nan ya fara samun ssalin sunansa na *AJI*
******
*SATURDAY, 28 APRIL 2022*
8:50PM.
A cikin anguwan Dubai Quaters Usman makama ya kama gidansa mai kyau anan aka saka Amarya.
Tun 7:30pm na yamma aka kawo Amarya gidanta saboda yanayin tsaro, daga nan Amarya da gayyarta za su wuce wajen dinner da abokan Ango suka haɗa. Acikin motocin da suka kwaso Amarya da tawagarta har da motar Aji amman ba shi ya ja motar ba Ahmad ne domin shi ya ce ba zai je ba, Nasir ya ce ya ara masa ya ce bazai ba shi ba sai da ya ba ma Ahmad aro.
Nasir ɗin yana da mota saida ita ya yi daga baya, ana ɗaura aure Aji ya zille musu ko hotunan da aka je gidan Amarya aka yi bai je ba gida ya koma ya kwanta ya juta abun sa.
Sun je dai Reception suka ci abinci daga nan ya hau mashin ya koma gida tunda daman key ɗin motarsa na wajen Ahmad. Dinner dai sun ce ko ya so ko bai so ba sai ya je, ga shi ya yi musu tsiya bai sanya kalan kayansu ba wani farin yadi ya saka mai shara shara. Wai shi ba yaro ba ne ko mace da zai saka anko.
Hakanan suka kyale shi, ya saka nashi dabam a wajen ɗaurin auran ma dakyar ya bari suka yi hoto cewa ya yi wai hoto na yara ne, komai sai ya ce ba aji aikin yara ne.
Sun je gidan su Amarya sun sha hotuna, Mu'azzam ya so ya ga yayar Amaryan da Nasir ya ba su labarin ta kankame komai a sha'anin bikin, sai Makama ya ce Bibi ta ce Anty Baby ta je karɓo ɗinki ita da kawarta Anty Mimi.
Kuma har suka gama hotuna su ka tafi ba su dawo ba, suna tafiya sai ga su sun dawo tella ne ya yi musu tsiya.
Mimi sai masifa ta ke yi tana cewa "Rukky ke kika ja mana da kin bari na kai ma tela na da tuni ya ɗin ka mana."
Rukky ta ce"Ina na san haka Habu zai yi mana ,ai ya ci taliyan karshe."
Ko makeup ba su samu yi ba mazan ma'aikansu daga karamchi Talabijin da suka zo musu ɗaurin aure ma ba su haɗu ba sai dai suka yi ma Rukky fatan alheri ta waya. Matan ne kaɗai suka samu tunda su sun jira su, saboda bakin ne yasa ba su samu zuwa kwalliya ba Rukky ta ce su bari anjuma su yi na dinner.
Tun Safe Mimi ta baro gida sai da za'a kai Amarya ta ɗauki Rukky a motar ta suka koma gida ta ɗauki jaka da takalmin da za ta yi amfani dashi tare da ɗan kunne da sarka suka tafi wajen kwalliya daga can za su wuce dinner.
Hajiya ta ga yadda Mimi ta yi kyau cikin Atamfar yinin biki saboda ajikin Atamfar akwai ja, a cikin ranta addu'a take yi mata Allah ya haɗata da wanda zai sauya mata rayuwa a daren nan.
Baaba Uwani kuwa har hqraban gidan ta raka su tana faɗin" Binta Allah ya tsare ya sa a dawo lafiya, Rukkaya Allah yasa a watse taro lafiya." Suka amsa mata da Amin, sun je shagon kwalliyan daman sun yi booking, Rukky aka fa ra yi mawa.Wacce za ta yi ma Amarya gida suka tura ta. Sai kira Bibi take yi ta na faɗin an gama mata kwalliya ta shirya suna jiran angwaye ne yanzu za su tafi can in da za'ayi Dinner ɗin.
Da za su jira sune, Mimi ta ga yanzu ma aka fara mata nata kwalliyar sai ta ce kawai su tafi in sun gama sai su zo daga baya.
Haka aka yi Amarya Bibi da tawagan ƙawayenta da ƴan'uwa suka yi gaba su Nasir suka zo da motoci suka kwashe su.
Sai wani Hall haɗaɗɗe mai kyau wanda, ya ke tashe a garin Gombe wajen yin bukukuwa. Ko da suka je an gama tsara komai daman kuma sai da Ango ya jira zuwan Amarya sannan tare da ƙawaye da abokan ango suka shiga wajen.
