Sai ta juya da sauri za ta koma shine ya daka mata tsawo ya ce ta dawo ta zauna. Sai gata ta dawo sumi sumi jikinta na rawa ta zo ta zauna kan kujera ta kuma ga mijinta a ƙasa wani kallon da Baba inna ya yi mata ta bakin ta yasa ta sauko kasa bata shirya ba.   Gyara zamansa ya yi shi cikin kaushin murya da ba wasa ya kalli Bashir yana faɗin"Me ya faru ne? Ka yi mini bayani tun daga farkon rigimar har zuwa yau. Bashir ya gyara zama ya fara faɗin duk fa rigiman akan less ne da ta gani a jikin Hadiza ne shine ta saka rigiman ya ci amana ya siya ma Hadiza leshi bai siya mata ba, shi kuma ya rantse mata da Allah ba shi ya siya ba da kuɗin adashenta da ta kwasa ta siya saboda ƙaninta zai yi aure.   Shi ne Bintu taki yarda ta rika zage zage tana cewa ya ci amananta shima sai ya siya mata wannan leshin za'a zauna lafiya, ganin abun nata yaƙi wucewa ya sa ya ce in ya samu kuɗi zai siya mata amman ta ce ba ta yarda ba har abun ya kai yau ta rufe kitchen ta ce ta ga mai girki a cikin gidan balle aci abinci." "Wlh karya yake yi, shi ya siya mata saboda cin amana..!"   Kafarsa ya saka ya hambareta ya ma manta ba a filin ƙwallo ya ke ba, da ace da karfi ya haureta da sai ta ci haɓo da bakinta. Cikin tsawa ya ce" Ashe baki da mutumci ban sani ba?  mijin naki kike ƙarya ta wa? Ya faɗa cikin takaicinta yarinyar nan fa ta yi nisa. Ita kuma sai ta koma gefe ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh ba gaskiya ya faɗa ba, shi ya siya mata ni dai na ce wanda ya zalunce ni ban yafe ba." "In kika ƙara mgana ba tare da nace ki yi ba, na rantse da Allah sai na yi biji biji da rayuwarki anan wajen."   Ya faɗa mata cikin tsawa ganin yadda yake huci ya sa ta shiga taitayinta kar ya yi ƙwallo da ita ya za ta ko ball ce ya samu, ta kuma san shi da bakar Zuciya kamar Kuturi ya yi zuciya to sai fa ran kowa ya ɓaci. Shi ya sa ta koma gefe ta yi shuru ta na hararan Bashir kamar Idanuwanta za su faɗo. Ba dai ita zai haɗa da Baban Inna ba, sai ya gane kuransa. Kuma duk yana ganinta ta na harare harare, kuma abun haushi Baahir din na bata hakuri da hannu. Sai ya ji ba Bintu ba ce abun duka harda Bashir din tunda ya fahimci sakarai ne. Bai yi mgana ba sai da ya saka Bashir ɗin ya kira matarshi Hadiza.   Ta sako hijabinta tazo ta zauna itama ta tambayeta ta maimaita abin da Mijinta ya ce ta karishe da faɗin "Wlh ni na siya leshin nan da kuɗina, ba Baban Afra ya siyamin ba gaskiyan magana kenan." Ba domin Baban Inna na wajen ba mikewa za ta yi ta karyata su ammh tasan ta sake magana sai an yi abun kunya a gaban kishiyarta. Shuru ya yi na wani lokaci kafin ya kalli Bintu ya na faɗin "Ba ki da kaya ne da za ki ta da rigima saboda leshi? Ko a tsirara kike yawo ba mu sani ba? Bintu ta yi kwalkwal kafin ta ce"Ina da shi, amma Baban Inna."   