Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ke a tsakiyar falon sa, a saman cafet ya y filo da hannayensa idanuwansa suna Rufe ne amman yana fuskantar POP ɗn da ke falon. Bashi da riga daga shi sai ƙaramin wando sannan babu nepa falon ya yi duhu Tunani yake yi, tunani mai zurfi kamar a lokacin haka ya ke ji amon kukanta na shiga ransa, shi ya yi mata tsawa ya saka ta kuka amman ba ta kaishi shiga bakinciki ba. Allah kaɗai ne ya kaisa in da za shi lafiya a ranar yana tuna kukan da take yi da yadda ya ture ta.   Saboda haka a daran ranar kusan kwana ya yi ya na gudu a studio sai da ya ji ya gajiyar da kanshi sannan ya sarara. Muskutawa ya yi ya juya zuwa da jikinsa bangaren dama. _Ya sunan ka?_ _Ni? Ke ya sunan ki?_ _Ni sunana Mimi Mimin Abi_ Ya tuna mirmishinta da dariyanta tun alokacin sai da kumatunta suka loɓa,  ba zai manta amsar da ya ba ta alokaci ba _Sunana Mansoor Aji."_ _"Aji ?_ Ta faɗa da sigan tambaya alokacin sai da ya yi dariya kafin ya yi magana ta yi zaraf ta ce. _To wajen wa ka zo?. Wajen Hajiya? _A'a ni wajen Innata na zo_ _"Inna Mari mai girkin Hajiya?_ Dariya ya yi alokacin kafin yac e"Eh ita, ai innata ce." Baki ta buɗe tana yar dariya har kayan jikinta bai manta kalansu ba, a lokacin iyakarta shekaru sha shidda kuma wannan shine gani na biyu da ya yi mata kuma maganar su ta farko shi da ita..! Me ya sa ya kasa mantawa da ita? Me ya sa ya kasa mantawa da duk abinda ya shafe ta? "Saboda har yau kana sonta Mansoor."   Amsar da wata zuciyarsa ta bashi kenan. Da gaske yama sonta? To me ya sa zai cigaba da sonta ahalin akwai bambanci mai tarin yawa a tsakaninsu?. Kaddara ba ta haɗa su domin su zauna waje ɗaya ba, ita kaddaran da kanta ta raba tsakanin su. *BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.* *09069067488* *80032773332* *Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar* *09069067488* *NA GODE.* *Janafty* Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI 08066726866 *Page 11* A Jihar Gombe a kafatanin manyan unguwannin da suka zagaye anguwan Arawa da ma nesa da anguwan da kuma waɗanda ke gabas zuwa yamman da su ba wanda bai san da zaman gidan marigayi salihu wanzam ba, wanzancin gidan ba haye ba ne gadon shi suka yi, abun sai yake bin jini, in uba ya gada sai ya gadar ma ɗa, ɗa ya gadar ma jika jika ya gadar ma jikan jikan to a haka tushe da asali gidan Wanzamai ya fara. Inna Mari ta tsinci kanta da aure a gidan wanzamai mai cike da tsohon tarihi tun bayan rasuwar mijinta na farko, Inna Meri mai suna Maryama ba'arata daga shiyar kasar gida ta Argugun ta fito daga cikin wani yanki na garin Argugun ne, kuma duka danginta da ahalinta arawane sai dai mahaifinta ya rasu sai ta tashi tare da mahaifiyarta wacce a ke kira Inno soro. Mallam Ibrahim sufi mutumin kwami ne karamar hukumar dake jihar Gombe a arewa maso gabashin Nageria. Mazaunin hedikwatan mallam Sidi dake garin kwami. Kuma ya kasance manomi ne kuma mai sana'ar kamun kifi, tunda mutanen garin Mallam Sidi sun fi karfi a noma da sana'ar kifi tunda suna da ruwa sosai a garin. A dalilin sana'arsa ta kifi ya sanya yake da mu'amalan arziki da mutanen argugun kuma yana zuwa garin sosai ta sanadin wannan