Wajejen goma na dare aka fara gudanar da Dinner ɗin Amarya ta yi shigan Blue ne shima Angon kalar shaddar jikinsa kenan.
Ƙawaye kuma Less ɗin su mai ruwan ash ne da zanen pick, sun yi ɗinkin fitted gown gabadaya sai suka yi amfani da head pick.
Makama ya tambayi Bibi da cewa shi fa yau kwata kwata bai ga Anty Rukky ba
Bibi na danna wayarta ta ce"Suna wajen kwalliya ita da Anty Mimi su nake kira ma yanzu."
Makama ya ya fito Ahamd da hannu yana faɗin " Nima wani abokin mu muke jira, bai zo har yanzu."
Bibi ta kalle shi kafin ta ce" Wai wannan ɗan ƙwallon da kake ba ni labarinsa,?
Sai ya gyaɗa mata kai dai dai karisowan Ahmad yana faɗin" Ango ya aka yi ne?
Makama ya duba agogon fatan hannun shi yana fadin" Aji ba zai zo ba ko?
Ahmad ya ce" Mu'azzam ya je ya ɗauko sa, na kirasa ya ce suna hanya."
Makama ya sauke Nunfashi kafin ya ce" Allah ya ɗorani akan sa kenan ya ga dama zai zo." Ahmad na dariya ya ce"Gaskiya ka ci babbar sa'a."
Ita Bibi rabin hankalinta na kan wayanta sai ji suka yi tana faɗin"Anty Mimi ku yi sauri an fara fa tun ɗazu"
Sai da ta gama wayar ne angonta ya ga duk ta bata rai sai ya ramkwafa ya na lallashinta.
Aji da Mu'azzam sun shigo hall ɗin Sha ɗaya dai dai na dare.
Aji na sanye da wata ɗanyan shadda mai Ruwan ƙasa shi ya na son abu mai ruwan ƙasa da bakin abu da kuma fari.
Hulan kansa dara ce baka, gefe da gefe gashinsa kansa da ya tara ya samu wajen zama a gefe da gefen hulan kansa, kafarsa kuma baƙin takalmi mai rufi na gata mai kyau agogon hannunsa ma baƙi ne na fata.
Suna shigowa Nasir ya je ya yi ma Mc raɗa sai hall ya kaure da muryan Mc da ya ratsa ya shiga kunnuwan mutane da faɗin.
"Kai jama'a ashe dai yau kila sai na tafi gida da kujeran hajji, bikin na masu ƙasa ne yanzu na ke samun ,labarin Aji jiharmu Captain ɗin kwallon kafa na kungiyar Gombe United matashi nan mai tashe MANSOOR AJI aminin Ango ne kuma ya shigo wannan Katafaren ɗakin taro domin taya wannan Ango mai kunya da Amaryarsa mai kyau murnan zamowa ma'aurata kai jama'a don Allah a yi tafi masu garin ne suka shigo." Sai tafi taf raf! Sannan kallo tuni ya koma wajen Aji da Mu'azzaam shi yasan suna shirya wani abu tunda suka matsa masa sai ya zo, Mu'azzam ya rakasa har wajen zaman su shi da Ahmad da Nasir dai dai Mc na kara faɗin" kai jama'a yau dai gani ga Aji matashin da kaf garin gombe ba wanda ya kaisa iya taka leda ni a nuna min Aji in kai gaisuwa nima ina cikin masoyansa"
Nasir ya nuna Aji Mc ya zo ya duka ya kwashi gaisuwa yana faɗin " Gari naku ƙasa ma naku sannu da zuwa ɗan ɓaiwa kuma wallah ya ci sunan shi akwai Aji ga shi nan ya bayyana kansa."
Hall ya ɗauki Ihu, yan mata sai waige suke suna kallon shi ,Aji ya yi tsam ko dariya bai yi ba ya na kallon Nasir ga shi duk kallo ya koma kanshi. Bibi na hightable ita da Angonta ta kalle shi tana faɗin" Wanne ne abokin naka ɗan kwallon?
Sai ya gyaɗa mata kai lokaci ɗaya yana Faɗin"Mansoor Aji ba."
Sai ta jinjina kai kafin tace"Ya ci sunan shi Aji domin tunda ya shigo wajen bai yi dariya ba." Dariya ya yi mata kafin ya ce"Haka yake shi" Mc dai ya nace sai zuba kirari yake yi karshe dai mu'azzam aka bari da yi ma Mc likin yan dubi faɗi yake yi" Allahu Akbar an ce ƙanin Aji ne da wannan ban girman, ni fa yau na zo bikin masu jihar da kansu."