A tsawace ya ce"Ke sunan nan ya fita daga Bakin ki ko naci ƙaniyan ki wlh." Daga nan ta san kuskuren da tayi da sauri ta gyara da faɗin" Yayanmu  shi ya siya mata fa, kuma ai ina da haƙƙin nima ya siyamin tun da adalci aka ce ayi." Ta gama faɗa ta na harare harare. Cikin jin haushi ya ce"To na ji ya siya mata ke bai siya miki ba sai aka yi ya ya? uwarsa ce ke da dole sai ya siya  miki duk abin da bai yi niyya ba? In ma ya siya mata da ita  kika zo gidan kika gansu kuma gidansa ne yana da Ikon ya yi abin da ya ga dama, kin rufe kitchen kin ce ba wanda ya isa ya ci abinci  nace abinci daga gidan Wanzamai kika zo da shi?. Na ce daga can kika zo da shi? Ya karishe faɗa cikin tsawa sai Bintun ta saki kuka za ta sake  mgana cikin ƙara daka mata tsawa ya ce"Ba da ke nake mgana ba? da sauri ta ce"A'a.   Kai tsaye ya ce"To ashe iskanci ne a cikin kanki ban sani ba, ba ki da mutumci na jima ina jin labarin ki kuma daman ina jiran wannan ranar, daga nan wajen wallahi na kashe wannan mganar, ko da wasa kika kara tada mganar leshi na ji labari zan yi miki abin da ba ki yi tsammani ba, sannan ki ɗauko Key din kitchen ki ba ma mijinki ki kuma bashi hakuri, sannan kar na sake jin kin fito kin yi zage zage ko rashin kunya, kin sanni kin san halina ba ni da kyau ko nayi wanka kika bari na kara takowa cikin gidan nan sai nayi miki dukan mutuwa wlh, kuma kinsan ina faɗar abinda zan iya aikatawa ne ba wanda bazan iya ba."   Ya karishe faɗa lokaci ɗaya yana mike wa Bashir  ma ya miƙe shima da sauri yana faɗin "Ai Yaya Mu'azzam ma ya kirani ya ce shi zai siya mata leshin ma." Da sauri Mansoor ya ce"Ba zai siya mata ba sai dai ta mutu, hakkinta baya kan mu yanzu ya na kan mijinta ne, abin da ka yi mata ta yi hakuri da shi, zan kira shi Mu'azzam ya siya mata leshinan shima sai na ɓata masa rai." Ai daga Bintu har Mijinta ba wanda ya samu bakin mgana Hadiza kuma sai jin daɗi take yi a ranta tana faɗin daman akwai mai maganin Bintu haka aka barta tana iskancinta. Har sanda zai fita sai da ya juyo ya kalleta yana faɗin"Ki natsu ki zauna lafiya kar ki kara tada ma Inna da Baba hankali in ba haka ba kin fi kowa sani na." Daga haka ya fice Bashir ya bisa, Bintu ba ta saki baki tayi ihu ba sai da ta tabbatar da Baban Inna ya bar gidan. Sannan ta kwanta anan in da ya barta tana kuka Hadiza ta mike ta na yar dariya ta fice daga dakin. Bashir kuma daga raka Mansoor bai dawo ba yana tsoro. Shi dai Mansoor ya faɗa masa in bai gyara gidansa ba wani na waje ba zai iya zuwa ya gyara masa gidansa ba. Bintu tasan halin Baban Inna wajibi yasa ta fito da key ta mikama Hadiza sannan bakinta gum.   Sai dai Bashir ne ya gane bashi da wayau ta fara gaba da shi, shi kuma yana ta bin ta yana ba ta hakuri, ita bakincikinta ɗaya faɗan da Baban Inma ya yi mata a gaban kishiyarta, Har Mu'azzam ta kira tana kuka ta gaya masa lallashinta ya yi shima yana faɗa mata yadda Yayan nasu ya kirashi ya yi masa faɗaan cewan da ya yi zai raba gardama da siyan leshin. Daman Mu'azzam ne ke biyema iskancin Bintu ya yi ta lallashinta, dole dai ƙanwar naki Bintu ta hakura da maaganar Leshi.   