Babban mgana shi Baban Inna ya san da mganar?
Inna Meri ta ce"Ina zan bari ya sani kasan halin shi da bakar zuciya."
Baba Ɗanjuma ya ce"To ka da ki yi masa zencen, mu bari mu ga abin da ubangiji ya tsara a tsakanin su."
Inna Meri ta ce daman shi yasa ta ki yin zebcen da kowa. Baba Ɗanjuma kuma har Magajiya sai da ta sakar masa mganar Agolan gidansa zai kara jawo masa wani rigiman shi dai bai ce mata komai ba ta yi ta faɗa da bala'a akan abunda ya wuce tuntuni.
Shi ko a bangaren Mansoor ya kasa sukuni sai da ya kira Mu'azzam yana tambayansa ko sun yi waya da Inna? Mu'azzam yace"Eh jiya ma daddare mun yi mgana har ta ce min kwana biyu ba ka zo ba."
Cikin son kara samun tabbaci ya ce" Bayan nan ba ta yi maka wata mgana ba?
Mu'azzam ya ce"Ta yi ta faɗa ne kan bikin da za ta tafi Bauchi ta ce kuma ka zo amman ba ka zo ba."
Aji ya sauke Numfashi kafin ya ce"Daga nan ba ta ce wani abu ba?
Sai Mu'azzam ya fara mamaki kafin ya ce" Shike nan mana."
Aji ya sake cewa"Ka tabbata shike nan? ba ta ce maka ko ta yi wata bakuwa ba?
Mu'azzam ya yi shuru kafin ya ce" A'a gaskiya ba ta faɗa min ba, ko ka ji labarin ta yi wata baƙuwa ne?
Sai kawai Aji yace shikenan daganan ya kashe wayarsa Mu'azzam ya yi ta mamaki tunda kuma ya ji haka a ransa yasan akwai wani abu a kasa ya so ma ya kira Inna ya tambayeta ko ta yi bakuwa ne sai kuma ya sha'afa.
******
Da Sassafe kamar wanda a ka koro sai ga shi ya zo gidan daga morning training yake har kayan ma bai sauya ba tunda dai bai koma gida ba. Sai dai Inna Meri ta gan shi kamar daga sama suna cikin karyawa ita da Walida sai ga shi ya ɗago labule ya shigo.
Dukawa ya yi a kasa ya gaida Inna Meri ta amsa tana faɗin "Idon ka kenan Baban Inna? Sai ya dukar da kai yana faɗin" Inna wasa gare mu, muna ta shiri ne."
Walida ta gaisheshi ya amsa sai ta tashi ta shiga ciki tunda yau ɗin ba su da jarabawa.
Inna ta kalle shi kafin Ta ce"Wasa ai yafi maka sada zumumci Baban Inna."
Kai tsaye ya ce" To ki yi hakuri Inna."
Ta yunkura ta mike tana faɗin"Koko da kosai muka yi bari na zuɓo maka"
Dama yunwa ya ke ji nan ya gyara zama Inna Meri ta zubo masa ya sha Sosai sai da ya ji cikinsa ya cika. Inna Meri na kallansa ta na tausaya masa magidanci kamarsa abinci ma ba ya samun ci sai raɓe raɓe.
Shikuma yana ta jira ya ji ko Inna zw ta yi masa zencen zuwan Mimi sai ya ji ba ta yi ba sai ma ta fara masa faɗan ta gaya masa Babansa yakubu zai aurar da yara har biyu tana so ya shirya su tafi tare, kai tsaye ya ce"Inna ina naga wani lokacin zuwa biki kamar wani mace? Zan dai baki gudummuwa kikai musu Allah ya ba da zaman lafiya in kina neman ɗan rakiya ne ki tafi da Walida mana."
Inna Meri ta aika masa da dakuwa kafin ta ce"Ai ba ka yi kuɗin da za kaki zumunci da dangin Babanka ba, zuwan ka yafi kuɗin da za ka aika muhimmamci."
Cikin shafa sumar kansa da ta taru ya ce"Inna ki yi hakuri na je na gaba tunda shi naga duk kusan sati sai an ce ƴarsa za ta yi aure."