Aji duk ya ji ya takura saboda ƙaran Speeker sun kusa kashe masa dodon kunne, sai kawai ya karɓi ɗin key motar Mu'azzam lokacin ana kokarin fara ciye ciye, ya mike yana faɗin "Zan je gida, hayaniya ya yi yawa a nan."
Kafin ma su samu zarafin mgana ya kama hanyar fita daga hall ɗin.
Daidai Rukky sun sawo kai ciki ita ce a gaba ta sha kwalliya ta juya baya ta na yi ma Mimi mgana ba ta ga Aji ba. Shi kuma daman yana da tafiya Sassarfa da gaf gaf sai ya yi ƙokarin kauce mata bai san da wata a bayanta ba yana kauce mata sai ya saka kanshi da niyar fita daga wajen sa ji ya yi wani abu kamar mai nauyi ya daki Kirjinsa.
Ƙamshin turarenta mai sanyaya zuciya ya fara yi ma hancinsa maraba
Tsayawa ya yi cak ya na tunanin abin da Ya tokare shi haka, ita ma Rukky sai ta juyo jin shuru sai ta hangi bayan wani dogon mutum baƙi da sauri ta dawo daga baya ta na faɗin"Mimi are u ok?
Ta faɗa ta na kallon Mimi dake faman sosa goshinta.
Ashe kanta ne ya bugi kirjinsa, tana faman gyara hannun doguwar rigarta tunda mai wani zalo zalon igiya ya yi musu ɗayan kuma jakarta ne da wayarta.
Ta ɗago ta na kallon Rukky kafin ta ce"Am fine Rukky Allah yasa ban faɗi ba."
Rukky ta kalli Aji sai ta ga ya ƙurama Mimi ido idanuwansa sun kankance yana sakin huci kamar zai kai mata duka sai ta yi saurin riko hannun Mimi tana faɗin"Ka yi hakuri ba ta ganka ba ne"
Ko kallon Rukky bai yi ba sai kawai ya kauda kansa ya raɓa ta gefen Mimi zai wuce. Yanayin bugun zuciyarta ta ji ya sauya lokaci ɗaya da ya sa ta kalli mutumin da suka ci karo ya riga ya gifta ta.
Amman ai ta ga gefen fuskarsa sannan ta juya da sauri ta ga bayanshi da yanayin tsawon shi. Tabbas soyayya ba karya ba ce, yau Aji ta gani wlh shi ne ta gani.
Aji ne ajinta ne MANSOOR AJIN Mimi.
Ba ta san lokacin da ta kwace hannunta a na Rukky ba, yana shirin fita daga ɗakin taro ta yi amfani da muryanta mai zaƙi ta kira sunan shi.
"Aji...!
Bai Tsaya ba da karfi ta buɗe murya ta kara kiran sunan shi da sunan da take kiran shi a baya.
"Aji Nah...!!.
"Ajin Mimi..!"
Cak ya tsaya saboda ji ya yi kafafunsa sun kasa cigaba da tafiya duk ko kokarinsa na ya bar wajen kada ta fahimci shine, alokacin hankalinsu Mu'azzan ya kai wajen Bibi ta ga yayarta acan kofar shigowa tana tsaye ga Mimi a tsaye ga abokin su Usman, ko kafin kace me ta baro wajen zamanta ta sauko tana faɗin "Anty Baby me ya faru?
Suma sun Mu'azzam sun taso sun rufa mata baya Ango ma ya Biyo amaryansa Mc na ganin haka ya tsaida sauti shima yana raba ido sauran ƙawayen Amarya da abokan Ango suka bi bayan ayarin masu kallo suma da tamtaman abin da ya faru.
Muryanta da ya ji sai ya ƙara samun tabbacin ita ce, kawai sai ya yunkura da doguwar kafarsa ya taka zai bar cikin hall din, Mimi na ganin haka ta tattare rigarta bayan ta wancakalar da takalmin kafarta mai tsini da jakar hannunta tare da wayarta ta rufa masa baya. Baki buɗe aka bi ta da kallo Rukky ta kwashi gudu ta bi ta tana kiran sunanta ƴan Dinner na ganin haka suka rufa musu baya.
Sunan da Rukky ke kirana ne ya sa Mu'azzam da Nasir suka kalli juna.
"Mimi.."
Ahmad shima ya maimaita sunan
"Mimi."
Makama ya riko Amaryansa dake shirin bin bayan Yayarta yana faɗin"Mimin mai aikin gidan tibi?