Haka ta je gida tana Inna abunda Baban Inna ya yi bai kyauta mata ba, zaginta ya yi ta yi a gaban kishiyarta. Inna meri ta ce"Dakyau gwara da ya yi miki haka tunda sakara kike mara wayau." Saboda Inna ta goyi bayan ɗanta  ya sa bata daɗe ba ta gudu gidan Yaya Amina.   Itama nan ta sanar mata da abin da aka yi mata, itama dai hakuri ta ba ta to wa ya isa ya ce Baban Inna bai kyauta ba? Ko su Inna bai faɗama ya je gidan ba ammh kowa fa ya ji daɗin haka tunda Bintu ta natsu tana tsoron ta kara wani abu Bashir ya sanar da Baban Inna ta shiga uku. Wai kura ma tayi lafiya kenan da ace a baya ne kila sai ya barta kwance zai bar gidan. *BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* *09069067488* *80032773332* *Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar* *09069067488* *NA GODE.* *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL MUNA ADASHEN GATA SBD YANA YIN DA MUKE CIKI 500 DUK SATI IN KIN KAMALLA ABAKI DUK ABINDA KK SO INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYA IRIN SU WAYA BLENDER WASHING MACHINE 08066726866 MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT Y'AR MUTAN SAKWATO *Page 4* *ABUJA GWARIMPA, N0:770* *Saturday 18, Feb. 2022* 11:44am. Gidan retire Major Kabir Sulaiman Dabo tun yana cin zamaninsa gida ne da ya amsa sunansa gida, yana cikin garin Abuja sannan a cikin wannan kyakyawar anguwan nan ta samu kusa a gwanmati wato Gwarimpa. Gidan nyana nan da kyansa kamar baya, ko da megidan ke kwance ba shi da lafiya Dr. Sulaiman da Daddy Hamza ba su bari gidan ya bukaci wani abu ba.   Akwai tarin ma'aikata acikin gidan tun daga megadi zuwa masu kula da haraban gidan, ciki kuma masu aikin bangaren share share da girki saboda Barr. ba mazauniya ba ce tana fita kotu in tana da shari'a. Ammh kafin ta fita sai ta gyara mijinta tsab ta masa duk abin da yake so sannan take fita, in ta na gida ita da kanta ta ke shiga kitchen ta girka masa irin abincin da yake ci saboda yanayin jikinsa.   Major Kabir ba shi da wani aiki daga kwanciya sai ko in ya gaji ta kama shi ta ɗora shi saman Wheelchair da taimakon wani Musa mai kula da fulayoyin gidan tunda ita kaɗaai ba zata iya ba. Duk da kuma tana ma iya bakin ƙokarinta. ƴayansu suna nesa da su amma suna zuwa ganinsu lokaci bayan lokaci musamman ma Dr. Sulaiman da duk wata shi da iyalansa suna zuwa Mimi kuma sai ta yi wattani uku bata zo ba suna dai magana ta waya.   Wannan watan ba ta kai karshe ba suka haɗu gabaɗayansu a Abuja Saboda jikin Abi da ya motsa, da ya ke akwai likitan  na musamman ne daga babban Asibitin Abuja yake zuwa ya na dubashi ko da aka san laluran bata warkewa ba ne, amma zama waje ɗaya dole akwai bukatar tallafawan likitoci da sharwarwari. Bayan Dr. Sulaiman da iyalansa har da Khadija(Khadi) ta zo itama sai Mimi da Hajiya wacce ta na jin Mimi zabta je ta ce ita ma ba za ta zauna ba, dole Mimi ta yi musu bucking din jirgi suka taho ranar jumma'a da yammah. gidan sai ya yi albarka Sosai Madiha ce kaɗai bata samu zuwa ba ta ce sai karshen wata za ta shigo tayi hutun ta, daga nan har Gombe za ta shiga ta ga dangi kafin ta koma.   