Inna Meri ta girgiza kai tana yar dariya kafin ta ce"Allah ya shirye ka Baban Inna, yana da ƴaƴa mata ne da yawa kuma baya barin su tsawaita karatu shi ya sa yake yawan sha'ani kuma ko wancan sha'anin sai da ya yi min zencen ka ni fa ina jin kunyarsu domin sun nuna min kara su ka bar min kai ka girma a hannuna. Gwggon ka ma yalwa ba ka kara zuwa ka duba ta ba sai dai ka yi musu saƙo Babanka Karimu har hatsari ya samu na yi na yi da kai amman ba ka je ka duba shi rana ɗaya dai Haba"
Kansa na ƙasa ya ce"Inna ban samu zuwa ba a wanchan lokacin ba, amman in sha Allahu zan samu lokaci na leƙa"
Kai tsaye tace" Bauchin fa?
Shima kai tsayen ya ce"Har can zan je Inna ba shike nan ba,"
Inna Meri ta ce"Ba shike nan ba ai ba sau ɗaya ba zumunci za ka riƙe domin su ne makwafin mahaifinka shi ya sa ko yaran nan su Amina ba na barinsu haka ko da yaushe ina tunasar da su su yi zumunci da dangin mahaifiyarasu Mu'azzamu dai ba shi da matsala yana zuwa sosai kaine dai sai a hankali, ina kuma maka faɗan ka gyara domin Allah da kanshi ya tanadi Aljanna ga ma su sada zumumci."
Shi fa ai tunda ya kawo kansa shike nan Sai da Inna ta gama mai wa'azi sannan shi ma ɗin Baba Ɗanjuma ne ya cece shi da ya shigo ɗakin a ranar da yamma ya dawo ya kawo ma Inna kuɗin gudummuwa da kuɗin mota ita kaɗai za ta tafi ta mallam Sidi za ta biya su tafi da yalwa tunda taji sauki sai ya ba ta ishaahen guzuri har Mu'azzam ma ba'a bar shi a baya ba Inna na ya bari Baban Inna ya ba ta kuɗi ya ce shima ya na neman albarka ne.
Walida ta so zuwa suna da jarabawa ita kuma Bintu ranar kanwar Mijinta na aure ta so ta gudu ta bi Inna, Inna Meri ta ce ba in da za ta bi ta ita ba Merin mahaukata ba ne.
Ranar alhamia ta tafi mallam Sidi ta kwana washegari suka tafi Bauchi suna can garin Hajiya ta kirata sai ta gaya mata ba ta gida ta bari in ta dawo sai ta zo har gida ta sameta. Su ba can ciki garin Bauchi Alhaji Yakubu ke zaune da iyalansa yana da rufin asiri tunda yana kasuwancin ne.
Ko a wannan zuwan sai da ya tambayi Mansoor ta ce ya ce yana da buga wasa.
Yana dariya ya ce"Dakyau ai ina bibiyan wasannin shi, wata rana a kasuwa wani abokin kasuwancina Alhaji Ubale na zencensa na ce masa ɗana ne ɗan yayana mai rasuwa ne yana ta mamaki nace masa ya daina mamaki da ya ke ba'a wajen mu ya tashi ba ya na tare dake ne, amman na masa alkwarin duk ranar da ya zo zan kira shi ya gan shi shima yana bibiyan wassanin shi sosai." Inna Meri ta yi saurin cewa"Ai ya ce zai zo in sha Allahu."
Alhaji Yakubu ya ce" Ya kamata saboda yara nan duk ba su san shi ba daga masu auran har ƴan matan" Da ya ke matansa biyu ne kuma suna yawan haihuwan kai da kai kuma Allah bai ba shi ɗa namiji ba sai mata sun kai goma bayan waɗanda ma ya aurar.
Inna Meri na Bauchi aka kirata daga can Argungun aka faɗa mata wani kawunta ya rasu da ke zaune a jega ba ta ko gama cin biki ba ta dawo Gombe ta fara Shirin tafiya Argugun daman Mu'azzam na son garin nan domin Inna Meri ta sha zuwa da shi tun yana yaro yanzu kuma yana son komawa sai dai ba lokaci ga aiki ya sa bai samu zuwa ba, Mansoor shi ya nema ma Inna tashar Golf Yaya Halima ta ce za ta rakata Walida kuma jarabawa Bintu kuma ta kara ɗaura ɗamara Baban Inna na ji ya ce ta zo taje ɗin in ta isa ai ta na jin haka ko sallama ba ta zo ma Inna ba. Amman ta tafi da yan biyunta tunda sun saamu hutu suma ɗin Aji sai da yace ba'a za je da su ba Inna Meri ta ce ita ta ce a haɗo kayansu za ta je da su.