Bibi tace"E, itace ƙawar Anty Baby ce."
Ai sai makama ya ji ya fara zufa Bibi tabi bayan Yayarta shi kuma ya yi saurin bin bayan su Nasir yana faɗin" Yau fa an haɗe Mimi ce da gaske MIMIN AJI ce."
A tare suka rumtuma zuwa waje domin ganin abinda ke faruwa, suna fita suka hangi Aji tsaye a haraban wajen Mimi ta sha gabansa sun ƙura ma juna ido.
Akwai hasken farin gulop tar ga shi nan ana ganin komai kamar a magiji.
Shi ya juya baya ba'a ganin fuskar shi ita da ke facing ɗin shi ake iya gani.
Hawaye suna sintiri a saman kyakyawan fuskarta da ta sha kwalliya.
Nasir da Mu'azzam suka kalli juna Ahmad da Makama ma suka kalli juna.
A tare suka furta" inna lillahi wa'inna Ilaihirraju'un.."
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT
SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA
MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA
HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU
INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM
INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI
INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL
INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/JMpd8nXr7TIDD3ILDXh64z
*Page 9*
Gani Mimi take yi kamar a mafarki yau ita ce a gaban Aji tana kallon shi yana kallonta, Yau ita ce ga ta ga shi wanda tazaran dake tsakaninsu bai wuce taku biyu ba, sannan yau ita ce ta ke fitar da numfasshi tare da jin ɗumin numfashin Mansoor a cikin nata numfashin. Farinciki ne ya saka ta kuka yau kimanin shekaru goma rabon da ta saka shi a idanuwanta irin haka. Sai dai ta hangoshi a hoto daman ya ce ta yi nisa da ganinsa shima zai yi nesa da jin ta da ganinta na har abada. Daɗi ne ya cika mata zuciya da ya sa har ta kasa iya rike kanta sai kuka hawaye suna ta faman sintiti saman kyakyawan fuskarta da ta sha kwalliya mai kayatarwa.
Shi kuma so yake yi ya hana idanuwansa kallonta amman sun ƙi bashi haɗin kai kamar an manne masa idanuwansa daga kallon Mimi, ga shi kuma kishi ne da wani irin bakinciki ke yunkuro maasa, in da ya binne tasirin soyayyarta ke kokarin taso masa ya hana tasirin haka bayyana, acikin kirjinsa ya ke jin wani irin zafi zafi iskar wajen ta fara masa kaɗan domin ya ji hucin zafin na fita daga cikin wuyansa zuwa cikin bakinsa, jiyoyin kansa sun mike raɗau kirjinsa na sama da kasa alamun bacin ransa da yanayin da ya ke ciki ya kai makuran kololiya. Bakinsa ya yi wani irin nauyin da ya kasa mgana duk a kokarinsa ya cira kafarsa da sauri ya bar wajen tun kafin Siirin da ke cikin zuciyarsa a kulle a wani bangaren ya fallasa kansa.
Yana ƙokarin dauke kafarsa daga gabanta ya raɓa ta gefenta ya wuce ya ji maganarta cikin zaƙin muryanta da tun asali wannan muryan ce ke kwantar masa da hankali. Sannan ganin mai murya na saka shi cikin farincikin da bai san iyaka ba, amman sanadin abin da ya faru yanzu jin zaƙin muryan yake yi kamar saukar dalma acikin zuciyarsa sannan ganinta na sanya sa bakinciki yana guje ma ganinta ne kamar mutuwarsa.
"Aji Nah.."
Ta ƙara kiransa cikin rawan murya sai kawai ya yi kamar bai ji ya ba, ɗaga kafarsa da sauri zai wuceta ita kuma da azama ta riko gefen hannun rigansa domin ba za ta taɓa bari ya subuce ma ganinta ba, yadda ta rikesa ne ya sa ya tsaya ya na bin hannunta zara zara da yaji kunshi baki da ja da kallo rike da gefen hannun rigansa na hagu sannan ya sauke saman fuskarta kallon da ya yi mata ne ya sa dole ta sake shi wasu hawayen na kara yi mata ambaliya a saman fuskarta. Tana sakin shi ya fara takunsa cikin sassarfa da gifi gif ɗin sa kamar wani Sadauki a fagen yaƙi jii yake yi in bai bar shakan numfashi tare da wannan yarinyar ba za a iya samun matsala.