Jiya kwana suka yi hira Abi yaji daɗi sai dai yana kwance yana ta faman mirmishi kamar yau ɗin ma da gabaɗayansu suke cikin Bedroom ɗinsu shi da Mommy tunda yace a barshi a kwance yafi jin daɗin kwanciyar. Gabaɗayansu suna ɗakin ƴayan Dr Sulaiman su biyu kacal duka kuma mata da mai sunan Mommy Murjanatu suna kiranta Ummita sai mai sunan Hajiyar Shagamu suna kiranta Momi. Sune ke tare da Abi suna ta nuna masa abu acikin Kananun tab ɗin su na yara da yake hannunsu. Hajiya na gefen kafafun Abi ta na mgana da Mommy.   Dr.Sulaiman na daga gefe tsaye ya harɗe hannayensa a saman kirjinsa dogon farin Bafullatani mai cike da fara'a da zati. Matarsa kuma mai suna Jawahir ta na gefen Mimi, ita tana zaune a saman kujerun Dreesing mirro, Mimi kuma tana daga saman madubi sai dai waya ce a hannunta tana ta faman latswa rabi da rabi hankalinta ke wajen Hajiya tana jin hiran da take yi ma Mommy, jefi jefi kuma Big bro na saka musu baki Sisto kuma ta fita ta je za ta yi wanka.   Duk Lokacin da Mimi ta ɗago kanta sai ta ga Abi na kallonta sai ta yi masa mirmishi kawai shima sai ya mai da masa martanin mirmishinsa Allahu Akbar rayuwa kenan Abi na bata tausayi in ta kallesa shi ya sa ka bi rayuwa a sannu in kasan mafarin ka, ba ka san karshen ka ba. Ba za ta manta Rayuwar da suka gudanar a wannan gidan ba shi ya sa har gobe bata kaunar duk wani aiki na kaki saboda gani ta ke yi kamar yadda Abi ya rika tafiyar da rayuwarsa a baya saboda kakin da ke jikinsa ne.  Abi ya yi zamanin da duk abin da ya ce ba wanda ya isa ya ta da shi, hatta Hajiya da ta haifesa kuwa, Mommy kuwa da suka yi auran soyayya ba ta isa ya nemi shawaranta ba ra'ayinsa ya ke bi da abunda ya yi masa dai dai shi ya ke aiwatarwa. A zamanin baya mutum ne mai murɗewa da ka'ida mai tsauri, amma sai ga shi rayuwa ta sauya komai yanzu ya yi sanyi Abi ya koma rayuwar kwanciya cikin ibadar Jinyar ta Ubangiji sai ta ga ya yi sanyi rayuwar ma kamar tsoro ta koma ba shi. Duk sanda zata zo ta koma tsakaninsu sai ban hakuri ya rika cewa Ki yi hakuri kin ji ko Mimi? Sai ta ce bakomai Abi zan cigaba da yi maka biyayya har karshen numfashi na.   Yana so ya yi mata mgana amma kuma har gobe ya kasa iya furta wani abu. Ko mganar ta ƙi sauraran kowa ake yi a gabansa sai ya ce a kyaleta a daina takura mata, in kuma yan'uwansa suka zo suka fara mganar Mimi taki aure har yanzu kuma shekarunta na tafiya sai ya ce kar da wani a cikinsu ya ce zai takura mata a kyaleta ta yi aure a lokacin da take so da kuma wanda ta ga ya dace da ita. Kowa yasan dalilinsa na cewa a kyale Mimi to bakin alƙalami ya riga da ya bushe abin da ya faru a baya ba wanda ya isa ya iya sauya shi.   "Habibi ko Dr zai ɗaura ka saman Kujeran nan ne, na ga tun jiya fa kake ta kwanciyar nan?   