Tafiyar Inna shiyar gida ya sa Hajiya ba ta ganta ba har ƙara kiranta ta yi sai ta gaya mata an mata rashi ta na gida sai dai idan ta dawo, sun rabu akan ta na dawowa za ta neme ta Inna Meri da niyar Sati biyu za ta yi su dawo sai ga shi su ne har wata daya yan'uwa sun hanata dawowa Yaya Halima taji daɗin garin ta share kafa ta bar miji da yara Inna Meri kuma duk da ba ta da ƙananan yara hankalinta ya koma gida, ga Halima tare da ita da su Hussaini su da ba su damu ba dakyar su ka bari ta dawo sai da ta yi kwana talatin da biyar.
Bayan ta dawo hutawa kawai ta yi na kwana biyu ta raba tsaraba ta shirya ta je gidan Hajiya Saboda kada ta ɗauka da gangan taki zuwa sai ta iske ba kowa a gidan Hajiya suna Abuja matar marigayi ta fita takaba Mommy kenan.
Haka ta dawo ba ta ganta ba sai ta yi Tunanin kiranta a waya kuma wayar ba ta shiga ba, ashe a gida Hajiya ta manta wayar ta mace ba chaji tunda har da Baaba Uwani suka tafi wajen kwanansu uku acan za'a yi mganar rabon gado ya sa suka ɓata lokaci ma ma ba su dawo ba.
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
*NA GODE.*
*ZAINAB INUWA(MY ANTY)*
*MARYAM JUMARE*
*NANA HALIMA(MASOYIYA)*
*AISHA ALTO(SISINAH)*
*SURAYYA DEE*
*KUN YI TA JIMARIN YAƊA WANNAN LITTAFIN TUN DAGA RANAR FARKO HAR ZUWA YAU DA SHAFUKAN KYAUTA SUKA ZO ƘARSHE, NA GODE ALLAH YA BAR ZUMUNCI AMIN*
*Tushen labarin ne a littafi na ɗaya, cin uban sabadan yana cikin littafi na biyu har zuwa na uku, akwai soyayya mai tsayawa a zukata bayan dabarwan dake ciki, ga dai Aji ga Mimi shin me yake shiryawa da ya amince da auranta? Ko yana nufin ya yafe ɗin ne? Akwai sauran rina a kaba tabbas, ku ƙara zaɓa ta ina mai ba ku tabbacin ba zan ba ku kunya ba in sha Allahu. Ku yi tururuwan biya domin sai kun cika adadin sannan zamu fara littafi na biyu, daga yau zuwa gobe da jibi in sha Allahu Na gode.*
*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*07030645342*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*
Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.
*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*
Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0
*Page 20*
An raba iya ada din dukiyar da Abi ya mutu ya bari, an kuma raba shi dai dai yadda addini ya hukunta. Tare kuma da malamai da alkalai aka yi rabon a gaban Daddy da yaran duka sai Hajiya har da Yaddiko. Hajiya ma ta samu gida tunda ya bar gidaje da motoci da kuɗi ma su yawa a cikin banki, sannan gidan da Mommy ke ciki ita da Sulaiman suka ci gidan shi kuma ya ce ya bar mata halak malak domin ta cika wasiyar mijinta ta ce za ta cigaba da zama a gidan tun da ga aikinta sannan gefe ɗaya ta ce za ta je kano ta ɗauko ƴaƴan ƴan'uwanta saboda su taya ta zama tunda Inna Ladidi za ta koma gida bayan ta fita takaba.
Kwanan su huɗu ne su ka dawo, Mommy kuma washegari ta bi Jirgi zuwa kano ita da Inna Ladidi za ta raka ta sannan itama ta je gida ta gaida ƴan'uwa da iyaye. Rana ɗaya su ka tafi da Khadi ita ta yi kaduna ita kuma Madiha kwananta uku ne ta bi Jirgi ta koma Lagos Mimi da Hajiya da Daddy da Yaddiko tare sua je kuma tare su ka dawo Gombe gabaɗaya. Ko bayan an gama rabon gadon Mommy ta so ta yi mganar Mimi sai kuma ta fasa a cikin ranta ta kuduri niyar daga kano Gombe za ta sauka sai an san yadda za'ayi daga can. Ba ta ɗauka ma za ta jima a kanon ba sai ga shi ta yi sati biyu daga kanon ne ta biyo Gombe Hajiya ma ba ta san tana tafe ba, tunda ba ta faɗa mata ba ta dai san sun rabu akan cewa daga kanon za ta biyo nan. Mimi kuma ba ta ɗauka zuwan Mommy da wani abu ba,ta ɗauka dai ta biyo ne kafin ta koma Abuja ta kuma ji daɗin zuwan Mommy domin hakan ya bayyana har saman fuskarta.