Kuma cikin su Mu'azzam an rasa mai karisowa kowa ya harɗe hannu a kirji yana kallon ikon Allah. Hatta Rukkaya dake gefe ta kasa karisawa, Tsabar mamaki da Al'ajabi ya hana ta magana ballantana ta karisa wajen tambayoyi biyu ne acikin ranta.
" A ina Mimi ta san wannan baƙin mutumin mai bakin rai haka?
"Me ya sa take kuka saboda ta gan shi?
Wata zuciyar daga can gefen ta gaya mata" ko dai ko dai shi ne?
Shi ne wannan ɗin?
Sai ta kara kallonsu ta na Nazarin wani abu dai dai lokacin da Mimi ta kara tattare riganta ta sha gaban Aji a karo na biyu, wannan karon da karfinta ta tare masa gabansa ta kuma saka hannayenta guda biyu ta tare hanyar tana faɗi da ƙarfi.
"Ba zaka bar nan wajen ba har sai ka yi min mgana, ni ce Mimin ka fa Mansoor?.
Ta faɗa kuka na son ƙwace mata, Mimin ka ce? Kalmar ta fi ɓata masa rai da ya sa a fusace ya kalleta cikin kakkausan murya ya ce"Ni na san ki ne? Kin sanni ne?
Ya faɗa yana nuna kansa. Jikin Mimi ya fara rawa, ta fara nuna kanta ta na rawan baki ta ce" Ni ce fa? ba ka gane ni ba ne?
Kai tsaye ya ce"Ba maganar ganewa ba ne, ban san ki ba, ban kuma taɓa ganinki ba kar ki kara ganina ko a hanya irin haka ki ce kin sanni in ba haka ba zan saka rayuwarki a uku, ni kin ga na yi miki kama da sakaran namijin da ya san shashashan mata irin ku? Iyayena talakawa ne har yanzu muna lallaɓa rayuwarmu ne a inda Allah ya ijyemu ba zamu faɗa inda ya fi karfin mu ba."
Ya ƙarishe faɗa ya na nuna ta da babban yatsan dake hannunsa zuwa lokacin tuni su Rukkaya sun ɗumgume wajen dai dai lokacin da Mimi ta fashe da kuka tana faɗin"Ko ba domin soyayyarmu ba, na ci arzikin kaunar da ta haɗamu ka tsaya mu yi gaisuwan mutumci Aji."
Kamar ta yarfa masa ruwan zafi haka ya saka jannu da karfi ya ture hannunta cikin tsautsayi ta yi gefe har sai da ta faɗi bai juyo ba cikin ɗaga murya ya ce" Har Abada babu sauran mutumcin da ya rage tsakanina da ke Fatima Kabir Sulaiman Dabo, har Abada kuwa saboda haka kar ma ki yaudari kanki." Daga haka ya taka jelan riganta zai wuce ita kuma ta yunkura da niyar tashi kawai sai ji ka ke keeeeee!
Rigar jikinta ta yage ta wajen kugunta da aka saka raga raga a wajen saboda ya taka ita kuma taja sai ya yage ana ganin kaurin cikinta a waje.
Ya ji karan yagan abu sai ya ɗan juya kaɗan yaga kaurin cikinta a waje wani irin hayaki yaji kamar idanuwansa na fita na zafin kishi, yanzu maza nawa ne a wannan wajen? In suka kalle mata jiki fa?
Kawai sai yaji kamar ya mutu.
Ita kuma Mimi kuka ta fashe da shi cikin raunin murya take faɗin "Don Allah don Allah Mansoor."
Rukkaya ce ta ƙariso wajenta da gudu ta riketa ranta ya baci cikin masifa ta ce"Mimi me ye haka? Ta ya ya za ki
zauna wani wanda bai isa ba yana wulakanta ki haka?.
Ya ji ta saboda har ya fara takawa zuwa wajen Motar Mu'azzam sai kuma ya fasa ya dawo da zafin namansa lokacin Rukkaya da wata kawar Bibi sun tada Mimi tsaye sai ya ga ana ganin jikinta, tuni idanuwansa suka rufe yana tafiya kamar ya ji ya tashi sama.
Tsabar kishi da ya rufe masa ido yasa bai san lokacin da ya daka mata wani irin tsawa ba.
"Ki tsaya anan kar kuskura ki ƙara taku ko ɗaya FATIMA.."