Mommy ta faɗa Lokaci ɗaya tana mikewa Hajiya ta ka da baki ta ce"Gaskiya kwanciya da zama waje ɗaya ba daɗi. Kabiru Allah yasa kaffara ne amma ana ta Ibada Allah ya bamu sa'a kawai." aka amsa mata da Amin Shi kuma Abi sai ya yi mirmishi kafin ya ce" Honey kyaleni kawai nafi jin daɗin kwanciya in na zauna sai kuguna ya rika min zafi zafi wani lokacin.' Sulaiman ya kariso yana faɗin "Abi to ai saboda kana jimawa a kwance ne, yawan zaman zai rage lanƙwashewar da jikin ka ya yi a waje ɗaya" Kwallah suka cika kwarmin Idanuwan Abi ya yi saurin shanyewa yana faɗin"Ku kyaleni kawai, na fi jin daɗin kwanciyar fiye da zama."   Yadda ya yi mganar ne ya sa sai jikin Kowa ya yi sanyi, Hajiya ta yi tagumi kafin kuma ta fara sharan ƙwallah tana faɗin "Lafiya lau kabiru ya bar wajena ina saka masa albarka, sai ganin Hamza nayi yazo cikin ɗimuwa ya na faɗa min Kabiru sun samu hatsari a hanyarsu ta komawa Habuja, Allah ya jiƙan Mallan Sale ina ganin fuskarsa a cikin Idanuwana har yau wlh." Sai ɗakin ya dauki shuru aka koma Jimami, Abi kuma hawaye suke ziraro mai ta gefen kunnuwansa duka biyu Mommy ke saka tissue tana share masa, Mimi ta sauke wayar hannunta ta na sauke numfashi hankalinta duk ya tashi, in ta kalli Abi sai ta ji ta kara tsoron rayuwa gabaɗaya ba Abin da ta sani a baya ba ne jajirtacce namiji wannan Abin a kwance yake yana kokuwa da kaddaran Ubangijinsa.   Sai da Hajiya ta dai na kukan sannan Abi shima ya dai na. Shigowar Sisto Khadi ya sa sai a ka shiga wata hirar na dabam, Jawahir kuma taja ƴayant azuwa Kitchen suna kukan yunwa suke ji, ita kuma Mimi sai ta koma kan wayarta tana karanta sakon Baby Rukayya. "Don Allah ko sunan shi ki faɗa min Mimi ta"   Charting suke yi tana ta mata magiyan sai ta faɗa mata sunan wanda ta ji yaddiko da Hajiya na mgana ita kuma ta ce mata wannan wani abu ne da ya shuɗe bukatar taso da mganar da ba ta da amfani. A wajen aiki ma haka Rukky ta rika yi mata magiyan wai sai ta ba ta labarin shi ko wannan mutumin waye shi da Mimi ta kasa mantawa da shi. Ita kuma Mimi ta ce ta bar damunta da wannan mganar, abu ya riga ya wuce ba amfanin ta da maganar yanzu. "Sunan shi Hayatu.."   Sai ta fara yar dariya saboda yadda Rukky ta turo mata emojin kuka da damuwa, saboda Hayatu sunan saurayin Rukayya ne da suka rabu shi ya sa ta mata shakiyanci. Tana cikin Mirmishi taji Hajiya na faɗin"Hamza fa ya matsa kan mganar Jaheed da Binta, yaddiko ma ta yi min ƙorafin tunda shi Jaheed ɗin na sonta mai zai hana ayi yar gida? Mimi ta tsaya cak da abin da take yi tana kallon Hajiya cikin mamaki. Har sau nawa za ta faɗa mata bata son Jaheed amma Hajiya ba za ta fahimci yaren ba kenan "Mimin ta amimce da shi ne yanzu Hajiya?   Mommy ta katse Hajiya da wannan tambayar Sulaiman ma ya ce"Matsalan har shi Jaheed din ba ka gane in da ya dosa ne." Mommy ta ce"To nima shi na gani mai so ai shi ya ke nema ko Hajiya? Khadija da ta fi kama da Mommy ta gyara zama tana faɗin "Mommy

Chapter 5 of 26