Zuwan Mommy ya sa Hajiya ta ƙara kiran Inna Meri a waya a nan ne ma take jin labarin ashe ta zo ba su nan Hajiya ta ba ta hakuri ta ce ta bar wayar a gida ne, ba ta je da ita ba amman in ta na gida za ta shigo ko yau da yamman ko zuwa gobe. Ita kuma Inna Meri surutun mutane ne ba ta so sai ta ce ma Hajiya ta bari ita za ta zo, Amman Mommy ta nuna gwara su je da kansu su suke nema bai kamata su tsaya jiran sai ta zo ba. Da haka suka tsara zuwa gidan Wanzamai ba tare da kowa ya sani ba ita kanta Mimi ba su yi mgana da ita ba, ba kuma ta san abin da suke shiryawa ba.
******
_WednesDay 24 May, 2022_
*10:54am.*
Gidan Wanzamai.
Inna Meri na cikin uwar ɗakinta zaune saman sallaya ta idar da sallar Walha sai barci ya kwasheta ba ta sani ba sai dai ta ji muryan Walida na ƙwala mata kira da karfi da yasa ta mike a firgice har wuyan hijabin jikinta na shaketa tunda ta taka shi wajen saurin ta miƙe Cikin tashin hankali Ta ce
"Me ya faru Walida? domin ta ɗauka wani mummunan abu ne ya faru ganin Walida a gabanta tana haki sama sama.
Cikin leken falo ta matso Kusa da Inna Meri Lokaci ɗaya tana faɗin"Inna Bali kika yi Inna" Inna Meri ta maimaita" Baƙi kuma?
Da sigar tambaya sai Walida ta karkace kai kafin ta ce"Hajiya ce fa da wata mata suka zo ga su nan a falo suna jiran ki."
Inna Meri ta yi shuru ta na tunanin wata Hajiyar ce kafin tunaninta ya ba ta Hajiyar Shagamu ce. Ƙirjinta ya amsa ji kake Ras! amman sai ba ta nuna ba illah kallon Walida da ta yi kafin ta ce" Ki kawo musu ruwa." daga haka ta gyara zaman hijabin jikinta ta fita falo, abun ya kara ɗaure mata kai ganin Hajiya da wata mata ƴar gayu sai da ta zauna anan kasan Cafet suka gaisa da Hajiya da matar sannan Hajiya ta kalleta tana faaɗin "Sai kika gan mu ko? Murja ce ta ce gwara mu zo kawai, mahaifiyar Binta ce matar marigayi."
Sai da Hajiyar ta faɗa sannan ta gane ta gani ɗaya ta taɓa yi mata kuma ganin ba na cikin kwanciyar hankali ba ne. Cikin gyaɗa kai ta kalleta kafin ta ce"Allah Sarki Hajiya ya karin hakuri? Allah ya jikan sa da rahma."
Mommy ta amsa da Amin Amin ta na ƙare ma falon kallon tsab tsab daman Walida tun safe ta gyara shi ta share Inna Meri na cikin faɗin da basu wahalar da kansu ba,da ita ta zo gidan Hajiya. Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce"A'a ai muke so gwara mu bi yo sahu, ni na ce ma Hajiya ta bari mu za mu zo da kanmu."
Inna Meri ba ta ce komai ba, tunanin ta ɗaya yanzu magana zai yaɗu acikin gidan da zuwan su Hajiya ba ta son abun mgana.
Walida ta kawo musu Pure water a filet Hajiya ta yi mata sannu ta na tambayan Bintu tace ta na gidanta, daganan ba ta zauna ba sai ta zari hijabi ta fita. Tana fita da ga shashen Magajiya su Gaje da Harira sun yi zaman dirshan suna kuskus suna ganinta sai su ka yi shuru sai ta yi kamar ba ta gansu ba, ta yi ficewarta daga gidan gidan Dije mai waina ta shiga wajen ƙawarta Bahijja.