Ya kirata da sunanta da ba kowa ke kiranta da shi ba. Jikinta na rawa ta juya ta lna kallonsa kowa kuma sai ya koma yana kallonsa baki sake hatta ko su Mu'azzam Nasir har sai da ya Murmusa shi fa daman yasan har gobe Aji bai daina son Mimi ba, kuma a kishinta kamar mahaukaci haka ya ke jin kansa. Wajensu ya nuna yana zuwa ya cilla ma Mu'azzam key ɗin motarsa ya caɓe da sauri, shi kuma sai ya mika ma Ahmad hannunsa da sauri ya ɗora masa key ɗin motarsa ya juya kamar wani namijin zaki ya wuce wajen motarsa shi duk saurinsa kar Mimi ta juya baya wajen maza su ga jikinta in hakan ta faru ai sai ya kusa mutuwa saboda bakinciki.
Rukkaya kuma haushi wannan mulkin mallakan ya kamata a fusace ta ce"Dilla mu tafi yanzu ya gama wulakantaki sai kuma ya dawo ya na ba ki umarni? waye shi ɗin?
Mimi na hawaye ga kuka cikin sauri ta ce"Umarninsa kamar dole ne a gare ni na bi Rukkayya"
Rukky ta saki baki galala tana kallon Mimi dai lokacin da Aji ya dawo da wata bakar Jaket baka tana da tsawo nashi ne ta jima acikin motarsa ashe zata yi masa amfani.
A gif gif ɗin sa ya dawo gabansu ya saita rigan ya saka a jikin Mimi bai samu salama ba sai da ya ga jaket ɗin ta sauko har ta rufe in da ya yagen sannan ya sakar mata rigan.
Bai kalleta ba duk kuwa nacin kallon da take yi masa , ga hawaye a saman fuskanta lokaci ɗaya da wani irin mirmishin da ta jima ba ta yi kamar sa ba.
Kamar walkiya ya bar wajen har ya shiga motarsa Rukkaya ta saka hannu za ta warce rigan jikin Mimi tana fadin"Ba za ki saka ba, ya damu da ke ya ture ki, ki ka faɗi a gaban jama'u? Gam ko Mimi ta rike rigan idanuwanta da hankalinta na kan Aji da ya shiga cikin mota. Duk da motar baƙin gilasai ne jikinta na ba ta ita yake kallo, kamkame rigar tayi cikin Mirmishin dake tafe da hawaye Ta ce"Ki bar min Rukky a kallah bayan tsawon shekaru na kara samun tabbacin matsayina bai sauya ba, yana sona har gobe tunda bai daina kishin wasu mazan su ga jikina a buɗe ba"
Rukky ta bi ta da kallo kamar mai taɓin
hankali sakinta ta yi ta so ne ta isa wajen motarsa ta zage shi sai dai kafin ta karisa ya fige motar da gudu ya fice daga haraban wajen Rukky ta ɗaga murya tana fadi'n"Ɗan wulakanci kawai, za ka haɗu da dai dai da kai a gaba kana baƙin mutum sai faɗin rai da nuna isa aikin banza kawai.".
Ranta ya baci ganin gabaɗaya ya ɓata musu biki ta na juyawa ta nufi wajen su Usman da kamar an da sa su. Bibi kuma da sauran ƙawayenta sun rufe Mimi suna yi mata sannu.
Cikin masifa Rukky ta ce" Usman wannan wani ɗan wulaƙanci ne? A gaban ku ya ci zarafin ƙawata waye shi?
Kai tsaye Nasir ya ce"Aji.. MANSOOR IBRAHIM AJI. Gombe State United Captain"
A fusace ta wurga ma Nasir harara kafin ta ce"Aikin banza shi ne me? don yana ɗan ƙwallo sai ya yi mata wannan tozarcin wallahi ya ci sa'a ya bar wajen nan da sai ya raina kansa wlh."
Nasir ya ba ta amsa kai tsaye da cewa" Sai dai ki raina kanki, ke ba ki ga abin da ya yi ma ita ƙawar taki ba ne,?
Rukky za ta kara mgana Usman ya tare ta da faɗin"Ki yi hakuri Anty Baby ko an yi miki bayani ba za ki gane ba. Aji abokina ne tare mu ka tashi dukkanmu nan tare muke wannan kuma da kike gani ƙaninsa ne Mu'azzam" Ya faɗa ya na nuna mata Mu'azzam wanda ya yi shuru kamar ruwa ya cisa. Cikin ƙufuluwa Rukky ta kallesa kafin ta ce" Miye haɗin ɗan'uwanka da ƙawata da zai mata wannan wulakanci.?
Sai ya kasa ba ta amsa Nasir ne ya ce" Alaƙace mai karfi a tsakaninsu ke ba ki gane haka ba? To
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 26