mu'amalan Allah ya haɗa auran mallam Ibrahim da meri wato Maryama. Ta baro garinsu shiyar Argugun zuwa garin mallam Sidi yan'uwan Ibrahim suka zame ma Meri uwa da uba da dangi gabaɗaya. Uwa uba kuma mijinta na sonta kuma ya na tattalinta sannan ita kanta Meri mace ce mai alheri da maida kowa nata shi ya sa ta kasance a bar son kowa suka riketa kamar ƴar su, duk da shima ba shi da iyaye amman yana da kanne da yan'uwa. Duka duka auransu bai kai shekaru biyu ba ta haihu ta samu ɗa namiji sai aka sanya ma sa sunan mahaifin Meri wato Mansoor, shi ne silan da Meri take kiran Mansoor da suna Baban Inna, a farkon rayuwarta ba ta taɓa tunanin wata rana mutuwa za ta yi sanadin rabata da wannan rayuwar da take ciki ba, ta zama yar garin mallam Sidi sai dai in ta je gida ziyara da ganin ƴan'uwa kowa sha'awarta yake yi ganin ta kowani Fanni ta samu jin daɗin rayuwar da kowacce mace take fatan ta samu. Sai dai kash ita mutuwa ba ruwanta da jin daɗi  da zaran lokacin ka ya yi sai ka tafi. Mansoor na da shekara biyar a duniya Mallam Ibrahim ya rasu sakamakon kayar kifi da ta makale masa ya yi ta amai dare zuwa safe an yi an gama, Meri ta yi kuka kamar ranta zai fita ba abin da ke kara saka ta kuka sai in ta ɗaga ido ta kalli Mansoor mai kuruciya da kananun shekaru da bai san komai na rayuwa ba har ya zama maraya, yan'uwanta sun zo har akayi bakwai sannan Inno soro ta zauna tare da ita har akayi arba'in ta so ta tafi da Meri can gabanta ta ida sa takabanta sai ƴan'uwan Ibrahim suka hana suna kuka suna rokon Inno soro ka lda ta raba su da Meri da  Mansoor su kaɗai suke gani su tuna da ɗan uwansu Ibrahimu. Sai inno soro ta tausaya musu kuma ganin ba abin da Merin ta nema ta rasa sai ta bar ta a nan ta koma argugun, Allahu akbar Allah mai tsara komai yadda ya so a hanyarta ta komawa gida har ta sauka a garin argugun ta samu a kori kuran dake ɗaukan mutane zuwa cikin kauyakun su to anan ajalinta ya sauka suka samu hatsari nan take Allah ya yi ma Inno soro rasuwa Meri ta yi kamar ta haukace ga rasuwar miji ga ta uwa abun sai ya yi mata yawa dole ta shirya ita da Mansoor da Yalwar kanwar Ibrahim suka tafi can har aka yi bakwai da farko Meri ta so ta yi zamanta a garinsu ne sai 6an'wan ibrahim suka ce ko bayan kasa ya shafe idanuwan Ibrahim ba za su bari Iyalansa su rasa mafaka ba, da roko da ban baki kawun Meri mai suna Surajo ya amince ya ba su Meri da ɗanta Mansoor suka dawo garin Mallam Sidi da zama a kuma cikin dakin mijinta suka riketa ita da ɗanta. Bayan ta fita takaba saboda halin rayuwa duk da suna kokari a kanta ba za ta ce ta zauna a haka ba. Sai ta fara sana'ar cikin gida saboda dogara da kai ba domin yan'uwan Ibrahim ba su barta ta neme wani abu ta rasa ba amman ai ba zaka zama a kwance komai sai an dauka an baka ba a kallah dai kai ma a ga kana wani abun domin taimakawa. Ta zauna da su na tsawon shekara ɗaya har Mansoor ya fara makaranta fimari anan cikin garin Mallam Sidi. Tun tana garin Mallam Sidi a ke kiranta da Inna Meri, saboda ita Innar kowa ne yara da manya kowa nata ne kyauta da Alherinta ya sa ta ke zaune da kowa lafiya Mansoor kuma ya na ganin gata saboda su na ji da shi suna kallonsa kamar makwafin