Mommy ce ta sha ruwa Hajiya kuma ta ce cikinta ya cika sai dai kafin su tashi tafiya, Hajiya mike kafarta ta yi tana faɗin"Meri haka waje ya sauya,gabaɗaya na kasa gane gidan sai da muka yi tambaya bayan kuma mun shigo shima dai gidan duk ya sauya."
Inna Meri ta ce"Eh an yi gyara sosai an raba mana bangare da su Gaje mun koma farko, nan ma ciki an raba bangarena da na Magajiya aikin duk na Baban Inna ne."
Hajiya ta washe baki kafin Ta ce" Masha Allah Allah ya sa albarka." Inna Meri ta amsa da Amin. Kafin shuru na wani lokaci sai can Hajiya ta muskuta kafin Ta ce.
"Meri magana ce mai muhimmanci ke tafe damu, ina fatan megidan na nan?
Inna Meri Ta ce"Gaskiya ya fita amman dai ba nisa ya yi ba ina kyauta ta zaton yana kan hanyar dawowa."
Sai Hajiya ta kalli Mommy kafin ta ce" kin ji Murja, ko za mu jira har ya dawon ne?
Sai Mommy ta ce"Hajiya shi yaron fa?
Sai Hajiya ta kalli Inna Meri lokaci ɗaya tana faɗin"Meri har da shi Mansoor ɗin Murja ke son gani za ta sauke nauyin marigayi ne da ta ɗauka."
Inna Meri ta yi kasaƙe kafin ta ja gauran numfashi Ta ce"To sai dai na kirasa a waya Allah yasa yana kusa." Ta faɗa lokaci ɗaya tana miƙewa Walida ta ke kira sai taji Shuru sai Mommy ta ce in wayarta taje nema gata nan saman Kujera. Sai ta ɗauka ta shiga ciki da yake Inna Meri ba ta da duhun kai ta iya dubo suna ta yi kira.
Baba Ɗanjuma ta fara kira ta tambaye shi ko yana ina ne? ya ce ga shi ma a kofar gida sai ta ce ya kariso suna da baƙi.
Baban Inna kuma kira byu ta yi masa bai dauƙa ba tana shirin ijiye wayar ta fito sai ga kiran shi Muryan shi a Cunkushe ya ce mata ya ɗan kwanta ne, ba ji kiranta daga farko ba Itama Innan muryanta a cushe ta ce ya zo gida tana son ganin shi, bai kawo komai ba ya ɗauka ko wani abu ne ya taso, bai taɓa tunanin wani abu daya danganci yarinyar da sanadinta mafarkinsa ya ruguje ba.
Inna Meri na dawowa falon ta faɗa musu Hajiya ta kira su a waya sai ga Baba Ɗanjuma shi tun a waje ma ya ga mota, Gaje ce ta shigo samun ruwa wajen Magajiya ta ga shigowar su Hajiya shi ne ta je ta kira Harira suna ta tsegumin son sanin su waye suka zo wajen Meri masu kudi haka sun tambayi Magajiya ta ce ita bata sani ba, Walida kuma da ta fito sanin halinta yasa ba su tambayeta ba domin su san ba za ta gaya musu ba. Kuma ganin Baba Ɗanjuma ya shigo kuma ya wuce bangaren Inna Merin da sauri ya sa su ka san tabbas da wani abu. Kuma suna son sanin abin da ke faruwa amman ba hali ita kanta Magajiya sai tunane tunane take yi Hajiyar ne take ganin kamar ta taɓa ganin ta sai dai ta rasa in da ta santa amman acikin ranta tana tunanin kamar akwai wani abu daya danganci zuwan da yarinyar nan mai aiki a gidan tibi ta yi, jikinta na bata kamar taron ya na da alaqa da ita.