ɗan uwansu Ibrahimu ne, tun Mansoor  ya na ƙaraminsa Inna Meri ta fahimci cewa ya na da bakar zuciya da kafiya ga naci ko faɗa ya haɗasu da yara sai ya yi kwanaki bai bar mganar ba, tun mahaifinsa na da rai in ta yi mgana sai ya ce zai bari yarinta ne. Ko ita ce ta dakesa sai ya kame a waje ɗaya yana huci da kumburi kamar wani mai Aljanu in za ta kara masa sai  ƴan'uwan uban su hana su a tunaninsu yarinta ne ya na girma zai daina  sannan ga shi da fitina komai shi a wajensa na fitina ne, saukinta ɗaya suna tare da masu kaunar su shi ya sa abun sai bai cika damunta sosai ba sai da kaddara ta sake jefa ta a wata rayuwar sannan ta san illar halayen Baban Inna a wani muhallin. Gaddaafi Ɗanjuma wanzan. Ya kasance wanzamin dake yin wazanci a tsakanin kauyen su na karamar hukumar kwami saboda sunan da gidan su ya yi, ya sa duk tsukin nan suna zuwa cire beli ko kaciya ko wani abu da ya shafi kuna suna ba da maganin gargajiya sai a samu dacewa. To Ɗanjuma ya kasance wanzamin gidan su Ibrahim Sufi sannan har shayi ma shi ke yi ma yaran gidan in aka haife su, Mansoor ma shi ya yi masa shayi lokacin da ya cika shekaru uku, sannan akwai abota tsakaninsa da Ibrahim tun ya na raye, ya na siyan Kifi a wajensa akwai dai mu'amala mai kyau domin hatta Inna Meri ta san shi, har bayan rasuwan Marigayi Ibrahim in ya shogi garin yana zuwa ya ganta har ya yi ma Mansoor kyauta baya dai zuwa hannun rabbana. Tun Meri ba ta fahimci akwai wani abu a zuciyar Ɗanjuma ba har su Yalwa suka fahimta  sai ba ta ɗauki abun da gaske ba, tunda ta san matansa biyu a lokacin ashe abunda ba ta sani ba ɗaya daga cikin su Allah ya yi mata rasuwa ta rasu ta bar Ƴaƴa uku mata biyu da ƙaramin yaro namiji. Kuma ta san hakane bayan Danjuma ya gama zagaye zagayensa ya fito ya sanar da Inna Meri manufarsa na son auranta domin ta taimaka ta riƙe masa yaransa duk da yanzu suna hannun dangin ita matar tashi ne, amman ya fi son shi ya rike ƴaƴansa da kansa. Bai ɓoye mata komai game da labarin matarsa ba wato uwargidansa Magajiya kenan. Fitinanniya ce mara kirki, ta yi rantsuwan ba za ta rike masa ƴaƴa ba nata sun isheta har ga Allah da farko Inna Meri ba soyayyar Ɗanjuma ya sa ta amince da auransa ba, sai illah tausayin yaran da aka mutu a ka bari tunda yace har da ƙaramin yaro dan shekaru uku da wani abu da ba ya yarda da kowa, Sai ta juya ta ga itama marayan da aka mutu aka bar mata ɗa na kowa ne ba ka san wanda zai rike  maka na ka ba watarana bayan kasa ta shafe idanuwanka ba. Ba ta yanke hukunci ba sai da ta yi shawara da yalwa ita kuma sai ta yi mgana sauran ƙannen Ibrahim wanda acikin su ashe akwai wanda ya so ya auereta sai bai furta ba ganin kamar Inna Meri ta nuna ra'ayinta a kan Ɗanjuma saboda rike marayu sai ba su hanata ba saboda in dai kyawun hali ne da hakuri da kawaici da sanin ya kamata Danjuma ya cancanta tunda sun san shi tun ya na matashinsa kuma gidansu babban gida ne mai kunshe da tarihi. Sai su ka ba ta damar ta yi zaɓi cikin guda biyu ko kanin ibrahimu mai suna Muftahu ko Ɗanjuma ita kuma sai ta bar ma Allah zaɓinsa sai taji tafi natsuwa da auran babba wanda ya mallaki hankalinsa kansa tunda a lokacin Muftahu saurayi ne bai taɓa aure ba, ƙannen nasa maza uku ne Karimu ne babba sai yakubu yalwa sai muftahu shine ƙaramin su daman Ibarahimu ne babban su. Karimu ne ya yi aure da matarsa acikin gida yalwa ma ta yi aure nan makota da su, sai yakubu da shi ba agarin yake kasuwanci ba yana garin bauchi ne kuma shi bai wani damu da zumunci ba sai ya jima bai zo garin ba. Ita kuma Inna Meri sai ta yi duba da gwara ta auri Ɗanjuma ko bakomai Allah zai ba ta ladan rike marayun da suka rasa uwa a ƙananun shekarunsu. Lokacin da ta gaya musu zaɓinta ba wanda ya nuna bai ji daɗi ba sun yi mata fatan alheri yalwa ce ma ta yi ta kuka tana faɗin za ta yi nesa da su Inna Meri tace suna tare ina nisa tsakanin garin mallam Sidi da Gombe za ta zo itama ai nan gidansu ne zata rika zuwa ta na ganinsu tana kuma kawo musu Mnsoor. Tunda akwai kyakyawan alaaqa da fahimta a tsakaninsu shi ya sa ba za su iya raba ta da Mansoor ba amma sai dai Ɗanjuma ya ba su tabbacin shima Mansoor ɗansa ne kuma yayi alkwarin yadda suka ba shi Amana to zai kula da amanar Mansoor har karshen Numfashin sa, sun kuma aminta da shi sai suka bashi Amanar Inna Meri tare da Mansoor ba daɗewa aka yi auran Inna Meri ta bar garin Mallanm Sidi tana kuka yalwa da Marliya matar karimu suna kuka sula kuma rakata har Gombe a ɗakinta na gidan Wanzamai. Tun a ranar sula san Meri ta shigo wata rayuwar da ba ta saba gani ba, ba wanda ya karɓe su a gidan nan sai Harira Magajiya kuwa sai bala'i ta ke yi tana zage zage tun a ranar farko Inna Meri ta san sai ta ninka hakurinta kuma ba ta damu ba tunda Danjuma ya gaya mata komai bai rufe ta ba, Abun bakincikin su ganin Inna Meri ta zo da yaro shikenn Magajiya ta rika sakin habaicin Ɗanjuma da kwashe kwashe ya je ya kwaso wata kuma mai ɗa ta zo musu da Agola acikin gida, kafin su Yalwa su tafi sai dai suka kara jadaddama Inna Meri hakuri da kauda kai ta ce in sha Allahu zata zauna da kowa lafiya suka rabu suna kukan sabo Mansoor kuma sai jin daɗi  yake yi a ganinsa kamar irin sun koma sabon gida ne sai da su yalwa za su tafi ya saka kukan sai ya bi su dakyar aka lallashe sa sai da Danjuma ya ja shi shago ya siya masa alawa sannan ya yi shuru amman ya yi ta kuka ya na numfaashin zuciya. Inna Meri ta shaida ta bangaran Miji ta gama dace sai dai ba za a haɗa samun Ibrahimu da na Danjuma ba acan ita kaɗai ne nan kuma ga magajiya da sauran yara to abubuwan dai sai godiyar Ubangiji kawai, sannan tun ranar farko da ta shigo gidan nan take hakuri da kowa kuma ta ko yi zaman lafiya da kowa in ka yi mata sharri sai ita ta saka maka da Alheri ba mai sonta a gidan hatta kannnen Danjuma su Ɗanlami kenan Mansoor kuma sai suka sanya masa suna Agola ba acikin gida ba har a waje shi kuma sarkin zuciya ko da yaushe cikin fada suke a dake shi kuma ya fara zuciya yana cika ya na batsewa bata mgana sai dai Danjuma duk wanda ya taɓa Mansoor sai inda ƙarfinsa ya ƙare kalamansa kenan yaron nan amana ne a wajena don Allah ku tayani kula da amanarsa. Tun daga lokacin sai suke ganin kamar ya fifita Agola sama da ƴaƴan sa na cikinsa. Tunda sanda inna Meri ta zo gidan ya'yan magajiya uku ne, Auwalu ne babba sai Jummai sai Zuwaira ashe ma alokacin tana da wani ƙaramin ciki amman