Cikin girma da arziki Hajiya suka gaisa da Baba Ɗanjuma yana zauna a kasa kusa da Inna Meri Mommy ma ta sauko ƙasa ta zauna lokaci ɗaya ta gyara zama Inna Meri ce ta faɗa masa matar Marigayi ce shima nan take ya yi mata gaisuwa ta amsa kafin ta ɗora da faɗin" Bisa abin da ya faru shekarun da su ka gabata ne tsakanin yaron ku da ƴar mu Mimi wanda har ya jawo rashin fahimta abubuwa suka faru da ba su yi ma kowa daɗi ba, dalilin haka ya sa sai zumunci ma ya yanke gabaɗaya, saboda kalaman major a kan yaron wajen ku sai dai wallahi tallahi kun ji rantsuwan Musulami Habibi ya rasu ana gobe za mu zo Gambe da niyar ya zo ya baku hakuri ya kuma jemi gafaran Mansoor sai dai Ubangiji bai amince ba yana gangaran mutuwa yana jaddamin wasiyar na nema masa gafara a wajen sa daku iyayensa shi ne naga ya dace na tako da kafata na zo na wakilce sa don girman Allah ku yi hakuri, ku yafe abunda ya faru kuskure ne kuma kowani ɗan adam ba ya wuce kuskuren sa domin tara yake ba mu cika goma ba. Ku duba Allah ku yafe masa tunda ba shi a duniya nan kuma kafin rasuwarsa ya yi nadama matuka har ya so ya nemi gafaran abin da ya faru da kansa."
Mommy ta dakata tana sharan ƙwalla da gefen mayafinta kafin ta cigaba da faɗin.
"Habiba ya cika a gabana sannan da Mimi a bakinsa ku yi hakuri ku yafe masa."
Baba Ɗanjuma ya yi saurin tare ta da faɗin"Haba Hajiya ki daina kuka, wallahi ba komai tun a lokacin mu ba mu riƙe ku a ranmu ba mun yafe Allah ya yafe mana gabaɗaya, shi kuma Allah ya jiƙan sa da rahma ya sa ya huta."
Gabaɗaya su ka amsa da Amin Inna Meri Ta ce"Ai na gaya ma Hajiya tuni wannan ya wuce a wajen mu tuntuni."
Baba Ɗanjuma Ya ce"Kwarai ma kuwa kuskure duka aka samu tun a wancan lokacin, rayuwar duka nawa take ma Allah na tuba? Allah dai ya sa mu dace ko da ba ku zo ba ma Hajiya babu komai."
Hajiya tace"Hakane mun gode kwarai Allah ya bar zumunci Amin."
Mommy kuma kanta na ƙasa Ta ce" Ina son ganin Mansoor domin shima na bashi hakuri." Inna Meri tabce" Yana hanya zai zo in sha Allahu."
Sun yi shuru na wani lokaci sai Baba Ɗanjuma ya miƙe da niyar fita sai Hajiya ta kira shi ya dawo ya zauna.
Mommy ta kallah ta ga kuka take yi sai ta girgiza kai kafin ta ce"Meri tun kwanaki na faɗa miki kafin rasuwar Kabiru ya janye kalamansa kan Mimi ya ce ya amince in har ta na son Mansoor to a aura mata shi saboda farincikinta"
Inna Meri ta yi shuru kafin Ta ce"E, kuma ai tun a lokacin na gaya miki ni ba ni da matsala, in ma da matsala yana wajen Baban inna ne"
Baba Ɗanjuma Ya ce"Gasikiya sai dai a jira a ji ta bakinsa ko ba haka ba Hajiya?
Hajiya tace to shike nan sai a jira ɗin, nan Hajiya ta cigaba da ga ya musu saboda Mansoor har yau Mimi ta kasa kula kowa kuma har gobe yana ranta shi take so farincikinta na tare da Mansoor.
Inna Meri ta yi shuru ba ta yi mgana ba domin ta san halin abin da ta haifa shi kuma Baba Ɗamjuma kai tsaye Ya ce"Dama mu ba muki ta ba, matsalan daga bangaren kune amman tunda ku da kanku kun amince sai ayi mgana da shi Mansoor ɗin sai muji ko yana ra'ayinta har yanzu, mu namu fatan alheri ne kawai."
"Assalamu Alakaimu."
Muryan Mansoor ta katse Baba Ɗajuma da zence da ya kwararo, gabaɗayansu suka ɗaga kai ya na tsaye a kofar ɗakin bayan ya ɗaga labulen ɗakin, sai dai fuskokin da ya gani ne ya sa bai shigo ba.
Biri daman ai ya yi kama da mutum, ya ga mota a kofar gida sannan ya shigo ya ga su Magajiya na binsa da wani kallo ya zo kuma ya yi mummunan gani. Da ga Hajiyar har Mommy ba wacce bai gane ba, shi ya sa ya wani ƙara haɗe rai kamar an aiko masa da sakon mutuwa. Ƙokarin ma komawa da baya ya ke yi Baba Ɗanjuma ya kira sunanshi ya amsa ya kuma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 26