cikin yara nan ba mai kallon Mansoor a komai sai a matsayin Agola, ko waje ya fita sunan da ake kiran shi kenan tunda sun gama gayama kowa shi ba ɗan gidan su ba ne Agola ne. Ko ya dawo da kuka lallashinsa Inna Meri take yi sai taga ya damu ba shi da wani ɗan uwa na kusa da shi, sai ta yi tunanin gwara ta yi ma Danjuma mgana ya dauko mata yaran marigayiya ta haɗa su da yaronta ta rike kila su su karɓesa a matsayin ɗan uwa. Yana dawowa ta yi masa mgana sai ya ce daman suna ransa ita ya ke jira kada taga kamar daga zuwanta ya takura mata  jin ita da kanta ta ke son a ɗaukosu sai ya ce ta shirya su tafi tare su taho da yaran nan, Haka ko akayi tare su ka je can Bolari gidan su Habiba inda yaran suke, Amina ce babba sai Halima sai ƙaramin yaron Mu'azzamu. Ganin kirkin Inna Meri da yadda ta nuna zata rike yaran sai Mahaifiyar Habiba ta amince ta ba su yaran tun acan gidan Mansoor ya rike hannun Mu'azzam a fuskarsa kaɗai Inna Meri ta ga ya yi farinciki, sai taji daɗi acikin ranta saboda ita macece mai son yara. Ta dauko su Amina ta rumgumesu kamar itace uwarsu ba su taɓa maraicin wani abu ba, Mu'azzam kuma ya ke ganin gata saboda karami ne shi Inna Mari ta rene shi har ta sanya masa suna wato Ɗn Inna shi kuma Mansoor tana kiran shi Baban inna. Tunda Magajiya ta ga Inna Meri na riƙe su Amina kamar ita ta haife su sai ta fara bullo da rigima yau ta ce wannan gobe ta ce wannan a irin haka ne ta tada rigima sai da aka raba girki kowacce sai ta koma yin nata saboda a zauna lafiya, Ita a tunaninta kamar Baba Ɗanjuma na cutar da ita ba ta duba da cewa Ƴan uwan Habiba na yi ma yaranta sako itama daga su Yalwa tana samun alherai ma su yawa sai take rage ma Baba Danjuma wasu hidimdimun, sai da aka raba girkin Magajiya ta gane kuranta tunda a baya da girken ke haɗe  komai Meri ta barshi a na su gabadaya da aka raba kuma sai ta ja bangarenta ita da ya'yanta. Ba ta shekara a gidan ba ta samu ciki lokacin Magajiya ta haihu an samu Namiji Saddiqu, ita kuma sai ta haifi mace aka saka mata suna Fatima suna kiranta Bintu, sai ta haɗe kan Ƴaƴanta  gabaɗya saboda ba ta nuna bambamci suma kuma yaran ba su da wata uwa da ta wuce Inna Meri. Ko can gidan kakkaninsu suka je ba su da labari sai Inna ta ma na kaza tana mana kaza sai iyayen Habiba suka samu salama da cewa su Amina sun samu wata uwar kamar Habiba sai su ma suka maida Inna Meri kamar ƴa duk wani abunda za'a yi a gidan tare da ita a ke yi sannan in yaran suka samu hutu suna zuwa can su yi musu Hutu shima Mansoor tana tura shi can wajen su yalwa ya gaishe su. Tana da cikin walida Muftahu ya rasu har ya yi aure ba jimawa ciwon ciki shima daga dare zuwa Safe, Inna Meri ta yi kuka nata mutuwan mijin kawai take tunawa, duk da shekarun sun ja amman ta kasa mantawa, sannan ga halin rayuwar da suke ciki samun Baba Ɗanjuma ya ragu ga iyalai da hidimdumu Allah ma yasa su Amina suna samun taimako daga dangin Habiba shima Mansoor daga can mallam sidi ana yi masa saƙo Yakubu dake bauchin in ya zo can kwami yana ba da saƙon kayan sawa masu kyau sai Yalwa ta aiko yaronta da shi ko kuma ita ta zo ta kawo masa da kanta. In kuma aka kawo kayan Mansoor zai ɗauki kaɗan sauran ya ba ma ƙaninsa Mu'azzam in Inna Meri ta ce sun yi masa yawa sai ya ce"In ya ƙara girma sai ya saka Inna." Tun suna kananunsa kaunar junnasu yake cikin jininsu duk da Mansoor ya girmi Mu'azzam kusan da shekaru biyu da wani abu, amman ji yake yi da shi kamar abokinsa duk abin da ya samu sai ya raba shi biyu ko uku ya ɗauki kashi ɗaya kashi biyu kuma yace na Mu'azzam ne. Kuma ya na faɗa da duk wanda yace Mu'azzam ba ƙaninsa ba ne, Saboda su Jummai suna yawan gwaba masa magana da cewa Mu'azzam ba ƙaninsa ba ne shi kuma sai ya ce" ƙanina ne saboda innata take ke rike da shi, in ƙanin ku ne me ya sa magajiya ba ta rike shi ba? Saboda fitinasarsa ya sa suke shayin masa mgana ya ga dama ka zage shi ya rama kuma ba wanda ya isa ya taɓa Mu'azzam ko a makaranta yanzu sai aga tashin hankali. Yadda ya ke kafa kafa da shi ko su Bintu da ke mace baya yi musu irin haka Baba Ɗanjuma daɗi ya ke ji in ya ga haka sai ya ce ko bayan raina Meri Mu'azzamu da Baban Inna su ne za su rike mini iyalaina. A can waje kuma bangaren abokai in kana son abota da Mansoor sai ka yi abota da Mu'azzam shi ya sa Mu'azzam ya taso ba shi da abokai sai abokan Mansoor, Mansoor ma ba shi da abokai sai abokan Mu'azzam an sha faɗa da tsiya sai an fara abota abu kaɗan zai haɗasu Mansoor ya watse abotan su Nasir ne abokan gasken da ko an yi faɗa bayan kwana biyu bayan an gama gaba za'a zo a shirya. Sannan islamiyar su ɗaya kuma boko ma duk tare suke sai abotan su ta jima sannan ko an yi tsiya bayan wani lokaci za'a haɗu ko da a filin kwallo ne, da farko Mu'azzam ne ya ke son ƙwallo Mansoor kuma shi kwallo ba ta gabanshi, Saboda Mu'azzam ya fara zuwa kallon ƙwallo har ya fara bugawa duk da shi ra'ayinsa in ya gama makaranta soja yake son zama shi kuma Mu'azzam ya ce yana son ya zama ɗan kwallon kafa. Amman a fili Aji in yana buga balla sai ya baka mamaki ya ƙware in dai ya na fili sai ya buga kwallo a raga shi yasa lamba goma yake bugawa tun yana matashinsa Mu'azzam kuma dake son ƙwallon har cikin jinin jikinsa bai iya taka kwallon haka ba Su Nasir su yi ta faɗin "Aji da za ka sanya ra'ayin ka a kwallo da kila kai ma watarana ka iya zama Ahmad musa ko mu ji ka a turai ka koma buga kwallo da irin su Muhammad sala" in suka faɗi haka sai ya gwasale su da cewa"Ina meye wani ƙwallo kuma? Malamai ni fa Soja ne, Sojan kasata in sha Allahu." Kwatan kwacin yadda Mu'azzan ke son zama ɗan kwallon kafa kwatan kwacin yadda Mansoor ke son zama Soja, kowanne bawa daman yana da na shi burin da mafarki sai dai daman ba duka mafarkan mu ke zama gaskiya ba wasu suna zama a raye wasu kuma har kuma ga Allah suna matsayin mattatu ne. A komai na Mansoor ya sha bambam da na Mu'azzam a ra'ayi da hallaya Mansoor yana da faɗaa ga zuciya da naci sannan ga riko a cikin kwakwalwarsa har wani waje garesa na musammn kamar blacklist ko sau ɗaya wani abu ya taɓa haɗa ku to ya kulla da kai kenan har gaban Abada. Saɓaanin Mu'azzam ba ruwan shi mai hakuri ne sannan ba shi da fitina shi kuma mai son zaman lafiya ne amman Mansoor bai ƙi gayyar duk ta watse ba, Allah ya sa ma kada a zauna lafiya tun yana ƙaraminsa yan gidan wanzamai suka sa ya fahimci ba nan ne asalinsa ba saboda

Chapter 14 of 26